Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wa d’an adam. Ita dashi har abada in shaa Allah ta gommaci talauci ya kashe ta data sake masa aiki.
 
     _One week later..._

    Haukacewa ne kawai Anas beyi ba yarasa me ke ajiye Fannah har yanzu batazo neman aiki gunsa ba. Gashi koya tura Idrees ce masa yake Fannah bata fita, toh why? Ta hak’ura da neman aiki kenan komeh? Bare iya explaining ya yayi missing coffeen ta ba tun rananda tabar masa aiki har ila yau baicin abinci kamar yadda ya saba ci da. Shi yanzu abu d’aya ne yasan inya aiwatar dolen Fannah zata dawo masa aiki shine in zeje gidansu, gashi dama Idrees yamasa bayanin yadda gidansu Fannah yake basuda arziki. Wayarsa ya d’auko ya kira Ahmad. “Hello Boss good day.”
   “Yawwa kaje ka d’au credit card d’ina cikin mota a bud’e ne kayi duk siyayyan dakasan magidanci zeyi wa family’nsa I mean food items, kayan sawa home appliances komi da komi ka gane?”
    “Yes Boss angama.” Nan ya katse wayarsa. “In baraki dawo ba Fannah I will force you to.”

    _5 hours later..._

    Anas na zaune a office nasa yana jiran call daga Ahmad baya son se Maghrib yayi, aikuwa a lokacin Ahmad ya kirasa “Hello Boss komai is in place kamar yadda ka buk’ata motan kayan na nan pake a bakin main gate.”
     “Good gani fitowa.” Turare ya sake feshe jikinsa dashi ya giara gashin kansa ya tabbata he is looking okay sannan ya fice. Motarsa ya shiga motan kayan kuwa Ahmad ne ciki yana gaba Anas na biye dashi har gaban gidansu Fannah suka tsaya. Sosai yasha mamaki ashe saisa Fannah batta wasa da aikinta ashe basu da k’arfi ne sosai. Kallon gidan ya tsaya yi dan ko a Bama gidansu yafi wannan kyau.

    Daidai lokacin Aiman ta taso daga islamiya se b’antare charbin Malam dake hannunta take tana nufowa kusa da gidan alokacin data d’aga fuskarta Anas yaga alaman kamannin Fannah tattare da ita nan take ya yanke hukuncin kasancewar ‘yar yarinyar k’anwar Fannah. Daidai tazo shiga gidan ya dakatar da ita ta hanyan kiran ta da “‘yan mata.” A hankali ta d’ago kai tana kallonsa bata gane kamanninsa ba kasancewar yasa sunglasses.
   “Wace ‘yanmatan” ta kalli left and right “ni? Barin d’an maka tambaya bature ne kai please naga kayi fari dayawa”
   Dariya sosai Anas ya tsaya yi sekace ba shi ba, kawai se yarinyan ta tuna masa da Angel nasa Amal.
   “ A’a ni ba bature bane ‘yanmata”
   “ Nifa kadena cemin ‘yanmata, ai Ya Fannah tace ni yarinya ce ba ‘yan mata ba wai ita da Ya Afrah ne ‘yan mata.”
    “Toh Ya Fannah ta miki k’arya ai ‘yan mata ce ke.”
   “Toh kaikuma fa? Samari?” Ta tambayesa tana jefa charbin malam data b’are a baki tare da taunawa.
    “Ni big uncle ne suna na Anas, kinacemin Ya Anas.”
   “Ya Anas.. Ya Anas ni Aiman a ina na tab’a jin wannan suna?” Ta tsaya tana tambayar kanta.
   Yana ciro glasses nasa aiko kamanninsa ya bayyana.
  “Laaaaa!!! Blue eyes na TV. Me kazo yi agidan mu? Ashe ba bature ne kai ba, kazo ne muma asamu a TV’n?”
   Dariya sosai yake wanda ya mugun masa kyau, fararen hak’waransa suka bayyana, dimple nasa d’aya ya lotse. “Kinasan kiga kanki a TV?”
  “Eh mana ai social studies teacher’n mu tace celebrities kawai ake gani a TV nima inasan in zama d’aya.”
   “Toh kar ki damu, yanzu kizo ki kaini cikin gidanku.”
“A'a'a'ahhhh chabdi! Ai Ya Fannah ta hana. Maza basu shiga gidanmu gaskia me blue eyes kayi hak’uri karka sace min iyaye da yayu. You are a stranger.”

   “Kefa kikace kina gani na a TV karki damu b abinda zan miki. Ahmad ina sweet d’incan?” nan Ahmad ya koma mota ya ciro packet na sweet Anas ya amshi, “ungo zo ki karb’a.” Ya fad’i yana mik’a mata.
    “Blue eyes tsakanin ka da Allah baka sa abin sace yara ciki ba?” dariya sosai Ahmad yake.
   “Kice min Ya Anas ba blue eyes ba.”
    “Toh Ya Anas.” Ta fad’a yawunta na d’iga k’asa.

      “Bari kiga” nan ya bud’e ya ciro d’aya tare da sha “kinga ba abinda yamin. Zoki karb’a se ki kaini gidanku. Ya Fannah tasanni, nine Mr. Fauzi. ”
    “Ohhh ashe kaine me sa Ya Fannah kuka.” Yi yayi kamar be jita ba yace, “karb’a mu shiga toh.” Ba musu ta amshi pack na sweet d’in “muje toh Ya Anas.” Bayan ta yabi suka shiga gidan kam ba laifi tsatsaf ba k’azanta.
    “Mami! Ya Fannah! Ya Afrah! kufito munyi bak’o kuma ya bani sweet har packet.” Fannah ce ta soma fitowa ko hijabi batada ‘yar vest ne kawai jikinta tana shan iska.

      “Aiman ban hanaki shig-” bata k’are maganar ba suka had’a ido hud’u da Anas ai a guje ta koma ciki se nishi take. K’wak’walwar Anas sanda yabar functioning na d’an lokaci ganin Fannah ba kayan arziki. “Ke Ya Fannah wa kika gani haka kike wannan nishi” cewar Afrah dake game as always. Kasa magana Fannah tayi kawai waje take nuna mata da hannu. “Meh gamo kikayi?” Kai ta kad’a mata still tana nuna waje. Kafin Afrah ta tashi suka jiyo muryan Mami na masa lale su Mami anga Mr. Fauzi. Lek’awa Afrah tayi tagansa zaune kan tabarma d’aya da Mami.

    Ashe haka bawan Allan keda kyau, yama fi kyau a fili akan a gidan TV lallai Allah yayi hallita. “Ya Fannah Mr. Fauzi nefa! Mr. Fauzi a gidanmu!” ai da gudu tayi wajen sa kayansu taciro kayan sallarta. “Ki sa hijabi mu fita mu gaishe sa. Ma meyazo yi tukun? Halan bikonki” Duk ta kidime se suratai take tayi.
      Hannunta Fannah ta rik’o “ke jakar ina ce? Ina zaki? Meh Mr. Fauzi yazo yi gidan mu? Nashiga uku Allah sa ba sharri ya taho dashi ba.” Afrah ta bud’e baki zatayi magana suka jiyo kiran Mami “Fannah! Afrah! kufito mana Mr. Fauzi nefa yazo.”
    “A’a Mami Anas de” cewar Anas sewani behaving yake kamar d’an arziki. “Kufito da sauri” Mami ta sake k’olla masu kira. “Toh” Afrah tace. “Ya Fannah kiyi sauri.”
  “O’o ni barin fita ba ni yama yasan gidanmu? Ya Allah help me!” Hannunta Afrah ta fisga daga rik’on Fannah ta fice a guje har k’asa ta gaishe da Anas ya amsa da fara’a se murmushin show off yake. “Aiman kawo wa Ya Anas ruwa kinji?”
   “A’a Mami ta bari daga office nake yanzu naci abinci.”
   “Allah Babana ko ruwa bara ka sha ba?”
   “Eh Mami, ina Baba? Ya jikin nasa?” Fannah dake mak’ale jikin window tana jinsa ji take kamar taje ta shak’uresa ji yadda yake abu kamar d’an arziki.
   “Jikin Baba da sauki. Afrah ina Fannah newai? Fannah!” Ta danna mata kira.
     “Na’am Mami” ta amsa kan wanda zatayi kuka. “Kifito mana me kikeyi ne?”
    “Mami gani nan.” Hijabi ta zumbura sewani kumbure kumbure take.
   Koda ta fito bata d’aga kai ta kalli Anas ba shikuwa idanunsa na kan ta rabuwansa daya sata a ido har ya manta.

    “Baki ga Mr. Fauzi bane da baraki gaishe sa ba?” yi tayi kamar bata ji me Mami tace ba.

*© miemiebee*

beeenovels.mywapblog.com
[12:49, 12/18/2016] ‪+234 903 612 6826‬: •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫

❣🎀❣🎀❣

*_written by miemiebee👄_*

In dedication to *Aunty Sis💕*
3⃣0⃣





Kallon Fannah Mami ke cike da mamaki, wannan ne karo na farko da Fannah ta sab’a wa umarninta bakuma tare da ta nuna damuwa ba. “Fannah dake fa nake magana, meke damunki ne? Baraki gaishe sa ba?” Ta sake tambayarta. Nan ma shiru tayi, a kunyace Mami tace, “Anas kayi hak’uri bansan meke damun Fannah ba.” Murmushi yake kaman ba shi ba “ba komai Mami maybe bata san yin magana ne” blue eyes nasa ya d’ago yana kallonta sosai, haka kawai yasamu kansa cikin niahad’i in yana kallon innocent face nata, sarai taji yadda yake kallonta amman ko d’aga kai batai ba. “Fannah tunda baraki gaisheni ba ni zan gaisheki ina wuni?”

Shiru tayi bata amsa ba, Mami de tashiga cikin duhu wai ace Mr. Fauzi na gaishe da Fannah amman barata amsa ba. “Anas kayi hak’uri dan Allah bansan meke damun Fannah ba yau, Afrah ko kunyi fad’a ne?”
“A’a Mami ba abinda ya had’a mu.” Afrah ta fad’i cike da zumud’i se satan kallon Anas take.
Giaran murya Anas yayi “uhm Mami nasan kuna mamakin ko me nazo yi anan koh? Bikon Fannah nazo yi, dama misunderstanding muka samu tabar min aiki akan had’a coffeen da take min ne tace ta gaji dayi sede in zan bata aikin daya fisa nikuma alokacin banida aikin da zan bata.”

Baki wangalau Fannah ta bud’e tana kallon ikon Allah yanzu ko kunya baiji yake wannan k’arya. Kut lalle! “Mami walla-” ta gwada kare kanta.
Katse ta Mami tayi “se yanzu bakin ki yaga daman bud’uwa Fannah? Toh kiyi shiru Anas ya gama, ina jinka Baba na.” Idanun sa ya d’aga yana kallonta, itama kallon nasa take, murmushin mugunta ya saki mata wanda ta murgud’a masa baki in return tare da kawar da kallonta daga garesa. “Yawwa, shine tayi resigning amman yanzu da nake neman Personal Assistant (PA) kuma gashi takardun ta sunada kyau zan d’auke ta aiki. Albashi dubu d’ari biyar da kuma weekly allowances N5,000.”

“Alhamdulillah!” Mami ta fad’i cike da murna. “Alhamdulillah! Aiki har gida Allah ya kawo miki Fannah, wallahi Anas ba abinda zance sede Allah maka albarka ya k’ara d’aukaka da girma, aiki ba inda Fannah bata nema ba amman seta koma washegari se suce sun fasa, abin de ba dad’i”
“Fannah ke baki iya godiya bane?” Mami ta tambayeta. Shiru tayi kamar bata jita ba.
“Mami kibar Fannah yau kawai bata san magana ne, ai mutane yanzu sun sa san kai a gaba, su yasu kawai suka sani. Se hak’uri.” Idanunsa ya d’aga yana kallon Fannah dake tsaye har yanzu ta had’e gira gu d’aya. “So Fannah zaki dawo min aikin? Tunda na canza miki post yanzu”

“Anas yanzu har seka tambaya ko zata koma ne? Ai komawa ta riga ta koma kawai ka fad’i yaushe kakeson tayi resuming office.”
“Mami!” Fannah takira sunanta cike da takaici. “Wai me haka?”

Sanyi yaji a ransa jin muryarta kawai.
“Eh mana Fannah, a jinki akoi inda zaki samu aiki me kyau haka ne? Gaskia Anas mungode sosai sosai Babansu na bacci da ya maka godiya shima.”
“A’a Mami ba komai nine da godiya. Gobe nakeson Fannah ta soma aiki.”
“Allah kaimu Anas, In shaa Allah a goben zaka ganta” Hannu yasa a aljihu ya ciro bandir na d’ari biyu tare da ajiyewa gaban Mami “ga wannan a saya wa Baba magunansa dashi da kuma sweet wa Aiman ko?” ya dawo da kallonsa kan Aiman dake manne a jikinsa se mamakin gashin hannunsa take.
“Yeyy! Ya Anas nagode. Ya Fannah ba sekin sake min rowan naki ba Ya Anas yace a siya min” kallo Fannah ta watsa mata wanda batasan Anas na kallonta ba.
“Anas Babana da wahala haka? Toh mungode Allah saka da alheri.” Fannah ji take kamar ta k’urma ihu ita wallahi barata koma masa aiki ba sede sama da k’asa su had’u.
“Ermmm Ahmad!” ya danna masa kira nan Ahmad dakw waje yashigo bayan ya gaishe dasu Mami Anas yace ya shigo da kayakin. Dama already yariga ya tara almajirai nan suka soma shigowa da kayaki. Ba Mami kad’ai ba har Fannah sanda tasha mamaki wato siye mata iyaye zeyi da kud’i da kayan duniya, lallai kuwa.

Kap tsakar gidansu sanda aka cika da kayaki tun Mami da Afrah suna godiya har suka gaji sukayi shiru. Addu’a sosai Mami ta riga ma Anas tana suburbud’a masa albarka ga kyautan kud’i ga kuma na kaya, abinde ba’a cewa komi. “Anas kace ko ruwa baraka sha ba? In aika Aiman ta siyo maka ko maltina mana.”
“A’a Mami ba komai”
“Gaskiya Anas ba abinda zance maka, ka gama mana komi naso ace idan Babansu biyu wallahi yamaka godiya, Allah saka da alheri ya k’ara bud’i”
“Haba! Mami ai ba godiya tsakaninmu, ya isa please.”
“Toh ina zuwa, Afrah biyoni.”
“Afrah kad’ai Mami nikuma fah?” Cewar Aiman “ni ma sena bi ku.” Cak ta tashi daga gefen Anas ta bi bayan su Mami zuwa d’akin Baba. Ya rage daga Anas se Fannah itama juyawa tayi zata shiga d’akinsu ya mik’a dogon hannunsa ya cafko ta da hijabi chak ta tsaya ba tare da ta kalle sa ba tace, “Mr. Fauzi ka sake min hijab.” K’in sakewa yayi, ya mik’e tare da shan gabanta yana d’auke dawani murmushin mugunta a fuskarsa.

“Stop pretending, nasani you miss me.” Yace da ita.
“Miss you? A dalilin me zanyi missing mutumin da yake sa ni kuka all thetime? Mr. Fauzi kasan meh? Ni barin sake koma maka aiki ba, na bari na bari forever, ko coffee maker’n ka barin sake zama ba bale PA, kuma wannan tarukucan kayakin daka kawo ka tattara ka mayar dasu inda ka kwaso su bama buk’ata.”

“Ai aiki min kin riga kin dawo k’arfe 8:00AM gobe don’t be late, wannan kayaki kuma anan zasu zauna, tunda kikayi resigning ba tare da kin sanar da ni ba nima haka zan dawo dake ba tare da sanin ki ba. Karki manta everything can be bought with money kamar yadda na saya family’nki yanzu. Inba wai so kike ki b’ata wa Mami rai ba zaki dawo min aiki gobe.”

“No Mr. Fauzi you are wrong, not everything can be bought with money, aiki maka kuma na riga na bari ba dawowa.” Hijabin ta ta fisge tashiga ciki. Murmushi yake sosai danko yasan definately yes Fannah zata dawo masa aiki, ya riga ya saye Maminta. Bada jimawa ba Mami ta fito dawani farin handkerchief me flower a hannunta. “Yawwa Mami zan tafi kar Maghrib yamin anan, in Baba ya tashi a gaishesa please.”
“Da wuri haka Baba na? Toh mungode fa sosai, in shaa Allah zan fad’a masa. Ga wannan ba tsada amman naji yakamta in baka wani abu kaima da abinda ka mana.” Hannu yasa ya amshi, “thank you Mami, nagode sosai ai ba tsadar abu ne yadamu ba value nasa ne. Aiman, Afrah na tafi.”

Baki na b’ari Afrah tace, “mm..mungode Mr. Fauzi Allah kare hanya.” “Ameen” yace. “Ya Anas yaushe zaka sake zuwa nima asani a TV?”
“Very soon Aiman” ya amsa ta yana murmushi. “Mami ki tunawa Fannah k’arfe 8:00AM gobe kar ta makara please. ”
“In shaa Allah Anas karka damu a gaida mutan gida. Fannah! Fannah! Zo ki raka Anas mana.” Yana jin haka ya rage saurin tafiyar sa yasoma tafiya a hankali.
Fannah daka lab’e jikin window ji take kamar ta kashe kanta ta huta wato handkerchief da tunba yau ba take bin Mami ta bata tak’i amman ta kama ta bawa Mr. Fauzi, dakyau ta kyauta. “Fannah!”
“Na’am” ta amsa. “Kifito mana.” Tana zumbure zumbure tafito “gani” tace tana kallon k’asa. “Bakiji Anas ze tafi bane? Wuce ki raka sa.”
“Mami!” Tace kan wanda zatayi kuka. “Ki wuce nace” Mami ta bud’e mata ido. A sanyaye tabi bayan Anas yanajin footsteps nata a bayansa ya sakar da murmushin mugunta. Bayan sun kai bakin k’ofa ya juyo ya kalleta, kallonta ta kawar daga garesa “zaki iya komawa, kinsan rules d’ina bana tolerating late coming.” Can k’asa tace, “damuwanka saboda ni ba aiki zan dawo maka ba.”
“Haka kikace? Se mugani.” Nan ya shiga motarsa ya fice bayan ta dawo ciki ta tarar da su Mami se bud’e bud’en ledoji suke ji take kamar ta tattara kayakin ta k’ona har ta kai da shiga d’aki Mami ta kirata “zo nan Fannah.” A sanyaye ta juya “gani” tace.
“Kin kyauta min kenan yau? Ba se Anas d’in yace ban ba ki tarbiyya ba.”
“Ba seya che d’inba” tace can k’asa k’asa aikuwa Mami ta juyo ta “aww abinda ma zakice kenan yace d’inko? Ni bansan me ya shige kiba yau Fannah, keda ya kamata kiyi murna ki gode wa Allah har gida Anas yazo yayi bikon ki amman kike wannan rashin hankalin? Kiga alkhairun daya mana, haba Fannah.”

“Mami ni barin koma masa aiki ba gaskia, zan cigaba da neman wani.”
“Ya Fannah mesa?” Cewar Afrah dake k’ok’arin bud’e leather’n set na comb.
“Bansani ba kema k’aramar munafuka sekace baki san halin Mr. Fauzi ba. Wallahi Mami kullum seya sani kuka sede in banje office nasa ba ni gaskia banaso.”
“Ji zancen banza dukanki yake ne?”
“A’a amman yata min masifa yana daka min tsawa.”
Cike da mamaki Mami ke kallon Fannah. “Wato har yanzu baki bar halin ki na kuka da an d’an miki magana ba koh?”
“Ai Mami magana daban masifa daban ni gaskia barin koma wa Mr. Fauzi aiki ba.”
“Shikenan Fannah, kin mana k’ok’ari ai dama dole wataran ki gaji, mungode. Da kud’in da Mr. Fauzi ya kawo zanyi k’ok’ari in nemowa Afrah polythecnic itama, inda hali ma zan ma Mr. Fauzin magana ya cika min sauran tunda ke kin gaji.”

“A’a Mami niba abinda nake nufi ba kenan.”
“Toh me kike nufi Fannah? Aiki har gida a kawo miki da albashi me kyau amman kice bakiso? Me kike nufi toh Fannah?”
“Hummm yi hak’uri Mami” cewar Afrah. Wani kallo Fannah ta watsa mata k’anwar shed’an kawai ta fad’i a zuciya. “Afrah ‘ya ta, Fannah ta gaji damu ki dage kema kiyi karatu zan nema miki babbar makaranta.”
Fannah batasan nayi ba kuma again tasan halin Mami sarai in ta kama surutu bata gajiya in bawai yanzu ta karb’i aikin Mr. Fauzi bane shikenan zasu b’ata ga Afrah k’anwar shed’an abinda takeso kenan. Da k’yar tace, “Mami kiyi hak’uri dan Allah ni ba abinda nake nufi ba kenan. Gobe zan fara zuwa aikin in har it will make you happy.”

“Toh ko kefa Ya Fannah?” cewar Afrah.
“Afrah kinga kimin shiru ba ruwanki.” Matsowa tayi kusa da Mami. “Mami kiyi hak’uri.”
“Haba Fannah keda kullum nake yaba hankalinki. Shi masifa haka Allah yake halittan wasu mutane dashi, ko magana suke maka sekaji kamar masifa ne. Kekuma sekiyi hak’uri Anas nada kirki ba kowani Boss bane zezo yayi bikon ki musamman ma da kika bar masa aiki saboda kin raina post daya baki.”
Fannah ta bud’e baki zata k’aryata hakan kawai tayi shiru dan there will be no point Mami ba yarda zatayi ba. Nasiha sosai Mami ta mata kan tana hak’ura da halin Anas na masifa is not easy ace d’an shi yana running babban Enterprise irin Flames Enterprises.

****

Fannah duk tashiga tashin hankali, tana nata Allah na nasa. Ita gabad’aya ta riga ta cire Mr. Fauzi daga ranta a cewarta ba abinda ze sake had’a ta dashi se gashi wai zata koma masa aiki bama as coffee maker ba personal assistant yadda kulum *_TANA TARE DA SHI_*

Ta b’angaren blue eyes kuwa tun barin Fannah aiki be sake samin kwanciyan hankali da nishad’i kamar na yau ba. He can’t wait ta had’a masa coffeen ta me uban dad’in gaske already ya riga ya sa an wanke masa manya manyan flasks guda biyu da zata cika masa cikinsu dashi.

_Washegary..._

Tun k’arfe bakwai saura 6: 40AM Mami tazo ta tada Fannah tasata wanka ta mata breakfast da kanta, d’aya daga cikin ready made hijaban da Anas ya kawo musu Mami ta zab’a mata d’aya sam Fannah tace barata sa ba, tayi k’arya wai batta san kalan haka Mami ta barta tagama shirinta cikin baby pink. Kwalli, lip gloss da powder kawai ta sa ta d’au jakarta ta fice bayan Allah kare da Mami ta mata. Takwas saura minti biyu ta sauk’a daga keke napep. Tana shiga suka ci karo da Yusuf had’iyeta ne kawai beyi ba dan murna, finally aiki ze dawo normal kamar yadda yake da. Gaisuwa kad’an sukayi dan kar ta makara sosai Mr. Fauzi yasamu abin surutu kai. 8:03AM tashiga office nasa tsaye ta samesa da wata staff yana bata orders bayan d’an lokaci ta fice ya rage daga Fannah se Anas.

Sanye yake da pitch shirt da ocean blue neck tie, suit nasa na rataye kan hanger. Ganin bata da niyan magana yace, “baki iya gaishe da Boss naki bane?”
Ba tare da ta kallesa ba tace, “good morning.” Be amsa ta ba ya koma kan kujera ya zauna tare da kirawota steps kad’an tayi sanda ta iso gaban table d’insa ta tsaya.

Magana yake sekace ba shi ke murmushi da dariya jiya ba. “So kamar yadda kika sani you’re now my personal assistance, right?”
Kai ta giad’a a hankali. “Good incase kin manta rules d’ina zan making miki clear yanzu.”

“Banasan body language in na miki magana dole kema kimin
Banason shisshigi.
I don't tolerate late coming.
Ke PA na ne yanzu meaning a koda yaushe muna tare amman hakan be baki daman kina kallo na anyhow ba.
Don’t fall for me in the process, dan ko kin soni ni baran so ki ba.” Har tsakiyan kanta ta jiyo wannan kalamu, dan wannan zagi ne.
“Ki mayar da hankalin ki sosai wajen aiki, banasan aiki da mistake always.
As my PA duk abinda nace kiyi shi zakiyi ba objection ba musu.
Hiran da kika saba zuwa yi da Yusuf has to stop, in an tashi daga aiki sekuje ku cinye kanku.
Normal lokacin tashinki k’arfe 4:00PM ne amman in aiki yayi yawa I might hold you.
Na k’arshe obey all my rules. I hope am clear?” Ya tambayeta

“Yes you are amman ka kwantar da hankalin ka Mr. Fauzi ni barin tab’a san mutum me hali irin naka ba, kuma Yusuf ba saurayi na bane.”

“Incase ban fad’i wannan part cikin rules d’ina ba

Please Login or Register in order to submit comment