Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba amsani zeyi ba.”
   “Bakomai Ummimi zan masa in shaa Allah seda safe” ta rufo mata k’ofar.

****
   Bayan Anas ya kashe musu wuta suna kwance kamar yadda suka saba Fannah ta kira sunansa, “Habeebi.”
   “Yes Flower.”
   “Thank you so much for everything.” Ta fad’a tare da sake shigewa jikinsa.
   “You don’t have to thank me Flower, ma godiyan me kike?”
   “Aika fini sani d’azu Mami takirani tace in maka godiya mekayi musu, nayi nayi da ita ta fad’amin tak’i.”
   “Haha!” yayi dariya kad’an “hakane?”
  “Eh mekayi musu?”
   “Babu.”
  “Kamar ya babu Habeebi duk alkhairun da kake musu da a baya Mami bata tab’a cemin na maka godiya kamar na yau ba meh ka musu please?”
    “Nace miki babu lets sleep tomorrow is a big day.”
   “O’o ni seka fad’amin wani alkhairi kamusu.”
   “Nace miki babu please kiyi bacci ko Hanan ma zata samu tayi, goodnight” yayi pecking kanta. Shiru tayi chan ta kira sunansa “Habeebi.”
   “Yes Flower lets sleep.”
  “Thank you kaji? Allah k’ara bud’i.” Magana yake cike da gyangyad’i “Flower nace miki banason godiyan nan.”
   “Bakasan akan mefa nake maka godiyan ba.” Ya nisanta “akan meh?”
    “Ummimi ce tace na maka godiya.” Shiru yayi bece komai ba. “Kaji My Lion?” Nan ma shiru data d’ago kai ta kallesa setaga idanunsa a rufe she is sure ba bacci yake ba, bayason maganan Ummimi ne. “Liar nasan ba bacci kake ba kadeji Ummimi tace ta gode” nanma bece komai ba murmushi ta saki tare da jan hancinsa. “Awwch!” Ya sakar da k’ara “kinsan da zafi koh?”
    “Aww! kana jina kamin shiru kenan.”
   “Sa’an ki d’aya Baby Hanan if not da na rama.” Gwalo ta saki masa sannan yajata jikinsa suka kwanta***

    _washegari..._
   As early as possible suka shirya luggages nasu duk na acikin mota Anas yabari asa akwatin Ummimi a motansu yak’i taxi aka tsare mata ta shiga ciki, kusan a tare suka isa airport akayi musu ciki da akwatinansu. A sama su Fannah suke a yayinda Ummimi ke k’asa ita kad’ai ba yadda Fannah batai da Anas yabar Ummimi ta samesu ba yak’i.

_2 hours later..._
     Miqe Anas yake kan wani medium sized bed se baccinsa yake sha ayayinda Fannah ke zaune a d’ayan side d’in da Qur’ani a hannunta se karatu take tayi daidai takai inda k’arfinta ya k’are ta tsaya tare da miqewa ta sauk’a k’asa gun Ummimi as always ta sameta ta ta had’a tagumi bayan ta zauna a gefenta ta dafe kafad’arta se anan Ummimi tasan da shigowarta. “Fannah” takira sunanta a bit suprised.
   “Na’am Ummimi kin zauna shiru ko TV ne ki kunna mana.”
   “A’a barshi karki damu, ya Anas yake?”
   “Yana bacci kema ya kamata ki kwanta.”
   “A’a nikam, se hankali a kwance ake iya bacci ai.” D’an murmushi Fannah ta sakar mata “toh ga Qur’ani ki karanta” ta miqa mata. “Nagode kema kije ki huta wannan hawa da sauqan ze dameki kinga already k’afafuki sun kumbura.”
   “Toh Ummimi.”
  “Nace yaushe ne jikan nawan ze fito?” D’an dariya ta saki dan kunya ma takasa fad’a mata. “Surikar tawa tana jin kunya na ne?” Ummimi tayi teasing nata.
    “Nanda wata uku in shaa Allah.”
   “Ahh ashe ma kin kusa toh Allah raba lafiya ‘yata Allah ya sauk’eki lafiya.”
   “Ameen Ummimi nagode barinje in huta nima.”
  “Yawwa ‘yata” ahaka suka rabu beside Anas taje ta kwanta alokacin har ya tashi. “Flower ina kikaje?”
   “Gun Ummimi.”
  “Baraki koyi zama gu d’aya ba ko kinga k’afafunki kuwa? Wai bakiya jin tausayin kanki ne?”
   “Habeebi please ya isa ai dama kumburin dole ne kaide kace kanason min surutu ne saboda gun Ummimi naje inda toilet nace na shiga ai barakayi magana ba.”

    “Ohkayyyy haka kika ce? Toh har mu isa banason kisake sauk’a wajenta am not asking you am ordering you as your husband.”
   “Sekayi ai” tayi maganar k’asa k’asa.
  “Kuma najiki nide na fad’a miki.” Baya ta juya masa ba tare da tace komai ba haka tundaga nan bata sake masa magana ba kodaya tasheta Sallan Azahar haka La’asr ma shima be mata magana ba.
    10 hours ya d’aukesu sannan suka iso Nigeria inda suka sauk’a a Sandralia Hotel Abuja har anan Fannah bata sake ma Anas magana ba, ruwa ta watsa taso shiga duban Ummimi amman Anas ya hanata. Bayan ta shirya cikin kayan baccinta ta zauna kan gado tana ma kanta tausa a k’afafunta, fitowan Anas daga wanka kenan singlet da nickers yasa ya hauro gadon yana k’are mata kallo.
   “Flower.” Shiru tayi bata tanka sa ba. Kusa da ita ya matso “Flower bara kimin magana ba?” Nanma shiru se massaging kumburarrun k’afafunta take hannunta ya d’aga daga kan k’afan nata nanma bata ce masa ko k’ala ba. “Flower wai barakimin magana?” Nanma shiru. “Okay I’m sorry kinji? I’m sorry.”
  
    “Kasakemin hannu as you can see am massaging my legs.”
    “Flower I said I’m sorry.”
   “Naji sakeni toh.”
  “Bari zan miki.”
  “Banaso zanyi abuna da kaina.”
  “I’m sorry” ya sake hannun nata tare da kama kunnuwansa ko kallonsa batayi ba ta cigaba da massaging k’afanta. “Flower please.”
  “Wai hak’urin me kake bani? Nace kamin laifi ne?”
   “Baki fad’a ba amman nasan na miki laifi and I’m sorry kije kisameta in kinaso.”
   “Banaso” ta fad’a stubbornly.
  “Yi hak’uri mana Mom Hanan” ya sake matsowa kusa da ita closing the gab between them, gashin kanta data barbaza a kafad’anta yahau shafawa. “Yi hak’uri kinji barin sake ba.” Kallonta ta miyar garesa “I’m sorry sweetheart” d’an murmushi ta sakar masa ma’anan ta huce. “Thats my woman!” Lips nata yasoma laluba bata hanasa ba se dab da bakinsu ya kusa had’iye tasa hannu ta kama mai baki “no kisses today thats your punishment” tayi maganar tare da miqewa daga kan gadon ta sanya hijabinta.

   “Oh common please Flower ko peck ne.”
   “Nace NO! Gobe zaka sake repeating abinda kayi yau.” Tana kaiwa nan ta fice zuwa d’akin Ummimi.

   Some minutes later ta dawo har anan Anas beyi bacci ba yana jiranta, a nitse ta cire hijabin ta haye gado ta kwanta ganin bata matso kusa dashi ba yasa ya matso dakansa tare da zama. K’afanta ya miqar kan cinyansa sannan ya fara mata massaging.
   “Ta nan ka b’ullo kenan? Saboda in ka gama in baka kiss as token of appreciation, uh-uh yau ba kiss na fad’a maka smart guy, wannan logic nakan bareyi aiki ba yau.” Dariya yaso yi dankuwa ta kamasa amman seya matse.
    “Ni ba haka nace miki ba am massaging your legs because I love to”
“Humm! Allah sa de, nagode” bayan daya gama yaja d’ayan ma yamata godiya ta masa sannan ya kashe musu wutan ya koma ya kwanta agefenta yana wasa da gashin kanta duk wani salo nashi yayi applying amman Fannah tak’i bari yayi kissing nata haka yatayi har ya gaji seda tajishi yayi shiru sannan ta juyo tana kallon shi unexpectedly tayi pecking nasa a lips. Kafin ta d’ago kanta ya riqeta gagam yasoma sarrafata haka sukata romancing junansu har seda bacci b’arawo yayi gaba dasu.

   

*© MIEMIEBEE*

beeenovels.blogspot.co.ke
[13:00, 12/18/2016] ‪+234 903 612 6826‬: •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫

❣🎀❣🎀❣

*_written by miemiebee👄_*

In dedication to *Aunty Sis💕*

9⃣3⃣









_washegari..._
Da safe Anas ya tashi yayi wanka sannan ya had’a wa Fannah ruwan ta itama tayi, dakansa ya shafa mata mai ya cire mata d’aya daga cikin had’ad’d’un maternity gowns nata tasa sannan suka karya. “Habeebi ya naga kana zipping mana akwati?”
“Yes Baby zamu wuce Maiduguri yau ina zaki iya ko mu bari se gobe?”
“No its okay with me toh baka sanar dani ba bale in fad’awa Ummimi, barinje in ce mata ta shirya.” Hannunta ya riqo da wuri “no Mom Hanan baramu tafi Maiduguri da Ummimi ba anan Abuja zan barta zan mata renting gida tayi zamata anan we don’t need her again.”
“Haba My Lion wani erin magana kake haka? Ita da wa zaka barta anan?”
“Ita kad’anta kamar yadda muka sameta ita kad’ai a NY ai dama cemin kikayi zamu dawo da ita 9ja bawai zata bimu gida ba.”
“Oh Habeebi wallahi banajin dad’in abinda kakeyi ko kad’an banaso haba mana Ummimi fa mahaifiyarka ce ko kak’i ko kaso itace mother’nka baka iya canzawa.”
“I know ba abinda zan iya thats why I need her out of my life.”
“Wai meke damunka ne Baby? Nifa ba haka nasanka ba Ummimi is following us home.”

“Sede in ke zaki biya mata kud’in jirgi which I’m not allowing you.’
“Fine karka bari zan kira Abuu in sanar dashi I’m sure shi ze biya mata.”
“No Flower you are not doing that I forbid you to call him wai mesa kikeson muna fad’a ne? I’m your husband amman ko kad’an bakiya jin magana na, Ummimi is not following us and that stays that period!” Ya fad’a a tsawace tare da matsawa yakoma kan kujera ya zauna. Kuka ta tsaya tanayi a wajen chan takoma kan gado ta zauna se kuka take wanda ke mugun tayar wa Anas da hankali gani yayi kamar ze iya jure sautin kukan nata amman ina he can’t. “Flower wai baraki bar kukan ba?” K’ara k’arfin kukan nata tayi cike da tashin hankali ya matso kusa da ita yana aza hannunsa ajikinta taja da baya.

“Flower kibar kukan mana wai ke bakisan its bad for your condition bane?”
“Kai da kasani kuma kake sani kukan fah? Ni ka tashi min akai” ta juya masa baya. Gadon ya haye yadawo ta inda take fuskanta. “Ya isa toh I’m sorry Flower ke kike sani miki masifa nace miki banason zancen Ummimi amman bakiya ji sekita min maganarta. Kiyi hak’uri kinji? Kidena min magananta se baramuna samun midunderstanding ba.” Baki ta murgud’a mai “ni katashi min kuma barin iya tafiyan ba yau mara na naciwo.”
“Toh naji sannu, se gobe zamu tafin kenan.” Ta gyad’a mai kai “kuma ni barin tafi ba seda Ummimi.”
“Kingani koh?”
“Toh Habeebi wani erin magana kake please?” Ta tashi ta zauna “taya zamu taho da ita 9ja kuma semu barta anan ita kad’ai ai gwara ma ace tun farko mun barta achan NY, ni gaskia in bada Ummimi ba barin bika ba.”
“Se mu gani ai” daidai ze juya kenan tariqo hannunsa “Habeebi please dan Allah kayi hak’uri mu koma da Ummimi please Habeebi kamin wannan ka gama min komai Habeebi please don’t say no please please sweetheart, the father to my children please say yes kaji Baby? Say yes please.” Shiru yayi bece komai ba dawowa tayi ta zauna kan cinyansa “please Habeebi say yes kaji my Baby?” Nanma shiru “Sweetheart please...”

“Toh inta bimun aina zamu ajiyeta?”
“A gidan mu zata sauk’a for the meantime.”
“A gidanmu? No barin kaita gidana ba never.”
“Toh naji ba’a gidanmu ba, a gidanku nasan Abuu ze bata d’aki inbe bata ba ko gun Mami zan kaita please say yes Habeebi.”
“Naji” amsar daya bata kenan. Hannayenta ta zagaye a wuyansa tare da pressing masa hot kiss “I love you Habeebi, I love you so much” tayi pecking nasa a kumatun damansa sannan a na hagu se tip na hancinsa “mufita sight seeing (ganin gari) yau kasan bansan cikin Abuja ba.”
“As you wish Mom Hanan” yayi pecking lips nata “sa hijabinki muje.”
“Yauwa Abu Hanan zamuje da Ummimi?”
“Bansani ba in zaki tashi muje toh fine inkuma a’a muyi zaman mu.”
“Dama wasa nake nasan ba yarda zakayi ba” daidai zata mik’e kenan Hanan tayi kicking. “Habeebi Habeebi! Hanan moved tayi motsi!” tasa hannunta daidai inda tajiyo motsin, shima hannun nasa yasa wajen kad’an kad’an sukejin motsinta nan da nan suka fita basu suka dawo ba se kusan Maghrib Sallah sukayi Fannah ta wuce d’akin Ummimi inda ta sanar da ita zasu wuce Maiduguri gobe.

Hira kad’an suka tab’a Fannah tamata seda safe ta dawo d’akinsu anan suka kwanta da wuri kasancewar zasu hau hanya gobe.

****
K’arfe 10:30AM su Fannah suka isa Maiduguri already driver na jiransu a airport, anan ma sam Anas yak’i barin Ummimi shiga motansa haka ta shiga taxi gidansu suka fara wucewa inda shida Fannah suka shiga suka watsa ruwa aka bar Ummimi cikin taxi tana jira, Fannah tayi tayi da Anas yabar Ummimi ta shigo ta watsa ruwa itama amman yak’i ba yadda ta iya haka ta hak’ura bayan sun sake shiri suka fito suka wuce gidansu Anas. Daidai gaban gate Anas ya tsaya bayan me gadi ya bud’e gate ya shiga, itako Ummimi a waje driver ya ajiyeta da kud’in da Fannah ta bata ta biya sa.
Fitowar Fannah daga mota ta kama hanyan waje dan shigo da Ummimi ta soma tafiya kenan Anas ya tsayar da ita.
“Flower where to?”
“Zan shigo da Ummimi ne kafara shiga we will follow afterwards.”
“Mschw! Wai ita batasan hanyan ciki bane da sekin shigo da ita? Ni kidena wahalar min da Hanan akan Ummimi.”
“I’m sorry Babe yanzu zan shigo da ita ko zaka jira ni neh mu shiga tare?”
“Mschw! You are trying me koh?” D’an murmushi ta sakar masa sannan ta fice a waje ta samu Ummimi.
“Bismillah mushiga daga ciki Ummimi.”
“ ‘Yata nace gidan da muka baro d’azu shine naku dana Anas?”
“Eh Ummimi.”
“Masha Allah gidan naku yayi kyau sosai kamar a ture wallahi.”
“Kai Ummimi mungode Anas ne yayi desinging gidan da kansa kinsan architecture ne ayanzu haka shine CEO na Flames Enterprises one of the biggest Emterprise a Nigeria in whole, he is being referred to as Nigerias youngest billonaire, Ummimi ki godewa Allah Anas naki is very bright.” Hawayen jin dad’i ne suka soma gangaro wa Ummimi “Alhamdulillah! Oh! Allah sarki Anas Allah ya cigaba da mai bud’i ya kare shi daga sharrin maqiya, ameen.”
“Ameen Ummimi mu shiga.”
“A’a Fannah tukuna, ina ne nan?”
“Nan gidansu Anas ne mushiga Abuu na ciki.”
“Kina nufin wannan babban gidan na Abuun su Anas ne?”
“Eh Ummimi”
“Allah mai iko, me azirtawa dakuma talautarwa, Allah sarki ban kyauta wa kaina ba wallahi ko kad’an, da ace na k’ara hak’uri na cigaba da zama da Ya Ibraheem da atare zamuyi wannan arziki, Allah cigaba da masa bud’i yakuma rabamu da sharrin shaid’an gabad’aya.”
“Ameen Ummimi mushiga.”
“Fannah banida courage na shiga, ina tsoro nasan cikinsu ba wanda zeyi accepting d’ina sabida abinda na musu da ciwo zasu ce ban tashi dawowa ba sedana ga Ya Ibraheem yayi arziki, please ki kaini wani gun daban kokuma in zan iya tuna hanya in je gidanmu that is in iyayena suna raye.”
“Ummimi just trust me kinji? Mushiga ciki please na tabbata idan duk sukaji labarin ki zasu yafe miki musamman ma Shettima I know him shi ze fara accepting naki” Hannu tasa ta share hawayen nata sannan tabi bayan Fannah hannunta riqe cikin na Fannah.

Amal na bud’e k’ofa taga Anas ne tsaye jikinsa ta d’ale tana mai oyoyo!
“Ya Anas I missed you so much, shine zaku dawo baku sanar dani ba tun shekaran jiya nake trying numban ka dana Ya Fannah basu shiga.”
“Sorry Angel we wanted suprising you su Abuu suna ciki?”
“Yes kowa na gida ina Ya Fannah da Hanan d’ina?”
“Gata chan!” yayi mata nuni da yatsa. Tafe Fannah ke da Ummimi behind her.
“Ya Anas ita da wa wancan?”
“Nima bansan taba kinsan me nakeso dake Angel?”
“A’a” ta girgiza mai kai.
“Karki kuskura kimata magana kinji? Koda ta miki karki mata magana she is a bad person.”
“Really Ya Anas? Mesa toh?”
“Trust me kinji Angel? Karki kuskura kimata magana” Yayi pecking nata a goshi. Alokacin da su Ummimi suka gama k’arisowa Amal ta ruga tayi hugging Fannah har agarin haka ta bige mata ciki.

“Amal kinason kijiwa Hanan naki ciwo ne?”
“A’a Ya Fannah barin k’ara ba its just that I missed you wallahi gashi munyi hutu ba gun zuwa Ya Shettima kullum na cikin bullying d’ina.” duk maganganun nan datake bata kalli Ummimin da tayi mutuwan tsaye tana kallonta ba ko kyaftawan ido ba.
“Aiko ga Ya Anas naki ya dawo seki kai masa k’orafi.”
“Haha! Ai kibari Ya Anas yace ze rama min ko Ya Anas?” Tayi maganar tana k’ok’arin maida kallonta kan Anas a garin haka idanunta suka sauk’a kan Ummimi da idanunta suka ciko dam da hawaye ganin ‘yar data bari a cikin tsumma ne ta girma haka tazama babbar budurwa kuma kyakkyawa. Kallon cikin ido suka tsaya sunayi wa juna na kusan minti biyu, wani erin yanayin da Amal bata tab’a tsintan kanta ciki ba tasoma yau.
Aina na santa? tambayar data ke tayi wa kanta kenan. “Amal” cewar Ummimi tana mata murmushin daya zame mata dole. Ta bud’e baki zata mata magana kenan seta tuna abinda Anas yace mata sekuma tayi shiru.

“Amal barakiyi mata magana bane? Bakiji ta kira sunan kiba?” Cewar Fannah.
“Baruwanki, bata santa ba taya zata mata magana zo Angel d’ina na siya miki iphone 7s ma taho kinji?”
“Dagaske Ya Anas yeyy!” Taje tayi hugging nasa. “Ina yake Ya Anas?”
“Nachan gida tare zamu koma yau zaki kwana mana ba?”
“Yeyyy!!! Mushiga ciki toh” dake hankalin ta har a yanzu na yara ne anan ta mance da chapter’n Ummimi taja hannun Anas suka shige ciki.
“Ummimi please karkiyi kuka dan Allah, nasan da akwai k’wararren dalilin dayasa Amal tak’i miki magana Anas ne ya hanata kuma jin maganansa take har fiye da yadda takejin na Abuu, duk abinda yace mata yi take but karki damu with time zaku saba she is fun to be with mushiga daga ciki.” Da k’yar tayi convincing Ummimi data kariya da reaction na Amal tabita suka shige ciki bakowa a parlourn illa Anas dake a dining space yana shan ruwa bayan ta zaunar da Ummimi kan kujera ta nufa inda Anas yake.
K’asa k’asa take maganar ta yadda Ummimi barata jisu ba. “Habeebi yanzu abinda kayi ka kyauta kenan?”
“Menayi kuma yanzu?” ya bud’e goran ruwan ze kai baki tasa hannu ta k’wace. “Ma tambaya na kake ko? Mena hana Amal yima mahaifiyarta magana?”
“Haka Amal tace miki ni na hanata? Ma in ni na hanatan toh ina
ruwanki? Tsakaninsu su biyu bata santa ba taya zata mata magana bani ruwana insha.”
“Barin bayar ba.”
“Ki riqe akwai wani cikin fridge d’in ai” daidai zebud’e kenan tasa hannu ta taresa. Murmushi ya saki “I will excuse you Flower saboda dama mata masu ciki sunada taurin kai.” pecking nata yayi a goshi wanda tuni ta tunkud’esa, killer smile nasa ya kashe mata “Shettima! Shettima!” Yau hau k’wala masa kira. Daidai nan Ummie da Abuu suke fitowa har Amal taje ta sanar dasu dawowan su Anas dawata mata me kama da ita da Anas harma da Shettima kad’an kad’an.

“Oyoyo! Mutanen New York ne a gidan namu, maraba lale!” cewar Ummie alokacin data ga Fannah, hugging nata tayi ahankali gudun karta jimata ciwo anan sukayi exchanging greetings. Ummimi dake a parlour ba abinda take se kallonsu hawaye na bin k’uncinta.
“Me kuke tsaye anan?” Abuu ya tambayesu.
“Uhm ruwa nazo d’aukawa Anas” Fannah tamai qarya “gashi Anas” murmushi ya saki sannan ya karb’a.
“Toh mu k’arasa parl-” be samu daman k’arisa maganan ba kasancewan ido hud’u da sukayi da Ummimi kwata kwata ya kasa amincewa da abinda idanunsa ke gane masa cewa ma yayi ko imagination nasa ne kawai, Ummie ma was at shock alokacin data ga Ummimi she couldn’t believe it either.

Cike da rashin yarda Abuu ya juyo yana kallon Anas fuskarsa d’auke da son k’arin bayani har b’ari bakinsa ke. “A.. An.. Annas wac..wacce wancan?” yana nuna Ummimi da yatsa, shida Ummie suka kasa kunne suna jiran amsar sa. Daidai nan Amal ta falfalo da gudu, Shettima na biye da ita yana huci sanadin d’aukar masa cookies dayayi niyyan kaiwa Afrah da tayi.
“Ai wallahi yau se jikinki yayi tsami, sa’an kine ni da zan ajiye abu ki d’auka har kichi?!”” Yayi maganar se binta yake a yayinda take ta gudu tana kiran sunan Anas “Ya Anas! Ya Anas! Shettima ze min duka.” Suna isowa dining area’n duka suka sa full stop tuni Amal tayi bayan Anas. Ganin Abuu Shettima ya dakata kaman ance ka juya ya juya idanunsa se akan crying Ummimi. Idanunsa ya zaro sosai kamar ze ciresu sam shima ya kasa yarda da abinda idanun nasa ke gane masa. “Abuu wace wancan?” Abinda ya iya tambaya kenan.

“Ya Anas meke faruwa haka? Ya naga su Abuu sunyi shiru.” Amal ta tambaya.
“Anas magana nake maka wacece wancan?” cewar Abuu.
“Abuu Nima bansanta ba Flower keda kika kawo ta seki musu bayani” anan duk suka maido da kallonsu kan Fannah suna jiran amsarta seda ta kalli Ummimi sannan ta kallesu bakinta ya bud’u “Abuu wancan Ummimi ce, Ummimin ku.”


*© MIEMIEBEE*


beeenovels.blogspot.co.ke
[13:00, 12/18/2016] ‪+234 903 612 6826‬: •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫

❣🎀❣🎀❣

*_written by miemiebee👄_*

In dedication to *Aunty Sis💕*

9⃣4⃣





  “Um... Waye?!”Abuu yayi maganar cike da k’in yardan abinda Fannah tace.
   “Eh Abuu Ummimi ce” ta sake tabbatar masa, juyawa yayi ya miyar da kallonsa a gareta “Aysha?” Yayi questioning nata hawaye ne ke ambaliya kan fuskarta “nn..na’am Ya Ibraheem”
  

Please Login or Register in order to submit comment