Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baya hangenta


Bïñ hannun tayi da kallo tana kallon band din data dauramashi ranar valentine

Saita maido kallonta kan nata itama

Ahankali ta danna dan botton din fuskar abin yakawo wuta
_*DEEZEEN 💞*_

tasake dannawa

_*TOGETHER FOREVER ❤️*_


Murmushi tadanyi ta dago tana kallon Deen jin motar tafara tafiya

Har a lokacin daga mata hannu yakeyi har Saida suka fita daga school din


Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya maida hannayenshi cikin aljihu yana cigaba da bin inda suka bi suka fita da kallo kafin daga baya yajuya yakoma inda yafito.





Tun daga ranar da sukayi magana da daddy tashiga wasan 6uya dashi


Idan tasan yana wuri bata yarda tafito wurin haka ma idan ya ritsata gaisuwa ce kawai a tsakaninsu babu irin wannan wasan nasu


Da farko tayi tunanin itace ta dauke mashi wuta sai daga baya taga ashe shima Hakan take a wajenshi don maimakon ya damu kamar yadda yasaba yi duk lokacin da take fushi akan abu sai taga tayi biris daita kamar ma besan tana yi ba wanda Hakan na nuna alamun babu gudu babu ja da baya a Maganarshi.


Hakan yaqara sakata cikin damuwa, don tasan muddin aka rabata da Deen to rayuwarta ta tagayyara don Deen shine farincikinta, idan babu shi zata qarasa rayuwarta ne babu ko digon farinciki.


Ta rasa yadda zata 6illowa daddy ya fahimceta yakuma fahimci Deen don taga alamun ma kwata2 Deen be yimashi ba don ko Maganarshi bayason ana tadawa a gidan.



Rannan data rasa yadda zatayi saita yanke shawarar samun mummy da maganar

Batasan ra'ayin mummy akan wannan case din ba amma sai taga kamar mummy na son za6inta duba da yadda bata nuna rashin amincewa ba akan Hakan kamar yadda daddy yayi.



Ranar Saida tagama sallar asr sannan ta tashi bayan tagama bitar abubbuwan dazata gayawa mummy din


Direct dakinta ta nufa don bataji fitowarta ba Tun bayan shigarta sallah



Ahankali tafara knocking acikin zuciyarta kau tana addu'ar samun nasara

Tasan idan har mummy ta goyi bayanta to abin zaizo da mugun sauqi don zatasan yadda zatayi convincing din daddy kamar yadda tasaba a abbubuwa da dama.


Saida tayi knocking uku sannan aka bata izinin shigowa


Ahankali ta murda handle din ta tura kofar tashiga da sallama a bakinta


Mummy dake ninke sallayarta ta dago ta kalleta ta amsa sallamarta sannan ta cigaba da ninkinta ta ajiye a ma'ajiyarta.


Qarasowa zee tayi jiki a sanyaye kamar ta allah sannan ta zauna bisa sofa dake dakin


Zama itama mummyn tayi a gefen gadonta tana kallonta, kallo daya zakayimata kasan tana cikin damuwa

"yes? Meya faru ne?" inji mummy a tausashe


Hakan yasa taji zuciyarta na raunana


Shiru tadanyi tana jujjuya abinda zatace sannan ta dago ta kalli mummyn

"mummy... Dama akan.. Maganar Deen ne.." saikuma tayi shiru


Itama mummy shiru tayi tana kallon ta kawai

"mummy, daddy kwata2 yaqi fahimta ta, wai saboda kudi Deen kesona kuma wlh ba Haka bane hasalima shi bema damu da abin mutum ba, idan ma ka bashi baya son amsa.

Deen na sona sosai mummy, bazai ta6a yaudarata ba kamar yadda daddy ke cewa saboda bema san yadda ake yaudarar ba

Babu ruwanshi, he's so innocent, shine silar gyaruwan wasu daga halayena marassa kyau, shi yafara saitani a hanya mai kyau batareda nasan saitanin yake ba.

He's always there for me, yana taimakona a karatu sosai mummy, sosai.

Shi yafara sona tsakaninshi da allah tun kafin ma yasan sona yake.

A school babu mai sona harta wadanda nakema daukar qawaye, duk kowa qina yake sai shi kadai dukda abubbuwan danayi mashi marassa kyau"


Saita fara bata labarin farkon haduwarta dashi dakuma haduwarsu ta biyu da abinda yafaru

Ta cigaba da bata labarin yadda ta maida shi errand boy dinta har zuwa lokacin da case din assignment dinta ya hadasu da kwanciyar asibiti data jamashi

Ta gangaro zuwa yadda suka shirya dakuma yadda yafara nunamata kuskuren da takeyi har ta gangarowa zuwa ranar da abinnan yafaru tsakaninta da master.


Labarin take badawa tana kukan da batama san tanayi ba

Ta cigaba da cewa
"mummy har waya na siyamashi lokacin da za'a sallameshi ganin bayada waya tashi ta fadi a wancan ranar amma yaqi amsa Saida nayi fushi sosai sannan ya amsa kuma bama amfani yake daita ba don tun daga ranar ban qara ganinshi da ita ba

Be ta6a roqona yar biyar ba, kuma bayaso nabashi, ko tashi mukayi daga makaranta Saidai yayi min karyar akwai abubbuwan dazai tsaya yi a makarantar duk don kar nace yazo mu rage mashi hanya.


Mummy tayaya za'ace saboda kudina yake sona? Wlh ni nasani soyayyar Gaskiya yakemin mummy, idan narasa shi bazan ta6a samun wanda zai soni ko rabin son da yakemin.

Please mummy kisa baki, kema ai kinsan halinshi, he's very nice and obedient.

Aunty Feenah ma tasan shi da ita da yaya Auwal suma duk sunce yanada kyawawan halaye don su sukama gayyaceshi a bikin su kima tambayesu kiji, wlh babu ruwanshi, bazai ta6a yaudarata ba mummy"


Tunda tafara maganar mummy ke kallonta

Lallai Zainab, ba qaramin kamu soyayyar Deen tayimata ba, ji yadda tabi ta rikice


Ita dama tun a hospital tafara zargin Hakan amma sanin halin zee na high taste dinta akan namiji shiyasa bata ta6a kawoma ranta soyayyar ce dagaske



Ajiyar zuciya mummy ta sauke sannan ahankali tace
"Zainab, nima nasani, Deen bazai yaudareki ba Amma abinda nakeso kisani shine, baka kwallafawa ranka abu kace dole dole sai abin don Mafi yawancin abubbuwan da mukeso baya zama alhairi agaremu shiyasa allah ke musanya mana da wani abin, idan mukayi hqr sai kiga munci ribar haqurin.


Zanyi mashi magana kamar yadda kika buqata amma kuma inason kisa a zuciyarki koma menene idan har Kamal mijinki ne to saikin aureshi idan kuma ba mijinki bane ko duniyar nan zaki gayyato suyima daddyn magana Hakan bazai faru ba

Abinda nakeso ki dinga yi shine addu'a, ki dinga addu'ar allah ya za6amiki abinda yafi alhairi bawai ki nace Lallai lallai sai shi ba, idan shine yafi alhairi allah ya za6amiki shi idan kuma bashi bane to allah ya musanya miki da wanda ya fishi, kinji ko?


Kada kai tayi ahankali acikin zuciyarta tana cewa insha allah shine ma wanda yafi alhairin


Cigaba da yimata nasiha mummy tayi mai kwantar da hankali wanda Hakan ya rage mata kaso Mafi yawa na damuwar ta kafin daga baya ta sallameta akan zata sameshi tayi mashi maganar, kawai tayi addu'ar allah yasa ya gane don ita tana maraba dashi a matsayin suruki don hallayarshi ta dade tana burgeta.


Da wannan zee taqara samun qwarin gwiwa, tashiga addu'ar allah yasa qarshen case dinnan kenan, allah yasa ya fahimta.




***



Suna Kwance suna dan fira irin na kafin barcin nan cikin nishadi

Mummy nata son yimashi maganar su Deen Amma tarasa ta ina zata fara don a kwana biyun nan ta fuskanci idan akwai maganar wanda ke 6ata mashi rai to na Deen ne


"jiya ma munyi waya da Ummu batool ai tace tana gaisheka wai ta nemi number ka bata shiga" inji mummy


"ita ta nemi number ta Ko ni na nemi number ta? Tunfa shekaranjiya nake neman number ta bata shiga" inji daddy


"nima haka nace mata don nima na nemeta ban samu ba wai ashe layi ta chanza, jiya ma da sabuwar number ta kira"

"ayyah to duk ya suke? Yasu batool?"

"Duk suna lfy lau ai har gaisawa mukayi da batool shi yayan nata ne bayanan yana wajen aiki"

"ai wadannan yaran naso naga lokacin da zasu dinga zuwa nigeria frequently musanmman babban, rabonshi da nigeria ai za'ayi shekara biyar ko?"

"ko fi ma, ai kasan halin aikinsu they're always busy gwara gwara batool ita ana dan zuwa daita dukda itama wani sa'in school na hanata zuwa"


"ai babu komai, insha allah lokaci zan fidda mu kwasa dukanmu muyimusu zuwan bazata"

Yar Dariya mummy tayi tace
"dakau mun kyauta, ai yakamata a dinga tunawa da zuminci ko yaya ne bawai business ba kowanne lokaci"

"to? Dani ake kenan?"

Yar Dariya taqara tace
"ni bance ba Saidai idan tsarguwa kayi"


"har tsarguwar ma nayi tunda nasan dani ake"

Dariya sukayi sakeyi atare


Shiru yadan biyo baya

"diyarka fa nacan, kodayaushe very moody, abinci ma saina tilasta mata takeci, na rasa gane kanta"


Nan take mood din daddy ya chanza

"ai dole kiga Hakan tunda tana can kullum wancan yaron na zigeta"


"Yana zigeta kamar ya?"


"hmm, ai duk motsinsu yanzu akan kunne na yake don tun ranar da mukayi maganar qarshe akanshi daita nasamu balarabe nayi mashi Tambayoyi akansu yace min shidai ada lafiya lau take huldarta ita daya amma daga baya ya dinga ganin yaron na liqemata wai har budemata mota yake idan zata shiga ma Hakan wai harda riqe mata jakka.

Bayan naji daga gareshi na sallameshi na kuma samu wani akan ya dinga samin ido akansu a school din and the same amsa dasamu dana bala harda ma qari wai duk inda zataje yana maqale daita har hotunansu ma Saida ya daukomin don su zama evidence.

Gabadaya ya shiga rayuwarta kullum da irin zugar da yake mata yana huremata kunne yana nuna mata wai sonta yake itakuma dayake she's dull takasa ganewa, mataki zan dauka akai tsatsaura kau, lokaci kawai nake jira" yafada cikin 6acin rai


Kan mummy ya kulle

"ni sai inga kamar wannan duk misunderstanding ne, yaron is very calm and quiet, kamar bazai iya Hakan ba"


"hmm wai ke kenan da kike babba bare ita da take qarama, kice inbar ganin laifinta don bata gane abinda nake nusar daita ba tunda kema gaki kin gaza ganewa"

"ba Haka bane Alhaji, Zainab ta sameni tagayamin komai kuma da gamsu dasu, wlh daddy a kallo daya idan kayima yaron zakasan yanada nutsuwa sosai, bakaga Zainab ta chanza ba taqara hankali a yan kwanakinnan? Tafada min duk shine sila bayan Hakan ga siyarda rayuwarshi dayayi wajen cetonta a wannan incident din nasu a school, da ba don shi ba da wani labarin mukeyi daban yanzu"


Daddy dayayi sakato Tundazu yana jinta ya girgiza kai cikin takaici
"ansha fadamin mata basuda hankali amma ban ida yarda ba sai yanzu.

Wato ta nan kuma ya 6illo? Dama ai shi tallaka be ta6a taimako don Allah ba, dole don ribar kanshi yakeyi Yayinda mu kuma sukeso mu kyautata masu don Allah

To idan maganar taimakon ta dayayi ne yazo yayi naming price dinshi ko nawa yakeso zan bashi, ladar taimakonta dayayi, ba shikenan ba?

Yazo ya fadamin ko nawa yakeso zan bashi amma wlh diyata tafi qarfinshi, diyata matar manya ce!

Kuma shiriya ta allah ce idan baki sani ba, dama can nasha gayamiki yarinta ke damun ta zata bari kece baki yarda ba shine kuma yanzu da shiriryar tazo zaki alaqanta ta da wani can, dama mutum ke shirya mutum ba allah ba?"



Mummy da duk ranta ya jagule akan magangganun da daddy ke fadi tace
"Alhaji ba Haka bane..."

"to yaya ne? Yaro yabi ya kallalameku da qarya da komai kun yarda dashi?

Nifa matafiyine mai shiga jama'a daban daban mai kuma hulda da juma'a masu mabanbantan hallaya.

Na fiku sanin me duniya take ciki.

Ke kanki kinsan case din Alhaji Hassan da surukinshi wanda haryanzu abu yaqi ci yaqi cinyewa

Shima ba ta wannan sigar yazo ba ya kwantar dakai ya ruda diyar mutane aka bashi ita

Yanzu kullum gasucan hanyar court suna sintiri ya danne duka dukiyarta yasa ta chanza komai nata da sunanshi ya handame komai, ko zakice baki san da Hakan ba?" yafada cikin hayayyakowa


Shiru mummy tayi takasa cewa komai

"shifa tallaka a duniya bayada babban maqiyi kamar mai arziqi don gani yake be kamata shi a hanashi ba wasu kuma abashi besan komai ikon allah ne ba muma bamu mukayi wa kanmu ba.

Kullum burinshi tayaya zai ra6emu ya kwashi na kwasa ya gudu

Babu wata soyayya a tsakanin tallaka da mai kudi duk qarya ce don kowacce qwarya da abokin ragayarta.

Idan har kikaga Hakan to akwai cuta aciki musanmman irin wannan case din da ita macen itace mai kudin, dama ace namijin shine mai kudin da da sauki don ana saran zai iya controlling dinta amma a wannan case din fa? Ita kanta kacokam a qarqashinshi take inaga maganar dukiyarta?

Saboda haka na riga na ajiye magana kuma ta ajiyu

Tunda kika ga nayi burus daita dukda nasan halin datake aciki Hakan ya isa ya nuna miki babu gudu babu jada baya a wannan maganar don bazan ta6a barin inzama silar cutar da diyata daya da allah yabani ba.

Don haka taje taita nema, ni ba matsa mata zanyi ta kawo miji dawuri ba, she should take her time wajen Fiddo wani responsible one bazan damu da tsawo lokacin dazai dauka ba Amma batun wannan yaron abu ne da bazai yiwuba wlh.


Kuma shima zan sameshi, zan bashi damar rabuwa daita ta lallama idan kuma yaqi zan gwadamashi true colour dina, zai gane ba kowanne mai kudi ake jadashi a wanye lfy ba"

Yana kaiwa nan ya juya ya gyara kwanciyarshi ya rufe jikinshi har kai ranshi na qara 6aci yana kuma qara jin tsanar Deen a zuciyarshi


Shiru mummy tayi takasa cewa komai, sosai ranta ya jagule taji komai ya sake kwa6e mata, batasan daddy yayi nisa har haka ba, nisan da bazai ta6a jin kiraba inba wani iko daga allah ba.


Gyara kwanciyarta itama tayi ta lumshe idanunta batareda ta qara cewa komai ba ta cigaba da saqa da warwarar wannan rikittacen al'amarin a zuciyarta... ✍️



Ummin fasihu 🧚🏻‍♀?
8/2/21, 9:38 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?*











*047*










*THE PROMISE*










Washegari Zee tayi ta jiran feedback daga wajen mummy amma shiru don ko makamanciyar maganar mummy bata tadomata ba

Haka ta haqura ta wuce school ranar tana tunanin qila bata kaida yimashi maganar ba, haka ta haqura a zuciyarta tana fatan koma da yaushe zata mashi maganar allah ya dorasu a kanshi.



A school ma ranar tare suka wuni da Deen wanda bayada lecture ma kwata2 a ranar kawai zuwa yayi don ita.


Sunyi karatu sosai don yanzu sun koma kamar da karatu suke babu kama hannun yaro don exam is at the corner dukda da dan saura ga lokacin.



Sai bayan zuhr sukayo gida inda su zee ne suka fara tafiya sannan shima daga baya yafito yasamu abin hawa shima ya wuce unguwarsu.


Deen hankalinshi Kwance yake gudanar da al'amuranshi don ko kadan besan abinda ke faruwa ba a 6angarensu zee ba.

He never saw anything like that coming shiyasa yake gudanar da al'amuranshi hankali Kwance.





Ya dade yana daily addu'o'in shi daya saba duk bayan kowacce sallah sannan ya shafa.


Saida ya dan qara yin Jimm a masallacin kafin daga baya ya tashi ya fito.


Babu mutane sosai a wajen masallacin Hakan yasa ya zura takalminshi kawai ya fito daga masallacin don komawa gida don dama shi daga masallaci sai gida, salmanu yasha tsokanarshi wai kamar mace ko irin fitowa wajen mai shayi beyi yadan rage dare yafison daya gama sallar isha'i yakoma ya qunqume gida kamar matar kulle

Shidai be ta6a tanka mashi ba Saidai yayi Dariya kawai a wuce wajen don shi bejin zai iya wannan zaman na majallisar mai shayi duba da yadda kodayaushe wurin ke cike da matasa anata hayaniyar cafta irin nasu na maza, shi idan yaje ma ai ciwon kai zai jama kanshi a banza saboda hayaniyar wajen, gwara shi salmanun dayaga zai iya yayi.




Tun daga nesa ya hangi wata mota parke a daga dayan gefen santarsu daidai gaban gidan Mallam Nasiru


Be kawo ma ranshi komai ba ya cigaba da tahowa kai a qasa yanata lissafe lissafe a zuciyarshi


Daidai yayi hanyar shiga gidansu yaga an dallareshi da hasken motar

Dan juyowa yayi yana kallon motar yana dan kare fuskarshi saboda yadda hasken yayi reflecting din fuskarshi

Kamar kau mai motar ya sani sai gani yayi an kashe hasken

Sake Juyawa yayi zai wuce aka qara dallaro hasken wannan karon harda dan horn Hakan yasa ya qara tsayawa ya juyo yana kallon motar.


Gani yayi an bude murfin mazaunin driver wani ya fito.

Tsayawa yayi yana kallonshi har ya tsallako 6angarenshi ya qaraso wajenshi sai a sannan ya lura da fuskar mutumin, bala ne drivern zee.



Qarasowa bala yayi wajenshi cikin fara'a ya miqa mashi hannu shima Deen ya miqa mashi hannu yana murmushi suka gaisa



"Tundazu muke nan muna jiranka, wani yaro yace mana kana masallaci"


Murmushi kawai Deen yayi tareda Kada kai alamun haka ne

"lafiya dai ko?" inji Deen yana kallon motar dake can gefen titin parke


"lfy qalau wlh, kawai Alhaji ne keson ganinka, mu qarasa idan babu damuwa yana ciki" yafada yana nuni da motar


Qara bin motar Deen yayi da kallo sannan ya kalli bala yayi mashi dan murmushi yace
"ba damuwa, muje"


Atare suka sake tsallakawa dayan barin da motar take suka nufi inda motar ke a parke


Saida suka qaraso sannan bala yayi saurin Qarasowa ya bude back seat saiga daddy ya bayyana a zaune takardar jarida a hannunshi yana dubawa


Jin an bude kofar yasashi Dagowa daga kallon jaridar dayake ya kallesu.


"Gashi nan Alhaji" inji bala yana komawa daga baya yadda Deen zai bayyana ga Alhajin


Ganin daddy yasa Deen jin kunya don be ta6a tunanin shine ba

Fuska dauke da murmushi Deen ya zame qasa ya tsugunna yana gaida daddy cikin girmamawa.


Sai ji daddy yayi wani iri don rabon da ayimashi irin wannan gaisuwar harya mance

Sai kuma yayi saurin kawar da zancen a kanshi yana tuna tattaunawar da sukayi da Alhaji Abubakar dazu har yana cemashi talaka babu abinda bazaiyi ba na kwantar da kai duk don yasamu shiga domin suna iyayin komai don cikar burinsu.



Kawar da wannan tunanin yayi yashiga amsa ma Deen cikin fara'a yana cemashi ya tashi.


Tashin Deen yayi cikin sunkuyar dakai don shi harga allah kunyar daddy yakeji sosai


"zagayo abokina, zuwa nayi mu tattauna" inji daddy cikin fara'a


Gaban Deen yadan fadi da jin Hakan, badai yasan komai ba? Wayyo ya zaiyi da kunya?


Haka dai ya zagayo din kamar yadda ya buqata, ya bude kofar dayan gefen ya shigo ya zauna a darare yana dan wasa da band din hannunshi kamar irin amaryar nan idan ana siyan baki duk yabi ya takura.



Ajiye jaridar hannunshi daddy yayi ya gyara zama ya juyo yana kallonshi yana kallon yadda yakasa sakewa kwata2, sai yadanyi murmushi


"Kamal ko?" inji daddy yana kafeshi da idanu


Dagowa Deen yayi ya dan kalleshi sai kuma yayi murmushin tabbatar da Hakan




"Ina wuni Alhaji" yasake gaidashi a karo na biyu


Dan murmushi daddy yayi yace
"lfy lau, ya mutanen gida?"


"Duk suna lfy lau

"ya school? Ana dai maida hankali sosai ko?"


Murmushi Deen yayi yace
"insha allah daddy"


Shima daddyn murmushin yayi yana Kada kai
"to allah ya taimaka"


Da amin Deen ya amsa trying so hard wajen controlling nervousness dinshi


"dama wata yar magana ce takawoni wajen ka ko ince alfarma"

Dagowa Deen yayi ya kalleshi in surprise sai kuma ya maida kanshi qasa bece komai ba

"naji ance kai abokin yarinyata ne sosai kodayaushe ma kuna tare ko?"

Sake Dagowa yayi ya kalleshi again sai kuma ya sake sauke idanunshi
"eh daddy"


"dakyau, dama wata alfarma nazo nema awajenka akanta nasan kai kadai zaka iya yimin Hakan"

Shiru Deen yayi be kuma dagoba saima jin maganar daddy dayake wani banbarakwai, wai alfarma, ina shi ina yiwa mutum irin wannan alfarma?


"Dama akan Zainab ne, kwanan nan narasa gane kanta gabadaya, ta tsiro wasu hallaye da ba nata ba, bansan inda matsalar take ba ko itace ta chanza ko chanzata akayi oho?"


Qara Dagowa Deen yayi ya kalli daddy saikuma ya sauke idanunshi
"Wani abu takeyi ne?"

"Abubbuwa ma kai, lokaci daya yarinya ta chanza? babu irin wannan biyayyar ta da da jin magana ta, tabar saurarona ma bare tabi abinda nake nunamata"


Hankalin Deen ne yafara tashi kuma Hakan ya nuna a fuskarshi

"ya sallam! To meyasa?"

"nima shine ban sani ba Amma nafi kyautata zaton huremata kunne akeyi don ada ba Haka take ba.


Munyi maganar wani yaro daita, ita tama kawoshi da kanta tace tana so nakuma aminta da Hakan saboda yaron nagarttace ne sosai, yanada kyawawan hallaye ga tarbiya, yana sonta sosai itama tana qaunarshi


Lafiya lau muka tsaida magana da manyanshi akan idan tagama school za'a aura mashi ita

Amma kwatsam lokaci daya Abubbuwa suka fara chanzawa, bata saurararshi yanzu, bata bashi damar ganinta ko yin waya daita.

Tabi ta chanza a yan kwanakinnan duk mun rasa gane kanta, bata sauraron maganarmu sam bare tayi amfani daita kuma da ba Haka take ba, Zainab yarinya ce mai sauraron maganar iyayenta most especially ni amma yanzu ta chanza tayi fatali da duk tarbiyar da muka bata.

Mun rasa yadda zamuyi mata don sosai yaron yake cikin damuwa saboda yana sonta sosai amma duk yadda mukaso ta fahimcemu ko ta fahimtar damu meye matsalar taqiya.

Shiyasa danaji ance kai abokinta ne sosai kusan ma kullum tare kuke yasa na yanke shawarar zuwa wajenka wataqila ka iya abinda ke neman gagararmu"


Tunda Daddy yafara magana wutar Deen ta dauke diff, kanshi yafara jujjuya mashi ahankali, fadin tashin hankalin da zuciyarshi ta fada 6ata baki ne, jin magangganun daddyn yakeji kamar a mafarki


"shiyasa nazo wajen ka, please ka jawo ra'ayinta akan Hakan tunda naji ance kai abokinta ne, kana iya yin abinda mu muka gagara yi, ka kuma samata ido kaga ko wani ke zugata don ni nafi tunanin Hakan, ta yiwu wani ko wata ke zugata yana dorata a keken 6era da nufin kaita yabaro.

Please do this for me, kaji d'ana?" yafada yana kafeshi da idanu cikin son karanto yanayin dake fuskarshi kuma yasamu abinda yake nema don tsagwaron tashin hankaline rubuce all over fuskarshi


"bakace komai ba kamal" inji daddyn still yana kafeshi da idanu


Sai a lokacin Deen yadan qaqaro murmushin yaqe yahau yi

"insha allah daddy.. I'll try my best"

Murmushi sosai daddy yayi cikin nuna farinciki sosai

"yauwa d'ana, naji dadi sosai, allah yayi maka albarka, don Allah ka kulamin daita sosai, ka nusar daita sosai idan ma kaga alamun zugata akeyi to let me know, sai na tabbatar na koyawa munafukin hankali don na tsani munafurci kana gani na nan, duk yadda muke da mutum daya munafurceni to wlh nagama dashi kuma zamu sanya kafar wando daya ne dani dashi"


Kasa dago kai Deen yayi don jiyayi kamar ma dashi yake, gudu sosai zuciyarshi take acikin zuciyarshi yana lissafa cewa kenan shine mai huremata kunnen, da daddy yasan da Hakan da da wane ido kuma zai kalleshi?

Hakan yasashi jin duk ya takura, a zahiri sauraronshi yake amma a badini duk bayama gane abinda yake cewa.

Dakyar dai yasamu yagama magangganun shi yana kuma qara jaddada mashi ya taimaka mashi wajen ganin sun shawo kan matsalar.

Da insha allah kawai Deen ke amsawa batareda ya iya hada idanu dashi ba


Godiya sosai daddy yayi mashi yana Tambayar kaka shikuma yana amsa mashi da tana cikin gida


"to my regards to her"

Sai kuma ya karkata gefe ya shiga lalubar aljihunshi

Shidai Deen besan yana yi ba don kanshi na qasa haryanzu yana sake jujjuya magangganun daddy a ranshi


"ga wannan babu yawa" yaji daddy na fada

Dan Dagowa yayi sai yaga ashe kudi yake miqomashi


Dan murmushi yayi sannan ya girgiza kai ahankali
"A'a daddy, ngd qwarai"


"haba ka amsa mana" inji daddy

"don Allah daddy kabarsu"


"meyasa? Ko sun maka kadan ne?"

Sake Dagowa yayi ya dan kalleshi sai kuma ya sauke idanunshi

"ba Haka bane daddy, kaka batason haka, zatayi fada kayi hqr"


Dan ta6e baki daddy yayi ya maida kudin a aljihunshi

"to shikenan ai, babu damuwa, ngd kaji, please kayimin qoqari akan Hakan"

"insha allah daddy"

"bari mu wuce, dare sai qara yi yake"

"to" inji Deen yana fitowa daga motar dama bai rufe kofar ba


Maido mashi kofar yayi ahankali ya rufe yana mashi sallama da fatan isa gida lfy shikuma daddy ya daga mashi hannu kawai yana murmushi bala yaja motar sukayi gaba



Bïñ motar yayi da kallo harta fice daga layin nasu

Lumshe idanu yayi ahankali ya bude yana jin kanshi na wani irin saramashi.

Meke shirin faruwa ne?

Wanene Zainab keso har aka tsaida maganarsu?

Wake huremata kunne?


Bayada wanda zai bashi duk wadannan amsoshin Hakan yasashi Juyawa jiki a sanyaye yashige cikin gida.



Koda ya shiga Saida kaka ta tambayeshi dalilin dadewarshi awaje yau sai cemata yayi suna dan fira ne da salmanu.


Duk yadda yaso 6oye

Please Login or Register in order to submit comment