Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya dauki shiru tun bayan sanarwar isowarshi

Miqewa duk mutanen kotun sukayi bayan mai buga guduma ya buga

Saida alkali ya zauna sannan duk suka koma suka zauna

Mai gabatar da qara ya tashi ya gabatar da qarar daza'ayi a lokacin sannan ya miqa takardun ga mai girma mai shara'a

Shiru dakin yayi Saida alkalin yagama yan dube dubenshi sannan ya dago ga jama'ar wajen yace
"kotu zataso lauyoyin 6angarorin biyu su bayyana kansu"


Lauyan su zee ya tashi yafara gabatar dakanshi sannan mai kare su master shima ta gabatar dakanshi


Saida yaqara yan rubuce rubuce sannan ya dago yana bawa Lauyan su zee damar farawa

Lauyan ne ya buqaci su master da zee su fito

Daddy dake gefen zee ya dafa kafadarta cikin qarfafa gwiwa don ganin yadda tabi ta takura kanta, sannan yayi mata nuni da ta tafi

Tashi tayi jiki a sanyaye tanajin idanun mutane akanta ta nufi bayan dan akwatinan ta tsaya inda suma su master da sukayi wujiga wujiga dasu suka tsaya bayan dayan akwatin dake dayan gefen

Saida aka sasu gabatar da kansu suka kuma yi rantsuwa akan fadin Gaskiya sannan aka fara

Gyara zaman rigarshi ta lauyoyi Lauyan su zee yayi sannan ya kalli alkalin yana neman izinin abashi damar yiwa su master tambayoyi

Bashi daman alkalin yayi Hakan yasa ya wuce wajensu master daketa muzurai kamar zasu ci babu

Master yayi facing yace
"zaka iya fadamin yaya sunanka?"


Wani kallon sheqeqe yayi wa Lauyan sannan yace
"dazu toshe kunnuwanka kayi da auduga halan shiyasa bakajiba?"

Buga guduma alkali yayi sannan ya gargadeshi akan ya iya kallamanshi nan kotu ce ba wajen wasan yaraba

Kauda kai yayi yana Gyara tsayuwarshi irin ta tattatun yan tashan nan marassa tsoro, duk jikinsu tabon ciwone don ba qarya yan kwanakinnan dasukayi a cell sun jibgu don iskancinsu ya zarta tunani Hakan yasa duk sadda suka kawo masu iskanci jibgarsu ake kamar kayan wanki kuma Hakan be hanasu fasawa saima abinda yaci gaba shiyasa polisawan ma ke allah allah afara zaman kotun Ayi a yankemasu hukunci sutafi ko sa huta

Lauyan yasake cewa
"Ana tuhumarka kaida tawagarka akan neman yiwa Zainab Farouq Dan Faranshi fyade, meye zakace akan Hakan?"

Gyara tsayuwa yasake yi yana qara babbakewa harda pocketing din hannuwa a aljihu yace
"me fa?"

"ina nufin haka ne ko kanada ja?" inji Lauyan

Yanzun ma Saida yaqara Gyara tsayuwa sannan yace
"inada ja..."

Dagowa zee tayi tana kallonshi bama ita kadai ba harda kingin mahalarta kotun

"ba yunqurin yimata fyade ba kawai mukayi harda ma kisa don da munci nasara da bazamu barta da numfashi ba, kuma ko ayau muka qara samun dama saimun aiwata nufinmu don babu wanda ya isa ya jada master ya zauna lfy" yafada yana qara babbakewa yana muzurai



Qananu qananun magangganu suka shiga tashi a dakin har Saida alkali ya buga guduma sannan aka nutsu

Lauyan ne yaqara cewa
"kenan kun amsa laifinku akan Hakan?"

"da alamu dai kunnuwanka na buqatar likita" ya bashi amsa ataqaice

Qara buga guduma alkali yayi wannan karon a fusace yaqara bigemashi warning akan ya kiyayi harshenshi

Kauda kai kawai yayi bece komai ba

Dan murmushi Lauyan yayi sannan yaqara cewa
"zaka iya fadamana dasa hannun wa wajen taimaka muku don ganin kun cimma burinku?"

"eh zan iya" ya amsa a taqaice

"to muna jinka" inji Lauyan

"qawayenta ne"

"su wa kenan?"

Kamar bazaiyi magana ba saikuma yace "su sumee take ko wa?"

"sumee da wa da wa?"

"ban riqe sunan sauran ba" ya bada amsa a taqaice

Maida kallonshi Lauyan yayi ga alkali yace
"ya mai girma mai shara'a, zanso kotu tabani dama wajen gayyato qawayensu Zainab don amsa wasu yan tambayoyi" yafada yana dan russunawa

Dago kai alkalin yayi daga rubutun dayake yace
"kotu ta baka dama"

Nan kau aka kirasu gaban akwatin tambayar suka fito suka tsaya kusada su master kowacce na matsar qwallar danasani

Tunda suka fito zee ke binsu da kallo tana hawayen da batasan tanayi ba, zafi take ji sosai a rsnta don da ciwo wanda ka yarda dashi ya munafurceka

Suma Saida sukayi rantsuwa akan fadin Gaskiya sannan yafara masu tambayoyi

Suma b@su ba shara'a wahala ba suka shiga fadin Gaskiya suna fadin yadda suke zaune da zee a munafurce dakuma dalilin dayasa suka hada kai dasu master akan ganin bayanta


Sosai zee tashiga matsananciyar mammaki jin saboda Deen suka shiryamata wannan qullin, wai don tana sonshi, wai _*so*_

Jin ta bakin zee akayi itama inda itama ta warwaremasu yadda suke tareda su sumee, ta kuma nuna ita babu wata alaqa ta soyayya a tsakaninsu da Deen kawai abotace kuma ta karatu sannan kuma ta gayamasu abinda ke tsakaninta dasu master ta qarashe da gayamasu makircin da sumee tayi mata ranar da abin yafaru wanda Hakan yayi sanadiyar Fadawa tarkonsu


Saida aka maida akalar tambayar gasu sumee dasu master akan suna da ja akan abinda zee tafada suka nuna basuda ja duk abinda tafada haka yake

Kasancewar babu wanda yaba shara'a wahala a kowanne bangare yasa shara'ar tazo da sauki sosai inda Lauyan ya rufe jawabanshi da ambatar wanda ya taimaki zee wato Deen dakuma halin jinyar dayake ciki yanzu, sannan yayi Godiya yakoma mazauninshi ya zauna


Tsit dakin ya dauka kowa hankalinshi akan mai shara'ar daketa rubuce rubucenshi na fama ana jiran jin me zai yanke, a gefe guda kuma ahalin wadanda ake tuhuma wato su sumee dasu master harsun fara matsar kwalla ta baqinciki tunma kafin a zartar da hukunci

Saida yagama sannan ya dago ya kalli Lauya mai karesu sumee dayayi tsamo2 kamar zakaran da aka tsoma a ruwa yace

"Lauya mai kare wadanda ake da zargi, ko kanada abinda zaka dora dashi?"

Me zece? Bayan duk kowa ya amsa laifinshi, wannan ai tozarci ne agareshi.
Dama sunsan saurin miqa wuya zasuyi suka jajiboshi? Koda su keda laifi ai yakamata su dan ja bawai suyi saurin miqa wuya ba irin haka

Tashi yayi cikin jin haushi, yadan russuna yace
"banida tacewa ya mai shara'a"

Dan rubutu alkali yayi sannan yabashi izinin zama yadan qara rubutun sannan ya dago yana gyaran murya

Duk qara nutsuwa akayi don sauraron abinda zaya zartar


"Abisa hujjoji da aka gabatar dakuma miqa wuya da wadanda ake tuhuma sukayi batareda sunba shara'a wahala ba, zamu yanke hukunci kamar yadda constitution ta gindayar"

Shiru yayi Hakan yasa dakin yaqara daukar deadly silent

"abisa hujjoji dakuma amsa laifikansu dasu summaya Abdallah, nadeeya umar, nuratu shehu da ruqayya muhammad sukayi na munafurci da cin dunduniyar wacce ta yarda dasu dakuma hada kai da wasu don ganin bayanta an yankewa kowaccensu zama gidan yari na tsawon shekaru bibbiyu da tarar naira dubu dari biyar ga kowacce kamar yadda dokar constitution ta...... Da........ ta tanadar"


Dakin shara'ar ne ya dauki hayaniya yayinda su sumee suka fashe da kuka wiwi suna dora hannu akai

Yanzu ma Saida alkali yabuga guduma sannan dakin yadawo normal

Qara gyaran murya yayi don fara karanto hukuncinsu master Hakan yasa dakin qara daukar deadly silent

"A sakamakon hujjoji da kuma amsar laifin dasu Murtala lawal, Aliyu hassan, täjudeen garba, bashiru Ahmad da isma'il muntari sukayi na yunqurin yiwa Zainab Farouq Dan Faranshi fyade da kisa, Hakan yasa aka yankemasu hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru goma goma tareda aiki mai tsanani"

Dakin ne ya kaure da hayaniya wanda Saida alkalin yayi dagaske sannan yasamu akayi shiru


Ya cigaba dacewa

"abisa kuma kalaman barazana dayayi na ko yanzu suka samu dama saisun aikata abinda sukayi niyya an yankemasu zaman gidan yari na shekaru biyar tareda aiki mai tsanani dakuma yarjejeniyar duk abinda ya sameta na ta6a lafiyarta zamuyi holding dinsu responsible sannan suma kowanne zai biya tara na naira dubu dari biyar na tadowa bawan allah ciwon shi mai mugun hadari, idan aka hada da wancan yazama zama gidan yari na shekaru 15 tareda aiki mai tsanani sai tarar kudi naira dubu dari biyar biyar kowannensu, idan akwai wanda wannan hukuncin beyi mashi ba yana iya daukaka qara a supreme court"

Yana gama fadin Hakan ya bubbuga guduma Sau uku sannan ya miqe

Duk miqewa kowa yayi suna hada baki wajen cewa court!!!


Sosai zee ke hawaye tana kallon su sumee daketa rusar kuka kamar zasu shide Saidai su master ko gezau saima muzuran dasuke kamar basu ji hukuncin da aka yankemasu Dakyau ba

Saida alkali yafita sannan duk aka fara fita bayan an tasa qeyar su sumee gaba su master kau polisawa na zagaye dasu don bayan mintuna 30 za'a qara gabatar da shara'arsu na kayan mayen dasuke huldarsu

Sosai wuri ya kaure da hayaniya, masu kuka nayi masu murna nayi haka dai daddy da mummy suka kama zee suka ficewarsu daga kotun gabadaya yayinda sukuma su sumee aka tusa qeyarsu cikin motar gidan yari suna kuka danginsu nayi aka fice dasu daga harabar kotun

Dayawa basu tafi ba saida aka gabatar da dayan shara'ar tasu master inda anan ma an yanke masu hukuncin zaman gidan yari na shekaru goma goma wanda idan aka hada da wadancan sun zama shekaru 25 kenan

Zokaga kuka ga ahalinsu Saidai su ko gezau don sun dake ko a fuska basu nuna wata dakuma ba dukda kowanne taciki na ciki

Haka aka tusa qeyarsu suma cikin motar gidan yari akayi gaba dasu akabar danginsu daketa faman ganin kuka... ✍️


😭wayyo ina team dinsu master dasu sumee? Kufito mutayasu kuka 😭 don yau baqar ranarsu ce


Allah sarki zamuyi missing dinku 😭😫



Ummin fasihu 🧚🏻‍♀?
8/2/21, 9:35 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?*










*028*






Wunin ranar zee yinshi tayi a kasalance, she can't believe su sumee zasu zama prisioners na tsawon shekaru biyu

Dukda ita suka munafunta sai kuma taji tana tausayinsu, yanzu shikenan sun tafi prison suda fitowa sai nan da shekara biyu

Sunyi wasting din karatunsu sunyi tarnishing din mutuncin gidansu


Wannan tunanin yasa ta qarashe yininta a sanyaye tanajin komai baya mata dadi

Da daddare mummy tashigo dakinta ta zaunar daita tashiga yimata nasiha mai ratsa zuciya tana nunamata illar hulda da qawayen banza saboda gudun irin haka, yanzu da allah ya basu nasara akanta da yanzu wani zancen ake

Ta dade tana mata nasihohin kamar yadda tasaba yimata akai akai, abin mammaki sai ji taji nasihohin sun shigeta sosai sa6anin da datake ganin duk salon takura ce irin ta mummy

Saida tagama mata nasihohin sannan ta rufe da addu'a sannan ta umarceta ta tashi ta sauko suci abinci

Tashi tayi jiki a matuqar sanyaye don sosai nasihohin mummy suka qara saukarmata da kasala tabi bayanta suka fita


Koda ta kwanta ma barcin qin zuwa yayi dawuri, sosai nasihohin mummy suka qi barin brain dinta tanata jujjuyasu tana hango tsantsan gaskiyarta aciki

Ahaka barci ya dauketa can cikin dare batareda ta shirya ba.







*WASHEGARI*



Zaune yake a kan gadonshi na asibiti, ya jingina da pillow qaffafunshi a miqe hannunshi riqe da dan qaramin littafin hisnul muslim yana karantawa

A gefe daya kuma kaka ce zaune kan sallaya tana can charbi don gama sallar walha dinta kenan

Duk sunyi nisa a abubbuwan dasuke akayi knocking din kofa

Tare suka dago suka kalli kofa sannan suka kalli juna

Ganin kaka na niyyar tashi yasashi cewa
"bari naje kaka"

Yasan gardama zatayi mashi Hakan yasashi saurin saukowa kafin tayi magana ya nufi kofar


Daidai za'a murda handle din tawaje shima ya murda ya jawo kofar

Kasancewar na wajen be shiryama Hakan ba yasashi yowa gaba Hakan yasa Deen saurin tareshi

Gasping tayi cikin rintse ido cikeda tsoro

Jin an tarota yasa ta bude idanu ahankali nata yafada cikin nashi

Dan wara nata tayi cikin nashi tana saurin janyewa tanajin wani abu na tsirgamata a duk ilahirin jikinta

Shima dan jada baya yayi shima kamar a tsorace yana cewa
"oh... Sorry"


"wai ya naji shiru kamal?" sukaji muryar kaka daga ciki Hakan yasa Deen kallon ciki dukda ba hangen kakan zai iyayi ba

"A'a dama nabude ne saita fado..." qara yasaki sanadin take mashi qafa da zee tayi saurin yi ganin zai saki layi

"kyakyawana?!" inji kaka tana saurin miqewa tsaye jin qararshi

Saurin qarasowa wajen tayi taganshi duqe yana kama kafar da hannu guda yana yarfa hannu sai zee datake duqe itama tana jeramashi sannu a rude don ita batama san sadda ta tareshi da qarfi ba Haka

"subhanallilah! Lfy kuwa?" inji kaka tana duqawa itama tana taya Deen din kama kafar a rude Hakan yasa zee sake daburcewa

"eh... Dama... Kawai turo qofar nayi.. Ashe yana kusa sai ya buge kafar" tafada tana zazzare idanu irin na marassa Gaskiyarnan

6ata fuska yayi yace
"O'O! Ba Haka bane"

Dan waro idanu tayi kafin tayi magana yace
"ba kofa ta bugeni ba" yafada yana cije le6e alamun zafi

"h.. Hakane mana" inji zee tanajin zuciyarta na jumping tana tuna abinda yafaru ranar da ta tareshi daga su master

"A'a ba Haka bane" yafada yana qara tamke idanu alamun zafi

"to garin yaya? Kaida kasan ba cikakken lafiya ke gareka ba, tashi muje ka zauna tukunnan"

Zee data sure Tundazu tayi saurin cewa
"eh.. Eh, tashi muje ka zauna.. Sorry"

Taimaka mashi sukayi ya tashi yana dangyasawa kamar gaske Dariya na cinshi ganin yadda zee tabi ta rude

Har gadon suka kaishi ya zauna yana nishi yana sauraron zee daketa jeramashi sannu kamar ma ba a hayyacinta ba

Zee kau a bangarenta a rude take, tasan halin Deen yana iya cemata ita ta takashi idan ta tambayi dalili kuma yace don tayo gaba zata fadi ya tareta

Ina zata da wannan kunyar? Gashi ita yanzu tsoro ma takeji wani abu yasamu Deen ata dalilinta ganin yadda kaka bata wasa da abinda yashafeshi, afili take nuna qaunarshi tana nuna batason abinda zai ta6ashi Hakan yasa take tsoron wani abu yasake samun shi a sanadin ta gudun ata dalilin ma allura ta tono galma tasan itace wannan yarinyar data watsamashi abu mai sanyi, tasan idan tasan Hakan qila farfesunta zatayi


Kaka ce ke dan matsamashi kafar tana mitan ai dama kicihi yasashi tashi yaje bude kofar, banda gulma meye na zuwa bude kofa a matsayinshi na majinyaci? Ai ga irinta nan


Zee dai anyi tsuru2 tana ta zare idanu tama kasa zama

6ata fuska Deen yayi yace
"O'O! Nifa kaka ba koface ta bigeni ba"


Jin Hakan yasa zee wara idanu sai tayi saurin katsesu da
"kaka ina kwana ya mai jiki? Kinga mummy batazo ba ko? Wlh yau unguwa zataje shiyasa bata samu zuwa ba Amma tace in gaidaki" ta qarashe tana qaqalo murmushi

Jin Hakan yasa kaka sakin wancan zancen tayi murmushi tace
"Allah sarki, mummy ko mutumiyar kirki? Wlh babu komai, ai tana ma qoqari wlh, samun irinta acikin masu kudin yanzu sai an tona, wlh babu komai allah ya saka da alhairi yajiqan mahaifa"

Yaqe zee tayi tana cewa amin tana satar kallon Deen dake 6ata fuska haryanzu

Ganin zaiyi magana yasata qara saurin katseshi da cewa

"ga wannan kaka inji mummy, kuma tace a gaida mai jiki" tafada tana ajiyemata basket din abincin agabanta, da kaka ta lura daita sosai data gane a matuqar daburce take

"ohni ma'u🤔 wannan abu babu ko gajiya, kullum saikun aiko na rana daban na dare daban? Allah dai yasaka da alhairi ya jiqan mahaifa" tafada muryarta na rauni tana jawo ha6ar zani tana rufe fuska

Ganin Hakan yasa tayi saurin kallon Deen dake kallon ta itama

Hade rai tayi tana zaromashi idanu tareda cije haqoranta 😬

Ganin Hakan yasa ya 6ata fuska yana kallonta gira ahade


Ganin kaka ta dago daga kukan kicihinta yasa tayi saurin gyara yanayin fuskarta tana qaqaro murmushi

"zauna mana aminiya, kinyita tsayuwa?"

Sai a lokacin ta tuna da zama Hakan yasa tayi saurin jawo kujerar dake gefe ta zauna tana qara fadada yaqen fuskarta


Don dole zee taita jan kaka da fira don kawar da hankalinta daga kan Deen daketa 6ata 6atan rai don atambayeshi wanda she's very sure idan aka tambayeshin abinda take gudun zai fada Hakan yasa ta dage suna fira da kakar tama mance dawata kunyarta datake ji

A bangaren kaka kau abin nema ne yasamu nan sukayita firarsu abinsu


Deen kau sosai Dariya ke cinshi ganin yadda zee ta dage sai zubo zance take wai duk don karya fadi Hakan ba qaramin Dariya yake bashi ba Saidai yana qoqarin dannewa yana sauraronsu, dayaga tafara relaxing irin tana tunanin ya mance dinnan saiya 6ata fuska yana ta6a kafarshi yayi kamar zaiyi magana Hakan sai yasa taqara saurin jawo wata firar

Sai gashi harda labarin akun gidansu dasuke kiwatawa take bata bayan labarin school dinsu kala2 databata, dama labarin abinda yafaru a kotu jiya shine farko farko da labaran suka qare ne tafara bada duk wanda yazo kanta kawai muddin dai Hakan zai kawar da wancan zancen

Haka Deen yakoma yayi relaxing yana sauraronsu yana ta kyalkyala Dariya cikin zuciyarshi

(kai Deen muna maka kallon ustaz🤭)


Saida ya wajigata son ranshi sannan yaqara 6ata fuska yace
"ouch!!"

Duk juyowa sukayi suka kalleshi, kaka na saurin miqewa tana tambayarshi menene yayinda zee tashiga fargaba sosai

Hade gira yayi yace
"ni kaffafuwana sunyi dayi, nidai zan dan fita na dan yawata"

"yawo kuma? Idan ka kamu da sanyi fa?"

"bafa iska ba ake kaka, bakiga zafi ba ake? Danaji iskan yafara isata saina dawo"

"to kai ina kasani a asibitin nan da zaka yawata? Idan ka 6ace fa?" inji kaka kamar irin allurar nan, wai zai 6ace 🙄

"ai ga Zainab, ita tasan hospital din sosai, nidai wlh nagaji da zama wuri guda" yafada yana narke fuska

Shiru tayi kamar mai nazari sai kuma tace
"to yan dubiya fa? Idan sukazo bakanan fa?" tafada da alamu dai batason yatafi

Shiru yayi kawai amma kana ganin yadda ya maida fuskar baby face kasan kawai haqura yayi ba don yaso ba

Ganin Hakan yasa kaka cewa
"to ai shikenan, amma fa karku dade... Aminiya ai kina iya rakashi ko?" tafada tana maida akalar tambayar ga zee dake sauraronsu Tundazu

Murmushi zee tayi tace
"sosai ma kaka" tafada tana niyyar tashi

Ganin Hakan yasa shima Deen saukowa daga kan gadon cikin jindadi

Saida kaka ta gargadesu akan karfa su dade sannan suka fice


Fitowa sukayi daga dakin zee agaba Deen biye daita sukaita tafiya har suka sha wata kwana da babu mutane sosai Hakan yasata juyowa ta tsaya tana kallonshi hannuwa riqeda kugu fuska a Hade

Jan burki shima yayi yana kallonta trying so hard wajen controlling dariyarshi

"menene?" ya tambaya innocently

"menene? Menene ma zaka tambayeni?" tafada cikin tada jijjiyoyin wuya

"O'O!"

"O'O! Nabi O'O da gudu, kai kenan ba'a sirri dakai, daka bude baki, da nufinka gayamata komai zakayi? Ansamu ta manta amma saboda shegen naci saika tuna mata?"

Yadda ta haqiqice tanata bala'in yasa dariyar dayake dannewa Tundazu taqi dannuwa yashiga kyalkyala abinshi

Sakin baki tayi tana kallonshi saikuma ta jinjina kai ta juya tafara tafiya

Ganin Hakan yasashi saurin binta yana cigaba da dariyar

"look, it's not what you're thinking.. Listen" yafada cikin Dariya yana cigaba da binta

Banza tayi dashi ta cigaba da tafiyarta kamar zata tashi sama don haushi

"hey... Listen mana, please" yasaka fada cikin Dariya yana Binta cikin qoqarin ganin ya taddota

Ganin taqi sauraronshi yasashi yi kamar yayi tuntu6e ya duqe yana Sakin yar qara

Zee dake gaba tana tafiya cikin fushi tayi saurin juyowa ta kalleshi

Ganin shi a duqe ya riqe qafa yana runtse idanunshi yasata waro nata tareda komowa wajenshi da sauri

"hey, are you ok?" Ta tambaya tana tayashi duba qafar

"wash! Zafi" yafada yana yarfe hannu

"a ina? Ina ne wajen?" tafada tana qara duba qafan tana son gano inda ya bige din

Jin shiru yasata dagowa sai gani tayi kallonta yake fuska dauke da murmushi

Tsuke fuska tayi ta tashi cike da jin haushi tawuce, Ganin Hakan yasa shima saurin miqewa yabita yanata mata magana amma taqi sauraronshi saida suka zo wani wuri inda ba jama'a sosai tasamu karkashin wata bishiya ta zauna

Shima zama yayi dan nesa da ita yana maida numfashin biyo tan dayayi

Dagowa yayi ya kalleta yaga danne danne ma take a wayarta

"O'O! Ni menayi to? Why are you strong-headed?"

Ganin yadda ta dago tana gallomashi harara yasashi dan daga hannuwa in surrender yace
"ok, ok. Am sorry, shikenan?"

Bata kalleshi ba kuma bata tankamashi ba

"O'O! Banace sorry ba? What did you want me to do again?"

Harararshi tasake yi bata ce komai ba

"honestly, niba gayamata fa zanyi ba, ke kike ganin haka, i was just kidding you"

Sai a lokacin ta kalloshi tace
"kidding? Ka kusan sa zuciyata ta buga saboda fargaba shine zaka kira Hakan da wasa? Sai gashi nazama ru66a6iyar redio ta qarfi da yaji"

Dariya Deen keyi tunda tafara har takai aya

"but why? Are you that scared of her?"

"fiyeda tunaninka, yadda batason komai ya sameka dinnan idan tasan takeka nayi ai babu kanta"


Murmushi yayi yace
"kibar tsoro babu abinda zatamaki, kakata nada kirki"

"dama aiba kirki nace batadashi ba, Saidai cikin few days dinnan na karanci yadda take sonka kuma bata qaunar abinda zai ta6aka"

"meyasa kikace haka?"

"saboda haka ne, just imagine idan tasan nice na watsamaka coke kwanakin baya, me kake tunanin zai faru?"

Murmushi yayi yace
"babu komai, ai tsautsayi ne kuma kowa yasan tsautsayi"

"no ba tsausayi bane ganganci ne, ni dakai munsan Hakan, ya kake ganin zatayi reacting? Ga kalamanta na ranan nasan reaction dinta won't be good"


"shine dalilin dayasa kikayi fushi?"

"fushi? Cema akayi nayi fushi?"

"A'a kawai ni nasani"

"to baka canka daidai ba" tafada tana harararshi

"to amma meyasa baki zoba ranar da daddare kamar yadda kika saba?"

"saboda banajin dadi ko ba Haka mummy tace ba"

"haka tace kuma tace Hakan ne don haka kika gayamata amma kuma a zahirin Gaskiya ba Haka bane, kinqi zuwa ne saboda abinda kaka tace"

"eh naqi zuwa ne saboda abinda kaka tace amma ba a sigar daka fahimta ba, ni banyi fushi ba, why on earth ma zanyi fushi? Me zaisa inyi Hakan bayan ni keda laifi? Kawai jinkaina nayi very guilty a lokacin naji kamar duk nice silar wahalhallun dakuke sha daga kai har kaka a sanadiyar ciwon nan naka daya tashi Sau biyu duk ta dalili na, abinda yasa nace wahalhallun dakukasha bance da kasha ba don itama kakar zan iya cewa banbancinka daita alokacin shine kai kana kwance unconcious ita kuma she's concious Saidai physically ba emotionally ba

Tinawa nayi da yadda ta damu matuqa, ta yini kuka, every now and then tana dauke hawayen dake sakkomata, a fuskarta naga tsoro, tsoron rasaka wanda kallo daya zaka mata kasan idan wani abu yasameka akwai matsala, ban ta6a sanin tanada surutu ba don da farko ko magana sai takama dole takeyi ko fira ake bata cika sa baki ba Amma kana samun lfy tazama talkative, labari harna saidawa

A lokacin nakama tunanin qila yadda tayi a lokacin dakake a kwance haka tayi wancan karon da na tadomaka ciwon, nasan ga lokacin ma tayi dararen dabata rintsaba

Tunanin halin dazata shiga da wanda kaima yashiga yasa naji guiltiness atattare dani, idan kuma na tuna silar faruwan komai sai inji narasa inda zan saka kaina don guiltiness, shiyasa... Shiyasa ranar naji bana iya zuwa, bana iya zuwa naganta ko naganka don zuciyata tayi nauyi sosai, i can't face you guys"


Deen dake Sauraronta keenly Tundazu yayi murmushi yace
"kibar wannan tunanin, kibar jin guiltiness akan abinda yafaru a ranar, rashin sanine, gashi kina cikin fushi, fushin kuma mai dalili don honestly ko nine akayiwa haka I'll get mad

In 6ata lokaci na inyi important assignment irin wannan wanda shizai zame mani tsani wajen hayewata a wannan subject din, in baje kwalwata inzuba komai wato inyi maqurar qoqari akanshi sannan wani wanda ban tabbatar da ya iyaba yazo ya yaga ya chanza dawani nashi without my permission? Konine zan fusata matuqa kuma komai na iya faruwa, so ni banga laifinki ba kuma koda kaka zataji bazataga laifinki ba don koba komai akwai rashin sani aciki don am perfect sure da kinsan inada pneumonia bazakiyi Hakan ba, so kibar tsangwamar kanki akan Hakan don bakida laifi koda kaka taji barema bazata jiba Saidai idan ke zaki fadamata"

Murmushi zee dake kallonshi Tundazu tayi, wani lokacin idan yana magana kamar bashi ba, idan yaga dama ya dinga abu maturely idan yaga dama ya dinga abin yara, ta rasa gane kanshi

"wa? Rufamin asiri, Saidai ko kai zaka fadamata, yadda take nuna sonka dinnan bana fatan na 6atamata rai ta wannan bangaren"


Dariya sosai yayi ganin yadda tayi da fuska

"waya gayamiki? Kaka nasona kamar yadda kowa keson nashi"

"A'a, na kaka ya zarta"

"be zarta ba"

"ya zarta!"

Murmushi yayi yace
"how?

Please Login or Register in order to submit comment