You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
ta tsallen murna tana ihu
Dakyar dai takai kanta bakin motar tashige ciki fuskarta a washe
Komawa tayi cikin kujerar motar ta lafe ta dora hannayenta saitin zuciya tana sauke numfashi ahankali
Ita kadai tasan yadda takeji, farinciki takeji marar musaltawa, farincikin da rabon da taji irin shi harta manta
Lumshe idanunta tayi broad smile shimfide a fuskarta Deen nayi mata gizo a idanu
Tanajin tashin Motarsu dakuma fara tafiyar ta, ahankali ta bude bakinta cikin rada tace
_bye ruhiiβ€οΈ_
Saida ya tabbatar sun tafi sannan shima ya tashi ya hada tarkacenshi shima yafito
Cikin sa'a yana fitowa wata napep tazo wucewa ya tareta sukayi ciniki ya hau suma suka lula
ππππππππππ
_first let me tell you_
_I cannot wait to see you π_
_you're the treasureοΏ½? I've been waiting for ππ_
_Did you know? Did you know?_
_how much I really need you?_
_I dey pray for the day when_
_I can finally kiss π you π_
_you know say everyday I dey pray π€²π» for you π_
_in my heart oh there's a permanent place for you ππ»β€οΈ_
_that's why my heart dey beat like.._
_duduke π *duπ* *du π* *keπ*_
_cos na you I choose oh_
_Ayonfemi π©ββ€οΈβπβοΏ½? ayonfeπ_
Waqar datake bi kenan na simi mai taken _Duduke_ tana tsane gashinta kasancewar bata dade da gama wanka ba don wani irin zafi ake garin yau
Da rawar fairy ta isa gaban closet dinta tana cigaba da bin waqar ta bude shi tana duban kayanta tana shawarar wanne ya kamata tasa
Wata blue black armless gown ta ciro marar nauyi da farar hula takuma koma gaban mirrornta da rawar data taho
Kallo daya zakayi mata kasan yau fa take sallah a wajen ta don farincikin datake ciki be 6oyuwa kwata2
Saka kayan tayi sannan taja kujerar gaban dressing mirror din tana busar da gashinta
Saida tagama sannan ta dan shafa powder sama sama tasaka kwalli kadai a idanun sannan tayi amfani da roll on mai sanyin qamshi a duk kusurwar jikinta sannan ta feshe kayanta da turare shima marar hayaniya don dama duk yawancin turarrikanta sai kana gab daita zakaji qamshinsu bata cika son wanda da kaje wuri ba turarenka zai fara tonaka
Kashe disc din dake waqar tayi ta bude kofa ta fice
A dining ta tardasu har sun fara cin abincin
"daddy na!" tafada da yar qara sannan tayi wajenshi tabashi side hug
Dariya daddy yayi yace
"daughter na!" cikin yanayin da tayi magana
Dariya sukayi gabadaya mummy ma tadanyi murmushi tana cigaba da cin abincinta
Ja mata kujerar kusadashi daddy yayi ta zauna fuska fall murmushi sannan ta kalli mummy tace
"mummy ina wuni?"
Dagowa mummy tayi ta harareta saita sunne kai tana sosa kai
Dariya daddy yayi yace
"kyaleta, kishi take don baki fara yimata magana ba, me zakici? Tundazu na aika akiraki shiru"
"daddy wanka nake shiyasa" tafada tana daukar spoon tasaka a plate din daddyn alamun tare zasu ci
"guess yau tsintuwa kikayi, wannan fara'ar haka? To Gaskiya raba daidai za'ayi"
Rufe fuskarta tayi da tafuka tana Dariya tace
"kai daddy"
"eh mana, naga yau farinciki akeyi, kwananan you're so moody amma yau shar"
Murmushi tayi cikin zuciyarta tace
'bazaka ganeba daddy'
Azahiri kuma tace
"mood swing ne daddy"
Cigaba da cin abincin sukayi suna firarsu da daddy mummy na dan samasu baki jefi jefi, kallo daya zaka su burgewa don they are small example of a Happy family
ππππππππππ
Bude kwalin yayi ya ciro wayar dake kwance carefully yana jujjuyata a hannunshi
Wayar ta hadu iya haduwa, he can't believe shi zai dinga amfani da wannan wayar
Jin alamun za'a bude kofa da muryar kaka yasa yayi saurin ajiye wayar bayanshi Saidai he's too late don taga alamun ya 6oye abu
"hmm me ake 6oyemin?" tafada tana qarasowa
Dan kumbura fuska yayi yace
"ashe kece nayi tunanin 6era ne"
"eh 6era ce mai qaffafu biyu" tafada tana gallamashi harara
Murmushi yayi sannan ya fiddo wayar daga bayanshi ya miqamata yana cewa
"kalla kaka"
Dan wara idanu kaka tayi ta zauna kusadashi ta amshi wayar itama tana jujjuyata
"wannan ba wannan wayar bace?" inji kaka tana qara jujjuyata a hannu
"itace kaka"
"to ba kace ka mayar ba? Ya akayi kuma na ganka daita?"
"itace ta maidomin kuma"
"wa? Mummyn?"
Sai a lokacin ya tuna ashe kaka batasan zee ce mai kyautar ba
"A'a Zainab ta aiko"
Tagumi kaka tayi tace
"ni ma'u, dukda an maida Saida suka maido? Yanzu ya kake ganin za'ayi"
Shiru yadanyi sannan yace
"Kaka mu amsa kawai tunda babu dadi aqara maidawa Saidai bazamu qara abu hannunsu ba, koko?"
"kuma fa, ka kawo shawara kawai mu amsa tunda sun nace ya zamuyi?"
Murmushi yayi yace
"tanada kyau ko kaka?"
Dan yamutse fuska kaka tayi tace
"ni ai kasan ban cika ganin kyan irin wadannan wayoyin ba, dadai irin tamuce"
Murmushi kawai Deen yayi ya ciro tashi qaramar wayar ya budeta yafara zaro sim card da memory card dinshi
"to amma badai riqeta ba zakayi, sayar da ita zakayi ko?"
Dakatawa yayi daga abinda yake yace
"meyasa?"
"tayaya zaka riqe wayar dubu hamsin? Wannan ai almubazzaranci ne, zaifi maka ka Saida kasamu wani abu mai muhinmmanci kayi dasu wannan ta hannunka ta isheka"
Dan jimm yayi sai kuma yace
"kuma fa, insha allah haka xa'ayi"
Cikin jindadi kaka tace
"yauwa kyakyawa na, kaga sai muyi wani abu dashi ko jari yadda zamu dinga samun kudi ta wata hanyar bayaga namu ko?"
Kada mata kai yayi alamun eh yana murmushi amma deep down yasan tatsuniyace don babu abinda zai sashi siyarda wayar, yasan idan zee tasani to daidai yake da yankewar alaqarsu
"yauwa to yanzu maza ka shirya katafi"
"A'a kaka yanzu marece yayi, mubari sai gobe idan ba Haka ba tayin wulaqanci zasuyi mana"
"kuma fa, to shikenan a bari sai goben sai kutafi da salmanu don naga yafika baki idan katafi kai kadai qwararka za'ayi"
Murmushi kawai yayi bece komai ba
Tashi tayi ta nufi kofa tana cewa
"bari naje naduba abinda yake kan wuta karyayi kamu, kai amma mun gode wannan aka bamu kudinta ai mun warware"
Saida ya rakata da kallo harta fita sannan ya sauke Ajiyar zuciya ya maida hankalinshi kan wayar hannunshi yana ida zuramata sim din da t-card sannan ya kunnata
'wow!' yafada under is breath ya shiga daddanata yana shige da fice a wurare dayawa cikin ta yana jin wani irin nishadi a ranshi
π π π π π π π π
Tun dazu waya ke hannunta tana danne danne Saidai a zahiri ba danne dannen take ba, wani abu take jira
Kira take jira, kiranshi amma haryanzu shiru
Tunda tadawo daga school take kasa kunne da baza idanun ganin kiranshi amma shiru wai mallam yaci shirwa
Da tagaji da jira saita kunna datar ta tashiga whatsapp dinta
Gani tayi Aunty Feenah na online Hakan yasa tayi mata sallama
Bayan minti daya ta amsa mata nan suka shiga fira both typing da voice note inda Feenah ke Tambayar ta ya ake ciki ita kuma ta gayamata sun hade yau har sun koma sun jone kamar da tana kuma gayamata yadda yake nuna damuwarshi akanta kamar yana sonta shima din
Qarfin gwiwa Feenah taqara mata na karta sare kuma ta dinga yawaita addu'a dakuma neman za6in allah
Sun dade suna fira Feenah nata bata shawarwari yadda kasan yaya da qanwa sannan daga baya Feenah tace insha allah kwanan nan zata shigo katsinan itama zee tayi ta murna tana cewa allah yakaisu lokacin
Da haka sukayi sallama duk suka sauka
Duba lokaci tayi na saman wayar taga har 12 na dare
Haushi taji ya turnuqe ta
Wannan wane irin slow mutum ne mai ban haushi?
Dama yasan ba kiranta zaiyi ba ya amshi number ta?
Koko duk salon jan rai ne daya saba?
Wannan idan aka tafi a haka ga yadda take ganin alamu Koda sonta yake saita kusan zarewa sannan zai bayyanamata
Kashe wayar tayi cikin jin haushi ta tillar daita can tsakiyar gado taja bargo har kai tana jan tsaki
A ranar ta dade barci bai dauketa ba sai juyin datake tayi, tsaki kau tajashi yafi cikin kwando, daga baya dai tasamu barcin ya sadado ya dauketa
*WASHEGARI*
*02:40pm*
Zaune suke ita da mummy Kadai a dining suna lunch
Bakajin komai a Wurin sai qarar cokali sai kau maganar t.v dake dan kawomusu anan
Zee sai tsatsakurar abincin take don dole don kwata2 batada appetite
Yau haka ta tashi zuciya a cunkushe komai ma bata haushi yake shiyasa batada walwala sosai
Mummy data lura da Hakan taita mammaki don kwanan nan zee takoma kamar wata mai aljannu, yanzu zaka ganta cikin farinciki anjima kuma ka rasa gane kanta
Yanzu dai kamar jiya haka fa tayita washe baki kamar wacce aka biyawa hajji amma yau kwata2 babu wannan fara'ar saima kumbure2 data lura tana yi Tundazu
Ringing din wayar zee ne ya katse shirun Wurin wanda Hakan yayi daidai da dakatar da cokalin da zee tayi niyyar kaiwa a baki
Kallon screen din take ganin sabuwar number ce zuciyarta na qara gudu
Dagowa tayi ta kalli mummy taga itama ita take kallo
"ki daga mana" inji mummy ganin wayar takusan tsinkewa
Kamar dama umarnin mummyn take jira saita dauki wayar ta daga kiran ta karata a kunne batareda tace komai ba
"Assalamu alaiki..."
Luu... Tayi baya baya ta jingina da kujerar datake akai kamar marar lakka tana lumshe idanu ta bude daidai lokacin da muryar tashi ta daki dodon kunnenta... βοΈ
Ummin fasihu π§π»ββοΏ½?
8/2/21, 9:36 PM - Buhainatπ: *ππ»ββοΈDEEN ππ»ββοΏ½?*
*037*
_jiya nayi mistake, *Ruma* cikin qaramar hukumar *BATSARI* take ba *6atagarawa* ba. Afuwanπ_
"Hello?"
Muryarshi taqara ratsa dodon kunnenta dama zuciyarta baki daya
Ahankali ta bude lumssasun idanunta ta saukesu akan na mummy dake kallonta itama
Saurin zabura tayi zaune don ita harga allah ma manta a inda take zaune
"hello" tafada tana miqewa tsaye
"excuse me mummy" tafada tana wucewa hanyar stairs da sauri
Mummy ba tace komai ba sai Binta datayi da idanu
"hello?" Deen yaqara cewa a karo na uku
"hy" zee ta amsa daidai tashiga daki ta maido kofa ta rufe
Sautin murmushin shi taji wanda ba qaramin tasiri yayi a gareta ba
"aslm alaiki"
Zamewa tayi ta zauna gefen gadonta tana shaqar numfashi ta fesar ahankali tana jin yadda 6acin ran data wuni dashi na fecewa ahankali yana bin iska
"wslm.."
Sai shiru ya biyo baya
Jin shirun na neman yin yawa yasata cewa
"yes? Whoβs this?"
Sautin murmushin shi taqara ji sannan taji yace
"Kamal ne"
Itama murmushin tayi amma marar sauti tace
"Kamal?" tafadi sunan cikin wani salo da Saida Deen yakoma ya jingina da bangon dakinshi ya lumshe idanu
Jiyayi tasake cewa
"wane Kamal din?"
Murmushi yayi wanda tajishi sarai yace
"like seriously baki gane muryata ba? Deen ne fa"
Murmushi tayi cikin zuciyarta tace
'ko cikin muryoyi dubu naji muryarka saina tantanceta"
A zahiri kuma tace
"Oops! Deen? Dama naji muryar sounds familiar ashe kaine?"
Murmushi yasakeyi yace
"eh nine, good afternoon"
"afternoon, how you? Ina kakata?"
"lfy lau, kakarki na nan lfy lau ina mummy na?"
"mummy tana dakinta"
Murmushi taji yasake yi sai jitayi dama tana ganinshi taga smiling face din
"just call to say hello"
Murmushi itama tayi mai sauti tace
"thank you so much, how's weekend?"
"weekend alhamdullilah, zaki zo school on monday?"
"why not?" tafada tana jawo pillow tana rungumewa a qirji
"ok saimun hadu monday din" inji Deen a dayan bangaren
Ba haka tasoba don ita nan gyara zaman susha firarsu tayi amma ya ta iya?
"ok allah ya kaimu" tafada ahankali
"bye ki gaida min mummy"
"zataji nima ka gaida kaka"
"ok bye"
"bye"
Kittt... Taji an katse wayar
Lumshe idanu tayi ta Janye wayar daga kunnenta ahankali tana sauke wani nannauyan numfashi
Wani kayattacen murmushi ya su6uce mata tayi wani juyi a kan gadon wanda yakaita tsakiyar gadon ta kwanta rigingine still pillon a qirjinta
Number daya kirata dashi ta shiga kallo fuskarta dauke da murmushi
Latsa wajen adding contact tayi tayi saving din number shi da
_*Dβ€οΈ*_
Sannan ta maida wayar ta rungume a qirji ta maida manyan idanunta ta rufe.
***
"kyakyawa na! Kyakyawa na!!"
Kiran da kaka keyi mashi yasashi ajiye wayar ya tashi ya fito
"kakata?" yafada yana qarasawa kitchen din datake
"maza ga abincinka nan ka dauka ka cinye ka kawo na qara maka"tafada tana nuna mashi kwanon abincin
Waro idanu yayi yace
"aqara kuma? Kaka wannan ai yayi yawa"
Dan harararshi tayi tace
"kuma saika cinyeshi ba, maza dauka bari na shinfida mana tabarma waje" tafada tana fita daga kitchen din
Tabarma ta fiddo ta shinfida daidai Deen yafito da abincinshi dana kaka
Zama sukayi kowa yaja abincinshi gabanshi sukayi bismillah suka fara ci
Can kaka ta dago tace
"yau za'a Saida wayar nan ko?"
Dago idanu Deen yayi ya kalleta sannan ya kada kai kawai
"yauwa ai gwara ayi a saidata ko mun samu jari, jiya kusan raba dare nayi ina tunanin yadda zamuyi dasu harna samu na yanke shawara
Idan aka samu kudinnan zan qara jarin kokon nan don dama sau dayawa ba isa yake ba kafin takwas ya kare azo kuma aita nema babu, kaga saimu qara yadda zamu dinga samu da dan kwari ko?"
Kada kai Deen dake aikin sauraronta yayi alamun gamsuwa
"Sai kuma wata shawarar dana yanke, mezai hana nafara siyarda dambu?"
Dagowa Deen yayi ya kalleta
"Dambu kuma kaka?"
"eh dambu, kaga da hantsi wajajen 12 haka zuwa azahar zanyi kuma naga babu masu yi anan unguwar sai inga kamar za'a samu alhairi, koko?"
"to kaka muda bamu ga kudin ba tukkuna"
"ai zamu gani ko? Ba yau za'a siyar daita ba?"
"eh"
"to? Ina wannan lissafin ne yadda komai zai qara zo mana da sauqi, kaga yanzu ba aiki kuke samu ba can wajen aikinku sai wannan yar sana'ar tawa ta koko ita ke dan taimaka mana ga kudin makarantarka don ma aski yazo gaban goshi kaga ya kamata mu qara himma ko kuwa?"
Deen dake sauraronta Tundazu ya kada kai ahankali zuciyarshi fall tunani kala2
Yasan tanada Gaskiya don yanzu sunfi raja'a akan abinda ake samu a sana'ar ta na koko da qosai don ba aiki suke samu ba sosai yanzu yawanci yan gyare gyare ne da kudinsu basu taka kara suka karya ba, ga kudin makaranta
Gaskiya so samu a siyarda wayar don zata taimaka sosai amma kuma bejin yana iyawa bawai don yana kwadayin riqeta ba don gayu ko wani abu, A'a kawai jiyake bazai iya siyarda kyautar da akayi mashi ba, kyautar kuma ta zee
"yauwa kayi da jiki ka gama kaga idan ka fita siyan geron gobe sai ku wuce kasuwar tsaitsayen ku sayar"
Da to ya amsa mata ya cigaba da cin abincin cikin sanyi, zuciyarshi fall tunani
Atare suka gama cin abincin ya kwashe kwanikan yakai kitchen din yadawo ya xauna kusada kaka dake qilga kudin dazata bashi yayi sayayyar
Saida tagama sannan ta bashi ya amsa ya tashi ya shiga daki ya dauki wayar yafito yayi mata saiya dawo ita kuma tabishi da adawo lfy
Koda yafito hanyar gidansu salmanu yayi Saidai kafin ya qarasa yaci karo da qannen salmanun nan yake Tambayar shi ina salmanun sai yace bayanan yafita
Hakan yayi ma Deen dadi sosai sai kawai yayi tafiyarshi kasuwa don yiwa kaka sayayya
Koda yadawo da batun wayar ta tareshi nan ya gayamata ai be samu salmanun ba shiyasa basuje ba
Bataji dadi ba Amma saita haqura akan ai akwai gobe, sai aje siyarwa goben
Deen kawai jinta yake amma bayajin zai iya Hakan don he valued the phone kamar yadda yake value mai ita
Da daddare bayan sun fito sallar isha'i Deen ya tari salmanu yayi convincing dinshi akan Koda kaka tayimashi maganar siyarda waya yasan abinda zai gayamata
Dayake salman dan maqocinsu ne kuma sunzo tsararraki da Deen kuma ba laifi suna mutunci sosai Hakan yasa ya amince bayan yagama tsokanarshi akan to ya tanaji kudin dazai biyashi na qaryar da zaiyi don buhari ya hana aikin banza
Shidai Deen Dariya kawai yayi sukayi musabaha ya wuto gida
Washegari ma haka yaita raina ma kaka hankali akan bega salmanu ba can dai taje gidan da kanta tabada sallahun idan salmanu yadawo yazo tana nemanshi
Dayake shima yasan kiran ko na menene be tashi zuwa ba sai bayan isha'i, sanin cewa babu halin zuwa lokacin saita cemashi yatafi yadawo gobe da marece zai raka Deen kasuwa
Da to kawai ya amsa ya tashi yayi tafiyar shi.
A bangaren zee kau yau ma haka taita jiran kiran Deen Saidai bata qwalaffa rai ba irinna shekaranjiya Saidai har dare babu kira babu alamun shi
Bata wani damuba don tasan gobe zasu Hade school Hakan yasata kwanciyarta hankali kwance wani barci mai shegen dadi yayi gaba daita
*MONDAY*
Tafiya take ahankali cikin tafiyarta data zame mata jiki
BΓ―Γ± harabar school din take da kallo ganin yadda yacika sosai yau don dama kowa wannan monday din ne harinshi
Qara gyara zaman gyallenta da iska ya saukoshi daga kafada tayi tana cigaba da tafiyarta
"Zainab..."
Taji an kirata daga baya wanda ko bata juyaba tasan mai kiran
Yitayi kamar batajiba ta cigaba da tafiyarta tana murmushi slightly
"Hey! Zainab.." taqara jin muryarshi na qara kusantota
Wani murmushin tasake saki tana dan daga gira daya sama batareda ta tsayaba
"Zainabbb!" taji a kusa kusa da ita da alama yana gab da ita
Sai a lokacin tafara slowing down ta juyo ahankali cikin son ganin wa ke kiranta
Deen din ne, sanye cikin baqin wandon jeans sai farar t-shirt mai zanen baqi a gaba, as usual sumarshi a dan tuje take dan akwai zirin dama ya biyo mashi ta fuska
Ganin shine yasata tsayawa tana kallon yadda yake ida qarasowa yana dan yatsine fuska
"my goodness Zainab, are you deaf?" yafada yana sauke numfashin saurin dayayi
Dan daga gira daya tayi cikin alamun tambaya shikuma daidai ya qaraso
"tun daga bakin gate nake kiranki amma bakiji, are you sure Kunnuwanta lafiya lau suke?"
Harararshi tadanyi suka cigaba da tafiya tace
"kokuma kaine za'ayi ma wannan Tambayar ba? Are you sure maqoshinka lfy lau yake? Dama tayaya zani jika da wannan voice din naka?"
"Allah da qarfi nake kiranki, cewa nake Zainab! Zainab!! But unknown to me ashe kurma ce"
Juyowa tayi tayimashi mugun kallo shikuma yadan matsa gefe yana Dariya
"Allah, gashi energy dina ya qare Wurin shouting"
"dama kanada energy din ne? Lazy bone" tafada tana dan Harararshi
"O'O! Am not lazy"
"O'O! You are" ta kwaikwayeshi
Kafin wani yasake magana a cikinsu sukaji daga bayansu ance
"hey! Ku biyunnan kuzo"
Atare suka juya daidai wanda ya kirasu din shima ya kallesu sai kuma ya dauke kai yana cigaba da Fiddo abubbuwan dayake fiddowa a booth din motarshi daya wuto da ita ciki sosai yadda kayan zasuyi dadin kaiwa office.
Kallon juna Deen da zee sukayi saikuma suka qarasa wajenshi kamar yadda yace
Deen ne cikin ladabi yafara cewa
"Good morning sir"
Amsawa mr ibrahim yayi batareda ya dagoba sai sannan itama zee ta gaidashi itama ya amsa mata batareda ya kalleta ba
Suna nan tsaye a bayanshi har yagama fiddo kwalayen daga booth sannan ya rufe ya juyo ya fuskancesu
"help me with these" yafada yana nuna masu kwalayen
"ok sir" inji Deen yana wucewa don daukar daya
Itama zee wucewa tayi Wurin qaramin cikinsu ta dauka sai jitayi ashe babu nauyi ma da alamu takardune ciki ko littatafai
"ga key, ka bude kushiga dasu ciki saiku dawo mu ida kwashewa" inji mr ibrahim yana miqama Deen key din office din
Amsa yayi sannan suka jera da zee suka wuce don kaiwa
Saida sukayi nisa sannan Deen cikin muryar rada yace
"mutuminki"
Kallonshi tayi tana dan Harararshi tace
"Amebo" itama cikin rada
Murmushi mai sauti yayi yace
"eh din"
Ajiye nashi kwalin yayi bayan sun qarasa ya bude office din zee tashige sannan shima yadawo ya dauki kwalin shima yashiga
Ajiyewa duk sukayi a qasa sannan suka fito yasake rufe kofar sannan sukayo hanyar dawowa
"guess ya haqura" inji Deen yanzu ma cikin rada dukda basuma shawo kwanar da zasu hangi mr ibrahim din ba
Daga kafadu zee tayi tace
"may be, maybe not"
"gashi nan ya kiramu"
"ai besan mune ba, bakaga reaction dinshi ba dayayi realizing nice"
"ni ban gani ba"
"dama ya xa'ayi ka gani da wadannan small small eyes din naka kamar na cinnakaπ"
Dan 6ata rai yayi yace
"kekuma da naki big big eyes kamar na kwadoπΈ"
Dan wara idanun tayi
"nidin?"
"exactly"
Yitayi kamar zatazo wajenshi yayi saurin matsawa yana Dariya
Kwafa tayi tana murmushi suka shawo kwanar da zasu dinga hango mr ibrahim suka hangoshi tsaye yana magana da wani lecturern shima
Cikin rada zee tace
"yaushe kake ganin ya kamata na sake samunshi? Now?"
"No not Now, kibari zamuyi magana but not Now" yafada daidai sun qaraso wajensu mr ibrahim din
Gaida dayan lecturern sukayi sannan suka sake daukar kwali guda guda ya rage saura daya sukayo gaba
Kafin ma ya bude kofa sukaga shima mr ibrahim yataho da kwalin qarshe
Kafin ya qaraso har sun shiga sun ajiye yana isowa shima ya shigo ya ajiye yayi masu Godiya sannan ya sallamesu suka fito
"yanzu ina zaki?" inji Deen
"Sabon department dinmu ofcourse"
"kinje copying timetable?"
"No kaifa?"
"nima yanzu zanije"
"ok muje, Hakan ma yakamata nafara ko?"
"nima haka nagani"
Daga nan sai suka sha kwana suka kama hanyar inda ake liqa timetable suna tafe suna fira gwanin sha'awa
Tare sukayi copying din timetable din anan suka ga ashe duk basuda class yanzu
Zee sai 12pm saikuma na 2:30pm shikuma yanada na 1pm shima da 2:30pm.
Ganin Hakan yasa suka wuce library don a lokacin duka qarfe 10 da yan mintuna
Anan sukayi zamansu sunata fira har lokacin shiga lecture din zee yayi ta tashi tabarshi anan
Ganin Hakan yasashi daukar wani Littafi yana karantawa to wine time away, lokacin shigarshi class nayi shima ya tashi ya fice ya nufi sabon department dinsu
Zee tarigashi fitowa Hakan yasa tawuce cafteria ta siyamusu snacks ta dawo library din
Bata dade ba sai gashi shima yayi joining dinta
Tare sukaci abinda ta siyo din suna duba lecture din da suka dauka yau
Sai wajajen 2pm suka tashi suka nufi masjid gabadaya shi yayi bangaren maza ita tayi na mata
Koda suka fito classes dinsu duk suka wuce don duk sunada lecture a daidai lokacin
A kusan tare suka fito inda a lokacin har Motarsu zee ta qaraso
As usual sallama sukayi don Deen cewa yayi akwai abinda zaiyi ba yanzu zai tafi ba
Bata damuba itama sukayi sallama tashige mota bala yaja suka fice tanajin kanta cikin nishadi marar musaltawa
Haka ranaku sukaita tafiya masu, kodayaushe zaka gansu a school atare Saidai idan daya ya shiga class yabar daya, sosai wata iriyar shaquwa datafi tada tasake shiga tsakaninsu Agefe daya kuma wutar soyayyar Deen tana cigaba da balbala a zuciyar zee
Yanzu yana dan kiranta don wani sa'in yana kiranta sau daya a rana wani sa'in kuma sai bayan kwana biyu yake kiranta, itama tana dan kiran shi amma ba sosai ba kuma yasha bata kaka su gaisa ta waya
Duk yadda takejin soyayyar shi a zuciyarta tana iya bakin qoqarinta na dannewa tayi acting normal musanmman ma a gaban shi dukda wani sa'in Dakyar take iya controlling din emotion dinta
Sosai soyayyar shi ke qara hauhawa a duk kowacce daqiqa a zuciyarta abin har tsoro yake bata don wani sa'in har kuka take tana fargabar kar allah ya jarabceta ta wannan fannin don tasan ba qaramar wuya zatasha ba
A gida ma mummy tayi noticing chanji sosai daga gareta
Don yanzu kusan kodayaushe indai tana gida to batada Wurin zama kamar garden, can zataje ta xauna shiru ko ta buga tagumi tana kallon waje guda tana murmushi kamar ta6a66a
Wani sa'in ko a dining suke haka kawai sai takama murmushi tun abin na ba mummy mammaki har abin yafara damunta
A bangaren Deen kau haryanzu be furta soyayyar shi ga zee ba Saidai yana bata kulawar dake sata tantamar anya babu sonta a ranshi kuwa?
Saidai kuma data tuna waye Deen da abinda yake iyawa sai ta bar wannan tunanin don ba qaramin aikinshi bane ace duk kulawar nan babu sonta ko daya a ranshi kawai abota ce
Yanzu haka satinsu uku da komawa school, komai yana tafiya masu daidai a karatunsu musanmman ma zee don sosai Deen ke warware mata abubbuwan dasuka shigemata
Gashi sun shirya da mr ibrahim don taje ta sameshi personally tabashi hqr dukda Saida Deen yasha fama kafin ta yarda taje don sau uku ana saka rana sai ranar tazo taji bata iya zuwa daga qarshe dai Dakyar ya iya convincing dinta taje sai gashi mr ibrahim din ne gwasaleta ba kamar yadda take gudu yayi accepting
Book Chapters
Chapter 27
Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81