Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

qasa ta tarbesu tawuce dasu dakinta daya jiqu da kayan more rayuwa

Duk sadda zasuzo gidan nan sai hassadarta cikin ransu taqara farashi don ba qarya zee tayi dace, tanada komai da mutum zai buqata arayuwarnan shiyasa wani sa'in basa blaming dinta idan tana wani abin don yes ta isa tayi ne

Haka suka baje dakin suka shiga koromata bayyanan abubbuwan daya faru a school da batazo ba harda qarin gishiri da maggi don abin yabada taste.

Sosai abin yaqara bata haushi nan ta dauki alwashin saita basu mammaki, zata gwadamasu cewa kunya gaba tabata ba bayaba.

Haka taita banbami suna tirata yayinda naciki ke cikinsu, basu sukabar gidan ba sai can goshin magrib, mummy ta hadasu da turraruka masu kyau da tsada ita kuma zee ta hadasu da kayan kwalama dake tile a dakinta suka jide suka tafi akan sai ran monday idan sun hadu a school.

Bayan tafiyarsu zainab taita saqa da warwara akan yadda zata 6ullowa yan school din, sotake ta gwadamasu cewa tawuce duk inda suke tunaninta

Haka ta qarar da weekend dinta wurin tsara yadda zata 6illowa kowanne dan air dayayi qoqarin kawomata wargi a school din.


*MONDAY*..... โœ๏ธ


NO EDITING๐Ÿ™๐Ÿป


ummin fasihu ๐Ÿงš๐Ÿปโ€โ™€๏ธ?
8/2/21, 9:31 PM - Buhainat๐Ÿ˜: *๐Ÿ™๐Ÿปโ€โ™‚๏ธDEEN*



*008*




*MONDAY*


Zaune suke suna labarin duniya kamar yadda suka saba, saidai bala nayi yana duba agogon hannunshi jefi2, ganin abin yayi yawa yasa security din cewa
"yadai mallam bala? Naga sai wani duba agogo kake tundazu"

Tsaki bala yaja yace
"kaidai bari, wlh tundazu madam takirani akan infito tunda wuri zamu fita amma kalla yanzu kusan awata biyu da zuwa amma babu ita ba alamunta" ya qarashe maganar yana jan tsaki

Dan guntun Murmushi security yayi yace
"indai madam ce kaga fin haka, yanzu haka idan ance bata tashi daga barci ba ba'a gardama, kaidai kawai Allah ya cigaba da bamu haqurin zama da wadannan mutanen"
Tsaki bala yasake ja yace
"amin ai ina ganin rayuwa, wlh da badon ina samu sosai da sana'arnan ba wlh da tuni nabar dan iskan aikin, wlh nikadai nasan wulaqancin danake fuskanta a aikinnan"

"Sai muyita haquri ai tunda Allah yariga ya qaddarta tanan zamu samu abinci kuma inda suke burgeni akwai fita haqqin ma'aikata don wlh nasan kafin kasamu inda ake biyan ma'aikata kamar mu sai kaci kwakwa, ga ci da sha mai kyau, kawai dai matsalar itace madam don Hajiya gaskiya babu ruwanta shima Alhaji sai an ta6amashi madam yake rashin mutunci"

"kumafa da gaskiyarka don wlh suna biyanmu fiyeda yadda yakamata, shiyasa na liqe na nace nake shanye duk wulaqancin da akemin amma wlh wani sa'in yadda kasan mammaketa haka nakeji" inji bala

Dariya sukasa security yace
"ai ina ganin qoqarinka wani sa'in har tausayi kake bani idan naga ka rude kana rawar kafa wajen yimata abu"

Dariya suka sake yi, bala yace
"ba dole ba? Ai nikadai nasan tsiwarta da rashin mutuncinta, duk wanda yasani saidai yabiyo bayana"

Kafin su sake wata maganar suka hango fitowarta, hakan yasa bala saurin miqewa yana cewa
"To lambata ta fito"

Dariya security yayi yace
"aikaudai lambarka ta fito"

Be qara sauraronshi ba yawuce wurin Motar dazai kaita da ita ya bude mata kofar baya tun kafin ma ta qaraso.


Tafe take cikin tafiyar ta ta yanga tana taku daddaya

Sanye take cikin baqar after mai igiyoyi a gaba duk ta daddauresu, kaffafuwanta Sanye da black hills masu tsinin gaske, kanta yafe da siririn veil baqi shima wanda tayi simple yafi dashi

Sai black shade data toshe idanunta dashi, ta saqalo black handbag mai masiffafiyar kyau a hannu dayan kuma riqe da faskekiyar wayarta.

Fadin haduwar datayi acikin Wannan shigar 6ata baki ne don baqi ne ya hadu da farar fata hakan yasata fitowa acikin shigar sosai.

Kamar kullum, yau ma heavy makeup ne a fuskarta saidai glass din idanunta ya rufe kusan rabin fuskar baka hangen komai sai jan qaramin bakinta mai daukeda qananun soft lips wadanda suka qara jaa saboda janbakin dasuka sha.

Zee is the real definition of beauty, tanada duk abinda mace ke muradin mallaka a bangaren hallita.

Zee farace irin tass dinnan wanda harda gudunmawar hutu na irinna masu kudi wajen sa fatar yin tass da sheki

Tanada round shaped face mai daukeda dara daran idanu dasuke farare tass sai dan madaidaicin hanci wanda yayi daidai da fuskarta.

Bakinta yafi komai qanqanta a fuskarta wanda yake dauke da two little lips masu tafiya da mutane


Bakinta da idanunta sunfi komai daukar hankali a fuskarta.

A 6angaren structure kuma doguwace amma ba can ba

Tanada diri mai tafiya da hankalin abokan hallitanmu

Tanada madaidaicin boobs cikkaku kuma tsayayyu sai flat tommy dinta mai Kama da wanda ba'a zubama abinci wanda yaqara taimakawa wajen fiddo shape dinta sosai.

Tanada hips sosai don yafi komai girma a jikinta.

Daga wajen cikinta zuwa waist dinta a tsuke yake sai daga waist din zuwa cinyoyi daya bude yabada curve mai tada hankalin mai kallo.

Tanada hips sosai wanda duk a jikinta yafi tafiya sa hankalin mutane, gashi ta iya sarrafashi yadda yakamata don idan tana tafiya ke dake mace saikin bita da kallo bare akaiga namiji.

A taqaice dai Allah yayi mata baiwar kyau da diri da duk wata mace zatayi alfahari da samun irinshi.



Koda ta qarasa ko kallon bala batayi ba bare ta amsa gaisuwarshi saima shigewa datayi cikin Motar a yangace tareda qamewa a bayan motar.


Rufe kofar yayi yayi saurin zagayawa ya shige mazauninshi shima yarufe nashi kofar ya tada motar tareda janta

Zuwa sukayi suka wuce security da tuni ya wangale musu gate suka fice daga gidan gabadaya.



*UMYU*


kasancewar safiya ce kuma safiyar ma ta monday hakan yasa dalibbai harma da mallaman school din kai kawo a harabar school din kowa na abinda yake gabanshi.

Shigowa motarsu zee tayi cikin harabar school din.

Babu wanda ya lura da ita don kowa harkar gabanshi yake kuma babu wanda yakawoma ranshi ita don tuni sunyi concluding tabar makarantar kunya bazai bari tazoba duba da duk kingin rannakun wancan week din batazo ba.

"Bala... Kayi abinda zaijawo hankalin jama'a akanmu" tafada hankalinta na kan wayar hannunta datake daddanawa

Satar kallonta yayi ta mirror kafin yace
"angama madam"


Kamar kau yadda ta buqata hakan yayi, da wani irin gudu mai tada qura ya qarasa parking space din wanda hakan yaja hankalin mafi akasarin mutanen dake harabar school din.

Kowannensu dakatawa yayi da abinda yakeyi ya maido hankalinshi kacokam akan motar kowanne da tunanin dake mashi kai kawo a zuciya


Murmushi tayi ganin duk taja ra'ayin mutane, hakan yasata ba bala umarnin yafita ya bude mata kofa

Babu musu yafita acikin zuciyarshi yana nema mata shiriyar Allah

Cire shade din fuskarta tayi tareda after dress din jikinta sannan ta ciro bubble gum ta jefa a baki.

Tun fitowar bala mutane suka shiga tsantsar mammaki don sunganeshi sosai, shine drivern zee. Wow! Tagama 6oye 6oyen kenan? Tambayoyin da mutanen harabar sukayi kenan a zuciyoyinsu yayinda duk aka kafe motar da ido anason ganin fitowarta.


Kamar kau tasan cike suke da doqin ganinta don saita ta mula tasha iska sannan ta zuro kafar dama mai dauke da hill mai shegen tsini sannan tabiyota abaya cikin wani irin slow motion

Duk sakin baki sukayi suna kallonta dumpfounded

Sanye take cikin royal blue t-shirt mai guntun hannu sai baqin straight skirt mai tsaga a baya wanda ya taimaka wajen bayyana fararan kaffafunta

Agaban rigar daidai gefen saman boobs dinta na haggu akayi wani logo mai kyau da daukar ido mai daukeda zanen crown ๐Ÿ‘‘, zagaye da logo din kuma aka rubuta *BORN TO RULE*

A bayan rigar kuma aka rubuta *THE MUD QUEEN*

Bude shade dinta tayi sannan ta qwamama fuska tana taunar chewing gum din bakinta ahankali sannan ta amshi handbag dinta daga hannun bala daya fitomata da ita ta sagala a hannu sannan tafara tafiya cikin takunta na sabon salo don Wannan salon yafi wanda tasaba zuwa dashi.

Duk binta da kallo akayi baki sake ganin salon datazo dashi school din yau, babu wanda ya ta6a tunanin haka daga gareta don duk a tunaninsu bazata iya hada ido da kowaba don kunya amma saigashi ta shayar dasu ruwan mammaki ganin iskancinta ma gaba yaci ga sunan datayi printing a rigarta wanda yakamata su dinga amfani dashi wajen tsokanarta, alamun sunan yayi mata kuma bazai 6ata mata raiba.


Babu wanda yayi yunqurin tankamata sai rakata da kallon dasukayi kowannensu dauke da yanayi mabanbanta.

A class suka hade dasu rukky wadanda basu san ta iso bama.

Wara idanu sukayi suna ganinta duk sukaje suka rungumeta cikeda murna inda suka zamo yan kallo ga mutanen class din.

Nan suka fara tambayarta ya tabaro spain din? Kamar yadda suka tsara zasuyi ranar dasuka je gidansu

Cikin shan qamshi take amsawa da alhamdullilah sun dawo Suma kuma gifts dinsu na can na jiransu.

Shigowar lecturer class din yasa duk aka nutsu kowanne yanemi mazauni ya zauna aka shiga gabatar masu da darasin.

Sai wajajen 10:30am suka fito daga lecture din, kai tsaye cafteria suka nufa inda duk inda suka gifta sai an dinga satar kallonsu musannman ma zee da labarin iskancin datazo dashi ya karade school din.

Snacks kawai suka saya da drinks sannan suka wuce wajen usual mazauninsu dake bayan classes.

"wow baby! Amma kinyi yaqa fa!" inji sumee

Dan kalkada manyan idanunta tayi tace "haba?"

Amasawa tayi da
"na rantse, kinga kau yadda ake binki da eyes?"

Murmushi kawai tayi batace komai ba sai sipping din drink din hannunta datayi

"ba dole ba? Ai abinne yazomasu a bazata, basuyi expecting haka daga gareki ba, gaskiya Wannan salon yayi" inji Nurr ta mata jinjina๐Ÿ‘๐Ÿป

"Hmm bar yan iska, ba dai taqamarsu iskanci ba? Zan gwadamasu na damesu na shanye a Wannan harkar, kadan ma suka gani, wlh ba'a isa a maidani laughing stock saidai na maida mutum wlh" ta qarashe tana crossing din kaffafu

"aikaudai babe na, gashi yanzu duk cika bakin da iyayin sun kasa maki komai, dama duk rubace" inji deeya

"To dama me suke iyawa? Nan gani nan bari wlh, duk wanda yaci tuwo damu miya yasha, kuma a sannu zamu koyawa duk mai kawomana wargi a harkarmu, mu bama shiga harkar wani haka zalika duk wanda yashiga harkarmu bazamu kyaleshi ba" inji rukky

"wai waye gayen nan ne?" inji zee tana kallonsu

"Hmm wama yasani? Nidai ban ta6a ganinshi ba sai ranar daya jefarmaki da gyale saikuma ranar da ya jefaki ta6o" inji deeya

Tsaki taja don kalmar _ya jefaki ta6o_ din yabata haushi hakan yasata juyawa ga sauran tace

"waye shi? Waye babanshi? Kuma meyake taqama dashi da har zai shiga gonata" tafada a gadarance

"Gaskiya babu wanda yasan wayeshi acikinmu tunda muma ba saninshi mukayi ba amma fa da alamu dan manya ne idan akayi duba da yanayin gogewar fatarshi da mode of tafiyar shi sai inga Kamar dan manya ne" inji nurr

"nikuma sai inga kamar ba kowa bane duba da yanayin dressing dinshi, yes yanada kyau da fata mai kyau amma hakan baya nufin dan manya ne don akwai qabilun dazakiga sunada kyau sosai da gogewar fata ba don arziqinsu ba sai don haka Allah ya hallicesu, gashi yana behaving somehow, ni sai inga kamar he's not normal" inji sumee

"well, babu ruwana da normalness dinshi ko rashin normal dinshi, kamar yadda babu ruwana da arziqinsu da rashin shi, kawai abinda nasani shine yayi crossing limit dina kuma bazan barshi ba" tafada tana kalkada kafarta data dora kan dayar

"Gaskiya ne, don kyaleshi kamar bude wata qaface ta raini agaremu, yakamata mu dauki mataki gaskiya" inji nurr

"inane department dinshi?" inji zee


"Banace ba amma ina yawan ganinshi abayan office din business admin. He's always lonely, is either ka ganshi yana karatu ko ka ganshi zaune shiru" inji deeya

"kin tabbata?" inji zee

"very sure" deeya tabata amsa

"muje!" tafada tana miqewa tsaye.

Duk miqewa sauran sukayi suma kowacce ta rataya jakkarta suka nufi inda deeya din tace


Cikin sa'a kau suka hangoshi zaune a wajen shi kadai littafi a hannunshi yana dubawa.

Sanye yake cikin farar shirt mai layi layin baqi sai baqin jeans trouser da baqaqen takalmi, sumar Kanshi a dan tuje as usual wanda hakan na faruwa ne ta dalilin yawan hargitsashi dayakeyi da yatsun hannunshi duk bayan lokaci lokaci

Hankalinshi kacokam na kan littafin hannunshi yana nazari shiyasa bema lura da qarasowarsu wajenshi ba

Fitt... Yaji an fizge littafin daga hannunshi hakan yasashi saurin dagowa don ganin waye

Acikin manyan idanunta oily eyes dinshi suka sauka wanda hakan saida yasata Jin wani yarrr ajikinta

Da daddaya yafara binsu da kallo kafin ya miqe tsaye yana cigaba da kallonsu Batareda yace komaiba

"kai a tunaninka kana iya shiga gonarmu katafi scot free ne" inji nurr tana watsamashi harara

Bece komaiba sai idanu daya kafamata wanda hakan yasata kauda nata saboda tsananin kaifinsu

"kai kasan ko wacece Wannan agabanka kuwa?" inji sumee tana nuna zee da ke kallonshi still taqi magantuwa

Maida kallonshi yayi akan zee din da sumee ta nuna still bece komaiba

"To bari kaji, sunanta Zainab Farouq Dan faranshi, diya tilo ga shahararen mutumin nan Dan faranshi, duk fadin school dinnan babu mai arziqinsu, kowa shayinta yake a school dinnan shine zaka rasa abinda zatayi mata sai jefata a ta6o?" inji sumee tana Girgiza

Dauke idonshi yayi daga kan zee ya kalli sumee yace
"ni ban jefata ba, fadawa tayi" yafada cikin cool voice dinshi

Sai a sannan zee ta motsa ta hanyar zaburomashi tace
"ni na fada zakace?! Kawai hakanan zan fada cikin dirty ta6a saboda gani sabuwar kamu ko?!" ta qarasa a tsawace


Saurin jada baya yayi yana dode kunnuwanshi yana cewa
"O'O! Kinga kin fara kuma ko?" yafada yana yamutsa fuska

"kakata tace in gayamaki banason tsawa kuma tace ai laifinki ne, da bakiyimin tsawaba da ban sakeki ba" yafada yana dan turo baki

"ina ruwana da abinda kakar taka can tafada? Kuma tun farko waya kawoka hanyata da har ka bangajeni?!" tafada atsananin fysace, ga yarda ta shirya sotayi da sunzo tafara daukeshi da mari kamar yadda tasaba saidai tana zuwa taji takasa hakan, haka kawai wata zuciyar ke radamata fuskarshi ba'a yita don duka ba

"O'O! Ni ban biyo hanyarki ba, kece kika fadomin a hanyata, nayi qoqarin kauce maki kika bangajeni cos you're too clumsy"

Wara idanunta tayi tace
"what? Ni kake cewa am clumsy?"

Dan 6ata fuska yayi sannan yace
"then why kika fadomin? Nayi qoqarin taimakonki kuma kiya yimin tsawa bayan na riga na gayamaki tsawa na Tsorata mutum kuma idan mutum ya tsorata adrenaline hormones dinshi..."

"Adrenaline hormones din qaniya! Ina ruwana dashi! Kai kasan Wannan ni bansanshiba! Shin kasan ina iya sawa a kulle duka familynku?!"

"harda kaka?" ya tambaya yana dan waro idanu

"harda jika ma! Zan iya sawa a daure duka family dinku har igiya tayi rara kuma babu wanda ya isa ya amsheku" tafada tana nunashi da yatsa

"ai nida kaka ce kawai babu sauran wasu" yafada Hankalinshi kwance

Sosai abin yaqara tunzurata ganin yana son maidata wata 13 14

"kuma ma ai laifinki ne, daga taimako sai kiyimin tsawa? Kuma na fadamiki zai iya cutar dake, ko yasa muryarki tashake ko yajamiki sore throat"

Rukky da tundazu keta faman danne dariyarta tace
"mallam maimakon ka bata haquri har kanada bakin fada tana fada?"

"inbata haquri?" ya tambaya yana maido kallonshi akan rukky din

"Eh mana, ko bakasan tana iya sawa sojoji da yan sanda su kamaka ba?" tafada cikin sigar tsoratarwa

Dan Wara idanu yayi yace
"To ni menayi?"

"na farko ka yagamata gyalle ka jefar, na biyu ka jefata a ta6o"

Bata rai yayi yace
"Ai gyalenta ya sarqaho min bracelet dina kuma nayi nayi incire yaqiya shiyasa naja"

"To wayace kaja? Kasan tsadar gyallen kuwa, atleast sai kayi magana a ciremaka"
Dan tsuke baki yayi yace
"Ni bansan gyalenta neba ai, gani nayi yayi Kama da irin abin tatarmu"

Dariyar dasuke qoqarin dannewa tundazu ya kufcemasu suka shiga yi banda zee data cika tayi famm

"wai Wannan wane irin wukaqanci ne rukky zaki tsaya ki biyemashi kuna hauka?" tafada cikin 6acin rai sannan ta juya wajen Deen dake kallonta tace

"you know what? Just know that you're doomed!" tana kaiwa nan tajuya zata wuce a fusace deeya tayi Saurin kamo hannunta sannan tajuya ga Deen dake kallonshi with his innocent face tace

"kasan wani abu? Wannan dakake gani kawunta commander sojoji ne, baffanta kuma comissioner of police, yanzu haka zuwa zatayi ta kirasu azo a kamaka a tafi dakai can a kulle bazaka qara fitowa ba kuma bazaka qara ganin kaka ba"


Bece komaiba but his look said it all don kallonsu yake cikin fargaba

"idan aka tafi dakai bazaka qara dawowa ba, kaka bazata qara ganinka ba kaima bazaka qara ganinta ba and za'ayi maka horo sosai irinna sojoji" tafada threateningly

Nan ma bece komaiba sai kallonsu dayake

"kanason haka din?"

Girgiza kai yayi Batareda yayi magana ba

"then kayi abinda yakamata" tafada tana mashi nuni da zee naketa cika tana batsewa

Kumbura fuska yayi sannan yace
"Am sorry but kema nan gaba kibar yiwa mutane tsawa"

Kallonshi tayi tana zaro mashi manyan idanunta tace
"Sai nayi tsawan! Sai ka hanani idan kana iyawa!" tafada atsawace

Fuskarshi still a kumbure yace
"O'O! I don't like you!"

"nima cemaka nayi I like you? Kuma ka kaddara nakira sojojin na gama"

Su sumee me zasuyi banda Dariya

"ba nayi apologising ba?" yafada yana rungume hura hanci

"da kayi apologising sai kuma kabani sharadi? Harda wani I dont like you, ni gayamaka akayi I like you?"

Kauda kai kawai yayi yana cigaba da kumburi

Rukky dake Dariya sosai tace
"kagani ko? Ka qara fusatata, she'll call the police"

"but I apologised" yafada cikin kare Kanshi

"yes and you insulted her after that"

Wara idanu yayi yace
"insult? Ni ban zageta ba, I just said I dont like her"

"To ai kamar insult ne awajenta"

"ok Am sorry, shikenan" yafada yana watsa hannaye

"ba shikenan ba" inji Rukky

"what again?" yafada cikin qosawa

"zaka zama boy dinta" inji Rukky

Atare zee da Deen suka waro idanu sukace
"mene???"

"yes! I mean zaka zama errand boy dinta".... โœ๏ธ

Wash! Gaskiya typing beyiba ๐Ÿค• idanuna har yaji yaji suke ๐Ÿฅบ

Not edited ๐Ÿ™๐Ÿป

Ummin fasihu ๐Ÿงš๐Ÿปโ€โ™€๏ธ?
8/2/21, 9:32 PM - Buhainat๐Ÿ˜: *๐Ÿ™๐Ÿปโ€โ™‚๏ธDEEN ๐Ÿ™๐Ÿปโ€โ™‚๏ธ?*





*010*



Ahaka Wannan satin yawucewa Deen cikin takurar zee, kodayaushe cikin takuramashi take Da sashi abubuwa musanmman aike

Shidai Deen iyakarshi kumbure2 da fadin _I don't like her_ a zuciya

A bangaren su rukky kau abin sai yazaman masu kamar comedy don kullum sai sunci Dariya saboda yadda Deen ke fusata zee, kullum da abinda zaiyi mata na quluwa gashi itakuma ba haquri nan da nan takeyin sama

Saboda cin dariyar dasuke na dramar su yasa ko batayi niyyar kiranshi ba saisu matsa mata da tambayar akirashi? Har saitace akirashin, yawan takurawar tata yasa besamun lokacin ke6ewa yayi karatun shi kamar yadda yasaba don yadda kasan gadinshi suke dayazo ya zauna da niyyar karatu zasuzo kiranshi kuma babu yadda ya iya, hakan yake binsu ba don ranshi yasoba.


Kamar kullum yau ma saida sukayi fada sannan yatafi siyomata abinda ta aikeshi, su sumee sai 6a66akar Dariya suke yayinda zee keta huci

"Hhhh Deen mutumin mu, wlh dramar ku na mugun bani Dariya" inji nurr

"Dole ai, wlh dama comedy kukeyi da kunyi kasuwa" inji sumee itama cikin Dariya

"wlh kau, Wannan ko tom & jerry sun shafamaku lfy" inji deeya

Tsaki zee taja tareda yin Kwafa sannan tace
"hmm wlh dani yake zancen, bashi dan rainin sense ba?"

"kema zee banga abin tada jijjiyoyin wuya anan ba, daga yace he dont like you shikenan? Sai kace wanda ya zaga?" inji nurr

Qara zaburowa zee tayi a masifance tace
"kar yayi liking dina mana, dama cewa nayi yayi liking dina? Wlh idan bebar cemin haka ba zan bashi mammaki, tom!"

"ai zee Dole yace baya sonki don bayason tsawa ke kuma babu inda kikafi gwanancewa kamar yin tsawa" inji deeya

"To idan ba tsawa ba me zanyi mashi, zabgegen mutum masha Allah kamar shi ba sense sai iya qule mutane" tafada tana jan tsaki

"hhhh mudai yan kallo, iyaka ayi abin dariya muyi" inji sumee tana Dariya su nurr na tayata

Tsaki taja sannan ta fuskanci deeya tace
"wai ina rukky taje haka shiru?"

"ohon mata, wai qawarta tabi ta amshi expo, kinsan fa gobe ake submiting din assignment din mutumin ki" inji deeya tana Dariya

Tsaki zee taja tace
"Duk tana aikin me ace har kamar yanzu batayi assignment din ba bayan tasan yace 20% ne na exam?"

Ta6e baki nurr tayi tace
"shiririta ko? Ni wlh mr ibrahim yabani mammaki, shida duk magiyar da mukayi mashi qin saurarenmu yayi saigashi rana tsaka ya chanza qudurinshi ya sassafto mana fiyeda yadda mukayi tsanmmani"

"wlh nima abin yana dauremin kai, saidai fa ya sassafto be sassafto ba don Wannan assignment din yaci uban wanda yasaba bamu, ace questions yacika gaba da bayan fliscap? Nidai nayi iya yina na sallama sauran don Wannan ko a google danayi searching answers din duk rikitani sukayi Dole na tsintsinta nabar sauran" inji deeya

Sumee tadan Wara idanu tace
"cewa fa yayi idan ka duba google zai gane"

Ta6e baki deeya tayi tace
"ya dade be gano ba, nufinshi duk mu zamuyi Wannan uban aikin dakanmu kamar masu kwakwalen computer? Halan ke dakanki kikayi?" tafada tana kallon sumee sheqeqe

Itama Ta6e baki tayi tace
"ina? Kawai wani neighbour dinmu naba yayimin shima bana yake graduating, ni saida yagama na duba naga kamar ma duk shirme yayimin dama yafimin Kama da masu kwakwalen kifi masu zama bayan aji, Allah yasa ba shirme ya rubutamin ba don Koda nabashi dafarko yayi kamar be ganeba can kuma ya nuna ya gane"

Dariya duk suka Fashe dashi banda zee data dan Ta6e baki tana jinsu tundazu taqi tankawa

"yo ke kiduba kigani ko shirmen ne mana" inji nurr

"induba inga me? Atleast shi ya iya rubuta shirmen ni ko shirmen ban iyawa gwara na lalla6a nayi submiting hakanan qila idan yaga yadda nacika takardu har biyu ya tausaya yabani maki"

Dariya suka qara tuntsurewa daita deeya tace
"Wato har paper biyu ya cikamiki kenan, Allah yasa ba lissafin bashishikan da ake binshi ba yayi miki a takardu"

Harararta sumee tayi tace
"shegiya yana dan masu kudin zaici bashi?"

"To Allah yasa ba wanda yakebi ba ya lissafa maki a takardu ke kinanan kina jindadi an cikamiki takardu" inji nurr itama cikin Dariya

Bugu sumee takai mata tayi Saurin kaucewa tana Dariya

"ba bakinki ba, bakinki yasari danyen kashi mai wari, ai gwara ni da wadanda basuyiba kwata2"

"su waye basuyiba? To ingayamaki tun washegarin ranar daya bada nayi abuna" inji nurr tana Harararta

"wayayi miki?" inji sumee

"wafa? Koko ance miki kowa mai kwalwar kifi ne irin ki?" tafada tana Harararta itama

Ta6e baki sumee tayi tace
"da dai ba'asan asalin balbela ba da saitace daga misra take, Allah yasa ba zero over kunnuwa zakici ba"

"ba bakin mutum ba wlh, insha Allah saina linkaki maki" inji nurr itama tana Harararta

Dariya duk sukayi sannan deeya ta kalli zee dake sauraronsu tundazu tace
"kefa hajjaju? Kinyi?"

Yatsine fuska tayi tace
"tun shaidan na dan qauye? Ko yanzu akace kule cass zance don yanzu haka yana cikin jakkata"

"kaji manya, Allah yasa kema be baki wahala ba" inji deeya tana dan Ta6e baki

"Allah dai yasa asamu abinda akeso, batun bada wahala kam ai dolene tunda yasanyo mugunta aciki saidai kuma ta Allah bata mutum ba, mudin da akayi don mu sai munci Koda rabi ne saidai uwar diya taji kunya" tafada tana sake Yatsine fuska

"To Allah yasa" inji nurr

"amin dai" deeya ta amsa

Sumee data hango rukky tafe tace
"tofa? Da alamu dai andace Wannan zabga sauri haka?" tafada tana Dariya

Suma duk kallonta sukayi suna Dariya qasa qasa.

Qarasowa rukky tayi wajen tana sauke numfashi

"yane? Halan ta samune" inji deeya tana Dariya

Rukky dake sauke numfashi tace
"tasamu a ina? Kuna nan hankalinku kwance ga dan mutane can za'a kashe"

Gaban zee ya yanke ya fadi ta dafe qirji kamar yadda kingin sukayi

"mene?" inji nurr tana waro idanu

"wlh ga Deen can su tawagar master sun tareshi suna..."

Zaburar da zee tayi ta miqe ya hanata idawa

"mene? Deen? A ina?" ta jero tambayoyin ajere, bata kuma tsaya Jin amsa ba ta figi jakkarta tabar wajen hankali atashe

Suma maramata baya sukayi da sauri kowanne hankalinshi tashe



Sauri sauri gudu gudu ta qaraso inda

Please Login or Register in order to submit comment