Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fuska tayi lokacin dataji muryar daddynta

"daddy na"

Murmushi mai sauti daddy yayi daga can bangaren yana cewa
"my jewel! Har kun dawo"

Komawa tayi da baya ta kwanta tana lumshe ido tana jin sanyi na ratsa zuciyarta

"eh daddy na, nidai daddy na yaushe zaka dawo, i missed you sooo muchhhh"

Dariya daddy yayi daga dayan bangaren yace
"missed you more and more darling, wannan satin naso dawowa amma allah beyiba inajin sai kuma next week qila"


"kai daddy, next week is too far, i can't wait" tafada a Shagwa6e

Dariya yasakeyi yace
"then bari nabaro komai nadawo tunda sweetheart dina bata iya jira"

"but daddy kingin aikin fa?"

"that can wait i guess"

Murmushi tayi tace
"kai daddy"

"yes, ina iya barin komai nazo na ganki inhar Hakan zai farantamiki"

"no daddy tunda ka kusa kabari saika gama sannan kadawo"

"no, bayan kin tadomun tsumin son ganinki? Gobe zaku ganin daga sama, don't tell your mummy about this"

Tashi tayi zaune tana dan wara idanu tace
"wai dad da gaske kake? Daddy am joking please karka taho saika gama abinda yakai ka"

"Sai kiyi, am done talking"


Sai gashi ita takoma bashi haquri yabari saiya kammala abinda yakaishi sannan ya dawo don tasan qaramin aikinshi ne ya taho din muddin Hakan zai sata farinciki

Dama haka yake koda yaushe farincikinta shine nashi, yasha yin abu don farincikinta koda kuwa Hakan na nufin sadaukar da nashi farincikin ne, that's daddy for you


Dakyar tasamu ya yarda zai zauna din yana mitan zata hanashi ganinta, nan tace indai don ganinta ne suyi video call ba shikenan ba?

Haka kau akayi, nan take sukayi switching din kiran zuwa video call


Sun jima sosai suna wayar sannan sukayi sallama kowanne murmushi a fuskarshi


Izuwa yanzu kaso mafi rinjaye cikin 6acin ranta yabi iska tareda firarsu da daddy

Tashi tayi ta shiga toilet can ta fito hannunta da fuskarta Duk ajiqe

Idanuwanta ne suka sauka akan ledar wayar dake a tsakiyar gadon

Yarfe hannunta tayi ta dawo gefen gadon ta zauna tajawo ledar ta bude ta Fiddo kwalin tana jin ranta na qara 6aci

Bude kwalin tayi taga wayar gatanan kamar ma ba'a ta6a ta6ata ba


Cirota tayi tana jujjuyata a hannunta cikin zuciyarta tana tambayar kanta kodai ya raina wayar ne? Inba haka ba wa za'a ba this kind of kyauta ya mayar? Kodai besan ko nawa take ba? Ko ba kalarta yakeso ba? Ko... Ko... Ko..

Tama rasa abinda zata hasaso again


Danna power din wayar yayi tafara booting

Saida tajira ta bude dakanta sannan tayi swiping

"wow!" tafada ganin tana preparing apps din wanda Hakan ke nufin ko ta6a kunnata beyi ba

Kada kai tayi cikin qunar rai tana dan murmushin takaici

Tarasa dalilin dayasa abin yake 6ata mata rai har haka

Ko don bata ta6a yiwa wani kyauta ba ya maido mata?

Tunawa tayi dasu sumee wadanda kamar dama jira suke, data basu abu zasu amshe suta murna, ta tabbata da daya daga cikinsu taba wannan kyautar da tun ranar inbox dinta zai cika da sms din Godiya harma da kiraye kiraye amma wai shi ko kunnata beyiba


_*mun gode qwarai amma bazan iya amfani da wannan ba, nama riga na chanza wata so no need to worry*_
Maganarshi ta dazu ta fadomata arai

Wai ya chanza wata, badai wannan calculator din yake kira waya ba
Badai akanta yayi rejecting nata ba


Wai kuma to top it all yaqi tambayarta number wayarta

Ita abin ma mammaki yake bata, mutum ba kowan kowa ba sai shegen jin kai da nuna halin ko in kula

Ta tabbata da wani ne tun farko farkon haduwarsu zai nemi digits dinta amma shi be nema ba kuma beda niyyar nema gashi ta bashi a 6agas ko sanin ta bashin beyi ba


Kwafa tayi cikin zuciyarta tana cewa
"you'll come and beg for it, I promised"


πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–



Deen haka ya qarashe Wunin a sanyaye shikuma


Duk iya hasashenshi ya rasa what went wrong, abu daya dayake iya pointing finger akai shine mayar mata da wayan dayayi


To amma shi bega abin fushi akai ba kuma ma kafin ya maida mata ya lura da yadda taqi sake mashi don yaga ko kallonshi ma bata sonyi

Idan ma maida wayar ce shi bega abin fushi anan ba

To be honest bazai iya amfani da waya worth #50,000, waye shi? Dan gidan waye?

And also beson alfarma ko kyauta, yafison yayi amfani da abinshi don yama fi sakewa yayi amfani da abu idan yasan nashi ne amma idan akasin hakane duk saiya ji yakasa sakewa yayi yadda yakeso dashi


Haka ya qarasa ranar cikin rashin jin dadin komai, komai nashi a sanyaye yake yinshi kamar marar lakka dama qaqa lafiyar giwa?



****


Kamar yadda tayiwa kanta alqawari haka take qoqarin yi


Sosai take qoqari wajen ganin ta cire Deen daga cikin tunaninta ta ajiye Saidai fa abin gaba gaba yakeyi yadda kasan qara mata akeyi don kodayaushe abin qaruwa yake with every passing seconds

Abin harya kai ko barci ta kwanta sai tayi mafarkinsu shi da ita in a romantic mood suna fira cikin annushuwa


Tun tana daukar abin wasa har yafara bata tsoro don haka kawai zata zauna tayi zugum ita kadai

Wani sa'in tafara rairo baitin waqa gamedashi batareda ta sani ba


Sosai wannan abin ke damunta don the more take son yakiceshi a zuciyarta the more yake qara mannewa a zuciyar



Kwance take akan gado rigingine idanunta bisa p.o.p ta kafeshi da idanu

Kewa takeji sosai, everything seems boring to her

Ga bata fita don dama Mafi yawancin fitarta school ne to yanzu suna hutu

Ga ba qawaye, no more su sumee gashi babu daddy agida dazai dan debemata Kewa, mummy ce kuma ita sai ahankali

The worst part of it kuma tunani da kewar wanda be damu da itaba daya maqalemata a zuciya yaqi barinta sukuni, fushi take dashi amma kuma idan da abinda tafi son yin arba dashi to shine


Sau biyu mummy na gayamata sunyi waya da kaka harma da Deen din amma ko sau daya be ta6a cewa abashi itaba koba komai atleast su gaisa

Dama haka yake? Tasan yanada ban haushi amma wannan is freeky more annoying

Wani sa'in ma har mammaki take ba kanta idan tashiga irin wannan yanayin na tunaninshi, har tambayar kanta take wai meye ma dslilin liqemashi har haka?
The last time she checked ita mace ce da bata cika damuwa da abu ba, abin ma wai namiji
Ita irin matannan ne masu i don't care manner wanda class dinta ma baya bari kagane if she really cares din amma wannan yana neman gagararta


Tsaki taja tana maida jan lower lip dinta ciki tareda cijewa

_Am a big big girl_

_in a big big world_

_it's not a big big thing_

_if you leave me_

_but i do do know_

_that i do do will.._

_miss you much_

_miss you much πŸ˜”_


Lumshe idanunta tayi sai ganinshi tayi a idanunta yana wannan murmushin nashi mai fito da innocence dinshi

_murmushi.. Kyauta ce_

_murmushi.. Baiwa ce_

_murmushi.. tsani ce_

_kyawu nee!_

_mai qarawa kyawu kyawuu!_

_Haske ne.. mai qarawa fuska annurii!_

_me matso da tazara yai kusa_

_mai zabura duk mai nakkasa_

_mai yad'a manufofi akusa_

_mai matso da nesa taxam kusa_

_somewhere.._

_somewhere.._

_there's someone who dreams of your smiling..._



Bude idanunta dasukayi ja tayi ahankali tana kallon p.o.p din, saikuma tayi murgina tayi ruff da ciki tana rungume pillow a qirjinta


*meke damuna ne?*

*kodai nafara hauka ne?*

*am running mad*

*am crazy*


Ahankali tashiga raira wata waqar

_what's wrong.. With the calmly me?_

_what's wrong with the classy me?_

_what's wrong with the rude me_

_why am i crazy over him?_

_I miss your smile but I miss my own even more._

_am waiting.. Am still waiting_

_Nothing hurts more than waiting since I don’t even know what I’m waiting for anymore._

_I’m not gonna miss you, I’m just going to wait_


_till you realize your mistake._... ✍️


Please kuyi Manage, mura ta addabeni 😀 naso page din yafi haka.

Amun addu'aπŸ‘



Ummin fasihu πŸ§šπŸ»β€β™€οΈ?
8/2/21, 9:35 PM - Buhainat😝: *πŸ™πŸ»β€β™‚οΈDEEN πŸ™πŸ»β€β™‚οΈ?*










*030*






Da sallama yashigo gidan hannunshi riqe da leda mai layi layi guda biyu kowacce a hannu guda

Qara sallamar yayi lokacin daya ida Shigowa tsakar gidan don yasan ba'aji na farkon ba don dama qaida ne idan zai shigo gidan sai yayi sallama sau biyu ko uku saboda yadda muryarshi take, sai yana kusa akeji


Amsa sallamar kaka tayi daga cikin daki Hakan yasa yanufi dakin shima

Sallama yasakeyi sannan ya shiga dakin

Amsawa kaka tayi tana dagowa daga abinda takeyi

"yauwa kyakyawa na har ka dawo amma kayi sauri"

Zama yayi yana ajiye ledojin yana cewa
"ai sama nadawo shiyasa, nagaji nasha yawo akasuwa ashe geron ya tashi duk inda naje haka suke cemun shiyasa kawai na haqura na siya sai kawai na auno waken tiya daya da rabi maimakon biyu" yafada yana tura mata ledojin

Jawo ledojin tayi tana dubawa tana cewa
"ohni ma'u, yanzu kuma qara mashi kudi akayi, ya akeso tallaka yayi don Allah? Yanzu mun siyoshi haka ya sukeso mu Saida bayan mun sarrafashi? Dama bawata ribar kirki akeci ba ina ga yanzu"

Deen dai bece komai ba don baida tacewa

Maida ledojin tayi bayanta tana cewa allah ya kyauta

Sai kuma tamiqe tsaye tana cewa
"yauwa, dama kai nake jira tundazu, bayan tafiyarka na bubbude kayyayakin nan nasu mummy, bari kaga abinda nagani" tafada tana dauko wata baqar leda ta dawo ta zauna sannan ta turamashi gabanshi tace
"bude kaga ikon allah"


Gyara zama yayi sannan yajawo ledar shima ya budeta ya leqa ciki

Dan waro idanu yayi yana kallon abin cikin ledar sannan ya dago ya kalli kaka dake kallonshi itama

"Kaka, ina kika samu wannan?"

"ina fa bayan cikin kayan wadannan mutanen, nima ina gani na maida na ajiye nace saika dawo zan gwadamaka" inji kaka


Fiddo kwalin yayi daga cikin ledar yana qara BΓ―Γ± sunan wayar dake rubuce 6aro2 a kwalin da kallo

*Spark 8*

Bude kwalin yayi yaciro wayar sabuwa gadagau sai shining take kalar dark blue sai bluetooth dinta da charger sai script dinta dake daga qasan kwalin

Jujjuya wayar daketa daukar ido yayi tayi a hannu yana kallonta haka kawai zuciyarshi tabashi wannan aikin zee ne


"kayi shiru bakace komai ba" inji kaka

"me zance kaka? Kinsan ko nawa wannan wayar take?"

"nawa"

"dubu hamsin da takwas fa"

Qwalalo idanu kaka tayi kamar zasu faddo daga raminsu tace
"iyyee?? Dubu nawa?"

"dubu hamsin da takwas shima banida tabbaci ko be qara ba abinda yasa ma nasani don kwanaki dana raka sanusi siyan waya kasuwar tsaitsaye muka tadda wani na cinikin second dinta wai dubu 30 amma mai ita yaqi bari anan ne ma naji yana fadamashi ainahin kudin sabuwarta"

Kaka da Tundazu tayi kasaqe tana jinshi tace
"to kodai dubu biyar da dari takwas yace kaine bakaji ba?"

"kai kaka, ya za'ayi asamu irin wannan wayar dubu biyar? Ko vivo akwai wanda tafi hakan"


Tafa hannuwa kaka tashiga yi sannan ta riqe ha6a

"ni ma'u naga abinda yafi zare tsayi, dubu hamsin! Akan waya shegiya da kawai kira zakayi a kiraka?"

Shiru Deen yayi yana qara Jujjuya wayar

"ca6! Masu kudi na sha'aninsu, dubu hamsin da takwas! Ni ko ta takwas din saman ma ina iya saye? Wlh bazan iyaba koda kuwa filo nakeyi da kudi, waya idan tawuce dubu biyu to akai kasuwa, meye amfaninta? Ka kira a kiraka ne fa, abinda wannan zatayi shine rakani kashi zatayi to meye banbancin? Amma tsabar almubazzaranci shine za'a Fidda dubu hamsin harda takwas a siya wannan yar iskar wayar wanda da yatsu biyu ma ina iya riqeta, yo nabada dubu hamsin ai wlh Saidai abani wanda sai anyi kama kama za'a iya daukarta

Ana babu kudi babu kudi ashe akwai su inda suke, yanzu fa wadannan kudaden tarin wani ne na shekara biyu amma a wofi anba yan danfara sun hadasu da molaqaqen qarfe, banda shirme ma aini banga abin burgewa ba a wayar nan, wayar kutare? Don fa su akayota saboda basuda yatsun dazasu latsa yar latse amma tsabar rashin sanin ciwon kai shikenan sai kowa yabi ayari, mutum da lafiyarshi ya maida kanshi kuturun qarfi da yaji, ni wlh masu ita basu burgeni, idan na gansu yadda kasan na kashesu da mari wlh, mtcheew wlh wasu mutanen basa ta6a wayewa" tafada tana maida numfashin maganar datayi

Shidai Deen be tanka ba kamar yadda ya saba sai bin wayar daya cigaba dayi da kallo

"yanzu ya kake ganin za'ayi?" inji kaka

Ajiye wayar yayi saman kwalin yayi yace
"Kaka kamata yayi a maida masu, Gaskiya abin yayi yawa, koko?"

Shiru kaka tadanyi tace
"kuma fa, amma mu ina muka san inda zamu qara ganin su?"

"ai mummyn tace min zasu dinga dan zagayowa"

"idan basu zagayo bafa?"

"saina ajiyeta har mukoma school sai inba Zainab ta maida masu"

"kuma fa hakane, Gaskiya gwara a maida masu din, abin ai yayi yawa ga wannan ga wannan, inma kyautarce zasu yimaka bada saisu baka kudin ba kayi wani abin mai amfani dasu ba?"

"A'a kaka, bama buqata, abinda sukayi mana ma ya isa, ai sunmana hallaci"

"kuma fa, tunda kaga dukkan zaman mu asibitin nan ko kwandala bamu kasheba da sunan jinyarka, Gaskiya sunyi mana hallaci don ba qaramin zuga kudi sukeba

Asibitin kudi? Ca6 taci sunanta ai don komai na kudi ne, har wannan washe bakin dasuke mana da kulawa duk biyansu akayi, da ba'a biyasu ba basuyi ba, munafukai duk kar nake kallonsu, da zuwa mukayi bamuda ko sisi ko kallo bazamu ishesu ba, harda wannan baqar nass din mai fihilin tsiya kallonta kawai nake dashi kanshi daftan mai sanqo, wannan sanqon duk na son kudi ne, tsabagen munafurci har wani a kula sosai yake kamar irin yafini sonka dinnan, inbanda tsautsayi dama wazakagani a asibiti? Mtcheew

Ai saika je ka ajiye da sunzo abasu tsiyarsu dama ba don Allah sukayi ba, don dai sunsan sune silar komai shiyasa suke wani nan nan damu don mu haqura, yo to dama ai sukeda alhakin biyan kudin asibitin tunda ta dalilin diyarsu abin yafaru.

Mtcheew, bari naje na jiqa geron, kaima katashi kaje ka dauki abincinka yana kicin, babu kyau zama da yunwa rabonka da abinci tun shayin safe, kar qwalsa tazo ta kamaka in shiga uku" tafada tana ficewa daga dakin

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya mamaida komai cikin kwalin yasaka cikin ledar yana jin ba dadi

Shi jima yake wama yasashi amsar kayan jiya din?

Shi idan akwai abinda beso to shine alfarma, inba dole ba be amsa yafison yayi amfani da abinda allah ya horemashi, kuma jiyan ma don mummy ta sauya fuska yasa ya amsa don sosai take mashi kwarjini shiyasa tana Hade fuska yaji be iya yimata musu

Adana wayar yayi sannan ya fito yawuce kitchen kamar yadda tace ya dauki kwanon abincinshi yawuce dakin shi




*BAYAN SATI DAYA*


Zee Batasan komeye kalmar *kewa* ba sai a cikin kwanakinnan


Sosai takejin kewar da har abin yafara bata tsoro


Batada damar yin wani kwakwarar motsi saiya fadomata arai

Tasha tana abu amma ta shagala da tunaninshi ta manta da abinda takeyi

Yanzu har tsoron saukowa cin abinci da mummy take saboda mafi yawancin lokuta Saidai taji mummy ta girgizata tayi sauri ta dawo daga duniyar tunaninshi sai taga ashe dining take

Kokuma haka kawai taita murmushi kamar sabuwar kamu

Mummy tayi maganar tayi fadan akan tafada mata idan wani abu ke damunta amma kodayaushe amsarta dayace, *babu komai*



Kiran wayarshi kau datake tsanmmanin shigowarshi tun ranar dasuka rabu haryanzu shiru

Tayi tunanin tun a ranar daddadare zai kirata don Saida ta samashi sim card har biyu a wayar kuma tayi mashi saving number ta amma shiru

Dafarko tayi tunanin ko aranar be dubaba Hakan yasa ta yanke shawarar jira zuwa washegari sai gashi har aka wuni aka kwana shiru har zuwa yanzu da akayi sati daya

Abinda bata fahimta ba anan shine, saqonne beje mashi ba koko yaje kawai sharewa yayi?


Sau da dama saita dauki waya tashiga contact din ta tsaya tayiwa number quri taji kamar takira amma jin kanta da class dinta ya hana sai jima tayi taji haushin saya tun farko karde ace don tayimashi Hakan yayi wani tunanin daban ko ya raina class dinta


Koyaya wayarta tayi beeping sai tayi sauri ta dauka hoping shine amma to her dissappointment data duba sai taga bashi bane

Tun tana mashi uzuri dazai kira har abin yafara bata haushi

Rannan saboda yadda kanta ya dau chaji da tunaninshi Batasan sadda ta goge number tashi ba cikeda haushi, jitake kamar ta bigi kanta don takaici

Saidai ta goge number ne a wayarta amma tana nan daram a kwakwalwarta

Wani sa'in idan tana latse latsenta awaya bata sanin lokacin da take rubuta number shi Saidai kawai taga ta rubuta, gabadaya duk tabi ta susuce ta rasa meke mata dadi




Yanzu ma zaune take kan dining suna lunch tareda mummy Saidai kawai cin abincin take ba don dadi ba kawai komai ma yanzu haushi yake bata, tarasa meke mata dadi


Dagowa mummy tayi ta kalli zee dake sipping ruwa dake cikin glass cup tace
"kiyi da jiki kigama zaku fita da bala"

Ajiye cup din hannunta tayi tace
"to mummy"

"kuma kafin kuje zaku biya supermarket kudan yimasu sayayya, naso ace dani za'a amma am busy don yau order na zai iso, kice duk ina gaidasu, kicema kaka insha allah zanshigo kwanan nan"

Cokalin da tayi niyyar kaiwa baki ta dakatar ta dago tana kallon mummy ido waje

Kallonta mummy tayi itama tace
"ya dai?"

"mummy, gidan... Kaka zani?" ta tambaya cikin son gasgata abinda kunnuwanta suka jiyemata

"eh, ko da wani abu ne?" inji mummy tana kafeta da ido

Saurin girgiza kai tayi ta maida kanta kan abincin dake gabanta Saidai turawa kawai take batareda halshenta na banbance mata taste din ba

Tarasa me takeji, dadi ko akasin haka

Jitake kamar karta je don shima shareta yayi dukda yanada hanyar dazai sameta amma kuma qasan zuciyarta cike take da dokin ganinshi, dokin ganin cute innocent face dinshi.



***

Saida ta 6ata lokaci sosai wajen shiri kamar yadda ta saba don ita bata iya simple makeup dinnan ba, tafison ta gyara fuskar tafito fess kamar ka hadiye don kyau


Fitowa tayi daga dakinta ta fara taka stairs tana saukowa qasa


Takunta yasa mummy dake falo riqe da remote ta dago tana kallonta

Sanye take cikin Arabian gown bubu style tasha adon pink agaba sai gyalen gown din pink data yafa akai ta maida jelolin abaya


Hannunta na dama sanye da tsaddadiyar pink agogo sai qaffafunshi dake sanye da pink hill shoes sai yar jaka pink kamar an roqo mai shegen daukar ido irin ta goyawarnan mai dogon hannu ta goyata ta tsayamata daidai tsakiyar baya sai wayarta dake hannunta


Dauke kai mummy tayi daga kanta acikin ranta tana tasbihi ga ubangiji daya hallici wannan baiwar tashi yayi mata komai daidai kamar ita tayiwa kanta

Sosai take alfahari da diyar tata don duk inda mace mai jida kyau da aji takai itama takai, komai nata acan acan kamar ita tayiwa kanta

Qarasowa wajenta tayi ta zauna bisa kujerar dake facing dinta

"mummy am ready" inji zee

Dagowa tayi ta kalleta sai kuma ta dauke kai tana cewa ta miqomata purse dinta dake kan centre table

Tashi tayi ta dauko ta miqamata ta amsa

Bude jakkar tayi ta fiddo wasu kudade tabata tana cewa
"ki siyo fruits haka da drinks kafin ku wuce, extend my greetings to her kice nima zan leqo insha allah"


Amsa zee tayi tana cewa
"ok mummy"

"karku dade, kinayin abinda yakai ki kujuyo, hope am clear"

"to mummy"

"Allah ya tsare"

"amin mummy tafada tana miqewa tsaye ta dan sauko jakkar bayanta ta bude ta cusa kudin ciki sannan ta maida ta goye

"saimun dawo mummy"

"to allah ya kiyaye"

Da amin ta amsa tana ficewa

A harabar gidan ta hango bala wanda dama jiran fitowarta yake

Da sauri yataso ya qaraso motar dazasuyi amfani daita ya bude mata back seat yana mata sannu da fitowa

Amsawa tayi kamar yadda takeyi a yan kwanakinnan sannan tashige cikin motar tana gyara zaman bluetooth dinta ta cikin gyalenta

Maida mata kofar yayi ya rufe sannan ya xagaya shima yashiga motar ya rufo kofar sannan ya tadata yafara reverse


Kamo waqar datakeso tayi ta kunna tanaji ta bluetooth din kunnenta takoma cikin kujerar motar ta lafe tana saurare

Dama haka take, sauraron waqa na daya daga hubby dinta musanmman cool music shiyasa tsabar sonsu datake har qirqirar nata takeyi wani lokacin, da zata shiga studio da ba qaramar fasaha zata zuba ba Saidai bashi ne gabanta ba kawai tana yine for fun


Fita motar tayi daga gidan suka halba saman kwalta

Kamar yadda mummy tace musu Saida suka biya supermarket sukayi musu siyayya sannan suka dauki hanyar unguwarsu Deen.






πŸ’– πŸ’– πŸ’– πŸ’– πŸ’– πŸ’– πŸ’– πŸ’– πŸ’– πŸ’–



Tunda suka shigo unguwar taji zuciyarta ta chanza bugu


Kalle kalle tashiga yi ta tinted window din motar kamar mai son hango wani abu

Jin motar ta tsaya ne yasa zuciyarta ta qara gudu fiyeda kima

"madam bari na d'an tambaya kar ace mun wuto wajen" inji bala cikin ladabi

Kada mashi kai kawai tayi trying so hard to control her heartbeat

Tana jinshi ya bude murfin kofar ya fita ya maido ya rufe

Komawa tayi jikin kujerar motar tana lumshe idanu

_ya sallam! Meke damuna ne? Meyasa zuciyata ke bugawa da sauri_
Tambayar da tayiwa kanta kenan

Anya zuwan nan nata bazai jamata raini ba? Ta bashi waya da number ta aciki da tsanmmanin jin kira daga gareshi amma beyiba gashi kuma ta biyoshi har gida?

Wannan ba zubda class bane?

_ai ba zuwanshi kikayi ba, mummy ce ta aiko ki wajen kaka_
Wata zuciyar ta gayamata Hakan

Kada kai tayi, yes mummy ce ta aikota kuma ba wajenshi tazo ba sai kuma ta furzar da iska takoma ta lafe a kujerar

Bude kofar mazaunin drivern akayi Hakan yasa tadan dago idanu ta kalli bala dake qoqarin Shigowa

"madam na gano, ashe ma mun dan wuto layin amma yanzu zamu koma"

Bata ce komai ba sai maida idanunta datayi ta rufe tana jin yana sake tada motar


Basuyi wata tafiya mai nisa ba taji motar ta tsaya Hakan yasa taji zuciyarta ta tsinke ta fadi

Fita bala yayi daga motar ya zagaya ya bude mata kofar

Saida ta hadiye wasu yawu dasuka taru a maqoshinta sannan ta zuro kafarta tafara fitowa


Wani sanyayar iska ce ta bigi fuskarta Hakan yasa ta lumshe idanu ta sake budesu

Kallon kofar gidan take, tabbass gidan ne don bazai iya 6acemata ba dukda Zuwansu daya

"ina jin nan ne gidan, amma bari mu tambaya" inji bala

Dakatar dashi tayi da
"eh nan ne basai ka tambaya ba"

Dan kallon wasu samari biyu masu wucewa sun wani sakarmata na mujiya tayi sannan ta dauke kai ta nufi kofar gidan bala na binta a baya da ledar kayan da suka siyo

Da sallama suka shiga gidan amma shiru Hakan yasa suka qarasa ciki zee na qara sallama

Jitayi ana amsawa daga cikin daki kuma ta shaida muryar kaka ce

Shiru tayi zuciyarta na cigaba da gudu tana jiran taga ta inda za'a bullo

"maraba!!" suka sake jin muryar kaka tana daga labule ta fito

Jan burki kaka tayi tana qwalalo idanu ganin Hakan yasa zee maida nata qasa tana dan murmushi

"wa zan gani kamar Zainabu?" tafada mammaki a fuskarta

Murmushi zee tasakeyi tace
"mune kaka"

"lale lale da baqin ogas, yaushe rabo? Gaskiya yau muna da manyan baqi" tafada tana shigewa daki can kuma ta fito hannunta riqe da tabarma ta baza masu tana cewa
"daki zafi nima sallah takaini ciki kunsan yanzu sirkawa akeyi ga zafi ga ruwa"

Zama zee data cire takalminta tayi tana murmushi tace
"ai ana zafi sosai... Ina wuni kaka"

"lfy qalau lumi aminiya, kwana dayawa"

Murmushi kawai tayi bata ce komai ba

Shima bala gaidata yayi sannan ya ajiye ledar hannunshi kusada zee yace bari yaje ya jirata waje, Kada mashi kai kawai tayi ya juya ya fice

Tashi kaka tayi tana cigaba dayi mata maraba tashiga kitchen can tafito da kofin silba mai murfi ta ajiye mata agaba tace

"ga ruwa Zainabu abu mai tagwayen suna, kun shawo hanya dole maqoshi ya bushe"

Murmushi tayi tadan ja kofin gabanta Saidai bata bude ba tace
"Kaka mun sameku lfy? Ya mai jiki?"

"wlh duk lfy qalau yar nan. Ya bayan rabuwa kuma? Mu bamu san inda kuke ba gashi baku sake zuwaba, munga kaya rannan amma ba hanyar Godiya tunda cikinmu babu wanda yasan ta inda zamu sameku"

_shi jikan naki ya sani ai_ tafada a zuciyarta amma a zahiri murmushi kawai tayi

"yasu

Please Login or Register in order to submit comment