Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Sallah ya riga yayi nan ta fad’a bayi tayi alwala shima haka sannan ya jasu Sallah bayan da suka idar ya sake feshe jikinsa da turare binsa kawai take da kallo seda yazo fita takira sunansa ganin baida niyyan fad’a mata inda zasa.

“Anas.” Chak ya tsaya “wani abu ne?” Ya tambayeta bayan ya bud’e k’ofar. “Nace ina zakaje?”
“Toh wifey kishi ne ya motsa?”
“Nifa ba kishin ka nake ba.”
“Toh why asking? Karki damu ba wajen wata zanje ba”
“Toh ni ina ruwa na? Inma chan zakaje Allah kare ni I thought ko zaka sauk’eni a gida ne.”
“Kin tab’a ganin inda amarya ta fita?”
“Anas zaman nan d’in ba dad’i.”
Wani murmushin tsiya ya saki, “just say it you are gonna miss me, karki damu I won’t take long yanzu zan dawo.” Bejira jin me zatace ba ya rufe k’ofar. ‘Yar tsukar ta taja tare da hayewa kan gadon, game na candy crush ta hau yi batasan seda bacci yayi gaba da ita ba.

_40 minutes later..._

A nitse ya bud’e k’ofar kamar ko yasan tana bacci. Ledar chocolates da ice cream daya siyo musu ya bud’e fridge d’in yasa ciki sannan ya nufa kan gadon inda take kwance bayan ya zauna gefenta ya zura mata ido. wayarta dake kwance a gefenta ya zaro yayi quitting game d’in. Hannu yasa a fuskarta a hankali ta yadda bare farkar da ita ba, gashin dake kwance kai ya d’ad’d’aga sannan ya jawo bargo ya rufeta.

****
Seda La’asar ya tada ta suka idar da Sallah tare da musu ordering abinci, suna cikin ci aka yi knocking a k’ofa “get it” yache mata ba musu ta mik’e ta bud’e kad’an daga photo album na bikinsu ne aka kawo musu. Bayan ta amsa ta masa godiya. “Mugani” Anas yace.
“Nima ingani mana.”
“I’m your husband you follow my instructions so bani.” Kallo ta galla masa “awww ni kike harara?”
“Bafa harararka nake ba.” Nan ta mik’a masa. Na english dinner’n su ya soma bud’e “wow!” Tace cike da jin dad’i ganin yadda tayi kyau a hoton.
“Wow me or you?”
“Ni de, ni ba kai nake kallo ba.”
“Da banga idanunki kan fuska na bane seki fad’a min maganan banza.”
“Nide ba kai nake kallo ba.” Ignoring nata yayi suka cigaba da kallon pictures d’in se anzo page dayaga tayi kyau se ya wani wuce da wuri wuri in akazo inda yayi kyau kamar ba gobe kuma seya tsaya yana admiring kansa. K’ananun tsuka take ja.

“Toh Anas a wuce page d’innan mana munfi minti uku fa muna kallo.”
“In kin gaji seki tashi, thank god I’m handsome and admit it you enjoy looking at my handsome face.”
“Nide I don’t enjoy.” D’ayan page d’in ya juya ganin tayi kyau yayi sauri ya juya “Anas ka tsaya mana muga nan d’in.”
“Keda wa? Page d’in beyi kyau ba bara’a kalla ba.” Bata sake ce masa komai ba ya juya next page d’in. Babban hotonsa da Fannah ne kad’ai a page d’in wanda tabar wani duk abinda takeyi tana kallonsa zallah. Kunya taji sosai ita kanta bata san ya akayi hakan ta faru ba. Hannu tasa ta rufe. “Me haka? D’aga hannun mana.”
“A’a Anas dan Allah ka juya.”
“Nak’i, ni nace ki tsaya kallo na awajen d’aga hannun. Kinga I can’t touch you saboda a contract namu ba body contact, d’aga hannun ki.”

Tana d’agawa ta bar wajen. Dariya yakeson yi amman bayason ta raina sa. Tana kallonsa ya d’au hoton a wayarsa.

*****
Bayan sun idar da Sallan Isha sukaci abinci bayi Fannah ta fad’a ta watsa ruwa a cikinsa ta canza kaya tana fitowa kamar jiya ta jera pillows tsakaninsu. Kallonta kawai yayi tare da kad’a kai bayan data kwanta yaje ya watsa ruwan shima. Pillow d’aya ya zaro ya koma kan cushion daya kwanta jiya ya mik’e akai bada jimawa ba shima yayi baccin. Kamar jiya yau ma ta farka da ihu nan shima Anas ya tashi. Kukan da takeyi yau kamar ma yafi na jiya. Kamar jiya haka ya samu yayi calming nata da k’yar tabar kukan sede b’arin da take har yanzu.


“Toh sakeni zan koma in kwanta.”
“A’a dan Allah Anas karka tafi wallahi mutumin ze dawo.”
“Bare dawo ba, sakeni toh.” Gangamesa ta sake tana girgiza kai.
“Haka kikeson mu raya daren a zaune?”
“A’a nide kawai karka tafi dan Allah” ta rok’esa cikin sautin kuka. “Toh ka kwanta anan.”
“A’a achan zan kwanta ba kece sarkin yin katanga da pillow ba? Kwanta abinki zan kwana achan nima.”
“A’a zan cire dan Allah karka tafi Anas.”
“Nifa barin kwana nan ba sekin cire pillows d’in da kanki.”
“Naji zan cire” hannunsa ta kama gudun kar ya gudu tayi watsi da pillows d’in tas. “Nacire dan Allah don’t leave me, inma zaka barni ka kira Mami tazo.”
“Naji I won’t leave you barin d’auko pillow na.”
“A’a ga nawa dan Allah kar ka tafi.” Murmushi ya saki. “Toh matsa ciki” ba musu ta matsa kan pillon nata ya kwanta. “Azaune zakiyi baccin ne?”
Kai ta girgiza. “Kicire hijabin toh. Wai ma bakiya jin zufan da kikeyi ne?”
Nanma kai ta girgiza “fine zan koma kan kushion na kwanta.”

“Anas dan Allah karka tafi” har yanzu bata bar b’arin da take ba. “Toh kicire you are sweating.” A hanakli ta yaye hijabin ta shiga kare k’irjinta. Kansa ya kawar daga gareta “seki kwanta.” Pillow d’aya taja ta matso dashi kusa da nasa duk tsoro yabi ya ratsa ta. Bayan minti biyar Anas ya juya yaga har yanzu batai bacci ba se b’ari take tana had’a gumi sekuma ta basa tausayi. “Kin kasa bacci neh?” Ya tambayeta cike da damuwa.
Kai ta gyad’a a hankali. “I’m here kinji? Ba mutumin daze zo, ina zuwa.” Hannunsa ta rik’o “Anas ina zakaje?”
“Bathroom ya amsata.”
“Dan Allah kar ka tafi please.”
“Fannah I want to use the bathroom ba tafiya zan yi ba, kibani just a minute.” Ai sam tak’i sake hannun nasa. Haka har bakin bathroom d’in tabi sa tana jiran fitowarsa se waiwaye waiwaye take kar mutumin yazo mata. “Anas kayi sauri dan Allah kaji?” Se buga k’ofar takeyi sam tak’i barinsa yagama biyan buk’antansa. Yana fitowa ta kama hannunsa ahaka suka isa kan gadon suka kwanta. Ta sake masa hannu ma tak’i.

Ahaka har tayi bacci, hannun nasa ya gwada cirewa daga nata amman gam ta matse cikin nata bibbiyu...


*© miemiebee*

b[truncated by WhatsApp]
[4:32PM, 8/29/2016] Rukayya: sorry ashe 57 suka sama number 58
[12:55, 12/18/2016] ‪+234 903 612 6826‬: •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫

❣🎀❣🎀❣

*_written by miemiebee👄_*

In dedication to *Aunty Sis💕*
5⃣8⃣




*A/N*
      *ASSALAMU ALAIKUM MASU KARATU INASON YIN AMFANI DA WANNAN DAMA DAN BAKU HAK’URI GABAD’AYA GAME DA RASHIN POSTING DA BAN SAMU NAYI BA JIYA, NAGAMA TYPING UNFORTUNATELY SEYA GOGE KANSA BEFORE I COULD GET TO SAVE IT.*
      *SECONDLY, TO ALL MY BLOG READERS INA ME BAKU HAK’URI DA PROMBLEM DA BLOG NAWAN YASAMU, I’M STILL WORKING ON IT. I HOPE ZAKU CIGABA DA SAMUN CONTINUATION D’IN WANNNAN LITTAFI WAJEN OTHERS KU KARANTA KAFIN AGAMA GYARAN, INHAR HAKAN BE YUWU BA KUWA NAKEGA NEW BLOG ZAN BUD’E WANDA ZAN SANAR DAKU NEW ADDRESS D’IN WHEN AM DONE.*
   *LASTLY TO ALL MY FANS DA SUKA MIN MAGANA TA PRIVATE JIYA DA KUMA YAU DA SAFE KUYI HAK’URI BARIN IYA SAMUN DAMA INYI REPLYING MESSAGES NAKU GABAD’AI BA SOBADA YAWAN CHATS SESA NA GOGE DUKA KAWAI, IN DAMA DAN GAISUWA NE TOH MIEMIEBEE NAGODIYA, INKUMA DAN JIN DALILIN DAYA HANANI POSTING JIYA NE GASHI NAYI EXPLAINING, IN KUMA SAB’ANIN HAKA, YOU CAN PING ME AGAIN.*
   *THANK YOU SO MUCH FOR YOUR LOVE AND SUPPORT. MIEMIEBEE LOVES YOU SO VERY MUCH*  


      Cikin baccin tace, “Anas dan Allah kar ka tafi please.” Alokaci guda kuma yaji wani irin tausayinta ya kamasa, bacci take amman idanunta basu bar zuban hawaye ba. D’ayan hannunsa yasa ya share mata hawayer. “Bar kuka kinji? I’m here.” Hannunsa ya raba da nata na k’arfi ganin yadda ta kama nasa gagam. Firgit ta tashi tana hawaye “Anas please don’t go.”
   “Ba tafiya zanyi ba Fannah” ya sanar da ita a lokacin dayake k’ok’arin kwantar da ita kan k’irjinsa. Bayan ya kwantar da itan ya soma shafa bayanta yana kwantar mata da hankali.
   “I’m here ba tafiya zanyi ba kinji?” Kai ta gyad’a cikin tsoro. Chan yaji nauyinta ya dad’u a kansa, beyi yunk’urin d’agata ba, barinta yayi ta cigaba da baccin gudun kar ya tayarda ita.

    Tunanin me yake sata mafarki haka yake. Waye mutumin? Mesa take kuka? Me ya tab’a mata? Me kuma take tsoron ze sake yi mata? Mesa kullum take irin mafarkin? For how long take erin wannan mafarkin dayake mugun tsorata ta haka? Me wannan mutumi ya mata? Har bacci yayi gaba dashi besamu amsoshi ga wad’annan tambayoyi ba.
    Asubar fari Fannah ta tashi a hankali ta bud’e idanunta, hannunta taja daga kan cikin Anas a hankali. Ta rasa meke sata mafarkin mutumin kullum kwana biyu, a da ne da abin yafaru take mafarkin kullum but as days passed by tadena yi kullum setayi kwana uku ma wani sa’in batayi ba amman tunda tayi aure takeyi kullum yanzu, kuma na yanzu yafi nada kayan ban tsoro. Me dalili? Bata kawo wani tunani a ranta ba ta miqe tayi alwala har a yanzu tsoro takeji mafarkin jiya yafi kowanne abin tsoro bayan tafito ta yi musu shimfid’a sannan ta tada Anas.
    Sun idar da Sallansu sunyi Azkhar suka koma kan gado. Pillow’nta ta matsar baya daga nasa tare da duk’unk’unewa cikin hijabinta tana kallon d’ayan side d’in. Anas ya karanchi hakan, yagano har yanzu tsoro takeji ga rashin maganar da takeyi yau kamar ba ita ba. Tausayinta yasake ji ya kama sa making him so anxious jin labarin mafarkin nata.
 
      “Fannah” ya kira sunanta cikin wani irin salo.
    “Na’am” ta amsa ba tare da ta juyo ba.
    “Are you still scared?”
   Kai ta girgiza masa tana matse ‘yar k’wallarta batadamu ko yana kallonta ko a’a ba.
   “I’m here for you kinji? Kibarjin tsoro ba mutumin da ze zo.” Yayi assuring nata. Kai ta gyad’a.
   “For how many months now kike mafarkin?” Bata masa k’arya ba tace, “7 years now.”
   7 years? Ya nanata a ransa, Allah sarki poor Fannah. “Turn and look at me.” Ya buk’ace ta. Ba gardama ta juyo hawayen da take ta k’ok’arin matsewa ne suka soma gangara. Hannunsa ya bud’a mata “come.” Matsowa tayi kusa dashi cije da tsoro, kanta ya aza a kan k’irjinsa. “Everything is going to be alright kinji? Stop crying.” Hannu yasa ya share mata hawayen. “Do you want to talk about the dream?” Kai kawai ta girgiza masa.
  “Even now that I’m your husband?” Ya tambaya cikin wani irin demanding salo. Kuka ta fashe da, “Anas nima bansani ba anytime na kwanta kawai se inji wai wani mutumi yazo yana bina ze gudu dani.” Ta masa k’arya dan battason sanar dashi sirrinta.

   “Shhhh! Is okay bar kukan, lets sleep.” Hannunta ta zagaya akan cikinsa ayayinda yake ta shafa bayanta har tayi bacci.

  ****
    Da misalin k’arfe 10:00AM Fannah na zaune shiru kan cushion, game data saba yin ma tak’iyi yau. Yanzu suka gama breakfast da Anas. Observing nata yake tun da suka tashi haka take ta acting strange, ya rasa me ze mata koda ya mata magana amsarta befin ‘eh’ ko ‘a’a’. “Fannah” ya kira sunanta a nitse. “Na’am” ta d’ago kai tana kallonsa. “Kinason kifita yau?” Kai ta girgiza masa da nufin a’a sekace ba ita ba..
     “In kaiki wajen Mami?” Batasan lokacin da ta saki murmushi ba “eh” ta basa amsa cike da jin dad’i. “Lets go then.” Dama abaya ne a jikinta, gyalenta ta d’auka tayi rolling tare da feffeshe jikinta da ture haka shima Anas d’in.
   
    Hannunta rik’e cikin nasa suka fice motan ma shiya bud’e mata da kansa ya rufe bayan ta shiga. Zaman tsit suke cikin motar chan da shirun ya masa yawa yace, “mesa bakisha ice cream naki ba? Bakiya son flavour’n ne?”
    “Inaso.”
   “Mesa bakisha ba toh?”
   “In muka dawo zansha in shaa Allah” ta amsa sa a takaice. Shiru ne ya sake ratsa su chan yace, “I miss your coffee” sincerely. Kuma hakan ne rabuwansa da coffeen ta he can’t even remember.
    “Muje office naka ko painthouse in had’a maka.” tace. Duk wannan magana da suke bata juyo ta kallesa ba shiko fuskarta yakeson kalla dan tayi kyau sosai, maroon jan bakin data sa ya mugun amsarta dukda kuwa fuskarta yad’an kumbura dan kukan data sha jiya dakuma yau da safe.
 
    “Fannah look at me.” Ya buk’ace ta ba musu ta juyo. Murmushi ya saki mata daga heart nasa, “kinyi kyau.” Murmushin ta mayar masa “thanks and you too.”
    “Nikam ai kullum ina yin kyau” ya gwada janta da surutu.
   “Yes Anas, kullum kanayin kyau.” ta fad’a tare da miyar da kallonta gare da windon. Daga yadda take maganar ya karanchi batason surutu. Be sake tuhumarta ba dan bayyason tak’ura mata, abinda ke damunta kad’ai ma ya isheta. Enterprise nasa suka nufa ya bud’e mata k’ofar dan neman magana ba rik’e hannunta yayi ba wannan karan. Hannun nasa ya zagaya a waist nata tsam ya matso ta jikinsa suna shaqan k’amshin turaren juna. Ko uffan batace masa ba, duk abinda zeyi yayi atleast sunada aure yanzu ba zunubi. Tun shigarsu cikin Enterprise d’in ake ta congratulating nasu. Bayan sun shiga office nasa ya zauna kan couch a yayinda ta ke had’a masa coffeen ba abinda yake banda binta da kallo, flask dam ta cika masa tare da sa masa cup ta kawo masa. Hannunta yaja ta zauna gefensa.

     “Thank you” yace da ita. Murmushi tamayar masa as a reply. Bayan ya kurb’e rabi yayi pausing. “Kefa zakisha?” Kai ta girgiza masa. “Why?” ya tambaya.
    “Toh ka tab’a min tayi neh?” Ta amsa tambayarsa da tambaya, abinda ya tsana kenan.
    “Da biyu kikayi hakan koh?”
  “Meneh?” Ta juyo tana kallonsa.
   “Again! Aswering my question with another question.”
   “I’m sorry Mr. Fauzi na manta rules naka ne.” Cup nasan ya mik’a mata da ragowar coffeen ciki. “Shanye lets go.”
     “Se wanda kasha zaka bani?”
  “Admit it Fannah kidena so kina kaiwa kasuwa, tunba yau ba kike kallona in ina shan coffee kinason sha daga cup d’ina. Na baki yau so kisha.”
   “Oh please Mr. Fauzi girman kanka yayi yawa wallahi, I pity duk wata macen dazata aureka.”
  “Kema haka I pity duk wani mijin da ze aureki, kisha lets go.”
   “Ni barin sha ba” ta fad’a stubbornly.
   “Okay shikenan tashi mukoma hotel namu toh, da rabon bakison ganin Mami.”
    “Haba! mana Anas me had’in shan coffee na da kaini gida gun Mami kuma?”
    “Nima bansani ba all I know is that sekinsha zan kaiki.” Harara ta watsa masa aiko yaganta.

    “Ni kike harara ko me ake kiran abun?”
    “A’a nifa ba harararka nake ba abu nagani agashin ka” ta masa qarya, nan tasa hannu cikin gashin nasa seyi take kamar tana cire abu. Chan taciro hannun nata. “Ina abun?” Ya tambayeta.
  “Na yasar.” Yasan sarai k’arya take kawai ya mata murmushi. Coffeen ta kurb’e tas ashe de da dad’i. Zata iya irga so nawa take shan coffeen befi sau uku ba dana yau kenan, gaskia she have been missing. Harshe taciro ta lashe lips nata. Kallonta yake in a cute manner.
   “Zaki k’ar” Sarai yasanta da ci zatace eh aikuwa ta gyad’a kai.
   “Toh baraki k’ara ba ai nawa ne tashi mutafi.”
   “Toh Anas I will make another one.”
   “Zaki b’ata min lokaci mutafi.”
   “Anas please.”
  “Fannah please lets go.” Haka Anas ya hanata shan coffeen. Ahmad yasa ya sauk’o masa da coffee machine da flask nasa ta yadda zata na had’a masa coffee always.

    Bayan isarsu gidansu Fannah ta ruga a guje tashiga da Mami ta soma cin karo hugging nata tayi har tana hanata nishi. Bayan sun zazzauna Mami ta kawo musu d’anwake me rai da lafiya yasha had’i kam. Bajewa Fannah tayi taci kamar ba gobe sekace wacce batayi breakfast ba kallonta kawai Anas yake ko tab’a nasa beyi ba saboda he is not a fan of d’an wake be iya ci ba, inma zeci sede ya tsotse zak’in kawai.
    “Baba na ya baka cin naka?” Mami ta tambayesa.
    “Bakomai Mami kawai ban iya chi bane, I'm sorry.”
   “Su Mr. Fauzi ajebo, gaba takaini” Fannah tace chan k’asa k’asa yadda Anas kad’ai dake kusa da ita ya jiyota. Ignoring nata kawai yayi. Plate nasan taja ta soma chi bayan data k’are nata.
   Afrah da Mami kam baki suka bud’e suna kallon ikon Allah. Cike da kunya Mami tace, “haba Fannah taya zaki d’au nasa kuma.”
   “Mami bakiji me yace bane? Cewa yayi baya ci, ajebo ne shi.” Cike da mamaki Mami ta bud’e baki zata masifeta. Da wuri Anas ya katse ta, “A’a Mami barta please, chi abin ki kinji?” Taci morethan half of plate nasa sannan tajita dam.
    “Mu tafi koh?” Ya tambayeta. “Mami zamu koma inason mu gaida su Ummie ma.” Kafin Mami tayi magana Fannah ta rigata. “Tafiya kuma Anas? Na d’au fa zaka ajiye ni ne kayi tafiyarka se anjima kadawo ka d’aukeni.”
   A ransa yace dake driver’n kine niba?
 
    A fili yace, “Fannah sweetheart kinsan zamuje mu gaishe dasu Ummie fah, ba time.” Ganin zasu fara muse-musen ma’aurta Mami tayi excusing kanta tare da jawo Afrah ma suka basu space.  
  Ganin haka yace, “Driver’n kine ni ai da zaki sani jeka ka dawo, tashi mutafi, aikinga su Mamin.”
   Fuska ta maraice “ayyah amman banga Baba ba fa yana bacci. Yi hak’uri please kabarni in wuni anan wallahi chan ba dad’i.”
    “Ohonki tashi mutafi, ina ni kike cema ajebo kina zagina, stand up lets go.”
   “A’a I take that back dan Allah kayi hak’uri.”
   “Nak’i tashi mu tafi.”
   “Anas please” ta shakwab’e fuska tana murza ido. Yasan sarai zata iya fashe masa da kuka anan. Nanne mami ta fito daga d’akin. Ganin ta cika hawaye a idanunta yasa hannu tare da rik’o fuskar natan, “muga yafita?” Iska ya hura mata a idon “sannu ko?” Kai ta gyad’  “eh ya fita.” Chan k’asa k’asa tace, “ka yarda?” Harara ya galla mata tare da gyaran murya.

    “Uhm Mami zan tafi , zan bar Fannah anan I’ll be back in d’auketa.”
   “Toh toh yayi kyau sannu ko Baba na?” Dad’i sosai Fannah taji sebinsa da kallo take har yasa takalmansa. “Adawo lafiya baby.” Juyowa yayi tare da sakar da best smile nasa. “Thank you” sannan ya fice.
   “Soyayya ruwan zuma...” Cewar Afrah tana gyad’a kai. “Su wani baby kuka samu sara?” Banza da ita Fannah tayi seda Mami takoma d’aki bakin Fannah ya bud’u. “Amman ke mena cemiki? Bance karki samin english wears cikin akwatunan da zan tafi dasu ba?”
   “Toh meh? Ai naga da english wears ake amarchi” nan ta kewaya taga ba Mami “Ya Fannah ya first night d’in? Kinyi kuka?”
   “K’asaran ki maras kunya kawai nima bansani ba.”
   “Heheh!” ta sheqe da dariya, “Toh Allah kawo zuriah d’ayyiba yasa du sharpshooters ne” nan iphone nata yayi k’ara alaman shigowar message. Tana bud’ewa taga airtime ne na dubu biyu hot baby nata yamata sending. Bayan tayi replying nasa tace a fili “Allah bar min kai yau akwai flexing a instagram da kallon stories a snapchat.”

      Har yanzu Fannah ta kasa rufe baki a iya sanin ta de Iphone 5s ce wayar Afrah how comes take rik’e 6s plus yanzu?
    “Ke ina kika samu wannan k’aton wayar? Waya baki?”
    “Wanne wai?” ta tambaya cike da tsiya. “Awww Iphone d’ina? Hot baby ya siya min wallahi, yayi kyau ko?”
   “Hot baby wa kenan?” ta kuma tambaya cike da rashin fahimta.
   “Wa kuwa inba Shettima darling ba, business nasa se bunk’asa yake wallahi.”
   Dariya sosai Fannah ta sheqe da dan tasan ina yake samun kud’in daya ke kashe mata. “Shi business d’in kenan?”
  “Eh mana abin hassada ne kuma?”
  “A’a babyn Shettima Allah barku tare ni taho ki tayani in shirya atamfofina gu d’aya dasu zan koma.” Afrah ta bud’e baki zata kuma wani zancen Fannah ta katse ta “a’a banason bayani muje.” Suna hira suna shirya kayakin har suka gama.

_11:30AM_

    Daidai nan Anas ya dawo d’aukanta beso sake shiga ba se kawai ya kira ta ta waya alokacin wayar tata na d’akinsu itako tana d’akin Baba se hira suke bazawa kamar ance ta mik’e tace bari taje d’aki. Tana shiga taji rurin wayarta nan ta d’aga tare da duban waye. ‘Anas’ taga tubuce kai. K’in picking tayi dan battason sake komawa hotel nasun nan its so boring. Se a karo na biyu ta d’aga nanma seda ya kusa tsinkewa.
    “Kifito I’m waiting for you.”
   “Anas mana please, bamu had’u da Aiman bafa, tana school se 1:00AM zata dawo kaji? In jira?”
   “Banji ba kuma baraki jira ba, Fannah kifito don’t let me repeat myself.” Karap ya katse wayar, tsuka taja. Aiko ya fad’a kunnen Mami. “Keda waye ne?” 
  “Erm.. Ermm...” kafin ta had’o k’arya Mami tace, “keda Anas ko? Fannah tun ba’ayi nisa ba kin soma masa rashin kunya, iyyeh? Me dalili?”
   “Mami waifa har ya dawo infito mu tafi.” ta fad’a tana turo baki.
   “Toh se meh? Out!” ta nuna mata k’ofa. Dake kafad’a tayi. “Fannah zan sab’a miki fa!” Haka kamar wacce zatayi kuka taja akwatinta ta fice ko sauraron Afrah batai ba. Bayan fitarta ta bud’e gidan baya tasa akwatin yana kallonta bece komai ba. Tana shiga ya kunna motar ba wanda yace ma wani ko uffan. Bayan isarsu gida suka gaggaisa, Ummie kamar ta cinye Fannah. Besamu ya had’u da Amal ba dake tana school haka Shettima ma.

     “Kuyi sauri ku gama gaisawan ku zan d’au abu cikin d’akina ne yanzu mukoma.”
     “Kai Babana daman ba yini kuka zo mana ba?”
   “Yini? A’a fa Ummie gaisuwan minti biyar ne kacal.” Yana kaiwa nan yashige d’akinsa. “Oh! Fannah kinga halin mijin naki ko? Yafiye rowa dayawa.” Murmushi cike da kunya ta saki tana kare fuskarta.

     Bayan shigan Anas d’akinsa ya nufa wajen safe dan ciro kud’ad’ensa wanda ze buk’ata to his suprise yaga  an kwashe kusan rabin kud’ad’en. Dubawa dakyau ya kuma yi yaga eh fa kud’in nasa ne babu to waye ya masa wannan d’anyen aiki? Rufewa yayi tare da dawo

Please Login or Register in order to submit comment