Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ana tantama akan marks din saiya sake yin wani don shafe tantanmar ko kuma ayi cancelling din abin gabadaya... Ke wanne yayi miki? Kin yarda zaki sakeyin wani agabana domin shafe tantama na ko kin yarda kinyi malpractice a cansile?" yafada yana kallonta


Ta dade bata ko motsa ba kuma bata cire hannayenta daga fuska ba hakan yasashi qara cewa
"mallama am talking!"


Sai alokacin tacire hannayenta daga fuskarta, idanuwanta sunyi jawur saidai ko digon hawaye babu a fuskarta

Kallonshi tayi da bloodshot eyes dinta sannan ta lumshe idanu ta bude

Ahankali cikin cracking voice tace
"fix the date, zan.. Chanza wani"

Dama yasan amsar dazata bashi kenan don bata Saurin accepting defeat, ego dinta bazai bariba.

Hakan yasashi cewa
"next week monday, exactly irin wannan lokacin" yafada yana duba agogo


"Thank you" tafada ahankali sannan ta miqe dakyar tanajin haryanzu kanta na sarawa.


Hanyar waje tayi tana dan hada hanya hakan yasata rakata da kallo harta fice sannan ya ta6e baki yana daga kafadu ya cigaba da abinda yakeyi.


Tafiya take Batareda tasan inda take tsoma qafarta ba, jin tafiyar na neman gagararta yasata samun wani icce ta jingina dashi sannan ta sulale ahankali ta zauna qasa.

Ahankali taqara dago takardar tana binta da kallo, ahankali rubutun yafara yimata dishi2 sanadin ruwan daya taru a cikin idanunta, kifa takardar tayi a fuskarta daidai da 6allewar hawayenta... ✍️



Ummin fasihu πŸ§šπŸ»β€β™€οΈ?
8/2/21, 9:32 PM - Buhainat😝: *πŸ™πŸ»β€β™‚οΈDEEN πŸ™πŸ»β€β™‚οΈ?*




*014*



Batasan tsawon lokacin data dauka ba ahakan sai jitayi an dafata hakan yasata tsagaita kuka marar sautin datake ta dago ahankali.

"ya sallam! Zee lfy?" inji su sumee dama jin shirun yayi yawa yasasu Bin sahu sai ganinta sukayi can jikin wani icce cure wuri guda

"haba zee Wannan ai ba girmanki bane kuka in public ba, idan wani yaganki fa? Hakan ba qaramin zubda m bane" inji deeya tana kamota suka miqar daita tsaye


"komai yayi zafi maganinsa Allah, menene don bakici Wannan ba? Insha Allah zaki fanshe a exam" inji rukky cikin yanayin tausayawa


Dagowa tayi ta kallesu da rinnanun idanunta da sukayi ja sosai saboda kuka, ahankali ta motsa bakinta tace
"ina.. Deen"

Babu wanda yayi magana acikinsu sai kallonta da suke

"tell me please" tafada tana lumshe idonta don ba hawayen dasuka taru damar sauka


"me zakiyi mashi kuma? Kibari ya farfado daga wancan abin da kikayi mashi mana kafin kiyi tunanin dora mashi da wani" inji nurr da dama a wuya take daita akan abinda tayi mashi rannan

Kallonta tayi ta hadiye wani yawu mai daci tace
"where is he? Please" tafada tana kafeta da idanu


Sumee dake bayanta taji tace
"zee, rabon Deen da makarantar nan tun wancan ranar, ashe dama yanada pneumonia, coke din dakika watsamashi ya tado mashi ita, yanzu haka shekaran jiya akayi discharging dinshi daga asibiti kamar yadda mukaji labari"


Juyowa tayi ta kafe sumee da ido tunda tafara magana, jitayi kamar ansa guduma an make mata kai.

Babu abinda kemata kai kawo a kunnuwa sai

_*ashe yanada pneumonia, coke din dakika watsamashi ya tado mashi ita*_

_*ashe yanada pneumonia, coke din dakika watsamashi ya tado mashi ita*_


πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–


Ahankali wasu sabbin hawayen suka qara gangaromata wanda bataba kanta wahalar sharesu ba


*"this?"*
Cool voice dinshi tadawo mata lokacin daya miqomata takardar

*"kai wane irin daqiqi ne? Nace kai wane irin daqiqi ne!!"*

*"how dare you temper with my work?! How dare you!"*
WaΙ—annan kalaman nata Suma suka shiga eoching a kunnenta


Tunawa tayi da yadda yaja wani mugun numfashi lokacin da coke din mai mugun sanyi ya sauka a jikinshi

Tunawa tayi da yadda yaja baya jikinshi na 6ari, yadda ya kama Kanshi da hannu bibbiyu, yadda yatafi taga2 yafadi


Dago takardar tayi wanda tunda aka bata takasa ajiyeta, sake warwareta tayi tana binta da kallo

Duk tadanyi jirwaye saboda ruwan hawayenta dake diga bisa ita duk lokacin datake kallonta, tarasa dalilin dayasa hawaye ke rige rigen zubomata aduk sadda take kallon takardar, dukda tanada Saurin kuka but this is too much

Kallon unique handwriting dinshi take tana kallon neat calculations din sannan ta gangaro kan marks dinta

*19%*

She can't believe saboda Wannan ta tadoma mutum irin Wannan mugun ciwon pneumonia, She can't believe saboda shi ta kwantar da mutum jinya na kwana uku.

Wannan tunanin ba qaramin qaramata nauyin zuciya yake ba, karo na farko datayi abu taji tana danasani sosai, taji tanajin kamar ta maido hannun agogo baya


Jin kamar za'a bude kofa yasata Saurin share hawayenta ta cusa takardar qarqashin pillow sannan ta kwanta tana juyawa kofar baya.

Mummy ce tashigo da kanta don tadota don yanzu ta aiko wata maid dinsu tace kofar arufe take kuma tayi knocking shiru

Qarasowa tayi wajen gadon tana kallon zee daketa barci, kai hannunta tayi ga wuyanta domin feeling temperature dinta taji akwai dan zafi hakan yasata zama gefen gadon tashiga tadata.

Saida tadan jima tana tadata sannan ta bude idanunta dasukayi ja cikin yanayin barci

"tashi, wai haryanzu jikin?" inji mummy

Tashi tayi zaune tana dan yatsine fuska sannan ta daga mata kai

"kinsha maganinki na rana?" inji mummy

Girgiza kai tayi ahankali

"kin gani? Dama kina wasa da magani yaya za'ayi ki ida warwarewa? Yanzu tashi muje kici abinci saiki dawo kisha maganin" tafada tana miqewa tsaye

Itama yaye bargon jikinta tayi ta sauko qaffafunta qasa sannan ta miqe tabi bayan mummy datayi gaba.


Abincin ma tsatsakurarshi tayi badon yana mata dadi ba sannan mummy ta tsareta tasha maganin tadawo ta kwanta don dama dare yayi lokacin har 9 saura.


Saidai koda ta kwanta din barcin qauracewa idanunta yayi ta sake lulawa duniyar tunani, yanzu ina zata ganshi? Yaushe zaizo school? Anya yama ida warwarewa kuwa? Inane gidansu? Wurin wa zata samu hint akanshi no matter how little it may be, kawai ita atunaninta tanajin guiltiness akan abinda tayi ne hakan yasata shiga damuwa sosai, bayan haka babu komai (to Allah yasa)


Yau ma ta jima sosai kafin barci yayi nasarar yin gaba daita.


***

Shiru master yayi yana sauraron Bash harya kai ayar zubar dayake tayi.

Tsaki yaja yace
"itakuma meye hadinta da trash irinshi? Ni nama yi tunanin wani dan qusa ne a qasar nan, wai koko da qosai, mtcheew!" yaqarashe yana jan wani tsakin

"nima wlh boss musanmman idan ka lura da ajebo ne, nayi tunanin tsabar gata ya maida shi hakan ashe the reverse is the case"

"Gaskiya ne, kawai Wannan ba wani amfanin dazaimana tunda bawani jituwama ke tsakankaninsu ba, kawai mu fiddashi a jadawali tunda mun samu daya daga makusantarta ta bamu hadin kai"

"bama ceba, kawai mucigaba da samasu ido muna kuma samun information akanta daga ita makusanciyar tata, duk qumu baza'a qarashe Wannan semester dinba saina ja rayuwarta a ta6o na kacalcalata, that's a vow" inji master yana jan ciggarette din hannunshi

"hakan ma yayi master! Dolene taji a jikinta, Dolene a gwadawa kowa babu wanda ya isa yajada master ya kwan lfy" inji Alex


Murmushi master kawai yayi yacigaba da jan ciggarette dinshi yana ayyana abubbuwa da dama aranshi.


πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–


Washegari da dan qarfi2 ta tashi, qila harda maganin datasha yasata jin dan kuzari ajikinta, ba laifi zuciyarta ta rage Wannan nauyin datayi tadanji dama2 hakan yasa tayi shirinta cikin qanqanin lokaci tafito.


Saida tayi breakfast sannan ta fito suka hau mota suka halba school.

Yau duk yininta qarar dashi tayi cikin qunci, tarasa abinda ke mata dadi, tayi tunanin zaizo yau din tunda yanzu kwanakinshi 4 kenan da sallamoshi asibitin da akayi kamar yadda akace mata

Gashi ko kadan taqi bayyana halin da take ciki ko a fuska ne don ko su friends dinta basu gane halin datake cikiba, gashi takardarta ta jiyama bata nunamusu ba, kawai hakanan taji bataso su fuskanci komai nata kuma don da da hali da zataso subata space don ba qaramin takuramata sukeyi ba yanzu

Sosai takeson ta kadaice ko zata samu tayi tunaninta hankali kwance amma ba dama don duk inda tanufa suna nan maqale daita kamar bindi hakan yasa duk bataji dadin school ba ranar haka kawai ta daure suka ida lectures dinsu na ranar Batareda ta fahimci komai ba suka kamo hanya suka dawo gida.



Wasa2 wednesday tazo tawuce babu Deen, thursday nanma haka har gashi yau friday babu shi babu mai Kama dashi.

Ixuwa yanzu ko bakasan zee ba ada da ka zauna daita na wani lokaci saika gane tana cikin damuwa.


Yanzu bata cika magana ba don mugun wuya take bata yanzu don ko maganar ake mata sai anci sa'a take amsawa dakyar

Azahiri bata nuna damuwarta saidai ka gane hakan a hallayarta

A bangarenta kau komai yabar yimata dadi, ta sukurkuce, school din yanzu ya ida fice mata arai saidai dukda hakan batason fashin ko rana guda gudun kar suyi sa6ani yazo ita bata zoba.

Tarasa yadda zatayi placing yadda takeji, abin dai kamar damuwa da rashin sanin halin da yake ciki wanda koma wane halin yake ciki itace sila kamar kuma kewa, gata nan dai ita kanta bata ganema kanta ba.

Kwata2 ma ta mance da deal dinsu da mr ibrahim na sake wani text din, gashi yau friday kuma ranar monday za'ayi amma kwata2 batashi takeba hasalima mantawa take da hakan Tsabar bashi ke gabanta ba



Jin surutun dasukeyi yafara hawan mata kai yasata dagowa daga phone dinta datake jagulawa tundazu tadan kallesu taga firarsu kawai suke hankali kwance.

Dan duba agogonta tayi taga haryanzu akwai sauran time kafin su shiga last lecture dinsu hakan yasata daukar jakkarta ta miqe


Duk Dagowa sukayi suna kallonta da alamun tambaya

"bari naje cafteria nadawo" tafada tana rataya jakkar

"bari na rakaki" inji deeya tana niyyar tashi

Saurin dakatar daita tayi ta hanyar cewa
"no never mind, yanzu zan dawo ai"

Bata sake jiran komaiba taqara gaba don dama surutunsu zata gujemawa idan ta biyota ai anyi ba'ayiba kenan.

Cafteria din tanufa direct, burger kawai tasiya da freshyo na roba don dama idan ba gidaba da wuya taci abinci tafi ganema snacks dai


Packaging dinsu akayi mata a leda tabiya kudi aka bata chanji sannan ta juyo da nufin tafiya.


Idanunta ne suka sauka akan bayanshi dadai zai fice daga wajen.

Kafin ta tantance shi dinne ko bashi ba harya fice.


Da sauri ta saka abubbuwan data siyo cikin jakkarta tayi hanyar fita itama da sauri.

Saidai koda ta fito babu shi babu alamunshi, waige waige tayita yi don ganin inda zata ga wulginshi saidai bataga ko mai Kama dashi ba


Nufar inda yasaba zama tayi taga ko can yanufa saidai wurin wayam babu kowa kamar yadda wurin yake cikin yan kwanakinnan

_to kodai bashi bane?_ tambayar datayiwa kanta kenan

Girgiza kai tayi, tabbas shine dukda bayanshi tagani bata tunanin tana iya kasa ganeshi

Dukda kallon yan sakkani tayimashi kafin ya fice taga komai gamedashi, tafiyarshi, structure dinshi, sanyinshi


Department dinshi tawuce ko zata ganshi acan saidai wayam ma class din yake sai yan tsirarun mutane daketa kai kawo wajen


Dafe kanta tayi tana furxar da iska
_karfa ace gizo yayimata? Tunda ga lokacin data fito be isa ace ya 6acemata ba Koda kuwa sauri yake bare tasan yanayin tafiyarshi be iya sauri ba ko kadan.


Juyowa tayi jiki a sanyaye tabar wajen.

Ranta ne yaqara jagulewa taji duk ta sake quntata, sanin cewar idan takoma wajensu sumee ida jagula mata lissafi zasuyi da surutunsu yasa kawai ta nufi library don acan take saka ran ke6ancewa Batareda wani ya takuramata ba.

As usual kamar yadda akasan library da shiru haka shima Wannan yake.

Babu mutane dayawa aciki sa6anin yadda yake cika idan exams yakusa.

Kamar yadda yake dabi'arta bata kalli kowa ba tanufi wani seat din dake empty wanda ke kusada window tayiwa kanta masauki anan

Ajiye jakkarta tayi a kan desk din gabanta Tafiddo abubbuwan data saya don dama yunwa takeji don bata wani ci abincin kirki ba kafin tafito

Kai burger din tayi abaki bayan tayi basmallah ta gutsira tafara tauna ahankali

Cak ta tsaya da taunar lokacin da idanunta ya sarqe da oily hazal eyes dinshi... ✍️


Kuyi manage please, banida isashen chaji aradu😞


Ummin fasihu πŸ§šπŸ»β€β™€οΈ?
8/2/21, 9:32 PM - Buhainat😝: *πŸ™πŸ»β€β™‚οΈDEEN πŸ™πŸ»β€β™‚οΈ?*







*015*




Jitayi komai nata ya tsaya cak, kafeshi da idanu tayi cikin son tabbatar wa kanta yanzun ma ba gizo yayi mataba.

Shi din dene, zauna daga can gaba yana facing dinta.

Sanye yake cikin qananun kaya, wando jeans sai jar riga, kasancewar rigar mai guntun hannu ne hakan yaba damtsen hannunshi damar bayyana sosai

Yaqara haske, lips dinshi sunqara pink sai gashinshi dake adan tuje as usual

Batasan tayi missing dinshi har haka ba sai yanzu don jikinta har tsuma yake deep down datake kallonshi.

Janye idanunshi yayi daga kanta ya maida kan book din dake kan desk yacigaba da rubutunshi, fuskarshi expressionless


Itakau a bangarenta kasa janye nata tayi sai kallonshi take hoping zai qara dagowa.


Tunda suke dashi yau tafara tsayawa tayi mashi kallon tsaf.

Fuskarshi oval shaped ce, yanada wasu irin fararen idanu masu mugun daukar hankali, idanun basada irin girman nan haka zalika ba lumsassu bane, gasunan dai. Idanunshi irin masu maiko2 dinnan ne wanda hardasu suke taimakawa innocent look dinshi fitowa.

Asaman idanun akwai girare dake cunkushe da gashi wanda har sunkusa hadewa don koyaya yadan yamutsa fuskarshi sai sun hade

Yanada hanci mai tsayi sosai sai madaidaicin baki dake dauke da pink tausassan lips

Yanada saje kwantattu dasuka qara qawata fuskarshi sai dan dimple dinshi dake tsakiyar gemushi wanda ko magana yake yana lotsawa

Fari ne saidai yanayin fatarshi zai saka kokwanton ko dan nigeria ne don irin farin nan gareshi tass babu sirki ko kadan don idan ba sani kayi ba sai kayi mashi daukar balarabe kuma...


Tashin dataga yayi ya dawo daita daga duniyar kallonshi

Ganin ya juya zai fita yasata Saurin zabura itama ta tattara kayanta ta watsa a bag sannan itama ta tashi ta fito.

Abin dariya sai alokacin ta tuna da burger din bakinta da tundazu tagaza taunewa.

Furzar daita tayi tashiga bin Deen dake tafiya da dan sauri


Ganin haka yasa itama qara pace, nan da nan ta taddoshi tasha gabanshi daidai wani silent wuri dake cikeda bishiyoyi.


Tsayawa tayi gabanshi hannu riqeda kugu tana kallonshi

Shima jan burki yayi ya tsaya yana kallonta fuskarshi babu walwala.

"da kake neman guduwa cemaka akayi kana iya tseremin ne?" tafada tana dan Girgiza

Kauda kai yayi still fuska ba walwala

"kaii.." tafada tana kyakyafta mashi yatsu hakan yasa yajuyo yana kallonta

"To gani, kabani haqurin" tafada tana Kauda kai gefe still hannunta Riqe da kugu

Tsayawa yayi yana kallonta da alamun mammaki a fuska

Jin shiru yasata sake waigowa gareshi tace
"kabani haqurin mana, ba nemana kake don kabani haquri ba? Naji ance babu inda baka zagaye a fadin school dinnan don nemana ka bani haquri ba, yanzu gani na taqaita maka wahala, go ahead ina jinka"


Ganin abin nata rainin hankali ne yasashi zagayeta da nufin tafiya taqara Saurin shan gabanshi


Bude baki tayi zata qara magana yariga ta
"what again? Me kuma zaki qara yimin? Am sorry amma ban ida warwarewa akan abinda kikayimin ba rannan, haquri kike son inbaki? To am sorry, sorry for everything, laifi nane dana ta6amaki kaya Batareda neman izininki ba, am sorry, hakan bazata qara faruwa ba, please free me.. Ki kyaleni hakan inyi rayuwata, please. Tsawon kwanakinnan nayi iya bakin kokari na don gujewa haduwarmu shiyasa banama bin hanyar da nasan zata hadamu, please leave me alone now, let me live my peaceful life again.. PleaseπŸ™πŸ»" ya qarashe yana hade hannu alamun roqo


Tunda yafara taji kamar an zaremata lakka daga cikin jiki taji jikinta yayi lakwas

Zagayeta yayi ya wucewarshi hakan yasa itama ta juya tana kallon bayanshi

Yayi nisa ya tsinkayi muryarta

"Deen!"

Dakatawa yayi da tafiyar shi ya tsaya Batareda ya juyoba

Share hawayen daya gangaromata tayi sannan ta tako zuwa kusa dashi

"am.. Sorry" tafada ahankali tana kallon bayanshi

Bece komaiba haka kuma be juyoba

"I.. I don't know what came over me that day, I was mad and..." Sai kuma ta kasa qarasawa, idanunta ta rintse tareda kamo lower lip dinta ta cije wasu hawaye da batasan dasuba suka gangaro mata

"am so sorry" tafada cikin rada still idanunta arufe


Sai a sannan yajuyo ahankali ya fuskanceta, jin alamun ya juyo din yasata bude idanunta itama dasuke ajiqe suna kallon juna.


πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–


"... Wannan dalilin yasa nayi iyakar bakin qoqarina na ganin nasamu wani abu a assignment din don ko ba komai zai dan taimakamin daga barazanar carryover din da nake fuskanta, shiyasa lokacin da nagane ka chanzamin takarda naji hankalina ya tashi sosai kuma na fita hayyacina don aganina shikenan Wannan damar tariga ta kufcemin.... bansan kanada pneumonia ba, lokacin da labarin ya riskeni naji ba dadi sosai, ban ta6a tunanin reaction dina zai kai ga hakaba, am sorry" ta qarashe tana Dagowa ta kalli Deen dake zaune daura daita da shima ita yake kallo

Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace
"nima tsotsai yasa na ta6a takardar, bayan nakoma gida ranar, nafiddo littafin ki don inyi maki copy din saina tsinci takardar aciki, koda naduba sainaga assignment ne kuma kinyi, sai nayi going through din takardar naga duk akwai errors a calculations dinki, da farko naso inyi correcting dinshi a paper din sai naga zata 6aci shiyasa na samu wata sabuwa nayimaki ashe rabon kwanciya asibiti yasani yin hakan" yafada yana hade gira

Maka mashi littafin hannunta tayi kadan tace
"ba nace am sorry ba"

Sosa inda ta makamashi littafin yayi yace
"O'O!"

Dariya tayi tace
"wai kai idan baka ce O'O ba bakajin dadi?" tafada tana jin zuciyarta wasai yanzu

Daga kafadunshi yayi yana ta6e baki sannan yace
"yanzu ya assignment din? Nawa kikaci?"

Yatsina fuska tayi tace
"as I feared, zero over idanuwa" tafada tana gwale idanu

Dan chuckling(Dariya marar sauti) yayi wanda yaba dimple din gemenshi damar lotsawa yace
"O'O! They're big"

"menene?"

"wadannan" yafada yana nuna idanuwanta

Hade rai tayi tace
"ina ruwanka dasu? dama rannan kace baka sonsu" tafada tana qara zaro mashi su

Rufe fuskarshi yayi yace
"O'O! Kibari"

"idan naqi fa? Mexakayi" tafada tana qara qwalalosu

"mefa? Aini yanzu tsoronki nake" yafada yana maida fuskarshi kalar tsoro🀒

Dan Wara idanu tayi tace
"tsorona kuma?"

"eh mana, wancan karon kinyi landing dina hospital Wannan karon bansan inda zanyi landing ba"

Bata fuska tayi tace
"nida ka fallamin mari fa?"

Shima dan Wara idanu yayi ya rufe bakinshi yana Dariya
"O'O! Nidai babu ruwana"

Yitayi kamar zata sake makamashi littafin tace
"akwai ruwanka harda gwadogwadonka"

Hakanan take jin kanta cikin nishadi, zuciyarta wasai kamar bata ta6a quntata ba

"kece kika gigitani ai, bakiji ba sadda kika watsamin coke dinnan, kamar zan shid'e, the thing is so sudden and unexpected, sainaji kamar zan mutu"

Jitayi tausayinshi duk ya lullu6eta, he's so innocent and simple, bayada matsala ko kadan

"sharrin zuciya ne, alokacin am mad with anger shiyasa nayi duk abinda yazo min akai" tafada tana 6ata fuska

"da ranki ya 6aci meyasa bakiyi inhaling tasbih kiyi exhaling tahlil ba? Nasha fada maki kakata tace idan ran mutum ya 6aci yayi inhaling tasbih yayi exhaling tahlil sannan kuma idan kashiga tashin hankali ko wani masifa ta tunkaroka Allah (s.w.t) yace " *wa basheeris- sabirina lathina iza asabathum musibatun qalu innalillahi waina ilaihi rajiun*°° *ula'ika alaihim salawaatun min rabihim wa rahmatun, wa ula'ika humul muhtaduun*

Ma'ana : *kuma kayi bushara ga masu haquri wadanda idan muka jarabcesu da wata musiba suna cewa 'daga Allah muke kuma gareshi zamu koma'* °° *wadannan mutanen albarka da rahmar ubangijinsu zai tabbata agaresu, kuma wadannan mutanen sune abisa tafarkin gaskiya*

Yin abu kai tsaye cikin fushi yana jawo aikin danasani, danasani marar amfani, kuma ambaton Allah a lokacin tsanani ko tashin hankali yana kawo rangwame ga mutum akan Wannan abin, don haka ki dinga kulawa"

Zee daketa sauraronshi tundazu tace
"hmm gaskiya ne alarrama Deen, shikenan daga yau zan dinga inhaling da exhaling din"

"dama wadancan din" yafada cikin son tunamata

"eh tabbas, dama wadancan din" tafada tana kada kai

"yauwa, kingani idan kinayin haka bazaki dinga over reacting ba kuma Allah zai sauqaqamiki duk abinda yayimiki zafi" yafada in a serious tone

Murmushi tayi don ita dariyama yake bata
"hakane kam, shukran"

Shima Murmushin yayi sannan ya dan karkace ya fiddo biscuit daga cikin aljihun wandonshi ya fasa sannan ya miqomata

Murmushi tayi sannan ta zari guda tana cewa
"biscuit kamar wani qaramin yaro?"

Dan Wara idanu yayi yace
"ni babba ne?"

"qatoto ma" tafada tana nuna girman da hannu

6ata fuska yayi yace
"O'O! Niba qatoto bane"

Dariya tayi tana taunar biscuit din tace
"To nufinka kai qarami ne? Ca6!"

"eh din amma ai ba qatoto bane, qatoto fa babba ne sosai mai qiba da tunbi"

Dariya tasakeyi sosai ganin yadda ya 6ata rai sosai shi adole beson acemashi qato

"kaima kanada tumbin ai"

Wara idanu yasakeyi

"ni? Ina?" yafada yana qoqarin daga rigarshi don gani

Saurin Kauda kai tayi tana Dariya tace
"kaga dawasa nake maka bakada wani tumbi"

"amma kika cemin qatoto" yafada yana sakin rigar

"ai shine nace da wasa nake ko?"

Harararta yayi yakoma ya jingina da iccen dake bayanshi yana cigaba dacin biscuit din hannunshi

Bude jakka zee tayi itama taciro burger dinta da freshyo ta Ajiye tsakiya

Shiru wajen ya dauka na wani lokaci ganin haka Yasata sake lalubar jakkar ta fiddo takardar assignment din ta miqomashi

Kallon takardar yayi ya kuma kalleta yadan daga gira daya alamun meye?

Daga kafadu kawai tayi tana qara miqomashi hakan yasashi amsa

Warwarewa yayi ya duba saikuma yayi slight Murmushi yana Kauda kai

"kaga zero over kunnuwa dakasa naci ko?" tafada tana antayamashi harara

Murmushi kawai yasakeyi bece komaiba

Sake duba takardar yayi sannan yace
"meyasa ta jiqe haka?"yafada yana nuna jirwayen datayi

Daga kafadu tayi tace
"qila ruwa ya ta6ata"

"hmm you're careless" yafada yana 6ata face

"whatever" tafada tana juya idanu

"yanzu nasan bakida fargabar carryover tunda nasan marks da zaki samu a exams idan aka hada da wannan zakiyi average"

Duum! Gabanta yafadi ita sai yanzu ma ta tuna da yadda suka kaya da mr ibrahim

"hmm, tukkuna dai, Wannan marks din basa cikin lissafi" tafada tana gutsirar burger kadan

"why not?" ya tambaya yana kallonta

"well, cewa yayi zan sake wani cos yana tantamar bani nayi wancan ba"

"so what? Ba assignment bane? Idan yanaso Kuyi dakanku why beyimuku a class ba as test?"

Watsa hannuwa tayi alamun oho ranta na qara jagulewa

Shiru yadanyi kamar mai nazari sannan yace
"yaushe zakuyi?"

"monday" ta amsa a gajarce

Dan Wara idanu yayi yace
"Wannan coming monday din?"

Kada mashi kai alamun eh tayi kawai

"so hope kindai shirya"

"shirin me zanyi? I'll just do my best and leave the rest"

Dan Dariya yayi ganin tana magana a dan fusace

"inhale and exhale, zakiji sauqi" yafada yana Murmushi

Wata harara ta maka mashi ta Kauda kai

"mutuminnan hates you" yafada yana still yana Murmushi

"I know, and I hate him more" tafada ranta na qara 6aci

Wani Murmushin yasakeyi yace
"I'll help you"

Sai a sannan ta juyo ta kalleshi

Shiru tadanyi sannan tace
"really?"

Kadamata kai yayi yace
"yes, I'll help you da dan abinda na iya"

Jitayi farinciki ya lullu6eta
"dade dayawa daka iya" tafada tana Murmushin jindadi

"ni me na iya?" yafada yana warware takardar

"komai ma, imagine Wannan uban aikin amma naci 19/20 kuma nasan duka naci kawai rage dayan yayi"

Murmushi kawai yayi yana duba takardar

"yanzu dai mufara da solving wadannan" yafada yana Ajiye takardar gabansu

"bring out your writing materials"

Hakan tayi ta fiffido kayan amfani cikin zumudi sannan tadan rage taxarar dake tsakaninsu

"you know, mathematics subject ne dake buqatar aiki da brain, duk cikin subjects babu mai chaxa kwalwa kamar shi, idan kinaso ki qware akai to you have to be alerted always, ki dinga practicing din difficult difficult solving on your own Koda kuwa ba'a ta6a koya mukuba, kidinga karambani na solving din kome zaki gani Koda kuwa baxakici daidai ba, da haka da haka zaki ga kema kin gwanance"

"kamar kai?"

Harararta yayi ya Kauda kai Batareda yace komaiba

"yanzu bari mufara da wadannan, shi mathematics steps of calculations gareshi, missing din step daya na iya 6atamiki aiki, bayan formula(s) abinda ya kamata ki laqaita sune steps, yanzu kamar Wannan..."

Nan suka shiga solving din aikin, sosai zee ta maida hankalinta akan abinda sukeyi kuma sosai abin ke zama akanta.

Saida suka shafe awa 1 da rabi ahaka don sosai yake fayyacemata komai shiyasa kafin su bar wani question sai sun dan jima don be bari su qara gaba sai ya tabbatar tagane Wannan sosai

Ita

Please Login or Register in order to submit comment