Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

qanqame idanunta taff hawaye tana cewa
"Akhie ka kyaleshi, don Allah"


A daidai nan wasu mutane hudu cikin mufti suka iso wajen


I.D card din dasuka nunama su Aymaan yasa suka gane jami'an tsaro ne

Hankalin zee yasake tashi

"you're under arrest" inji daya daga cikinsu yana kallon Aymaan

Fizge hannunshi yayi daga riqon zee a fusace yace
"saboda me? Me nayi?"

"idan munje station zakaji dalili, a shawararce zaifi kyau kayi shiru ka Adana duk abinda zakace har saimunje station don duk abinda kace yanzu will be use against you in the station"


Hankali a tashe zee tace
"sir, ba laifinshi bane, you guys should listen"

"sorry ma'am, aikinmu mukeyi"

Sannan suka maida kallonsu akan Aymaan da yakejin wani abu mai wuyan wucewa ya tokaremashi wuya

"shall we?" suka fada suna nuna mashi hanya

Hannu yasa a aljihunshi ya zaro I.D card dinshi shima yace
"Dr Aymaan, gynaecologist a As-shifa'u specialist hospital.

Zan biyoku amma a motata"

"No.."

Sukaji ance a bayansu

Juyawa sukayi sukaga mussadiq ne da haryanzu fuskarshi ke jajur

Zuwa yayi gaban Aymaan yana kallonshi eye-in-eye

"bazaka tafi a motarka ba, su zakabi"

"nafison idan ina magana da masu hankali kar mai empty kwalwa yayi min trespassing, na tsani shiga muhallin daba na mutum ba" inji Aymaan shima yana kallon cikin idonshi


"zan nuna maka, zan nuna maka ni cikkaken marar hankalinne.. Arrest him!" Yafada authoritively


Zee ce ta matso gaba
"kaga, dani kakeda case bada shi ba, idanma arresting dinne ni za'ayi arresting"

"in that case... A hada da ita" yafada yana maida shade dinshi a idanu sannan ya juya


"Akhie!" inji Aysha cikin tashin hankali amma ko tsayawa beyi ba bare ya kalleta

"let's go please" inji daya daga cikin jami'an yana nuna musu hanya


Juyawa sukayi babu musu suka shiga binsu suna a tsakiyar su


"ummie!" inji Aysha dake kuka sosai saikuma ta ruga wajen mussadiq daya shiga motarshi

Saurin kama murfin motar tayi
"Akhie please ka tsaidasu, gasucan zasu tafi da..."

Kallon daya watsamata yasata kasa cigaba da maganar sai rufe bakinta datayi da taffukan hannu tana cigaba da hawaye

"get in" yafada in a low but angry voice

Bata motsa ba sai kukan data cigaba dayi

"I Said get in!!" Yafada cikin qaraji wanda yayi mugun firgitata

Batasan sadda ta zagaya ba ta bude dayan murfin tashiga ta zauna tana sobbing


"ki yimin shiru kafin na karkaryaki!"

Babu shiri tayi tsitt sai hawayen dasuka kasa tsaiduwa


A fusace ya tada motar yaja a 360


Ta glass din gaba Aysha ta hangi su zee na shiga motar dasu jami'an sukazo daita


Fitt sukazo suka wucesu sanadiyar gudun da sukeyi suka fice daga makarantar

Itama motar dasu zee ke ciki ta maramasu baya suma suka fice daga makarantar


Aysha ta baya take Juyawa tana kallon motar dasu zee suke ciki, suna kaiwa wani junction sai taga Motarsu zee ta kama wata hanya daban da wanda suke akai sun wuce


Juyowa tayi ido taff hawaye da niyyar yima mussadiq magana Saidai yanayin fuskarshi yasa takasa cewa komai sai hadiye yawun datayi ta koma ta lafe a kujera tana matsar hawaye




Basu dade ba suka shigo unguwarsu kasancewar ba qaramin gudu yake falfalawa ba akan titin don Hakan na daya daga cikin dalilin da yasa ummie bata barin yayi tuqi da kanshi dole saita hadashi da mai tuqashi don kwata2 be iya tafiya ahankali, on normal days dayake cikin Good mood ma ya aka kaya bare yanzu da ranshi ke a 6ace


Kallo daya zaka yima unguwarsu kasan ta shahararrun masu kudi ne don ko street din wajen ka kalla shikadai saiya baka amsa


A kofar wani tangamemen gate mussadiq ya taka burki wanda Saida sukayi gaba ba don seatbelt dake jikinsu ba da sai sun daki gaban motar


Horn ya danna mai irin mugun tsawon nan don tunda ya danne be daga hannu ba har Saida aka wage tangamemen gate din don ko ba'a fadama securities din ba sunsan shine don dama sun haddace salonshi

Dagudu wasu securities din suka nufo motar da har lokacin bata shiga ba dukda anriga da an bude gate din

Juyowa yayi ya kalli Aysha dataci kukanta ta qoshi sannan cikin Hade fuska yace
"ukhrujj!"

Dan kallonshi tayi sai tadan share hawayenta da bayan hannu ta sa hannu ta bude kofar tafita

Wining glass din wajenshi yayi Hakan yasa securities din qara matsowa suna kwasan gaisuwa

"karku bari tasake fita!" Yafada cikin bada umarni

Cikin sarawa suke amsawa da angama

Be qara sauraronsu ba yafara dage glass din

Daya daga cikin securities din yayi qarfin halin cewa
"erm.. Yalla6ai ko nashigo na tuqaqa naga kamar ka gaji"


Ko kallo be isheshi ba ya ida dage glass din yayi reverse da qarfi yaci taya sannan ya wuce da mugun gudu


Duk bin motar securities din sukayi da kallo cikin zullumi don tabbas sunga ranshi a 6ace yake kuma tuqi a gareshi a wannan yanayin ba abu mai kyau bane, haka suka juya suka shige cikin gidan suma don dama Aysha tana sauka tashige gidan Dagudu tabarsu nan.






Maimakon akaisu police station sai aka kaisu headquarter ta c.i.d bisa umarnin Sir mussadiq


Saida aka amshe wayoyinsu sannan aka shiga dasu wani daki mai kama da office Saidai it's empty dai wani dogon desk da kujeru dake kewaye dashi


Dafarko cewa akayi su zauna aka tafi aka barsu nan, zee banda hawaye babu abinda takeyi, shikau Aymaan kawai zama yayi ya jingina da kujera yayi folding hannayenshi a qirji yana karkada kafaffu shikadai yasan abinda yakeji a zuciyarshi ga sniffing da zee keyi akai akai dake qara dagula mashi lissafi, gashi yakasa rarrashinta don bayajin ko magana yana iya yi a wannan lokacin


Suna ahakan wasu ma'aikata biyu suka shigo suma cikin kayan gida suka zauna a kujerun dake facing dinsu

Gyaran murya daya daga cikinsu yayi sannan yace
"zamu iya sanin sunanka?" yafada yana kallon Aymaan da ko kallo mutumin be isheshi ba

"magana muke" mutumin yaqara fada

I.D card dinshi na dazu yasake Ciro wa ya turamashi a gabanshi


Dauka mutumin yayi ya duba suka kalli juna da dayan mutumin sannan mutumin ya maida kallonshi kan zee

"kefa? Zamu iya sanin sunanki?"

Qara sniffing tayi sannan tace
"Zainab"


"to malama Zainab da mallam Aymaan kunsan akan me ake tuhumarku?"


Shiru sukayi

"akan spying, mai girma sir mussadiq yana zarginku da bibiyarshi wanda yana alaqanta Hakan da leqen asiri ko mugun nufi da aka saba yiwa manyan yan kasuwa irinshi, me zakuce gameda Hakan?"


Nan ma shiru

"munaji" inji dayan mutumin

Aymaan ne ya kallesu for the first time tunda suka shigo

Kamar bazaiyi magana ba sai ya motsa baki Dakyar yace
"zakuyi magana da lawyer na"


Kallon juna mutanen biyu sukayi sai suka sake kallonshi

"munsan da lawyern naka ai, yanzu kai muke tambaya tunda ku abin ya shafa ba lawyern ba" inji dayan, kana iya jiyo 6acin rai kadan a muryar

"zakuyi magana da lawyer na, that's it" yasake fada firmly batareda ya kallesu ba

Kallon juna suka sakeyi, ba don sir mussadiq yace kar ata6asu da babu abinda zai hana daya daga cikinsu fallamashi mari, babu abinda yafi basu haushi kamar yadda yake masu magana a gadarance

Kada kai na farkon yayi sannan ya kalli dayan cikin harshen larabci yace mashi sutafi sai suka tashi suka fita daga wajen suka qara barinsu alone



*AYSHA*





Dagudu tashiga cikin qaton gidan, harabar gidan ba dai girma ba gashi qasan shimfide yake da kwalta ga flowers of different types shufke a gefe gefen titin


Tayi tafiya mai nisa koko ince gudu mai nisa kafin ta isa maid entrance din gidan

Saida kofar tayi scanning face dinta sannan ta bude tashige ciki

"Ummie!" tafada cikin daga murya tana shiga makeken falon daya qawatu da kayan alatu ga tattausan carpet da duk takawa daya zakaji kamar zaka nutse aciki don taushi da laushi


Sama tanufa tafara hawa stairs din da shima kanshi abin kallo ne da gudu

Kasancewar stairs din mai lanqwasar maciji ne Saida ta dauki lokaci kafin ta qarasa saman

Wani qaton falon taqara cin karo dashi shima mai mugun kyau ta wuceshi sannan tashiga passage din dazai sadata da dakin Ummie


Koda ta qarasa kofar dakin ummie banda haki babu abinda takeyi don tasha gudu ba qarya

Bubbuga kofar dakin tahau yi da qarfi qarfi

Can aka bude kofar wata maid ta bayyana

Russunawa tayi tana gaidata Saidai har tayi gaba tashige cikin dakin


Wata mata dattijuwa na hanga zaune bisa tattausan carpet gefe kuma irin pillow dinnan ne masu kyau zagayayyu irin wanda akafi gani mostly a gidajen sarauta ta kishingida akai, plate a gabanta cike da yankakkun fruits wanda take dauka da daddaya tana ci


"Ummie!" Aysha ta qara kiran sunanta tana nufota

Saurin dagowa matar tayi ta kalli saitin Ayshar

_Tsarki ya tabbata ga ubangiji mai hallitu_ (abinda nafada kenan a raina don sak fuskar Deen nake kallo a gabana, kawai banbancin shine wannan mace ce kuma tadan manyanta)

Qarasowa zee tayi ta fada jikin Ummie taqara Fashewa da wani sabon kukan

"subhanallilah! Ya bunatie, meya faru?" tafada a rude tana tashi daga kishingiden datake

Cigaba da kukanta Aysha tayi tana qara qanqame Ummin

A rude Ummie ta cigaba da Tambayar Aysha meya faru cikin harshen larabci hankalinta duk ya tashi, tuni maids din dakin suka shiga sulalewa daya bayan daya suna fita


Dakyar Aysha ta samu ta tsagaita kukanta, cikin larabci tashiga cewa
"Ummie, yaya ne"

"yaya? Meya faru dashi?" ta tambaya hankali tashe

Girgiza kai Aysha tayi tace
"kawai daga zuwa saiyasa aka kama bestie ta da ita da yayanta akaje aka kulle" tafada cikin kuka


"aka kulle? Bangane ba"


"Ummie, wannan qawar tawa danake baki labarinta? Itace yau yaya yazo school don ya ganta don kodayaushe cikin matsa mashi nakeyi yazo ya ganta shine yau yazo amma daga zuwa sai suka kama fada wai spy ce tana spying dinshi ne wai don ya ganta wasu wuraren kafin nan, shine ita tace ba spy bace shine yaji haushi zai mareta sai yayanta yazo From nowhere ya tare sai fadan yakoma kanshi sai yasa aka kamasu aka kulle"


Tunda tafara maganar ummie bata fahimci ko kalma daya nata ba din a dunqule take bata labarin Hakan yasata zama so confused

"look Aysha, ki nutsu. Ki fadamin komai cikin kwanciyar hankali yadda zan gane"

Kada kai Aysha tayi tana share hawayenta da bayan hannu

"to ina jinki yanzu, wace qawarki kike cewa?"

"wannan wanda nake baki ku gaisa?mai sunanki"

Kada kai ummie tayi cikin gamsuwa
"eh nagane, takwarata? To meya faru?"


Cikin nutsuwa Aysha tashiga bata labarin abinda yafaru From A-z


Ajiyar zuciya ummie ta sauke tana dan dafe kai

"ya sallam, yanzu shikenan duk wanda ya ra6eka yazama abokin gabanka? Wannan wane irin hali ne ga bunnaya?" tafada cikin rashin jin dadin abinda yafaru

Qara share hawayenta Aysha tayi tace
"ummie nayi qoqarin fahimtar dashi itama tayi qoqarin fahimtar dashi amma yaqi ya saurari ko daya daga cikinmu, ita batama san shine Mussadiq al-hassan ba, batasan status dinmu ba don ban ta6a gayamata ba kawai nadai bata labarin mu ne in a simple way bance nice qanwar mussadiq al-hassan mai companies din Nurul-haqq ba, tayaya to zatayi mashi leqen asiri mutumin da batama sani ba, ni babu abinda yafi dagamin hankali kamar idan na tuna yanzu haka suna can kulle" tafada cikin kuka


"kiramin shi a waya, wannan abin nashi yafara wuce gona da iri, shikenan kowa saiya dora mashi alamar zargi? Soyake ya hana kowa mu'amalla da kowa kamar yadda ya hana kanshi? Kiramin shi"


"ummie kinsan bazai daga ba, ki kirashi da wayarki zaifi saurin dagawa"

"miqo min ita gatacan bisa cushion, wai ina ma yake shi?"

Aysha data tashi da sauri zata dauko ta amsa da
"ya dai ajiye ni yatafi"

"badai gudu yake ba kamar yadda yasaba, ya tafi da driver?"

"bana tunanin Hakan, can dai shikadai yazo"


Amsar wayar ummie tayi daga hannunta tayi dialing din number ta kara a kunne


Ringing daya biyu aka daga

Daga can 6angaren sukaji muryar mussadiq yana cewa
"Aslm alaiki ya ummie"

Dan Hade fuska ummie tayi wanda yayi mugun yimata kyau kamar dai yadda Deen keyi
"wslm, ina kake?"

"ina wani aiki ne ummie"

"wane aiki? Aikin kama mutane da basuji ba basu gani ba?"

"Ummie waya..."

"kazo kasameni gida yanzu yanzunnan, fatan kajini" tafada in warning

Cikin amsar umarni yace
"to Ummie"

Katse kiran ummie tayi sannan ta cigaba da kwantar ma autar tata hankali akan ta kwantar da hankalinta komai zai warware




Sai gashi ko minti tallatin ba'ayi ba ya iso gidan

"bunnaya, me kake so kazama ne? Shikenan kowa ma abokin gabarka ne? Shikenan kowa ma bazai ra6eka ko ya ra6i wani naka ba? Wannan wane irin aqida ne?"


"ummie mutane ba abin yarda bane, maqiyi bazai fito da pasta manne da goshi na rubutun shi maqiyinka ne, kowa na iya zama maqiyinka"

"kai shikenan baka kyautatawa kanka zato? Kalleka.. Bakada aboki ko daya saboda rashin yarda, yan uwanka ma baka zuminci dasu yadda ya kamata, kowa.. Kana iya yiwa kowa kallon maqiyi.
A dalilin Hakan yasa baka bayyana kanka, anfi sanin sunanka fiyeda kai kanka, yan tsiraru kawai suka sanka, kana iya zuwa wuri kayi hidimarka kafita ba'asan dakai ba Amma dukda Hakan zargin kowa kake, anya wannan hanyar daka dauko mai 6ullewa ce?"

Shiru yayi

"Nan gaba waya sani qila har muma zargin mu zaka dinga yi, a dalilin wannan halin naka ko budurwa baka ta6a yi ba, ga yanmata nan masu sonka a cikin families dama abokan arziqi amma kai bama ta aure kake ba, mussadiq nima inason ganin jikana, inason ganin jininka dana Aysha kafin na mutu dukda ita mutuwa bata ga babba bata ga yaro saita dauki yaro tabar tsoho amma ai ko babu komai anfi sama babban ran fara tafiyar, mussadiq Koda banga 'ya'yanku ba zanso ganin auren ku"

Jikin mussadiq yayi sanyi, dama haka yake kuma ummie tasan lagonshi data ambaci mutuwa sai komai nashi ya sure, ya tsani ummie takira ma kanta mutuwa sai yaji kamar da gaske din tafiya zatayi ta barshi kamar yadda mahaifinsu da dan uwanshi sukayi

Dagowa yayi ya kalli ummie
"ummie kibar fadin haka don Allah"

"to ai Gaskiya ce bunnaya, kowanne mai rai saiya dandani mutuwa, kuma ita wannan yarinyar ni kaina na santa don muna Gaisawa da ita ta waya, da ba alhairi bace ba agareku da naji Hakan a jikina, tun magana ta daita ta farko ta kwanta mun, be kamata kome yazo kanka ka yanke hukunci dashi ba"

"ummie sau uku kenan nake haduwa daita..."
Nan ya fayyace musu yadda duk haduwarsu ta kasance

"bunnaya, akwai coincidence, bayan Hakan wata haduwar ta allah ce kuma alhairi ce, ta yiwu allah keta hadaku wataqila yanada wata manufa akanku amma kayi bincike, abinda ya kamata kayi kenan tun farko bawai kaita zargi ba"

"nafara, yanzu haka school din nakoma nasa an daukomin file dinta, muna tsaka da Hakan kuka kirani"

"yauwa, bincike ya kamata kayi saika kamata dumu2 da hujjoji sannan zaka yanke hukunci bawai ka yanke hukunci akan zargi ba
Yanzu kasa a sallamesu ka kuma basu haquri inyaso sai ka cigaba da binciken ka akansu

Insha allah babu wani mugu dazai ra6eku, kodayaushe kuna cikin addu'o'ina dare da rana, kuma zaku cigaba da kasancewa cikin addu'o'ina, insha allah babu mugun dazai ra6eku"


Kada kai mussadiq yayi cikin gamsuwa


Cigaba dayi musu nasiha tayi mai ratsa jiki kamar yadda tasaba yimasu sannan ta sallami mussadiq akan yaje yasa asake su.





***



A can gidansu Aymaan kau hankalinsu duk ba a kwance ba, driver yaje daukar zee Saidai batanan, duk inda ake saka ran ganinta a fadin makarantar ba'a ganta ba

Ga shima Aymaan wayarshi bata shiga kamar dai ta zee

Kuma sun kira Ahmad sun sanar dashi yaje asibitin ance shima ya dade da fita

Haka dai Ahmad yaita yawon nemansu musanmman ma zee da ba koina tasani ba a garin, ga numbobinsu basa shiga Hakan yaqara dagula masu lissafi.






*AYMAAN/ZEE*






Suna zaune Jigum Tundazu abin duniya ya ishesu musanmman zee take jinta a matuqar takure

She can't believe wai yau ita aka rufe a custody dukda ba irin wannan rufewar bace ta wulaqanci

Tunda nan Wajene mai tsafta ga fili ga fresh air don akwai fankoki masu bada iska sosai aciki ga abinci mai kyau da aka basu Tundazu wanda haryanzu babu wanda ya kalleshi gashi babu duka babu zagi don tunda mutanen nan suka fita banda wanda yakawo musu abinci babu wanda yaqara Shigowa

Saidai kullewa kullewa ce Koda a cikin gidan aljannar duniya aka kulleka, dole wannan right of movement din da aka tauyemaka ya dameka


A 6angaren Aymaan kau abin yafi 6ata mashi rai, shi ba kulleshi din ba yafi 6ata mashi rai wanda yasa aka kulleshi dinne

Gani yake bekai wannan matsayin ba, gani yake qasqanci ne Hakan mutum kamar mussadiq yasa a tsareshi dukda kau yasan ya isa yasa ayimashi fiyeda Hakan ma kuma ayi din babu yadda ya iya

Amma ya rasa meyasa tun haduwarsu ta farko yaji baya son gayen, yana jin haushinshi fiyeda tunani shiyasa yake ganin tsareshi da akayi ta dalilin shi ba qaramin qasqanci bane a gareshi



Suna ahaka sukaji ana bude kofa


Babu wanda ya dago acikinsu bare ya kalli mai shigowar


"kuna iya fitowa" inji wanda yashigo din

Dagowa sukayi atare suka kalli mutumin sai kuma suka kalli juna da alamun tambaya

"you're free, zaku iya fitowa"


Wata nannauyar Ajiyar zuciya zee ta sauke tana jin sanyi a zuciyarta shikuma Aymaan yadan ta6e baki alamun ko ajikinshi


Atare suka tashi suka fito

Ce masu yayi su biyo bayanshi sukayi yadda yace harya kaisu wani office daban

Ce masu yayi su shiga suka shiga shikuma yafito ya rufo kofar yayi tafiyarshi


A tsaye yake jikin window yana kallon waje ta window din hannayenshi zube a aljihunshi


Wani qululun baqinciki ya sake tokare Aymaan, da yasan shi zasu gani a office dinnan da babu abinda zai sashi Shigowa


Ahankali mussadiq ya juyo yana kallonsu still hannayenshi zube a aljihu


Shiru ya ratsa dakin na wasu daqiqu babu mai uhm bare uhm uhm


Can saiya tako ya dawo kusada wani table din office din yadan jingina dashi yana dora hannu daya akan desk din


"seems yau ma is a Lucky day for you guys, Saidai rana 99 na 6arawo rana daya kuma na meshi, ku tafi amma idan kere na yawo zabo na yawo zasu hadu Saidai ku kuji haduwarmu ta gama don it gonna be worst"


Atare suka ta6e baki kamar hadin baki

Aymaan na shirin magana zee ta rigashi

"a juri zuwa rafi dai, kuma am assuring you wannan tsaremu dakasa akayi na few hours saikayi regretting dinshi, saiyasa watarana ka kasa hada idanu damu

Mutum darajja gareshi kowanne mutum da baiwar da allah yabashi wanda sai an taqa zai gane Hakan

Kayi amfani da matsayinka ka tsaremu, to kajira ranar da kai kanka kunyar kanka zaisa ka kasa daga idanu ka kallemu straight in the eyes kamar yadda kayi yanzu

A lokacin zaka gane arziqi is nothing don arziqin besa kasamu abinda wadanda ka wulaqanta suka samo maka ba, a lokacin zaka gane kowama da ranarsa kuma gamewar bazata amfaneka da komai ba don it's like crying over a split milk"



Aymaan ne yadanyi murmushi
"haba lil sis, meyasa kike 6ata yawun bakinki har haka? Magana ta hankali mai hankali ake yimawa don shi zaifi ganewa, it's better Kiyi saving din yawunki mai daraja for something more valuable"


Takowa mussadiq yayi gabansu ya tsaya yace
"kamar yadda nafada dazu, you guys are very Lucky, shiyasa har kukeda damar maida yadda akayi yanzu, amma ku guji ranar da Luck din xaibar side dinku cos you'll regret it. Kuna iya tafiya tun kafin Luck din ya fece yabarku tun yanzu"


"kai kalmar Lucky ta cancanta don albarkacin wani kakeci da nasa akowanne daqiqa ka dinga tuna ni cikin qunar rai amma unfortunately bazan iya ba saboda darajar shi dama mai daraja akecin darajar shi" inji zee


"out.. Kun isheni da hayaniya and this is not market, so out!" Yafada yana nuna kofa

"ko baka fadaba, amma ka tuna zuru batacin zuru" inji Aymaan sai ya kama hannun zee suka juya suka fita daga office din suna maido mashi kofar da qarfi


Bïñ kofar yayi da kallo sannan ya sauke Ajiyar zuciya yakoma ya zauna bisa kujerar Wurin mai jujjuyawa yafara jujjuyawa


_the girl_


Meyasa presence din yarinyar kesashi jin wani iri, absence dinta ke dada jefashi wani hali

Meyasa yakasa mancewa da ita tun haduwarsu ta farko

Meyasa yakasa mance fuskarta tun a gani na farko?


Shi ba mutum bane mai yawan maida kai ga kammanin wani musanmman mace amma sai gashi ita tun a ganin farko kwalwarshi tayi capturing face dinta

A haduwa ta farko bayan ya warwatsa mata kudade ajiki yayi tafiyarshi yaji wani yanayi marar dadi kamar yasa ajuya ya koma wajenta


A haduwarsu na biyu ma bayan yatafi yabarsu da cashier gab da zasu sha kwana ya juyo yana kallonta Daga nesa suna barin wajen, nan ma Wannan feeling din yaji kamar ya tsaidata kamar yakoma wajenta


Yanzu ma basu ida fita ba yaji kamar ya dakatar da ita inda Koda dakatar da itan yayi besan me zaice mata ba


Menene Hakan to?

Meye ma'anar Hakan?... ✍️






Ummin fasihu 🧚🏻‍♀?
8/2/21, 9:41 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?*










*067*






*THE UNVEIL*









Fitowa sukayi harabar wajen suka nufi hanyar gate


Aymaan kanshi na kan wayarshi da aka maido masu abinsu dazasu fita yana kunnata

Babu dadewa ta kunnu yashiga contact ya lalubo number Ahmad yayi dialing


Ringing daya biyu aka daga

"ya sallam Aymaan ina ka shiga? Na nemeka kamar zan zauce.." abinda Ahmad yafara dashi kenan yama manta da sallamar


"hmm, ai gashi yanzu kajini ko? Kana ina?"


"ganinan nadawo gidanku daga yawon nemanku, kasan kau zee ta 6ata?"


Dan murmushi Aymaan yayi ya dan kalli zee dake kallonshi shima saita Janye nata idanun


"gamunan tare, kazo ka dauke mu"


Jin sallalamin su ummy da ihun murnar batool yasa yadan Janye wayar daga kunnenshi kadan


"dagaske? Amma kai dan air ne, ina kuka shiga munata neman ku harda hadawa da police station?"


"kazo c.i.d headquarter ka daukemu" be jira amsarshi ba ya katse kiran


Sake kallon zee yayi yaga bashi take kallo ba Amma ta kare goshinta da hannunta saboda hasken rana


Juyawa yayi yaga wasu kujeru qasan wani tent saiya kalli zee yace
"muje can mu zauna mu jirashi"


Kallonshi tayi kamar zatayi magana saikuma tafasa suka wuce inda yace din suka zauna


Shiru wajen ya dauka na wani lokaci

Can zee tadan muskuta wanda Hakan yasa Aymaan Dagowa yana kallonta

Batareda tabari sun hada idanu ba ta fara cewa
"Am sorry.."


Shiru yayi yana kallonta Hakan yasa ta dago idanunta itama ta kalleshi

"for what?" ya tambaya yana kallonta cikin ido


Sauke nata idanun tayi sannan ahankali tace
"I caused it all, duk ni naja komai"


Murmushi yayi mai kyau yace
"bake ya kamata kibada haquri ba.. Nine.

Am sorry nakasa hanaki zama a tsare for some hours"

Dagowa tayi tasake kallonshi cikin wani yanayi sai ta girgiza kai

"nice najamana, naja maka tsarewa na wani lokaci"

Murmushi yayi ya kalli gate daga inda yake zaune

"I can do more than that... For you." ya qarashe yana maido kallonshi akanta

"kawai baqincikina shine kasa kareki danayi daga zaman tsarewar, dani kadai ne ko shekara nawa zanyi bazan damu ba Amma the thought of ke a tsare shiyafi komai dagula min rai... Am sorry"


Sunkuyar dakai kawai tayi batace komai ba sai wasa data cigaba dayi da zoben hannunta


Shima be sake cewa komai ba sai maida hankali dayayi yana hango gate ta inda suke zaune


Babu dadewa motar Ahmad ta iso wajen

Ajiyar zuciya Aymaan ya sauke

"ya iso... Muje" yafada yana tashi tsaye

Itama Dagowa tayi ta hango motar sannan ta tashi tabi Aymaan daya fara tafiya

Har Ahmad ya fito saiya hangosu Hakan yasashi tsayawa


Kofar baya Aymaan ya budewa zee ta shiga ya rufo sannan ya bude ta kusada driver yashiga shima Ahmad ya shiga suka rurrufo kofar, tada motar Ahmad yayi yaja suka bar wajen.




Tafiya sukeyi ahankali cikin normal speed babu mai cewa komai


Can Ahmad ya juyo ya kalli Aymaan da idanunshi ke kan titi


"Aymaan, wai meya faru ne? Meya kawoku wancan Wurin?" yafada yana maida kallonshi a titin

"muje gida sannan" Aymaan ya amsa a taqaice

Ajiyar zuciya Ahmad yayi ya cigaba da tuqinshi


Zee na Jinsu amma batace komai ba sai kallon waje datake ta window din motar


Koda suka isa gida duk

Please Login or Register in order to submit comment