Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rana mai zafi wajen dawowarsu. Dan sanyin bawai ya zauna bane sosai. Radio suke ji ita da Sabeena har bacci ya dauke su.

Ji tayi ana sallama sama-sama kamar cikin mafarki. Bude idanuwa tayi jin an sake sallamar kuma kamar muryar Abba. Da sauri ta mike tana fitowa. Abba ne ya dawo, bata damu da girman datai ba, batama san lokacin da ta ruga da gudu tana fadawa jikin Abban ba. Wata irin kewarshi na danneta duk da gashi tsaye a gabanta.

Dariya Abba yayi yana dago ta. Idanuwanta cike taf da hawayen da suka samu zubowa tace

"Abba... Sannu da zuwa"

"Menene na kukan kuma Tasneem? Bagani na dawo ba"

Abba ya fadi yana jin zuciyarshi tayi nauyi, yasan bazai wuce matsalar Ummi ba, yana can amman hankalinshi gabaki daya yana wajen tunanin halin da suke ciki. Bawai sun gama aikin bane ba. Ya dawo ne da karfinshi dan yabar musu abinda zasuci saiya koma.

"Zoki tayani dibo kaya a waje"

Da gudu ta koma daki ta dauko Hijab ta rufama Abba baya. Buhun shinkafa ne karami, taliya da macaroni sai mai a galan har biyu daya manja daya na kuli sai ledoji da Tasneem ba zatace komeye a ciki ba. Amman bakinta yaki rufuwa.

Suna gama shigo da kayan duka Abba yace ma Tasneem

"Ina kuka siyo gawayi? Ko rabin buhun a siyo a ajiye an huta da siyan kadan-kadan"

"Nan baya wajen Salihu yafi kyau Abba"

Juyawa yai da niyyar fita Tasneem tace

"Daka huta Abba, yanzun ka dawo fa"

"A'a Tasneem kinsan halin Ummin ku, kamun ta dawo gara duk abinda ake bukata in siyo"

Addu'a tai mishi, ya amsa yana ficewa, zama Tasneem tayi ta tisa kayan a gaba tana kallo ranta na mata dadi, rabon dataga buhun shinkafa saidai ko in taje shago awo, amman yau gashi a gidansu. A matsayin nasu.

"Dukkan sharri Allah ya nisanta mana kai dashi Abba"

Ta tsinci kanta da fadi. Abba bai jimaba ya dawo, sai lokacin ta lura da har kiba yayi, ya sake, wadata dabance, ta kuma fi alaqanta kibar da yayi da rashin ganin Ummi. Ruwa takai mishi dan ya watsa ko zaiji dadi, ta tattara kayayyakin daya kawo tana kai wasu kitchen ta samar musu wajen zama. Wasu kuma takai dakin su.

Harda kalanzir Abba ya siyo musu dan karamin galan, dan haka yau gawayin yai mata saurin kamawa. Ruwa ta dora da niyyar macaroni zasuci ranar ta manta rabon da suci ta. Abba na fitowa ya nufi dakinsu yaganshi a kulle. Tabarma Tasneem ta shimfida mishi suka zauna. A nutse ya kalleta

"Ya kuke? Me yasa bakije makaranta ba yau"

"Babu wanda zai zauna da Beena. Muna lafiya Abba. Ya aiki? Ka dade sosai"

Jinjina kai yayi

"Nasani, wallahi kuna raina, bama mugama aikin ba na dawo dan inga halin da kuke ciki"

"Allah ya taimaka ya kara wadata Abba"

"Amin thumma amin. Allah yai miki albarka keda sauran yan uwanki"

Murmushi tayi

"Amin Ya Rabb..."

"Ayo cefane ko?"

Girgiza kai tayi, dan mansu na shafawa ya kare, ga sanyi fata da mai ma ya ta kare.

"A'a Abba muna da sauran yaji, gara ayi wani abu da kudin dai. Muna bukatar man shafawa ma..."

Jin tayi shiru yasa Abba fadin

"Dame kuma kuke bukata?"

Girgiza kai Tasneem tayi, badan babu abinda suke bukatar ba. Sai dan batason dorama Abba wani nauyin, tasan siyayyar da yayi nada yawa kuma ba karamin kudi bane ba. Hannu yasa a Aljihunshi ya zaro duka kudin da suka rage mishi ya kirga. Dubu sha uku ne.

Dubu biyar ya ware daga ciki ya mikama Tasneem da fadin.

"Duk wani abu da bakuda shi ki sai muku"

Ware idanuwa Tasneem tayi

"Abba sunyi yawa.... Kaima ka siyi wani abin. Kuma kace zaku koma wajen aiki, kudin motar komawa"

Murmushi Abba yayi.

"Da Alhaji zamu koma jibi in shaa Allah. Shima yazo yaga nashi iyalan. Kedai ki dauka kije ki sissiyo muku"

Cike da nauyin zuciya tasa hannu ta dauki kudin. Hira suke da Abba harta karasa girkin, ta zuba mishi.

"Abba in Allah ya hore, in za'a koma hutun gaba tunda na karshen zangone a saka Sabeena ma"

"Kamar kin shiga zuciyata. In shaa Allah in na dawo zamuje a siyo uniform harku ma a sake muku naku"

Jinjina kai tayi tana mikewa. Ita da Sabeena suka fita. Man shafawa ta siyo musu, sai takalma silifas dan ba karamin jin jiki nasu sukai ba. Musamman na Hamna da dinki yafi biyar a jikinshi. Hancin takalmin ma dabanne aka samu aka saka. Biscuit ta saima Sabeena duk da tasan karshema baci zatai ba. Dan kayan zaki bai dami yarinyar ba sam.

Ko dubu daya bata kashe ba. Suka dawo. Daki ta shiga ta boye sauran kudin. Ta nunama ma Abba abinda ya siyo musu. Albarka ya samata tukunna ya fice daga gidan. Tsakar gida sukai kwanciyarsu ita da Sabeena, tana biyema shirmen hirarta har bacci ya sake daukarsu.

*

Abincin su suka kara ci sukai Sallar isha'i, dayake akwai wuta, suna zaune tsakar gida suna hira abinsu

"Wallahi Abba kamar karka koma, munyi kewarka sosai"

Cewar Azrah. Murmushi Abba yayi

"Nima nayi kewarku. Amman aiki ne dole in koma"

"Yaushe zaka dawo inka tafi?"

Hamna da sai lokacin ta tsoma baki cikin hirar sa suke ta tambaya.

"Bansani ba, amman in shaa Allah dana samu lokaci kamar yanzun zan dawo inganku"

Jinjina kai Hamna tayi tana mayar da hankalinta kan Tasneem.

"So nake fa ki tunamun wasu abubuwa a Umdatul Ahkam, zamuyi test gobe in Allah ya kaimu"

"Wai Hamna, dauko muga Allah yasa ban manta ba nima. Yaushe rabo, in na kasa Azrah saita tuna miki"

Mikewa Hamna tayi ta shiga daki, Abba kallon su yake cike da kaunarsu, da yanda rashin wadatarshi bai hanasu maida hankali a karatunsu ba. Hamna na fitowa Ummi na shigowa da Sallama. Abba ne ya amsa mata. Su dukkan su fuskokinsu babu alamar murna da ganinta.

"Ka tuna kana da iyali kenan ka waiwaye mu"

Ummi ta fadi tana kallon Abba cike da takaici. Kai kawai ya girgiza baice mata komai ba. Karasawa tayi cikin gidan ta ajiye jakarta da wani buhu dayaji duniya. Dakinta ta bude ta daga labulen tana jefa Hijab dinta ciki. Kanta tsaye kitchen ta nufa ta leqa.

Kayan abinci tagani da gawayin daya siyo duk a ajiye. In ranta yai dubu ya baci, saboda bataga dalilin dazai sa Abba ya kwaso kayan nan ba, kamata yayi ya bata kudin abinda taga dama ta siyo.

"Kudin daka samo dinne ka kaso haka? Saboda bakin cikin karka bani in karu? Shisa kaje ka kashe su haka ko?"

Kallonta Abba yayi, muryarshi dauke da wani yanayi yace

"Kayan abincin dana siyo ne laifi Bara'atu?"

"Ni bance laifi bane ba, amman ai bakasan me muke bukata ba, koda zaka siyo saika bari in dawo in lissafa tukunna, satinka nawa baka gidan, meka barmun? Kasan yanda muke muna ci a gidan nan?"

Hawaye ne cike da idanuwan Tasneem, ji take kamar kasa ta tsage ta shige ciki ko kuma wani abin ya toshe mata kunnuwanta daga jin abubuwan da Ummi take fadama Abba. Azrah ma ji take daman Ummin bata dawo ba, suna cikin nishadin su tazo ta dagula musu komai.

"Ni dai na riga na siyo. Yanzun magana ta kare ai"

Tafa hannuwa Ummi tayi da fadin

"Lallai, ai wallahi yanzun aka fara magana, dan kudi zaka bani, akwai abubuwan da nake bukata da yawa"

Hannu Abba yasa a aljihunshi ya zaro sauran kudin da suka rage, duka yai niyyar bata, amman kamun ya mika mata ta warce kudin tana dunkule su a hannunta. Bude baki Abba yayi da niyyar magana, ganin yanda su Azrah suke kallon Ummin yasa shi fasawa. Mikewa yayi da niyyar barin gidan, muryar Hamna na rawa tace

"Abba ina zakaje? Ita da ta shigo yanzun ya kamata ta fita..."

Cikin tashin hankali Abba ya juyo, saidai kamun yai wani abu, da zafin nama Ummi ta karasa inda Hamna take tana dauketa da wani irin mari dayasa Tasneem tashi tana son shiga tsakanin Ummi da Hamna din, saidai ta makara dan kuwa Ummi ta janyo Hamna ta fara kaimata duka duk inda ta samu

"Dan Ubanki ni zaki fadama magana? Hamna har nawa kike? Bakin hali irin na Ubanki, Wallahi gara in karyaki in huta"

Abba ne ya tako har inda suke, ranshi yagama baci matuka, karfi yasa ya banbare Hamna daga hannun Ummi, yana janye Ummin gefe da fadin

"Meye matsalarki? Dan Allah meye matsalarki a rayuwa Bara'atu?"

Kallon shi Ummi takeyi hawayen takaici taji sun zubo mata. Har yana da bakin dazai tambayeta matsalarta bayan yasa yaranta sun tsaneta, ko hira basa zama suyi da ita, har Hamna na fada mata ita ya kamata ta fice tabar musu gida bashi ba.

"Kana da bakin da zakaimun wannan tambayar? Muftahu kana da bakin da zaka tambayeni matsalata? Bayan kasa yarana sun tsane ni"

Zafin zuciya irin na Hamna, ko alamar hawaye babu a idanuwanta, duk jibgar data sha wajen Ummi, zuciyarta a dake, muryarta can kasa tace

"Abba dan Allah ba gidan da zamu koma? Inda babu Ummi?"

"Hamna..."

Abba ya fadi zuciyarshi na rawa, dan ba a muryar Hamna ba kawai, har a fuskarta yana ganin tsanar datai ma Ummi din, da yasa jikinshi yin sanyi. Ita kanta Ummi kallon Hamna take, wasu sabbin hawayen na zubo mata. Daman duk cikin yaran Hamna tun tana karama babu wata wadatacciyar shaquwa a tsakanin su. Tana wata shidda ta yaye kanta da kanta.

Koda ta fara girma ba yawan magana gareta ba, a rana banda gaisuwar safe, shima in ta tashi kamun su tafi makaranta Hamna bata sake mata magana, sai dai ko in ita tai mata magana kota aiketa. Bata taba sanin akwai randa Hamna zata fadi maganar datai mata zafi ba sai yau.

Juyawa Ummi tayi tana shigewa daki, Abba kuwa Hamna yake kallo. Muryarta can kasa ta sake cewa

"Dan Allah Abba ka mayar damu wani wajen inda ba zamu dinga ganinta ba"

Daga zuciyarta take jin kalaman data furta din, da gaske take jin batason ganin Ummi, ko kadan batason ganinta. Batasan abinda take ma Abban su, tana lura, tasan badan Tasneem ba da yunwa ta kashe su. Ummi bata damu dako sunci ko basuci ba. Halayen Ummi basuyi mata ba, dan suna cikin halayen da malamin su ya fada musu ba masu kyau bane a Islamiyya.

Da kuka Azrah ta shige daki, ita kanta Tasneem din tana jin hawaye na shirin zubo mata. Badan abinda Ummi tayi ba, sai yanda take fita daga zuciyoyinsu. Sai yanda Ummi ta zubda hawaye akan Hamna, shiyafi komai daga ma Tasneem hankali, Sabeena kuwa baccinta take hankali kwance, batama san me ake ba.

Dakin Ummi Tasneem ta nufa, tana barin Abba daya kama hannun Hamna ya zaunar da ita kan tabarma, yama rasa mezaiyi, dan haka ya dauki kofin dake ajiye gefe yaje ya dibo ruwa ya bata, hannunta na kyarma ta karbi ruwan tasha, sai lokacin taji zuciyarta ta karye. Wani irin kuka ta fashe dashi mai cin rai tana fadawa jikin Abba.

"Me yasa Ummi ba zata zama kamar kowacce uwa ba Abba? Me yasa take maka haka? Me yasa bata son mu?"

Hamna take tambayarshi tana ci gaba da wani irin kuka da ya daga mishi hankali. Riketa yayi saida kukanta ya fara tsagaitawa tukunna a nutse yace

"Wayace Ummin ku bata sonku?"

Shiru Hamna tayi tana sauke ajiyar zuciya a hankali. Jin batace komai ba yasa Abba ci gaba da fadin

"Akwai halayen Ummin ku da basu da kyau, nasani amman haka wasu mutanen suke, Umminku na daya daga cikin su, tana sonku ko da bata nuna muku ba. Ba zaki tuna ba, da kina karama, lokacin kina kyanda haka Ummin ku take kwana batai bacci ba tana kula dake, banda kudi lokaci, ita taita yawo saida ta samo kudin data kaiki asibiti, Ummin ku nada halayya kala-kala, amman tana sonku sosai"

Hamna na kwance jikin Abba tana kuma jin duk abinda yake fada.

"Ummi ta kwana batai bacci ba da banda lafiya?"

Kai Abba ya daga mata. Dan jim tayi kamun tace

"Allah na fushi dani ko Abba? Malamin mu yace karkai ma iyayenka rashin kunya, musamman mahaifiya"

Kai Abba ya sake daga mata dan jikinshi yagama mutuwa. Hawaye suka sake zubo ma Hamna

"Ka bata hakuri Abba"

"Zan bata hakuri, amman kema sai kinmun alkawari ba zaki sake fadin in kaiku wani waje da Umminku bata nan ba, saikin mun alkawarin ba zaki kara tsanarta haka ba"

Muryarta na rawa tace

"Abba banaso Allah ya karayin fushi dani, banaso in zama munafuka, Ummi zata sake wani abin dazan tsaneta irin nayau, banaso in maka alkawari in karya"

Numfashi mai nauyi Abba ya sauke, Allah ya basu yara masu hankali, amman Bara'atu taki nutsuwa ta fahimci hakan, tana gab da rasa yaran bai kuma san yanda zaiyi ya gyara hakan ba.

"Kimun alkawari zakiyi kokari to, in tayi wani abin zaki yafe mata"

Saida ta dauki yan mintina tukunna ta daga mishi kai, dagota Abba yayi amman ta rike shi gam, dan haka ya gyara zamanshi. Wani irin kadaici take ji, ji take gidan ya kara mata girma, kamar inta saki Abba zata bace ne cikin gidan. Runtse idanuwanta tayi gam tana ruqunqume Abba.

Tasneem kuwa tana shiga dakin Ummi ta sameta zaune kan gado tana matse hawaye. Goge nata hawayen tayi, Ummi ta dago cikin kuka tace

"Kema zuwa kikai ki fadamun maganar ko?"

Da sauri Tasneem ta girgiza mata kai.

"Dan Allah Ummi ki yafe mata, ki daina kukan nan, hawayen da kike zubdawa akanta zai iya zamar mata fitina..."

"Ita bata san hakan ba ai Tasneem, ku duka kun tsaneni ko? Saboda ina fada muku gaskiya, kunfi son Abban ku akaina, dan kawai halin rashin da muke ciki na damuna"

Shiru Tasneem tayi dan tasan in tace ta fahimtar da Ummi zasu dauki duka darenne suna abu daya batare da Ummi ta fahimceta ba. Ba tazo bane dan ta fahimtar da Ummi kan yanda halayenta ke nisanta kaunarta da zuciyoyinsu. Tazone ta tabbatar data yafema Hamna.

"Kiyi hakuri, dan Allah ki yafe mata, damu ma in mun bata miki rai"

"Hmmm"

Ummi ta fada cike da takaici da kunar zuciya, tana jin ta kara tsanar Abba, duk shiya ja mata wannan matsalar.

"Ummi mana, dan Allah"

Tasneem ta fadi tanajin wasu hawayen zasu zubo mata.

"Shikenan ya wuce"

Dan murmushi tayi tana ma Ummin saida safe da bata amsa mata ba. Fitowa tayi ta samu su Abba a zaune, hannu takai ta kama na Hamna da hakan yasata bude idanuwanta, mikewa tayi daga jikin Abba, Tasneem na taimaka mata ta tashi. Kwanciya tai a jikin Tasneem din yanda suke a tsaye.

Kallon Abba Tasneem tayi, da idanuwanta take nuna mishi karya damu zata gyara komai. Kai ya jinjina mata da murmushin karfin hali.

"Sai da safe Abba"

Bai iya magana ba sai kai daya jinjina mata, da Hamna rike a jikinta suka shiga daki, Abba ya jima zaune a wajen yana godema Allah daya bashi Tasneem, koba komai ta zame musu kamar HASKEN LANTARKI (Aynarh Dimple) a rayuwarsu. Tare da ita komai yana zuwa musu da sauki.

*

A kwance ya samu Ummi sanda ya shiga dakin, ko da taji shigowarshi bata nuna alamu ba, dan ko motsi batai ba.

"In har baki gyara halayenki ba, kina gab da rasa yaranki Bara'atu, dan Allah ki gyara, badanni ba, dan kanki, dan kar yaranki su tsaneki"

Abba ya fadi muryarshi can kasa. Tunda ya shigo tana jinshi, bata kaunar ganin shine, kome yake faruwa shiya janyo musu, rashin wadatarshi ne ya ja musu komai. Tunda ya bude bakinshi ya fara magana take jin kamar yana zuba mata wuta. Mikewa tai zaune ta juyo tana kallon shi.

So take ta tuna dalilin dayasa ta aure shi tun daga farko ta rasa, dan ba zabinta bane ba, zabin mahaifinta ne ya kuma rasu yabarta da wahala da zabinshi, ba tun yanzun tasan ita na sa'ar auren shi bace ba, tana da kyau, kamata yai ace tana gidan hutu, inda zataci me kyau tasha me kyau, ba zama da muftahu da bai kareta da komai ba banda rabon yaran da yasa suka tsaneta yanzun.

"Aurenka bai kareni da komai ba, babu ranar dazan tashi banyi dana sanin aurenka ba Muftahu"

Runtsa idanuwanshi Abba yayi, wani abu na tokare mishi zuciya. Lokutta da dama in ta guma mishi wani bakin cikin yakan zauna yayi tunani, yana neman dalilin da zaisa yaci gaba da zama da ita, tun farko farkon auren su ya fara gane halayyarta, tun lokacin son da yake mata ya soma dishewa harya neme shi ya rasa.

Sai dai bazai iya rabuwa da itaba saboda amanarta da mahaifinta ya danka mishi, sai kuma don yaranta, amman indai danjin dadine na zaman aure, bazai tuna randa ya samu na rana daya da Bara'atu ba. Yana so ya fada mata shima yayi dana sanin aurenta, kyawunta daga wajene kawai. Amman a gajiye yake jinshi, bazai iya wani sabon tashin hankalin ba.

Dan haka ya zagaya yahau kan gadon can karshe ya kwanta. Cikin takaici Ummi take kallonshi, idanuwanta na cika da hawayen bakin ciki.

"Dan Allah ka sawwaqemun aurenka in huta, Muftahu ka sakeni ko zan samu farin ciki"

Ta karasa siraran hawaye na zubo mata, har cikin kashinta takejin yanda tagaji da zama dashi. Maganganun da take ba karamin daga mishi hankali sukai ba, ko motsi ya kasa dan kar hakan ya sake tunzurata su duka shaidan yai musu busa yayi abinda zai dana sani, zuciyarshi zafi take kamar zata tsaga kirjinshi ta fito.

Inalillahi ya shiga jerowa, yanaji ta sauka kasa ta kwanta, tun yanajin sautin kukanta harya daina. Ya dade idonshi biyu kamun wani wahaltaccen bacci ya dauke shi.

*

Randa Abba ya tafi su dukan su ji suke kamar marayu. Ummi ta fita harkarsu, gaisuwar su ma dakyar take amsawa, daman ba wuni take gidan ba. Inta fice abinta sai dare zasu ganta. Ranar nema ta dawo ana idar da Sallar Maghrib. Jinsu suke a takure, Sabeena na rungume jikin Tasneem, Hamna na dayan gefen ta kwanta jikin kafadarta, haka Azrah ma, da Ummi ta shigo haka suka sake naniqe mata, kamar zasu koma cikin jikinta.

Sunci abinci, dan haka suna yin alwalar sallar isha'i suka shige daki, suna idarwa, Hamna na zaune tana karatun Qur'an akai rafka Sallama wai ana son ganin Tasneem. Da hijab a jikinta dan haka mikewa tayi.

"Fita zakiyi yanzun?"

Azrah ta bukata da alamar tuhuma a muryarta. Dan murmushin karfin hali ta dora a fuskarta da fadin

"Bana son tashin hankalin Ummi, in naje muka gaisa shikenan"

Kan katifa Azrah tahau tana juya bayanta. Da sauri Tasneem din ta fice daga dakin kamun Hamna ta idar da karatun tai mata wata maganar, Ummi tagani tsaye bakin kofa, hada idanuwa sukai, murmushi Ummi tai mata hadi da dan daga mata kai. Ta manta rabon data ga murmushi a fuskar Ummi sai yau.

Sanda ta fita Alh. Madu na cikin mota, glass ya sauke yana washe mata hakora. Cike da takaici take kallonshi, hadi da tausayama yaranshi da suke tashi da sanin yanda da duk fitarshi yake zubda musu mutuncin su. Ta bangaren da yake ta karasa tai tsaye a wajen hadi da gaishe dashi.

"Tasneem, ki zagaya ki shigo ciki mana"

Fuskarta a hade ta girgiza mishi kai

"Nan ma ya isa. Ina jinka"

"Haba Tasneem, ni bari in fito to saimu gaisa sosai"

Kamun ta bude baki ya fara turo murfin motar har yana shirin buge ta saboda kyarmar jikin da yake. Matsawa tayi gefe, ya fito yana mayar da murfin ya rufe. Tsayawa yai gefenta kamar kafadarshi zata gogi tata.

"Tunda mun gaisa nizan koma ciki, dare ya soma yi"

Bata fuska Alh. Madu yayi yana fadin

"Me yasa kike haka ne Tasneem? Kamar da ba yar makaranta ba"

Harara ta watsa mishi, tanajin kamar ta kwada mishi mari, dan bashida sauran mutunci a idanuwanta. Ganin yana kara matsawa yasa Tasneem juyawa, hannunta daya riko yasa tsikar jikinta gabaki daya tashi

"Auzubillahi..."

Ta fadi tana kwace hannunta tana murzawa da dayan kamar hakan zaisa ta daina jin rikon dayai mata ko ta goge shi gabaki daya daga jikinta. Idanuwanta cike taf da hawaye take kallonshi, ko ina na jikinta kyarma yake dan kuwa ko a yan uwanta maza babu wanda ya taba rike mata hannu, ko bisa larura da duk fitar da suke da Tariq bai taba rike mata hannu ba.

Ko titi zasu tsallaka sai dai ta rike rigarshi dam, amman yau namijin da baida kusanci da zama Muharraminta ya rike mata hannu a banza, yasa an rubuta mata zunubi. Ganin tsanarshi dake cikin idanuwanta yasa shi saka hannu a aljihu yana dibo kudi yan dari bibbiyu da batasan yawansu ba yana miko mata hadi da fadin.

"Ga wannan, sai gobe ko? Zanzo da wuri dan mu samu mu gaisa sosai. Kar kiji komai, duk abinda kike bukata ki fadamun, kome kike so zan siyo miki shi, inma kudi ne zan baki"

Runtsa idanuwanta Tasneem take tana bude su da sauri-sauri, zatai kuka amman ba'a gabanshi ba, cike da tsanar kanta tasa hannu tana karbar kudin daya rike dam, saida ya hada da hannunta yana murzawa tukunna ya saki kudin yana wani kankance mata idanuwanshi.

Jikinta na bari ta shiga gida, harda gudu-gudu ta hada, Ummi na tsakar gida a zaune bakin kofa, batama kula da cewar Tasneem din a hargitse take ba.

"Harya tafi? Me ya kawo miki?"

Ta tambaya, kudin dake hannunta ta mika ma Ummi gabaki daya tana juyawa zata nufi daki

"Yaushe yace zai dawo?"

Juyowa Tasneem tayi, da idanuwanta da suke cike da hawaye take kallonta, tana son ganin menene babu a tattare da Ummi, me yasa ba zata zama kamar sauran iyaye mata na kawayenta ba. Amman ta rasa ganin komai, muryarta can kasan makoshi tace

"Kin samu abinda kike so Ummi, ko yaushe yaga dama zai dawo"

Bata jira amsarta ba ta shige daki, tabe baki Ummi tayi, kasa-kasa take fadin

"Shegen bakin hali, arziki na binki kina gudu"

Daki ta shige itama dan ta kirga kudin da Alh. Madu yaba Tasneem. Ita kuwa tana shiga daki ta samu su Azrah suna kwance har sun saki net, hijab dinta ta cire ta soma ajiyewa. Kamun ta sake fita da sauri. Ruwa tasa tana wanke tafin hannunta da damtsen ta inda Alh. Madu ya taba, sai dai har a zuciyarta take jin yabar mata shatin hannunshi da bata san ranar gogewarshi ba.

Hawaye ne masu dumi suke zubo mata, gajiya tai da dirzar hannunta da harya fara zafi, dan haka ta koma daki, cikin net din ta daga ta shiga, tukunna ta ziro hannu ta kashe fitilar dake kunne, kuka take data dauka a hankali ne, dan sam batasan shesshekarta na fitowa fili ba, saida taji Hamna tace

"Me yai miki? Ya miki wani abu ko?"

Duk da cikin duhu ne bai hanata girgiza kai ba, saidai ta kasa magana, saima wani kukan daya sake kwace mata, cike da tsoro matsananci, inta mutu batasan bayanin da zatai ma Allah ba, Ummi ta ja mata, ba kuma zata tayata daukar zunubin ba, dan kowa da nashi kason, tana jin Hamna na matsowa ta riketa, juyawa tayi tana sake fashewa da kuka.

Azrah ma hannun Tasneem din ta lalubo ta dumtse gam cikin nata,su dukansu ukkun kuka suke, duk da basu san dalilin nata kukan ba, ita ta kasa yin shiru balle ta lallashe su. A haka har bacci ya dauke su.

*

Duka jarabawar da akai guda biyu Tasneem tayi, dan Ummi ba zama take ba ballantana taje makaranta. Ko kwana biyun da Abba yai daya tambaya karya tayi mishi cewar sun fara hutu dan batason Ummi ta bata mishi rai. Da yake kwanakin gudu suke, sai taga kamar jiya aka fara, musamman su Azrah, taga saurin gamawarsu.

Sai dai hutunsu ya mata dadi ba kadan ba, ko ba komai kamun lokacin Islamiyya yayi suna debe mata kewa. Akwai kudi a hannunta tun wanda Abba yabari, su na da komai na abinci wannan karin. Harda su Maggi a kayan da Abba ya kawo da yawa. Alh. Madu bai sake dawowa ba tun ranar dayazo ya bata kudi.

Zatai karya intace da Isha'i tayi gabanta baya faduwa, har sai taga dare yayi sosai baizo ba, Ummi ta kulle musu gida take iya samu tai bacci. Addu'a take Allah karya dawo dashi.

"Ya Tasneem daman kiyi mana alale"

Cewar Azrah.

"Ba sai in akwai wake da yawa ba tukunna"

Hamna ta fadi tana daquna ma Azrah fuskarta.  Murmushi Tasneem tayi

"Akwai wake da yawa ma Abba ya kawo, ina gudun karya fara kwari ma. Sai dai kamar rana tayi yanzun"

Da sauri Azrah tace

"A'a wallahi rana batai ba, zan tayaki gyarawa ma, ko

1 Comments On ALAKALAMIN KADDARA PART 1
avatar
khadija-7-4

1 year ago

Reply

Yayi

Please Login or Register in order to submit comment