Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[16:09, 12/19/2016] Swtbaby: •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫

❣🎀❣🎀❣

*_written by miemiebee👄_*

In dedication to *Aunty Sis💕*
0⃣1⃣



*ANAS*
     K’auyen Bama dake jihar Maiduguri, Borno.

            Da yammacin ranan Asabar misalin k’arfe biyar da mintuna aka. Ruwan sama akeyi me ni’iman gaske, ga wani iskan dake hurawa me kad’a bishiyoyi da flawoyi, ko ina ya d’au sanyi. Tsit kukeji a garin, yara da manya, maza da mata kowa na cikin gdajensu, masu tafiya akan hanya kuwa sun faka gu d'aya, motoci dabasu fi a k’irga ba ke wucewa time-to-time. Can k’ark’ashin wata bishiyar ’yim na hango wasu samaruka guda hud’u wanda barasu gaza kuma barasu fi shekaru 17-18 ba.

        Daga nesa nake, amman hakan be hana ni tantance kyakkyawan cikin wad’annan samarukan ba. Wani kyansan ma sanda na gama k’arisowa, fari ne yellow shar da gashi kwance a duk sassan jikin d'an Adam da akasan na tsirar da gashi. Gashin kansa nada yawa saidai bawai afro tayi ba saboda tsantsin gashin bai tsayuwa, luf-luf yake kwance a kansa, bak’i k’irin yana yalk’i wane yasha mai.

      Saje ne kwance akan farar fatar fuskarsa wanda da ace yanada gemu da sun had’e. Gashin girarsa ba a cike take erin thick dinnan ba, silky yake a kwance d’an siriri wane yayi carving nasu. Dogayen eyelashes nasa wanda suke kallon k’asa santsi ne dasu. Bashida dara-daran idanunu, idanun nasa suna nan madaidaci da k’wayoyin idan nasa light blue wane na bature.

          Nasha jin ana cewa a Africans akoi masu blue eyes ban tab’a yarda ba sanda naga wannan saurayi. Hancinsa ma ba dogo har bakan nan bane, daidai yake cikin 'yar fuskarsa wanda yakasance shi ba dogo ba bakuma gajere ba. Bakinsa light red yake d’an madaidaici cikin fuskar tasa. Dukda cewar ya d’aure fuska hakan be hana dimple na kumatun damarsa lotsewa ba wanda babu hakan a na hagun.

   A zaune yake amman hakan be hanani tantace tsawonsa ba, dogon na miji ne, yanada faffad’ar k’irji duk da cewar siriri ne. Ofcourse ana cewa d’an Adam bai cika goma but za’a iya kiran wannan saurayi hallitar data cike goma bansani ba halan ya gaza ta hali amman inde ta hallita ne kam masha Allah, Allah yabasa, ban tsammanin akoi macen da zata ga wannan saurayi bata kuma kallonsa ba. I mean ba mace kad’ai bama kowa in all.

      Sanye yake da mint blue T shirt wanda ya mugun amsar farar fatarsa, jeans na jikinsa kuwa tad’an kod’e alaman tasha ruwa. Rik’e yake da kara a hannunsa yana wasa dashi da siraran yatsunsa wanda suke nan kan ba na miji ba.

      Gefensa saurayi ne me kama da shi sak, saidai komi na wannan kyakkyawan yafi nasa, kuma shid’in be kai kyakkywan fari da k’war jini ba, duk yadda akayi wansa ne na jini saidai na kasa tantance wane babba cikinsu. Sauran biyun k’arshen kuwa chocolate skinned suke, saidai still d’aya yafi d’aya haske.

     “ANAS na mata kenan!” Cewar d’an bak’i na k’arshen tare da kewayo da kallonsa kan kyakkyawan cikin nasun wanda nake da tabbacin shine ANAS d’in yana mai murmushi wanda hakan ya bayyano da brown teeth nasa, tabbacin kanuri ne shi kenan. “Uhm uhm fa BAANA!” cewar me haske na gefen d’an bak’in da yayi magana yanzun kenan. BAANA yace, “ah’ah barni in tsokanosa de.” Shide kyakkywan nasu da ake kira da ANAS be tanka saba, hasali, yi ma yayi kamar besan ana magana a gefensa ba se b’antare karan dake hannunsa yakeyi yana kallon yadda ruwan saman ke sauk’owa.

        Wanda nake kyautata zaton wan Anas d’in ne yace da d’an bak’in gefen nasa “barsa de KASHIM, neman magana yake yau gun ANAS.” KASHIM ya karkato da kallonsa kan BAANA “aikam naga alama rad’au a fuskarka, kuma wallahi kasan inya shak’ure ka bame k’wato ka, kasan halin mazan namu. Ko mata ma bai ragar masu ba bale kai,” ya d’an yi shiru sannan ya k’arisa “gardi” Yafad'a cike da gatsine.

     BAANA yace, “hummm zagen dai, naga kap nan gardawa ne har Shettima k’anin mun ma(k’anin Anas knan)” Duk suka k’yalk’yale da dariya illa shi wannan kyakkywa da suke kira da Anas wanda yayi burning face sekace besan me kalmar dariya ba.

        Niko miemie na matsu injiyo muryan wannan kyakkyawan da suke kira da Anas. Yawancin anacewa wanda yafiye kyan fuska bai fiye zaqin murya ba kuma hakan ne sanda na jiyo muryan Anas na k’aryata wannan batu.

        “You see, ruwan nan na tsayawa barama kuganni anan ba to talk more of kumin tsiya mtschww.” Cewar Anas tare da watso musu harara sekace mace.

      Lallai! Allah yayi murya anan, muryar Anas sautin na miji ne da anji amman saidai ba tattausar murya bace, zaqi ce ga me sauroro, bakuma zaqi erin ta mata ba saboda yadda muryar ke cracking a hankali in yana magana.

       “Toh Anas meyayi zafi daga fad’in gaskiya? Ai gaskiya ce wallahi kap ‘yan matan garin nan basu san wani na miji sekai, narasa menene kake dashi bamuda, ni da bansanka bama se ince asircesu kayi.” Cewar Baana yana nuna yadda abin ke damunsa.

      “Ahhh lallai Baana ka soma zarewa” cewar Kashim cike da mamaki. “Yanzu har seka tambayi ko mesa matan garin nan basu kula kowa se Anas? Bakada ido ne?” Shettima ya karb’esa “gaskia da alama.” Kashim ya cigaba, “k’warank’wasa ace yau ni mace ce nima sena so Anas wanga blue eyes sekace bature, ko ka manta teacher'n English namu da ke sansa.” Suka sake sheqewa da dariya at once kuma sukayi shiru suna jiran tsiwar Anas to thier suprise be ce masu ko uffan ba miqewa yayi da niyar tafiya dukda cewar ruwa akeyi fuskarsa a tamqe kwata kwata abin be basa dariya ba.

        “Haba maza yi hak’uri mana karka fad’a min cikin ruwan nan zaka tafi!” Cewar Shettima wansa tare da rik’o shirt na Anas. Harara Anas ya galla masa da nufin ya sake masa kaya, kafin ace me k’arfin ruwan saman ya dad’a k’aruwa ba yadda ya iya dole ya koma ya zauna. “Wai zanso inga Anas yayi aure wataran, muga ya zena controlling wannan uban temper'n nasa da matarsa.” Cewar Baana. Take Shettima ya juya ya kallesa tare da zaro masa ido yana me masa warning.

         Dukda cewar Anas be tanka sa ba amman fuakarsa takoma ja alokaci d’aya ya had’e girarsa gu d’aya kallo d’aya za’a masa asan ransa ya b’aci ko dan meh oho? Kodan kiran kalmar ‘aure’ da abokin nasa yayi ne?

      Cikin tsiwa yake maganar ba alamar walwala a tattare dashi. “Baana don't push it, nasha fad’a maka time without number bana san kana min maganan aure ko kuma ‘yan mata in muna tare, that goes to both of you” ya nuna Kashim da Shettima. “Banaso! Banaso! Inhar kuna sona yaci ace kundena for goodness sake!” Shettima ya dafe kafad’arsa “toh maza we are sorry.” kallonsa yayi ba tare da yace masa komi ba sannan ya kau da kai. Baana ya numfasa sannan yace, “toh ka fad’a mana why mana, kullum se kace bakasan kalmar aure ko budurwa amman baka tab’a gaya mana mesa ba, as friends we have to know ko bahaka ba Kashim?”

      Kashim ya giad’a kai “sosai mah kayi gaskiya.” Shettima kuwa dayasan mesa wan nasa bayasan wannan kalmomi guda biyu kawai ya kad’a kansa cike da nadama, yayi yayi ya ganar da d’an uwansa gaskia yakuma sa ya yafe wa mahaifiyar su amman ina abin ya gagara sam saboda abinda tayi ta sa Anas ya kariya, zuciyarsa a toshe take da bak'ar kiyayya is hardly aga Anas yana dariya, murmushin ma se in abu yakai ya kawo ne yakeyi.

      “I can't tell you guys, I'm sorry saboda talking about it makes me sick kawai ni kudena tareraya ta da wannan magana banaso give me a break please.” Baana ze sake magana Shettima ya dakatar dashi ta aza yatsa kan lips nasa. In akoi abinda yafi damun wannan abokai guda biyu, (Baana da Kashim) befi wannan halin abokin nasu ba, ace da an kira kalmar aure se mutum ya b'ata rai, aure da ta kasance sunnah me k’arfi wanda kowani d’an Adam keda burin cikata. Gaskiya da abun duba.

     Kashim yakasa hakura shikam sanda ya kuma tambaya “Anas munsan baka san maganan nan amman ka dage ka fad’a mana, who knows! we might be of help.”

     Juyowa Anas yayi ya kalle sa tare da wata murmushin takaici ta gefen lips nasa wanda a sakamakon hakan ya bayyano da fararan hak’waransa da suke kamar an daidaita tsawonsu “help? Hmmm, k’arshen k’ok’arin da zaku iyayi shine ku dawo da ita kuma koda kunyi hakan ma barinyi appreciating ba saboda tafita a raina, bana san sake sata cikin idanu na, ta cuceni ta cuci two siblings d’ina Shettima da Amal, and most of all ta cuci Abuu (mahaifinsu). I don't want her ever in my life.”

      Cike da mamaki Baana yace, “subhanallah wa kenan?” “Bade mahaifiyarku ba?” Kashim ya tambaya. Anas bece dasu komai ba Shettima ne ya giad’a masu kai da nufin eh mahaifiyar su Anas ke nufi. “Subhanallah! Subhanallah! Anas be kamata kana maganar mahaifiyar ka da ta kawo ka duniya haka ba, uwa uwa ce. Kome tayi maka ka tuna ita ta kawo ka duniyah.”

   “Thats my point!” Anas ya fad’a a masifanche. “Ita ta haifeni, ita ta kawo ni duniyah abin dayafi ban haushi fiye da komai kenan. Taya matar da ta kawo ni duniyah zata tafi ta bi wani na mijin daban ta bar family’nta a baya, How? Why? Mesa mata basuda tausayi? Mesa Allah yayi su mugaye masu san kai da abin duniyah mesa? Mesa basuda Imani? Mesa tayi breaking heart na Abuu haka? Har yau yakasa trusting wata ‘ya mace a duniya. Why does it have to be this way? Why? Mstchww!” yaja tsaki cike da haushi.

       “We are sorry” Kashim yafad'a cike da tausayi, so wannan grudge d’in Anas ke holding a zuciyarsa har yanzu saboda abinda mahaifiyarsa da Shettima tayi musu. Yau shekaru kusan bakwai kenan da sanin junansu amman be tab’a sanin mesa Anas ke cikin k’unci ba, kullum ba walwala a tattare dashi se yau. Tun ba yau ba yakeson jin me tarihin Anas amman Anas ko kad’an baisan maganar haka zalika ya hana wansa Shettima fad’a ma kowa. Yau d’inma halan saboda sun tak’ura masa ne yasa ya fad’a.

         Tun da suke a secondary school haka Anas yake, ko erin secondary school dating da akeyi d’innan Anas be tab’ayi ba hasali betab’a showing koda slightest interest akai ba ma. Unlike his brother Shettima daya d’au komi as k’addara yake living life nasa peacefully cikin walwala da dariya.

       Tunanin ya zeyi ya karkato da hankalin friend nasan kan gaskiya yake. Gyaran murya yayi sannan a hankalche yace “Anas we are all here for you, we are like brothers yanzu. Nasan how hard this must be for you amman dole kayi haquri ka rungumi qaddara kamar yadda Shettima yayi.”

       “No Kashim, I can’t baran iya ba. Karka had’ani da Shettima, Shettima was a small kid back then time da abin yafaru, definately ya manta komai bare iya tuna koda abu ba, but me? Da wayona da komai na wannan matar ta tattara kayakinta, we were all begging on our knees muna roqarta karta tafi... Mschww I don't want to talk about it banasan ciwon kai, you two have heard enough.” Anas ya fad’a tare da miqewa daga mazauninsa. “Finally ruwan ya tsaya” yayi qoqari canza topic d’in, yana miqa wanda a sakamakon haka joints na jikinsa suke sakar k’ara. “Shettima lets get going, yakamata mud’an taya Ummee da aiki kafin Maghrib yayi” (Ummee; k’anwar mahaifinsu wacce takasance tamkar uwa a garesu tunda mahaifiyarsu ta tafi ta barsu take kula dasu).

        Shettima ya mik'e shima suka d’anyi manly shake da juna, “alright! Se mun had’u a masjid” Anas yace da Baana da Kashim da suke zaune har yanzu sannan ya juya shida Shettima suka soma tafiya.

     “Huh!” Kashim ya numfasa, “ina tausaya wa abokin nan namu, like sosai. Zuciyarsa ta riga ta toshe da tsantsan k’iyayya.”  “Sosai fa Kashim, but tsaya kaga wani abu yanzun nan ze dawo” cewar Baana yana murmushin jin dad’i. “Bade ya manta blessing d’inba?” (Yaren da masu shaye shaye ke amfani dashi wajen kiran ‘wiwi’). Baana yace, “Yup!” Tare da d’aga girarsa sama yana murmushi.

*© miemiebee*
   beeenovels.mywapblog.com
[16:09, 12/19/2016] Swtbaby: •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫

❣🎀❣🎀❣

*_written by miemiebee👄_*


0⃣2⃣




Tafiya suke a sahu d’aya, tsayin nan nasu na nan d'ai da kad’an Anas ya d’ara Shettima inba wai ance ya da k’ani bane za’a zata agemates ne. Daidai lokacin da suka yanko wata corner kenan Anas yasa hannu a aljihu yaji wayam ba komai, cak ya tsaya hakan yasa Shettima tsayawa shima. “Ya maza lafiya?” “Ba lafiya ba, go ahead I'll catch up nayi mantuwa.” cewar Anas. Shettima ya tsaya ya k’are ma d’an uwan nasa kallo sannan yace, “bade blessing d’in ba.”

      Anas ya kallesa da gira d’aya d’age sannan yace, “toh meh? Kadega yadda su Kashim suka sani tono maganan chan definately nasan ciwon kai ze kamani and despite that, yadda akayi ruwan saman nan I'm gonna enjoy sleeping.” tare da d’anyin murmushi wanda ya sake bayyano da kyansa tare da lotsar da dimple nasa dake kumatun dama. “Kona yau baraka hak’ura ba?” Shettima yasake tambaya. “Se in na amso karka sha” cewar Anas.

       Dariya kad’an Shettima yayi “zan d’an tab’a mana, naji ance da akoi dad’i cikin tea.” Anas ya dafe kafad’arsa “lets go?” Da d’aga kan da Shettima yayi suka juya suka dawo gun Kashim da Baana. Suna iso wurin nasu, Anas yace, “maza bani!” Baana yaci fuska “ban gane baka ba, mezan baka?”  “Wai me ka maidani ne? Give me!” Anas ya fad’a a little bit pissed. Dariya Kashim yayi “basa please kaga har yafara losing temper.”

     Nan Baana yasa hannu a aljihu yaciro wata leda ya raba into two saidai d’aya yafi d’aya yawa sannan ya mik’a wa Anas kad’an din. “Are you serious? Naga fa wannan abu ni nasaya da kud’ina so kabani me yawan ko in hanaka duka.” Baana yace, “haba! Anas namu na kanmu, kap qauyen nan fa kai kad’aine me blue eyes yi hakuri mana. Aikasan da inada kud’i dana siya nima.”  “Toh ni na hanaka yin noma ka samu kud’i? Abeg give me and stop wasting my time.”  “Dan Allah fa nace” Baana yafad’a pleadingly. “Okay naji talaka kawai semun had’u a masjid then.”

      Daidai sunkai ga shiga corner'n gdansu kenan wata budurwa tafito daga wani gida, sanye take da hijabi iya guiwarta, dududu barata fi shekaru 15-16 ba. Idanunta suna sauk’a kan Anas ta sakar dawata murmushi. Tsuka Anas yaja yasa qaninsa a gaba yana tunkud’esa dan suyi sauri subar gun shiko Shettima daya gano haka tuni ya rage saurin tafiyarsa dukda tunkud’in da Anas kemasa.

     Se k’arisowa wajen nasu wannan budurwa ke. “Anas kamar kayi bak’uwa ko? Wannan ba Aisha bace? Ka tsaya kaji me zatace mana.” Cewar Shettima yana murmushi. “Wallahi in bakayi shiru ba zan mareka, kuma barakayi tafiya bane?” Daya wani tunkud’a gaba Shettima besan sanda yasoma matching dasauri sauri suka bar wurin ba.

     Isarsu gidah keda wuya suka tarar da Ummee a tsakar gidah tana tsince shinkafa. Da sallama suka shiga ta amsa da fara'arta. ‘yar dattijuwa ce wacce barata fi shekaru 45 a duniya ba, tanada haske sosai amman bara’a kirata da fara ba, ga kyau daidan gwargwado masha Allah!. “Ohhh mazan nawa sun iso ne? Sekuma ruwa ya tareku a hanya ko?”  “Eh Ummee” cewar Anas yana k’arisowa wajen da take. “Me kikeyi haka?”

     “Tsince nake baba na, tuwon shinkafa Abuu keson ci gashi har ruwan ya tafasa ban gama ba.”  “Toh Amal fa mesa bata tayaki ba? Anyways kawo in tayaki Ummee.”  “Kai Baba na kaide Allah shi maka albarka” ta d'ago kai tana kallon Shettima dayayi kamar besan ma me suke fad’i ba. “Kai yanzu Shettima koda aiki ze taru ya kasheni ba ruwanka da bari ka tayani ko? Baka ganin wanka ne?”

    “Toh Ummee fisbailillahi ina aka san maza da tsintar shinkafa.” Baki wangalau ta bud’e tana kallon Shettima dududu shekarunsa sha shida ne fa da abu aka yake wannan tsiyar bayan ga wansa Anas me shekaru sha takwas bece komi ba. “Ehh hakane, sannu fa” tafad’i cike da gatsine. “Oyoyo Ya Anas” cewar wata kyakkyawar yarinyar da baratafi 8years ba fitowarta daga wata d’aki, ba shakka itace sistersu da suke kira da Amal, kyakkyawace sosai kamar sauran yayun nata bata gama kai Anas fari ba amman tafi Shettima. Su uku kap kamanninsu d’aya.

          (Bayan tafiyar mahaifiyarsu daga gdansu da wata takwas ta turo da Amal da wasiqa na cewa tabar gidan da cikin Amal ga ’yarsu nan ta haifota, kwanan ta d’aya a duniya kenan) sanadin haka Anas yake mutuwar san Amal duk rashin kunyarta bata masa saboda duk fitar da zeyi seya siyo mata abun k’walama unlike Shettima da cikinsa kawai ya sani thats the reason why basu shiri da Amal kullum cikin fad’a sukeyi duk sanda Anas yazo kuma seya bata gaskiya, wani sa’in har taran dangi suke masa.

     “Oyoyo my angel” yafad’i tare da bud’e hannunsa tazo da gudu tayi hugging nasa. “Ina sweet d’ina ya Anas?” kafin ya amsa mata ta zira hannu cikin aljuhunsa taciro ’ya’yan wiwin da Anas ya amso gun Baana sekuwa idan Ummee yakai kai. “Baba na meh wannan!?” Ta tambaya tare da zaro idanu waje. Nanfa Anas yasoma kame-kame can yace, “laaa Shettima kalli wannan abin da abokin Baanan can yace na rik’e masa” yama Shettima ido. Shettima yace, “ohh yamanta be karb’a ba kenan?”

      “Gashi anan kuwa!” Cewar Anas. “Anyways meh abun nema?” ya amshi daga hannun Amal. Ummee tace, “maza ka mayar masa wannan abu shaye shaye akeyi dashi, mayar masa maza!”  “Toh Ummee amman bansan ina gdansu ke ba, agidansu Baana muka had’u.”  “Nide koma me ka mayar masa.”  “Toh Ummee bari in muka fita Maghrib zan bawa Baana ya mayar masa.” Anas yafad’i a hankali
“Toh” tace tare da numfasa. “Ya Anas to ina sweet d’ina toh?” Cewar Amal.

      “Angel bansamu na saya miki ba, shops d’in duka a rufe I promise gobe kinji?” A hankali ta giad’a kai tare da turo baki. “Tsaya kiji wani batu” nan ya daidaita tsawonsa yakamo nata tare da rad’a mata wata magana a kunne aikuwa tahau tsalle suna ido hud’u da Shettima ta galla masa harara. “Wallahi Amal niba sa’anki bane wa kke harara? Maras kunya kawai.” Kafin Ummee ta masa magana Anas yace “ah’ah karka zagarmin k’anwa now go inside okay? Anyi ruwa kar mura ya kama ki.” Tana tsalle takoma ciki.

     Ba tare da b’ata lokaci ba Anas yataya Ummee suka gama tsince shinkafar banda Shettima daya tsaya kansu yana kallonsu cike da mamaki yarasa meke burge Anas a aikin kitchen bama aikin kitchen kad’ai ba. Bayasan ganin abinda ze tab’a Ummee ko Amal, he is so protective of them, duk abinda zeyi zeyi inhar it will keep them save and happy.

   *****

        Bayan sunfito daga masallaci iyayensu sukayi gaba a yayinda Shettima, Anas, Baana da Kashim suke tafiya a bayansu suna tattauna warsu ta maza. Wata budurwa ce ta b’ullo gabansu, dakatar dasu. “Ina wuni?” ta gaishesu duk suka amsa illah Anas

Please Login or Register in order to submit comment