Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kamun ya samu wajen zama a zuciyarta.

"Abba ya samu shaida mai kyau a wajen mutanen da basuda kusanci dashi, bansan me yasa ke kadai kike ganin bakin halin shiba Ummi, bansan me yasa ba. Yabar miki duniyarma bai huta ba...babu abinda nai musu, aikin ne kawai nabari, daman nice nace zanyi daga farko yanzun kuma na ajiye. Shine abinda ya faru..."

Tasneem ta tsinci kanta da fadi, mamaki Ummi take dan koda wasa Tasneem bata taba mayar mata da magana ba irin yau. Kuma ranta ya baci sosai.

"Rashin kunya zakiyimun Tasneem? Wallahi ajiye aikinki ku zai shafa. Dan banda yanda zanyi in ciyar daku, saiki san yanda zakuyi dan bawai..."

Tasneem bata bari Ummi ta karasa maganar ba ta juya ta shige daki tana rufo kofar duk daba kullewa sukeyi ba. Tayi hakanne kozai rufe mata jin Ummi, kirjinta takejin kamar an kunna wuta a ciki. Jingina jikinta tayi da kofar tana zamewa kasa.

"Me yasa Ummi ba zata daina mana haka bane? Daman ai ba ita take ciyar damu ba. Me yasa zata dinga miki fada bayan baki mata komai ba?"

Hamna take maganar muryarta na rawa da alama kuka take.

"Hamna..."

Tasneem ta fadi, danko alamar hawaye bataji ba. Kirjinta ne kawai yake ciwo, saikuma duniyar da take jin ta hade mata waje daya babu inda zata shaqi numfashi na daban.

"Daman ita ta rasu ba Abba ba"

"Hamna mana!"

Tasneem ta fadi kirjinta na kara zafi da maganganun Hamna din. Cikin kuka Azrah tace

"Ba ita kadai take wannan tunanin ba. Nima inayi wallahi. Nasan bakyau amman inayi lokutta da dama"

"Oh Allah na"

Shine abinda Tasneem ta iya fada kawai tana mika musu hannuwanta. Tasowa sukayi daga inda suke kowannen su na kama hannuwanta dai-dai suka rike suna wani irin kuka. Kwantar dasu tayi a jikinta. Yanda rayuwarta tayi wayam ba zata bari tasu tayi haka ba, zata karesu daga komai na rayuwa dai-dai iyawarta. Komai zai tabasu zata shiga tsakani koda Ummi ce da kanta kuwa.

Anan jikinta sukai bacci, ko runtse Tasneem bata runtsa ba, saboda zafin da kirjinta yakeyi. Kan kunnenta aka kira Sallah tukunna ta tashi su Azrah. Dakyar ta iya yin alwala dan ko tafiya dakyar takeyin ta. Ciwuka takeji a ko ina na jikinta. Azkar din safema batai ba, ta koma kan katifa ta kwanta ko zata samu bacci ya dauke ta, kilan kanta da yake sarawa yai mata sauqi.

BAYAN WATA SHIDDA

Kallon kanta take a karamin mudubin dake riqe a hannunta. Zuciyarta ta kasa gane taswirar dake cikin mudubin, daga kan janbakin dake labbanta, zuwa komai na fuskarta ya canza. Daga randa Haidar ya cinna ma darajarta wuta tasan wani abu ya canza tattare da ita.

Halin da suka shiga na bakar yunwa watanni kadan bayan wannan ya sake busar mata da wani bangare na zuciyarta. Bata sake jin duniyar ta mata wayam ba saida Ummi ta fara zaman gida, tana aiken su Azrah, samari na soma musu zarya a kofar gida. Tasan abinda ya faru da ita zai faru dasu Azrah Ummi ba zata taba damuwa ba indai zasu kawo mata abin duniya.

Batajin akwai wani abu daya rage mata banda kula dasu Azrah, banda tabbatar da abinda ya faru da ita bai faru dasu ba, ganin sun samu duk wani abu da Abba yake da buri su samu a rayuwar su. Da taimakon Ummi da ta bata zabin ko ita ta dinga tsayawa da duk wasu samari da zasu aiko kiranta ko kuma tabarsu Azrah, ciki kuwa harda Alh. Madu yasata fahimtar abubuwa da dama.

Sosai take kallon kanta a mudubin tanajin daudar da duk yanda ta sama jikinta ruwa baya bata barinta yanzun. Tana kumajin da duk rana daudar na kara mata nauyi, zuciyarta na kara bushewa da duk fita siyayyar da zasuyi da Alh. Madu yanda hannuwanshi ke yawo a jikinta. Bata kokarin hanashi, zama take kamar gunki, sai abin ya isheta ne zatace mishi zata shiga gida.

Bakinshi a washe zai bata kudi masu yawa, Abbanta ne kawai yake sakawa batama maza kudin goro, tasan a cikin tarin dubban lalatattu ba'a rasa ko mutum daya mai nagarta. Saidai duk wanda zaizo wajenta da burin hannunshi yakai jikinta ne. Daudarsu da yanda tabarsu suna shafa mata ya canza ta ta fanni da dama.

Ajiye mudubin tayi, Alh. Madu take jira yauma dan yace zaizo su fita siyayya. Bakin Ummi a washe yake yanzun kullum, ko fada ba koyaushe take ba, inkaji ta itada Hamna ne, dan basa zama inuwa daya.

"Fita zakiyi"

Hamna ta fadi da wani yanayi a muryarta dayasa zuciyar Tasneem daukar zafi. Inbasu ba, babu abinda yake taba mata zuciya yanzun. Su kadai take kallo ta tabbatar tanajin wani yanayi yanzun. Mudubin ta ajiye tana juyawa, kallonta Hamna take kamar bata ganeta ba. Kamar tana nemar yayarta a da take da tabbacin tana wani waje a cikin Tasneem din amman batasan yanda zatayi ta fito da ita ba.

"Siyayya kawai zamuyi Hamna. Ba dadewa zanba"

Girgiza kai Hamna tayi

"Banaso, kin canza, kuma banaso"

Hannu Tasneem tasa a kirjinta inda yake mata zafi tana dan dannawa ko zataji sauki.

"Hakanne kadai zai rufe bakin Ummi, kuma kinga muna samu muci abinci, kuma kuna zuwa makaranta"

"Alh. Madu ne kawai da. Yanzun wasune daban, bashi kadai bane kina fita tare da wasu daban. Ki auri daya a ciki mana..."

Hamna ta karasa kamar zatai kuka. Murmushin takaici Tasneem tayi, cikinsu babu wanda ya taba mata maganar aure koda wasa. Ba aurenta suke sonyi ba tasani, bashi bane a gabansu kamar yanda itama yanzun bashi bane damuwarta.

"In lokaci yayi Hamna...ki yarda dani, zan iya kula da kaina daku duka"

Hawayen da Hamna take riqewane ya siraro kan kuncinta. Hannu tasa ta goge shi, muryarta can kasa tace

"Karkiyi abinda Abba bazai so ba, karki boye bayan kula damu..."

Tana karasa maganar ta fice daga dakin takoma tsakar gida inda su Azrah suke zaune ita da Sabeena. Tana barin Tasneem da nauyin maganganun data yaba mata. Suna samun waje sukai mata zaune a gefen daudar da take tare da ita. Saidai tanajin lokaci ya kure mata yanzun. Ana kiran Maghrib ta tashi tai Sallah dan ta dauro alwala datai wanka daman.

*

Jikinta take ji a sanyaye tun safe, agogon hannunta da ba zata tuna sunan saurayin daya siyaba ta janyo ta duba lokaci, koyaushe su Azrah zasu iya dawowa daga islamiyya yanzun. Wani irin zafi ake gashi babu wuta koda fankar dakinsu bawani yi take ba sosai saboda tsufa amman takan rage wani abun.

Dan haka Tasneem ta tashi tana fitowa tsakar gida ko zata danji sauqi-sauqi. Ko zama batai ba Hamna ta shigo da gudu tana mayar da numfashi kamar zata shide da alama gudun data shane da kuma Sabeena da take goye da ita. Sauke ta tayi tana kokarin dai-daita numfashin ta

"Lafiya?"

Tasneem ta tambaya duk da kallo daya taima Hamna din tasan ba lafiyarta ba.

"A... Azrah..."

Hamna ta fadi dakyar hawaye na zubar mata. Sai lokacin Tasneem take kallon Hijab din Hamna din da jini yake a jiki da gefen wandon ta, hakama jikin Sabeena, girgiza kai take a karona farko bayan watanni da dama dataji idanuwanta sun ciko da hawaye, ta dauka wannan bangaren nata ya rigada ya mutu.

"Azrah..."

Hamna ta sake fada tana kasa dai-daita hankalinta waje daya taima Tasneem din bayani. Bata jira bayaninta ba, takalman dataji a kofar daki su ta zurama kafafuwanta dayan ma ba nata bane na Ummi ne, kuma ba kafar ba, amman bataji ba. Cikin wani irin tashin hankali ta ture Hamna tana fita da gudu ko Hijab babu.

"Yaya Tasneem!"

Hamna ta kira da karfi, amman ko waiwayowa Tasneem batai ba, kiran ne ya fito da Ummi daga daki tana kallon Hamna data zame a kasa tana wani irin kuka.

"Hamna? Lafiya? Meya faru?"

Dago kai Hamna tayi, da rarrafe ta samu ta fara tafiya kamun ta dafa kasa ta mike tana fadaw jikin Ummi data riqeta a tsorace, dan ko rasuwar Abbansu bataga rikicewar Hamna haka ba.

"Inalillahi... Hamna meya faru ne? Menene?"

Ummi take tambaya. Kuka Hamna take tana riqeta dan tunda take a rayuwarta bata taba sanin asalin tsoro irin nayau ba. Dakyar tana wani jan numfashi take fadin

"Az...Azrah... Ummi Azrah.. Mota..."

A tsorace Ummi ta ware idanuwanta kan Hamna

"Me ya sami Azrah din? Tana ina?"

"Mota ta bugeta... Ta mutu Ummi.. Jini...Jini ko ina..."

Hamna ta karasa dakyar, tureta Ummi tayi tana rugawa daki da sauri, hijab ta dauko ta fito, takalmanta tazo sawa taga sai wari daya. Haka ta hada nata dana Tasneem ta saka, ta kama hannun Hamna dana Sabeena suna ficewa. Gidan ma janshi tayi, har can kofar gabaki daya bata kulle ba, janta kawai tayi. Rabonta da karatun Qur'ani mai yawan wanda take yanzun a hanya harta manta. Dako a sallolinta surori marassa yawa take yi.

Bakuma zatace ga abinda take karantawa ba. Bason su Azrah bane batayi, batasan yanda zata nuna ba, bakuma tasan son ya girma haka ba sai yanzun. Rasa Abbansu bakomai bane ba, daman soyayyarshi bawai girma tai a zuciyarta ba. Amman tunanin rasa Azrah, tunanin rasata kawai yasa hawaye na dishe ganinta. Bata taba sanin islamiyarsu nada nisa ba sai yau. Dan tafiya take amman taga sun kasa zuwa, badan su Hamna da take riqe dasu gam ba data fadi, danko hanya bata gani sosai saboda kukan da take.

*

Tasan mutane na kallonta, amman bata damu ba, kafafuwanta kawai take so yakaita titin da zai tsallaka da ita islamiyarsu Azrah. Mutanen data gani a gefen titin yasa zuciyarta kara gudu wajen dokawar da takeyi. Ture mutane kawai take tanason karasawa.

"Baiwar Allah lafiya?"

Wani mutum ya tambaya. Ko kallonshi Tasneem batai ba, wanda yake gabanta kawai tasa hannu tana fisgo rigarshi ta ture shi gefe daya. Ganin yanda take ture mutane ya sasu tabbatar da tana da alaqa da yarinyar dake kwance, dan haka suka matsa mata.

"Wai ya ma akai mai motar nan ya gudu? Wanne irin rashin imani ne wannan?"

Tasneem taji muryar wani mutum na fadi, saidai ba ita bace matsalarta. Idanuwanta na kafe kan Azrah dako motsi batayi, hijab dinta ko ina jini ne. Kasa ta zauna batare data kula bama, tana kamo Azrah ta rungume a jikinta tana sa dayan hannunta tare da shafa fuskar Azrah din

"Azrah... Azrah... Azrah..."

Tasneem take fadi a tsorace, ko motsi batai ba, hawaye ke zuba daga idanuwan Tasneem kamar an mata gorinsu, bata yi kokarin gogewa ba, fuskar Azrah kawai take shafawa ko zata samu taga ta motsa.

"Ba zaki barni ba kema... Kina jina ko? Tashi zakiyi Azrah... Wallahi ku kadaine dalilin da nake kokarin rayuwa kullum... Karki barni a wannan lokacin... Azrah ki tashi"

Tasneem ke fadi tana wani irin kuka. Dai-dai lokacin da Ummi ta karaso, dafa Tasneem din tayi data juyo.

"Ummi taqi tashi wallahi... Taqi tashi..."

Tasneem take fadi tana riqo hannun Ummi dam, dan yau bukatar lallashi take data jima batayi ba. Batajin zuciyarta zata iya daukar rashin Azrah.

"Akaita asibiti mana"

Wani mutum ya fadi, hakan ya kawo tunanin su Ummi zuwa asibiti. Ummi da kanta ta sunkuya ta dauki Azrah tana sabata a kafadarta. Adai-daita sahu aka taro musu suka shiga zuwa karamin asibitin dake nan unguwar, saidai kallo daya sukai ma Azrah sukace su tafi babban asibiti.

Aikuwa adai-daitar suka sake shiga zuwa Aminu Kano, badan wani mutum daya bisu ba, da basu san yanda zasuyi ba. Dan ana cewa hadari ne sukace ba zasu karbeta ba saida yan sanda. Shiya barsu ya koma da mai adai-daita ya dauko dan sanda aka shigar da report. Hatta kudin shiya biya tukunna yai musu fatan samun sauqi ya tafi.

Sai lokacin aka shiga da Azrah dan a dubata. Kowa ya daina kuka banda Hamna. Har lokacin kuka take har zazzabi ya fara saukar mata. Kamun wani likita ya fito ya kira Ummi zuwa office dinshi. Su duka suka bita ya dakatar dasu bakin kofa.

"Ita kadai nake son gani. Ku jirata anan"

"Kome zaka fada mata inya shafi Azrah ya shafemu duka. Inkaga ban shigo naji me zakace ba bana numfashi ne malam"

Hamna ta fadi muryarta a dakushe. Tasneem ma da idanuwanta take fada mishi babu abinda zai hanasu jin kome zai fada. Numfashi ya sauke dan baigama amfanin shiga office din ba. Kamun ya kalli Ummi da ta dan daga mishi kai alamar zai iya fadar koma menene.

"Ciwukan dake wajen jikinta basu da wani hadari amman tana zubda jini ta ciki, da alama akwai ciwo a cikinta. Dole saimun mata aiki, kamun mu tabata muna bukatar dubu tamanin..."

Ware idanuwa Ummi tayi tanajin hanjinta ya daure waje daya. Danko dubu biyar bata ajiye ba bata kuma san inda zata damo ba balle har dubu tamanin. Kallonshi Tasneem tayi zuciyarta nayin shiru a kirjinta.

"Zan kawo...ku dubata wallahi zan kawo"

Dagashi har Ummi da mamaki suke kallon Tasneem din.

"Ki zauna dasu Ummi, zan kawo kudin..."

Tasneem ta sake fadi bata jira sunce komai ba ta wuce da gudu tana fita daga asibitin. Mai machine ta samu daga nan zuwa gida direct dan batason bata lokaci. Cikin gida ta shiga ta dauko mishi kudinshi ta sakama jikinta Hijab. Sannan ta fito, tana tafiya tanajin duniyar sama-sama.

Gidan Alh. Madu ta tsinci kanta da yake nan cikin unguwarsu. Tako yi sa'a ya fito yana shirin shiga mota ganinta yasa shi washe baki.

"Tasneem?"

Ya fadi cike da shakku da mamakin ganinta. Muryarya can kasan makoshi tace

"Dubu tamanin nake so"

Ware idanuwa Alh. Madu yayi da fadin

"Toh! Dubu tamanin?!"

Kai ta daga mishi a hankali.

"Tasneem kudin da yawa"

"Nasani shisa nazo"

Tace tana kallon shi. Wani murmushi yai mata daya sa tajin abincin dataci na shirin fitowa daga cikinta.

"Mu shiga daga ciki in duba ingani. Amman dubu tamanin..."

Ya fadi yana kara jinjina maganar. Bin bayanshi Tasneem tayi suna komawa cikin gidan. Tanajin ana kiran Sallar Maghrib, tana kuma jin idanuwan maigadinshi na binta da kallon kyamata. Bashi bane matsalarta a yanzun, yanda zuciyarta tai shiru a kirjinta ne damuwarta, tasan imaninta ne tai nisa dashi sosai, shaidan ne yake son mamaye hasken dayai saura a rayuwarta, bakuma ta da karfin fada dashi.

Haka taci gaba dabin shi har cikin gida, har cikin wani daki, da duk takun datai da yanda takejin duhun na sake mamaye ta, har saida ta shiga ciki ya mayar da kofar ya rufe da sauran hasken daya rage mata.

*

Bata koma asibitin ba sai bayan sallar isha'i. Danko tsoron daren ma bataji ba sam. Hannunta damtse da ledar da kudin da ta siyarma Alh. Madu jikinta ya bata. Dubu dari ya bata cif tare da alkawurran kome take so tazo wajenshi zai bata da sauran surutai da bata bari sun zauna mata ba.

Tana shiga asibitin ta karasa inda su Ummi suke ta taso da fadin

"Kin samo kudin Tasneem?"

Ledar ta fiddo daga Hijab dinta ta mikama Ummi tana samun waje gefen Hamna dake rungume da Sabeena datai bacci ta zauna. Ummi kuma na barin wajen.

"Ina kika samo kudi?"

Hamna ta tambaya. Batare da Tasneem ta kalleta ba tace

"Ba satowa nayi ba"

Yanda taji Hamna ta gyara zama kusa da ita yasata jin wani iri da yanayin datai mata magana. Batare da Hamna ya kamata ta raba laifinta ba, dan batai komai ba.

"Kiyi hakuri"

Hamna ta fadi muryarta a sanyaye da alamar kuka. Sauke numfashi Tasneem tayi

"Alh. Madu yaban"

Kai kawai Hamna ta daga batare da tace komai ba. Sai kanta data jingina a kafadar Tasneem din da takeji kamar ta tureta dan batason daudar da take jikinta ta shafi Hamna ko kadan. Duk da tayi wanka yafi a kirga a gida kamun ta taho tai salloli, a sujjadarta ne kawai hawaye suka zubo mata. Dagashi ko digo har yanzun.

Anan suka kwana. Ga sauro ga rashin abinda zasu ko shimfida. Dan ita Tasneem ko runtse bata runtsa ba. Idanuwanta ma data lumshe dole ta bude su. Saboda babu abinda take gani banda Alh. Madu da kazantar da suka aikata.

*

Sai karfe goma na safe tukunna aka fito da Azrah zuwa wani daki aka kuma basu damar cewar zasu iya zuwa su ganta. Haka suka shiga suka zauna. Su shidda ne a dakin, Ummi ta fita bakin asibitin ta siyo musu fanke da lemuka, amman ko dandane Tasneem bataci ba. Haka ta ajiyeshi a gefe ta zubama Azrah idanuwa.

So take ko motsi taga tayi. Amman shiru har Azahar. Ummi da Hamna suka koma gida dansu dafo wani abin, kuma Hamna ta taya Ummi su kawo musu kayan da zasu dan bukata. Suna bar mata Sabeena. Sai bayan sun tafine tukunna Tasneem ta riqo hannun Azrah dan dayan jini ake qara mata. Dumtsewa tayi cikin nata tanajin yanda hannun yai sanyi karara.

Dago hannun tayi tana kwantar da fuskarta a jiki.

"Azrah ki taimakamun ki tashi...bansan yazanyi in baki tashi ba. Ganin idanuwanki a bude zai bani kwarin gwiwar daukar nauyin abinda na aikata dan lafiyarki...dan Allah ki tashi haka... Ki tashi inji muryarki ko zanji sauki..."

Ta karasa hawaye sirara na zubar mata. Motsi taji hannun Azrah yayi cikin nata, da sauri ta bude idanuwanta tana kallon fuskar Azrah din data bude nata idanuwan dakyar kamar hakan kawai na mata wahala.

"Ruwa..."

Ta fadi can kasa, badan hankalin Tasneem gabaki daya na kanta ba da ba zataji abinda tace ba. Ruwan dake ajiye gefe Tasneem ta dauka da sauri tana dago kan Azrah din a hankali dan nade yake da bandeji bata kuma san inda yake da ciwo a jiki ba ta bata ruwan. Kurba biyu tayi ta kauda kai. Ajiyewa Tasneem tayi.

"Azrah..."

Ta fadi hawaye na sake zubo mata, wannan karin wani nauyine taji ya daga daga kirjinta da zubar hawayen. Nauyin daya danneta na rashin tabbas akan tashin Azrah.

"Na daga miki hankali ko? Ina kika samo kudin magani na? Tun yaushe nake nan?"

Azrah ta fadi tana runtse idanuwanta da alama karfin hali kawai take. Tasneem girgiza mata kai take saboda kukan da take ya hanata magana. Hannun Azraj kawai ta riqe tana cigaba da kuka sosai. Shiru kawai Azrah tayi tana dumtse hannun Tasneem din cikin nata.

*

Satin su biyu a asibitin da Azrah, Ummi take kwana a wajenta wani lokaci da Sabeena. Da yamma ita da Hamna suke komawa gida. Kamun a nemi wani abu Tasneem taba Ummi kudin, saidai tana kula da bata su a gaban su Azrah. Musamman Hamna dako sun dawo gida ta fita inta dawo haka zata tsareta da idanuwa cike da tuhuma kamar tasan abinda ta aikata.

Tun abin yana damunta harya daina. Kome zatayi akan kula dasu zatayi. Kuma zata tabbatar rayuwarsu bata fada inda tata tayi ba. A asibitin ne ta samu kawa, Kausar data ke jinyar mahaifiyarta a dakin da aka ajiye su Tasneem din. Sosai shakuwa mai karfi ta shiga tsakaninsu, danko bayan an sallami su Tasneem din tana zuwa duba mamansu Kausar.

Haka ma bayan an sallame su basu yanke zumuncinsu ba. Takanzo har gidansu Tasneem, itama tana zuwa gidansu dake gwammaja. Inda duk Tasneem take son zuwa Ummi bata hanata, bama tambayarta take ba, bakuma koda yaushe take ce mata ta fita ba. Su Azrah kawai take fadama ta fita da kuma lokacin da zata dawo.

*

Haka rayuwa taci gaba da tafiyar musu, a hankali wata irin wayewa take shigar Tasneem, haka tace ma su Hamna ta sake samun aiki a wani company buga leda saboda tambayoyinsu sun fara isarta. Unguwa duka babu wanda baisan tana tare da Alh. Madu ba yanzun. Dan ana ganinsu suna yawo a gari yana kuma zuwa gurinta.

Haka yanzun da wahalar gaske kaga mai mai babur yazo wajen Tasneem. Alhazawane yan kasuwa manya. Inbabu kwalliya a fuskarta ba lallai ka sake mata kallo na biyu ba. Dan tana da duhu kamar Abba, duk da ba zaka kirata fara ko chocolate ba, su Hamna ne sukai fari da kyawun Ummi. Hancinta ba tsayi gare shi ba, haka bawata doguwa bace ba kuma siririya ce sosai. Hakoranta na gaba manyane sosai, duk daba fitowa waje sukai ba, irin hakoran da mutane kema laqabi dana zomo. Su dukkansu banda Sabeena haka hakoransu na gaba suke, dan Ummi suka biyo.

Wasu lokutta takan rasa abinda maza suke bi a tare da ita. Kalilan matasan dake cikin samarinta kan jata wajajen shaqatawa, anan tai kawaye da suka kara bude mata idanuwa suka kuma kara wayar da ita yanda zata karbi kudin samari batare da wani babban abu ya shiga tsakanin su ba. Ta rasa lokacin ranar data wayi gari ta daina jin laifin da take aikatawa.

Amman ya bace mata. Yanzun ta saba da rike kudi sosai. Takuma saba da jin dadi. Ga wani irin shiri da suke da Ummi dan duk fadan nan ta daina. Haka kusan koda yaushe tana gida. Shisa tun makota na kawo mata magana akan Tasneem suka bari, dan ta bata da kowa akan Tasneem a cewarta bakin cikine kawai dan anga yarta nada farin jini. Komai kuma ya canza musu, tana aikinta tana samun kudi shisa.

Yanzun gashi har Azrah da Hamna na ajinsu shidda a makaranta. Girmansu na bata mamaki. Musamman Hamna da kyawunta yake kara fitowa. Haka samari ke musu zarya, amman Tasneem ta hanasu tsayawa da kowa, Ummi kuma ta goyi bayanta tunda ita take da gidan yanzun. Abinda duk take so shi akeyi.

Yauma kamar koda yaushe saurayinta ne Baffa yazo wajenta shida abokinshi TJ da kuma budurwar TJ din Aliya.

"Gaskiya Tasneem zakiyi missing in bakije wajen nan ba. Kuma wallahi Jenifer ba zataji dadi ba..."

Aliya ta fadi, Jenifer kawarsu ce itama, yaren igala ce girman Kano, taji hausa kamar me. Itace take shagalin ranar zagayowar haihuwarta, kuma ba za'a fara shagalin ba sai karfe goman dare, a cewarsu kwana za'ayi. Ba zuwa bane batason yi, ba zata kwana a wani waje ba.

Abinda bata tabayi ba kenan, duk yawon data fita karfe bakwai hankalinta inyai dubu a tashe ta dawo gida, dan intai dare batasan me zatace ma su Hamna ba. Ko karya tai Azrah ta yarda a idanuwan Hamna take ganin tasan karya take. Bata damu da maganganun mutane akanta ba, bata damu da mutuncinta a idanuwansu ba. Dan batajin sauran mutunci a tare da ita. Amman ta damu da yanda su Hamna zasu kalleta.

"Ai ba karamin kwafsamun zakiyi ba wallahi"

Baffa ya fadi yana kallonta da idanuwan shi da su kadaine abinda ke mata kyau a tare dashi. Kasa tai da muryarta

"Kasan bazan iya zuwa ba. Da da yamma ne"

"Kabarta sai muyi maka sabuwar budurwa kawai"

TJ ya fadi yana kashe mata ido daya. Hararshi tayi bawai dan ta damu da budurwar dayace zaima Baffa ba. Tasan ba ita kadai bace budurwarshi kamar yanda yasan bashi kadai bane saurayinta. Zuciyarta su Azrah ne kawai a ciki, bata da wajen wata damuwa bayan tasu.

"Nikam zan shiga gida. Kar in tsayar daku. Aliya kiba Jennifer hakuri dan Allah"

Tasneem ta fadi, hannunta Baffa ya riqo yana marairace fuska. Murmushi Tasneem tai mishi daya tsaya iya fuskarta.

"Da gaske tafiya zakiyi kibarni? Haba Pretty karkimun haka mana..."

Hannunshi dake riqe da nata ta dumtse tana murza yatsun shi.

"Kayi hakuri ba..."

"Tasneem???"

Taji kamar daga sama. Juyawa tayi, hasken motar da TJ yake ciki ya tayar yana haska mata shi gabaki daya, kamun zuciyarta tai wani tsalle tana dawowa kan harshenta. Inda idanuwanshi yake ta fara kallo tana sakin hannun Baffa da sauri kamar wuta, tukunna ta mayar da hankalinta kan Tariq da idanuwanshi suke kafe a kanta yanzun.

"Baffa kaje zamuyi magana..."

"Pretty..."

Ya fara ta katse shi batare data kalle shi ba.

"Kaje zamuyi magana"

Ta sake maimaitawa tana takawa ta karasa inda Tariq yake tsaye yana kallonta har lokacin. Zuciyarta na cigaba da dokawa take kallonshi. Shekaru wajen uku kenan rabon data sashi a idanuwanta. Ya canza sosai, kallon yanda yai tsayi da girma take, dan da wahala kanta yakai ko kusa da kafadarshi. Ga suma cike da kanshi, saidai akwai wani abu tattare da idanuwanshi da bataso.

"Tasneem..."

Tariq ya kira da mamaki, kamar yanason tabbatar ma kanshi ita dince bawai karya idanuwanshi suke mishi ba.

"Ya Tariq..."

Tasneem ta fadi tana kallon shi itama cike da mamaki. Tun tunaninshi na damunta harta samu waje gefen zuciyarta ta danna shi ta adana. Hannunshi ya daga kamar zai taba fuskarta.

"Tasneem..."

Ya sake fadi yana kasa samun wasu kalamai banda sunanta, yana son yace mata ta canza daga kwalliyar dake fuskarta zuwa komai nata, amman ya kasa samun kalamai, sun makale mishi.

"Ka canza sosai..."

Murmushi yai mai sauti yana sauke hannunshi.

"Kin canza kema..."

Dan daga kafadunta tayi, tanajin zuciyarta

1 Comments On ALAKALAMIN KADDARA PART 1
avatar
khadija-7-4

1 year ago

Reply

Yayi

Please Login or Register in order to submit comment