Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ma Jawwad, hannunshi yasa yana murza kirjinshi inda zuciyarshi take ko zaiji saukin ciwon da take mishi.

'Kai da yaranka ba matsalata bane, dan ba a kayan daki aka zubomun su ba, bazan zauna wahala da nakasasshe ba, bayan ga mai lafiya na sona'

Numfashi Jawwad yake ja da sauri da sauri, ko ina jikinshi kyarma yake, juyawa yayi yana kokarin hawa machine dinshi, dakyar ya samu yahau,amman kyarmar da hannuwanshi suke yasa ya kasa saka mukullin cikin kofarshi. Hannunta yaji kan bayanshi, riqe jikinshi yayi yana dauke numfashi.

"Dan Allah ka saurareni, wallahi inata nemanku, shekara uku ina nemanku bansan inda kukayi ba. Jawwad dan Allah ka saurareni..."

Take fadi tana wani irin kuka da Jawwad yake ji jar tsakiyar kanshi. 'Karka saurareta' shi yake ta maimaitawa cikin kanshi, Allah ya bashi sa'a ya samu ya saka mukullin cikin machine din ya murza yana tayar dashi. Dayan hannunshi yakai ya tunkude nata dake kan bayanshi yana jan machine din batare daya duba ba yahau titi.

Yana kai inda zai iya juyawa yai corner yana kama hanyar da zata mayar dashi gida, ko ganin gabanshi bayayi sosai, sau biyu yana kusan jan hatsari, bai damu da zagin da masu motar suke mishi ba. Kawai so yake yaganshi cikin gida. Gudun da yake yasa cikin mintina goma ya karasa gida, shigowar dayai yana gabje kofa ta fara tabbatar ma da Anty ba lafiya ba.

Da sauri ta fito daga daki, taganshi yana zare mukullin machine, kallo daya taima fuskarshi da tai fari kamar wanda yaga fatalwa tace

"Lafiya? Me ya faru?"

Girgiza mata kai Jawwad yakeyi yana kokawa da numfashin shi.

"Jawda! Kawomun ruwa"

Anty ta fadi, tana kama hannun Jawwad din ta zaunar dashi. Bai musu ba ya zauna a kasa, har lokacin numfashin shi yaqi dai-daita. Jawda ce ta fito da ruwa a kofi tana bama Anty.

"Yaya... Me ya same shi?"

Jawda ta tambaya tana ware idanuwa cikin tashin hankali. Anty batako juya ba balle ta kulata, ruwan taba Jawwad daya karba yana sha kamar sauqin shi na tare da ruwan.

"Inalillahi, jinin meye wannan a kafarshi?"

Jawda ta fadi tana tsugunnawa hadi da zare takalmin Jawwad din, wani irin yankane a gefen kafar ke fitar da jini sosai, dankwalin dake kanta Jawda ta cire batare da tunanin komai ba tana dafe wajen dashi.

"Jawwad kaimun magana... Me yake faruwa wai? Menene? Hadari kukayi?"

Anty take tambaya a rikice. Girgiza mata kai yayi yana dafe kanshi da duka hannayenshi.

*

"Dan Allah karki tafi...karki barmu... Wallahi bansan yanda zan dasu Jawda ba, kinga Abbu bashida lafiya. Dan Allah mama karki barmu..."

Jawwad ke fadi cikin kuka yana riko hijabinta. Juyowa tayi ta fisge hijabinta hadi da ture shi yakuwa fadi kan dan yatsan shi na hannun haggu, yanajin karar dayayi da azabar data shige sh har tsakiyar kanshi.

"Jarabar naci kamar ubanka. Me zan zauna in muku? Ka dauka haka na tsara rayuwa da yara kaca-kaca? Allah yaban wata damar dazanyi rayuwa yanda nake so. Kayi duk yanda zakai dasu kana jina? Bazan zauna ba, kuma koka nemeni ba samuna zakayi ba..."

Azabar da hannunshi yakeyi bai hanashi binta da kallo ba, karar akwatin da take ja har cikin zuciyarshi...!

*

"Yaya!!!"

Muryar Jawda ta katse mishi tunanin da yake. Bude fuskarshi yayi, yana dafa bango ya mike tsaye. Hanyar falo ya nufa, daga Anty har Jawda babu wanda ya hanashi. Baikuma damu da ciwon dake kafarshi ba. Kai tsaye dakinshi ya wuce yana doko kofar da karfi kamar zai karyata.

"Ciwon dake kafarshi na buqatar dinki..."

Anty ta fadi.

"Bazai fito yanzun ba kinsani ba, bazai tsaya ba. Saidai ko idan Izzat ta dawo ita kadai zata iya..."

Jinjina ma Jawda kai Anty tayi da fadin

"Allah ya rufa asiri"

"Amin"

Jawda ta amsa. Dan sunsan abinda kawai zai iya saka Jawwad shiga yanayi. Abune da ba'a tattauna shi a cikin gidan, abune da yake da haramci mai girma a cikin gidan gabaki daya, koda a bayan idon Jawwad ne kuwa. Falon suka koma, Jawda na karfin halin kunna TV din sa suka zubama ido badon suna fahimtar abinda akeyi a ciki ba.

**

KADUNA

A jikin motar Majida tabar mukullin tana fita hadi da doko murfin da karfin dayasa Altaaf runtse idanuwanshi. Fushi take tunda yaki yarda a tsaya asibiti a dubashi. Bakuma zai iya fada mata rashin lafiyar dayake baga da alaka da asibiti ba.

Rumfuna ne sunfi shidda cikin gidan an shimfida tabarmi, dayake akwai hali ga abinci da lemuka an fiffito dashi yasa wajen shaqare yake da mutane. Numfashi Altaaf ya sauke, bayason hayaniya a halin da yake ciki. Inda son samun shine ya koma gida ya kwanta a daki shi kadai.

Karar shigowar text yaji a wayarshi. Da sauri ya dauko yana dubawa. Karamin tsaki yaja ganin MTN ne suka aiko mishi da saqo, gogewa yayi yana duba saqon dake sama. Ya shiga, duk kusan iri dayane, sunfi guda hamsin duk shige suke da juna, ban hakuri da neman yafiya, ga alamar ya shiga har an karanta amman kuma babu amsa.

'Me yasa ba zaka yafe mun bane haka Ashfaq?'

Ya fada cikin ranshi yana jingina kanshi da gaban motar, runtsa idanuwa yayi hotunan yaran na dawo mishi, zuciyarshi na sake sabon salon dokawa, zazzabi sabo na sake lullubeshi. Yana so wani ya fada mishi ya kwantar da hankalinshi babu abinda zai faru, ya fada mishi zuciyarshi ce kawai take wasa da kwakwalwarshi.

Amman hotunan yaran daya dauka a zuciyarshi kawai sun ishe shi. Yanajin agogon bomb din dake kirgawa a cikin kanshi, kamar yana jiran wani abune ya fashe dashi gabaki daya.

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"

Altaaf ya furta cikin neman sauqi daga yanayin da yake ciki. Kwankwasa glass din murfin motar yaji anyi, hakan yasa shi dagowa ya bude murfin motar.

"Badai jikin bane kuma?"

Aslam ya tambaya cikin kulawa. Kai kawai Altaaf ya iya girgiza mishi yana fitowa daga motar.

"Kabar mukullin a jiki"

Juyawa yayi yana zira rabin jikinshi ya miqa hannu ya zaro mukullin yana rufewa. Cikin aljihu ya saka mukullin suna jerawa shida Aslam suka nufi inda mutane suke ana karbar gaisuwa. Sama-sama suka gaggaisa da mutane ya dauki buta yai alwala dan ko Magriba baiyi ba yana kuma da tabbacin isha'i ta wuce.

*

Aslam ne yasa aka kaisu masaukinsu, ganin yanayin Altaaf din, rakashi yayi har dakin tukunna ya juya yana komawa. Kwanciya yayi badan yanajin ko alamar bacci ba. Idanuwanshi ya lumshe yana sauke numfashi, dai-dai lokacin wayarshi ta dauki ruri. Baiko motsa ba ballantana yai niyyar dauka harta yanke.

Sake daukar sabon ruri tayi, hannu yasa ya zarota daga aljihunshi yana dubawa. Babu shiri ya dauka ganin Majida ce.

"Majee..."

Ya fadi muryarshi can kasa.

"Baka ci komi ba, ka hito gani nan zan taho bakin kohwa saika ansa..."

Dan dafe kanshi yayi

"Banajin zan iya saka ma cikina komai"

"Haka nan zaka kwanta da yunwa?"

Ta bukata, yanajin damuwar dake cike da muryarta.

"Harna kwanta ne"

Ya ce a gajiye.

"Mike damunka?"

Runtsa idanuwanshi yayi, jikinshi na wani iri da yanda yake so ya fadama wani damuwarshi.

"Zazzabi ne kuma ya sauka, bacci kawai nake sonyi..."

"Akwai abinda ke damunka, baka so ka hwadi manne kurun, kasan hushi nike dakai baka neman ba, ko baka lahiya kana cin abinci, ba abinda ke shiga tsakaninka da abinci..."

Ya manta Majida tasanshi, ko yace tasan Altaaf, tasan mutumin daya koma kamar yanda tasan kanta, baya kuma fatan hakan ya canza. Zuciyarshi ta fara mishi ciwo da abinda zai furta mata

"Ina son ganin yaran mune Majee, inason rike nawa dan a hannuna kamar kowa, sai yaushe zai faru damu?"

Shirun daya biyo bayan maganar da yayi yasa shi cire wayar daga kunnenshi ya duba dan yaga ko ta yanke ne, yaga tanayi shirun dai Majida tayi ya kuma san maganganun shi sun tabata. Muryarta can kasa tace

"Mi kakeso inyi?"

Girgiza kai yayi kamar tana ganin shi.

"Kin saurareni, shine kawai bukatata a yanzun. Saiki kwanta kuma karki bari maganganuna su dameki..."

"Hmm..."

Ta fadi daga dayan bangaren

"Majee..."

Ya kira sunanta cike da yanayoyi da dama. Yasan tana saurarenshi duk da bata amsa ba. Hakan yasa shi ci gaba da fadin

"Ina sonki...kome zai faru ina sonki wallahi"

Da sauri tace

"Kana bani tsoro, dan Allah ka hito in ganka, wai minene?"

Ta karasa maganar muryarta na karyewa, tana saka zuciyarshi matsewa a kirjinshi.

'Ka sata kuka, hankalin ka ya kwanta'

Wata murya ta fada mishi cikin kanshi. Tashi yayi zaune.

"Kawomun wani abu, barin fito"

Da sauri tace

"Me kake so?"

"Komai ma.."

Ya karasa yana mikewa tsaye, yanajin ta kashe wayar daga dayan bangaren. Badan zaici ba yace ta kawo, sai dan in bai karba ba yasan ba zata daina tunanin wani abu daban na damunshi ba. Fita yayi kofar boys quarters din da aka sauke su ya sake kiran Majida ya fada mata ta zagayo ta bayan gidan saboda mutane.

"Kayi sallah kau?"

Ta bukata data karaso, kai ya daga mata yana karbar ledojin dake hannunta.

"Yawwa to, sannu"

Duk da kallon fuskarta yakeyi yaki yadda su hada idanuwa. Hannu yakai yana ja mata hanci, ta ture hannunshi tana dariya hadi da matsawa.

"Sai wani ya ganka?"

Matsawa yayi yana hade space din dake tsakanin su. Ya kamo hannunta.

"Ba ruwana da wani, ni da matata"

Kanta ta sunkuyar kasa, dan murmushi ya kwace mishi, kunyar Majida kan bashi mamaki, shekarun nan basu sa ta daina jin kunyarshi ba. Rankwafawa yayi ya sumbaci gefen kuncinta.

"Kije ki kwanta. Ki kularmun da kanki"

"Sai da sahe... Allah ya kara lahiya"

Ta fadi har lokacin kanta na kasa, hannunta ya saki yana amsawa da

"Amin..."

Tsaye yayi saida yaga tasha kwana tukunna ya koma cikin gidan zuwa dakin da zasu kwana. Ledojin ya ajiye a kasa yana zama kan gado, wayar dake hannunshi ya duba yana danne-danne. Kamun ya tsinci kanshi da kiran lambar Ashfaq. Kirjinshi ke dokawa tare da bugun wayar.

"Meye?"

Yaji an fadi, saida ya dan zabura saboda bai taba zaton za'a daga wayar ba. Hannu yasa yana share zufar data fara fito mishi.

"Ashfaq?"

Ya kira yana son tabbatar da ko ya yarda wayarne wani ya dauka, ko kuma Tariq ne ya daga. Jin anyi shiru yasa shi sake fadin

"Faq?"

"Meye wai?"

Wani numfashi mai nauyi Altaaf ya saki, muryar Ashfaq din na canza mishi, saidai bazai iya tuna asalin yanda take a daba balle ya hadata data yanzun. Da yasan Ashfaq zai daga daya tsaya ya tsara abinda zai fada mishi, ya kuma san in har damar nan ta wuce shi da wahala ya kara samun irinta.

"Babu wanda zan kira, babu wanda na yadda dashi a halin yanzun..."

"Duk shekarun nan wa kake kira? Ina matarka?"

Ashfaq ya tambaya ta dayan bangaren da alamun dake nuna gab yake da katse kiran.

"Karka kashe Ashfaq...dan Allah karka kashe. Bazan iya fada mata ba, bazan iya fadaka kowa ba koda na tabbatar da abinda nake shirin fada maka.... Saboda bansan ta ina zan fara ba... Bangarene dana ke tunanin na rigada na wuce..."

"Kabar shan sigari ka koma zuqar hayaqin maganin sauro ko Altaaf?"

Ashfaq yai maganar cikin yanayin dake fassara 'anya kana da hankali'. Daga mishi kai Altaaf yayi cike da yarda dan shikanshi ji yake in dai da hankalinshi to yana gab da barin shi. Sigarin da Ashfaq ya kira na saka shi wasa da yatsun hannun shi, yana bukatar ta fiye da komai a yanzun.

"Ina tunanin ina da yara...yan biyu Faq"

Yanajin dariyar da Ashfaq yakeyi ta cikin wayar, dariya yakeyi sosai, dayayi kamar zai bari saiya sake dasa sabuwa, cikin dariyar yace

"Tariq na tunanin yaga Yasir, kai kana tunanin kana da yara guda biyu... Ni ina kwance da harbi a jiki...."

Dariya ta hana Ashfaq karasa maganar, dakyar ya samu yaci gaba da fadin

"Kuma ka rasa wa zaka kira ka fadama saini? Wayama muke ko? Yaushe muka zo nan?"

Altaaf ma baisan lokacin da dariya ta kubce masa ba. Sosai suke dariya shida Ashfaq din kamar sababbin mahaukata, kamun Altaaf ya goge kwallar dayaji tana bi mishi fuska da baisan kota mecece ba.

"Bansan yanda zan ba...in yarana ne..."

"Ka daina magana kaman bakasan hakan zai iya faruwa ba. Kaje ka tabbatar idan yaranka ne tukunna..."

Kai Altaaf ya daga yanajin yanda komai ya sake danne shi, wani irin sabon tashin hankalin daya saukar mishi tare da tunanin komawa Kinkiba.

"Nag..."

Ya fara, Ashfaq yai saurin katse shi.

"Karka sake kirana, karka sake damuna da saqonni... Yafiya abune me kyau nasani, haline na mutane masu kirki. Na jima da manta yanda duka biyun suke. Bazai faru a tsakanin mu ba"

Kamun yace wani abu, Ashfaq ya kashe wayar daga bangarenshi. Kan gadon Altaaf ya ajiyeta yana kwanciya ya hade jikinshi waje daya, kamar yanda yakejin komai ya hade mishi, sabon amai na taso mishi, ga zufa da yakeji har cikin tafukan hannunshi saboda tashin hankali. Inda zai samu sigari daya rage zafi.

Saidai a yanayin da yakeji ko daga kan gadon bazai iya sakkowa ba ballantana ya fita wajen neman sigari. Rufe idanuwanshi yayi, maimakon ya samu sauki saima hotunan yaran nan daya cika mishi zuciya. Bai kokarin kauda su ba, karfinshi nayau gabaki daya yagama karewa.

**

ABUJA

Amai taji yana neman taso mata, dakyar ta dafa kujera tana mikewa, dabin bango ta gano dakinta, kai tsaye bandaki ta wuce, babu wani abu bane a cikinta, dan haka ba karamar wahala tasha ba wajen kakarin aman, har hakarkarinta amsawa yakeyi. So tayi tadan watsa ruwa ko zata samu sauki-sauki amman bata da karfin da zata cire kayan jikinta ma.

Fitowa tayi tana janyo kofar bandakin, nan kan kafet ta kwanta, hawaye masu zafi na bin gefen fuskarta. Bata zaci Rafiq zai tsallaketa batare dayace komai ba, ya kamata yace wani abu, duka labarinta ta juye mishi, sirrin da daga shi sai samha ne suka sani. Ba zata manta lokacin da suka hadu da Samha ba, wajen siyan ankon bikinsu da Rafiq ne.

*

"Ki dauki purple din nan, kinga muma ita muka fitar ankon sister dina..."

Samha ta fadi, dan murmushin karfin hali Tasneem tayi, dan shigowarta shagon kallo daya taima Samha ta dauka zatai girman kai, badan kyan da take dashi ba kawai, sai dan yanayinta gabaki daya dayake nuna ta fito gidan da kudi suke zaune. Amman saita bata mamaki datai mata magana.

"Bari in dauketa kawai..."

Tasneem ta fadi tana zarar guda hudu, ita bikin gabaki daya bashi bane matsalarta, fitar da anko bashi bane damuwarta, saidai su Azrah ba zasu barta ta huta ba in bata fito dashi ba. Auren da take da tabbacin bawani dadewa zaiba. Kudin ta biya tana fitowa daga shagon, sai dai me, kamar jira hawayen dake shirin kubce mata sukeyi. Hannu tasa tana gogesu, amman ta kamar tunzurasu take.

Tun da aka kawo kudin aurenta, kamar an bude mata bangaren da take tunanin ya dade da bushewa ne, sai yanzun zabukan da tayi suke danneta, saida ta dandana soyayyar Rafiq tasan tayi babban kuskuren da zai zame mata tabo na har abada. Kausar ce kawar da take da ita nagartacciya a rayuwarta. Mamansu Kausar da kanta tajata gefe wajen walimar bikin Kausar din ta roketa data kyale mata yarinya ta zauna gidan mijinta lafiya.

Ta kaunaci Kausar da zuciyarta daya, ta kuma girmama rokon mahaifiyarta, bata sake nemanta ba, ko kalar gidanta bata sani ba. Sauran tarkacen kawayen datai ma, soyayyar Rafiq tasa duk ta watsar, saidai bazai gyara komai ba. Bazai dawo mata da darajarta ba, Haidar ya soma kwace babban bangare daga ciki, sauran kuwa da kanta ta rarraba a titi.

Kuka take sosai har saida ta daina tafiya, mutane sai kallonta suke, inma magana suke bata jisu ba, ga kirjinta kamar zai rabe gida biyu. Jitai an riqo hannunta ana janta, runtse idanuwa tayi tana bude su da sauri, kayan jikin Samha ta fara ganewa, batai gardama, hawayenta kuma basu daina zuba ba. Haka tabita har bakin wata mota, bude mata Samha tayi da alamar ta shiga. Batai musu ba ta shiga, batare da tunanin komai ba.

Dayan bangaren Samha ta zagaya ta shiga tana kunna motar taja suka fita daga cikin kasuwar. Waje ta samu gefe tai parking tukunna ta kalli Tasneem dake kuka har lokacin.

"Me yai zafi ke kuwa? Kuka a cikin kasuwa? Kina ganin yanda mutane suke kallonki har an fara taruwa?"

Samha take fadi da damuwa a muryarta. Kallonta Tasneem tayi da fuskarta da harta kumbura tace

"Kallon da mutane suke mun ne karshen damuwata..."

"Ki gwadani, me yake damunki?"

Girgiza kai Tasneem tayi, bata san Samha ba, tayi zabuka marassa kyau da ba zata iya komawa baya ta gyara ba, akwai wani abu tare da ita da yake fada mata bata da asara dan ta juye ma Samha duka damuwarta, tana son fadama wani, ko zata daina jin nauyin da kirjinta yake mata.

*

Samha bata taba sa taji daban ba, bata taba ce mata kinyi kuskure ba, dan ta gane ita da kanta tasan tayi kuskuren ba saita sake maimaita mata ba. Samha kawace da Allah ya jeho mata lokacin da take cikin halin bukata. Hannu tasa kan cikinta tana runtsa idanuwanta.

"Ina kaunarka tun kamun fitowar ka, kilan kai ba zaka gujeni ba, ba zaka rikeni da kuskuren da nayi ba..."

Ta fadi hawaye na sake zubo mata. In Rafiq nason magana da ita yasan inda zai sameta, ta ma kanta alkawari inba tsautsayi ba, ba zata sake nuna mishi fuskarta ba tunda bayason ganinta, ta kuma cancanci dukkan hukuncin dayai niyyar dauka. Shine abinda take nanata ma zuciyarta da taqi yarda, banda bori babu abinda take mata. Tana gaya mata Rafiq yai musu komai su biyun, amman karya rabu dasu.

**

Kanshi dafe yake cikin hannuwanshi, numfashin shi yake son saitawa amman abin na neman gagara. Hakan yasa shi sake jinjina ma su Fawzan, kanshi ya dauki dumi, ga kirjinshi dayai nauyi yana zafi kamar ana hura mishi wuta saboda rashin wadatacciyar iska. Mikewa tsaye yayi yana zuwa ya bude windows din dakin gabaki daya, yaje ya kunna fanka yana sake kai gudun AC din karshe, amman bai samu numfashin shi ya koma dai-dai ba.

Zama yayi kasa yana kwantar da kanshi dake ciwo kaman zai tarwatse kan kafet. Runtsa idanuwanshi yayi gam, ko zai daina ganin Tasneem da jerin mazajen dabazai iya dora muau fuskoki ba. Zuciyarshi na ci gaba da tafasa. Dagowa yai zumbur kamar wanda aka tsikara.

"Ya akai nasani? Ya akai nagane?"

Ya tambayi kanshi, amman ya rasa amsa, wani haske yaji ya gilma mishi ta cikin idanuwanshi, hakan yasashi rufesu, saidai hasken har cikin kanshi ya jishi da wani irin ciwo daya sa ya dafe kan yana kiran sunan Allah. Numfashi yake sama-sama yana samu kan nadan mishi sauqi. Da rarrafe ya karasa wajen gadonshi yana kama gadon yahau.

Wayarshi yake nema, bai ganta cikin dakin ba, tunawa yayi tana falo yabarta inda suka zauna da Tasneem. Yana bukatar wayar, amman bayason ganin Tasneem, ko kadan bayason ganinta. Tashi yayi yana tsayuwa na yan mintina dan ya tabbatar zai iya tafiya batare daya fadi ba. A hankali ya bude kofar dakin yana takowa cikin sanda.

Fara dubawa yayi yaga bata falon, ga wayarshi nan ajiye kan kujera, da sauri ya dauki wayar yana zira takalmanshi suma da suke cikin falon ya fice daga gidan gabaki daya. Kofar gida yai tsaye batare daya san inda zaije ba. Tambayoyi yake dasu da yawa, ya rasa me yasa yake da tabbacin Nuri ba zata amsa mishi ba.

Wayar ya danna yana cire mukullin jiki, lambar Muneeb ya lalubo ya kira yana karawa a kunnenshi. Bugu biyu Muneeb din ya daga

"Rafiq"

Ya fadi ta dayan bangaren da sigar gaisuwa.

"Kazo gidana yanzun..."

Rafiq ya fadi a kagauce.

"Lafiya dai ko? Rafiq me yake faruwa?"

Hannu Rafiq yasa ya murza goshin shi inda yakejin wani ciwo na daban na tattaruwa.

"Kazo kawai... Zan fada maka inkazo... Dan Allah kayi sauri..."

"Gani nan, ina wajen aiki ne, zankai mintina talatin ko dazan karaso. Zaka iya jira har lokacin? In ba zaka iya jira ba in kira Faruk yafi kusa..."

Girgiza kai Rafiq yayi kamar Muneeb din na ganinshi kamun yace

"Zan jira..."

Yana sauke wayar daga kunnenshi ya sakata cikin aljihunshi. Ya kasa tsayuwa waje daya, da kaga yanda yake kai kawo ba sai an fada maka ba kasan yana cikin yanayi na damuwa.

"Abu daya na bukata Neem, gaskiya kawai nace ki fadamun kamun in bukaci soyayyarki. Me yasa? Me yasa zakimun haka?"

Rafiq ya fadi yana girgiza kanshi. Kamun zuciyarshi tai wata irin dokawa dayaji har cikin bakinshi.

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."

Ya dinga maimaitawa yana runtsa idanuwanshi ko zai samu tadan nutsu, amman kamar ma yana tunzurata. Batare daya bude idanuwanshi ba ya ciro wayarshi daga Aljihu yana dan dumtse ta tukunna ya bude idanuwa. Lambar Nuri ya kira

"Assal..."

Bai bari ta karasa ba ya katse ta da fadin

"Nuri ina Fawzan?"

Shirun dayaji tayi na kara gudun zuciyarshi, wani irin tsoro marar misaltuwa na ziyartarshi.

"Yaya..."

Numfashin da Rafiq ya sauke saida yaji kafafuwanshi nason kasa daukarshi.

"Karka sake tsoratani haka Fawzan... Nayi yarinta da bugun zuciya"

Dariyar Fawzan din ta daki kunnenshi tana sauqaqa mishi wasu bangarori da baisan suna mishi ciwo ba sai yanzun.

"Hanyar kace ta fadamun yanda kake so na ko?"

Hararshi Rafiq yayi kamar yana ganinshi.

"Zaka fara surutun ka... Ya jikin ka?"

"Ni na warke...Alhamdulillah"

"Allah ya kara sauki. Ka dai zauna sai an sallame ka. Kana jina?"

"Yes Sir"

Fawzan ya fadi cike da tsokana, amman Rafiq din yasan yaji shi. Kashe wayar Rafiq zaiyi Fawzan yace

"Ball din yau tayi kyau ko kuwa?"

Nuri da Rafiq yasan tana nan zaune tare da Fawzan din zata dauka yana tambayarshi labarin wasan kwallon kafane. Amman yagane abinda Fawzan yake tambayarshi. Yana tambayane idan komai lafiya, yana kuma tabbatar mishi da zai saurara batare daya bari Nuri tagane komai in bayaso ba.

"Karka damu...ba wano abu bane da bazan iya dauka ba In shaa Allah, kaidai ka huta kawai"

Rafiq ya fadi, rashin Fawzan dinne yasashi ya kira Muneeb, ko cikin abokanshi Muneeb ne kawai yake sanin kadan daga cikin sirrikanshi. Gara ya raba damuwarshi da Fawzan ko bakomai dan uwanshi ne, ko da bazai bashi shawara ba.

"Ko dai ya aka tashi ka fadamun, ina nan"

Jinjina kai Rafiq yayi, Fawzan na nufin in har komai ya cakude kiranshi kawai Rafiq din zaiyi. Sauke wayar yai daga kunnenshi yana mayarwa cikin aljihu. Duk da jin muryar Fawzan ya nutsar dashi ta wani bangaren, sai da ya sauke wayar ne yaji har lokacin zuciyarshi bata daina dokawa ba.

'Zafira' wata murya ta fada mishi can kasan zuciyarshi, baya tabajin faduwar gaba irin haka idan ba wani abu bane ya sami wani makusancin shi. Saidaya dauko wayarshi yake tunanin rabon dayaji muryarta ma. Damuwarshi ta danne son jin lafiyarta a satikan nan.

Kiranta yayi harta yanke bata dauka ba. Sai da ya kira sau hudu tana yankewa bata dauka ba, wani abu na fada mishi ba lafiya ba. Babu yanda za'ai lafiya kalau taki daga wayarta. Ko bacci take zataji ringing din wayar ai. Bai hakura ba yaci gaba da kira, da duk yankewar da zatayi bata dauka ba da yanda zuciyarshi ke kara jagule mishi.

Na lokacin ya manta da tashi damuwar da duk wata tambaya da yake da ita, kawai so yake Zafira ta daga wayar yaji tana lafiya. Komai zaizo da sauqi in babu abinda ya sameta. Zai kamo bakin zaren tashin matsalar, amman yana bukatar sanin yan uwanshi dukansu lafiyarsu kalau. Yana bukatar wannan nutsuwar.

A haka Muneeb ya karaso ya same shi, lokacin ya kira Zafira babu adadi bata daga ba. Muneeb na fitowa daga mota yace

"Lafiya wai? Kaban tsoro wallahi"

Girgiza mishi kai yayi

"Bansan me ya sami Zafira ba, na kirata yafi sau goma bata dagawa..."

Runtsa idanuwanshi Muneeb yayi kamar Rafiq ya watsa mishi wuta, kamun ya matsa baya taku biyu yana bude idanuwanshi da wani irin yanayi akan fuskarshi. Jin yayi shiru yasa Rafiq dauke idanuwa daga kan wayar dake hannunshi yana mayarwa kan Muneeb. Kamun ya ware idanuwanshi cikin gane abinda yayi.

"Karka damu..."

Muneeb ya fadi, duk da haka akwai wani yanayi a muryarshi dayasa Rafiq saurin turama Zafira gajeran saqo da fadin

'In kin zo ki kirani'

Kamun ya mayar da wayar gabaki daya cikin Aljihunshi duk da har lokacin bawai zuciyarshi ta nutsu bane, sai dan shi mutum ne da yake duba halin da mutanen dake kusa dashi zasu shiga akan abinda yake aikatawa kamun nashi yanayin, duk da a wata biyun nan ya rasa kanshi. Muneeb din ya ki hada ido dashi.

"Ka nisanta ni da unguwar nan sai muyi magana"

"Ina zamuje?"

Muneeb ya bukata yana juyawa wajen motar shi hadi da bude murfin ya shiga mazaunin direba, sai da Rafiq ya shiga ya

1 Comments On ALAKALAMIN KADDARA PART 1
avatar
khadija-7-4

1 year ago

Reply

Yayi

Please Login or Register in order to submit comment