Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register



"Kudin da suke hannu na ba zasu isa ba"

"Zan miki transfer anjima... Karki sake damuna da maganar nan"

*

Girgiza kanshi Altaaf yayi, dakyar ya yakice inda tunanin shi yake son su kaima ziyara. Hannunshi yakai yana kunna Radio, yaci sa'a a tashar cool FM yake, sun saka wakar Justin Bieber-Love yourself, sosai ya kure volume din kamar zai fasa musu dodon kunne.

Majida kamar tasan bayason kwakwalwar shi ta samu nutsuwar da zata tuna mishi abubuwan dazaiyi komai danya goge, batai kokarin rage mishi volume din ba. Har suka karasa gidansu da yake a Hotoro.

*

Yana dawowa Sallah a falo ya zauna yana daukar remote, ya kasa tsayawa tasha daya. Gabaki daya bayajin dadin komai, ganin yaran ya taba mishi zuciya ta inda baikamata ba. Baiji fitowar Majida ba sai hannuwanta yaji cikin gashin kanshi tana yamutsawa,ta bayan kujerar da yake zaune.

Kama hannuwanta yayi yana janyota, ta zagayo, murmushi da bai niyya ba ya kwace mishi, kumatunshi ta ja, ya ture hannunta yana murza wajen. Zama tayi tana mishi dariya.

"Ko kai hwa. Kahi kyau da murmushin nan a huskarka"

Murmushin ya sake mata, yana jin sonta a wajaje fiye da zuciyarshi. Yasan shi ya kamata yana kwantar mata da hankali akan maganar haihuwar nan, amman ita take kwantar mishi, ta fishi buri saboda bata san abinda yasani ba.

"Wani abu nake sonci"

"Kamar me?"

Dan daga kafada yayi

"Ba yunwa nake ji ba...bakina ne yai switch off"

Dariya Majida take sosai.

"Kwadayin ka yahi karhina... Sai kace mai karamin ciki"

Daga mata gira yai duka biyun kamun ya matsar da kanshi saitin kunnenta yana fada mata maganar da sirri ce kawai a tsakanin su, dariya Majida takeyi cike da kunya, kamun ta ture shi tana mikewa ta nufi kitchen. Ita din bamai yawan ciye-ciye bace ba. Indai cikinta ya koshi.

Altaaf yasa dole bata rabuwa da wani dambun nama, wasu snacks a fridge da zata iya mishi warming. Ko kadan inba azumi yake ba baya barin bakinshi ya huta. Kayan zaqi har fada suke wani lokacin, dan in ciwon ciki ya tasar mishi ita yake bari da tashin hankali fiye da ciwon dake damun shi.

Sanda ta dawo waya Altaaf yakeyi, dan haka ta ajiye mishi plate din dambun naman a gabanshi ta samu waje ta zauna da fadin

"Mi zamu ci ne da dare? Tun dazun nike tunani na rasa"

Dan daga mata kafada yayi yana dibar dambun naman yasa a bakinshi.

"Ko in mamu dambun shinkahwa?"

Dariya Altaaf yake sosai, tun daga zuciyarshi yake jin dariyar,

"Majee ce shinkafa"

Ya bukata yana ci gaba da dariya, itama murmushi take, ta dauki pillow din kujera dake gefenta tana jefa mishi, ya tarbe da hannun shi yana ci gaba da mata dariya

"Ki ce ko dambun shinkafa zan mana... Ba mamu da shinkahwa ba"

Itama dariyar take, bata ga ranar da Altaaf zai daina tsokanarta kan hausar ta ba.

"Ka kyaleni, ban iya wa dakai da marecen nan"

Girgiza kai Altaaf yayi yana dariya. 'Marecen' da tace na tuna mishi farko-farkon auren su.

*

Kallon Majida yake data fito daga gidan, da wata hijabi zundumemiya kamar zata tashi sama, dan inda a kasa zasu tafi, tsaf zata share titin layin da hijab din. Sauke numfashi yayi cike da takaici, baisan randa zata waye ba. Yanayin yanda take tafiya tana lauyewa kamar zata fadi ne data karaso ya sashi fadin

"Meye kike tafiya kamar zaki karye?"

Turo baki tayi, gabaki daya yanayin fuskarta ya canza kamar zatai kuka tace mishi

"Bani son takalma masu tsini, yaman tsayi, ji nike kamar zan hwadi"

Murmushi yadanyi kawai, yana kallon ta, rana ce ta lumshe, hakan yasa ta daga kanta sama tana wani matse idanuwa.

"Hadari ke da kwai ma, inaga ruwan marece za ai"

Daquna fuska Altaaf yayi yana kallonta sosai.

"Ruwan me?"

Ya tambaya.

"Ruwan marece"

Ta amsa tana kallon yanda yake daquna fuska yana maimaita kalmar

"Marece, wanne ne kuma ruwan marece"

Hararshi Majida tayi, in akwai abinda ta tsana bai wuce tambaya ba, musamman ma ta rainin hankali.

"Meye marece?"

Ya sake tambaya

"Kwaddo"

Ta amsa shi tana jan murfin motar ta shige abinta.

"Marece, kwaddo, ruwan marece? ruwan kwaddo?"

Yake maimaitawa dan babu abinda yagane, fuskarshi a daqune da rashin fahimta ya zagaya yana shiga gidan motar shima ya rufe, mukullin yasa jiki yana murzawa, hankalin shi kan abin da yake yi yace

"Ke meye kwaddo din wai?"

Hararshi Majida tayi ta gefen ido, tana sauke numfashi mai nauyi ta bakinta, ya cika tambaya harta tsiya, ta ke fadi a zuciyarta, baima san bakar magana ta fada mishi ba. Shiru tayi

"Na tsani ina magana ai banza a kyale ni"

Ya fadi ranshi a bace, baisan meke damun Majida ba, kaman yanda baisan ya akai zuciyarshi ke da sanyi akan ta ba, wacece mace, dashi Altaaf Tafeeda zai mata magana tai shiru ta kyale shi, matan da suka fita aji, kyau da komai har so suke ya kula su.

"Dake fa nake"

Dira kafafuwanta tayi cikin motar tana wani bula katon hijab dinta kaman mai shirin hawa bori, muryarta cike da shirin yin kuka tace

"Nikau bani son tambayar tsiya... Wai baka kyaleni?"

Motar ya kashe, bakin shi a sake yake kallon ta, sun gama kwana waje daya shisa ta raina shi haka.

"Ke?"

Ya fadi, har lokacin mamaki yaki barin fuskarshi, kallon shi tayi tana jin bata kyauta ba, amman ya isheta ne da tambaya.

"Da gaske kake wai baka san miye marece ba?"

Ta bukata.

"In nasani me yasa zan tambayeki"

"Yamma hwa"

Ta amsa, yanayin datai maganar ne yasa bai gane ba har lokacin. In akwai abinda ya tsana bai wuce yaqi fahimtar wani abu ba, ko a makaranta Allah ya mishi nacin tambaya. In bai gane komai ba sam hankalin shi baya kwanciya, Majida ta fara sashi ciwon kai.

"Yamma fa kika ce, Yamma ta gabas ko wacce?"

Dafe kanta tayi cikin hannuwanta, gab take da kurma ihu, muryarta can kasa tace

"Evening...evening nike nihi"

Ware idanuwa yayi cikin mamaki, murmushi na kwace mishi, musamman yanda yaga ya kure hakurin ta. Baisan me yasa hakan yasa shi nishadi ba.

"Kwaddo fa?"

Takai minti daya shiru, har lokacin bata dago da kanta ba kamun tace

"Frog"

Dariya ta kwace ma Altaaf daya sa Majida dagowa tana kallon shi dan bata san me ya bashi dariya ba.

"Kwado ne kwaddo? Kwaddo fa..."

Ya karasa yana dariya, takaici ya sa bata ce mishi komai ba.

*

Ringing din wayarshi ne ya katse mishi tunanin da yake, daukar wayar yayi, har lokacin da murmushi a fuskarshi kamun ya kara a kunnen shi hadi dayin sallama.

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un.... Yaushe?"

Altaaf ya bukata, zuciyarta taji ta doka, dan tasan kowanne labari ne ake bashi ta dayan bangaren bamai dadi bane ba.

"Allahu Akbar... Oh Allah. Allah ya jikanta. Yanzun nan gidan zanzo mu tafi gabaki daya ko ya za'ayi?"

Shiru ya sake yi, Majida kuwa ta kagu ya sauke ya fada mata kowa ya rasu.

"To shikenan. Yanzun zamu taho muma In shaa Allah. Allah ya jikanta ya kara hakuri

Altaaf ya karasa yana sauke wayar daga kunnenshi, kallon Majida yayi.

"Gwaggo Rakiya ce ta rasu"

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un... Allah sarki... Baiwar Allah...oh ansha jinya"

Majida ta fadi, dan sau biyu suna zuwa Kadunar suna duba kanwar mamar Altaaf din, sosai tasha jinya baiwar Allah.

"Allah yasa mutuwar ta zame mata hutu gare ta"

Majida ta fadi. Altaaf ya amsa da amin yana dorawa da.

"Su Ammi har sun tafi, ki hada mana kayanmu, mu bi bayan su"

Mikewa Majida tayi tana nufar daki dan ta hada musu kayansu. Tana jinjina yanda duniyar babu wani tabbas a cikinta.

**

ABUJA

"Rafiq daka tashi ka tafi gida. Kaga har takwas da rabi... Kama kira matarka kuwa?"

Nuri ta karasa maganar da tambaya. Girgiza mata kai Rafiq yayi, in akwai abinda ya tsana a rayuwarshi bai wuce karya ba.

"Ka kyauta kenan? Sarai kasan hankalinta zai tashi tunda ka wuce lokacin komawarka gida..."

Katse Nuri yayi da fadin

"Hankalina ne bai a kwance ba Nuri...bari in kirata yanzun"

"Ka tashi ka tafi dai... Tunda duk muna nan"

Girgiza mata kai yayi. Babu inda zaije in baiga Fawzan ya farka ba. Yana son tabbatar da cewa zai samu lafiya da kanshi, bai yarda da maganar likitocin ba, tunda basu suka dauko Fawzan baya numfashi ba.

"Kiyi hakuri in kirata din...hankalina bazai kwanta ba in ba gani nai ya tashi ba"

Cikin taushin murya Nuri tace

"Rafiq... Ba yau yafara ba. Kasani, lokacin sanyi yana shiga yanayi daya wuce wannan ma. Sau nawa muna fidda rai akan Fawzan din? Sai kuma kaga ya tashi. Zamanka bazai canza komai ba... Addu'ar ka yafi bukata, kuma ko daga ina ne zata same shi"

Dan dafe kai Rafiq yayi, bayajin karfi ko kadan a jikinshi. Abubuwa sun taru sun mishi yawa, duk yanda yake son zama sai Fawzan ya tashi baikai yanda bayason jan magana da Nuri ba. In gidan ya koma ma hankalinshi ba kwanciya zai ba, zaman asibitin yadan cire mishi zuciyarshi daga matsalar can gidan.

Isa ya kira ya fada mishi yazo ya dauke shi. Bai sake cewa komai ba har saida Isa ya kirashi yana wajen asibitin tukunna ya mike da fadin.

"Allah ya kara sauki... Inya tashi ki kirani"

Kai Nuri ta daga mishi

"In shaa Allah...ka kwantar da hankalin ka dan Allah..."

"Hmm..."

Rafiq ya iya cewa yana jan wani numfashi.

"Nagaji dakin fadamun dalilin da yasa bana iya tuqi da kowa yakeyi Nuri...naso inji daga bakin ku... Koma menene zaimun sauqi in kune kuka fadamun. Nagaji da jira...nagaji da jira Nuri"

Ya karasa muryarshi can kasan makoshi kamun ya rankwafa ya sumbaci Nuri a kuncinta,sannan ya kalli Aroob

"Komai zaiyi dai-dai..."

Idanuwanta cike taf da hawaye ta daga mishi kai. Suna kallon shi harya karya kwana, hawayen da Aroob take tarbewa suka zubo.

"Nuri ta ina zamu fara fada mishi? Me zamu ce mishi?"

Ita kanta Nurin idanuwanta cike suke da hawaye lokacin da take amsa Aroob

"Bansani ba. Wallahi bansan me zamuce mishi ba"

"Kinsan Yaya Rafiq... Zai gano da kanshi...in bamu fada mishi da kanmu ba wani zai gaya mishi a waje"

Jinjina kai Nuri tayi cike da yarda da maganar Aroob din. Dan kullum zuciyarta dokawa take da sanin cewa kowanne lokaci wani zai iya subutar baki ya fadi abinda zai sake birkita musu komai. Duk da iya inda Rafiq yakan shiga, mutanen da yake mu'amala dasu daga wajen aiki har zuwa abokanshi tasan suna kaffa-kaffa kan maganar kamar yanda sukeyi.

"Mu kanmu bamu gama dawowa dai-dai ba... Bansan mezai faru ba"

Hannu Aroob tasa tana goge hawayen da suka sake zubo mata. Kamun tace

"Allah ya kawo mana dauki..."

Ajiyar zuciya Nuri tayi ta amsa da amin. Tana jingina kanta da bangon wajen hadi da rufe idanuwanta.

*

Da nauyin zuciya ya shiga gida, wani rauni-rauni yake ji, bazai iya tuna lokacin karshe da ya zubda hawaye ba. Yanayin da yake ji a yanzun, inda hawayen zasu zubo mishi kila da ya samu sauki. Ko ta ina rayuwar ta hargitse mishi, ya kamata ya tsayar da zuciyarshi kan Aslam ne, amman ya kasa.

Bayan damuwar Fawzan, akwai matsalarshi da Tasneem, bayan ita akwai son sanin kome ya faru dashi da kowa yaki fada mishi. Yana shiga daki, wayarshi kan gado ya jefata, nan tsakiyar dakin ya cire kayanshi yana nufar toilet. Ya jima tsaye ya sakar ma kanshi ruwa mai dumin gaske, in za'a tambaye shi bazai ce ga kalar tunanin da yake ba.

Amman sam babu nutsuwa a tattare dashi, yafi mintina sha biyar kamun ya fito daure da Towel a kugunshi, kayan daya bari ya dauka, in komai na rayuwar shi daga ciki a hargitse yake, bazai zamana har a wajen komai ya hargitse mishi ba.

Ya ninke rigar kenan yana daukar wandon kaman wanda aka dokama guduma akai ya dago yana ware idanuwanshi, gam ya runtse su yana girgiza kai. Sosai yake duba kwakwalwar shi amman ya kasa tuna komai.

"Me yake faruwa dani haka?"

Ya tambayi kanshi, zuciyarshi cike da tsoro, ko a cikin kanshi bayason maimaita abinda zuciyarshi take zargi, yasan inya tsaya dakin shi kadai abinda duk bayason yai tunani shi zaiyi. A gaggauce yasaka boxers dinshi da singlet yana fita daga dakin.

Badan yasan inda zaije ba, zuciyarshi ya bama ragamar gangar jikinshi, sai ganin kanshi yayi kofar dakin Tasneem. Kamun ya sake tunani yakai hannu yana murda handle din hadi da turawa. Kan gado ya hangota a kwance, dan haka ya qarasa shiga gabaki daya yana tura kofar ya kulle dakin.

Har kan gadon ya karasa, hasken da yake gauraye da dakin na bashi damar ganin fuskarta, zuciyarshi ta matse waje daya, dan ko motsawa batai ba ballantana tai kokarin boye mishi hawayen dake bin fuskarta suna jiqa pillow din da kanta yake a sama.

"Neem..."

Ya kira muryarshi can kasa, idanuwanta kawai ta motsa tana sauke su akan shi.

"Ban san me yake damuna ba..."

Ya fada muryarshi cike da wani irin yanayi da yasa Tasneem jin kamar takai hannu ta tallabi fuskarshi, sai dai batason ya tashi ya fita, karshen lokacin datai kokarin taba shi, bar mata wajen yayi. Dan haka jikinta taja tana matsawa sosai hadi da bubbuga mishi kan gadon cike da alamar cewar ya kwanta.

Sosai yake kallon wajen kamar yana so ya gano ko akwai wani abin cutarwa. Kamun a hankali ya maida dubanshi kan Tasneem din. Baisan me yake ji ba, baisan kalar tunanin daya kamata yayi ba. Kafafuwan shi yaja yana maida su kan gadon ya kwanta.

Jin shi gab da ita sosai yasa Tasneem matsawa, ko kadan bata son kara mishi damuwa, bata son saka shi cikin yanayi fiye da wanda take gani akan fuskarshi. Ga mamakinta hannun shi ya mika mata, cikin da shakku ta kama hannun tana shirin matsowa.

"No please..."

Rafiq ya fadi da sauri yana dumtse hannunta dake cikin nashi. Runtsa idanuwanshi yayi yana son kauda hotunan Tasneem da wasu dake mishi yawo, ga wani irin azababben kishi daya taso mishi yana barazanar sa numfashin shi ya tsaya.

"Sugar..."

Tasneem ta kira shi muryarta na rawa, har lokacin idanuwanshi a runtse suke gam. Sam baya son ya bude su ya kalle ta. Sosai kirjinta yake zafi, tana jin wani abu na tattarowa daga zuciyarta dake ciwo zuwa makoshin ta yana hana mata wucewar numfashi yanda ya kamata, hakan bai barta da wani zabi daya wuce soma tari ba.

Sosai tarin yake sarqe ta har dukkan jikinta na amsawa. Bude ido Rafiq yayi yana kallon yanda a tare da tarin Tasneem na kokawa da dai-daituwar numfashin ta, hannunta ta zame daga cikin nashi tana ci gaba da tarin.

Sauka yayi daga kan gadon, da alama bata ma kula ba, cikin sauri ya fita zuwa kitchen, yana dawowa da cup din ruwa, lokacin daya shigo tarin ya soma tsagaita mata. Mika mata Cup din yayi, ta tashi zaune tana kawo hannu dan ta karba.

Sai dai yaki sakin Cup din, nazarin fuskarta yake tashi a daqune. Yanayin dake cikin idanuwanshi ya sata fadin

"Menene?"

Dayan hannun shi da baya riqe da Cup din ya miqa zuwa labbanta, yana son dangwalo abinda yake gani a gefen bakinta, yana son tabbatar ma zuciyarshi abinda yake gani. Dangwalowa yayi ya kawo dan yatsan shi zuwa dubanshi, zuciyarshi na wata irin dokawa kamar zata fito daga kirjinshi.

Jini ne, sake kallonta yayi, kamun ya kalli hannun data miqo ta karbi ruwan, babu shiri ya ajiye Cup din a kasa yana hawa kan gadon sosai ya zauna.

"Sugar..."

Tasneem ta fara dan ta fahimci abin da yasa yake mata kallon nan yanzun. Kai kawai ya girgiza mata alamar bayason jin koma menene zata fada. Idanuwanta cike taf da sabbin hawaye tai shiru. Duka hannayenta ya kamo cikin nashi yana bude tafukansu. Tsilli-tsillin jini ne a jikin su dan tai amfani dasu ta rufe bakinta lokacin da take tari.

Fuskarta ya sake kallo, akwai wani baqi kasan idanuwanta dake nuna alamar rashin wadataccen bacci, ga wata irin ramewa datai, a cikin idanuwanta yake ganin alamar bata da lafiya. Hannuwanta ya saki, yana maida nashi jikin fuskarta. Sosai yake feeling din fuskar cikin hannuwanshi zuwa wuyanta.

Zuciyarshi na kara shiga yanayi da jin yanda jikinta yake ruf da wani irin zazzabi. Ya fara jin rashin kyautawarshi na rufe shi tun kamun zuciyarshi ta fada mishi.

"Tun yaushe ne baki da lafiya? Tasneem tun yaushe? Me yasa baki fadamun ba?"

Bata san yanayin sanyin dake muryarshi bane ko kuma son da zuciyarta take nason ya sake nuna mata kulawa komun kankantarta bane yasa wani irin kuka kwace mata. Hannuwanshi dake kan fuskarta ta riqe dam da nata, tana ci gaba da wani kuka marar sauti da yake fitowa daga ko ina na jikinta.

"Tarin jini kike...kina karkashin kulawata ban sani ba... In wani abu ya sameki ta ina kike so in fara yafe ma kaina? Abinda kikaimun bai isheki ba Neem?"

Rafiq yake fadi yana jin ta ko ina duniyar ta hade mishi waje daya. Yana kasa sanin yanayin da yake ji, dan bashi da kalaman da zasu dace da abinda yake ji. Tarin jini, baya son fara tunanin kome hakan yake nufi. Sakin fuskarta yayi, yana sauka daga kan gadon hadi da kama hannunta ya dago da ita.

Har lokacin bata daina kukan da take ba, shine cikin yanayi amman ita take kuka, ita take samun sauqi ta hanyar rage wani abin da zubar hawayenta. Inda yasan ta inda zai fara da yayi kukan shima kozai samu sauqi.

"Ina hijab dinki?"

Ya bukata, ta kasa samun kalamai saboda kukan da take balle ta amsa shi. Numfashi mai nauyi ya sauke yana fuskantarta. Ya rasa kome zaice mata, kanshi yake ji kaman zai tarwatse saboda tunaninka da sukai mishi yawa a ciki.

Space din dake tsakanin su ya hade yana dora hannuwanshi kan kafadunta, taqi dago fuskarta, kukanta kawai take, rigar dake tsakanin hannuwanshi da kafadunta bai hana shi jin zafin zazzabin da take ba. Habarshi ya dora saman kanta yana runtse idanuwanshi gam. Muryar shi can kasan makoshi yace

"Ya kike so inyi? Na dauka aurenki zai dai-dai tamun rayuwa ta wani fannin... Na dauka ko ba komai zuciyata zata samu farin ciki..."

Maganganun shi da kusancin shi da ita na kara mata yanayin da take ciki.

"Zuciyata na ciwo... So... Sosai zuciyata na ciwo Sugar"

Tasneem ta fadi wani irin kuka na kwace mata, sakin ta Rafiq yayi, yana da tabbacin zuciyarshi tafi tata ciwo. Sakinta da yayi ya bata damar kallon fuskarshi. Saida ta goge fuskarta da hannu, duk da hakan bai tsayar da hawayen da take ba.

"Dan Allah kabar asibitin sai da safe in Allah ya kaimu, bacci kawai nake sonyi"

Sosai yake kallon ta, sauke numfashi yai a gajiye, har lokacin yanajin wasu bangwaye da idanuwa basa iya gani na hade shi waje daya, numfashin da yake ja yana fitarwa kanshi a takure yake jin shi. Har kasan zuciyarshi yake fatan bazai dana sanin biye ma Tasneem da barin zuwa asibitin har safe ba.

"Ka ji..."

Ta fadi, kai ya daga mata, yana samun waje gefen gadon ya zauna, Itama karasawa tayi ta zauna gefen shi, zuciyarta na matsewa waje daya, karya matsa, ga mamakinta, kwantar da kanshi yayi a jikin kafadarta, yana sa ta juya da sauri tana kallon fuskar shi.

Jiyai wuyanshi harya soma riqewa saboda ya mata tsayi, hakan yasa shi dago wa, kafafuwanshi ya ja zuwa kan gadon, dasu yai amfani ya janyo abin rufar dake can karshe, sosai ya gyara yana rufe rabin jikin shi, batare daya kalli Tasneem dake binshi da ido ba ya zame jikin shi ya kwantar da kanshi a cinyarta yana rufe idanuwa.

"Kaina yamun nauyi, tunani yamun yawa Neem, nagaji sosai..."

Idanuwanta cike taf da hawaye ta dora hannunta akan fuskarshi. Muryarta na rawa take fadin

"Ka huta, yau kawai ka cire tunanin komai ka huta"

Tanajin ya ja wani irin numfashi yana saukewa kamun ya saki jikinshi.

"Sugar..."

Ta kira, yana jinta, bai amsa ba saboda ko motsi bayaso yayi, nutsuwa yake so ko ya take, inda zata taimaka mishi da tayi shiru. Hawayen ta tai saurin tarbewa dan karya digar mishi a fuska.

"Duk da ban cancan ci yafiyarka ba bazai hanani baka hakuri ba. Kayi hakuri... Kayi hakuri da Allah..."

"Shhhhh..... Pleasee"

Rafiq ya katse ta, baya sonji, baya sonjin komai, shirun kuwa tayi, batajin karfin jikinta, kuma bata son motsawa dankar Rafiq dayai pillow da cinyarta ya sauka, hannu takai dakyar ta dauko pillow, tana kwanciya kan bayanta, hadi da runtse idanuwanta.

Bawai bata dauka soyayyar dake tsakanin su ba zata canza a daren su na farko a matsayin ma'aurata ba, sai dai bata dauka zata yi kewar Rafiq har haka ba. Ciwon da take ji marar misaltuwa ne, ko yanzun da yake kwance a kusa da ita tana jin kewarshi. Sauke numfashi tayi tana laluba inda duk ta adana soyayyar shi dan tasan irin yau na jiranta.

*

Jingine suke jikin motarshi.

"Me yasa baka son muna zama cikin motarka? Kafafuwanka basa gajiya da tsayuwa?"

Ta tambaya tana kallon shi. Murmushi yai mata

"Nace in bude miki ki zauna, ni in tsaya a waje kin qi... Karki cemun kin gaji da tsayuwa Neem"

Shagwabe mishi fuska tayi

"Karki fara..."

"To ka fadamun ko me yasa?"

"Idon mutane, shi yasa, badan na damu dame zasu fada ba, saidan na damu da abinda zasu ce akan ki"

Numfashi ta ja tana saukewa

"Mutane na tarar ka da maganganu akaina ko?"

Ta tambaya cikin sanyin murya.

"Na yarda dake, kome zasu ce bazai canza yanda nake ji a kanki ba, ke kadai zaki iya sa hakan ya faru, karki taba bani dalilin yin dana sanin yarda dake"

Murmushi tayi tana kokarin boye yanda zuciyarta ke dokawa. Tana sa hannuwa ta goge fuskarta dan taji ta soma zufa.

"Kunshi, kinyi kunshu Neem"

Rafiq ya fadi yana murmushin da yakai har cikin idanuwan shi. Hannuwan ta sauke tana jujjuya mishi ja da baqin zanen lallen dayai matuqar yima hannuwanta kyau. Runtsa idanuwan shi yayi yana mayar da numfashi, kamun ya bude su a hankali.

"Ki mayar da hannuwanki inda bazan gansu ba"

"Me yasa?"

Ta fadi tana kara jujjuya mishi hannuwanta.

"Tasneem..."

Ya fadi muryarshi can kasan makoshi.

"Bakya sona ko?"

"Ina son ka mana"

Hararta yayi, hakan nasata yin dariya

"Kina so in aikata abinda bai kamata ba, ko in fadi abinda bai kamata kiji ba yanzun"

Hannuwanta ta mayar cikin hijab din dake jikinta. Komai na Rafiq daban yake dana sauran mazan da ta taba cin karo dasu a rayuwarta. Ita ya kamata ace tana jin kunyarshi, amman shi yake jin kunyarta. Ko tsaye suke, saiya tabbatar akwai tazara a tsakanin su.

Akan shi ta soma sanin menene son so. Menene kauna saboda Allah. Ta kula da yanda ya saka hannuwanshi cikin aljihun rigarshi, da yanda yake duk wani kokari nakin barin shaidan yai nasara wajen sashi ya riqe hannuwanta.

*

Bude idanuwanta tayi, muryarta a sanyaye, hawaye nabin gefen fuskarta take furta

"Ka yafemun Sugar, Allah ya baka karfin zuciyar yafemun, ba saika sake sona ba, ba saika sake yarda dani ba, inka yafemun zan yafe ma kaina laifin danai maka..."

Ta karasa maganar kirjinta na kara zafi kamar an kunna mata wuta a cikin shi, hakan yasata saurin runtsa idanuwanta, tana kokarin fitar da numfashi a hankali, dan hakan kamar kara mata ciwon da take ji yake yi.

**

"Majee wai har yanzun?"

Altaaf ya kwalla mata kira, dan ya rasa duminiyar da take wajen mintina ashirin, yamma na karayi. Mutuwa bata sallama ga wanda zata dauka, balle kuma makusantan shi, in ba haka ba, mai zaisa shi daukar hanyar Kaduna da yammacin nan, jikin shi ma wani iri yake jin shi.

"Yi hakuri, kayan nike ida hadawa"

Murmushi yayi yana girgiza kai, yanda hausar Majida bata daina saka shi nishadi a ko wanne hali yake ciki na bashi mamaki. Motsinta yaji, ya juya yana kallonta da doguwar hijab dinta da har kasa take ja.

Yar karamar jakar data hada musu kaya a ciki ta ajiye sai kuma wata karamar jakar daban.

"Me zakiyi da jakunkuna har biyu"

"Snacks ne na dibar maka, kar muje ko baka cin abinda suka dahwa"

Shiru yayi yana kallonta,a kana nan abubuwa irin wannan Majida kan nuna mishi yanda yau da gobe ta koya mata damuwa dashi.

"Miye kake kallona kamar baka sanni ba?"

Ta tambaya tana dakuna mishi fuskarta da tai mishi kyau. Mikewa yayi, baida kalaman da zai dora yanayin da yake ji a yanzun, dan haka baima ko gwada ba, jakunku nan duka biyun ya dauka yana nufar hanyar waje.

Majida batai mamakin shirun shi ba, inda sabo ma yanzu kam ta saba, ba komai yake da amsa a wajen Altaaf ba, in shi ya tambaya fa dole a bashi amsa, ko babu sai an nemo. Bayanshi tabi da sauri tana riqo hannun shi

"Ba

1 Comments On ALAKALAMIN KADDARA PART 1
avatar
khadija-7-4

1 year ago

Reply

Yayi

Please Login or Register in order to submit comment