Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

k’arisowa kusa dasu. “About the lunch I think zamu-” be k’are maganar ba idansa ya sauk’a kan hannun ta dana Boss. Ido wuru-wuru ya zaro sekace a mafarki! Me had’in Fannah da Boss to kodai soyayya sukeyi? Fannah da hanaklinta zatayi soayayya da me shaye shaye?
   “Oh I’m sorry bansani bane daban gayyaceki lunch d’inba” ya fad’a tare da juyawa. Fannah ji take kamar ta nitse k’asa. “Yusuf” Mr. Fauzi ya kira sunan sa chak ya tsaya tare da kewayo wa. “ *SWEETHEART* baki sanar dashi bane dama? Why?” Shiru tayi bata amsa saba. “Tell him now to clear all doubts.” Nan ma bata tanka saba.

    Hannunta dake cikin nasa ya matse yadda ze d’an mata zafi.
    “Na zata na fad’a masa, Yusuf I’m sorry.”
    “Sorry for what? Don’t apologise *HONEY* fad’a mashi yanzu.” Shiru tayi duk takaici yabi ya cikata.
   “ *QUEEN*,ko yunwan ne bakiya son magana? I’m sorry yanzu zamuje muci abincin just tell him kinji *HONEY BOO?* ” Wai meke damun Mr. Fauzi ne ta tambayi kanta so yake yayi ruining friendship nata da Yusuf ne ko me? In yacigaba da abinda yakeyi ai se Yusuf ya d’au k’arya ta masa d’azu batun aikin dayace ya mata yawa, se yace ko k’arya ta masa daman fita zatayi da Mr. Fauzi take b’oye masa.
 
    Ido kawai ta rufe tace, “Yusuf I’m sorry ban fad’a maka ba, Anas is now my boyfriend excuse us please zamuje muchi abinci.” Mamaki ne sosai ya ratsa Yusuf lallai ma Fannah tacika ‘yar halak.
  “I’m sorry for delaying you, by the way congratulations” a sanyaye ya juya yayi tafiyarsa, binsa da kallo Fannah tayi, ji take kamar tayi kuka, mesa Mr. Fauzi ze mata haka? Bata sake ce masa komai ba har suka isa hotel d’in shi da kansa ya bud’e mata k’ofa se dad’i yakeji saboda yasan definately yanzu Yusuf da yake zaton saurayinta ne ze rabu da ita tunda ya gansu tare.

  
     Abinci kala d’aya ya musu ordering kafin abicin ya iso ba abinda Anas yake inbanda kallon Fannah shi inama haka zata namasa shiri kullum. Duk lokacin data d’aga kai setaga ita yake kallo. Da k’yar kalamun dayakeson kiranta dasu tun d’azu da safe suka fito yanzu, “you are looking beautiful today.” Kai ta d’ago tana kallonsa da mamaki karara a fuskarta. Wayace mata tayi kyau? Mr. Fauzi? Kode k’arya kunnuwanta suke mata. “Eh sir?” Ta tambayesa.

    “Not Sir, Anas” yayi warning nata.
   “Anas me kace?”
   “Nace kinyi kyau yau.” Ido wuru-wuru ta zaro yau wata rana Mr. Fauzi ya yabata, sede bata san meh ba seta tsinci kanta cikin jin dad’i, toh se meh dan yace tayi kyau? Se komai ya faru k’wak’walwarta ta bata amsa. Murmushin jin dad’in datayi k’ok’arin kawar dashi ne ya kub’uta mata, kallon ta Anas yake dad’i yaji yasata murmushi. “Thank you” tace a hankali cikin jin dad’i, take ta nemi bak’in cikin daya tusa mata ta rasa. “You too kayi kyau.”
“I know already ba sekin fad’a min ba, I always look good.”
Toohhhh! Ta d’ago kai tana kallonsa yaga shima ita yake kallo, shegen girman kai tace a zuciyarta wai I always look good irin yasan shi kyakkyawan nan ne, Allah raba mutum da erin wanga hali.

“My girlfriend nasan ban isa in hanaki kallo na ba amman kallon yayi yawa unless you wanna eat me up.”
Wai lallai ma tace a ranta wato shi ya zage yana kallona in ni nad’an kallesa yace wani na cika kallo.
“But Sir naga nima ai kallo na kake, kuma tun d’azu tunda nashigo office naka yau.”
“Toh ai dan na kalleki doesn’t mean anything, ni kawai kallon ki nake saboda kin d’an yi kyau yau kuma ni bada wata manufa nake kallonki ba amman kinga ke kullum cikin kallona kike, day and night kuma da wata manufa kike kallo na. I can see it in your eyes, kallon soyayya kike min nikuma nayi warning naki don’t fall for me.”

Bakin Fannah seda ya kusa fad’i a k’asa dan yadda ta sakosa. “Nide ba kallon soyayya nake maka ba.” Ta fad’a tare da kare kanta.
“Ohonki nide na fad’a miki *SWEETHEART* don’t fall for me.” Dadai lokacin abincinsu ya iso. Waiter’n ranan ne ya kawo musu wanda ta tambayesa nawa ne kud’in plate. “Wow Miss Aleeyu you are looking amazing.”,Murmushin daya k’ayata ta tasaki “thank you.” Wani kallo Anas ya watsa wa waiter’n take yaji wani bak’in kishi ya tokaresa ji yake kamar ya tashi ya shaqure sa ai shi yakamata ya yaba kyan da tayi ba wani daban ba, kuma yayi.

“Can I have your number?” ya tambayeta, “zanso zama abokin ki.”
“K’ato dakai?” Anas ya tambaya a fusace, “toh barata bayar ba. Ko kunya ma bakaji ma mschww! Boss naka zan kira yayi firing naka next time baraka sake cewa kanasan wata da abokanta ba, stupid kawai.”

“Mr. Fauzi I’m so sorry dan Allah naga PA’rka ce am sorry please.”
“She is not my PA she is my girlfriend.”
“Omg! Mr. Fauzi please forgive me wallahi bansani ba.”
“Damuwanka, Boss naka zan kira abincin ma mun fasa ci.” Wallet nasa yaciro ya irga kud’in ya wurga masa.
“Fannah lets go” ya fad’i a fusace. Dakewa tayi, “Anas” ta kira sunansa cikin wani irin salon muryan da bata tab’a amfani dashi ba. “Calm down kaji? Calm down please.”

A hankali yaji hankalinsa na kwantawa. “Calm down please” ta sake fad’i. Idanunsa da suka kad’a taga sun soma dawowa asalin farin kalansu.


*© miemiebee*

beeenovels.mywapblog.com
[12:50, 12/18/2016] ‪+234 903 612 6826‬: •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫

❣🎀❣🎀❣

*_written by miemiebee👄_*

In dedication to *Aunty Sis💕*
3⃣7⃣





    Ita bata ma san wace chef Khadeejan ba, tambaya ta rigayi har ta sameta sam ta kasa fad’a mata abinda ya kawo ta. “Kece Fannah Aleeyu PA’n Boss koh?” Khadeeja ta tambayeta ganin Fannah batada niyan magana.
     “Eh” ta fad’i fuskarta cike da tausayi da damuwa, baiwar Allah Khadeeja kuwa tun ganin Fannah tasan Boss ne ya turo ta tayi firing nata saboda glass cups da suka fashe mata d’azu.
    “Boss ne ya turoki kizo kiyi firing d’ina ko?” Ta tambaya nitse, kai Fannah ta d’ago ta kalleta cike da tausayi. “I’m so sorry Khadeeja inda inada yadda zanyi da nayi ki cigaba da aiki anan.”
    “Ba komai Fannah, ba laifin ki bane kema.”
    “Me kikayi ne?”
      “Glass cups guda biyu ne suka fashe min mistakenly d’azu.”
    “Kawai? Shine Boss zeyi firing naki?” Fannah ta tambayeta cike da mamaki.
   “Wallahi shine kawai kuma ma bada gangan bane dan Allah ki rok’a min shi wallahi na rasa aikin nan bansan ya zan ciyar da yara na ba, miji na ya gudu ya barni da kula da yaranmu guda biyu, please Fannah.”
   
       Fannah uwar tausayi har idanunta sun cike da hawaye. Ai wannan ba adalci bane ita cups nawa ta fasa masa, mesa bece zeyi firing nata ba se wannan baiwar Allar data fita buk’atar aikin. “Karki damu Khadeeja zanyi iya k’ok’arina inga kin rik’e aikin ki barin je in gwada masa magana, bar kuka kinji?”
    “A’a Fannah karki rasa aikin ki a sanadi na kibari kawai.”
    “A’a Khadeeja I insist in shaa Allah barin rasa nawa ba.” Ahaka ta fice daga kitchen d’in takoma last floor inda tayi knocking a bakin k’ofar office nasa da “enter” da yace mata ta bud’e ta shiga a daidai gaban table nasa ta tsaya. “Mr. Fauzi” ta kira sunansa kanta sunkuye.
     “Yes” ya amsa ta “kin gama duka aikin dana bakin ne?”
    “A’a” ta amsa tana kad’a kai.
    “Meh kike jira then? Ko so kike nazo in tayaki?”
    “A’a Mr. Fauzi batun chef Khadeeja ce-” katse ta yayi “aw! Bakiyi abinda nasakin ba kenan?”
    “Mr. Fauzi I don’t think its fair ayi firing nata.” Kallonta yake cike da mamaki, lallai ma! Jingina yayi jikin kujerar sa tare da crossing arms nasa. “Ke ya kamata ayi firing kenan ko?” Ya tambayeta tare da d’age gira.
  
    “Eh!” ta basa amsa tare da d’ago idanunta suna kallon juna. “Mr. Fauzi ni yakamata kayi firing ba Khadeeja ba, sau nawa nake fasa maka glass cups mesa bakayi firing d’ina ba se ita data fasa guda biyu kacal? Mesa barakayi firing d’ina ba?” katse ta yayi a fusace.
   “Dalili kison ji? Nima bansani ba Miss Aleeyu, kina musu dani, kina karya min cup almost everyday, kina fad’amin magana iya san ranki amman na rasa mesa nakasa firing naki.” Ya fad’i a fusace saboda shi kansa abin ya soma damunsa gashi daga ya zauna seya soma tunanin Fannah koda ransa a b’ace ya tuna da ita seya nemi b’acin ransa ya rasa.

      “Toh itama kar kayi firing nata please, be fair and just. Tunda baraka iya firing d’ina ba itama kayi hak’uri kar kayi firing nata please tunda duk d’aya muke aiki muke maka. Bada gangan ta fasa ba, in ka koreta daga nan batasan dame zata ciyar da yaranta ba, please consider this”,ta fad’i tare da sunkuyar da kanta. A hankali maganganunta suke shiga kunnen Anas. Tunda yazama CEO’n wannan Enterprise ba wanda ya tab’a ce masa ga abinda zeyi kokuma yayi abu ba haka akeyi ba se Fannah kuma yarasa meke damunsa ya kasa tsawata mata se kawai yaji yanasan yayi abinda ta buk’ace sa.

      “Je ki ce mata ta cigaba da aikin amman ta kiyaye nan gaba.” Fannah bata san sanda ta d’ago kai tana murmushi ba, bata d’au akoi tausayi cikin zuciyar Mr. Fauzi ba. “Thank you Sir, thank you so much” da sauri tafice taje ta sanar da Khadeeja, har hawayen jin dad’i sanda Khadeeja ta zubar, godiya sosai tayi wa Fannah, itama Fannan taji dad’i ganin ta farantawa ‘yar uwarta rai.

    Mr. Fauzi kuwa yana cikin wani yanayi wai mesa baya iya turning Fannah down? Mesa da ta nemi alfarma wajensa seyaji yanasan yi mata, mesa? Shi bayasan haka, yafisan yana k’untata mata yana sata kuka kullum baya san yana farinta mata kamar yadda yayi yanzu. “Damn it!” Ya fad’a a fili. “What is wrong with me?”

  ****
    Bayan Fannah ta isa mailroon ta cicciro mails na Mr. Fauzi tana tantance masu amfani da maras amfani, tana gamawa tayi disposing mara amfanin sannan ta nufa wajen Kacallah inda ta amso duk wani business transactions da meetings na Mr. Fauzi. Komi da komi ya dawo hannunta yanzu tunda itace PA’nsa. Kafin ta shiga office na Mr. Fauzi ta wuce nata dan rescheduling business trip nasa kamar yadda ya buk’ata in 2 months time. Daga nan ta wuce nasa office d’in tayi knocking yace, “come in” nan tashiga. Sede ta karanci yadda ransa yake a b’ace cikin d’an k’ank’anin lokacin nan. Toh meya samesa? “Sir nayi rescheduling trip d’in ga kuma mails nakan.” Ta fad’i tare da ajiye masa kan table nasa.

    Bece mata komi ba yaja mails d’in yana duddubawa bayan yagama dubawan ya d’ago blue eyes nasa “ina mail da Enterprise Bank suka turo min?”
    Hannu Fannah ta aza kan fuskarta tare da toshe bakinta. Wallahi kuwa taga mail d’in ta yasar dan be mata kalan me amfani ba.
    “Tambayarki nake ina yake?”
     “Sir I’m sorry na yasar.”
    Blue eyes nasa ya zaro, “kin meh? Kin yasar? Da hankalinki kuwa?”
    “Sir I’m sorry naga kamar-” bata k’are maganar ba ya katse ta cike da tsiwa “kinga kamar beyi kalan me amfani ba ko? Na baki nan da 5 minutes kije ki nemo min mail d’in duk inda kika kaisa. Mschww!”
     Tana b’ari tace, “Sir I’m sorry amman an riga anyi disposing.”
    “Meaning what?! Kije ki nemo min, I don’t care, get out!” Hawaye tajiyo yana ciko mata a ido a sanyaye ta juya ta sauk’o zuwa first floor tare da neman waje ta zauna tana kuka batasan a ina zata nemo masa ba bayan motan kwashe shara ya riga ya tafi. Tayi kusan awa d’aya a waje sannan tajiyo ringing d’in wayarta tana dubawa taga Mr. Fauzi d’agawa tayi ba tare da tace komi ba.
     “Kin samun ne?” ya tambayeta.
    “A’a” ta amsa a takaice cikin muryan kuka.
   “Kuma shine bara kizo ki fad’a min ba? Come right away.” Nan ya katse fuskarta taje ta wanke sannan ta shiga elevator zuwa office nasa. Kallonta yake sannan ya karanci kuka taje tayi, sekuma yaji wani iri besan mesa ba presence na Fannah affects him yanzu. “Make me coffee and leave, na sallameki na yau.” Dad’i sosai taji amman bata nuna masa ba, nan da nan ta had’a masa cikin flask sannan ta fice. Bayan ta fita ya taso ya zuba kad’an cikin cup tare da zama kan kujera, seya kai coffeen baki seyaji kuma bayasan sha, wayasani ko san dayake ma coffeen ta ne yasoma dawowa kan Fannah. “No way!” ya fad’a a fili. Coffeen ya mayar cikin flask d’in shi a dole ya fasa sha bada jimawa ba yatashi yasake juyewa cikin cup duk yadda yayi ya hana kansa ya kasa he is already addicted to it.
Shima bada jimawa ba ya rufo office nasa yayi tafiyarsa, instead yaje gida seya wuce paint house nasa ba tunanin abinda yakeyi sena Fannah ya rasa meke damunsa kwalban giyansa ya d’auko ze sha abin mamaki ya tsaya cak kalamun Fannah na yadena shan giya yasoma yawo masa a k’wak’walwa. “Damn it!” Ya fad’i tare da rufewa ya mayar cikin fridge d’in. Toilet ya nufa ya rage kayan jikinsa tare da kunna shower ruwa na sauk’a jikinsa.

*****

Fannah kuwa tun isarta gida ciwon mara ya rik’e ta alaman wata ya zagayo kenan, haka tata fama da ciwon gashi kuma tak’i shan magani. A haka har bacci ya saceta a wahalince. Cikin baccin ta soma yin mafarkinta na kullum akan wanda yayi raping nata yadawo ze sake mata. Firgit ta farka ta soma kuka tana ihu Mami dake tsakar gida ne tashigo a guje da k’yar tasamu tayi calming Fannah tayi hugging nata. “Ya isa Habibti ki cire wannan abu daga ranki, ace yau shekaru nawa sede baki kwanta ba zakiyi mafarkin abin. Ya isa haka mana.”
“Mami wallahi inaji mutumin ya matso kusa dani wai yana *_TARE DA NI_* Mami tsoro nakeji.”
“Shhh! ya isa mafarki ne in shaa Allah kin rabu da mutumin har abada bashi ba ke, kinji? Ya ciwon marar?”
“Mami har yanzu yana min ciwo.”
“Toh kink’i shan magani ba dole ba, kin kwan biyu bakiyi ciwon ba ma ai Allah kawo sauk’i deh, sannu ki huta in jikin be sake kiba gobe barakije aiki ba.”
Sanyi sosai Fannah taji har cikin ranta, gobe barata je aiki ba.

Washegari Anas ya tashi da coffeen Fannah yayi breakfast sannan ya nufa office shiru shiru har 8:30AM Fannah bata zo office na “lallai ma yarinyan nan ta gama raina min wayo” yace a ransa tare da ciro wayarsa ya kira lambarta.

****
Afrah ne zaune kan Fannah suna hira, sosai Fannah taji sauk’i saboda Mami ta tilasta mata sanda tasha maganin jiya amma da taga Mami seta shangwab’e wai jikin ba sauk’i. Wayarta ne ya soma ruri aiko tana kai kallonta kai taga Mr. Fauzi “ungo Afrah gashi ki d’aga kice masa banida lafiya ne kinji? Zan baki 1k kisa kati.”
“Dagaske?!” ta tambaya tana washe hak’wara.
“Na rantse” Fannah ta tabbatar mata, ai karap ta d’aga wayar Anas yayi niyan fara suburbud’o mata masifa kawai seyaji muryar da ba nata ba “hello Mr. Fauzi.”
“Hello” yace cikin sanyin murya kamar ba shi ba. “Afrah ce?” Sanda tasa a handsfree sannan tace, “eh ina kwana Mr. Fauzi?”
“Lafiya call me Ya Anas kinji?”
“Toh Ya Anas, kaji Ya Fannah shiru yau ko? Batada lafiya ne.”
“Batada lafiya meya sameta?” gabad’aya yaji ya damu, a tunaninsa ko hannunta ne da yata sata rubutu jiya yayi worse.”
“Menstral cramp (mp) ne” ta amsa sa a takaice. Bugi Fannah takai mata a cinya “bakida hankali ne?” Ta fad’a k’asa k’asa yadda Anas bareji ba.
“Toh meh ba MP’n bane?” Afrah ta bata amsa itama chan k’asa k’asa.

“Uhmmm toh kun kaita asibiti?” Ya tambayeta shi kansa yaji kunyan zancen. Itama se yanzu taji kunyan abinda ta fad’a masan. “A’a” ta amsa cike da kunya.
“Toh yanzu zan turo mota se a kaita kinji? Ki sanar da Mami.” Kai Fannah take kad’a mata da nufin tace a’a.
“A’a Ya Anas karka damu tasha magani yanzu haka ma tana bacci.”
“Are you sure Afrah?”
“Eh Ya Anas gobe ma in shaa Allah zata dawo office.”
“Toh yayi kyau bye.” Yayi hanging.

“Bakiyi ba wallahi Afrah taya zaki che masa MP ke damuna? Da wani idan kikeson in kallesa gobe mschww! ni wallahi barin koma office ba.”
“Toh meh? Kefa kikace yanada k’anwa ai itama nasan tanayi, kuma mahaifiyar sa ma tanayi me abin jin kunya? Amman fa Mr. Fauzi I mean Ya Anas ya damu da lafiyarki, ko ince yana sanki ma, baki ji yadda ya damu bane?” Shiru Fannah tayi bata tanka ta ba tunanin ya next meeting nasu da Anas ze kasance kawai take wannan kayan kunyan da Afrah ta mata.

Ta fannin Anas kuwa ya kasa gane kan ranan gabad’ai coffeen data had’a masa jiyan ma ya shanye tas, haka kawai yaji yana san sata a idanunsa, yau da be ganta ba seji yake kamar yayi asaran wani abu a jikinsa. Hannayensa biyu yasa cikin gashin kansa yana hargitsawa. “What is wrong with me? I am not missing Fannah, I’m just missing her coffee, thats all.” Model nasa ya ciro dan cigaba da yi ko ze d’an manta Fannah da coffeen t, yana aza hannu kan model nasan se tunanin Fannah ya b’ullo masa akai. “Damn it!” Yayi wurgi da super glue dake hannunsa. A fusace ya mik’e ya nufa wajen fridge nasa yaciro kwalba d’aya daidai ya bud’e yakai baki se kawai kalamun Fannah suka soma masa yawo akai. “Ohh!!! What is wrong with me?” Ido ya rufe yasa kwalban a bakinsa sanda yasha rabi sannan ya ciro. D’akinsa ya nufa ya mik’e kan gado nan ma be bar tunanin nata ba musamman ma dayaji bata da lafiya yasha ganin yadda Amal ke kuka in menstral cramp yakamata.

Haka yayi yayi amman ya kasa bacci, meeting dayake dashi kawai ya tashi ya shirya. Driving ma kasa yi, tuk’asa driver yayi. Ko a wajen meeting d’in yakasa concentrating, har aka tashi besan me suka tattauna akai ba, mutanen kuwa sun karanchi hakan, koda suka tambayesa menene che musu yayi kansa ke ciwo. Daga chan ma gida yasa driver ya wuce dashi sosai Ummie, Amal da Shettima sukaji dad’in dawowansa, Abuu bai gida da yayi murna shima dan d’an kwana biyu da Anas yayi ba’a gida ba ya fitinesa.

Da k’yar Ummie ta ja Amal waje daga d’akin Anas dan barin sa ya huta, bada dad’ewa ba Shettima ya shigo har ya zauna Anas beyi noticing ba, sanda ya tab’a sa sannan firgit ya juya yana kallonsa. “Maza yaushe ka shigo?” Ya tambayesa cike da mamaki.
“About a minute ago tunanin me kake? Tunanin abinda Abuu ya fad’a maka shekaran jiya ne?”
Shi Anas ya ma manta da wan can batu, se yanzu da Shettima ya tunatar masa.

“Shettima ni bansan ina zan samu mace in kawo wa Abuu ba I don’t trust in love.”
“Ya Anas dade kayi hak’uri ka duba cikin ‘yan matanka wacce tafi hankali ko a aura maka Falmata.”
“Hankali? Ai dukansu bame hankali, they are after my look and money, ba wacce take sona tsakani da Allah saboda kud’i na da kyau suke bina. Ni nasani ba macen da zata tab’a sona tsakani da Allah.”
“Akoi Ya Anas kuma ina kan maka addu’a, Allah bayyano maka da ita nan da wata shidan da Abuu ya yanka maka. Macen da zata soka tsakani da Allah, wacce bara ta damu da kud’inka ba, ko kyanka ba, wacce barata damu da duniya da abinda ke cikinta ba, she’ll be a decent girl wanda bata shirin batsa ba kuma ruwanta da jan attention na mutane, me tarbiyya da hankali da kuma ilimi, wacce zata na maka wa’azi duk sanda kayi ba dede ba”

Duk wannan halaye da d’abi’un da Shettima ya lisafo se Anas yaga sak na Fannah kenan. Yaci ace a iya zaman sunnan ta fito tace tana sansa kamar yadda receptionist na sa ta masa da sauran ma’aikatan sa, koda ya bata iphone cewa tayi bataso dan bata da option ne yasa kawai ta amince ta karb’a meaning bata damu da kayan duniya ba kenan.
“NO!!! SHE CAN’T BE THE GIRL” ya fad’i a fili ba tare dayasan yayi hakan ba.
“Wace yarinya kenan Ya Anas?” Shettima ya tambayesa. “Yarinya kuma?” Anas ya wayince. “Wace yarinya? Waye ya kira wata yarinya anan?”
“Kaifa kace ‘no she can’t be the girl’ yanzu. Wata yarinya kak nufi kenan?”

“Kai kacika suratan banza wallahi ni tashi kabani gu, inji da problem dake damuna na neman matan aure in 6 months time.” Se da Shettima yakai bakin k’ofa sannan yace, “Ya Anas kode Fannah ce?”
“What?!” Pillow ya d’aga ya wulla masa wanda tuni ya fice yana masa dariya. Mesa hankalin Shettima ze karkato zuwa kan Fannah? Mesa se ita? To kode na fara santa ne?
“No way” ya fad’i a fili. “I can’t love Fannah, mezanyi da ita? Coffeenta kawai nakeso ba ita ba, kuma shi d’inma daga yau nadena sha. I can’t fall for Fannah.”


*© miemiebee*

beeenovels.mywapblog.com
[12:50, 12/18/2016] ‪+234 903 612 6826‬: •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°


Please Login or Register in order to submit comment