Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

WACE CE NI Book 4 Complete Hausa Novel Document by WACE CE NI Book 4


WACE CE NI Book 4

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 32822



WACE CE NI Book 4

Reading Time: 2 Hours

Added On: 22, Sep 2024

Author: Hafsat Sodangi ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 162.15 kb

File Type: txt

Views: 509+

Download: 581+

Last download: 1 day ago

Description/Story: [6/20, 9:22 PM] Hafsat C Sodangi: WACECE NI?

4

Na
Haj. Hafsat C. Sodangi
(Mrs. Yunus Abdullahi Dabai)






GODIYA
Godiyata har kullum ga Allah take Madaukakin
Sarki, gwani mai hikima cikin dukkan ayukanshi.
Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga
Shugabanmu Annabin karshe, Muhammad (S.A.W)
da Alayenshi da Sahabbanshi da wadanda suka bi
tafarki na gaskiya har zuwa ranar Alkiyama, amin.
Godiya mai dinbin yawa gare ku Makaranta
littafin nan na kusa da na nesa na gode da irin
kulawarku, Allah kuma ya kara zumuncin dake
tsakaninmu ya kuma saka muku da mafificin
sakamako amin summa amin.

TUKUICIN LITTAFIN NAKI NE
Yar uwa rabin jiki, Hajiya Khadija C. Sodangi
(Mrs Nasir Kiru)

SADAUKARWA
Sadaukarwar littafin taku ne makaranta
littattafaina, na nesa da na kusa na gode da irin
kulawar da kuke nunawa rubutuna, na gode.

JINJINA
Jinjinar taku ce.
Rabi'atu Abdul One Muhammad (Adawiyya)
Rabi'atu Barau Potiskum (Amarya)
Rahi'atu Ibrahim Gusau (Rabi)
3

Rabi'atu Bashir Sambo
Rabi'atu Maikudi lafiya
Rabi'atu Muhammad Aliyu

GORO
Goron littafin naki ne yar uwa, aminiya, Hajiya
Lami Nasiru Goshi, na gode da kulawarki.

JINJINAR LITTAFIN NAKA NE MIJINA
Alhaji Yunusa Abdullahi Dabai, babansu Maryam,
Aisha, Yunus da Abdulmajed, Ubangiji Allah ya
saka maka da alhairinsa, amin.

Hakkin Mallaka
Hakkin mallakar littafin na Marubuciyar shi ne;
HAJ. HAFSAT CHINDO SODANGI (Mrs Yunus
Abdullahi Dabai)

GORON NAKI NE
Zuhuriyya Ibrahim Usman Zaria

KINA RAINA
Diyata Hafsat Abubakar Mamadawa

GAISUWAR SADA ZUMUNCI GARE KI
Halima Salihu Kwayakusur Maiduguri, Borno
State.

4

YABO
Yabon naki ne Aisha B. Dahiru
(Mrs Shehu Tijjani)




5

Littattafan SODANGI:

NAGA TA KAINA

ABU NAKA

HATTARA

GARIN BANZA

DAGA KIN GASKIYA

DUK DAYA

DA KAMAR WUYA

YIWA WANI

RABON KWAD0

WACECE NI?

KIFI NA GANINKA...

MAI UWA A GINDIN MURHU...

6

WACECE NI? 4
D uk da ban wani samu isasshen bacci a
cikin daren ba, ga gajiyar wahalar biki ga
rashin bacci da suka hadu suka haddasa min ciwon
jiki mai nukurkusar kashi. Da gari ya waye na yi
kokari na fito bayan na idar da sallah na shiga kicin
na fara shirya abin karyawa saboda Ango da
Amarya da kuma sauran Jama'ar dake gidan. Tunani
sosai nayi don in shirya abin da zan gamsar da
mutane, sai da na dama kunun gyada na shinkafa
nayi alala sannan na shirya potato da corned Beef ga
abubuwan da nayi amfani da su:
(1) Dankalin Turawa manya takwas
(2) Butter cokali takwas
(3) Albasa guda biyu manya
(4) Naman jajjagagge daidai kima.
(5) Kayan kamshi dan madaidaici
(6) Dessert Apple guda biyu manya

Da yake abincin nawa bai wuce na mutum hudu
ba, to ga yanda nayi na sarrafa komai, wanke
dankalin nan nayi sosai ya wanku da kyau ba tare da
na fere shi ba, na ajiye shi wuri mai tsabta sai da ya
bushe sannan na goga mishi butter na dora shi kan
bakin sheet na saka sh1 a oven ya gasu na kusan awa
daya cikin madaidaiciyar wuta sai da naga ya gasu
7

Sannan na ciro su na kwakule cikinshi sai dai na
kiyaye ban lagabar dashi ba ban kuma huda wani
bari ba, na kawo jajjagagren naman nan na hada da
wannan garin dankalin da na kwakwale na hada da
maggi yankakken apple din nan da kayan kamshi na
cakuda shi da albasar da na soya cikin butter tayi
laushi sannan nayi ta cusawa cikin dankalin nan sai
da na gama maida shi ciki gaba daya na sake
sanyawa a oven ya yi ta gasuwa kafin na sake ciro
shi na sanya shi cikin kwanon da na tanada mai
tsabta.
Ina cikin kokarin dora ruwan zafin da na tafasa
cikin flask sai ga Baba Talatu ta shigo sannu da aiki
uwar dakina, na cc yauwa Baba kin shigo? Ta ce
mun ch, ta kuma kara marsowa kusa dani alamnar
wata magana zata gaya min, don haka na kara bata
hankalina. "Kinga idon wannan yarinyar kuwa?
ani mirsisi da ita ni nace anya ma ihun nan da
take tayi jiya na kama hannunne kuwa da gaske?
Banga alamar ta kai budurcin nan ba." Na ce "Baba"
Ta ce "Na'am." Na ce "Mu bar wannan magana." Ta
ce "To." Ta shiga taya ni kintsa wurin zuwa can sai
na sake jin ta ce min "in banga maigidan yayi
wankin kayan shimfida ba irin na wancan karnon,
anya budurcin nan..Nayi maza na katse ta na ce
"Baba Talatu daina yi min wannan maganar, tana
fadar min da gaba, don bana son jin ta wannan abin

8

da ya shafe su ne ita dashi bai shafe ni ba." Daga
bayana na ji muryar Yaya Almu yana cewa,
"menene bai shafe ki ba? Baba Talatu tayi maza ta
fita ni kuwa na soma gaishe shi bai wan1 amsa ba ya
kara matsowa gab da jikina, me zan samu Rabi? Na
sunkuyar da kaina don bana son kallon fuskarshi, na
ce duk abin da kake so akwai, ya ce 'to in dai haka
dan fara bani bakinki in ji kwananshi, in ji
laushin la6 6anki, nan da nan wani abu ya tokare ni
a zuci har ban san lokacin 'da na bude baki na ce
mishi, uh'uh in baka ji wadannan ba ai ka ji
wasu..bai bari na karasa ba ya ce mun kul, kar ki
rinka irin wannan maganar in ina tare dake ina tare
dake in bana tare dake kar ki yarda zuciyarki ta raya
miki komai ki dai yarda kawai a duk inda nake ina
kewarki ina kuma son ganinki a gefena, na ce haka
ne.
Na kammala shirya komai kan tire na dauko na
barwa Yaya Almu wanda zai taimake ni dashi
juyowan da zanyi sai kawai naga Lailatu tana
lekowa ta matsin kofarta tana kallon abin da ke
faruwa tsakanina da Yaya Almu. Na yi kamar ban
ga abin da take yi ba, na wuce naje na shirya komai
a falon shi na sake dawowa na shiga dakin nata
nace mata Amarya ina kwana? Ta ce min lafiya,
amma dai sunana Lailatu, na yi kamar ban ji ta ba

9
na ce mata ki zo falo maigidan yana jiranmu, na
juya na fita na barta.
Mun zauna muna karyawa dukanmu muna kuma
hira dukanmu saboda kokarin da Yayan ya yi wajen
ganin ya tsoma kowa cikin maganar tashi, da aka
natsu sai ya kalle ni ya ce mun Rabi ga Lailatu nan
na sani kishiyarki ce, to amma zan so ki maida ita
yar uwa ki yarda cewar taki ce zaki yi mu'amalla da
ita bisa adalci ba don kowa ba sai don ni, tunda kin
san ni na kawo ta na kuma san za kı 1ya y1 min
adalcin maida duk wani abu nawa ya zama naki ko
da kuwa ba akan son ranki yazo ba, saboda kin san
duk wani abin da ya shigo gidan nan arzikinki yazo
ci in kuma mallakarshi nayi to na ki ne."
Cikin natsuwa ba tare da zuciyata ta raya komai
ba, na ce mishi haka ne, sai kuma ya juya wajen
Lailatu ya ce mata, ke Lailatu ga Rabi nan matata ce
ko babu aure tsakanina da ita kuma 'yar uwata ce na
kuma san duk yanda kishi yakai da zafi cikin
zuciyar ta a ifin halinta da na sani da kuma irin
tarbiyar da aka yi mata zata yi iya kokarinta wajen
ganin tayi miki adalci, to ki bata hadin kai ki bata
girman da ya dace da ita don ina bukatar ganin kun
zauna lafiya kun samu fahimtar juna a tsakaninku.
Wannan shi ne sha'awata da burina game da mata
biyu, ke Rabi kinji abin da na ce? Na ce mishi ch,

10

naji Allah ya taya ka riko, ya yi maza ya ce min
"amin, Lailatu dai bata ce komai ba har na fita.
Zuwa can wajen karfee sha biyu da rabi bayan
fitar Yaya Almu, ina falona ni da Baba Talatu ina
kuma hango duk abin da tsakar gida ke ciki, yayin
da Lailatu ke falonta tana kallo sai ga Umma
Karama da Hajiya Hairan sun shigo gida da sauri na
fito ina yi musu sannu da zuwa na kuma jagorance
su don in kaisu dakina duk da dai nasan Umma
Karama bata taba takowa tazo gidan saboda ni ba,
to amma sanin da nayi cewar duk bakon da yazo
gidanmu matukar ya fara ganin Umma to ko ba
wajenta yazo ba to wurinta zata fara sauke shi ta
bashi ruwa da abinci kafin tasa a kai shi wurin
wanda yazo, to balle Umma Karama duk yanda
takai da kina dolenta ni 'yarta ce, kan idonta aka
haife ni ko babu wata alaka tsakanina da Baba ta
dalilin Umma kawai ita uwata ce, balle kuma inta
juya ta wurin Baba ni jikarta ce har yanzu kumna
surukarta matar dan mijinta, amma bata şhiga dakin
nawa ba sai ta ce min na rako Hairan ne tazo taga
dakin Amarya, bari mu fito tukuna. Cikin murmushı
na ce mata to, na shiga kicin na shirya abinci na
bisu dashi zuwa dakin Lailatu na shiga na same ta
tana cewa, in ana zancen aure ai babu maganar
Zumunci a ciki dukanku daya ne dukanku daidai
kuke in ta dauro ma kwanan nan sai ki kwace shi

11

tunda ke kam ai matar haihuwa ce kadan ya rage
banyi 6ari ba, nayi maza na shanye bugun da
zuciyata tayi nayi sallama suka amsa na shiga na kai
musu abin da na shiryo musu na kuma gaishe su har
na tsaya ina tambayar Umma, Umma daga Legos ku
ke ne? Ta ce a'a a satin nan ne dai zan tafi na ce ai,
na tashi na tafi nawa wurin da suka gama abin da
zasu yi kuwa daga tsakar gida ta yi mun sallama
wata kilama da ban ga fitowarsu ba da tafiyarsu
kawai suka yi ba tare da sunyi min sallamar ba,
Baba Talatu ta kalle ni ta ce tafdijam, wannan mata
da rashin mutunci take in ban da Hajiya ta samu da
ba a san irin tsiyar da ta
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download WACE CE NI Book 4

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album