Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[11/30, 10:15 PM] LubnaSufyan: ®
📖✏
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION

LubnaSufyan
Calmlubna@gmail.com

Alkalamin Kaddara

Prologue

"Na sha dauka mahaifiyar kowa haka take kamun inyi hankali, sai daga baya na fahimci ni kadai nai rashin sa'a. Na sha fatan in kwanta bacci in tashi a gidan da ba nan ba, har sai da na fahimci ba komai rubutun ALKALMIN KADDARA yake iya canzuwa ba. Ta wani fannin yau burinki ya cika...ta wani fannin ke da kanki kinyi nasara wajen wargaza burin naki..."

Muryar Tasneem ta sarqe saboda sabon kukan dake shirin kwace mata.

"Tsakanin yau zuwa gobe idan aurena ya mutu kece...Idan mutuwar shi bata faru a daren yau zuwa safiyar gobe ba, makomar shi kece sila. Abba bazai yafe miki ba Umma, kaman yanda nima bazan yafe miki ba..."

"Tasneem..."

Bara'atu ta fara muryarta da duk jikinta na kyarma, maganganun Tasneem din na zauna mata a wajajen da bata san da su ba. Girgiza mata kai Tasneem take hawaye na zubar mata.

"Bana son jin komai...lokacin da na sha jiran jin kalamanki ko bayanin ki ya wuce umma. Bazan roqi komai daga gareki akan su Hamna ba...Zan tuna miki mu duka Amana ne a wajenki... Idan baki dubi Allah ba bansan me yasa kalamaina zasu canza komai ba..."

Tana karasa maganar ta sa hannu taja mayafin da ta dage lokacin da aka shigo da ita daga dakin, tana rufe fuskarta dashi lokacin da hawaye masu dumi suka zubo mata. Dan ko zama batai ba daman, wani irin zafi kirjinta yake mata yau wajen wata biyu kenan, tari Tasneem ta soma ba kakkautawa da yasa Bara'atu da sai lokacin ta samu motsi tashi da sauri ta karasa wajenta tana kamata hadi da daga mayafin dake rufe da fuskarta.

Hannuwan da Tasneem ta sa ta rufe bakinta ta dawo dasu dubanta jin lema a jikinsu, har lokacin tarin da take bai tsagaita mata ba, tsilli-tsillin jini tagani a jikin tafukan hannunta.

"Tasneem tarin jini kike..."

Bara'atu ta fada hankalinta a tashe, zame jikinta Tasneem tayi daga riqon da tai mata tana nufar hanyar kofa, dan tarin ya fara tsagaita mata. Sai dai kirjinta da yake kaman ana hura mata wuta, har numfashinta sama-sama yake saboda azaba...!

**

Ko ina na jikin ta kyarma yake, musamman zuciyarta da take dokawa har cikin kunnuwanta, kallon shi take da bayanannen tsoro a kan fuskarta. Gam yaja kofa yana kulle zuciyarshi da duk wani emotions dazai iya samun fitowa, fuskarshi babu komai akai ya sauke idanuwan shi cikin nata

"Ni da ke bamu taba wuce wani abu da ya girmi nisha di ba, bansan me nayi daya saki tunanin ko zuciyata kin isa ki hango ba balle ki samu waje a ciki, bakuma zan baki hakuri ba dan babu kuskuren da nayi, banyi komai da babu amincewar ki ba..."

Hannu Fadila ta sa tana dafe cikin ta da yake yamutsawa da sabon tashin hankali. Inalillahi wa ina ilaihi raji'un take son furtawa amman kaman an kulle mata baki, sai lokacin nauyin komai yake danne ta, abin da yake tsaye a wuyanta take son hadiyewa amman ta kasa, sau uku tana bude bakinta da niyyar magana amman babu abinda yake fitowa. Numfashi take ja ta bakinta tana fitar dashi a wahalce.

"Nawfal???"

Ta kira sunan shi cike da shakku da alamun tambayoyi da dama, muryarta can kasa, idanuwanta na kasa yarda shine tsaye a gabanta. Zuciyarta na qin aminta da abinda kunnuwanta suka ji. Nawfal bazai mata haka ba, ba zuciyarshi kawai ta iya hangowa ba, tana da yaqinin har cikinta ta shiga ta samu wajen zama.

Ganin yanayin dake fuskarta yasa Nawfal kama hannunta yana janta, mamaki ya hanata yin komai banda binshi, har yakai ta bakin kofa ya hankada ta, badon bangon da ta dafa ba, babu abinda zai hanata mummunar faduwa.

"Ko meye kike tunanin yake tsakanin mu ya zama tarihi a yau!!!"

Bakin shi kawai take ganin yana motsi, kunnuwanta sun daina jin sauran kalaman, tashin hankalin da take ciki da maganganun shi na farko sun sa komai tsaya mata cik. Girman kuskuren yarda dashi na danne ta...!!

**

Hannun shi Tariq yake kokarin kwacewa yana juyawa hadi da kallon gidan, hawaye masu dumi na zubo mishi. Sakin hannun shi Ashfaq yayi yana tallabar fuskar shi ya juyo dashi.

"Ba mu da dalilin juyawa baya Tariq, babu abinda ya rage mana, komai ya kare, ni da kai ne kawai..."

"Ta ina zamu fara? Ina zamu je? Yaya haka rayuwa take da wahala?"

Tariq ya karasa wasu sabbin hawayen na zubo mishi, da ganin su kesa zuciyar Ashfaq wani irin ciwo marar misaltuwa. Fuskar Tariq din ya tallaba da dukkan hannayen shi, a zuciyarshi ya fara jin zaman kalaman kamun ya fito dasu.

"Ban sani ba nima...babu abinda yake da tabbas, na so labarin rashin tabbacin rayuwa kawai zan baka Tariq, bawai ka tsinci kanka a cikin shi ba, zuciyar dake bugawa a kirjina kanta babu tabbacin zata kai anjima, abu daya na sani a wannan matakin, da duk numfashin da zan fitar daga yanzun zuwa na karshe zan tabbatar ko yayane taka rayuwar akwai sauqi a cikinta...zan tabbatar hawayen ka sun zuba ne badan kunci na rayuwa ba. Kana jina? Baka bukatar kowa in ina nan..."

Idanuwan shi Tariq ya kalla, a cikin su yana ganin gaskiyar alkawarin da Ashfaq yai mishi, a cikin su Yana ganin rubutun ALKALMIN KADDARAr su da yaren da yafi karfin fahimtarshi...!
[11/30, 10:15 PM] LubnaSufyan: ®
📖✏
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION

LubnaSufyan
Calmlubna@gmail.com

01

Zaune take a gaban mudubin, jikinta sanye da doguwar riga ta material mai fari da purple mai haske a jiki, hannunta riqe da dankwali purple da take daurawa akanta. Turaruka ta dauko kala biyu tana feshe jikinta. Duk da kyan datai bai hana damuwa bayyana a fuskarta ba.

Idan tace ga yanda tayi rayuwa a wata dayan nan, cikin gidan Rafiq ba zata iya fada ba. Komai zuwa yake yana wuce mata, hannu tasa tana dafe kirjinta, wajen zuciyarta da yake mata zafi kaman zai kama da wuta. Kanta ta kwantar jikin mudubin tana maida numfashi ta bakinta saboda azabar ciwon da take ji.

Badan bata tsammaci kauce ma abinda yake faruwa yanzun ba, badai ta dauka zaiyi ciwo irin na yanzun ba, hukuncin data tsammaci Rafiq zai mata daban da wanda ya dauka. Duk da banbancin kalilan ne, da igiyar auren shi har ukku akanta. Wannan ma wani abu ne, zuciyarta ta fada mata.

Runtsa idanuwanta tayi, daren ta na farko a gidan Rafiq din na dawo mata, kamar a lokacin yake faruwa.

*

Kuka take da yake jin shi har kasan zuciyarshi yana kara mishi ciwon da takeyi, kamun ya janye jikinshi daga nata yana jin daudar dabai kamata ace yanajin ta ba. Hannunshi yasa yana goge bakin shi cikin son cire yanayinta daga jikin labbanshi. Runtsa idanuwa yayi yana kirga daya zuwa goma cikin kanshi, nutsuwa yake bukata ko yaya take kamun yayi abinda su dukan su zasuyi dana sani.

"Ni ya kamata inyi kuka Neem...ni ya kamata in zubda hawaye bake ba..."

Kamar maganganun shi take jira dan karama kukan da takeyi gudu. Muryarta na sarqewa ta soma magana

"Sugar...ka fa...ka fahimce ni dan Allah..."

Wata irin dariya Rafiq yayi da bata da alaqa da nishadi, yana dafe kanshi dake juyawa da duka hannuwanshi biyu, kamun ya mike yana nufar bandakin dake cikin dakin ya tura ya shiga yana doko kofar, karar da tayi na gauraye dakin kasancewar dare ne.

Mikewa zaune Tasneem tayi tana jingina bayanta da kan gadon hadi da janyo kafafuwanta ta hade jikinta waje daya. Kuka take har numfashin ta na barazanar daukewa, idan tace ga yanayin da take ji karya take, sai yanzun tasan in tashin hankali yai girma bashi da yanayi sam.

Hannuwa take sawa tana goge fuskarta da wasu sabbin hawayen ke sake batawa, jikinta ko ina bari yake, dakyar takai hannunta ta lalubo wayarta dake ajiye kan drawer din gefen gadon. Dannawa tayi tana swiping key din dake jiki. Karfe uku da rabi na dare.

Hakan bai hanata lalubo number din Samha ba. Bata jin zata iya magana dan haka ta tura mata text:

'Yagane Samha... Wallahi bazan iya rasa shi ba. Shi kadai ne dai-daito dana samu a rayuwata na tsayin lokaci, bazan iya rasa shi ba... Bazan iya ba'

Ko wayar bata ajiye ba kiran samha ya shigo, sai da Tasneem ta share hawayen da ya zubo mata tukunna ta daga ta kara a kunnenta, muryar samha na saka sabon kuka kwace mata.

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un... Tasneem.... Ya Allah. Wallahi na kasa bacci tun dazun gabana sai faduwa yake.... Yana ina yanzun?"

Cikin kuka Tasneem ta amsata

"Yana bandaki...na shiga ukuna samha..."

Ta karasa tana kokawa da numfashin ta da baya kaiwa inda ya kamata yakai.

"Ke! Ki nutsu! Ki saurareni.... Babu abinda zai faru In shaa Allah.... Shisa naso ki fada mishi gaskiya sanda ya tambaya..."

Har lokacin numfashinta bai koma yanda ya kamata ba, hakan bai hana maganganun da samha tayi su dauki tunaninta su watsa wani lokaci can baya ba.

*

A zaune ta same shi cikin motarshi, driver dinshi na dayan gefen. Sanin ko gaisuwa ba zata hada su ba yasa bata bi takanshi ba. Hankalinta nakan Rafiq da kafafuwan shi na daga waje, ya dafe goshin shi da hannuwanshi duka biyun. Bata san dalilin da yasa zuciyarta bugawa ba. Cike da shakku ta kira shi

"Sugar..."

Dago fuskarshi yayi yana sauke mata idanuwan shi da suka canza launi saboda bacin rai.

"Waye Alhaji Madu?"

Gyara tsayuwarta tayi dan zata iya rantsewa tana jin bugun zuciyarta har cikin tafukan kafarta. Ta bude bakinta yakai sau hudu tana rufewa saboda babu kalma ko daya data iya fitowa.

"Neem tambayar ki nake. Waye Alhaji Mando?"

Gudu tunaninta yake cikin kwakwalwar ta da hada karyar kamun ta dorata kan harshenta da fadin

"Kaman na taba jin sunan, ina tunanin ko a ina"

Tayi mamakin muryarta da batai rawa ba, da dukkan karfin halin da take dashi take jure idanuwan Rafiq da suke cikin nata da wani yanayi.

"Na gaya miki abu na farko dazai iya wargaza alaqar mu shine karya, ni da karya muna da tarihi marar dadin ji..."

Muryarta a karye, zuciyarta cike da wani irin tsoro da take addu'ar bai nuna akan fuskarta ba tace

"Ehen...Nasan na taba jin sunan, wani mutum ne da yasha zuwa kofar gidan nan wai yana sona. Sugar kallo daya zakai mishi kasan ba mutumin kirki bane ba...saida na daina fitowa in ya aiko tukunna ya hakura ya daina zuwa..."

Kallon ta Rafiq yake yi, kallon ta yake yana son fahimtar gaskiyar maganganun da tayi ta cikin idanuwanta.

"Ba koda yaushe nake yarda da shaidar mutane akan yan uwan su mutane ba... Allah yasa kar inyi dana sanin yarda dake"

Kai take daga mishi da sauri tana kokarin dora murmushi akan fuskarta.

"In shaa Allah ba zakayi ba...ka shigo mana"

Girgiza mata kai yayi yana jan kafafuwanshi ya mayar cikin motar. Hadi da jan murfin ya rufe kamun yace mata

"Akwai inda zanje... Abinda nazo tambayarki kenan daman"

Matsawa tayi daf da motar sosai tana yawata idanuwanta kan fuskarshi hadi da sauke muryarta

"Ranka a bace yake har yanzun... Zuciyata ba zata samu nutsuwa ba"

Numfashi yaja yana saukewa a hankali. Ranshi a bace yake batai karya ba, maganganun da yaji sun tsaya mishi, duniyarshi a birkice take, wajenta kadai yake samun nutsuwa, in ya rasata baisan abinda zai kama ba. Kallon ta yadanyi

"Abubuwa ne sukai mun yawa..."

"Are we okay? Ni da kai?"

Kai yadan daga mata. Yanajin ta sauke wani dogon numfashi da ita kanta bata san tana rike dashi ba. Tana kallon shi yaima driver din nuni da hannu alamar su tafi, batare da ya sake ce mata komai ba har driver din ya tayar da motar suka wuce. Sai lokacin kafafuwanta da sukai sanyi suke barazanar kin daukarta.

*

"Tasneem!!!"

Muryar samha ta katse mata tunanin da take, jan hanci tayi, muryarta a dakushe da kukan da takeyi tace

"Zamuyi magana da safe...ina son zama ni kadai..."

"Neem please..."

Samha ta fadi ta dayan bangaren muryarta na karyewa. Cikin karfin halin da Tasneem bata ji ta katse ta

"Karki damu...kawai banHa son magana ne yanzun"

Bata jira amsar da samha zata bata ba ta janye wayar daga kunnenta tana yaddar da ita kan gadon. Dai-dai fitowar Rafiq da kugunshi yake daure da towel. Da busassun idanuwanta da suka sha kuka har tana jin hawayenta sun kafe take binshi da kallo.

Sif din kayan dake cikin bangon ya bude wandon da hannunshi ya fara kaiwa kai ya dauko yasa ma jikinshi yana dauko riga batare da damuwa da kalar su ba. Asalima basu bane damuwarshi, wajen gadon ya karaso yana sa hannu ya dauki mukullin motarshi dake ajiye a kan kafet da wayarshi yana zurawa a aljihu.

Ganin yana shirin fita yasa Tasneem saurin sakkowa daga kan gadon tana shan gabanshi. Kauda kai yayi gefe baya son ganinta sam-sam. Rabata yayi zai wuce ta sake shan gabanshi. Hawayen da take tunanin sun kafe suna zubo mata, tasa hannunta ta goge.

"Ina zaka je cikin daren nan? Ba tuqi kake iyawa ba..."

Bai amsata ba yasa hannun shi yana ture ta gefe hadi da takawa ya nufi kofa, cikin zafin nama ta kamo hannun shi.

"Kabari saida safe"

Hannun shi ya kwace daga cikin nata yana kallonta cike da wani abu da bazai iya fassarawa ba, zuciyarshi naci gaba da tafasa, komai zai iya faruwa in yana ganinta a gabanshi.

"Bana son ganinki... Neem bana son ganinki wallahi"

Runtsa idanuwanta tayi tana jan numfashi, maganganun shi na sukar zuciyarta da ciwon da bata taba sanin shi ba a rayuwarta.

"Control dina gab yake da samun matsala, komai zai iya faruwa in ina ganinki..."

Tasan shi, tasan halin shi, saidai bata taba jin bacin ran da take ji a muryarshi ba tunda take dashi. Komai ciwo yake mata, zuciyarta na rarraba radadin da take zuwa ko ina na jikinta. Tana jin takunshi da murza kofar da yayi kamun tace

"Abinda yake faruwa yanzun...Shine dalilin yi maka karya. Tsoron rasa ka ya hanani fada maka gaskiya..."

Bugo kofar dakin da yayi ta fada mata cewa ya fice, nan inda take tsaye ta durkushe tana sakin wani kuka daya fito tun daga zuciyarta...!

*

Ringing din da wayarta take ne ya katse mata tunanin data ke, hannu tasa tana goge fuskarta saboda hawayen da bata ma san suna zuba ba sun jiqa mata kunci, mikewa tayi da niyyar karasawa kan gadon ta inda wayar take tana kara, babu shiri ta koma ta zauna tana runtsa idanuwanta gam, dakin jujjuya mata yake.

Ga kirjinta kaman an dora dutse saboda nauyin da taji ya mata.

"Ya Allah..."

Ta fadi tana sake runtsa idanuwanta gam ko zata samu jirin da yake dibarta ya daina. Tana jin wayar harta yanke, kiran ya sake shigowa amman ta kasa mikewa, tana alaqanta jirin da take ji da rashin cin abincin da rashin nutsuwa yake hana mata. Wajen mintina sha biyar ta dauka a haka kamun dakyar ta mike ta karasa kan gadon ta kwanta.

Wayar ta dauka ta cire key din dake jiki tana dubawa, Azrah ce, yanayin da take ji bai hana dan karamin murmushi ya kubce mata ba. Kiran ta mayar tana kara wayar a kunnenta, ringing din farko Azrah ta dauka da fadin

"Ya Tasneem ina kika shige? Inata kira baki dauka ba, lafiya dai ko?"

Muryarta can kasa, wata irin kewar Azrah din take ji.

"Bana kusa ne Azrah, lafiya kalau. Ya kuke? Ina su Hamnah?"

"Lafiya kalau, na ci intro dina. Yanzun aka kira ni ake fadamun"

"Haba dai? Oh Allah. Ma Shaa Allah... Kinga abin Allah ko?"

Tasneem din ta karasa muryarta da kwari fiye da sanda ta daga wayar. Ta jima bata ji wani labari mai dadi kaman na yanzun ba.

"Gabana yana ta faduwa. Kar ayi irin na wancen karin... Kiyi ma Ya Rafiq godiya please. Ko fara fada mishi na samu... Na kira shi bai dauka ba, nasan dai zai kirani inya gani"

Kiran sunan Rafiq din da Azrah tayi ya sake jefa Tasneem cikin yanayin da take dazun, dan jitai har cikinta saida ya kulle, kirjinta da yadan tsagaita da zafin da yake mata yana dawowa.

"Hello..."

Dakyar ta iya fadin.

"Congrats Nurse Azrah... Zan fadi mishi In shaa Allah"

Tanajin dariyar Azrah ta cikin wayar

"Tun yanzun har na zama Nurse din ma?"

Sam Tasneem ta nemi dariya koya take ta kasa.

"Ki gaishe da su Hamnah. Barin duba girki"

"Tam zasuji... Ki kula da kanki"

"Kema haka"

Tasneem ta fadi tana sauke wayar daga kunnenta. Cikin kanta tana lissafa kwanaki goma sha shidda cif rabon da tasa Rafiq a idanuwanta. Sai dai taji motsin shigowarshi da fitarshi wasu lokuttan. Duk da bata ga laifinshi ba, hakan bai hana abinda yake yi mata ciwo na gaske ba.

Hannu ta sa tana sake goge hawayen da ya samu wajen zama tare da ita yanzun. Yanda yake saurin zuba har mamaki abin yake bata. Mararta taji kaman zatai ciwo, ta lumshe idanuwanta, wannan karin tayi kari harna kusan sati.

**

KANO

Idanuwan shi kafe suke kan kwalaben codien din dake gabanshi. Hannuwanshi da suke a dumtse har kaikayi suke mishi na son daukar kwalbar. Zai iya rantsewa har kan harshen shi yana jin dandanon hadin da yake cikin kwalbar daya fi komai tafiyar mishi da damuwa.

Agogon dake bangon dakin yaji ya soma kukan da yake a duk lokacin da awa ta cika, kamun ya soma bugawar da yake jin kirgar har cikin zuciyarshi. Sai da ya buga sha biyu cif tukunna yai shirun daya gauraye dakin.

Hannunshi ya mika ya dauki kwalba daya, cike da sabo ya girgiza ta yana gauraye kwayoyin dake ciki da yasan sun gama narkewa. Zuwa yanzun abu daya yake ci mishi rai, damuwa daya ce ta addabe shi da hanya daya yasani dazai iya mantawa da koma menene.

'Kamun alkawari zan iya yarda dakai wannan karin...'

Kaman maganar ta tunkuda hannunshi ne, zuciyarshi tai wani irin bushewa, yana jin dandanon codien din da kwayar kan harshen shi ya lumshe idanuwanshi cike dajin yanda yake ratsa shi yana gamsar da kishin dayai watanni yana ji, da sauri ya kwankwade kwalbar gabaki daya yana maida numfashi.

Ajiyewa yayi yana daukar wata hadi da sake kwancewa, yana son ya daina ganin fuskar Yayan shi cikin zuciyarshi, yana son ya daina ganin fuskarta, yana son ya daina jin abinda yake ji. Ya daga kwalbar kenan wayarshi tai qara da saida ta tsorata shi har kwalbar na shirin subucewa daga hannunshi.

Juyar da kanshi yayi yana kallon wayar dake gefenshi ajiye. Ganin kowacce number ce aka kirashi da ita yasa shi ajiye kwalbar yana dauko wayar da sauri.

"Yaa Faq..."

Ya fadi zuciyar shi na dokawa.

"Muna Aminu Kano Tea...."

Bai bari ya karasa ba yai wata irin mikewa cike da tashin hankali.

"What? Ina Yayan? Meya same shi? Me ya faru"

Yake jero tambayoyin yana karasawa ya zura takalman da bai tsaya ya duba kowanne kala bane ba.

"Inka karaso zan fada maka... Ana bukatar jini ne shisa ma na kira ka"

Dan dafe kai yayi, yana jin an kashe wayar daga dayan bangaren.

"Damn... Dammit!"

Yake fadi zuciyarshi na dokawa da sauri-sauri. Da sauri ya fita daga bangaren su, yana ganin mutanen dake kai kawo a harabar gidan nasu, bai tuna mulillin motar shi baya jikin shi ba saida ya karasa inda motar take.

"Shit..."

Ya furta, bazai iya bata lokacin komawa cikin gida dauko mukullin mota ba, da gudu-gudu ya fita daga gidan, hakama ya karasa bakin titin unguwar tasu  ya koyi sa'a mai Napep yazo wucewa. Tare shi yayi ya shiga.

Hannunshi biyu dafe dakai yake zaune cikin napep din, inda zai iya daya zane kanshi da kanshi, me yake tunanin? Me yayi ma kanshi mintina kadan da suka wuce?

'Jini ake bukata shisa na kiraka'

Dago fuska yayi yana jan numfashi, group din jinin su daya da Yaa Faq din. Amman bayajin abinda yasha zai bari a diba, hadin nada karfi, duk da kanshi ya saba daukar cajin yana jin yanda idanuwanshi ke budewa cike da izzar da hadinne kawai yake saka shi ji.

"Malam tsoron Napep din kake yi ne?"

Tariq ya bukata ranshi a bace, gabaki daya ya raina gudun da mai napep din yake yi. Da yake bai hadu da dan rigima ba, murmushi kawai yayi baice komai ba. Suna karasawa AKTH ya zaro dari biyar ya bashi. Dan baima tambaya ko nawa ba ya wuce.

Number din Yaa Faq ya ke laluba a wayarshi ya kira dan yaji ko suna ta ina. AKTH ba bakonshi bane ba, asalima da asibiti na zama gida da an basu wani dan bangare a ciki saboda yawan zuwan da suke.

Kwatancen wajen yai mishi, sam baya son tunanin duk wani negative abu saiya karasa tukunna. Ganin Yasir tsaye ga kuma 'yan sanda guda hudu yasa Tariq jin zuciyarshi ta dawo cikin kafafuwanshi kaman duk takun da yake zuwa inda suke yana take ta ne shisa take bugawa da wani irin sauri.

Zai iya jin yanda duk wani jini yabar cikin fuskarshi saboda tashin hankali. Idanuwan shi yake yawa tawa kan rigar jikin Yasir da take jiqe da jini daga kafadarshi zuwa kan kirjinshi, ciwo yake nema dan ganin ta inda jinin ya fito ya kasa gani. Dan ko kadan baya son kawo ma kanshi jinin Ya Faq ne a jikin rigar Yasir. Muryarshi can kasa yana kallon Yasir yace

"Yana ina?"

"Ka kwantar da..."

"Damn it! Yana ina?"

Tariq ya fadi bai damu da mutanen da suke kallon su ba saboda daga muryar da yayi. Yanda abinda yasha yake mishi yawo batare daya ishe shi ba, inda zai karasa juye bacin ranshi yake nema. Dalili kawai yake son samu, kuma Yasir yana son bashi daya.

Idanuwanshi cike da ban hakuri yake kallon Tariq din da fadin

"Yana dakin Theatre..."

"Theatre?"

Kai ya dan daga mishi. Saida ya runtsa idanuwanshi da suke wani kasa-kasa da kansu tukunna ya bude su.

"Rashin hakurina gab yake da rinjayar hakurina....ka fara
DOWNLOAD
DOWNLOAD

1 Comments On ALAKALAMIN KADDARA PART 1
avatar
khadija-7-4

5 months ago

Reply

Yayi

Please Login or Register in order to submit comment