Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana daga mashi hannu fuskarta dauke da Murmushi

Shima murmushin yasaki yana rungume littatafan a qirjinshi yace
"barka dai ramla"

"ina zakane?"

Dan Wara idanu yayi sannan yace
"gida" agajarce

"ok shigo mutafi" tafada tana budemashi kofa

Kallon inda ta bude yayi sannan ya girgiza kai yana Murmushi

Dan hade rai tayi tace "meye hakan? Bazaka shigoba kake nufi?"

Girgiza kai yayi yace "A'a ngd yanzu zan samu abin hawa"

"nawa abin sauka ne halan?" tafada still bata saki fuska ba

Murmushin nan mai qara qawata qawattaciyar fuskarshi yayi yace
"A'a ina nufin adaidita"

"itama Wannan tana daidaitawa ai, wai deen meyasa kake min haka? Bafa sayar dakai zanyi ba" tafada cikin sigar tsokana

Qara fadada murmushin shi yayi yace
"ai bakiyi kalarsu ma ba"

"To kagani? Shigo mutafi kasa na tsaya kan hanya ko kaka ta hanaka shiga Motar mutane ne?" tafada cikin sigar tsokana tana Dariya

Dagowa yayi ya watsa mata hararar wasa yana dan turo baki sannan ka shiga tareda maido kofar ya rufe

"ato ai nasan halinka ne, komai kaka tace, kaka's boy" tafada cikin Dariya tana jan Motar

Bece mata komaiba sai murmushin daya sakeyi don dama shi murmushin shi yafi maganarshi yawa dukda wani sa'in idan yafara magana sai kasamashi full stop don besan ya taqaita bayani ba, taqarqarewa yake tsakaninshi da Allah yayi qoqarin fahimtar dakai

"ina ne unguwar tamu?" tafada tana dan satar kallonshi

Juyowa yayi ya kalleta yace
"unguwarku kuma? Ni tayaya za'ayi insani?" yafada yana dan Wara eyes

Lumshe idanu tayi ta bude acikin nashi, tana bala'in son innocent look dinshi

"To unguwarku nake nufi" tafada tana maida hankalinta kan kwalta

Daga gira daya yayi alamun aiyo? Sannan yace
"ke ina kika nufa?"

Juyowa tayi tadan saci kallonshi tace
"ina na nufa kuma? Kaike jana koni ke janka? Abeg mallam ina zan kaika don insan ko nawa zan chaza"

Kallonta yayi a mammakince yace
"dama kudi zaki amsa?"

Dariya tafashe daita har tana dukan sterring tace
"sannu dan son banza, nufinka kyauta zankaika? Ca6! Ai gwamnati ta hana aikin banza"

Murmushi shima yayi kawai bece komaiba

"inane?" tasake tambaya

"kofar kwaya wajen A.T.C" ya bata amsa
"wow hanyarmu daya Ni kofar saurii nike wajajen gidan sarki" ta amsa tana shan kwana

Bece komaiba sai Murmushin dayayi, satar kallonshi tayi itama tana murmushin tana ayyana da Allah zai mallaka mata deen da yagama mata komai, komai nashi burgeta yake.

Sanyi shi, muryarshi, murmushin shi, innocence dinshi, kai komai ma

Motar ce ta dauki shiru na wani lokaci kafin tayi breaking silent din da
"gaskiya fa dazu ka bada show, abinda kayi ya farantawa kowa"

Juyowa yayi ya kalleta itama ta juyo ta kalleshi tana Murmushi tareda daga mashi gira daya

Murmushi yayi shima sannan ya dauke kai cikin zuciyarshi yana mammakin yadda kowa kejin dadin abinda yafaru, dama haka kowa ya tsaneta? Sai jiyayi tabashi tausayi

"gwara da ka jefar da hegiya ta6o, ai ta raina uban kowa, ba students ba ba lecturers ba, kamin daidai wlh"

Shikau da be gajuya da kare Kanshi yace
"O'O! Nifa ba jefata nayiba" yafada cikin Jin haushin yadda kowa ke tuhumarshi akan fadawarta ta6on, mutanen dasuka tareshi da Wannan maganar yau basuda iyaka don har abin yafara isarshi

Ganin kamar ranshi ya 6aci yasata cewa "O'O! Nifa bacewa nayi kayi laifi ba ai hskanma dakayi daidai ne" itama tafada cikin salon maganarshi

"ba daidai bane, Ni ban jefata ba, itace tayimin tsawa shine na saketa Batareda na sani ba saboda na tsorata kuma wanda ya tsorata adrenaline hormones dinshi ke hawa yayi abu cikin fitar hayyaci ko abinda ya girmi hankali shiyasa nima bansan na saketa ba" yafada cikin son kare kanshi, yagaji da yadda suke fassara abin, shi harga Allah bakin gaskiyarshi yake fadi don a duniyar nan ya tsani tsawa fiyeda yadda kuke zato don da anyimashi firgicewa yake ya rude

"To ai shikenan tunda ba da gangan kayi ba, bakada laifi ai, Allah ya tsare gaba" tafada ganin fuskarshi ta nuna alamun rashin Jin dadi

Da amin ya amsa ahankali daga nan kuma babu wanda yaqara cewa komai

Cikin dan qanqanin lokaci suka isa unguwar tasu

Daidai makarantar A.T.C din ya sauka, yana shirin fiddo kudin taja motarta tafece tabarshi sagale da baki

Girgiza kai yayi yana wani slight Murmushi sannan yanufi wani mai saida yalo abakin titi ya sayi na hamsin sai agwalumar hamsin sanin kaka na sonta sosai ya bada kudin ya amsa bayan ansaka a leda sannan yayi hanyar gida cikeda doqin ganin kaka... ✍️


Ummin fasihu πŸ§šπŸ»β€β™€οΈ?
8/2/21, 9:31 PM - Buhainat😝: *πŸ™πŸ»β€β™‚οΈDEEN πŸ™πŸ»β€β™‚οΈ?*



*007*



Saboda 6acin rai ko knocking batayi ba bare ayi batun sallama ta murda handle din ta tura qofar tashiga

Bata wani lura da mutum falo din ba tanufi stairs

"ke!" maganar datasata Tsayawa cak kenan daga yunqurin hawan stairs din datayi

Juyowa tayi tana kallon mummy dake bisa daya daga cikin kujerun falon, remote a hannunta

Ajiyar zuciya ta sauke cikin ranta tana addu'ar Allah yasa karta qaramata wani zafin
"mummy? Barka da gida" tafada still tana inda take

Bata amsa gaisuwarta ba sai cewa tayi
"ke yaushe zakiyi hankali zainab? Ki wani fadoma mutum daki ba knocking bare sallama? Which type of manner is this?"

Zuciyarta taqara dagulewa hakan yasa tafara hawaye kamar an bude fanfo

Sakin baki mummy tayi tana kallonta ganin tama zame qasa ta hada kai da gwiwa tana shesheka


Tafa hannu mummy tashiga yi sannan ta riqe ha6a

"zainab lfy qalau kuwa? Abin naki har yakai daga magana sai kuka?"

Bata amsa mata ba kuma bata dagoba sai sheshekar data qarawa volume

"wai badake nakeba!" inji mummy atsawace har saida zee ta zabura

Fashewa da kuka taqarayi ta miqe tahaye sama dagudu cikin kuka

Binta da kallo mummy tayi harta haye sannan ta girgiza kai tanama diyar tata fatan shiriya


Koda tashiga dakin gado tanufa direct tafada akai tana cigaba da kukanta

Jitake komai na duniyarnan beyimata dadi, Gani take babu mai sonta a duniyarnan, kowa burinshi ya cuzguna mata idan ka cire daddy mai son farincikinta

Saida tayi mai isarta sannan ta tashi ta cire kayan jikinta cikeda kyankyami ta jefa a basket sannan tafada toilet ta sakarma kanta shower.



***

Da sallama yashiga cikin soron gidansu, kasancewar akwai wani dan soro(zaure) saikabi taciki sannan kashiga ainahin cikin gidan

Gida ne mai dauke da dakuna biyu sai kitchen dake daga bangaren dama sai kewaye dake daga can qarshen gidan sai tsakar gida mai dan yalwa, gidan dai kallo daya zakamashi kasan na masu rufin asiri ne

Qara wata sallamar yayi bayan ya shigo cikin tsakar gidan don da alama ba'aji na farkon ba, kodayake ya za'ayi aji bayan yana magana ne kamar da Kanshi yake? Ko kadan be iya daga murya ba gashi muryar tanada taushi ba irin husky voice dinnan bane na maza

Jin haryanzu shiru ba'a amsa ba yasashi nufar dan kitchen dinsu ganin hayaqi na fitowa daga ciki da alamu girki ake ciki

A bakin kofa ya tsaya yana kallon wata tsohuwa dake duqe gaban murhu tana hura wutar da iskar bakinta don wutar tamutu sai uban hayaqin daya turnuke kitchen din

6ata fuska yayi yace "O'O!"

Sai alokacin tsohuwar tasan da tsayuwarshi a wajen
"A'a Kamal? Ashe ka dawo?" inji dattijuwar tana miqewa tsaye baki washe

"O'O! Kaka ba nace kibar hura wuta da baki ba?" yafada yana 6ata fuska

Dariya tayi tace
"To Kamal taqi huruwa, ya zanyi?"

Cikin tura baki yazo yawuce ta ya nufi murhun wutar ya ajiye littatafan shi gefe wanda yayi Daidai da daukesu da kakar tayi, ya dauki makwashin shara(parker) ya shiga fifita wutar, saida shima tabashi wahala sannan takama sai a sannan yatashi yabiyo kakar wanda tuni ta fita ya tarda tana ajiye mashi ruwan sanyi data debo daga tulu acikin wani kofin silba akan tabarmar data shimfida mashi
Qarasowa yayi ya zauna still bakinshi a tunzure

Kaka itama zama tayi kusadashi tasa hannu ta shafa tulin sumar Kanshi tana Murmushi sannan tace
"waya ta6amin kyakyawa na?"

Sake kumbura fuska yayi yace
"O'O! Nidai A'a"

Dariya tayi sannan tace
"haba kyakyawa na? Idan kana fushi rage kyau kakeyi, ko kanaso ka koma mummuna kamar ni?"

Saurin kallonta yayi sannan yasake 6ata fuska yace
"O'O! Allah kinada kyau"

Dariya maganar shi tabata tashiga yi tana cewa
"A'a wlh, kaima kasani banida wani kyau, bakaga ni baqa bace?"

Zamewa yayi ya dora Kanshi bisa cinyarta yana jujjuya kai bisa cinyarta cikin shagwaba wanda tayi bala'in yimashi kyau

Itakau Dariya take mashi tana bashi hqr inda kamar qara tunzurashi take don sai qara shagwa6e mata yake

"kai ka tashi kaji, yau abinda kafiso nayi maka" tafada tana Dariya

Saurin miqewa zaune yayi yana dan Wara oily eyes dinshi
"dagaske kaka?" ya tambaya cikin doqi

"bari kagani" tafada tana yunqurawa ta miqe tawuce daya daga cikin dakunan gidan, can kuma tafito riqeda kwano mai murfi tareda plate din roba tazo gabanshi ta dire

Saurin jawowa gabanshi yayi ya bude

Lumshe idanu yayi cikin jindadi ya bude akan alalar dake ta tururi tayi jajur alamun taji taruggu kamar yadda yake sonta.

Washe baki yayi wanda yaba jerrarun fararen haqoranshi damar fitowa yana nuna alamun jingina ga kaka

Tallabe mashi keya kaka tayi tana cewa
"ja'iri kawai, meye anan?" tafada tana daukar ledar gabanshi

Be bata amsa ba sai 6are alalar dayake yi daga cikin leda

Budewa tayi tana leqa ciki, Murmushi tayi tana qara Jin soyayyar jikan nata acikin ranta

Tashi tayi taje ta daurayosu tadawo kusada Deen daya fara aika alalar shi

Haka suka zauna sunaci suna fira cikeda nishadi da annushuwa, kallo daya zakamasu ka hango tsantsar shaquwar dake tsakaninsu

Sai a lokacin nasamu damar qarewa kaka kallo

Baqace kamar dai yadda tafada, don bazaka ida tantance baqa bace sai idan kaga sun jera da Deen da fatarshi ke tass irin wanda ake cewa saika wanke hannu kafin ka ta6a

Batada muni hakama Batada kyau, kawai dai tanada dai tsaka tsaki wataqila harda tsufan datayi yasa baza'a iya tantancewa ba

Kaka a qiyasce takai shekaru sittin da wani abu amma tanada qarfinta don tanayin komai datakeso da kanta, haka zalika akwai zuciyar nema don kullum sai tayi koko da qosai na siyarwa dasafe

Da Wannan sana'ar take daukema kanta da dan jikanta nauyi dukda shima ba azaune yake ba, duk lokacin da babu school ko kuma beda lecture yana zuwa wajen wani carpentary shop dake qasan layinsu inda ake hada kayan furnitures Kama daga kujeru zuwa gadaje na amare.

Ko kadan babu wata Kama tsakanin Deen da kaka don idan bawai sani kayi ba sai kayi mashi daukar balarabe

Yana da kyau, irin kyawun nan mai tafiya da zuciya, komai nashi Daidai kamar shi ya hallici Kanshi, yanada cikar zati da qirar mazantaka don a kallon farko sai kayi tunanin wani jan wuya ne ko daya daga cikin ire iren jaruman nan na littatafan yaqi saidai a zahiri ba haka bane don wani irin mutum ne mai sanyin hali da mu'amala

Beda hayaniya ko kadan, komai nashi yana yinshi ne asanyaye, ma'abocin Murmushi, gwanin ban Dariya uwa uba he's so innocent, beda matsala ko kadan. Ataqaice dai Deen is a cool handsome guy da kowacce mace ke muradin samu a matsayin abokin rayuwa na har abada

Kaka... kaka ce komai na Deen don ko yanzu kuka fara haduwa dashi inhar zaka zauna na 10mins dashi saika fahimci kaka nada mutuqar muhinmmanci agareshi, beda wanda zai maye mashi gurbin kaka yayinda itakuma kaka ta maye mashi gurbin kowa.
Uwa, uba, aboki duk kaka ce. Yana qaunarta fiyeda tunanin mai karatu hakan ma kaka bata da kowa bayan shi kuma batada wanda yafiyemata shi, Ataqaice dai kaka ce duniyar Deen itama shine duniyar ta

Koda yagama harta sauke ruwan data dora a murhu ta sirka mashi takaimashi a bayi.

Saida ya kauda kwanikan sannan yashiga dayan dakin da nake kyautata zaton nashi ne ya rage kayan jikinshi yafito daga shi sai vest da nicker

Wow! Gaskiya Deen ya hadu takoina, ashe dazu kallon tsoro nayimashi?

Sosai mazantakarshi taqara fitowa acikin Wannan shigar, ata cikin vest din kana iya hango broad kirjinshi da flat tommy dinshi mai dauke da packs

Deen irin mutanen nanne masu gargasa wato masu gashi ajiki, hatta hannayenshi da kaffafu gashi ne kwanttace qawace dasu.

Zura slippers yayi ya dauki kwandon wanka yawuce makewayin dake can daga qarshen gidan

Makewayin ba rufi asama irin buddaden nan ne, shiga yayi bayan yayi addu'ar shiga toilet da kaka ta koyamashi ya rufo qofar.

Kaka kau gyara inda sukaci abincin tayi sannan ta zubo ruwa abuta tayi alwallar sallar asr wanda aketa kira, koda tagama saita qara zuba ruwa aciki ta ajiye tashigewarta dakinta

Kaka bata jima da shigewa ba yafito daga bayin riqeda bokitin qarfen wanka da kwandon soson sai qanqame jiki yake, saurin ajiyewa yayi yanufi dakinshi da sauri.

Ba'ayi minti 3 ba yasake fitowa Sanye da jallabiya baqa, yanufi ruwan da kaka ta ajiye ya tsuggunna yashiga daura alwalla.

Tashi yayi bayan yagama yaqara komawa dakinshi befi seconds goma ba yafito Kanshi Sanye da hular tashi da kwakwa fara sai counter dayake qoqarin sanyama yatsarshi

Kaka ce tafito Sanye da hijabi ta kalleshi

"kafayi sauri karka rasa sallar gashi can an kabbara" tafada tana miqamashi kudi

Da to ya amsa sannan ya amshi kudin hannunta yafice bayan yayi mata saiya dawo, da addu'ar dawowa lfy tabishi sannan takoma daki itama

Massalacin beda nisa da gidan su, koda ya isa har anyi ruqu'i hakan besashi zuwa aguje don karya rasa raka'arba, shiga yayi ya Daidaita sahu da wani sannan yatada kabbara lokacin har sun dago, haka yabisu har suka idar da sallar shikuma ya tashi ya kawo daya rasa

Koda yagama komawa yayi ya zauna yana danna counter din hannunshi, saida yaqara mintuna kusan talatin ahaka sannan yayi daily du'a dinshi yashafa.

Saida ya gaggaisa da yan tsirarun da suke cikin Massalacin sannan yafito, nan ma wasu ya iske waje suma saida ya gaida nasama dashi ta hanyar russunawa Daidai shi kuma ta hanyar musabaha, har rige rigen amsamshi dattijen keyi kowa na binshi da kallon sha'awa suma tsararrakinshi har rige rigen bashi hannu suke don su gaisa, saida suka gama gaisawa yajuya yanufi hanyar da zata sadashi da kasuwa don yiwa kaka siyayyar geron kokon jibi da waken qosan gobe idan Allah yakaisu


A bangaren zee kau tunda tashige daki bata qara saukowa ba, ko abinci bata nemaba, dama can batada yawan ci sai gashi abin ya hade da rannan she's in a bad mood hakan yasata loosing apettite dinta taji bata marmarin cin komai.

Zaune take kan gado jingine da kan gadon tana danne dannen waya saidai kallo daya zakamata kasan she's moody

Kwankwasa kofar da'akayi yasata dan dakatawa daga abinda takeyi ta kalli kofar Batareda tace komaiba

Sake Kwankwasa kofar akayi hakan yasata dan yamutsa fuska kafin tace
"waye?"

Ba'a amsa ba sai turo kofar da akayi aka shigo da sallama

Ganin mummy ce yasata sakin fuskarta data daure tamm tana jiran ganin wanene

Qarasowa mummy tayi fuska ba yabo ba fallasa ta zauna gefen gado don zainab ta gyara zama ta sauko kaffafuwanta qasa

"sannu mummy" tafada kanta qasa tana jujjuya wayar hannunta cikin rashin sabo don kwata2 bata sakewa daita yadda yakamata 'ya ta sake da uwa

"yauwa, kinyi sallah ne?" inji mummy tana kallonta

"eh nayi" ta amsa mata

"abinci fa.. Kinci?"

"A'a mummy, banajin yunwa?" ta amsa tana dan yamutsa fuska

"meyasa?"

"hakanan, banada apettite ne"

Ido mummy takuramata na wani lokaci wanda hakan yasa zainab Jinta atakure

"meke damunki?" inji mummy

Kallonta zee tayi sannan ta Girgiza kai tace
"babu komai mummy"

"meyasa kika dawo dawuri bayan kincemin 2:00pm zaki dawo?"

Rolling idanu tayi afakaice acikin zuciyarta tana cewa 'da mummy yar jaridace da duk wanda ta tisa gaba da tambaya ya bani'


"mummy banajin dadine" ta amsa asanyaye

"meya sameki?" inji mummy tana kafeta da idanu

"fever da headache" tafada tana kwa6e fuska

Kai hannu mummy tayi ta ta6a wuyanta saidai babu zafi

Janye hannun tayi ta tashi tana cewa
"tashi mutafi kici abinci kisha magani"

Zata musa taga mummy ta tamke fuska hakan yasata tashi badon tasoba tabi bayan mummy tana turo baki

Tisata gaba mummy tayi saida taci abinci tasha magani sannan ta kyaleta takoma saman.

Duk motsin da zatayi saita tuna abinda yafaru dazu kuma duk sadda ta tuna saita tsinci kanta cikin 6acin rai, yanzu shikenan mutuncinta yagama zubewa a idon wadancan kucakan yan school dinsu, tasan yau itace topic of discussion a school din, shikenan sunga wallenta.

Haka taita juyi a daren ranar ta rasa abinda kemata dadi gashi barcin ma yaqi zuwa, babu abinda kemata gizo sai fuskar Wannan gayen, haduwarsu tabiyu kenan duk bata dadi ba, lallai Wannan karon saita mashi rashin mutuncin da bata ta6a yiwa wani mahaluki ba, saita tozartashi fiyeda yadda yayi mata, da wannan alwashin barci barawo ya saceta


*DEEN*


Suna zaune abisa tabarma suna tsintar waken da Deen yasiyo na qosan gobe yana bata labarin abinda yafaru school yau kamar yadda yasaba kullum sai yabata lbrin abinda yafaru dashi idan yafita, idan shawara zata bashi saita bashi, idan yayi ba daidai ba saitayimashi gyara idan kuma yayi daidai saita yabamashi


Saida yagama labarta mata komai yadda yafaru sannan ya dago ya kalleta ta hasken wutar nepan dake akwai yace
"wai kaka laifina ne?" ya tambaya yana turo baki

Murmushi kaka tayi sannan tace
"eh to, gaskiya tafika laifi saboda ita tayi maka tsawa harka saketa, tayiwu kuma batasan bakason tsawaba amma dukda hakan be kamata tayimaba daga taimako"

Dadi yaji sosai cikin ranshi Jin ta goyi bayanshi hakan yasashi cewa
"kuma fa kaka itace bata kallon gabanta, itace taita biyowa hanyata bayan sai kaucemata nake amma saida ta bagajeni" yaqarashe yana turo pink lips dinshi

"Gaskiya bata kyautaba, kamata yayi ace tana kallon gabanta idan tana tafiya don koba yau ba tana iya zuwa ta fadawa wani abu dazai cutar daita kaga ina amfani?"

Cafewa Deen da duk dadi yakamashi don kaka tanuna bashi da laifi yayi dacewa
"kuma kaka kodayaushe a fusace take, itace fa Wannan dana cemiki tamin tsawa dana cire gyallen ta a bracelet dina, wancan karon ma haka tamin tsawa kuma na gayamata babu kyau zai cutar daita amma kuma taqara kuma fa na gayamata idan tana fushi tayi inhaling tasbih tayi exhaling tahlil amma kinga batayi ba... "

Murmushi kaka tayi tana qara Jin qaunar shi acikin zuciyarta, he's so innocent, maganarshi ma irin ta yarace, idan mutum yaji maganarshi sai yayi tunanin irin wadanda basuda lafiyar kwakwalwa ne amma rass yake kawai halitarshi ce hakan, haka Allah yayishi shiyasa yake bata tausayi don tasan ba qaramin qalubale yake fuskanta awajen mutanen waje ba don suna iya cutar dashi cikin sauqi don Deen mutum ne da duk wanda ya washe mashi baki to masoyinshi ne, yanada sanyi fiyeda yadda akeso kuma tasan hakan ba qaramin raini zai jamashi awurin jama'a ba musanmman a school, qila ma shiyasa yarinyar tayimashi tsawa, wama yasan adadin masu yimashi tsawan?

Wannan tunanin yakawo kwalla a idanunta tayi hanzarin maidasu don tasan daya gansu to an banu don barci na iya gagararshi tasan halinshi sarai, maida hankalinta tayi gareshi don tundazu zuba yake taji yana cewa

"... Kuma idan adrenaline hormones din mutum yaqara gudu yana iya yin abu Batareda yasani ba ko yayi abinda ya girmi tunaninshi amma taqi ganewa" yafada yana 6ata fuska

Murmushi kaka tayi tace
"ai wasu dama basa ganewa, yanzu dai gobe idan Allah yakaimu idan kaje kuka hade kabata haquri kakuma yimata bayyanin kai bada gangan kayiba, kakuma gayamata bakason tsawa, Tsorata kakeyi saigaka ta fahimceka itama ta baka haquri wataqila batasan bakason tsawa bane"

Kada kai yayi cikin gamsuwa yana cewa
"insha Allah kaka"

Haka sukaita firarsu har suka gama sukayi tatar qullun kokon gobe duk suka kai suka adana suka daura alwalla suka yiwa juna saida safe kaka na jaddada mashi yayi addua idan zai kwanta

Kowannensu saida yayi shafa'i da wutri sannan ya kwanta bayan sunyi addu'ar barci


*WASHEGARI*


Tun bayan sallar asuba suka fito suka fara kiciniyar daura koko da qosai
Deen ne ke hura wuta yayunda kaka ke surfa waken kosai

Saida wutar takama sosai sannan ya dauko qatuwar tukunyar dasuke amfani daita wajen yin kokon ya dauraye ya dora yazuba ruwa aciki

Itakuma kaka ta wanke waken ta cire duka hancin yayi tass, tasa a bokiti tasa watsa taruggu da albasa aciki taba Deen dake jiranta don yakai markade

Kafin yadawo harta tsiyaya ruwan qullun ta daddama acikin bokitai plastic ta rurrufe sannan tashiga hura wutar qosai

Wutar bata ida Kamawa ba yadawo, shi ya amshi hura wutar Itakuma tashiga hada qullun qosan.

Saida wutar takama sannan ya dauko kaskon tuyar qosan ya dora ya bulbula mai aciki ya tsugguna tsakankanin wutan biyu yana gyara duk wadda ta ije

Saida kaka tagama buga qullun qosan ya bugu sosai sannan ta dauki kujera yar tsugguno ta zauna gaban murhun qosai lokacin har man yayi zafi tashiga debar kullun da cokali tana sakawa a man

Ruwan kokon na tafasa Deen ya maido bokitan plastic din kusa2 yasake motsasu da miciya wanda suke amfani daita sannan yashiga sheqa kokon.

Izuwa yanzu har anfara shigowa saye, saida yagama ya maida wani ruwan sannan yazo yafara sallamar masu saye yana zubamasu kokon da qosan

Tun masu sayen suna yan tsiraru har sukayi yawa sosai don da an tsame qosai zakaji yaran nata kiran sunanshi, "Yaya Deen na kaza! Yaya Deen ni za'aba! Yaya Deen nine kan layi!"

Shidai saidai yaita Murmushi yana zubamasu kuma be runton layi, yana sane da wanda yariga wani

Ahaka suka saida duka, lokacin har tara takusa, tare suka tsabtacce gidan yashiga wanka agurguje don yanada lecture 10:00am, atsaitsaye yayi break da kokon da suke diba su ajiye Tun tukunyar farko da qosai sannan yayi mata sallama yafice kaka na rakashi da addu'ar dawowa lfy.


Bangaren zee kau qin zuwa school din tayi yau don batasan yadda zatayi facing school din yau ba bayan humuilation din jiya, tasan maidata zasuyi laughing stock susata jin ta muzanta hakan yasata fakewa da batajin dadi taqi zuwa.

Sosai daddy yadamu da rashin lafiyar qaryanta don ranar yafe zuwa company yayi yatsaya ya kula da shalelenshi, itadai mummy zama yar kallo tayi don yabake komai shi keyimata.


A school kau mutane dadama sunzo yau ne don su tunzura *mud queen* kamar yadda suka samata suna

Wasu ma basuda lecture Aranar kawai abinda yakawosu kenan saigashi tabasu gula taqi zuwa makarantar hakan yasa suka fara cewa kunya ya hanata zuwa.

Deen shima dayaje da niyyar bata hqr kamar yadda kaka tace mashi shima yasamu labarin rashin zuwanta, be damu da hakan ba ya cigaba da harkokin gabanshi

A bangaren mr ibrahim kau shima labarin jiya ya riskeshi yadda yaji labarin yasashi sanin abin yafarune bayan fitowarta daga office dinshi, guntun Murmushi yayi acikin zuciyarshi yana cewa somin ta6i kenan, batama ga komai ba yayinda yashiga shiryama yadda zai 6ullomata ya nunamata kowa yaci tuwo dashi miya yasha.


Suma su Alex sun so ganinta yau amma saiji sukayi bata xoba hakan be damesu ba saima cigaba da shiryamata tarkon dasukayi wanda suke fatan ya d'anu kuma tafada tazama prey dinsu (whoo zee baby mai farinjini πŸ˜†)


Wasa2 duk kingin ranakun satin an baza idanu an baza kunnuwa babu zee babu alamunta, nanfa akayi concluding cewa taji tsorone wataqila ma bazata qara zuwa school din ba, kunya yasa bazata iya facing kowa ba.

Sosai Alex ya tada hankalinshi dajin Wannan labarin don sosai ya kwallafa ranshi akanta, master ne ya kwantar masu da hankali cewa ko a qarqashin gadon uwarta ne ta 6uya saisun fiddota sunyi abinda sukayi niyya daita babu mahalukin daya isa ya hanasu.

Bangaren zee kau tana gida duk ranakunnan ta fake da ciwon qarya taqi zuwa saidai duk abubbuwan dake faruwa a school din da magangganun da ake akanta tana sane dasu ta hanyar qawayenta Wato su sumee.

Sosai ranta ya6aci, takuma sake daukar alwashin rama abinda gayen nan yayi mata gashi yanzu da mutuncinta da komai ya zubarmata dashi yaja school din ya gagareta zuwa.

Ranar asabar su sumee sukazo har gidansu zee dubiyar qarya

Zuwansu na uku kenan gidan, koda suka iso babu yabo ba fallasa mummy ta tarbesu don ita haryanzu basu kwanta mata ba dukda idan suna gabanta komawa suke salihan gaske amma kwata kwata basuyi mataba

Zee ta sauko

Please Login or Register in order to submit comment