Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duk asuba saita tadata tayi sallar

Kauda kai tayi daga kallon qofar tana zu6ura baki, jitayi tana jin haushin mummyn don kome yafaru duk itace sila da tana uk da ba haka ba

Jin still tana bugun kofar kuma ba barin bugun kofar zatayi ba saita tashi yasata janye bargon jikinta a fusace ta sauko sannan ta nufi kofar tana yan gunaguninta wanda ita kadai tasan abinda take cewa

Saida tasaki fuska ta maida ta kalar wanda ya tashi daga barci be isheshi ba sannan ta bude kofar

Mummy ta watsa mata harara tace
"ke shikenan idan kin kwanta kamar mai barcin mutuwa baki ko motsawa"

Dan turo baki tayi tace
"mummy Allah banfa jiba"

Tsaki mummy taja tace
"dama yaza'ayi kiji kina Wannan barcin asarar, kiwuce kije kiyi alwalla gashican sai assalatu akeyi"

Da To ta amsa sannan tajuya tawuce itama mummy tarufe kofar tawuce

Alwalla ta dauro ta chanza zuwa wata brown jallabiya da dama ta wareta mainly for sallah sannan tazura hijab ta shimfida sallaya tahau kai tashiga gabatar da sallar

Koda tagama komawa tayi ta jingina da gado sa6anin da da datagama take hayewa gado takoma barci

Tunanin mafita take ga matsalar mr ibrahim, Allah yasani abin na ranta sosai kuma yana damunta, tasan kome zatayi bazata iya cinye kingin 50% dinba kuma samun qasa da 50% din yana daidai da faduwa koda 49% ne kuwa, gashi dama yaya lafiyar giwa? Daman cikin 100% take takarkarewa tasamu 60 ko 62% Shima saita hada da sleepless nights ta hana kanta barci tana karatu sannan zata take samu, gashi fa tana ganin tayi iya qoqarinta na karanta duk abinda aka koyar a class amma be zama kamar yadda zata dauka a class din idan anyi lecturen daita kuma dama abinda zaka dauka idan aka koyar dashi cikin aji yafi wanda zaka dauka idan ka ware kanka kai kadai da niyyar koyawa kanka

Maida kanta tayi ta jingina da gadon tareda maida lower red lip dinta cikin baki tana tsotsa

Yanzu meye mafita? Taje ta roqeshin kamar yadda taji su rukky nacewa? Idan ta roqeshi zai saurareta? Koko ma qara samun kafar wulaqantata zaiyi? To idan ma taje ya xatace? Bata ta6a roqon alfarma ba kuma batasan yadda akeyi ba, kuma batajin tana iya strooping so low ta roqi alfarma, rashin roqon kuma na iya chazamata wulaqanta ta qarshe amma kuma ai batada tabbacin roqon zaisa ya saurareta

Cije lip din tayi tana lumshe ido cikin rashin samun mafita

Fuskarshi yayimata gizo a idanunta hakan yasata bude idanun

_inhale tasbih, exhale tahlil and stay safe_ maganar shi ta dawomata


Tsaki taja tana cewa "phsyco kawai" under her breath

Miqewa tayi daga kan sallayar ta ninke ta ajiye ta cire hijab dinta sannan takoma kan gadon ta kwanta tareda jan bargo da niyyar takoma barci saidai yaqi zuwa sai juyi kawai datake tana ta saqa da warwara



Haka tayi spending din weekend din cikin zullumi da damuwa tana addu'ar Allah ya dorata akanshi ranar monday.


*MONDAY*



Tunda wuri tafara shiri don ko komawa barcin nan nata na bayan asuba batayiba, tana gama sallah tashiga shiryawa agurguje don tana son taje school din da wuri ayita taqare


Saidai duk saurin datake saida tara takusa sannan tafita sakamakon ruwan da aka kece dashi wajajen qarfe bakwai

Cikeda takaici takoma ta zauna Dole tajira ruwan ya dauke sannan ta fito
Sanye take cikin riga da wando na pakistan mai irin bujen wandon nan, rigar kalar pink wandon kuma fari sai gyallen kayan Shima pink

Kaffafuwanta kuma Sanye da fararen baby shoes sai side bag mai hannun sarqa pink

Sosai tayi kyau, irin kyawunnan mai tafiya da imanin mutane, fuskarnan tasha heavy makeup don dawuya tayi simple makeup.

Fitowa tayi tana duba agogon hannunta batareda ta kula ma'aikatan dake gaidata ba

Ganin hakan yasa bala saurin tasowa yanufi motar dasu fita daita da aka lullu6e da rigar mota sbd ruwan da akayi

Yayewa yayi sannan ya zagayo ya budemata kofar, fadawa tayi ciki tana cewa
"dalla mallam kayi da jiki, am late"

Saurin mayar da kofar yayi ya rufe sannan ya zagaya dagudu ya bude mazauninshi ya zauna, tada motar yayi sannan ya figeta cikin yan sakanni suka fice gidan suka halba kan titi


*UMYU*


Fitowa yayi bayan yagama daidaita parking din ya zagayo ya bude mata.

Saida ta 6are bubble gum ta jefa abaki ta zaro shade dinta tasa sannan ta ziro qafa ta fito

Caa akayi mata da idanu don yau mutanen dake harabar makarantar nada yawa saboda duk yanzu ake zuwa

Bata damu da kallon ba as usual ta sallami bala tafara tafiyarta tana jin yadda iska mai dadi ke kadawa kasancewar ba'a dade da gama sheqa ruwaba

Mutane kau kallon nasu nayau dabiyu don master be dade da wucewa ba Shima hakan yasasu ji ajikinsu cewa yau fa za'asha show inda yawanci addu'a suke Allah yasa aci uban yar iska suga ta fulaku

Itadai batasan sunayi ba haka tazo tawuce cikin salon tafiyarta tawuce class direct.

Tana niyyar shiga su sumee na niyyar Fitowa, ganin ta yasa suka juya suka shiga class din gabadaya suka wuce inda suke yawan zama idan ba lecture suke ba

"yane?" inji zee tana dora jakkarta a cinyarta

"Normal.." duk suka amsa sannan suka fara tambayarta ya weekend ta amsa da lfy

Bin class din daya rude da hayaniya tayi sannan ta maida kallonta kansu tace
"wai meke faruwa ne? Naga class ya burkice"

Ajiyar zuciya suka sauke atare

Sumee tace "ba Dole ya burkuce ba? Ai idan ma akwai fin burkucewa saiyayi"

Gyara zama tayi tana kallonta tace
"bani insha"

Ajiyar zuciya sumee ta sauke tace
"yawuce mutuminki?"

Gabanta ne ya yanke ya fadi

"mr ibrahim?" ta tambaya fuskarta na nuna alamun fargaba

"shi fa, wlh yau naqara tabbatar da beda mutunci" inji Nurr

"meya faru kuma?" inji zee

"yanzu ya fattatakomu daga office dinshi" tabata amsa

"ya fatattakoku? Zuwa ku kayi?" inji zee

"bamu dade da shigowa class ba mukaji Ana shawarar zuwa wajenshi bada hqr, don fa mutane dayawa basuzo ranar ba, shine muma muka bisu mukaje, wai kinga wulaqancin dayayi mana? Hmm roqonshi muke amma yadda kikasan tirashi muke, ba arziqi muka fito bayan ya koromu" inji sumee

Tunda tafara magana zee ke kallonta hankali tashe har takai aya

"wlh mutuminnan wani sa'in beda m, kinga yadda ya fattatakemu kuwa?" inji deeya

"Hmm aini dama nasan fa bazai yadda ba don magana daya yakeyi, yadai tabbata saimunyi carryover tunda ba digon imani aranshi" inji rukky

Izuwa yanzu ran zainab yayi mummunan 6aci

"wai me mutuminnan ke nufi damu ne? Ina ya ta6a jin anyi wannan zaluncin? Idan mutum lalura ta hanashi zuwa ranar fa? Shikenan sai a kadashi? Mtcheew!" taqarashe tana jan tsaki sannan ta miqe

"Ina zaki???" suka fada har suna hada baki

"wajenshi yau za'ayita taqare" tafada tana wucewa
Deeya har zatayi magana rukky ta dakatar daita ta hanyar ruqo mata hannu tana wani makirin Murmushi.


Direct office din mr ibrahim ta nufa zuciyarta na qara qarfafa mata gwiwa.
Bata ja burki a koina ba sai a gaban kofar office dinshi inda aka rubuta sunanshi 6aro2 da manyan haruffa

Tsayawa tayi tana kallon kofar tanajin dan qwarin gwiwarta na neman fecewa

Saurin tattaroshi tayi ta saita kanta sannan tayi knocking

Saida ta bubbuga sau biyu sannan taji yabata izini cikin husky voice dinshi nake nutsar da duk wani mai rawar kai

Jitayi kamar ta juya saikuma ta daure ta tura kofar tashiga da sallama

Ansawa yayi batareda ya dago daga tattara takardun dayake ba

Zuciyarta ce tashiga racing tanajin kamar ma bazata iya bude baki tayi magana ba
Jin shiru yasashi dagowa daga abinda yake don ganin wanene

Turus yayi ganin itace saikuma slight Murmushi yayi forming agefen bakinshi ya dauke kai yana cewa

"uhum? How may i help you?" yafada yana cigaba da hada takardun

Qara gudu zuciyarta tayi Jin muryarshi akaro nabiyu sai yanzu tafara danasanin zuwanta ma

Tattaro nutsuwarta tayi taqara matsowa ta tsaya bayan kujerar dake facing din table dinshi ta dafa chair din sannan tace
"Good morning"

"morning" ya amsa a taqaice batareda ya dagoba

Dan gyara murya tayi sannan tace
"amm... Dama maganar attendance daka dauka last week thursday ne wanda kace zaka ajiyeshi amatsayin 50% of your exam" shiru tayi ganin ya dago ya kalleta hakan yasata janye nata don bata iya jurar kallon cikin qwayar idonshi

"Ehen? What about that?" yafada yana kafeta da idanu

"am... Dama sonake naji ko hakane?" tafada still bata yarda sun hada ido ba

"eh hakane" yabata amsa kai tsaye

"but why?" tafada tana dagowa tana kallonshi

"saboda na isa" yabata amsa yana komawa ya jingina da kujerarshi yana jujjuyawa

"amma aganina Wannan be isa hujjaba kuma ina aka ta6a hakan?" tafada calmly tana kallonshi saidai ba directly a ido ba

"gashi anfara anan, kuma inada ikon yin fiyeda hakan idan naga dama" yafada cikeda isa

Qoqarin danne 6acin ranta tayi tace
"amma sir baka ganin zai zama cutarwa ga wasu?"

"wasu? Su wa?" inji mr ibrahim

Hadiye wani abu tayi tana qara qarfafa ma kanta gwiwa
"wadanda lalura ta hanasu zuwa ranar"

"i dont care" yafada yana daga kafadu tareda sake jawo wasu files

Jitayi zuciyarta na tafarfasa don takaici

"but as a Good leader kamata yayi ka damu da damuwar na qasa dakai, akwai wadanda lalura zata hanasu zuwa kamar rashin lfy ko makamancin haka, idamma mataki zaka dauka bekamata kadau mai tsananin tsauri irin Wannan ba"

Dagowa yayi akaro nabiyu yana kallonta sannan ya ajiye pen din hannunshi yayi interlocking din yatsunshi akan table din gabanshi yace
"Good leader? Am i good?"

Dan ta6e baki tayi ta kauda kai tana cewa "haka suke cewa" ahankali don karya ji amma saboda sharpness din kunnuwanshi saida yaji hakan kuma ba qaramin hasalashi yayi ba

"naruga na yanke hukunci and there is no going back, so get out!" yafada yana zaro mata idanu

"amma kasan Wannan ba adalci bane, How will you feel idan akayi wa 'ya'yanka haka? Suma students 'ya'yan wasu ne you should treat them How you treat yours" tafada muryarta nadan kyarma ga daci2 datake ji a maqoshinta

"wait, are you talking on your behalf ne koko?" ya tambaya yana tsareta da ido don shi tunda tashigo beji ta furta kalmar ban haquri ba saima yi datake kamar bata cikin wadanda abin yashafa

"Am talking on behalf of wadanda lalura ta hanasu attending, wadanda basu jiba basu ganiba" tafada hawaye na ciko idanunta

Mammaki abin yabashi Wato ita tafi qarfin ta roqoshi kai tsaye saidai ta fake da wasu?

"ke meye ruwanki tunda bakya cikinsu?" yafada yana Jin ranshi naqara 6aci

"saboda nasan nice sila" tabashi amsa kai tsaye hawayenta na digowa wanda tayi Saurin sharcewa don bata buqatarsu yanzu

"mene?" ya tambaya yana wara idanu

Qara sharce wasu sabbin hawayen dasuka gangaro tayi tace
"yes, saboda ni kayi hakan kuma nasani amma idan zakayi hakan be kamata ka hada da wasu ba, ni kadai zakayi mawa"

"Are you insane!" yafada yana buga table da qarfi wanda saida ta miqe tsaye Jin yadda taji bugun har cikin kwalwa

"nace kina hauka ne zaki shigo har office dina kiyimin shirme?!" yafada Shima yana tashi tsaye

Zee dake hawaye sosai tace
"idan da nikadai kayimawa bazaka ma ganin office din naka ba don hakan bazai iya yimin komai ba, bazai hanani tsallakewaba!..." sai kuma tafashe da kuka tasa taffukan hannunta ta rufe fuskarta tacigaba dayi

Fadin 6acin ran da mr ibrahim yashiga 6ata bakine, shi sai yanzu yaqara tabbatarda yarinyar nan tantiriyace duk inda yake zaton takai ta wucenan

"dakyau! Dakyau!! Dakyau!!!" yafada yana tafi saikuma ya tsuke fuska yace
"ki tsallake to, albishirinki? Na safsafto hukunci na, attendance din ranar ya sauka daga 50% zuwa 30%, wadanda basuyi attending ba sunada damar neman 70% ciki harda ke.. Kuma qarin wani albishir... Acikin 70% zanbada gara6asar 20% a matsayin assignment, 50% kuma shine zaku ida samowa amatsayin exam, ki tsallake, nabaki wuri da babbar dama na tsallakewa, ki tsallake mugani... Kuma na rantse da mahallicina bazan ta6a yima kowa runton marks ba, kinsanni kuma kinsan abinda zan iya, bazan ta6a yiwa wani mahalluki rintoba a marks, da zanyi da tuni nayi hakan akanki don haka kitafi, Allah ba mai rabo sa'a"

Share hawayenta tayi ta kalleshi da rinnanun idanunta ta rataye jakkarta dakyau sannan cikin rashin ta ido tace

"sun gode, don ni ko ahakan aka tafi ba damuwata bace..."

"out!!!" yafada a mugun tsawace

Juyawa tayi tafice da dan gudu tana toshe bakinta

Bugun desk din mr ibrahim yayi yana cize lip din qasa cikin mugun takaici

Koda tafito dakatawa tayi da gudun tafara tafiya don kar agane yanayinta saidai ko ganin gabanta batayi sosai, 6acin rai da qunar rai sunsa batama gani sosai

Jitayi ta bangaji mutum hakan yasata yin baya baya zata fadi taji an cha6e hannunta an ruqo

Qara wara oily idanunshi yayi yana kallonta yanason ya sheda ina yata6a ganin Wannan fuskar

Jin wanda ya ruqo hannunta beda niyyar dagota yasata bude ido ta kalleshi taga yawani yi sakato yana kallonta

Batareda tama shedashi ba ta daka me tsawa cikin 6acin ran dake cinta tace
"kai hamago!!!"

Tsorata yayi wanda hakan yasashi sakin hannunta ba shiri tayi baya2 sai cha6all!! Tafada cikin chakwalon dake bayanta daya taru sanadin ruwan saman dazu... ✍️

Ga long page kusha yau da gobe, insha Allah duk ranar juma'a zamu dunga hutawa saboda falalar ranar kuma kasancewarta gajeriyar rana


Juma'at mubaraq in advance🧚🏻‍♀?
8/2/21, 9:31 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?*




*006*



Runtse idanuwanta tayi gamm tana sakin qara, cha6all!!! Taji ta fada cikin wasu ruwa wanda sanyinsu ya ratsa ilahirin jikinta

Daga inda take tana Jin gasping din mutane da yar hayaniya

Bude idanuwan tashiga yi ahankali har suka bude tangaram

Bin mutanen dasuka zagaye wurin tayi da kallo wasu baki a hamgame don mammaki wasu na qumshe baki don hana dariyarsu fitowa

Da daya daya ta dinga binsu da kallo har idanuwanta suka sauka akanshi

Sanye yake cikin qatuwar rigar sanyi baqa da wando jeans baqi sai hular sanyi dayasa wanda ta rufemashi kunnuwa itama baqa saidai anyi mata rubutu da farin zare a gaban hular, kasancewar shi fari sai shigar baqaqen kayan suka sake fiddoshi sosai

Wara mata oily idanunshi yayi ganin ta kafeshi da ido

"O'O! faduwa kikayi?" yafada yana dafe baki da tafin hannunshi yana qara wara idanu alamun al'ajabi

Dariya mutanen dake kewaye da wajen suka Fashe dashi sosai wanda hakan yadawo daita daga duniyar kallonshi ta maida kallonta ga jikinta tana duba yadda koina nata ya 6aci da chakwali

Rintse idanu tasake yi gamm sannan tafasa wata iriyar qarar takaici tana Fashewa da kuka

Dariya masu kallonta suka qara sawa yayinda wasu har waya suke zarowa suna daukarta hoto, abinka da dama haushinta sukeji

Shikau tun sadda tafasa qarar yaja baya atsorace yana cewa
"O'O!"

Su sumee ne suka kutso tacikin mutanen suka nufi inda take zaune rashe2 taci kwalliya da ta6o ga fuskarnan ta dauki combination din makeup dinta dana chakwali sai rizgar kuka take kamar zata shide

Dagudu sukayi wajen ta suka kakkamata suka tadata tsaye still tana kuka idanuwanta arufe

Yau wacce iriyar baqar ranace gareta, tunda take bata ta6a Jin ta muzanta ba irin na yau, jitake kamar qasa ta bude ta nitse ciki

Kamata sukayi suka fara barin wurin da ita

"yayi sarauniyar kyau! Wannan wanka ya wanku, gaskiya kin cancanci award mai taken mud queen!" wani acikin mutanen yafada

Wurin sake daukar Dariya yayi nan kowa yashiga tofa albarkacin bakinshi

Su sumee dai basu ko nuna sunsan dasuba suka wuce daita suna lalla6a ta cikin tausayawa saidai aqasan ransu fall yake da farinciki jisuke kamar su fiddo dariyar dake cikinsu suyi mai isarsu

Motar nurr suka bude suka sakata ciki sannan sumee ta zauna kusada ita riqe da jakkarta rukky kuma kusada sumee sai deeya data shiga gaba itakuma nurr tashiga mazaunin driver, tada Motar tayi tabata wuta ta figeta suka fice daga makarantar gaba daya.


Sukau students abin nema yasamu tuni school yakarade da labarin *mud queen* kamar yadda suka samata yanzu

Wadanda basunan akayi sai cizon yatsa suke dukda yawanci an gwadamasu hotunan da aka dauketa, kowa Allah yaqara yake mata abinka dama da tayi baqin blood Awajensu kuma dama kowa haushinta yakeji.

Suma su master dake bayan school cikin kangwaye inda suka saba zuwa su chake labari ya riskesu

Zokaga dariyar qeta, duk acikinsu Alex yafi farinciki da abinda yafaru, sai cewa yake ai dama fada da aljani ba riba kadanma tagani.



Zaune yake qarqashin wata bishiya yana cin chips hankali kwance, wasu students su uku suka zo wajenshi mace daya maza biyu.

Shewa suka saki gabadaya suna qarasowa wajenshi

Dago oily pure white eyes dinshi da zara zaran lashes sukaiwa qawanya yayi ya kallesu sannan yasaki Murmushi wanda ya lotsar da dimple dinshi na tsakiyar dan gemenshi ya matsa masu ganin zama zasuyi.

"na wajen kaka! Na wajen kaka! Gaskiya yau ka farantamana rai fiyeda tunaninka" inji daya daga cikin mazan

Murmushi kawai yayi ya saka chips din hannunshi baki sannan ya mimmiqa masu ledar chips din alamun bismillah
"Ah! Ai dole muci *Deen*, Wannan farincikin daka samu yau dole muyi kodimo" inji macen cikinsu

Duk daukan daddaya sukayi sannan suka daga sama sukace
"murna!!!" sannan suka saka cikin baki suna ci suna dariya

"Amma na wajen kaka yau kamin daidai, ashe baya ga qulluwa kanasa mutum farinciki" inji dayan mutumin

Bece komai ba sai Murmushin dayayi yaqara saka wani chips din a baki

"amma ka burgeni *deen* gwara daka jefa shegiya cikin chakwalon, ba ita yar iska ba?" inji na farkon

"wlh, ai bakaji dadin danajiba, ina class aka kirani da gudu na iso wajen don baxan bari abani lbr ba" inji macen tana dariya

"yo dama ai wanda bega show dinnan ba yayi rashi, duk fulakun dai yau itace dame2 cikin mud, dama ai ance qarshen alewa qasa"


"O'O! Be kamata kuna cewa haka ba, idan kune bazaku so haka ba, kuma kakata tace Annabi (s. a. w) yace kasowa dan uwanka abinda zaka sowa kanka" yafada yana zaro wani chips din

Dariya sukayi gabadaya sannan daya daga cikin mazan yace "idan hakane kai meyasa ka jefata chakwalin?"

Saurin dagowa yayi ya kalleshi yace
"ni?"

"eh mana, bakai ka jefata ba?"

"O'O! Ni ba jefata nayi ba, ita ta fada" ya amsa cikin son kare Kanshi

"ita ta fada? To waya saki hannunta? Kai kanka kasan da baka saki hannunta ba da bazata fadaba" inji dayan yayinda kingin duk suka kada kai alamun haka zancen yake

"O'O! Itace fa tayimin tsawa, sainaji tsoro na saketa.. kuma dama idan mutum ya Tsorata adrenaline hormones dinshi naqarayin sama hakan zaisa kayi abu cikin fitar hayyaci ko wanda ya girmi tunaninka, shiyasa bansan sadda na saketa ba. Kuma itama tsawar datayi tana iya zama cutuwa gareta, yana iya sa muryarta ta shaqe ko maqogaronta yayi zafi kuma..."

"yanzu dai *Deen* ya isa haka kafin mukai magariba kana kwararo zance don nasan halinka, kuma aimu bacewa mukai kaine mai laifi ba, ai Allah ne ya kamata, wai kaga iskanci da take tsulawa a school dinnan kuwa? Ta raina kowa, gani take kowa trash ne shiyasa bata ganin kowa da gashi akai"

Macen tace
"ga girman kai, yadda take daukar kanta kamar irin diyar qarunnan nan, batasan shi arziqi Allah ke badawa ba ga wanda yaso kuma yana iya kwacewa a lokacin dayaso"

"aikuma ta shiga uku don wlh saitayi danasanin zuwanta makarantar nan don yanzu tazama laughing stock, nan gaba zuwa school din saiya gaggareta"

"O'O! Babu kyau rama sharri da sharri, kakata tace idan mutum yayi maka sharri kai ka rama da alhairi, bazaka fadiba saima kaci riba, kuma ai bata ta6a tanka muku ba kawai tana harkarta ne, jijji dakai da girman kai ra'ayinta ne, kuma arziqin da take taqama dashi nasune kubarta tayi mana tunda bata dai cutar dakuba, watarana idan babushi baxatayi ba... Kuma kakata tace Annabi (s. a. w) yace *laa dirara wala dirara* karka cuci wani kaima kuma karka bari acuceka, jijji dakanta da taqamarta bata cutar dakuba ta kowane siga meyasa kukuma zaku so cutar daita?" yafada innocently cikin muryarshi mai tsananin taushi da gardi.

Kallon juna sukayi sannan suka fashe da dariya

Macen tace
"kai dama duk ta inda aka 6ullo maka saika gwalashe mutum"

"ato bakiji takenshi bane, _na kaka hassala mahaqurci, tunzura mahaukaci, Fashe na kan wuya_"

Duk dariya suka Fashe dashi shidai Murmushin nan nashi yayi yana shan ruwan pure water

"matarka zatasha fama, wai! Kwamacala kenan" inji macen

"saita nemi ayi harka sai kace kaka ta hana" inji dayan

Duk dariya suka sake sawa macen na rufe bakinta da hannu alamun maganar tagirmeta dinnan

"harkar me?" ya tambaya innocently

Dariya suka qara tunzurewa dashi, macen ta tashi tana cewa bada ita za'ayi bankadar nan ba tawuce tana dariya

Suma mazan tashi sukayi suna dariya, daya yace
"au bakasan harkar ba kenan, bari kaka zata gayamaka idan lokacin yazo" yaqarashe yana dariya

"wa? Bari a barshi daga shi sai ita kaga aiki da cikawa ai ire irensu sunfi jaraba alqur'an" inji dayan

"au haba?" na farkon yafada yana bashi hannu

Kashewa sukayi dayan na Cewa "am telling you"

Shidai Deen kallonsu yake yakasa pointing finger akan abinda suke nufi

"to na kaka, zamuyi sama" inji nafarkon

"me zakuyi sama?" inji Deen

Dariya suka qara kecewa daita dayan yace
"kamo tattabaru, kaidai naga sadda zaka waye, muntafi da alamu dai bakada lecture ko? "

Kada kai yayi yace" sai 1:00pm"

"toko zaka rakamu kallon kwallo" inji na farkon cikin neman magana

Girgiza kai yayi yace "A'a kakata tace..."

"Allah sarki, Allah sarki, basai ka qarasa ba, nagane ai. Kai majeed mutafi" yafada yana kamo hannun wanda yakira majeed din suka wuce suna dariya

Binsu da kallo yayi har suka 6acemashi sannan ya maida hankalinshi kan littafin hannunshi yashiga budewa


A bangaren su zee kau kuka taita musu acikin mota dukda kau yadda suke bata hqr suna rarrashinta, jin zuciyarta take kamar a oven don zafi

Abin yaxame mata biyu, ga cin mutuncin mr ibrahim ga na Wannan mutumin da batama san sunanshi ba

Wai waye mutumin nan? Ranan ya fizge mata gyale ya yaga yau kuma ya jefata a ta6o

"wlh Allah bazan yarda ba, wlh saiya gane ya ta6ani, sai yasan kowa ya wulaqanta daga shi har wancan immature ibrahim din, wlh saina koyamasu darasin lifetime!" saikuma taqara Fashewa da wani kukan

Dukkansu qoqarin kumshe dariyarsu suke hakan yasa kowa kauda kai don idan ka ganta dole tabaka dariya tayi gaja2 kamar ba classic zee ba

Rukky ce tayi qarfin halin cewa
"Haba zee? Don Allah kibar kukannan hakanan kar yaja miki ciwon kai, kuma batun koya hankali ai dole ne don wlh saiya san ya ta6a classic girl kamarki" ta qarashe a siffar gaya magana

Itadai bata ce komaiba saima cigaba da kukanta datake don data tuna taqara tunzura

Babu abinda yafi 6ata mata rai kamar kalmarshi ta *faduwa kikayi?* idan ta tuni sai taji wani qululun takaici yasake danne zuciyarta

Suma kingin haqurin suka shiga bata suna qara tirata akan karta kyaleshi wlh, ta banbance mashi tsakanin aya da tsakuwa

Itadai kawai jinsu take saidai bata tanka masu ba sai kukanta data cigaba dayi

Saida suka biya ta wani mall daya ta fita tasiyo after dress sannan suka dauki hanyar gida

Koda suka isa budemasu gate akayi, ganin sune yasa hantar cikin bala kadawa don beyi tynanin ganin ta ba yanzu don tace dai da asr zaizo daukarta, To ko takirashi be saniba ne?

Saurin bin bayan Motar yayi don karya qara laifi

Rukky ce tafara fitowa hakan yasa ta sallameshi akan yatafi kawai babu komai

Saida tazura after din acikin Motar sannan ta fito

Bata qara kallonsu ba ta wuce ba gode bare nagode ta shigewarta ciki wanda zata tashi sama

Ta6e baki sukayi suma suka koma cikin Motar nurr ta tada suka fice

Sai anan suka samu damar amayar da dariyar dake cinsu tundazu, aikau sukaitayi kamar sabbin kamu.


Tafiya yake cikin nutsuwa hannayenshi riqeda littatafai, komai nashi cikin sanyi yakeyinshi saidai akwai karsashi

Idan ba sani kayi ba saikayi tunanin tafiyar qasaita yakeyi nan kau haka yake Tafiya naturally
Wata mota tazo dagudu taja burki agabanshi wanda hakan yasashi dakatawa yana jan baya

Sauke glass din Motar akayi wata kyakyawar budurwa ta bayyana

"barka!" tafada

Please Login or Register in order to submit comment