Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

°•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫

❣🎀❣🎀❣

*_written by miemiebee👄_*


1⃣1⃣




Bayan tafiyan Ya Khaleel bada jimawa ba su Mami suka dawo gida, Fannah na d’aki tana kukan cire rai bata ma ji shigowansu ba kawai ganin Mami tayi tsaye a kanta take ta soma share hawayenta “sannu da zuwa Mami, yaushe kuka dawo?”
“Habibti kukan me kuma kike? D’an mayen can yazo ne?”

“A’a ba kuka nake ba Mami, inasu Afrah?”
“Fannah ga idanunki sunyi ja sun kunbura, fad’a min meneh? Keda waye?”
“Ya Khaleel ne yazo...” Nan ta irga mata duk abinda yafaru tana kuka.
Rungumota Mami tayi “Shikenan yi shiru in shaa Allahu Kawu da d’ansa barasu k’arisa da duniya lafiya ba, mugayen mutane kawai bar kuka kinji? Akoi Allah Fannah always have this at the back of your mind, in shaa Allah baraki auri Farouq ba.”

Hannu tasa ta share hawayenta, “Mami ni nasan zan auri Farouq ba abinda zamu iya Ya Khaleel yariga ya gama komi.”
“Fannah kin cire rai daga Allah kenan?” Kad’a kai Fannah tayi “toh ki bar fad’in haka, Allah ba azzalimin bawansa bane. Allah da kansa yace a Qur’ani auren mazinaci se mazinaci aikinsani koh?” Kai Fannah ta giad’a “toh kibar kukan ya iso mik’o mai in taje miki gashinki.” A sanyaye ta mik’e ta d’auko mai da comb mama ta taje mata gashinta takama mata gu d’aya sannan ta bata waje tasa kaya. Itakuwa ta fice zuwa d’akin Baba.

Kwance ta samesa, “Malam ya jikin?”
Baki na k’yarma yace, “da sauk’i.”
“Sannu, Malam ko kanada labari d’azu Kawu yazo ya cicci mutuncin Fannah? Duk nazo na sameta se kuka take.”
“Eh..Mam.. Maman Aiman saisa yazama dole in siyar da gwalagwalen da Umma (mahaifiyarsa) ta tab’a bani dana ajiye kan duk sanda Fannah tazo aure se in sayar mu mata kayan d’aki amman tunda ga yadda abu ya kasance dole mu siyar yanzu...” Tari ya tsaya yayi sannan ya cigaba.
“K’ark’ashin wancan akwatin akoi d’an kunne da sarqa da zobe dakuma warwaro guda hud’u na gwal, da ace ina da lafiya da a gobe zan jeni Maiduguri in siyar amman gajan haka yasa dole seke zaki Maman Aiman.”

“Ina jinka Malam, in mun siyar me zamu da kud’in?”

“Gidan nan zamu bari, garin nan zamu bari gaba d’aya mukoma Maiduguri inason bayan kinje kin siyar da gwala gwalen ki kama mana gida me arha koda 2 bedroom ne kawai wanda zamu iya affording, sekuma da essential abubuwan da zamu iya bu-” tari ne ya tsaida sa sosai.

“Malam shikenan ya isa nagane kar jikin ka ya tsananta. Amman Malam bara mu tafi da kayakin mu ba? Inaga zefi mana sauk’i inda hali ma gidan nan se mu siyar.”

Gyaran murya yayi sosai “inaaa... hakan bame yuwu wa bane Maman Aiman mukayi haka ai kamar mun fad’awa duniya zamu bar garin Bama ne kisani no one must know about this. Fannah kawai na yarda ki fad’a mata itanma dan mu cireta daga damuwa ne kuma ki gargad’e ta karta kuskura ta fad’awa Afrah kar da baki taje cikin jama’a ta tona mana asiri. Dan maganan nan na fitowa fili shikenan namu ya k’are dole Fannah zata auri Farouq, ni na fad’a miki.”

“In shaa Allah Malam, Allah kaimu goben zan wuce Maiduguri dan kasan matsalar samun gida, in bamu soma nema a kan lokaci ba zamu makara har lokaci ya k’ure we have just a month.”

****

“Fannah habibti. Fannah!” Kirar Mami dake tsaye daga bakin k’ofa.
Sanda Fannah takai k’arshen ayan datake karantawa sannan ta amsa “na’am Mami am sorry bansan yanke ayan ne.”
“Bakomai karatu kike ne?”
“Eh Mami wani abu ne?”
“Ina Afrah da Aiman?”
“Suna can parlour suna assignment.” Fannah ta amsa a takaice.
“Oh toh magana daman nazo miki.”
“Toh bismillah Mami” nan Mami ta k’ariso ciki tare da rufo k’ofar tayi joining Fannah kan katifar sanan a hankali ta sanarda Fannah abinda ita da Baba ke da shirin yi. Sosai Fannah taji dad’i harda hawayen nin dad’i.

“Mami dagaske kike? Zamu koma Maiduguri barin auri Ya Farouq ba?”
“Sosai Habibti ai dama na fad’a miki koda bamuda komai munada Allah, kuma Allah ba azzalimin bawa bane kamar yadda na fad’a miki gobe zani Maiduguri.”
“Toh Mami in bi ki mana muje tare.” Cewar Fannah tana share hawayen jin dad’i.

“A’a Fannah kinsan Kawunki wane bodyguard haka yake kusan kullum seya zo gidan nan inkuma yazo bani ba ke kinsan dole yayi bincike the moment asirin mu ya tonu kuwa kinga dole sekin auri Farouq. Saboda haka ni kad’ai zanje addu’a kawai zakimin Allah sa inje a sa’a in dawo lafiya.”

“In shaa Allah Mami Allah baki sa’a. Nagode sosai, keda Baba kun gama min komai aduniya Allah biyaku da gidan aljannah.”

“Ameen Habibti barin koma in had’a akwati na.”
“Toh muje in tayaki shiryawa.”
“A’a Habibti zanyi dakaina, go on da karatunki.”
“Toh Mami.” Har Mami takai bakin k’ofa Fannah ta danna mata kira da
“Mami!”
“Na’am Fannah.” Ajiye Qur’anin dake hannunta tayi ta ruga gun Mami da gudu tayi hugging nata “Jazakumullahu bikhairan keda Baba nagode sosai, Allah sak’a muku da gidan Al-Jannah.”
“Ameen Habibti Allah miki albarka kema.” “Ameen” ta ce sannan ta sako Mami tana kallonta har sanda ta shige d’akinsu da Baba. Sujjada tayi tana gode wa Allah sannan tashiga bayi tayi alwala tayi nafila raka’a biyu tare da sake gode wa Allah ji tayi kap matsalolinta sun gushe. Kan katifar su ta fad’a se murmushi take.

****
_4 days later..._

“Oyoyo Mami! Oyoyo Mami!” cewar Aiman tana daka tsale. “Oyoyo auta ta” Mami ta d’aga ta sama. Nan su Fannah suma sukazo suka mata oyoyo. Kwanan Mami uku a Maiduguri tadawo, tafiyar ta kuwa was a success kap addu’o’insu Allah ya amsa musu. Kud’in data samu bayan ta sayar da gwala gwalen ta kama musu gidan haya 2 bedroom dashi a unguwar jiddari polo, na shekara, seda katifu guda biyu da d’an kayan abinci da kayan kitchen. Alhamdulillah!

_2 weeks later..._

Farouq ne tsaye bakin gidansu Fannah shi a dole yazo ganin matarsa nan da sati d’aya da ‘yan kwanaki zata zama mallakinsa tsabagen iskanci ba abinda yake imagining illa first night nasa da Fannah. Wani almajiri ne yazo wucewa take ya tsaida sa “kai shiga nan kace wai inji Farouq matarsa ta fito.” Da “toh” yaron yashiga gidansu Fannah suna zaune tsakar gida suna tsintar shinkafa ita da Afrah.

Ita kanta Afrah mamakin yadda Ya Fannah ke walwala kwana biyu ke bata kukan data sobayi safe rana dare yamma duk tadena yanzu, dukda batasan reason nayin hakan ba itade tana ma yarta murnan dawowar farin cikinta.

“Assalamu Alaikum” cewar almajirin. “Wai inji Farouq wai matarsa tafito” dadai lokacin Mami tafito daga kitchen. “Me kace?”
“Farouq ne ya aiko ni wae matarsa ta fito.”
“Dan ubansa kace barata fito ba yaushe tazama matartsa? Fice kabani waje.”
“Almajiri tsaya” cewar Fannah “kace masa ina fitowa.” Kallo Mami ta watsa mata “Fannah baraki fita ba kinsan wannan d’an mayen yanzu seya saki kuka ki zauna.”
“A’a Mami kibari inje ai ba abinda ya isa yamin a waje a idan mutane, kiyi hak’uri.” Mami zata sake magana Fannah tace, “please Mami.” Da d’aga kan da Mami tamata Fannah ta shiga ciki ta d’au hijabinta sannan ta fice a zaune ta samesa kan benchi da alama yau ba a buge yake ba.

“Ke zo nan kizauna yaci ace kin saba dani yanzu, nan da ‘yan kwanaki zaki zama tawa.” A zuci Fannah tace, _taka? never! Allah ya riga ya kare ni daga auren mazinaci kamar ka._ Kawai jin hannun sa tayi kan kumatunta firgit ta matsa baya. Yasake matsowa kusa da ita “wai tunanin me kike haka? Kode tunanin first night namu?” Ya d’an murmusa “karki damu I'll take it easy on you” batace dashi komai ba illa kallonsa da take.

“Ke wai yau azumin magana kike ne?” Juyawa tayi zata tafi ya danna mata kira cak ta tsaya bata tanka sa ba. “Kiyi sha’aninki iya san ranki kimin rashin mutunci iya san ranki amman kisani nan da sati d’aya da ‘yan kwanaki ni zanna ja miki aji. You can go daman nazo inga kyakkywar fuskarki ne kafin na wuce bayan gari.” Kai kawai takad’a tashige ciki.

Tsaye ta tarar da Afrah da Mami da damuwa karara a fuskarsu. “Ya haka Mami wani abu ne?” Ta tambayesu

“Farouq fa inade be miki komai ba?” Cewar Mami.
“Kai Mami da Allah ki kwantar da hankalinki Mami, kema haka Afrah ba abinda Ya Farouq yamin banda suratan banzan daya saba wai yanzu haka ma bayan gari zasa.”
“Shege mazinaci” cewar Mami. “In shaa Allahu baraki auresa ba.”
“Amman Mami yau fa sauran sati d’aya da kwana uku ne bikin anya akoi abinda ze hana aukuwan wannan aure?” Afrah ta fad’i cike da damuwa.
“Akoi Allah Afrah, always have this at the back of your mind. Jeki huta Fannah nida Afrah zamu gama girkin.”
“Toh Mami, ina Aiman tazo mu mata tsifa.”

_3 days later..._
Ana saura sati bikin Fannah da Farouq. Ya Khaleel ne tsaye cikin tsakar gidansu Fannah. Mami, Fannah da Afrah suna tsaye kansa. “Toh nide nafad’i nawa tun ana wata bikin nan na fad'awa Fannah ta sanar dake batun gadon nan gashi har yau baku sai ba wallahi zakusha mamaki dan kuwa amaryarku kan tabarma zata kwana. Wasu erin matsiyata ne ku? Ace ‘yarku zatayi aure ko gado kun kasa yi mata? Wai ahaka ma dan na d’auke maku nauyin kayan kitchen. Allah wadar in erinku wallahi.”

“Kawu kayi hak’uri nan da ‘yan kwanaki zan kwashe adashe na se in sai wa Fannah gadon dan Allah ka k’ara hak’uri.” Cewar Mami.

“Wannan kuma ku ya dama, ko ku sai gado ko amaryarku tayi kwanan tabarma. Ni na tafi.”

Yana ficewa Mami taja hannun Fannah sukayi d’aki gudun kar Afrah ta fahimce wani abun. Itade Afrah tasoma zargin abu da a da ne Kawu yayi wannan magana definately Fannah zatayi kuka sega yau ko nuna damuwa batai ba.

Da daren ranan Fannah da Afrah suna zaune d’akinsu Aiman tayi nisa a bacci. Afrah tafi minti biyu tana kallon Fannah har sanda tasa ta tsarguwa. “Afrah wannan kalo haka?” Cewar Fannah tana duba pages nawani Government text book.

“Ya Fannah kallen.” D’ago fararen idanunta tayi wanda suka sha bak’in kwalli ta azasu kan Afrah. “Na kallekin” tace. “Kina b’oye min wani abu kinsan na sanki fiye da yadda nasan kaina I can tell in kina b’oye min bu.” Cewar Afrah

“Me zan b’oye miki Afrah? Kawai de inajin dad’i ne.”
“Dad’in me fah? Dad’in zaki aura Ya Farouq??” Ta tambaya tare da d’age gira.
Dariya kad’an Fannah ta saki “ko kad’an Afrah ina murna ne saboda inaji ajikina barin auri Ya Farouq ba.”

“Toh Ya Fannah Allah sa, kinsan happiness naki ya fiye min komai a duniya.” Hugging junansu sukayi cike da so da k’aunar juna.


****
_Ana saura kwana biyu biki..._
Da misalin k’arfe 8:00AM
“Farouq! Farouq!” Kiran Ya Khaleel yana zaune kan tabarma. “Na’am Baba” Farouq ya amsa yana isowa sannan yasamu waje ya zauna.
“Ni ya jiya ka had’u da Fannah kuwa? Mahaifiyarta tace mun cikin satin nan zasu kawo gadon gashi saura kwana biyu bikin naku basu aiko ba. Anya mutanen nan lafiya kuwa?”

“Ni Baba kawai mu share zancen gadon nan kafa san basuda kud’i ni Fannah ta zamo mata ta shine babba ban damu ba ko kan tabarma zamuna kwana bale ma ai ina gado se in tafi mana dashi.”
K’eyarsa Ya Khaleel ya tand’e “ai dama kai wawa ne, taya mu zamu masu komai tashi muje gidan nasu yanzu.” Ba gardama Farouq yabi bayan Babansa suka fice zuwa gidansu Fannah.

“Salamu alaikum!” Cewar Ya Khaleel a yayinda Farouq kuma ke knocking shiru kukeji ba amsa “waiko wannan matsiyatan bacci suke ne?” Ya Khaleel ya tambayi Frouq. “Toh ya zansani Baba inba wai shiga zamuyi ba.” Sa kai sukayi a tare Ya Khaleel na sallama sede har da suka iso tsakar gidan ba amsa dan haka Ya Khaleel yayi d’akin Baba yayi knocking nanma shiru hannu kawai yasa ya bud’e k’ofar yaga d’akin wayam! Daga katifa se katifa ba bakunan kaya ba komai. “Tashin hankali!” ya kira a fili. Farouq dake tsaye tsakar gidan yace, “lafiya Baba?”
“Ba lafiya ba” cewar Ya Khaleel “zo kaga ba kaya a d’akin nan. Tsaya duba d’ayan d’akin yaran tukunnah” nan Farouq yaje ya bud’e same story. “Nan ma ba kaya Baba.”

“Tashin hankali! Bade Aliyu da iyalansa sun gudu sun bar garin Bama ba.” Y fad’i cike da tashin hanakli. “Amman ai basuda inda zasu ma, through out rayuwarmu anan mukayi, baida ma kud’in biya masu kud’in mota bale ace ya kama masu gida a inda sukaje. Dole suna cikin garin nan suna b’oye cikin wani gida taho muje mu sami kakanka mu irga masa.”

Bayan sunje sun samu kaka Ya Khaleel ya irga masa komai. Matuk’a Baba yasha mamaki. “Tunda haka d’an uwanka yayi deciding, mu barsa mu ga iya gudun ruwansa. Mun nuna masa halacci ya nuna mana butulci. Ni badan komai na amince da wannan maganar ba dan kar ‘yarsa ta rasa mijin aure ne amman tunda haka yace se mu barsa.”

“Haba! Baba haka zakace!? Nida na d’au tsine masa zakayi. Guduwa fa yayi Baba ya bijire wa umarnin ka.”
“A’a Khaleel ba maganan tsinuwa anan fatan mu Allah sa hakan dayayi shine mafi alkhairi garesa da ‘yarsa dakuma iyalansa gaba d’aya.” Ko “amin” d’inma Ya Khaleel be amsa ba shida yagama sa rai Fannah zata haifo masa kyawawan yara ace sun gudu basu gidansu. IMPOSSIBPLE. “Tashi Farouq yau ko shadda suka shiga suka b’uya semun tonosu bayan nagama bazawa a gari zakayi aure se ace amarya ta gudu wallahi k’arya ne tashi nace. Aliyu be isa ba yau duk inda suke a b’oye sena nemo su!” Baba na k’olla masa kira ko a jikinsa yaja hannun Farouq a fusace suka bar gidan.

*Masu karatu kui hak’uri yau bansamu nayi typing kamar yadda na saba ba, severe back pain ke damuna in shaa Allah gobe zanyi dayawa. I love you guys!*

*©miemiebee*

beeenovels.mywapblog.com

[12:46, 12/18/2016] ‪+234 903 612 6826‬:  •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫

❣🎀❣🎀❣

*_written by miemiebee👄_*


1⃣2⃣




Da misalin k’arfe 7:30AM su Fannah suka isa garin Maiduguri daga can suka tsara taxi se sabon gidansu. Ba laifi gidan gaskia yayi arha d’akuna biyu ne da bayi biyu dakuma  kitchen. Fannah takasa b’oye murnanta, finally barata auri Ya Farouq ba.

     Ya Kaheel da d’ansa Farouq kuwa haka kaman zararru suka riga bin gida one-by-one a Bama su a dole suna neman Fannah da family’nta sam hankalinsa be basa Maiduguri su Fannah suka tafi ba. Har dare suna neman su Fannah ganin ba mahalicci se Allah yasa suka hak’ura suka dawo gida disappointedly.

     Fannah kuwa yanzu rayuwa yasoma mata dad’i, a hankali ita da family’nta suke settling a Maiduguri hankalinsu akwance basuda wata tsoro yanzu, Government school me kyau Mami tasamu aka zuba Afrah da Aiman. Fannah kuwa ko kad’an bata sa rai kan zata cigaba da makaranta ba se sanda Baba yayi suprising nata kud’in daya kamata abiya akaisa asibiti ya yafe kan Fannah tayi proceeding karatun ta. Admisson aka nemo mata a Polythecnic course na Business Administration.

         Sosai taji dad’i. Koda ta soma zuwa makaranta kuwa kullum cikin hijabi da nik’af take, mazan makarantar su basu ma san ya fuskarta take ba bale ace su gano kyawunta su soma binta. Haka Allah ya cigaba da yima rayuwar Fannah albarka, karatu take sosai ba wasa, Mami tana d’an sayarda irin gwanjon kaya hakan nan dashi suke cafanin gida. Baba kam jiki se worse yake ba kud’in kaisa asibiti a kullum burin Fannah ta gama karatu tasamu aiki ta kai Babanta asibiti.

     Ya Khaleel kuwa koda ya kira Mami a waya bata d’aukawa haka yagaji ya bari. Rayuwa de alhamdulillah...

   
★★★★
        _4 YEARS LATER..._
★★★★

             Abubuwa da dama sun gudana a both rayuwar Fannah da na Anas. Fannah tanada k’imanin shekaru ishirin a duniya yanzu. Kyanta yagama fitowa, hips nata da dukiyar fulaninta daidai jikinta beyi yawaba kuma be kasa ba masha Allah. Fannah takai mace duk inda ake neman mace,  shekarunta kusan biyu da gama poly tayi graduating under Business admin da excllent result. Sede aiki ne har yau babu ta kasa samu, duk wad’anda ake bata ba related to course nata bane daga baya dole ta hak’ura ta karb’a aiki as a waitress (me serving abinci ko drinks a shago kokuwa wajen taron jama’a) a wani babban coffee shop. Dad’in abin Coffee shop d’in nasu sananne ne sosai cikin garin Maiduguri yawancin meetings kokuma party ko biki da akeyi a Maiduguri a Coffee shop nasu Fannah ake zuwa a d’ibi waitresses kuma duk lokacin da akayi haka kud’i suke samu sosai. Da wannan take samu ta biya kud’in school fees na Aiman dana Afrah, amman de yanzu Afrah itama tagama makarantar tana neman kusan shekara da gamawa.

       Fannah na k’ok’ari sosai dan tasa Afrah a makaranta sede abun ya gagara, jarin Mami ya jima da karyewa lokacin da jikin Baba yatab’a yin tsanani dole ta tattara ribanta da uwarkud’in business natan duka aka kaisa asibiti. A takaice de yanzu Fannah ce breadwinner’n family’nta duk akanta sukayi depending. Allah sarki Fannah ‘yar Albarka Allah cigaba da miki albarka, ameen.

       Samari kuwa ba ta kansu take ba, sau afi a k’irga in aka d’ibesu serving food and drinks a meetings alhazai masu ji da naira suka ganta sesun neme ta amman saboda duk sanda ta tuna da past nata, ta tuna bata da  budurcinta martabarta setaji barata iya k’ara yin soyayya ba saboda definately randa aka gano gaskia ita ba budurwa bace za’a guje ta abinda bataso kenan. Bature yace prevention ia better than cure sesa tun farko ma bata sa kanta cikin soyayyar. Daga wanda zata musu k’arya tace takusa aure se wanda zata ce musu tanada aure.

         Zancen mafarki kuwa har yau bata dena ba kusan kullum setayi mafarkin mutumin dayayi raping nata wai ya dawo ze sake raping nata, Mami kullum ke calming nata in tayi mafarkin rananda Mami batta kusa kuwa haka zata riga kuka tana b’ari har wayewan garin Allah, Allah sarki!

       K’arfe 2:00PM...
      Dadai lokacin tashin Fannah daga aiki kenan kafin ta tsari napep ta dawo gida kuma 2:30PM yayi. Tana shigowa gida Aiman dake carafke tsakar gida tasoma mata “Oyoyo Ya Fannah” cewar Aiman dake da shekara 8 kenan baki kam masha Allah. “Oyoyo Aiman” cewar Fannah tare da hugging nata. “Ina sweet d’ina Ya Fannah?”
    “Laaa kinga yau na mance ban siyo miki ba in shaa Allah zan siyo miki gobe, yi hak’uri kinji?”
     “Ai dama haka kike cewa kullum inda saurayin kine ai baraki mance ba.” Cewar Aiman tana guna-guni.
      “Ya SALAM!!!” Fannah ta zaro ido “ban hanaki maGanan saurayi ba? Ni narasa ina kikejin wanga zance.”
     
        “Sekin tambaya ne Ya Fannah?” cewar Afrah data fito daga d’aki “wannan maras kunyan kuma.”
         “Ai wallahi Ya Afrah ko kiyi shiru ko in fad’awa Ya Fannah batun wancan saurayin dayazo wajen ki d’azu da Mami batta gida.”
    Kai Afrah ta dafe “banza! ai kin riga kin fad’a matan kuma wallahi kisani baran sake baki chocolates ba in yakawo min.”
        “Wait wait wait Afrah saurayi kika soma kawo wa gida bada sani

Please Login or Register in order to submit comment