Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*DEEN*


(The heartbreak💔)

An amazing love story💘



Story written by Ashaanty love💖

Marubuciyar
_AUREN KWANGILA_



_Am back again! Alhamdullilah!🧚🏻‍♀️_




*001*




_"So let me know, if you no wan do again, I no go disturb you, I no go hold you!... Let me know uwo uwo if you no wan do again, I no go disturb you, I no go hold you... But no call me back oo, no call me backkk! When you see sey I dey with another person, baby no call me back oo, no call me baaaack when you see sey I dey with another gele..."_

Kpaaam! Kpaaam!! Kpaaam!!! Aka sake bubbuga kofar toilet din kamar za'a 6allata

Inaa? Batama San anayi ba saima qara volume din muryarta datayi tana bin waqar dake tashi a earphones din kunnenta
_"Even if you call e no go connect, cos I no go dey, I no go dey make you forget, come another day..."_ tafada tana lallauye jikinta kamar wata macijiya tana shashafa jikinta dake lullu6e da kumfa cikin wani irin salo

Qara bubbugo kofar akayi da wani mahaukacin qarfi wanda saida taji qarar dukda earphones din kanta

Saurin waigawa tayi ta kalli kofar tana zame earphones din kanta a lokaci daya

"Wai don ubanki bazaki fitoba!!" Aka fada daga waje ana qara bubbugo qofar

Wara manyan idanuwanta tayi kamar zasu fado daga raminsu sannan tashiga dauraye jikinta cikin rawar jiki

*"ZAINAB!"* aka sake kwala kira daga waje, daga ji kasan mammalakin muryar amatuqar fusace yake

"Na... Na'am mummy, wlh yanzu zan...fito" tafada cikin rawar murya tana jawo towel dake rataye a hanger ta daura ba don ta ida dauraye jikinta ba ta sauko daga bathtub din ta nufi kofar cikin 6arin jiki

Kallon kofar take a tsorace tama kasa kai hannu ta bude saboda tsoro

"Wai bazaki fitoba?!" Aka sake fadi cikin tsawa wanda har saida ta zabura

Hannu na rawa ta zare sakatar kofar tana yin saitin gudu

Banko kofar tayi da karfi itama tayo waje aguje tana callara ihu cikin zazzaqar muryarta

Mummy datayi baya baya saboda bangajeta da Zainab tayi tayi saurin dafa wani qarfe dake gefe wanda ba don shi ba da tuni tajita qasa

Zainab kau tana fitowa, waje tayi ido rufe tana sake fasa qara tana kiran sunan Daddy

Bata damu da abinda ke jikinta ba ta sauka qasa da gudu hannu dafe da guntun towel din jikinta ta ratsa yan aikin dake falo suna karakaina

Duk dakatawa da abinda suke sukayi suka juyo atsorace suka bi *MADAM* da kallo cike da alhinin meya biyota

Basu qarasa tunanin zucinsu ba suka samu amsa don *HAJIYA* ce sukaga itama tayo qasa cikin gudu gudu sauri sauri, cable din chaza a hannunta tana kwala kiran Zainab ganin haka zata fita waje

Saurin sunsukuya kai sukayi hartazo ta ratsasu itama tafice sannan suka dago suna girgiza kai na takaicin halin *ZAINAB*

Zainab kau haka ta ratsa ma'aikata dake harabar gidan cikin gudunta wanda hakan yasa duk cinyoyinta suka fito waje, ma'aikatan sai binta da kallo suke amma ita ko ajikinta, itadai burinta ta cinma part din daddy kafin mummy ta kamata don tana jinta abayanta

Ganin mummy ta fito yasa dukkan ma'aikatan dasuka bi Zainab da kallo saurin kame Kansu suna gaidata cikin girmamawa

Babu wanda ta ko kalla sai nufar part din daddy datayi kamar zata tashi sama


Zaune yake yayi balancing a kan wata lumtsetsiyar kujera yayi bake bake yana kallon abinda managern shi ke nuna mashi a laptop

"Daddy! Wayyo Allah nashiga uku!" Suka tsinkayi muryar Zainab hakan yasa duk suka dago alokaci daya suna kallon kofar shigowa

Banko kofar akayi, sai gata ta dirko kamar wacce aka tillo

Kafin kiftawar ido harta qaraso gaban Daddy ta danneshi tana qara cikwikwiyeshi

Iya rudewa Daddy ya rude don sosai take kurma ihu gashi taqi bari ma yatashi zaune bare ya tambayi abinda ke faruwa, tawani qanqameshi tana ihu kamar wacce ake yankawa


Manager kau tsaye yayi agefe yana Kare mata kallo qasa qasa yana lasar le6e ganin yadda duk rabin fresh boobs dinta ke waje ga santala santalan jajjayen cinyoyi mallam

Shigowar mummy yasashi saurin shiga taitayinshi yayi qasa da kai

Ganin shigowar mummy yaqara volume din ihun Zainab tana qara maqalqaleshi cikin 6arin jiki

Sai a sannan shima Daddy yasan meke faruwa hakan yasashi dagowa ya zubamata idanu cikin fushi

Kallon da mummy tayiwa manager yasashi saurin daukar laptop din gaban Daddy ya rufe ya kwashe tarkacenshi yayi musu bankwana cikin girmamawa yayi waje

Fitarshi keda wuya mummy tayo kansu Daddy gadan gadan wanda hakan yasa Zainab sakin wata mahaukaciyar qara ta cusa kanta a qirjin Daddy jikinta na rawa

Ganin hakan yasa Daddy maidata bayanshi yayimata tsakani da mummy yana kallon mummy cikin huci

Mummy kau mazuranshi da siracinshi be hanata qoqarin jawo Zainab dake la6e a bayanshi ba

Qara kareta yayi yana riqo hannun mummy yafara magana cikin 6acin rai
"Wai Maimuna meke damun kwalwarki ne?!"

"Hauka ke damunta! Nace hauka nake, wlh yau babu mai hanani illata wannan shashashar anan!" Tafada tana qara yunkurin kamo Zainab dake bayan Daddy tana kuka sosai

"Saiki illata ta din! Nace ki illatata! Wai Maimuna kanki daya kau? Kibiyo Yar qaramar yarinya da gudu da wannan lafcecciyar wayar a hannu, nufinki me to? Badai nufinki akanta zaki dora wannan tsinnaniyar wayar ba?" Yafada rai 6ace

"Qaramar yarinya? Did you just called Zainab yarinya? Macen dake cikin shekara ta ashirin da daya? 21 ba 12 ba! Ace batasan daidai da rashin daidai ba? Bata iya ware fari da baqi? Kaikuma bakada aiki sai kareta? Bakada aiki sai lallata yarka da kanka!" Tafada cikin tsananin 6acin rai hawaye na kawomata

"Yanzu me tayi kuma dazaki biyota dagudu kamar wata qaramar yarinya riqe da wannan uwar bulaliyar kamar ta bugun jakki? Anya kinada tausayi? Yanzu da kin samu riqeta da zubamata ita zakiyi ko? Don rashin imani irin naki, wlh ba don agida kika haihu ba kuma kuna kama da jewel da wlh nace ke ba uwarta bace, 'ya guda tilo da Allah yabamu duniya da lahira shine zaki kashemana ita? Inbanda abinki duka nawa take dazaki dinga addabar rayuwarta haka? To wlh baniso, banaso! Karki sake min haka don ban hada diyata da kowaba kuma zan iya yin komai akanta, idan ke baki sonta to ni inason abuna" ya qarashe yana huci sosai

Mummy da tun lokacin daya fara zuba ta kafeshi da idanunta dake digar hawaye ta sa bayan hannunta ta share hawayenta ta saki wayar chazar dake hannunta ta juya tanufi hanyar fita afusace ta fita tana rufo qofar da qarfi

Wata wawiyar Ajiyar zuciya suka sauke mai nauyi bayan sun rakata da kallo

Komawa da baya Zainab tayi tafada kan kujera tana maida numfashi ahankali tareda furzo wata zazzafar iska daga baki

Daddy da duk jikinshi yayi sanyi ganin yanayin da mummy ta fita ya nemi guri kusada Zainab ya zauna ya miqa hannu ya jawota jikinshi

"Baby na, hope dai kina lfy?" Yafada cikin tsantsar kulawa

Fizge jikinta tayi daga riqonshi sannan tafara magana cikeda tsiwa
"Inafa lfy Dad? Ni wlh Allah yasani wannan Matar ba qaramin takurawa rayuwata tayi ba, can you imagine wai dukana zatayi? Yanzu data samu damar kamani fa dukana zatayi, am almost 21 amma ban girmi dukaba a gidanmu, imagine" taqarashe tana girgiza Kai fuska a yatsine

Qara rungumota Daddy yayi cikin sigar rarrashi yace
"Shiiii... Ya Isa haka, nayi maki alqawari zanyiwa tufkar hanci"

Cikeda rashin kunya da tsantsar sangarta tace
"Yaushe? Tun yaushe kake cewa haka amma abu ya gagara? Ni wlh haryanzu ban yarda wannan matar uwata ce ba, matarda kwata kwata bata qaunata? Ta tsani ta ganni cikin walwala da annushuwa, duk hanyar datasan zatabi domin daqile farincikina tasanshi, komai na duniyar nan idan nayi to ba daidai bane, tasamin ido tasamin hanci da baki, kai wlh nagaji, ace agidanku bakada freedom? A matsayina na diyar *Alh. Farouq Dan faranshi* diyarshi daya tilo ace banida freedom? Gasu kucakan friends dina wanda ko kwatan arziqinmu basu dashi suna life dinsu yadda sukaga dama, suna living free live babu takura, saini daddy? Saini the whole *ZAINAB FAROUQ DAN FARANSHI?*" ta qarashe zancen tana sakin kukan ta6ara

Qara rungumeta yayi sosai yanajin kukanta na ta6a Mashi zuciya sosai

"It ok Darling, Dan Allah ki daina kukan nan kar yajamaki wani ciwon, insha Allah zanyiwa tufkar hanci ok?"

"Till when Dad? Nace ka kaini abroad na qarashe karatuna ka qiya, ka biye mata kun Sani a wannan Yar iskar makarantar da duk tarin yan jagaliya ke ciki, kai shikenan duk abinda mummy tace saika biyemata, da farko ka yarda zaka kaini UK karatu amma daga ta janyeka daki tayimaka karatu saika chanza magana, wai Umaru Musa Yar adu'a, wai kamar ni a UMYAU, mtcheew!" Taja tsaki cikeda rashin kunya

Ajiyar zuciya Daddy ya sauke cikin rashin sanin tacewa saikuma can yace
"Yanzu dai it ok, banason ganinki a 6acin rai wlh, hankalina tashi yake, and batun karatu abroad bawai don mummynki ta nuna batasoba yasa nafasa turaki canba, kawai baxan iya jurar zama na tsawon wasu lokutaba batareda na sanyaki a ido ba, Zainab kema kinsan ina qaunarki sosai banason ko quda ya ta6a min ke, kece rayuwata kece fitilata, ke kadai zan Kalla naji sanyi a zuciyata, be kamata kina tadamin hankali da fushinki ba, am sorry uhm? Insha Allah zan tabbatar kinsamu freedom dakike buqata, uhm?" Yafada yana qara tausa murya

Zainab da tunda yafara magana tayo gaba da baki cikin sangarta tace
"To daddy, yawuce amma please kayi warning dinta ta sakarmin mara nayi fitsari"

Dariyar jindadi Daddy yayi yace
"Ki kwantar da hankalin ki ok? Insha Allah zanwa tufkar hanci... Yanzu kije kisaka kaya kinga towel kawai ke jikinki, ga gashin ki ajiqe halan baki dade da fitowa daga wanka ba?"

"To Ai daddy fitowar kenan, kawai ina cikin wanka naji ana bubbuga kofa kamar za'a 6alla, wai _Don ubanki bazaki fitaba_ inajin hakan nasan muguntar ta motso kenan shiyasa ina samu na bude na arto aguje" taqarashe tana kyalkyala dariya


Shima daddy biyemata yayi shima yana kyakyata dariyar sannan yace
"Maimuna? Ai halinta sai ita, yanzu dai rabu daita Babyna ki tashi kije kisa kaya kar sanyi ya kamamin ke"

Kwalalo idanu tayi tana cewa
"Inje ina insa kaya? Ca6! Sokake nakai kaina da kaina taji dadin farfesuna bare dama ka qara kunnata? Ca6!" Ta qarashe tana rungume hannayenta a qirji ta koma ta jingina da kujera tana karkada kaffafu

"To yanzu ya za'ayi?"

"Kawai kaimin shopping din kayan dazansa online don daga nanma school nayi don babu tsotsan dazai zaunar dani"

Murmushi Daddy yayi yana girgiza kai sannan ya dauki daya daga cikin wayoyinshi dake kan stool din gefen kujerar dayake kai zaiyi yadda tace

Fitt... Ta fige wayar daga hannunshi tana cewa
"Ni zanyi, kana iya yimin wanda bemun ba" tafada hankalinta nakan wayar

Maimakon yaji haushi saima murmushi daya saki yana girgiza kai

Saida tagama danne dannenta sannan ta cilla wayar a dayar kujerar dake gefenta ta miqe daga ita sai guntun towel din tana miqa mai tafe da hamma babu ko kare baki🤦‍♀?

"Daddy yunwa" tafada kamar zatayi kuka

Tashi shima yayi yana cewa
"Muje ga abinci can dining ba'ama dade da kawowaba ko budewa banyiba"

Binshi tayi tana so6are baki

Shi da kanshi yayi serving dinta ya dinga bata sai zubamashi shagwa6a da ta6ara take shikuma yana biyemata

Koda suka kammala har an kawo kayan datayi shopping

Ledar kayan daddy ya bata ta fizge tanufi sama da gudu gudu tsalle tsalle

Binta da kallo yayi sannan ya girgiza kai yana murmushi, yarintar diyarshi na qara burgeshi😒

Saida yaga hayewarta saman sannan shima yajuya yafita don zuwa lalla6o Yar matarshi don yasan haryanzu tana can tana kumburi



Saida tadauki fin awa asaman sannan tafito

Kallo daya zakayi mata kafara tantamar anya musulmace?

Sanye take da yellow din top ta roba mai dogon hannu rigar ta mugun lafe a fatarta har ana hango shatin bra dinta

Ta cusa rigar cikin high waist red skinny trouser dinta taci zanzaro, wandon yayi mugun dameta gashi iyakarshi idon kafa
Sai Ta Dora Farar After Mai Adon Red Stones Akai

tasha baby shoes red sai dan siririn yalolon gyale shima jaa data yafama kai wanda ana hangen tulin gashinta ta gyallen don shara2 ne sosai

Fuskarnan tasha heavy makeup sai shining take, hannunta daya rataye da wata guntuwar jar side bag dayan kuma riqeda faskekiyar wayarta


_yes! Am the princess of the sacred kingdom who rule the life and deathhh_

_am the Queen of the ocean who shines through the rays_

_am the fairly girl in the fairly tale of wonderlandddd_

_so keep calm... Cos the ruling is mineee_

Da wannan waqar ta sauko qasa ta nufi hanyar waje, bata ko damu da rashin ganin daddynba a falon ta fice

Tun kafin ta qaraso drivernta yataso da gudun tsiya yazo ya budemata kofa

Da waqarta ta iso motar, bata amsa gaisuwar da Bala driver kemata ba sai antayen matsiyacin kallon datayi mashi ta shige motar

Maidawa yayi yarufe ahankali sannan yazagaya dagudu ya bude mazauninshi

Ganin hakan yasa security saurin wangale musu tangamemen gate din, suka so suka gittashi suka fice yana daga masu hannu...✍️

Ya kukaga kafcen😎


Yawan comments dinku zaiyi determine cigaban littafin, make me go gaga with your comments yadda zan zubomuku flows of updates💃


Ummin fasihu🧚🏻‍♀?
8/2/21, 9:31 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂️🙍🏻‍♂?*
(The heartbreak💔)

An amazing love story💘

Story written by Ashaanty love💖



*002*




"Haba Maimuna? Be kamata akan qaramin abu kizo kina dacin rai ba, idan kika duba duka nawa Zainab din take? Kamata yayi ki dinga mata uzuri akan duk abinda take, nan gaba ko ance tayi baxatayi ba, kowa da kalar quruciyarshi, don Allah ki dinga dagama yarinyarnan qafa kinji?" Ya qarashe cikin sigar rarrashi

Ajiyar zuciya mummy ta sauke bayan ta gama hadiyar qululun takaicin daya tokare mata wuya tace
"Yanzu alhaji laifine don uwa ta kwa6i yarta? Karka manta fa Zainab macece, ko babu komai aure zatayi watarana, yanzu a tunaninka wa zai iya tolerating din nonsense dinta? Yarinya ace kwata kwata bataji? Koda yaushe abinda taga dama shi takeyi? Bata san daidai da akasinshi ba amma kai a matsayin wadda xaka tsawatar mata bakada aiki sai tunzurata? Wannan a tunaninka soyayya ce? Wannan ba soyayya bace ba alhaji, wannan salon sangarci ne da 6ata tarbiya, kai kullum gani kke kamar na tsaneta ne har cewa kake da ba gida na haihu ba da kace ba 'yata bace, yanzu tsawatarwa yaro yazama laifi. Idan banso Zainab ba amatsayin ta na 'ya talin qwal da Allah yabani was zanso? Inasonta kwatankwacin yadda kake ganin kana sonta koma fiye da hakan amma hakan baya nufin zan barta ta lallace kamar batada mafadi, karka manta bakin da karya kewa danta wasa dashi watarana dashi take cizonshi idan yayi ba daidai ba"

Zama yayi kusada ita ya rungumo kafadarta yace
"To shikenan zan kiyaye, ki saki fuskar hakanan, ni wlh tur6una fuskar ne baniso, indai baby ce zan mata magana bazata qaraba"

Dan ta6e baki mummy kawai tayi batareda tace komaiba

"Smile mana" yafada yana leqen fuskarta

Dauke kai tayi saikuma ta tashi daga zaunen datake daga gefen gado tace
"Yanzu muje kayi break din" tafada fuska babu walwala

Tashi shima yayi yace
"To da girman kujeranki, Ai yadda kika ce hakan za'ayi gimbiya" yafada yana dariya

Itadai gaba tayi don she's not in the mood


******


Danno kai qossashiyar motarsu Zainab tayi cikin harabar makarantar.

Tun shigowar motar yan tsirarun mutanen dake wajen suka karkatar da hankalinsu gareta don duk yadda kaso resisting din motar bazaka iyaba saboda daukar idon datake


Ahankali ta qarasa inda ake parka sauran mottocin ta samu wuri itama ta parka

Da sauri Bala ya bude murfin gefenshi ya sauko sannan ya zagaya ta dayan bangaren inda take yasa hannu ya bude mata murfin kofar

Zaune take ta dora kafa daya kan daya tana daddana waya tana humming waqa ahankali

Jin an bude kofar yasata tsayar da abinda take ta kalli driver dake tsaye still riqeda murfin ayatsine sannan ta watsar

Saida ta mula tasha iska sannan ta dauki guntuwar bag dinta ta bude taciro wani bubble gum ta 6are ta jefa abaki sannan ta zaro sunglasses dinta ta toshe idanu sannan tafara yunkurin fitowa


Ganin hakan yasa Bala qara ja baya sosai cikin girmamawa, ziro kafa daya tayi saida taja lokaci sannan ta ida biyota tafito cikin salon qasaita


Kamar yadda sukayi tsammani ita dince don tun shigowar motar suka ayyana itace.

Mafi yawa acikinsu tsaki sukaja suna kauda kai most especially yanmatan dake wajen don duk sadda ta 6illo sai sun raina Kansu da wankansu, duk yadda suka dau wanka na kece raini da jan hankalin mutane da tazo zata sirar masu dan guntun hayaqin Kansu, abin na matuqar 6atamusu rai most especially idan sunga yadda hankalin maxa ke karkata kacokam zuwa kanta

Yanmata sunsha 6atawa da samarinsu akanta don data 6illo kowanne saurayi shagala yake da kallonta yama mance da yana tareda wata

Gyara zaman yalolon gyalen kanta tayi ta miqama drivern jakkarta batareda ta kalleshi ba sannan tafara tafiya cikin salonta na catwalk tana taunar chewing gum din bakinta

Nanfa idanu sukayi mata caa kamar zasu cinyeta, kowanne ya saki baki da hanci da idanu yana kallonta yayinda yawancin maxan wurin ke hadiyar Yawu ganin yadda albarkatun jikinta motsawa cikin tafiyarta

Itakau ko ajikinta don tasaba and it gives her joy, babu abinda tafiso kamar ta dauki hankalin mutane, datazo waje asan tazo hakan yasa kullum da kalar shigar dazatayi don nunamasu eh fa wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa

Duk abubbuwan dake faruwa akanta a school din tasani, tasan yadda yanmata ke fada da samarinsu akanta, tasan yadda ta tsone masu ido, tasan yadda take gwara kan students da lecturers da salonta

Hakan ke qara fasa kanta taji tafi kowa kuma tana iya taka kowa

Watanta hudu da joining din school din amma tayi sunan da ko yau kazo saika San da zamanta don ko shedanun shigarta besa kasanta xaka santa don rashin mutuncinta don ta qware a rashin mutunci da wulaqanci shiyasa kusan kowa ke shayinta don idan ta takaka ta taka banza don ubanta tsaye yake akanta sosai


Daga nesa wasu yanmata hudu dasuma kowacce da shigar diban albarkan ta suka nufota suna dan sakarmata murmushi a yangace

Dan yatsine fuska tayi tana daga girarta daya datasha shaped jagira ta sauke

Saida suka qaraso sannan suka fara bata light hug daya bayan daya kowacce da abinda take fadi

"Hey!"

"Hyy!"

"Hello!"

"Xupp!"

Saida suka gama sannan tadan motsa baki a yangance tace
"How you?"

Duk amsa mata sukayi da fine suna tambayarta ya ta kwana

Juyawa tayi ta miqoma Bala dake bayanta riqeda jakkarta hannu

Da sauri yabata yana mata kirari sannan ya gaida yanmatan wanda qawayene ga gogar taku suka amsa dakyar

Da hannu tayi mashi nuni da zai iya tafiya hakan yasa yay musu bankwana sannan yajuya yatafi

Rataya jakkar tayi a kafada sannan ta dago ta kalli friends dinta dasuma sai motsa baki suke kamar ita da alamu dai suma chewing gum din sukeci

"Muje ko?" Tafada tana fara tafiya suma sai suka motsa suka jero su biyar suna tafe suna Yar firarsu da classic girls


Duk binsu da na mujiya akayi, masu Allah wadai nayi masu kushewa nayi masu yabawa nayi, masu ji dama su nayi.




"Kaiiii! Baabaa kalli can" inji wani yana qara kafesu da dissashin idanunshi

Wanda aka kira da baabaa din dake zaune kan booth din wata baqar mota wanda kallo daya xaka Mashi kasan tattacen dan iskane shima, yace

"Manta kawai, Ai na rigaka ganinsu yafada yana jan sigarin hannunshi idanunshi still akansu

"Kai baabaa alqur'an babes dinnan akwai kayan ruwa, kullum saisun sa dau sautina ya dau sauti" inji wani mai qaton baki, le6en duk sun dafe don zuqe2

Na ukun yace
"Ba doleba? Kajinne dagani zasuyi romo, wlh nima kullum sai sun kunnani"

Na hudun yace
"Babu kamar wancan mai yellow da red din, duk tafisu komai, Oga dakai kadai ta dace yasin"

Wani kafirin murmushin gefen baki nakan motar yayi yana qara jan cigarette dinshi batareda yace komaiba saima kafama kugun Zainab idanu dayayi kasancewar harsun gittasu

Na farkon yace
"Oga nidai yau abani izini in tashi yanmatan nan hakanan, kwalelen yayi yawa"

"Kana haukane Alex? Ka manta yadda take yaga duk wanda ya taremata gaba?" Inji na ukun

"Ai gaba kuma da gabanta gandu, mu munfi qarfin yaga"

Na biyun yace
"Ga yamashi dai Alex yaga Ai mune nan zamu yagasu kai bama yagawa ba saidai mu farka mutum dan kaza kazanshi" yafada yana gatsine irinna qaurayen nan

Alex ya kalli nakan motar wanda da alamu dai ogansu ne yace
"Oga kabani izini na kawoma ita har makwancinka"

Sai a sannan ogan ya dauke idanunshi daga Kansu zee dasukayi nisa ya kalli alex din sannan yadanyi wannan dan iskan murmushin na dazu da alamu dai shima miskilin kanshi ne sannan ya motsa baki dakyar yace
"Nabaka"

Kamar kau jira yake sai kawai ya nufesu cikin tafiyarshi ta bouncing suka bishi da idanu


Su Zee basusan sunayiba suna tafe ne suna firarsu sai gani sukai ansha gabansu

Hakan yasasu dakatawa suna kallonshi a dage

Ganin abinda ke shirin faruwa yasa mutane fara dan matsowa most especially wadanda suke acan nesa don sunsan wani show din za'ayi yau don anma dan jima ba'ayi show ba don kowa tsoron tunkararta yake don sunsan hakan ba riba

Gashi sunga daya daga cikin yaran MASTER ne wanda shima yayi qaurin suna a makarantar hakan yasasu qara matsowa don kashe kwalkwatar idanunsu


"Yane chicks? Ya yau?" Yafada yana pocketing din hannayen shi tareda karkacewa gefe daya

Anan ma babu wanda ya amsa mashi saidai da alama su qawayen zee sun dan sha jinin jikinsu sanin wanda ke gabansu itakau zee hankalinta nakan wayar hannunta tana taunar chewing gum tana qas qas dashi

"So batareda 6atamuku lokaci ba kuma na 6ata nau, dama big boss ne dama yagani kuma ya kyasa, yakuma bani kwangilar kawo muku wannan gara6asar wanda ba kowa keda sa'ar samunta ba, hasalima yanmata ke kawo Kansu gareshi badai ya nema ba amma dayake Ku sipeshial (special) ne shiyasa ya turoni da kanshi don tashin Ku musanmman wannan sarauniyar kyau din" yafada yana kallon zee da da alamu bata Masan me yake cewa ba yana dan lasar bussashen lower lip dinshi

"Ya? Mutafi ko? Gayacan yana jira, kunsan boss baya jira" yasake fada yana dake babbakewa yana dan jujjuyawa

Har yanzu babu wanda yace komai, saima basarwa

Please Login or Register in order to submit comment