Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

idan tazo school burinta ayi agama ta Kama gabanta ta koma inda tafito amma yanzu har qagara take gari yawaye taje school duk don su hade dashi

Tunda take bata ta6a sakin jiki da namiji kamar yadda tayi da Deen yanzu ba, kai ko mace babu wacce ta ta6a sakin jiki daita kamar yadda tayiwa Deen, lafiya lau suke wasa da dariyarsu, idan tana gabanshi itama komawa take mashiririciya kamar shi, daga abokin fada yakoma aboki yanzu kuma bestie duk acikin yan kwanaki. Sosai takeson tarraya dashi don he's fun to be with


Kallonshi tayi taga yana gyara setting agogon hannunshi

Shiru tadanyi tana taunar qasan bironta sannan ta janye tace
"Deen?"


Dagowa yayi ya kalleta

"inaso muyi magana dakai ne"

Jin haka yasashi maida dukkan hankalinshi akanta

Ajiyar zuciya ta sauke sannan tace
"akan maganar damukayi jiya ne... You know, nima banason gabar dake tsakanina da mr ibrahim but.. Bazaka ganeba, mr ibrahim mugun dan dizgi ne, dama abinda yafara hadamu kenan, duzga mutane, yanzu ina iya zuwa inbashi hqr ya yarfani, I know him very well" tafada tana 6ata rai


Shiru Deen yadanyi sannan yace
"kinaso ku shirya ne?"

Itama shiru tayi kamar mai nazari can kuma ta daga kafadu tace
"maybe"

Murmushi yayi yace
"bazai duzga ki ba, I bet you"

"no ni kadai nasan halinshi, bana sone wajen gyara a 6ata gabadaya don idan ya dizgani zuciya na iya dibana nayi mashi rashin kunya and I don't want that to happen"

Shiru Deen yasakeyi na wani lokaci kamar mai nazari sannan ya kalleta yace
"To, why not muyi haka? Karki tareshi directly kibashi hqr, kibi indirectly"

"how?" tafada cikin yanayin rashin fahimta

"first step shine kifara attending class dinshi ma'ana daga yanzu no more missing din lecture dinshi"

"tayaya hakan zai taimaka?" ta tambaya cikin rashin fahimta

"ta hanyoyi da dama, kinga na farko abin zai bashi mammaki, he'll be like anya kuwa kece? Na biyu hakan zai dan sauko dashi daga fushin dayake dake, idan kika tunkareshi daga baya baxaiyi bursting ba zaiyi considering dinki"


"hmm idan ya koreni daga class din fa?"

"bazai koraki ba, da farko zaiyi mammakin ganinki a class dinshi, sai kuma ya kyaleki yaga dame kikazo dashi, ke kuma alokacin sai kiyita neman kusanci dashi ta hanyoyi daban2 kamar amsa tambaya idan yajefo, tambayarshi abinda baki ganeba, kodama kin gane ki dinga tambaya, yadai kasance kuna communicating ko yaya ne, da haka da haka har muga perfect time daya kamata kibashi hqr"

Shiru tayi tana nazarin maganganunshi can tace
"To students fa? Me zasu ce gameda hakan? Baka ganin class dina zai zube?" saikuma tayi Saurin matse bakinta don zancen zuci ne yafito fili

Murmushi yayi yace
"kefa kikace bakya damuwa da abinda mutane ke cewa akanki, you see mutane baka iya musu, so far kinsan abinda kikeyi shine daidai to ki rabu da magangannunsu saidai idan abinda kikeyi dinne ba daidai ba Wannan saiki gyara, so dont think about what they'll say just act as if you dont care"

Shiru tasake yi tana nazari sosai, duk abinda yafada gaskiya ne, to amma tana iyawa kuwa? Ko babu komai akwai kunya, tayaya zatayi mursisi ta zauna a lecture dinshi bayan abubbuwan datasha yimashi

"please dont think negatively about this, Wannan shine daidai duk wani tunanin da zai zomaki daga baya to daga shaidan ne, dont give the devil a chance, act strong, show him you're stronger" yafada cikin qarfafa mata gwiwa

Kada kai tayi tana cewa
"ok" a sanyaye

Dadi yaji
"that means zakiji din?"

"yes.. Zan jaraba, amma fa da sharadi"

"meye sharadin?"

"idan yasaki ya dizgani akanka zan rama, zuwa zanyi saitin kunnenka da speaker inyita kwalamaka ihu harsai eardrum dinka ya Fashe"

Dariya yayi sosai sannan yace
"deal"


Kada kai tayi itama tana Murmushi tace
"kadai rubuta ka ajiye"

"no p, yanzu yaushe zaki fara?"

"gobe insha Allah, gobe thursday munada lecture dinshi har double period" ta amsa acikin zuciyarta tana tantanmar anya tana iyawa?

"good! Please try your best, na miki alqawari ke Kanki sai kinji dadin rayuwarki don dakun shirya jizakiyi kamar an dauke miki qaton dutse ne a qirji, zakijiki very free"

"dont worry zanyi insha Allah" tafada in affirmation

"To Allah ya yarda"

Da amin ta amsa suka cigaba da firarsu wanda kallo daya zakayi ka hango tsantsar shaquwa atsakaninsu yadda kasan sunyi shekaru tare





*****

"guys nifa na kasa ganema Wannan matar, tare zamu fito class daita amma the next minute mu nemeta mu rasa?" inji nurr

"hmm nima fa abinda ke daure min kai kenan kwana biyunnan, yanzu kwata2 ta rage hulda damu, bama ganinta ma sai lokacin lecture kuma da anfito mu nemeta mu rasa" inji deeya

"To ko wasu qawayen ta chanza?" inji sumee

"qawaye kuma? Kai I dont think so, kinsanta da shegen d'agin kai muma tayaya muka cika, kawai dai da abinda take 6oyemana nake tunani idan ba haka ba meye na janyemana haka?"


"Gaskiya nima abinda nake tunani kenan, tabbas akwai lauje cikin nadi, akwai abinda takeyi wanda batason musani kuma Dole musani" inji rukky

"Gaskiya kam, Dolene musamata ido, mu dinga lura da kowanne movement dinta" inji deeya

"Gaskiya, hakan xamuyi bazai yiwu ta maidamu shashashai ba" inji sumee

Haka sukaita firarsu duk akan yadda zasuyi monitoring dinta har sugano inda take zuwa a 6oye (Allah ka rabamu da mutanen da basa facing din tasu damuwar saita wani🤲🏻 Allah ka tsaremu daga sharrin duk mai sharri (Ameen)... ✍️


Manage please 🙏🏻 yanzu ba lallai bane ku dinga samun long page don haihuwa akayimana bansamun zama amma zan dinga yin yadda ta kama, da babu gwara babu yawa


Ummin fasihu 🧚🏻‍♀?
8/2/21, 9:33 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?*








*019*





*THURSDAY*



Tundazu takejin so nervous, jitake kamar bazata iyaba, kamar ta tashi ta fita.

Su sumee basu kawo komai aransu ba ganin rubutu take, atunaninsu da mr ibrahim yashigo zata fita tunda tasaba yin haka idan ya ritsata a class din

Shiru class din da aketa hayaniya yayi lokaci guda wanda hakan ke tabbatar da shigowar mr ibrahim.


Yan cikinta ne suka kada dataji kawo na tashi tsaye suna hada baki wajen gaisheshi.

Dakyar itama ta tattaro sauran kuzarinta tamiqe tsaye kamar sauran saidai takasa dago kanta dake a sunkuye

Tsitt class din ya dauka, shi be amsa gaisuwarsu ba kuma be basu izinin zama ba don shi nan jira yake ta fita kamar yadda tasaba yafara gudanar da abinda yakawoshi

Daga tsayen datake kanta a qasa takejin yawon idanu akanta wanda hakan yaqara mata restlessness din datake ji, sosai zuciyarta ke bugawa tana danasanin zama a class din tun farko


"sit!" ta tsinkayi muryarshi na cewa haka

Duk zama aka shigayi ga dunbin mammakinshi wai harda ita a masu xaman


Kauda mammakinshi yayi ya ajiye takardunshi acikin zuciyarshi kuma yana tambayar kanshi yau kuma dame tazo?


Gyaran murya yayi wanda saida zee tadan firgita don dama Duk a tsorace take kamar wanda za'acema kyatt ta ruga

Ta riga tagama sadaqarwa yau ta kawo kanta don bazai ragamata, cin mutunci zaiyi mata harna innanaha


"na'am, how are you guys?" yafada yana satar kallon zee qasa2 wondering ko yau buguwa tayi ne shiyasa bata tantance komai


Duk amsa mashi sukayi da they're fine

"good what was our last topic?" yafada yana bude handout din gabanshi

Dayake Duk ansan dabi'arshi na kafin ya dora wani darasi saiya bibiyi wanda sukayi na qarshe harma yayi musu tambayoyi akai, hakan yasa suke shiryama hakan don tsoron a cankoka ka kasa kata6us


Tare suka hada baki suka bashi amsa ta hanyar fadin topic din da sukayi qarshe


Tambayoyi yafara jefamusu akan topic din kamar yadda yake a al'adarshi suna amsawa


Duk abinda ake zee bata dagoba, tana nan dai zaune kanta aqasa saidai kallo daya zakayimata ka gano tana cikin takura matuqa


A bangaren su sumee kau suma sosai sukasha mammakinta, they can't believe yau zee ce zaune lecture din mr ibrahim, sosai gulma ke cinsu amma ba damar yi dole suka danne suna satar kallonta ta wutsiyar ido kamar yadda mafi akasarin Yan class din keyi suma.

Saida yagama tambayoyinshi tsaf sannan yasa kowa ya fiddo handout dinshi domin dorawa daga inda suka tsaya


Duk ciroshi sukayi including zee suka bude daidai inda yace, nan aka shiga karatun gadan2


Sosai tayi qoqarin saita kanta don ganin tayi yadda Deen yace saidai ko kadan takasa samun courage din yin tambaya kamar yadda yace ko ta amsa tambayoyin Dayake jefowa jefi2 Dukda tasan amsoshinsu


1hr lecture din ya daukesu wanda zee jinshi tayi kamar shekara daya, tsabar daburcewa ko rubutun kasa yi tayi

Saida yagama tsaf sannan ya kwashi tarkacenshi yaqara gaba, zuciyarshi fal mammakin abinda zee tayi yau

Fitarshi a class din yayi daidai da fitar wani nannauyan numfashi daga huhunta wanda yafi kama da na 'Dakyar nasha'

Class dinne yafara daukar hayaniya irin wanda yasaba dauka idan babu lecturer aciki


Saurin mayar da handout din tayi ta rufe ta jefa a jakka sannan ta miqe still tanajin idanu akanta

Bata damuba ta ciro baqin shade dinta ta toshe idanu dashi ta rataya jakkar tayi waje


Ganin haka yasasu suma Saurin miqewa suka maramata baya batareda sun bari ta lura dasuba


Tafiya take a nitse a zahiri amma a badini aqagare take taganta gabanshi, jikinta har tsumuwa yake, tanajin kamar ta ruga aguje taje ta sameshi ta amayarmashi abinda ke ranta.


Tun daga nesa ta hangoshi zaune yabata baya, kanshi a qasa wanda bata raba dayan biyu tasan duba littafi yake

Ganinshi yasata rage tafiyarta harta kaiga ta tsaya batareda ta ida qarasawa ba tana kallonshi

Su sumee ma da suka iso wajen suka samu ma6oya suka tsaya kallonsu ta ma6oyarsu wondering wanene gayen don suma bayanshi suke gani


Jin alamun ana kallon shi dayayi yasashi dan juyowa


Ganinta yayi tsaye a dan nesa dashi ta kafeshi da idanu wadanda ke qyalli sanadin hawayen dasuka taru aciki


Ganin haka yasashi saurin miqewa tsaye shima yana kallonta wanda hakan yayi daidai da warowar idanun su sumee cikin kaduwa

"DEEN!" duk sukayi exclaiming cikin zuciyarsu


Takowa yayi cikin tafiyarshi ta nutsuwa yazo gabanta yana rarraba idanu a fuskarta


Nurr saurin dafe saitin qirjinta tayi jin zuciyarta na baraxanar tarwatsewa by their mere sight

Dago idanunta dake salqi haryanzu da hawayen dataqi ba damar gangarowa tayi tana kallonshi itama


Ganin hawayen yasashi rudewa harya kamo hannunta batareda ya saniba don duk a tunaninshi wani abun mr ibrahim yayi mata


Tsakanin shock din da zee da Nurr sukaji bansan wanda yafi wani ba

Don sosai hakan yayi tasiri akansu su biyun saidai ta fanni daban2


Fitowa Nurr tayi niyyar yi daga ma6oyarsu taje wajensu ido rufe allah ya taimaka su deeya sukayi saurin kamota


Qoqarin fizgewa take cikin jin wani mahaukacin kishi na tasomata saidai sunqi sakinta saima janyeta da sukayi daga wajen ma gabadaya suka bar wajen suna rufemata baki don karta tonasu


Fizge hannunta zee tayi da sauri tana watsamashi wani kallo hakan yasashi dan ja baya yana dan wara ido

"am.. Sorry, I..." wuceshi datayi taje ta zauna inda ya tashi yasa kingin maganar maqalewa ya bita da kallo


Jiki asanyaye shima ya tako zuwa inda take zaune shima ya zauna dan nesa da ita yana kallonta


Tabbas abinda yake gudu yafaru, dole mr ibrahim yayimata wani abun, qilama dizgin datake gudun yayimata

Tunawa yayi da yadda yayi ta convincing dinta yau da safe kafin ta yarda zatayi attending lecture din don dafarko cewa tayi tafasa don ita gaskiya tsoro takeji

Haka yaita lalla6ata yana yimata alqawarin babu abinda zaicemata qarshema ya nuna yayi fushi kuma babu ruwanshi da ita harya miqe zai tafi saboda dama yau saboda ita yazo don baida lecture yau, Ganin Hakan yasata yarda zatayi, gashi yanzu abinda ya biyo baya


Hadiye wasu yawu dasuka taru a bakinshi yayi yana kallonta cikin yin fiki2 da idanu kamar marar gaskiya yace
"erm .. Are you ok?" yafada yana rarraba idanu

Gani yayi ko kallonshi batayiba

"amm.. Mud queen oop!.." ya dafe baki don tunawa da yayi batason sunan ga wani kallo na musanmman data juyo tana watsamashi


Bata fuska yayi yace
"O'O! Ni menayi kuma?"

Zaro mashi idanu tayi a masifance tace
"me kayi? Me kayi ma zakace? Ka turani can kai kananan hankali kwance? Bari kagani" tafada tana rarumo wani dutsi na kusada ita tanufeshi gadan2

Ganin Hakan yasashi saurin runtse ido yana qanqame jiki cikin jiran tsanmmani

Shiru yaji babu abinda yasameshi can kuma yaji sautin dariyarta tanayi ahankali


Ido daya yafara budewa ahankali sannan ya bude dayan ya waresu akanta yana kallon yadda take dariyar ga hawayen dasuka taru a idanunta sun gangaro

Sakin baki yayi yana kallonta yayinda itakuma yadda yake kallonta din ke qara Bata dariya

"Are you crying or laughing?" yafada yana kallonta cikin mammaki don shi beta6a ganin inda ake dariya da hawaye lokaci daya

Qara volume din dariyarta tayi harda dafe ciki
"ya kamata kaga fuskarka a mirror yanzu" tafada tana nuna fuskarshi cikin dariya

"ko kuma ke ba? Ke ke buqatar mirror, kuka fa kike da dariya" yafada cikin al'ajabi


Dariyar tacigaba dayi tace
"Hakan ake kira mixed feeling" tafada cikin dariya

Buga tagumi yayi yana kallonta yace
"to, nidai am i safe"

Dariya tayi ta dauki littafi tayi kamar zata kwalamashi tana cewa
"gaka kusada mahaukaciya ba?"

Kaucewa shima yayi yana dariya

"da farko nayi tunanin mr ibrahim ne, ashe..." saiyayi mata nuni da alamun mental problem

Littafin da Bata makamashi ba dazu ta makamashi yanzu tace
"nice mahaukaciyar?"

Dariya yayi yana sosa kanshi inda ta kwalamashi yace
"kinga laifina, laughing and crying altogether? Ca6 ban ta6a ganiba"

"gashi Ka Gani yau" tafada tana share tears dinta dasuka gangaro mata


"to ya? Tell me duk abinda yafaru" yafada cikin zaquwa

Harara ta gallamashi tace
"amebo! Ashe maza ma sun iya gulma?"


Dariya yayi yace
"whatever, nidai gayamin"

Murmushi tayi tace
"becemin komai ba kuma be dizgani dinba"

Washe baki deen yayi yace
"I told you ai"

Murmushi taqarayi tace
"amma fa baka ganiba, kamar na sume na dawo don tsoro, danaji zaiyi magana sai inji kamar zan sume don sai inta ganin dani zaiyi, wuhh! Na sha dakyar" tafada tana dafe kai


Dariya so sai deen yashiga yimata
"matsoraciya kawai!"

"eh ba komai" tafada tana Murmushi

"yanzu Are you still in ko zaki janye?" yafada cikin Murmushi


"am in! In!! In!!!" tafada sunayin dariya tare

"nayi tunanin tsoro bazai qara Bari kiyi ba" yafada cikin dariyar jindadi


"tsoro your head! Ni cema akayi kaine"

"who? Don't even compare me to you don nafiki jarumta"

Daga gira daya tace
"haba? Ahakan"

Huro hanci yashiga yi yana cewa
"kina tantama ne"

Dariya tayi tana rufe baki tace
"sunan wata unguwa" tafada tana nuna hancinshi dayake hurowa

"wai ita?" yafada yana qara hura hancin

"qofar marusa" tafada cikin Dariya sosai

Hade gira yayi ya dauki Littafi shima zai kwalamata tayi saurin tashi tareda fizge jakkarta tayimashi gwalo tajuya ta tafi cikin sauri tana waiwayenshi tana mashi Dariya ganin haryanzu fuskar ahade take




*NURR*




"wai nurr meke damunki ne haka? Kuka fa kike?" inji deeya


Kasa cewa komai nurr tayi kamar yadda takasa tsaida hawayenta, hoton her hot crush wato Deen kawai take hange riqeda hannun zee

Bata ta6a tunanin tanada irin wannan kishin ba sai yau don yadda ziciyarta ke tafasa da tasan yadda za'ayi ta cirota ta jefar da tayi ko ta rage jin radadin datake ji

"hmm aini ba tun yauba na karto jirginta ba, dama tun lokacin data fara xaqalqalewa akan al'amurranshi nasan sonshi take, bakiga yadda take mayar min da magana ba ranarda su master suka tareshi, kamar irin na ta6a qanin innansu? Tun anan nasan da walakin goro a miya, hmm aikau aiki ya ganki don inhar zee ce to ki qaddara kin rasashi kin gama don duk abinda tasa agaba to saita mallakeshi gwara ki tashi tsaye da wuri kisan nayi" inji sumee tana rungume hannaye a qirji tana girgiza qaffafu


"amma zee tacika baqar munafuka, dama ashe duk 6oye 6oyen datake tasan abinda take qullawa, wai yaushe ma Deen yadawo school din bamuda labari?" inji rukky cikin alhini


"ai dama ire iren zee su akecewa poisonious snake, maciji sari ka noqe, fuska musa zuciya fir'auna" inji sumee

"ai dama kun ta6a ganin tabarmu mun samu abun kanmu? Koda yaushe sotake ya kasance itace agaba muna abaya muna take mata baya, a kullum sotake muzama fadawanta shiyasa take qoqarin ganin ta mallake komai ta gaje duka, wataqila lura tayi kina sonshi shiyasa ta biyomiki ta bayan qasa don ta mallakeshi inba haka ba dama shiri suke? Mutumin da ta tsana take wulaqantawa?" inji deeya

"nima fa abinda ke bani mammaki kenan, Mutumin da tayi sanaddiyar kwanciyarshi gadon asibiti harna kwana uku shi zata dawo yanzu tace tana so? Wlh ba sonshi take ba kawai tsabar mugunta ce kawai, lura tayi nurr na sonshi shiyasa tabi ta wannan hanyar don kuntata mata takuma gwadamata tafita matsayi da iko ta koina, allah sarki bawan allah, na tabbata dadin baki tayimashi shikuma tunda ba cikakken hankali gareshi ba ya fada tarkonta, kawai nurr ki haqura kawai don fada da aljani ba riba, tunda tasanyo muguntarta kawai mu haqura ya muka iya?" inji rukky tana marairaice fuska

Aikau kamar jira nurr take ta zaburo tana cewa

"wlh bazata yiwuba! Deen nawa ne! Nawa ni kadai! Ba yar kaza kazan data isa ta rabani dashi, akanshi zan iya komai ma! Idan nace komai ina nufin KOMAI!!" sai kuma taqara fashewa dawani kukan mai cin rai


"aikau ina bayan ki nurr, lokaci yayi da zamu nunama zee muma da zuciya a qirjinmu, lokaci yayi da zamu nunamata bafa tsorontaba akeji, Shiru Shiru ai ba hauka bane" inji deeya cikin fushi

"aikau dai, lokacin daukar action yayi, lokacin da zamu nunamata ita ba kowan kowa bace, dolene mu dusasar da tauraruwarta mu hada qarfi da qarfe mu kwato soyayyarki, dole muje musameta muyi mata tass!" inji rukkyy cikin bala'i


Wani makirin murmushi sumee tayi tana cewa
"anzo wajen.. Guys albishirinku, nasamo mana hanya mafi sauqi wajen cin ubanta hankali kwance batareda mun tadawa kanmu hankali ba, tauraruwarta zata dishe, rayuwarta zata tarwatse, dukiya da kyau da duk abinda take taqama dashi bazasu amfaneta da komai ba, zatayi mutuwar tsaye inda saita gwammaci mutuwa da rayuwarta, are you Guys ready? Kun shirya bada hadin kai domin kwatar yancinmu?" inji sumee tana kallonsu da daddaya

"na shirya! Indai Hakan zaisa na mallaki deen to ashirye nake" inji nurr

"muma mun shirya! Mun gaji da mulkin mallakan da ake mana, ki fadamana koma menene ashirye muke mu bada hadin kai" inji deeya, rukkyy na kada kai itama alamun goyon baya

Wani makirin murmushi sumee tayi sannan tace
"to ku matso kuji"

Nan duk suka matso suka zagayeta tashiga radamasu mummunan qullin da suke hadawa zee... ✍️


_ashe makashinka yana nan tare dakai, duk inda kake ya bika_😭


Allah ka tsaremu Daga sharrin masu sharri 🤲🏻



Ummin fasihu🧚🏻‍♀?
8/2/21, 9:33 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?*










*020*




Kamar yadda kau zee tace haka tayi, tun daga ranar bata qara missing din lecture din mr ibrahim ba


Tun tana d'ari2 akan zaiyi mata harta dan saki jiki

Ganin Hakan yasata fara yin qoqarin zama active a class din ta hanyar daga hannu idan akayi tambayar da tasani

Saidai ko kallon gefenta beyi bare yanuna yasan abinda takeyi.

Da farko jikinta yayi sanyi har Hakan yaso ya sanyaya mata gwiwa amma da taimakon Deen dake qarfafa mata gwiwa ta cigaba batareda ta sare ba

Duk lokacin daya jefo tambaya wanda mafi akasari Duk ta sansu don haryanzu suna karatu da Deen ahalin yanzu ma they're ahead of the class don Duk abinda mr ibrahim zai koyar a class kamar revision ne agareta don sun riga sunyi da Deen, Hakan kesa karatun kezomata da sauqi sosai

Duk lokacin daya jefo tambaya saita daga hannu dukda tasan bazai ko kalleta ba, tun tana d'ari2 harta ware da kallon da yan class ke yawan binta dashi


Ana haka watarana mr ibrahim ya jefo wata tambaya wanda Duk aka rasa wanda zai amsata a class din sai zee don ita kadai ta daga hannu

A bangaren zee kau batasan ita kadai ta daga hannu ba don tasaba akwai masu kwalwa a bayanta don sau dayawa yana cankosu su bada amsa

Tsit class din yayi students din suka zubamasu ido don ganin mezai faru next


Mr ibrahim beda option tunda ita kadai ta daga hannu, rashin bata damar maganar na iya zama wani abun daban ga students din shiyasa ya cije ya fuske ya nunata yana cewa
"yes? Say it"

Zee batasan da Ita yake ba don ita harta saba daga hannu kawai take amma bata amsawa ganin duk an kallota yasata tsarguwa, ta juya bayanta taga babu kowa mai hannu sama ita daya dece

Hakan yasata jin cikinta ya murda don kwata2 bata shiryama hakaba, da tasan babu wanda ya iya da itama bata daga hannu ba

Ganin tana neman bada kanta yasata tattaro sauran nutsuwarta ta miqe tsaye, cikin confident data rasa daga ina yazo tashiga bashi amsar tambayar tashi dalla2

Tunda tafara yake kallonta yana mammakin wane irin brain ke ga yarinyar nan don har abinda be ambata masu ba ta ambata wanda Hakan ba qaramin faranta mashi yayi ba don shima kamar kowanne teacher yana bala'in son student mai sharp brain

"a round of applause for her" yafada bayan tagama zayyano amsoshin


Class dinne ya kaure da tafi wanda Hakan yasata jinta on top of the world

Umarni yabata akan ta zauna takoma ta zauna haryanzu tana jin yadda zuciyarta ke tsalle

Har aka qarashe lecture din bata qara gigin daga hannu domin amsa wata tambayar ba don harga lokaci takasa komawa normal


Bayan lecture din daje tasamu Deen ta karanta mashi komai daya faru a ajin cikin tsananin murna, tana ta nannata wai yau ita mr ibrahim yacema ayiwa tafi


Deen dai Dariya yayita mata yana cemata ba sabon ba yayinda take cewa eh babu komai


Tofa tun daga ranar zee tafara zama active student a class din mr ibrahim

Yanzu koda cikin mutane dayawa ta daga hannu yakan cankota jefi2, hakan kuma ba qaramin qara mata popularity yayi ba a class don a hasashen kowa yanzu kamar duk acikin class din ita ke topping din class din a subject din don wani sa'in ita kadai ke iya amsa wata tambayar

Hakan yafara jamata farinjini a class din (kundai san yadda akema maqwara a fanni maths kallon manyan qwari😜)


Sai yazamana tana qara burge yan class din, tana ba kowanne sha'awa donma sanin halinta na wulaqanci yasa duk ake shayin zuwa wajenta amma yadda tayi sunan nan da lafiya lafiya da taga yadda ake tururuwar zuwa koyon karatu awajenta.


Su sumee kau a bangaren su wannan sabon cigaban na zee ba qaramin qara masu kiyyayarta yayi ba, sosai hassadarsu da baqinciki akanta yaqara farashi don sun lura akoda yaushe cigaba take samu ba ci bayaba

Hakan ba qaramin rura wutar abinda suke shiryamata yayi ba azuciyarsu


Saidai dayake munafukaine masu 2face ko kadan basu ta6a nunamata komai ba a fuska saima qara jawota jiki dasuke kuma koda wasa babu wanda ya tadamata maganar Deen acikin su saima yi dasukayi ma kamar ma sun manta dawani hallita Deen bayan a badini koda yaushe suna nan suna yimasu la6el either a library ko a sabon wurin zamansu, koda yaushe saisun je sunganosu wanda yanayin da suke tardasu yake qara hura wutar kishin nurr tarasa meke mata dadi a duniya.



A bangaren zee da Deen kau wani sabon fejin shaquwa ne ya bude a tsakaninsu, ada akwai ranakun da basada lecture wanda hakan kesa basa zuwa ranar, amma a yanzu basa fashin ko wace rana, kullum sai sunzo kuma inhar ba lecture suke ba to suna tare

Suna dan zuwa school din ranar saturday don yin karatu duba da yadda exams keta qarasowa, hakan yasa suka dage kowannensu ya maida hankali fiyeda da a karatu


Abin mammaki yanzu idan ba tare suke karatu ba basa jin dadin karatun, kuma be cika zama ba ma

Sau da dama idan suna gida suka dauki Littafi da niyyar karatu sai suji abin dai gashi nan, karatun duk bawani dadi

Amma idan suna tare koda kuwa kowa da littafinshi a hannu yana karatunshi shikadai sai suji sunfi jindadi kuma yafi zama, wannan abin ba qaramin mammaki yake basu ba hakan kuma yaqara donqon shaquwarsu, yaqarawa Abin armahi👌




Yau ma kamar koda yaushe suna zaune a sabon wajen zamansu,

Please Login or Register in order to submit comment