Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ciwon. Bazai sanadin bude mata shi ya koma sabo ba.

"Bakomai Inna"

"Hmm... Hassan yace mun ka mari wani a waje"

Runtsa idanuwanshi Tawfiq yayi yana bude su, Hassan data kira nasa zuciyarshi dokawa da sanin A-Tafida yagan su, daga Hassan har Hussaina, bakuma zai manta yanayin daya gani a idanuwan shi ba kan yaran. Zufa yaji tana tarar mishi a goshi da tafukan hannuwan shi

"Tawfiq..."

Inna ta kira da damuwa bayyane a muryarta

"Surutun Hassan ne kawai Inna"

Tawfiq ya fadi, a kunnuwanshi ma yanajin yanda muryarshi ta fito da karya karara, balle kuma Inna da duk wani motsin su tana kula dashi, saidai in ta kyaleka kawai.

"Hmm... Dan Allah dai a dinga kai zuciya nesa Tawfiq... Ka dinga saka salama a ranka"

"In shaa Allahu..."

Ya fadi a sanyaye.

"Tuwonka na daki nasa ankai maka tun dazun"

"Yanzun ma zan shiga dakin"

Ya amsa yana juyawa dan baison wata magana ta sake hada su da Inna. Sai dai bai kai da karasawa dakin shi ba, Baba ya shigo gidan da sallamar da Tawfiq din ya amsa.

"Tawfiq... Kai dawa kukai rigima?"

Lumshe idanuwanshi Tawfiq yayi bude su, ba kinkiba ya tsana ba, yana alfahari da asalin shi, yana kuma son kauyen shi, mutanen cikin shine suke da matsala, da yanda bakin su baya shiru musamman kan abinda bai shafe su ba. Yanzun haka idan akace su Salele zuwa sukai har inda Baba yake suka fadamai ba a musu.

Juyowa Tawfiq yayi, saida ya fara kallo yaga Inna ta koma daki, tukunna muryarshi can kasa yace

"Yanzun Baba har an fada maka..."

"Au damuwarka an fadamun ne, ba zuciyarka da ba zaka sama salama ba"

Ranshi Tawfiq yaji ya sake jagulewa

"Me yasa duk wani abu saiku yanke mun hukunci bakuji nawa bangaren ba?"

Dan jim Baba yayi yana tauna maganar Tawfiq din, kamun cikin taushin murya yace

"Saurin fushinka ne yake jawo hakan, sunce rako shi sukai yana neman mai gyara..."

Jingina bayanshi Tawfiq yayi jikin bangon dakin nashi, fuskarshi dauke da damuwa, muryarshi da yanayi mai nauyi

"A-Tafida ne Baba..."

Kiran A-Tafida kawai da Tawfiq yayi yana jin yanda yanayin komai yai shiru, har iskar dake buso shi yaji tabari, yana nazarin fuskar baba da shekarun shi suka sake nunawa kan fuskarshi lokaci daya, muryarshi da nisantaccen yanayi yace

"A-Tafida dinne yazo kofar gidan nan? Kofar gidan nan Tawfiq? Me ya..."

Karar faduwar abu da sukaji ne ya katse ma Baba abinda yake fadi yana saka su duka biyun juyawa inda sukaji karar. Nuwaira suka gani tsaye, da alama daga bandaki ta fito, manyan idanuwanta take warewa akan Baba da Tawfiq da suke kallonta cike da tashin hankali. Takowa tayi tana zuwa inda suke, muryarta na rawa take kallon fuskokin su

"Yaya..."

Nuwaira ta fadi, Tawfiq najin yanda a kalma daya bugun da zuciyarta yake yi ya fito ta ciki, yana jin kaman ya koma mintinan da suka wuce ya goge abinda kunnuwanta suka ji, cikin idanuwa yake kallon ta yana son bude mata zuciyarshi batare daya furta komai ba.

Yake son taga yanda yake dana sanin abinda taji, yanda yake rokonta karta bari ya fama mata ciwon daya san take fifitawa tsayin shekaru hudu. Yana kuma ganin yanda itama take rokon shi da nata idanuwan da hawaye ke taruwa ciki daya fada mata bataji A-Tafida a bakin shi ba.

Ganin yayi shiru yasa Nuwaira girgiza kanta

"Bai tako kafarshi kofar gidan nan ba... Yaya kace mun bai zo ba...."

Sadda kanshi kasa Tawfiq yayi, ciwon da yake ji a muryarta nasa zuciyarshi daukar dumi. Cikin sabon tashin hankali Nuwaira ta maida dubanta kan Baba

"Baba kace mun ko kusa da Kinkiba bai zo ba..."

Shima shirun yayi, wani irin numfashi Nuwaira taja, duniyar na taruwa tana danne ta waje daya. Wani karamin yaki na soma faruwa cikin zuciyarta, dan dai-daiton data samu yana hargitsewa.

'A-Tafida...'

Wata murya ta fadi cikin kanta da tasa ta runtse idanuwanta tana jan wani wahaltaccen numfashi.

'Kina da kyau... Idanuwanki sunfi komai jan hankali na. Yanda kike bude su duk idan zakiyi magana...'

Muryarshi ta diro mata, girgiza kai takeyi, hawaye masu dumi na zubo mata, wani irin tashin hankali marar misaltuwa na ziyararta. Ganin yanda jikinta ke bari yasa Tawfiq karasawa inda take

"Nuwaira ya tafi...Ya tafi wallahi..."

Wani irin kuka take tana girgiza kanta, bata son muryarshi da take ji cikin kanta, ganin fuskarshi a jikin tasu Hassan ya isheta tashin hankali har karshen rayuwarta. Ba sai ta hada da jin muryarshi cikin kanta ba

"Bai dade da daina mun kutse cikin mafarkina ba Yaya... Kace mun baizo ba"

Nuwaira take fadi muryarta na karyewa da kukan da take. Hannunta Tawfiq ya kama yana nufar dakin Inna da ita, da ganin su da yanayin da suke ciki yasata mikewa, jikinta Nuwaira ta fada tana fashewa da wani irin kuka.

Sosai Inna ta rike Nuwaira ganin kukan da take da yanda jikinta ke bari. Tawfiq ta kalla da ido take tambayarshi kome yake faruwa. Da tsanar A-Tafida dake taso mishi yace

"Sallamar da akayi dani dazun, su Salele ne suka rako wani inmai gyaran mota... A-Tafida ne"

"Auzubillahi..."

Inna ta fadi da sauri tana sake rike Nuwaira kamar maison boyeta daga sunan A-Tafida din da Tawfiq ya furta. Juyawa yai batare daya sake cewa komai ba, haka yabar Baba da yake tsaye ya shige daki. Yana jin dadin yanda yai Sallar Isha'i.

Kota kan tuwon da Inna tace mishi tasa ankai mishi daki baiba, dan bashi bane a kanshi, ko yunwar bayaji. Kwanciya yayi kan gadon karfen dake dakin. Zuciyarshi na kara girmama da tsanar A-Tafida, da yanda sunanshi kawai yake da tasirin hargitsa musu zaman lafiya har haka.

Lumshe idanuwanshi yayi

'Dukkan tashin hankali Allah ya hada rayuwarka dashi A-Tafida, yanda ka hargitsa mana rayuwar mu, Allah ya hargitsa maka taka'

Itace addu'ar da Tawfiq yake maimaitawa har bacci ya dauke shi, cike da mafarkin A-Tafida.

**

ABUJA

Anma Tasneem gwaje-gwaje da yawa, tun Rafiq na kirgawa harya bari, in akwai abin so a asibiti yanda King's ke kula da marassa lafiyar su yake so. Duka gidansu nan suke da kati, Tasneem ma a kasan sunan Mustafa Shettima ya bude mata kati. Yana jin nisan datai ma zuciyar shi da kuma kusancin da take dashi a lokaci daya.

Fada musu da akai zasu jira Awa daya saboda wasu result dinne yasa Rafiq ce ma Tasneem

"Zaki jira anan inje wajen su Nuri ko zaki iya mu tafi tare"

"Zan iya"

Ta amsa shi da sauri, hannunshi ya mika mata, batai musu ba tasa nata ya taimaka mata ta mike, bangaren suka bari gabaki daya suna nufar wani waje. Nazarin asibitin Tasneem take, tunda take a rayuwarta bata zata a Nigeria akwai asibiti me kyau haka ba.

Tana can tana kalle kalle sai gani tai Rafiq ya tsaya dasu bakin kofar wani daki, ya tura da sallama. Dakine babba sosai, kuma gado dayane a ciki dake nuna alamar Fawzan ne kawai a dakin. Harda kujerun cushion manya manya. Sai kuma na robobi a dakin.

Hannunta da taji Rafiq ya saki na sata maida hankalinta kan su Nuri. A hoto kawai take ganin matar, yaune ranar farko da ta fara ganinta. Saita tsinci kanta da jin kunyar Nuri sosai, kanta a kasa suka gaisa tana tambayar mai jiki.

Kujera Rafiq yaja mata, ta karba ta zauna.

"Mai jiki da sauqi... Ya naki jikin? Har kunga likita?"

"Mungani fa... Kinsan gwaje-gwajen su, sai nan da awa daya zamu koma"

Rafiq ya amsa yana dorawa da

"Bai tashi ba har yanzun?"

Ya karasa gefen gadon Fawzan yana zama, yaji dadin ganin yana numfashi da kanshi bada taimakon engine ba. Kamun Nuri ta amsa Rafiq yace

"Aroob bacci ake?"

Yana bin inda take kwance kan kujera da kallo.

"Ko runtse batai ba jiya..."

"Kema haka Nuri... Kina bukatar hutawa. Da kinje gida sai in tsaya dashi"

Girgiza kai Nuri tayi

"A'a fa, ga aikinka, ga kuma matarka kaima ba lafiya..."

Dan murmushi Rafiq yayi yana sadda kanshi kasa. Duk da murmushin na yan daqiqai ne, kamun ya bace Tasneem taganshi, ta kasan idonta take kallon Rafiq din tunda ya zauna, muryarshi take sauraro, tana mamakin yanda zaka iya kewar muryar wani har haka.

Dan giccin murmushin dayai yasa zuciyarta matsewa a kirjinta da yanda ta jima bataga fara'ar shi ba. Zafi kirjinta ya somayi, hakan nasa tarin data soma gajiya dashi ya sarqeta. Da sauri Nuri ta tashi tana dauko ruwa a roba ta bude tana mika ma Tasneem din, dan a zatonta ko sarqewa tayi.

Ina numfashin ta da take kokawa dashi yasa ko jinsu batayi, so take ko yayane iskar da take shaqa takai mata cikin kirjinta. Dafa mata kafada Nuri tayi tana ta mata sannu. Rafiq kam yana tsaye inda yake, duk da zuciyarshi na mishi ihu ya karasa yaga Tasneem din, kunyar Nuri ba zata barshi ba.

A hankali tarin ke tsagaita mata, riqo hannunta Nuri tayi tana fadin

"Zo kidan kwanta kamun lokacin yayi, sannu..."

Kallonta Tasneem tayi idanuwanta cike da hawaye. Ta manta rabon da wani yai mata magana cike da kulawa haka. Kan dayan cushion din Nuri ta jata ta kwanta,  ta zauna gefenta tana mata sannu, hannunta dataji da lema lema data riqe na Tasneem dinne yasata kallo.

Cikin tashin hankali Nuri ta ware idanuwa ganin tsilli tsillin abu kamar jini, sosai take duba hannun ta, kamun ta kamo na Tasneem tana ware tafin hannun, jini ne a jiki. Kallon Rafiq Nuri tayi ta rasa me zatace, ko wata biyu basuyi da dauko yar mutane ba, tana tarin jini, abin ya tsorata ta.

"Rafiq...Wanda wuro gullami bikka dondiwona (Karka ce mun jiya ne bata da lafiya)"

Nuri ta fadi da yanayi mai nauyi a muryarta. Bata son mishi fada a gaban Tasneem din, shisa ta sake yare take tambayar shi da kanuri, da idanuwanta take tuhumar shi dame yake tuntuni bai kula da Tasneem din bata da lafiya ba. Dan ko yanayin rashin karfinta ka kalla kasan ciwon bana jiya bane.

Dan daquna mata fuska yayi yana turo labbanshi a hankali dake fassara shi fa baiyi komai ba.

"Bikko nungo (Jiya nasani)"

Ya amsa, da kanshi yanajin rashin kyautawarshi basai ya kara dana Nuri ba

"Chistu halnum guyi Rafiq (Rashin kulawa ba halinka bane Rafiq)"

Nuri ta fadi kamun ta mike zuwa toilet. Hannunta ta wanke da Dettol, ta jiqo towel tazo tana goge ma Tasneem nata hannuwan.

"Ciskukin (Zan kiyaye)"

Rafiq ya fadi can kasa, bayan ta fito. Ko taji bata kula shi ba. Hankalinta duka nakan Tasneem.

"Nagode..."

Tasneem din ta fadi a raunane. Murmushi Nuri tayi

"Karki damu... Ki dauke ni kamar mamanki..."

Wannan karin Tasneem ce tai guntun murmushi mai cike da takaici, yanayin Nuri kawai banda kudin da gayun ya nuna akwai nisa mai tsayi tsakaninta da Ummi. A kirkin datai mata na yan mintinan nan ya nuna cewa ita da Ummi ba zasu taba zama a inuwa daya ba.

Sannan Tasneem bata bukatar Ummin da kanta balle ta dauki wata kamar ita, zata dauki Nuri kamar Maman Rafiq. Sai da ta saka Mama take jinjina Nuri da suke kiranta dashi. Tasha nufin ta tambayi Rafiq saita manta, yanzun kuwa batajin zai amsata. Ko zata iya samun kuzarin tambayar shi.

*

Baccin wahala ne ya dauketa, dan Nuri ta tasheta cewar lokaci ya cika. Mikewa Tasneem take shirin yi, Nuri ta sake taimaka mata ta tashi tana fadin

"Rafiq kazo ka taimaka mata mana, kana gani bata da kwarin kirki"

Kanshi a kasa ya karaso yana kama hannun Tasneem, fuskarshi datai ja tadan kalla, kunyarshi ba zata daina bata mamaki ba.

"In kungama ku wuce gida ta huta..."

Bude baki Rafiq yayi zai gardama, dan yana son dawowa yaga Fawzan, Nuri ta katse shi

"Nasani... Inya tashi zan kiraka ka, ko kana gida saika dawo"

Kai ya jinjina mata, yana kama Tasneem din suka fita. Karfin hali kawai take na tafiya, amman jikinta babu karfi ko kadan, har suka karasa office din likitan da suka fita dazun. Saida ta sauke numfashi data zauna saboda gajiyar datai.

Sosai likitan yake kallon Rafiq da yanayin da bayama Rafiq din dadi, tukunna ya mayar da hankalin shi kan Tasneem.

"Tun yaushe kike jin tsaitsayawar numfashi? Da kasala?"

"Yafi wata uku"

Ta amsa a sanyaye, tana sa Rafiq juyawa ya kalleta, duk da idanuwanshi dake mata yawo baisa ta dago ba, tambayoyi yaci gaba da mata tana amsa shi dai-dai saninta. Kamun ya tattara takardun dake gabanshi yana bude wani file ya saka su. Kamun ya nutsa hankalin shi gabaki daya kan Rafiq

"Matarka ce ko?"

Daquna fuska Rafiq yayi kamun a hankali ya daga mishi kai.

"To cikin kashi dari, takai mataki tisi'in na gab da kamuwa da abinda muke kira CHF, wato congestive heart failure...duka alamomi masu karfi sun nuna, abubuwa da yawa kan jawo hakan, a nata case din jininta yahau fiye da misali..."

Kallon shi kawai Rafiq yake tunda ya soma maganganun da yake ji suna shiga zuciyarshi da tafasa duk wani jini da yake yawo a jikinshi. Taya za'ace heart failure na gab da kama Tasneem, hawan jini, a ina ta same shi? Bai gama tunanin da kwakwalwar shi take sonyi ba likitan ya sake jefa shi yanayi da fadin

"Kuma tana dauke da ciki sati hudu..."

Daga nan bai sake jin abinda likitan yake fadi ba, yadai ga bakin shi na motsi, amman babu abinda yake isowa kunnuwan Rafiq. Ciki sati hudu, baya son inda zuciyarshi take kaishi saboda yanda zuciyarshi ke tafasa. Dafe kai yayi da hannuwanshi duka biyun.

Tasneem kuwa tunda ya fara magana babu abinda ya bata mamaki, daga hawan jinin har ciwon zuciyar, amman yana kiran kalmar ciki saida taji zuciyarta tai wani irin tsalle kaman zata fito waje. Da sauri takai hannu tana dafa cikinta hadi da shafashi ta lumshe ido.

Wata saqa na qulluwa a zuciyarta da bata taba zaton akwai ta ba, wani irin kusanci take ji da cikinta ta fannin da bata zata ba. Akwai bangaren Rafiq a waje fiye da zuciyarta, akwai dan karamin Rafiq a cikinta. Ko da taga period dinta ya wuce lokaci bata kawo komai a ranta ba, dan sosai yakan mata haka. Rabonta tun sati biyu kamun bikinsu da Rafiq din.

Bata san hawaye sun zubo mata ba saida taji saukar su akan kuncinta, hannu tasa ta share hawayen, wasu na sake zubo mata hadi da murmushi mai sauti, ta manta rabon da tayi murmushin da ya fito daga zuciyarta haka. Sosai take shafa cikinta hawaye na zubar mata, tana sa dayan hannunta tana goge su.

Kallon ta Rafiq yake, yana ganin farin ciki bayyane a fuskarta, saidai duniya daban-daban suke a yanzun, yana akasin wadda take, kokawa yake ta gaske da zuciyarshi kar shakku ya darsu a ciki, kar taja mishi karewar auren shi da Tasneem batare da shiri ba. Baisan lokacin daya kamo hannunta yana sumbata ba.

Kusanci yake so dazai janye zuciyarshi daga inda take son kaishi, sosai yake dumtse hannu Tasneem din. Ta kasa kallon shi, batason abinda zai janye zuciyarta daga alaqar dake tsakanin ta da cikinta

"Wai kuna jina kuwa?"

Likitan ya fadi ganin sai surutu yake shi kadai, daga Rafiq din har Tasneem din sunma manta da zamanshi a office din, muryar Rafiq can kasan makoshi batare daya kalle shi bayace

"Kayi aikinka kawai...ka rubuta abinda zaka rubuta"

Girgiza kai likitan yayi kawai. Ya dauka shekarun daya dauka yana aiki babu abinda zai bashi mamaki, saiga Rafiq da Tasneem a gabanshi.

"Dole saikun saurare ni zanyi aikina"

Batare da su duka sunso ba suka maida hankulansu kan likitan, bayanin dokokin magunguna da kuma wasu daban ya shiga shimfida musu. Babu doka daya da Rafiq bai riqe ba. Nan office din suka zauna, likitan yai waya akazo aka amshi takardar magungunan da aka rubuta musu.

Aka siyo aka kawo, ya basu zabi kosu riqe Tasneem din kwana daya ko kuma gobe su dawo. Kamun Rafiq ya amsa tace ba zata kwana ba. Ta samu babban dalili na kula da kanta yanzun. Hannunta riqe cikin na Rafiq suka fita daga asibitin. Tana jinshi yai waya da Nuri ya fada mata sun wuce.

*

Suna shiga gida, a falo ta cire Hijab dinta ta zauna, tanajin wani sabon karfi, tsaye Rafiq yayi yana kai-kawo a falon, ya kasa zama, karfin mulkin zuciyarshi na soma kwacewa daga hannun shi, kallon Tasneem yayi, yana maida hankalin shi kan cikinta.

"Cikina ne a jikin ki ko ba nawa ba Tasneem?"

Rafiq ya jefeta da tambayar data sa zuciyarta tsayuwar wucin gadi. Mikewa tsaye tayi a hankali tana takawa ta karasa inda yake tai tsaye tana kallon shi da idanuwanta da suka bushe wannan karin suna sa tasan zubar hawaye sauqi ne a yanayoyi daban-daban.

Hannuwanta tasa duk biyun tana hankade kirjin Rafiq dako motsi baiba, taba wata irin qara data fito tun daga zuciyarta sautinta na raguwa kamun ta karaso makoshinta zuwa kan harshenta, ko ina ta samu a jikin Rafiq take kaima duka, me yasa zai mata wannan tambayar?

Baiko motsa ba, barinta yayi taci gaba da kai mishi duka tuntana yi da karfi harta soma rage karfin dukan, tukunna ya kama hannuwanta yana kokarin riketa a jikinshi, tana kwacewa, karfi yasa ya matse ta yana son taji yanda zuciyarshi ke ciwo da tambayar dayai mata, da ta bashi dalilin yai mata tambayar.

Sai lokacin hawayenta ya soma zuba, wani irin kuka take har jikinta ke kyarma.

"Me yasa zakai mun tambayar nan....laifina babbane a wajenka nasani... Na dade ban ji farin ciki a raina ba... Na manta yanda yake sai yau... Me yasa zaka kwace mun? Hukuncin da kakemun bai isa ba?"

Take tambaya tana ci gaba da wani irin kuka. Riketa yake, ta zame daga jikinshi tana durqushewa qasa, binta yayi yana rikota

"Neem.... Please.... Ina son sani ne... Ina son sani, zuciyata ba zata nutsu ba in baki tabbatar mun ba... Cikina ne?"

Ya sake tambaya yana sata sake rushewa da wani irin kuka, tana jin indai da haske koyayane a lahirarta gara mutuwa da rayuwar da take ciki. Da komai da take dashi take jin daman tana da ikon komawa baya ta sake wasu cikin zabukan da tayi.

"Kuskure... Kuskure daya nayi... Shine zai zame mun tabo har karshen rayuwa... Shine yasa kake mun tambayar nan Sugar..."

Tasneem ta fadi numfashin ta na sarqewa. Dazai samu hawaye su zubar mishi daya samu sauqin abinda yake ji

"Ba laifina bane Neem... Ke kika kawomu wajen nan"

Jinjina mishi kai tayi tana dagowa daga jikinshi hadi da saka hannu tana goge fuskarta.

'Kayi kokari ta rage damuwa'

Maganar likita ta dazun ta dawo mishi, baisan yanda zaisa ta rage damuwa ba in
kallonta kawai shi yana jefa shi cikin damuwa. Gyara zamanshi yayi yana kallon yanda take goge hawaye wasu na zubar mata

"Ki fadamun... Ya akai kika kawo mu nan... Ina son sani"

Kallon Rafiq tayi da rinannun idanuwanta. Da gaske yana son sani, tagani a fuskarshi, yana son jin yanda akai rayuwa ta kawota inda take yanzun, da yanda akai ta janyoshi suke tsaye tare. Numfashi mai nauyi taja tana saukewa a hankali...!
[11/30, 10:16 PM] LubnaSufyan: ®
📖✏
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION

LubnaSufyan
Calmlubna@gmail.com

Alkalamin Kaddara

04

TUNA BAYA (Rayuwar Tasneem Muftahu Tafida)

Kasancewar Tasneem ta tsinci kanta da tasowa cikin gidan da hausawa kan kira na yawa. Dan a tasowarta kamun rayuwa ta tafi dasu kan rubutun ALKALAMIN KADDARAr daya rarraba su wajaje da dama. Gida hudune cikin gidansu harda nasu data tashi a cikin shi, kofa daya zaka shigo kamun ka samu kofofin da zasu shigar dakai sauran gidajen.

Hakan yasa ta fahimci akwai abinda yake ba dai-dai ba a nasu gidan. Da duk ranar da zata wuce da karin hankalin da ke shigarta da kuma yanda take gane banbancin gidansu dana sauran mutane, musamman mahaifiyarta Bara'atu da suke kira da Ummi.

Ba zata manta ranar Juma'ar farko da zuciyarta ta fara sanin asalin damuwa ba, lokacin tana aji hudu sakandire,duk da a shekarun zaman ta da Ummi tasan menene bacin rai. Ta fito daga daki Abban su na tsugunne yana Alwala zai fita masallacin juma'a

"Abba lokaci har yayi?"

Tasneem ta bukata dan ganin ranar batakai ta karfe daya haske ba.

"A'a da saura, ina so dai inje ne in gabatar da addu'o'ina kamun lokacin ya cika..."

Murmushi tayi

"Allah ya karba m..."

Bata karasa ba saboda muryar Ummi da ta katse ta

"Ashe Masallaci zaka tafi, kasan dai bamu da abinda zamu ci a gidan nan ko?"

Numfashi Abba ya sauke yana kallon Tasneem da fadin

"Tasneem dame-dame ake yi da filawa?"

"Abubuwa da yawa Abba, ka siyo mana ne?"

Kai ya girgiza mata

"Bani akayi tun jiya..."

"Kayya Abba, bamu sani ba ai, danai mana wainar filawa naga akwai manja, su Azrah naso"

"Uban ki ne ya saimun manjan?"

Ummi dake tsaye ta tambaya tana watsa ma Tasneem harara, da sauri ta matsa gefe dan tasan halin Ummi, zata iya kai mata hannu daga hararar. Mikewa Abba yayi yana laluba aljihun yar sharar shi, Naira talatin ya lalubo, ya duba na wandon shi yana dauko wata Naira hamsin data ji duniya ya hada su waje daya yana mikama Tasneem.

"Kudin dake jikina kenan Tasneem"

Hannu Tasneem tasa ta dauki Naira Hamsin.

"Wannan ma ya isa Abba"

Tafa hannuwa Ummi ta shiga yi

"Oh ni Bara'atu..."

Abba baibi takanta ba ya mayar da talatin din a aljihu yana sakai zai fita. Da sauri Ummi ta riko mishi riga tana janyo shi, hakan nasa rigar yin wani qara ta yage daga wajen Aljihun zuwa bayan kugun

"Ina kake nufin zaka je? Ga mahaukaciya ko?"

Runtsa idanuwanshi yayi yana jero

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."

Dan Allah ya bashi hakurin jure abinda Ummi take ko dan Tasneem da take tsaye.

"Inalillahi tame kake yi? Sai an soma magana ka nuna ma kowa kai na Allah ne...me zan da wata filawa? Yaushe rabon da mu dora wani abin kirki a gidan nan?"

Wani abu ne mai daci Tasneem taji ya taso daga zuciyarta yana tsaya mata a makoshin ta. Idanuwanta cike taf da hawaye tace

"Haba Ummi? Haba Ummi?"

A hasale Ummi ta juya tana ma Tasneem wani mugun kallo

"Ki rufemun baki, bakin hali irin na Ubanki ko? Banda ruwan koko meye a cikin ku tun safe? Ke bai dameki ba ko? Kina tausayin uban da baya tausayin ki..."

Daki Tasneem ta shige hawayen da take tarbewa suna samun zubowa. Hannu Abba yasa yana banbare na Ummi daga jikin rigarshi hadi da wucewa dakin su. Wasu kayan ya dauka ya sake. Harya fito tana tsaye tana tijara.

Baice uffan ba ya dauki buta ya sake zuba ruwa yanayin sake wata Alwalar ya fita. Dakin su Tasneem din Ummi ta bita, jin shigowar Ummi dinne yasa ta saurin goge hawayen dake fuskarta

"Munafuka, kukan me kike?"

Shiru tayi batace komai ba, dan tasan maganar na iya ja mata duka indai Ummi ce. Sabeena dake kwance tana bacci ta bude idanuwanta, kan Ummi ta fara sauke su tukunna ta juyar da kanta tana kallon Tasneem.

"Yaya yunwa nake ji"

Sabeena ta fadi.

"Kina cin wainar filawa?"

Da sauri Sabeena ta mike tana murza idanuwanta

"Zakiyi mana?"

Kai Tasneem ta daga mata. Hakan ya sata mikewa tana daukar Hijab dinta kan kyauren dakin. Dai-dai shigowar Hamna da Azrah da sallamarsu.

"Ya kuka dawo da wuri haka?"

Ummi ta tambaya tana kallon su. Turo baki Azrah tayi

"Ba kowa gidan sai Anty"

"To duk ina yaran suka je?"

Shiru su Hamnah sukayi

"Me ta baku to?"

Ummi ta sake tambaya.

"Babu abinda ta bamu"

Azrah ta sake fadi, magana ba damun Hamnah tayi ba, dan wucewa tayi tana samun waje ta zauna.

"Matsiyaciya... Asabe ta koyi shegiyar rowa"

Girgiza kai Tasneem tayi. Taya ba zata koyi rowa ba, kowacce dama Ummi zata samu saita aika su Azrah gidan tasa su zauna ko zasu samo wani abu. Halin son abin duniya irin na Ummi kan bata mamaki. Tasan tun tasowar su Abban su bamai hali bane, saidai mutum ne mai wadatar zuci.

Sana'ar gini shine aikin shi, ba zata manta lokuttan da suke yara ba, abinci harda nama akan dafa musu akai-akai, har shayi suna sha da safe, dan Abban su mutum ne da in yana dashi baya ma iyalin shi kwauro, sosai samun aiki yake mishi wuya yanzun. Ga jikin manyanta kuma.

Dan ance sun jima shi da Ummi kamun Allah ya basu kyautar yara, kuma sai da suka jera su mata su duka. Ita Tasneem din, Azrah, Hamna, sai autarsu Sabeena dan shekararta bakwai yanzun. Rayuwa ta soma musu wahala ne sosai tun bayan haihuwar Sabeena.

Tunda can Tasneem tasan Ummin su macece mai fada da tsegumi, dan kome Abba zai kawo sai tayi mita akai da nuna rainuwarta. Musamman lokacin da sauran matan yan uwanshi na gidan. Dan duk randa ta shiga taga sun sabunta daga rayuwar data sansu ciki sai tazo ta sauke ma Abba tashin hankali.

Danginta harsun gaji da halin rashin godiyarta, dan ko yaushe tana cikin bin gidajen su da

1 Comments On ALAKALAMIN KADDARA PART 1
avatar
khadija-7-4

1 year ago

Reply

Yayi

Please Login or Register in order to submit comment