Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mun magana yanda zan fahimta Yaa Yasir"

"Harbin shi akayi!!!"

Maganar Tariq yake ji na amsawa a ko ina na jikinshi, kunnuwanshi sunyi wani dimm

"Umm?"

Ya fadi can kasan makoshi yana daquna ma Yasir fuska dake nuna yana son ya sake maimaita mishi danya fahimta.

"Harbin shi akai a hanyar mu ta dawowa..."

Dariya Tariq yayi saboda baisan abinda ya kamata yayi da ya wuce wannan ba. Sosai yake dariyar daya sa Yasir takowa ya karaso inda yake yana dafa mishi kafada dayai saurin kai hannu ya ture kaman an dora mishi wuta hadi da juyawa ya hankada shi baya.

"Duk sanda kuka fita tare sai an samu matsala... Ya akai harbin akanshi kawai ya tsaya? Maganin bindiga kasha da bai same ka ba?"

"Tariq..."

Yasir ya kira da damuwa hadi da kashedi a muryarshi. Sosai Tariq ya matsa dab dashi, fuskarshi cikin tashi hankali, muryarshi can kasa

"Ina son sanin yanda akayi ne kake tsaye anan.... Yaa Faq yake duk inda yake yanzun..."

Tariq ya karasa maganar yana barin Yasir yaga abinda yake ji ta cikin idanuwanshi, tsoro ne bayananne, daga cikinshi komai kyarma yake. Yana jin yanda duniyar ta kara mishi wani irin girma, fayau yake ganinta sai shi kadai a tsaye.

Wannan karin kyarmar har wajen jikinshi ta nuna kaman maijin sanyi.

"Wanda zai bada jinin baizo bane?"

Tambayar tasa su Tariq juyawa su dukansu, da sauri Tariq ya karasa inda likitan yake.

"Wallahi shi kadai ya ragemun.... Banda kowa.... Daga ni sai shi... Yana ina? Ya tashi? Kabarni in ganshi in yaji maganata zai tashi"

Ganin yanda Tariq din yake maganganun kaman ba cikin hayyacin shi yake ba yasa likitan kama hannun shi yana janshi suka nufi hanyar daya fito. Yasir yana bin bayan su har office din likitan, zaunar da Tariq yayi kan kujera yana mika hannu ya dauko robar faro din dake ajiye kan table ya mika mishi.

Ba musi Tariq ya karba ya bude yana shan ruwan sosai, duk da kishin da yake ji bana ruwa bane ba bai hana shi jin yar nutsuwa ba. A kasa ga ajiye robar yana kallon likitan

"Yana ina?"

Ya bukata yana kokarin saka nutsuwar da bayaji cikin muryarshi.

"Ba abinda zan iya ce maka yanzun... Jinin shi O ne yana wahala..."

Bai bari ya karasa ba ya katse shi da fadin

"Jinin mu iri daya ne... Amman bansan ko za a iya diba ba"

Tariq ya karasa muryarshi na sauka kasa cike da wani yanayi mai wuyar fassara. In wani abu ya samu Yaa Faq....girgiza kanshi yayi saboda tunanin wani abu zai iya samun shi dinma na neman saka numfashin shi tsayawa. Idanuwan shi ya sauke cikin na likitan.

"Na sha codien da mix... Bansan ko za a iya dibar jinina ba"

Wani irin kallo likitan yake ma Tariq cike da fassarori kala-kala. Rai a bace Tariq yace

"Karka ja layi a rayuwa ta batare da sanin farkon ta ba... Kaji da matsalarka inji da tawa..."

Da kallon dai a idanuwan likitan da Tariq baya so ko kadan, baya son mutane na yanke mishi hukunci tunda Asalin ikon hakan ba a hannun su yake ba. Laifukan shi da rayuwar shi ba matsalar su bane ba

"Za a iya samu.... Da tsada sosai in zaku iya siya"

"Duk abinda ya kamata ayi mishi ayi.... Sau nawa zan fada maka haka?"

Yasir dake tsaye ya fadi. Kai likitan ya daga musu yana fita, suma bin bayanshi sukai har saida ya juyo yace musu

"Iya nan zaku iya tsayawa..."

Kallon shi Tariq yake kaman yana son musa hakan, ko Yasir ya dauka zaiyi gardama. Sai yaga baice komai ba ya tsaya, idanuwan shi dai na kafe kan likitan harya shiga dakin Theatre din.

Sauke numfashi mai nauyi Yasir yayi yana zama kan doguwar kujerar dake wajen

"Tariq ka zauna"

Shiru yayi kaman bada shi yake ba.

"Tariq..."

Ya sake kira.

"In ba fadamun zakai inka bar asibitin nan kabar rayuwar yayana ba karka sake mun magana dan Allah...kabarni inji da abinda yake damuna..."

Shirun yayi ya kyale shi, baisan ta inda zai fadama Tariq da duk wani abu dazai samu yayan shi yake dorawa a kanshi cewar ba haka bane ba. Zai iya komai saboda Ashfaq. Inhar baifi karfin ikon shi bazai taba bari wani abu ya same shi ba saboda dalilai da yawa.

Baisan ko awa nawa suka dauka ba, banda bugun zuciyarshi babu abinda yake fahimta, sai zufar da yakan sa hannu lokaci zuwa lokaci ya goge daga goshin shi. Komai na asibitin na son dawo mishi da abinda baya son tunawa. Komai na yanayin na saka jikin shi yin sanyi.

Bude dakin Theatre din yaga anyi kamun a gunguro gado daga cikinshi ana nufar wani dakin dashi. Kaman wanda aka dasa haka yake jin kafafuwanshi sun mishi nauyi ya kasa karasawa, jikinshi ya dauki wani irin sanyi.

Har saida yaji Yasir ya tadan taba shi tukunna ya daga kafarshi datai wani irin nauyi yana fara takawa zuwa dakin da aka shiga da Ashfaq din. Hannuwanshi yake ji kaman babu jini a jiki,dakyar ya iya tura kofar a hankali yana tsayar da idanuwan shi kan Ashfaq dake kwance kan gadon. Wani siririn tube ne dogo a hancin shi.

Ga karin jini a hannun shi, fuskarshi tai wani irin haske da yasa duka wani fargaba da tsoro da Tariq yake ji yana kara hade mishi waje daya. Kafafuwan shi na rawa ya karasa cikin dakin inda gadon yake. Yaga bakin likitan na motsi, saidai kome yake fadi baya karasowa kunnen shi.

Tsugunnawa yayi yana dafa gadon da hannayen shi.

"Ya Faq..."

Ya kira a hankali, ko shi da wuya in yaji muryar balle Ashfaq da baisan duniyar da ake ba.

'Ka cika damuwa... Dan yankan nan hankalin ka duk ya tashi kaman ba namiji ba'

Tariq yaji muryar Ashfaq din can wani lokaci.

'Ka kalleni Tariq... Idan zan iya kauce ma mutuwa saboda kai zanyi okay? Kai kadaine dalilin daya rage mun na rayuwa... Babu abinda zai same ni in shaa Allah... I promise'

Idanuwan shi Tariq yaji sun cika da wani abu mai zafin gaske. Zuciyarshi na radadi har wani zazzabi zazzabi yake ji.

"Kamun alkawari...Yaa Faq kamun alkawari...In ramawa kake so kayi dan na karya alkawarin mu karka mun ta wannan hanyar...bana jin magana nasani...ina bukatar wanda zai fadamun hakan... Dan Allah kar kai mun haka... Karkai mun haka Yaa Faq..."

Tariq ya karasa yana kifa kanshi da gadon da Ashfaq din yake, hawaye masu dumi na zubo mishi. Hawayen dayai tunanin babu wani abu kuma dazai sake fito dasu. Babu dalilin da basu gani ba na fitowa a rayuwar shi.

Bai zaci akwai sauran abinda zai fito dasu ba sai yanzun, sai da yaga Ashfaq kwance haka, dago kanshi yayi yana sa hannu ya goge hawayen da suka zubar mishi.

"Yaa Faq ka tashi dan Allah... Kamun magana kawai saika koma baccin dan kake... Ina bukatar sanin kana jina..."

Ko numfashi baiga Ashfaq nayi ba ballantana kuma ya nuna mishi alamar yana jin abinda yake cewa. Tashi daga tsugunnon Tariq yayi yana zagayawa ya zauna kan gadon ta gefen Ashfaq din.

Nutsar da hankalin shi yayi kan fuskarshi yana son ganin ko motsi yayi, kayan dake jikin shi ne Tariq baya son kallo saboda suna son kaishi inda baya son zuwa. Shisa yaqi yawo da idanuwanshi inda ya wuce fuskar shi.

Sam baiji turo kofar ba sai maganar Yasir da yaji

"Doctor yace He will be fine... Saidai ba yanzun zai tashi ba"

Bai nuna ma Yasir yanda maganar tasa kaman an dauke mishi wani katon nauyi a zuciyar shi ba, balle yanda kunnuwanshi suke bukatar jin wani yace mishi babu abinda zai samu Ashfaq daya wuce zuciyarshi. Asalima ko inda yake Tariq bai kalla ba, har yaji ya tako ya ja kujera ya zauna.

**

ABUJA

Sosai ya jingina bayanshi da kujerar motar, inda wani yace ya hango mishi kasancewar rayuwar auren shi a wannan yanayin murmushi kawai zaiyi dan yasan ba abu bane mai yiwuwa, yarda da Tasneem ba zata taba barinshi amincewa ba.

Zafin da zuciyarshi take yi da azababben kishi har kanshi yake jin ya soma ciwon daya samu wajen zama tare dashi a wata dayan nan. Baima yi yunkurin shan kowanne magani ba, dan yasan babu abinda zai mishi. Lumshe idanuwanshi yayi yana maida numfashi.

'Ina son ka. Bazan iya rasaka ba'

Maganganun Tasneem suka dawo mishi. Kaman yanda amsar daya bata take yawo cikin kanshi.

'Karki mun karya, ita ce abu na farko dazai iya shiga tsakanin mu. Nafi bukatar gaskiyar ki akan soyayyarki Neem. Na samu soyayya mai yawa a rayuwata, gaskiya ce take da karanci'

Bude idanuwanshi yayi babu shiri, baya son tuno yanayin fuskarta, baya son tuna yanda ta kalli kwayar idanuwanshi, yanda ta kalli zuciyarshi daya bude mata ta cikinsu tai mishi karya. Ciwon da yake ji a yanzun ya ishe shi ba saiya kara da wani sabo ba.

"Isa mu biya ta K.F.C zan siya abu"

Rafiq ya fadi ma driver dinshi da yake jan motar.

"To yallabai"

Isa ya amsa yana shan U-turn din dazai kaisu K.F.C din. Suna karasawa Rafiq ya bude bayan motar ya fito yana shiga wajen. Burger ya siya da waffles, ledoji uku yayi, ya biya kudin kenan yana daukar ledojin yaji zuciyarshi tai wata irin dokawa cikin yanayin da bai taba tsintar kanshi a ciki ba.

Har tsikar jikinshi yaji tana tashi, kusanci yake ji da baisan daga inda yake ba, da sauri ya juya jin takun tafiyar dake kara jefa shi cikin yanayin daya tsinci kanshi. Matashiyar budurwace da ba zata shige shekaru sha takwas ba, jikinta sanye da Abaya.

Akwai wani abu tattare da ita daya kasa fahimta, musamman yanda suna hada ido duk wata fara'a dake fuskarta ta dauke, mamaki, shakku, da wani abu da Rafiq ya kasa fahimta yana maye gurbin fara'ar, sosai take kallon shi. Zuciyarshi ta ci gaba da dokawa, ji yake tamkar ya santa a wani waje, kusancin da yake ji a tsakanin su ya mishi wani iri.

Cikin hanzari ya damqe bakin ledojin yana fita daga wajen, iska yake shaqa yana jin kamar ta mishi kadan, murfin motarshi ya bude yana shirin shiga yaji zuciyarshi ta sake bugawa da karfin dayafi na dazun, juyawa yayi, daga babban mayafin dayake lullube jikinta ya gane mace ce, saidai bazai ce ga yanda kalarta take ba, saboda bayanta kawai yake iya gani, kamun ta shiga cikin K.F.C din.

Da dukkan wani abu da zuciyarshi take dashi take fada mishi yabi bayan matar, runtsa idanuwanshi Rafiq yayi yana girgiza kanshi, cikin son rabuwa da koma menene yake ji. Da sauri ya shiga motar yana ja ya rufe. AC din dake aiki bai hana shi kai hannu ya goge gumin da yake ji a goshin shi ba.

Sosai kanshi ya daure, abinda ya faru baqo ne a wajenshi. Yakice koma menene yayi gefe daya, baida lokacin shi a yanzun. Musamman da ya hango gate din gidanshi, yaga isa ya tunkari gidan, koma me yake ji sai yayi gefe, sauke numfashi yayi lokacin da suka karasa cikin gidan.

Leda daya daga cikin ukkun yaba ma Isa da bai tsaya jin godiya da addu'o'in da yake mishi ba. Ya shiga cikin gidan, da sallama ya taka babban falon duk da bai tsammaci amsa ba, dan yasan da wahala yaga Tasneem din a falo.

Rabon daya sata a idanuwanshi tun daren auren su, sai dai yakan ji motsinta wasu lokuttan, yana son yaji ko tana lafiya, ko ba komai zaman shi take yi a cikin gidan. Amman zuciyarshi bata son ganinta, ko kadan baya jin zai iya jure zama waje daya da ita a yanayin da yake ji.

Area din dining din ya karasa ya ajiye leda daya yana juyawa da niyyar nufar sashen shi.

"Sugar..."

Muryarta ta tsayar dashi cak, kamun ya juyo kamar wanda akai ma dole. Idanuwanta ta ware akan shi, kallon ta yake, zuciyarshi na matsewa a kirjinshi da wani irin ciwo. Kumburin da idanuwanta sukai bai hanashi ganin damuwa da ramar dake kasan su ba.

Hakan baiyi komai ba sai kara mishi kuncin da yake ciki. Yana kallon ta harta karaso dab dashi, tsayin dayai mata ne yasa ta dan daga kanta dan taga fuskarshi. Idanuwanta cike taf da hawaye.

"Na cancanci hukunci fiye da wanda kake mun a yanzun..."

Tasneem ta fadi tana sa hannu ta goge hawayen daya zubo mata. Kamun ta kai hannunta tana tallabar kuncin shi

"Sanin muna zaune gida daya...amman ganinka na mun wahala... Zuciyata na quna sosai..."

'Fuskar maza nawa hannunta ya taba?'

Zuciyarshi ta tambaye shi. Zame fuskar shi Rafiq yayi daga hannunta yana matsawa baya kadan, dan ji yai kaman wuta ta dora mishi. Fuskarta yake kallo yana jiran zuciyarshi ta buga mata yanda ta saba amman sam. Bayajin komai game da ita a yanzun sai kyama, da tarin dana sani.

Baida abinda zai ce mata, baida kalaman dazai dora akan harshen, dan haka ya juya kawai yana nufar bangaren shi.

*

Bin bayanshi da kallo Tasneem tayi, bata san meya sa ta fito da taji motsin shi ba, bata san me zuciyarta ta zata ba. Hannu takai tana dafa kujerar dake wajen kamun ta samu ta zauna tana runtsa idanuwanta saboda jirin da take ji.

Batai kokarin goge hawayen da suka zubo mata ba, tari ta fara yi da ciwon shi yake tasowa daga kirjinta, zuciyarta na mata ciwo kaman ana hura wuta, hannu tasa tana rufe bakinta, tarin na sake taso mata babu kakkautawa, takai mintina biyar tanayi, numfashin ta har Sama-sama yake, ga kanta kamar zai rabe biyu.

A hankali tarin ya soma tsagaitawa, wajen mintina sha biyar tana hutawa kamun ta samu ta mike dakyar tana nufar dakin ta, bandaki ta nufa ta kunna fanfo tana wanke hannuwanta. Ciwon kirjin da take ji ya kusan wata uku,amman tarin satin bikinta ta fara yinshi kadan-kadan, ya soma hadowa da jini randa aka daura aurenta, har zuwa yanzun.

Kurkure bakinta tayi tana samu dakyar ta fito daga bandakin. Tasan ko da bakinta baya so, jikinta na bukatar abinci, dan haka ta sake fita daga dakin tana nufar hanyar dining din, kaman ko da yaushe leda na ajiye, hakan yakanyi mata, in zataci taci, inma ba zata ci ba ta wani fannin ya sauke wannan nauyin.

Dauka tayi ta sake nufar dakin ta, hawaye na sake zubo mata data tuna da yanayin kyamar ta data gani a fuskar Rafiq din. Yanda ya zame fuskarshi daga riqon datai mishi kamar wuta ta zuba mishi. Harta samu waje ta zauna a dakin, zuciyarta bata ga laifin shi ba. Ta bashi dukkan wani dalili dazai kyamace ta.

Bude ledar dake gabanta tayi, waffle din ga fiddo dashi, ta soma gutsura tana sakawa a bakinta, ko taunawa batayi ba balle ta gane dadin shi hadiyewa kawai tayi. Haka ta ci gaba dayi saida taji inta kara amai zatai tukunna ta ja ledar gefe tana hade kanta da gwiwarta. Komai baya mata dadi.

Wata irin tsana ce take mata yawo a zuciya, tsanar kanta data umma data zama silar jefata cikin wannan bala'in. Inda zata samu dama data koma baya ta sake yin wasu zabin. Sai dai a wasu abubuwan rayuwa dama daya take baka. Wani lokaci can baya na dawo mata.

*

"Tasneem! Tasneem!!"

Umma take kira a fusace, da sauri ta Tasneem ta sauko daga kan katifar da take kwance akai tana fitowa tsakar gida inda umma take tsaye. Fuskarta kawai ta kalla tasan ranta a bace yake. Duka Umma ta kawo mata, cikin hanzari Tasneem ta kauce tana yin nesa da Ummar.

"Ke wacce irin yarinya ce marar rabo? Arziqi na binki kina runtse ido? In ke halin kuncin da muke ciki baya damunki sai akace miki ni baya damuna? Dan ubanki yaushe zaki yi hankali?"

Umma take fada cikin bacin rai. Kallon ta Tasneem take cikin qunan rai. Umma taci gaba da fada kaman zata ari baki.

"Ki wuce ciki ki dauko hijab dinki, Alhaji Mando na kofar gida yana jiran ki. Ashe tun Shekaranjia yake binki kuje siyayya kinqi. Saboda bakin ciki ko? Kwana nawa rabon da mu dora tukunyar abinci a gidan nan? Tun randa saurayin Azrah ya bata dubu biyu..."

Kallon Mamaki Tasneem take ma Umma kamun rai a bace itama tace

"Au umma! Kudin nan sai da kika bari ta karba? Duka Azrah nawa take da zata dinga fita zance... Kuma kinma ga dan iskan yaron?"

Juyawa Umma tayi tana rarumar wani tsohon takalmi dake ajiye ta wurga ma Tasneem din.

"Dan ubanki saiki fadamun abinda ya kamata...zaki bacemun dagani ko saina karyaki? Kuma wallahi ki dauko Hijab ki bishi"

Da gudu Tasneem ta wuce daki, ta dauko wani tsohon hijab dinta, hawayen baqin ciki taf da idanuwanta. Abu daya zai sata bin Alhaji Mando, dan hakan zai iya sa Umma ta daga ma Azrah da fita zancen da Tasneem ba ta ga alkhairi a cikin shi ba.

*

Kwankwasa dakin da taji ne ya katse mata tunanin da take yi. Batare data dago kanta daga jikin gwiwarta ba ta amsa da a shigo. A hankali Rafiq ya turo kofar yana shigowa kaman wanda akaima dole. Har dakin shi yana juyo tarin da takeyi dazun. Duk yanda yaso ya jure ya kasa.

Akwai muryar dake fada mishi yazo ya duba lafiyar Tasneem din, duk girman laifinta a wajenshi in wani abu ya sameta bazai yafe ma kanshi ba. Saidai ya kasa karasawa. Daga nan bakin kofar yace

"Lafiyarki? Naji kina tari dazun"

Da sauri Tasneem ta dago kanta, to wama take zaton zai kwankwasa mata daki in bashi ba, bata jin banda maigadi, akwai wani a gidan bayan shi da ita. Zuciyarta ta matse waje daya cike da buruka da dama. In har ya damu da halin da take ciki, ya dauko kafarshi yazo yaga ya take, tana da sauran hope.

Muryarta na rawa, cike da yanayoyi da dama ta amsa shi da

"Lafiya kalau. Nagode..."

Dariya Rafiq yayi mai sauti da bata da alaqa da nishadi. Tasneem ce take mishi godiya dan ya tambayi lafiyarta, yanayin rayuwa bazai daina bashi mamaki ba. Yanda komai yake canzawa cikin kankanin lokaci. Girgiza kanshi kawai yayi ya juya hadi da ja mata kofar.

**

KANO

"Arfa! Arfa!! Arfa!!!"

Yake kira cikin tashin hankali yana jijjiga ta, dago ta yayi yana rungumeta a jikinshi, yasan yanda tashin hankali yake, abinda yake ji bashi da suna, jiyai kaman kayanta a jiqe suke, hakan yasa yakai hannunshi yana taba dai-dai inda yaji lemar yana dawo dashi ga dubanshi.

Idanuwanshi a ware cikin sabon firgici da tashin hankali yake kallon jinin dake hannunshi, sake kallon Arfa yayi dake jikinshi, maimakon ya ganta sai Ashfaq yagani da jini na malala daga inda baya iya gani a jikin Ashfaq din. Waigawa yayi gefe ko zaiga wani dan ya kawo mishi dauki.

Baiga kowa ba sai Arfa dake kwance a kasa bata motsi, ya rasa wanne irin rikitaccen Al'amari ne yake faruwa dashi.

"Arfa!!!"

Ya kira da dukkan karfinshi.

*

"Tariq ka bude idanuwanka...Tariq!"

Bude idanuwanshi yayi yana maida numfashi da sauri-sauri, kamun ya soma yawatawa da idanuwan nashi a ko ina na dakin.

"Is okay..."

Da sauri ya dawo da dubanshi kan Ashfaq.

"Yaya..."

Ya kira kaman yana kokwanton in ya daga muryarshi zai ga Ashfaq din ma mafarki ne. Murmushi Ashfaq din yai mishi.

"Karka sake bani tsoro irin wannan... Duniyar zatai mun girma in baka nan"

Tariq ya fadi muryarshi na rawa. Kai kawai Ashfaq ya iya daga mishi, dan ko kadan bayajin karfi a jikinshi. Turo kofar da akai yasa su duka maida hankalin su wajen. Yasir ne ya shigo da Sallama, hannunshi riqe da ledojin Oasis. Karasowa yayi yana dora ledojin a kan table din dake wajen.

"Bacci ya kamata ace kana yi har yanzun"

Fadar Yasir.

"Bana jin wani bacci... Yaushe suka ce zan bar wajen nan"

Ashfaq ya bukata yana kokarin mikewa, da sauri Tariq ya mayar dashi.

"Zaka bar wane wajen? Yaya zaka fara ko? Wallahi babu inda zakaje in ba sallamarka akayi ba"

Yasir ya kalla.

"Ka daina kallona da gaskiyar Tariq. Wannan ba ciwukan da zaka iya yawo dasu bane ba"

Hararshi Ashfaq yayi. Yasir baibi takanshi ba ya dauko leda daya daga cikin wanda ya ajiye yana budewa. Sabbin brush ne a ciki, ya dauki daya yana miqa ma Tariq daya karba.

"Yanda kwakwalwar ka take tunanin abubuwan da ya kamata cikin yanayi irin wannan yana bani mamaki"

Tariq ya fadi yana mikewa ya nufi bandakin dake cikin dakin. Yana turo kofar Ashfaq ya kalli Yasir.

"Aikin Seyi ne ko?"

"Faq ba yanzun ba..."

"Ka fadamun kawai. Shine ko bashi bane ba?"

Ledar dake gabanshi Yasir din ya ture gefe yana jan kujerar da yake zaune zuwa gab da gadon Ashfaq, lokaci daya fuskarshi ta canza zuwa wani irin yanayi da zai tsorata ka, tabon dinkin dake gefen fuskarshi tundaga wajen goshi yabi ta gefen kuncinshi har kusan wuya yana haduwa da yanayin dake fuskar tashi. Sai dai yanayin fuskar Yasir ko dar bata sa Ashfaq yaji ba.

"Yanzun kake son yin maganar nan? Da ciwon dake jikinka? Da Tariq a cikin dakin?"

Kauda kai gefe Ashfaq, ciwon jikin shi bazai hanashi son yin maganar ba, Tariq ne matsalar shi.

"Ina son sani ne kawai"

"Tunanin me kake? Me kasha da zakai Deal da Seyi? Inda wani abu ya sameka fa? Faq kasan a halin daka sakani? Dame kake so in fadama Tariq?"

Kallon shi Ashfaq yayi dake fassara ka cika zuzuta abu.

"Da wacce tambayar kake son in fara?"

"Karka gwada hakurina Ashfaq Hisham Tafeeda"

Dariya Ashfaq yayi, dai-dai fitowar Tariq daga bandakin.

"Me ake yiwa dariya?"

Ya bukata, shiru sukai su duka, Yasir najan kujerar shi baya.

"Ga abin Sallah nan a ninke"

Ya fadi maimakon amsa tambayar da Tariq din yai mishi. Jinjina kai Tariq yayi yana kallon Yasir din

"Babu sirri a tsakanin mu har saida kazo"

Cikin idanuwa Yasir ya kalle shi.

"Tsanarka ba sabon abu bane a wajena Tariq, kayi Sallah lokaci na wucewa"

"Meye matsalar ka da Sallah ta? Gefena za'a binne ka?"

Tariq ya fadi rai a bace, bude baki Yasir yayi zai bashi amsa Ashfaq ya katse shi.

"Ba zaku samun ciwon kai ba...Tariq kayi abinda yake gabanka..."

"Amman Yaya..."

Idanuwa Ashfaq ya kafa mishi daya sashi kasa qarasa maganar daya soma. Qarasawa yayi ya dauki dardumar yana shimfidawa. Kunya na rufe shi da yanda hasken rana ya cika dakin. Baccin da baiyi ba daren jiya da kuma codien din daya sha suka hadar mishi waje daya.

Muryar Yasir kasa-kasa yace ma Ashfaq

"Kaga abinda kaja ko? Bai tsane ni haka da farko ba"

"Wayace ya tsaneka yanzun ma?"

"Hmm..."

Kawai Yasir ya fadi yana janyo leda daya ya dauko burger da lemon exotic dan yunwa yake ji. Rabon cikinshi da wani abu tun safiyar jiya, da sauri yake ci, dan haka bai bata lokaci wajen gamawa ba. Mikewa yayi

"Ina zaka je?"

Ashfaq ya bukata, muryar Yasir can kasan makoshi ya amsa shi

"Dattin daka zubar zan goge"

Ashfaq din baice komai ba, kamar yanda Yasir bai jira amsar shi ba ya fice daga dakin.

"Allah yasa ya tafi kenan"

Cewar Tariq daya idar da Sallah. Lumshe idanuwanshi Ashfaq yayi yana bude su kan Tariq.

"Meye matsalar ka da Yasir?"

"Kafi kowa sanin matsalata dashi... Ba haka kake ba kamun yazo... Yaya mu biyu ne kawai, a komai mu biyu ne. Tun zuwanshi kuka zama ku biyu... Kana kwanaki baka nan, bansan inda kake ba, amman shi ya sani... Abu irin wannan zai sameka shine farko a wajen bani ba..."

"Tariq..."

Girgiza mishi kai Tariq yayi.

"Karka soma gayamun abinda bazai faru ba. Ba ina fada maka dan nasan komai zai canza bane, ina fada makane dan ka tambaya"

Kai Ashfaq ya daga mishi. Wani abu na tokare mishi wuya. Girman sirrin dake tsakanin shi da Tariq din na mishi nauyi sosai.

"Ka zo kaci wani abu"

"Bana jin yunwa"

Tariq ya amsa shi.

"Ba tambayarka nayi ko kanajin yunwa ba. Canai kazo kaci wani abu"

Yanayin muryar Ashfaq din ya fada mishi babu wajen gardama. Dan haka ya mike yana nannade dardumar hadi da komawa kujerar da Yasir ya tashi yana zama.
**

ABUJA

Sallama ya sake yi a karo na ukku, baiji motsin kowa ba, harya karasa tsakiyar falon.

"Nuri!"

Ya kira yana samun waje ya zauna kan kujerar hadi da sauke numfashi mai nauyi. Yana ficewa daga dakin Tasneem kasa zaman gidan yayi kuma. Shisa yayo gidansu. Kilan ko Nuri yagani zuciyarshi zatayi sanyi.

"Nuri!!!"

Ya sake kira a karo na biyu. Asabe yar aikin su ce ta fito da sauri tana gaishe da Rafiq din da ya amsa yana dorawa da.

"Ina Nuri?"

"Sun fita ita da Aroob...amman kaman Fawzan yana nan"

Kai kawai Rafiq yadan daga mata, ta juya. Numfashi ya sake saukewa, yammacin dai yana zo mishi wani iri. Wayarshi ya ciro daga Aljihu ya

1 Comments On ALAKALAMIN KADDARA PART 1
avatar
khadija-7-4

1 year ago

Reply

Yayi

Please Login or Register in order to submit comment