Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba.

Ranar har Ummi suka rage ma abincin, dan ya musu yawa. Itama taji dadi, har fara'ar da suka jima basu gani a fuskarta ba tai musu. Baccin farin ciki sukai a nutse ranar.
**

Da duk kwanakin da zasu wuce na zamanta da Haj. A'i da yanda take karantar irin karamcin matar, kullum saita bata dari biyar in zata koma gida, ga abinci kala-kala, haka kuma in zata dafa wani abin saita saka Tasneem a gaba taga yanda tayi.

Dakin Haidar Tasneem take fara gyarawa dan duk yawancin lokuttan yana bacci, wani lokacin kuma bayama dakin. Da sauri-sauri haka zata gyara ta fito. Bata kara haduwa dashi ba, hakan kuma ya mata dadi. Kudin da Haj. A'i take bata adanawa take, kudin motar zuwa kawai take dauka Naira talatin, saiko in zasu siyi sabulun wanki.

Randa ta cika kwana talatin ba karamin aiki sukayi da safen ba. Dan Haj. A'i tace mata yaranta har su uku zasu dawo daga makaranta. Aikuwa wajen karfe sha daya Tasneem na jera kuloli a dining suka shigo da Sallamarsu. Maza biyu sai mace guda daya. Duk da ba farare bane suna da kyau sosai. Ga su tsaf-tsaf.

"Cikina har kullewa yake saboda yunwa"

Macen ta fada tana nufo dining din da Tasneem take tsaye. Kallon Tasneem tayi da a daburce tace mata

"Ina kwana. Sannu da zuwa"

Dariya yarinyar da ko zata girmi Tasneem din bazai wuce shekara uku ba.

"Sannunki da aiki, sunana Hamida"

"Tasneem"

Jinjina kai Hamida tayi tana jan kujera ta zauna.

"Tasneem..."

Ta maimaita sunan na mata dadi, plate ta janyo ta soma bude kulolin, wuce wa Tasneem tayi tana gaishe da samarin su biyu.

"Ke ni banaso ana gaishe dani, duk aita baka girma ana sa kanajin kunya"

Daya daga ciki ya fada, dayan kuma kai kawai ya daga ma Tasneem.

"Karki damu da Ahmad"

Haj. A'i ta fada da alama da wanda yai magana take. Tasneem batace komai ba ta wuce dakin datakan zauna. Tunda tagano tashar da ake Hausa bata sake taba remote din ba. Suna shirye-shirye masu dadi.

Sai wajen sha biyu da wani abu, Haj. A'i tazo tai mata magana dan a dora abincin rana. Wannan karin harda Hamida a kitchen din, sosai suke hira da Haj. A'i da yartata gwanin sha'awa. Sai suke sa Tasneem najin daman haka suke hira cikin nishadi da Ummi, kewar Abba na danne mata kirji da wani irin ciwo.

Tasneem ta fito ta ajiye jug din zobo da Hamida tayi a dining taga Haidar zaune a wajen, saida gabanta ya fadi, hannunta na rawa ta ajiye. Tanajin kallon da yake mata, da sauri tazo zata bar wajen yace

"Ke baki iya gaishe da mutane ba?"

A hankali tace

"Ina wuni?"

"Mtswww bar wajen nan"

Haidar ya fadi. Da sauri kuwa tabar wajen ba ta jira ya sake fada mata ba. Taji dadi da Hamida ta dauki sauran kayan takai ita ta tsaya wanke kwanonin da suka bata. Nata abincin taci a kitchen din ita kadai. Dan karta fito zuwa daki ta sake haduwa dashi.

Saida ta tabbatar sun gama tukunna ta fito ta wuce su a falo tana kwashe kwanonin. Tana cikin aiki a kitchen Haj. A'i ta shigo.

"Sauran abincin ki kwashe ki tafi dashi Tasneem. Ga kudin aikin ki nan, dubu goma ne saboda naji dadin yanda kike aiki babu ha'inci, koda zaki saima kannenki wani abu. Bance duk wata haka zan dinga baki ba"

Muryar Tasneem dauke da wani yanayi tace

"Wallahi sunyi yawama. Kullum saikin bani kudi, kuma kina bani abinci"

Dan murmushi Haj. A'i tayi, ta yaba da hankalin Tasneem, ta kuma sha gwadata ta fannin kudi ko abinci, har a kitchen takan ajiye kudi, amman Tasneem bata taba daukar mata ba, haka zata daga kudin ta goge wajen ta mayar dasu ta ajiye, wani lokacin har abu take sawa ta danne karsu fadi.

Haka abinci, inba wanda ta rage ba, kosu suka rage saidai ta hada waje daya, in Haj. A'i batace ta dauka ba, bata tabawa, gashi bata da karambani. Ta batane dan taga tana bukatar kudin sosai. Kuma ita macece da abinta bai rufe mata ido ba.

"Ki dauka bakomai. Kinyi wani abin dashi"

"Nagode. Allah ya kara arziqi ya baki ninkin su"

"Amin Tasneem. Zamu fita duka gidan, inkin karasa aikinki zaki iya tafiya sai gobe in Allah ya kaimu"

Jinjina kai Tasneem tayi

"Allah ya tsare hanya. Nagode"

Amsawa Haj. A'i tayi tana ficewa daga dakin. Tasneem najin fitarsu. Aikinta taci gaba dayi, gidan yayi shiru, hankalinta a kwance yake dan tasan ita kadaice a gidan. Karatun Qur'ani take a hankali wani sashi cikin Suratul-Ra'd zuciyarta na mata wani sanyi.

Sanin ita kadaice a gidan yasata sakin wata gigitaciyyar kara jin mutum a bayanta, hannu yasa yana rufe mata baki, dayan hannun kuma makale a kugunta. Da take kiciniyar kwacewa.

"Kunne zaki fasamun?"

Muryarshi ta gane, gashi dayan hannunshi da takeji kamar wuta na mata yawo a jiki, hannunshi dake bakinta ta gartsama cizo tana hankade shi, numfashi take zuciyarta kamar zata fito saboda dukan da take.

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."

Ta fadi tana kallon Haidar da ya zuba mata idanuwanshi cike da bacin rai. Nata idanuwan cike da hawaye, muryarta na rawa take fadin

"Na shiga uku, dan Allah ka rufamun asiri, karkai mun sanadin aikina. Wallahi shi kadaine hanyar abincin mu. Dan Allah ka kyaleni..."

Takowa Haidar yake tana matsawa harya hade sauran wajen dake tsakaninsu, ta makale jikinta da kantar kitchen din kamar zata koma ciki, duk addu'ar datazo bakinta take karantowa. Tana rokon Allah dayai mata katanga da Haidar dan tanason aikinta.

Hannunshi taji a fuskarta yana wasa da yatsanshi akai.

"Zaki bar gidan nan in kikai numfashi da iskar abinda ya faru a kitchen din nan kusa da Mummy balle kiyi kuskuren fada mata..."

"Wallahi bazan fada mata ba, dan Allah ka kyaleni..."

Ta fadi tana runtsa idanuwanta gam, hawaye masu dumi na zubo mata. Runtsa idanuwan dataine yabashi damar rankwafawa yana sumbatarta. Tureshi tayi tana girgiza kai, fita yayi yana dariya kasan makoshi, zamewa tayi ta zauna kasa ko ina na jikinta na bari. Tunanin karya dawo yasata saurin tashi ta karasa wanke tukunyar da takeyi tana kuka tana goge wajen.

Abincin ta dauka da kudin ta zuba duka a wata babbar leda tana ficewa. Tana tafiya tana goge hawaye. A bakin gate taga Baba Ayuba kamar yanda har Haj. A'i take kiran maigadin gidan. Ganin tana kuka yasa shi fadin.

"SubhanAllah Tasneem lafiya? Me akai miki?"

Kai kawai ta iya girgiza mishi tana bude kofar ta fice dan batasan abinda zata fada mishi ba. Ko hanya bata gani sosai saboda kukan da takeyi.

"Allah ka isarmun, Allah kaimun katanga da Haidar"

Take ta fadi harta kai kofar gida. Batada wata hanyar da zasu ci abinci, da ba zata koma gidan Haj. A'i ba, kuma batajin koda akwai wani gida, zasuyi mata irin karamcin da take mata. Koyau ba zata manta da ita ba, tunda taji zuciyarta na dokawa ko dakin Haidar ta shiga tasan babu alkhairi a tare dashi.

Ta jima kofar gida, saida ta tabbatar ta nutsu tukunna ta shiga, dan batason su Azrah su gane halin da take ciki. Amman saida Hamna ta kula.

"Kuka kikai"

Ta fadi da tabbaci a muryarta. Kai Tasneem ta daga mata a hankali.

"Nayi kewar Abba ne"

"Kullum sai inga kamar zanga shigowarshi, sai Ummi ta dawo ta tunamun ya mutu baibar mana komai ba tukunna..."

Hamna ta fadi da wani yanayi mai nauyi a muryarta. Muryar Tasneem din na rawa tace

"Karki bar maganganun Ummi a zuciyarki, tana fadane saboda hidima tai mata yawa. Kuma babu mai taimaka mata shisa..."

Shiru Hamna tayi, dan batason gardama kan abinda ba zata iya canzawa ba, baida amfani a wajenta. Ummi na goranta musune badan hidima tai mata yawa ba, in akwai wanda hidima taima yawa Tasneem ce, ita take kula dasu har Ummi din, har kudi tanaba Ummi, Hamna na kula.

Dubu biyu taba Ummi cikin kudin, aikam tasha albarka kamar me, suna kwance a daki da daddare Hamna tace mata

"Yaya Tariq shiru, tun ran Arbai'in din Abba"

Gyara kwanciya Tasneem tayi, magana ne batayi, amman shirun Tariq na ci mata rai sosai.

"Ya dade fiye da ko yaushe wannan karin"

Hamna ta sake fadi

"Yana lafiya. In shaa Allah yana lafiya"

Tasneem ta fadi tana son gamsar da kanta Tariq din yana lafiya, fiye da yanda takeson gamsar da Hamna.

"Allah yasa. Shirun yayi yawa, sosai"

"Satin nan zaku koma makaranta. Harda Sabeena in shaa Allah"

Ta fadi tana canza maganar, tana da abubuwa da yawa a zuciyarta yau, ba saita kara da damuwar Tariq ba. Ya saba kula da kanshi, wannan karin ma tasan zai kula da kanshi kamar koda yaushe. In abubuwa sukai mishi sauqi zai waiwaye su, yasan inda suke, zaizo da kanshi.

"Ba'a dinka mata uniform ba"

Azrah ta fadi

"In na dawo daga aiki gobe in shaa Allah, zan tambayi Haj. Sai in dawo da wuri inta barni..."

"Allah ya kaimu"

"Amin Hamna. Kuma zan siyo muku takalman makaranta da litattafai"

Kai Hamna ta daga. Kamun can tace

"Ya Tasneem?"

"Umm"

Tasneem ta amsa mata.

"Rayuwar mu zatai wahala sosai da bakya nan. Kinsani ko?"

Murmushi Tasneem tayi tana juyawa ta fuskanci Hamna dan ita da Sabeena ne suka sakata tsakiya.

"Nima tawa rayuwar ba zatai dadi ba inda bakwa ciki Hamna"

"Saida safe. Mungode dakomai. Allah ya biyaki"

"Amin. Allah ya tashemu lafiya"

Shiru tayi tana jin Hamna tayi addu'a ta juya kwanciyarta. Su dukansu sunyi bacci banda ita. Koya ta runtsa idanuwanta sai taga kamar Haidar zai shigone, zuciyarta dokawa take, sam ta kasa samun wani baccin kirki.

Ganin sai juye-juye take yasata tashi ta fita tayo alwala. Tunani bazai amfaneta da komai ba, Allah ne kawai zai iya share mata kukanta. Dan haka Sallah ta fara tana wani irin kuka, batason maraici yakaita inda yakai su Tariq.

Bataso Haidar ya shiga tsakaninta da hanya daya da take samu ta kula da kannenta. Dan haka kwana tayi tana hadashi da Allah dayai mata maganinshi. Ya kawo mata mafita, nan kan dardumar bacci ya dauketa...!
[11/30, 10:18 PM] LubnaSufyan: ®
📖✏
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION

LubnaSufyan
Calmlubna@gmail.com

Alkalamin Kaddara

07

Da faduwar gaba take zuwa gidan Haj. A'i harta gama aikinta, hankalinta baya kwanciya sai ta ganta a gida tukunna. In akwai abinda yake bata karfin gwiwar zuwa aikinta a kullum bai wuce ganin su Azrah sun koma makaranta ba. Musamman saka Sabeena, da murmushi a fuskarta take tafiya wajen aiki kullum da safe idan ta barsu suna shiryawa.

Wajen sati biyu bata sake haduwa da Haidar ba, sauran yaran Hajiya A'i nada kirki matuka kamar mahaifiyarsu. Haka zasu dauki kudi su bata lokutta da dama. Kuma basu taba sa taji kamar tana kasa dasu ba, in sunzo waje sun riga ganinta suna fara mata magana. Hamida har kaya ta bata sunfi kala goma, masu kyau da doguwar riga sabuwa.

Yau ma kamar kullum tazo yin aikinta, sallama kawai tayi badan tasa ran wani zai amsa mata ba, tasan bacci sukeyi. Dan haka ta shiga shararta, saida tagama share falon tas, tukunna ta nufi dakin Haidar, tasan bacci yake, a hankali ta tura kofar sanin a bude take, shiga tayi yana kwance falo kan doguwar kujera inda yawanci duk nan take samunshi yana bacci, sau daya ta taba ganinshi a kan gadonshi da safe.

Share falon tayi nan da nan, da yake bashida wani datti, ta goge, ta shiga dakin baccin shi, kayan daya cire ta fara tattarawa gefe, tukunna ta soma sharewa, zuciyarta taji tana shirin fadowa daga kirjinta da taji an turo kofar, kamun ta dago kuma an maida an kulle. Jikinta na bari ta dago dakai tana kallonshi.

Daga shi sai singlet da karamin wando a jikinshi, ya hade bayanshi da kofar yana kallonta kamar bashida wani muhimmin abu dazai yi daya wuce kallon nata. Sun dauki lokaci a haka, Tasneem na tsanar hawayen dayake taruwa cikin idanuwanta. Kayan wankin data dauke a kasa ta tattara tana riqewa a dayan hannunta.

"Zan wuce"

Ta fadi daga nan inda take tsaye, tana mamakin yanda muryarta ta fito da kwarin da bataji a zuciyarta. Ganin ko motsi baiyi ba ballantana ya nuna yaji maganar da tayine yasa ta fara takawa a hankali harta kusan gab dashi.

"Zan wuce"

Ta sake maimaitawa. Numfashi ya sauke yana mata wani irin kallo.

"Ya kike so inyi? Tunda sassafe na shigo dakina kina ciki?"

Makoshinta da taji ya bushe yasata hadiyar wani yawu kamun tace

"Shara nayi. Kayi hakuri"

Raba jikinshi yayi da kofar a kasalance yana matsawa gefe. Zuwa tayi ta rabashi tana budewa ta wuce, da gudu ta karasa ficewa daga falonshi, saida taganta a wajen dakin tukunna ta tuna ta manta mopper, da gudu ta sake shiga ta dauka ta fito, bama ya cikin falon.

Daga nan kitchen ta nufa, aikinta ya rage yawa tun zuwansu Hamida, su duka ukkun basa son tana share musu dakuna. Da kansu sukeyin abinsu. Garama Ahmad wani lokaci in zai fita zaice mata ta fito da kayan wankin shi daga daki. Shima saiya hada da Allah kamar alfarma zatai mishi ba aikinta ba.

Batasan me za'ayi ba da safe, dan haka tana gama gyara kitchen din ta koma daki ta kwanta itama. Bacci ne ya dauketa mai karfin gaske, dan har saida Haj. A'i tazo ta tasheta tukunna.

"Ki soya dankali da kwai Tasneem, ki hada da plantain. Zanje gaisuwa kauye yau. Hamida zata fada miki kome suke so da rana saiki tayata ku girka"

"In shaa Allah. Allah ya jikan musulmi ya kyautata namu karshen"

Ta fadi a sanyaye. Hajiya A'i ta amsa da amin tana ficewa daga kitchen din. Dayake Tasneem bata da nawar aiki suyar dankali ce kawai ta daukar mata lokaci. Haka tagama aikinta tsaf sannan ma Hamida ta sauko. Dayake takai musu nasu dining area, cup din shayinta ta dauka da nata plate din tayi daki.

*

Dambun shinkafa sukai da rana ita da Hamida, ko tace rabin aikin ma Hamida tayi dan hardasu hanta aka saka a ciki, bata taba ganin dambu irin haka ba. Sannan miyar yankakkun kayan miya Hamida tayi, ta hada Zobo dan Tasneem na kula da Hamida bata cika shan lemukan gwangwani kona kwalaye ba. Zobo take dafawa ta hada abinta.

Sosai dambun yaima Tasneem dadi. Harta kosa taje gida dan takaima su Hamna suma suci. Wanke wanke take tana shan Zobonta da Hamida ta cika mata wani babban cup dashi, harma ya huce, dan ta cika cikinta da dambun shinkafar. Fitsarin daya kamata yasata tsame hannunta daga ruwan wanke-wanken zuwa daki.

Gidan yayi shiru, tasan daga ita sai Hamida, su Ahmad sun ficewarsu. Hamida kuma na dakinta. Sanda ta dawo kitchen din tana daukar cup din zobon gabanta yai wata mummunar faduwa.

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."

Ta fadi da sauri tana dafa kantar kitchen din ko zuciyarta zata rage dukan da take a kirjinta da sauri-sauri. Zobon ta daga tana shanyewa duka ta ajiye cup din, jin zuciyarta bata daina faduwa ba yasata ci gaba da wanke-wanken da take. Saidai kamun ta karasa jikinta ya mata nauyi. Dakyar take motsa duk wata gaba ta jikinta.

Hakan ba karamin tsoro ya bata ba, bakuma tajin alamar rashin lafiya, kawai jikinta ne yai mugun nauyi, idanuwanta dakyar take dagasu. Ko goge wajen batai ba. Tana dafa bango tagano daki dakyar, tana shiga kamun ta karasa wajen gado kafafuwanta sun mata sanyi, babu shiri ta zauna a kasa, tanajin dakin na mata wani iri.

Nan kan kafet ta kwanta ta rufe idanuwanta, kamun taji kamar hakan jikinta yakeso daman. Can wata duniya daban taji kamar an shigo dakin, a duniyar kuma taji kamar an dagata cak daga kasa zuwa kan gado. Saidai bata gama fahimtar mafarki take kome ba, wani irin duhu ya mamaye mata duniyar gabaki daya.

*

Saloon Hamida zataje, dan haka ta fito, tanason cema Tasneem ta tafi gida kawai. Tasan su Ahmad abincin ranar ne zai zame musu na dare. Inma ba zasuci ba sun fita su dukansu suci wani abun a waje. Amman kitso take son zuwa ita kam.

Batai tunanin kwankwasawa ba, Sallama kawai tayi tana turawa. Wayar da take hannunta da mukullin mota suka subuce suna faduwa.

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."

Hamida ta fadi hankalinta a tashe, idanuwanta kamar zasu fito kasa, ga wani irin juyawa da cikinta yake saboda tashin hankalin ganin Haidar na daura belt a kugunshi, ga Tasneem kwance cikin mummunan yanayi, da alama batama san duniyar da take ba.

"Yaya... Inalillahi wa ina ilaihi raji'un, Yaya me kayi? Me kai mata? Na shiga uku Yaya... Ka kasheta ko?"

Hamida take fadi tana karasawa kan gadon gefen Tasneem wani irin kuka na kwace mata, hannu takai ta fara gyara mata zaninta tukunna ta soma jijjigata cikin tashin hankali.

"Tasneem...Tasneem!"

Take fadi amman ko dan yatsa Tasneem bata motsa ba ballantana tasan inda kanta yake. Juyowa Hamida tayi da idanuwanta da harsun yi ja saboda kuka da tashin hankali tana kallon Haidar dake tsaye bai motsa daga inda yake ba. Sosai take kallonshi tana neman kusancin da take dashi na yan uwantaka amman ta rasa a wannan lokacin.

Mikewa tayi tana karasawa inda yake, mari ta dauke shi dashi tana cakumar wuyan rigarshi. Jijjigashi take

"Kacemun bakai mata komai ba Yaya. Kacemun baka bata mata rayuwa ba. Yaya kace baka cuceta ka cucemu gabaki dayaba... Wallahi na tsaneka..."

Hannuwan Hamida ya kama yana banbarewa daga jikinshi. Babu alamar danasani ko nadamar abinda ya aikata yace

"Kina cikamun kunne da ihu, babu abinda zata tuna inta tashi..."

Cike da rashin yarda Hamida ke kallonshi, ta kasa yarda da abinda kunnenta yake jiye mata, hannu ta daga batama san abinda zatai mishi ba, ya riqe yana dauketa da marin da saida taga haske na gilma mata, da baya riqe da ita saita fadi, bata garma wartsakewa ba ya sake dauketa da wani mari wannan karin tana jin iska ta daina zuwa mata a bangaren fuskarta. Runtsa idanuwanta take tana budesu da sauri da sauri dan ta dauka dayan idon ma ya fadi saboda azabar da take ji.

"Kin mantani ko? Dan ina zama waje daya daku yasa kike neman rainani. Ni sa'anki ne da zaki dagamun hannu Hamida?"

Kai take girgiza mishi jikinta ko ina na kyarma, dama can suna tsoron Haidar, ballantana yanzun dataga asalin rashin imanin shi. Bawai labari aka bata ba. Abinda take gani cikin idanuwanshi yagama tsoratata.

"In Hajiya taji maganar nan saina danne kanki da pillow kina bacci, kinjini ko?"

Ya fadi yana girgizata. In hankalinta yai dubu yagama tashi, tsoronshi takeji har cikin kasusuwan jikinta. Ta tabbata zai iya din, kasheta zaiyi inta fada, kai kawai take iya daga mishi. Saida ya kara mata wani marin tukunna ya saketa yana ficewa yabarta nan durkushe. Kuka take kamar ranta zai fita, ko ina na jikinta kyarma yake.

So take idan mugun mafarkine takeyi haka ta farka, ko zata samu tayi sadaka Allah ya nisanta mata sharrin dake ciki. Amman ta ki farkawa. Takuma kasa fita daga dakin. Tsoron fita daga dakin takeji ko Haidar na waje yana jiranta. Har ruwa ta shiga bandaki ta dibo ta shafama Tasneem amman bata tashi ba.

Sai da ta kula tana numfashi a hankali tukunna ta tabbatar Haidar bai aikata kisan kaiba. Nan ta zauna da Tasneem din, ko Sallar Asr ta kasa tashi tayi tanajin aka kira, amman ta kasa tashi. Tasneem bata motsa ba sai wajen karfe shidda saura. Kanta takejin ya mata wani dum.

Kamun ta motsa jikinta taji wani irin canji har cikin zuciyarta. Wayam takejin cikin kanta, bata iya tuna komai banda barin kitchen zuwa daki, amman basai wani ya fada mata wani abu ya faru da itaba. Sosai ta bude idanuwanta jin kamar ana kuka. Juyawa tayi tana kallon Hamida, ganinta a gefenta yasata tashi da zaune da sauri, kanta take kallo da yanayin jikinta.

Wani bangarene na zuciyarta taji yana bushewa a hankali. Ganin kukan Hamida daya tsananta yasa Tasneem fadin

"Wani abu ya sameni ko Hamida?"

Hamida bata iya cewa komai ba, sai kukanta daya tsananta.

"Haidar yaimun wani abu"

Tasneem ta sake fadi muryarta babu alamar komai. Hamida na daga mata kai taji bangaren ya karasa bushewa a zuciyarta. Hawaye ko alamunshi bataji ba. Kawai duniyar ce tai mata wayam. Bata sake jin rayuwa tazo mata karshe ba saida ta sakko daga kan gadon ta mike tsaye tukunna. Zaninta ta kwance daga baya tana gyara daurinshi. Amman ji take kamar bata dauraba ma.

"Tasneem..."

Hamida ta kira cikin kuka. Batako juyo ba ballantana, hanyar kofa ta nufa ta bude tana ficewa. Batasan kafafuwanta na daukarta zuwa bangaren Haidar ba saida taganta cikin dakinshi. Yana zaune a falo yana kallo. Ganinta tsaye yasa shi maida hankalinshi kanta. Cikin idanuwa take kallonshi, tana barin zuciyarta daukar hotunanshi da wani irin kuna.

"Ka rabani da duk wani mutunci da mace take tinkaho dashi. Nasan kuma bani bace ta farko, bakuma lallai in zama ta karshe ba. Amman Allah bazai barka ba Haidar"

Tana karasawa ta juya tana ja mishi kofar. A tsakiyar falon taci karo da Haj. A'i. Da mamaki Hajiya take kallonta.

"Tasneem yau kinyi yamma..."

Kallonta Tasneem tayi, yanayin dake fuskarta yasa Haj. A'i fadin

"Tasneem? Lafiya?"

"Zan fita daga gidan nan saboda banda karfin fada daku, ko ina dashi babu wani dan adam dazai iya hukuntaku yanda nake so. Allah ne kawai zai hukunta ku, zan bar komai a hannunshi..."

"Tasneem me..."

Haj. A'i ta fara Tasneem na katseta ta hanyar daga mata hannu.

"Ki daina mun magana kamar bakisan laifukan da Haidar yake aikatawa kina kauda kaiba. Kirkin ki bazai wanke yanda kike kauda kai daga barnar da yakeyi ba. Karki ban hakuri, karkiyi kokarin bina ko nemoni"

Tasneem ta karasa tana raba Haj. A'i da ta kasa cewa komai ta fice daga dakin. Harta fita daga gidan komai wayam takejin shi a rayuwarta. Duk da akwai kudi a jikinta da kafafuwanta takai gida batare da taji gajiyar komai ba. Azrah ta amsa mata sallamar da tayi

"Ya Tasneem hankalinmu ya tashi. Baki dawo da wuri ba yau..."

Fuskarta Hamna take kallo, yanayin ta kawai ya nuna ma Hamna akwai wani abu daya faru daya girmi tunaninsu duka.

"Meya faru?"

Hamna ta tambayeta muryarta can kasan makoshi. Kallon su Tasneem tayi su dukansu, tanajin yanda babu abinda ya rage mata a rayuwarta daya rage su, Haidar ya kunna ma darajarta wuta batare da tasan meya faru ba, sai tokar ta farka tagani.

"Nabar aikina"

Shiru suka danyi nawani lokaci kamun Hamna tace

"Allah ya musanya miki da alkhairi"

"Wani abin ne ya faru?"

Azrah ta tambaya ita kuma tanajin babu dadi kodan yanayin Tasneem din da take gani.

"Koba abinda ya faru tunda tace tabari akwai dalili"

Hamna ta fadi a dakile, jinjina kai Azrah tayi

"Hakane. Allah ya musanya mata da alkhairi"

"Amin"

Hamna ta fadi, saidai Tasneem batace musu komai ba. Wajen ruwa ta nufa ta dauki babban bokiti ta shiga bandaki. Wanka ta farayi dan ta tsarkake daudar da takeji manne da jikinta duk da batasan lokacin da ta manne mata ba. Tukunna tasa sabulu ta sake wanke jikinta, bata wani dirje ba, dan hannuwan Haidar ba a wajen fatarta suke ba, sam batajin su, cikin tsokarta take jinsu, ba kuma zata iya bare fatar saman ta wanke ba.

Dan haka tabarshi kawai. Wankan da za'aima gawarta ne kawai zai wanke mata abinda takeji. Data fito alwala ta sakeyi, suma su Hamna ta shiga daki. Sallar Asr ta farayi tukunna ta mayar da Maghrib. Da kanta ta dauki kudi ta fita ta siyo musu biredi da shayi ta dawo. Tana shane kawai dan tasan ko kowa yasha in har ita batasha ba Hamna ba zata saka a cikinta ba.

A daki sukai sallar isha'i suka kwanta danko hira basayi. Suna jin Sallamar Ummi ta dawo gidan. Saida zuciyar Tasneem ta sake dagulewa dajin muryar Ummi.

"Tasneem!"

Ta kira jin basu fito ba. Tashi Tasneem tayi tana fita tsakar gidan. Ummi na washe baki take fadin

"Yau me aka samo mana gidan Hajiya?"

"Ba abinda na samo"

Tasneem ta fadi muryarta a dake. Sai yanzun take auna abubuwan da rashin aikinta zai janyo. Tun dazun wayam takeji a duka duniyar, dole tai tunanin wani abu kamun Ummi ta hargitsa rayuwar su Azrah, dan ita batajin akwai wani abu dazai sake hargitsa ta banda wanda ya faru da ita yau.

"To. Garin yaya kuma? Kinsan yunwar da nakeji kuwa?"

Kallonta Tasneem tayi

"Nabar aikin ne duka Ummi"

Cike da mamaki Ummi take kallonta

"Wanne irin kinbar aiki? Akan wanne dalili? Korarki sukai? Me kikai musu Tasneem? Duk abinda matar nan take miki saida kika nuna mata bakin hali irin na Ubanki"

Wani abune ya taso tun daga dan yatsan Tasneem na kafa zuwa ko ina na jikinta

1 Comments On ALAKALAMIN KADDARA PART 1
avatar
khadija-7-4

1 year ago

Reply

Yayi

Please Login or Register in order to submit comment