Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

even mind calling me.”
“I’m sorry, so yaushe zaka dawo?”
“Are you missing me already?” Ya tambaya yana jin dad’i.
“Yes I am missing you, I’m missing your your girman kai da masifa.”
“Ai nabar yin masifa yanzu.”
“Anya kuwa?” Ta tambaya tana murmushi.
“Yes, nikuma I’m missing your coffee, your crying and face.” Dad’i sosai taji ya ratsa ta, wannan na d’aya daga cikin abubuwan da takeson Anas, he is very sincere komin ya gaskia take yana fad’i unlike ita, itama tayi missing kyakkyawar fuskarsa sabida rabuwansu da juna tin ran tuesday yau thursday amman ta b’oye masa.

“To be sincere I miss your face you too.”
“I know you would, dole zakiyi missing handsome face d’ina ga kuma unguwan ku ba kyawawa ko?”
“Mr. Fauzi kaga irin halinkan ba, sesa banasan fad’a maka abu kacika feeling dayawa, I have to go Mami na kira na.” Karap ta katse tana murmushi, bawani Mamin dake kirarta bata san me zata ce masa bane kawai, duk lokacin da take waya dashi setanajin wani iri.

Shigowar Afrah d’akin kenan ansha gayu kamar ba gobe, “Afrah ina zuwa haka?”
“Wallahi hot baby na ne yazo, yana jira na ma yanzu haka. Madubi nazo kalla in fice” aiko tana ganin kanta ta fice. Tsaye tasame Shettima yayi crossing arms da legs jikin motarsa sanye yake da wata farar half jampa.
“My queen kinyi kyau” yace da ita alokacin data gama k’arisowa kusa dashi.
“You too my king.” Hira suka sha kamar ba gobe se kusan Maghrib yace ze tafi bundle na d’ari biyar ya tsakulo a aljihunsa ya bata. Ido tazaro “hot baby duka wannan?”
“Eh nakine sweetie, jiya mun samu profit sosai a business namu shine nima nace barin kawo miki rabon ki.”
“Thank you hot baby” ta amsa. Bayan ta dawo ciki ta wula kan gado ta sami Fannah. “Ya Fannah you won’t believe this.” Bandir na d’ari biyar d’in ta ciro ta miqa mata.

“Ke ina kika samo wannan?”
“Hot baby na yabani.”
“Shettiman? Aina yasamu? Yana aiki ne?”
“Yana business mana.”
“Business? Toh aini bansani ba. Ke Afrah bafa haka ake soyayya ba, ai kika cigaba da amsar kud’i dayawa haka gunsa seki talautar dashi.”
“Toh ai bani yayi ba rok’a nayi ba. Wayyo! A gobe zanje in siyo Iphone nima.”

****

Chan dare misalin k’arfe goma sha d’ayan dare a Morocco ko bacci Anas yakasa se juye-juye yake, ga gajiya amman yakasa baccin ba abinda yake inbanda tunanin Fannah. “Oh God! What is wrong with me? Why can’t I think of anyone se Fannah? Why?” Pillow ya d’au ya rufe fuskarsa dashi ko ze d’an rage tunaninta, ai se worse ma yake. Wayarsa ya d’ago daga kan bed side drawer ya kirata. Tana cikin baccinta tajiyo ringing na wayarta kamar wacce zatayi kuka ta d’aga ko duba wanda ke kira batai ba.
“Fannah” ya kira sunanta. Jin muryarsa ta tashi ta zauna.
“Mr. Fauzi what is it?” Ta tambaya cikin bacci.
“What are you doing?”
“Bacci mana” ta amsa sa a takaice rai ad’an b’ace.
“Okay shikenan” ya fad’a kamar d’an yaron da aka mai rowan sweet ya katse wayar. Wayar ta ajiye ta koma bacci sede kuma daga yadda Anas ya mata maganar kamar bacci ya kasa, sekuma taji tausayinsa yaje chan besan kowa ba wayar nata taja ta kirasa yana gani yak’i d’agawa.
“Toh ko har yayi bacci ne? Barin sake gwadawa inga.” A karo na biyu ne ya d’aga “Anas” ta kira sunansa a hankali, jin shiru tace. “Anas are you there?”

“Yes” yace chan k’asa k’asa.
“Ka kasa bacci ne?”
Nama “yes” yace. Shiru tayi tana nazarin me zata ce masa chan tace, “uhm if you need someone to talk to I’m here for you.”
“Just go, jeki kwanta.”
“Anas kaifa?”
“I can’t sleep” yanason yace mata saboda yana missing nata ne ya kasa bacci amman kuma yak’i.
“I can’t either.” Ta fad’a.
“Why? Ba bacci kikeyi ba yanzu?”
“Not anymore, you can’t sleep I’ll stay awake with you.” Dad’i yaji sosai.
“Are you sure?”
“Yes” ta fad’a tana giad’a kai.
“Thank you.”
“So yaushe zaka dawo?”
“Maybe in 3-4 days time.”
“Okay Allah kaimu.”
“Ameen, so ya Afrah da Shettima?”
“D’azu ma yazo wajenta, wai dama Shettima na business?”
“Business kuma wani erin business kenan?” Anas ya tamabaya cike da rashin fahimta.
“Nima I don’t know haka yace mata wai yana business harda kawo mata bundle na N500 dayazo.”
“Are you serious?? Lallai ma Shettima, abinda zeyi da kud’in kenan dama. LOL”
“Kamar ya Anas?”
Nan ya labarta mata yadda Shettima yasamu kud’in. Dariya sosai dukansu suka b’arke da. Haka sukata hira kamar ba gobe sekace ba Mr. Fauzi ba, sun fi awa suna waya har bacci ya sace Fannah.
Jin shiru ya kira sunanta, shiru bata amsa ba “kinyi bacci ne?” Nanma shiru. “Goodnight” ya fad’a ahankali, k’in kashe wayar yayi yana d’an jin nishin Fannah da haka shima ya samu yayi bacci wayar mak’ale a kunnesa.


*©miemiebee*

beeenovels.mywapblog.com
[12:54, 12/18/2016] ‪+234 903 612 6826‬: •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫

❣🎀❣🎀❣

*_written by miemiebee👄_*

In dedication to *Aunty Sis💕*
5⃣5⃣





    Shirye shiryen biki aka soma da zafi-zafi ba makawa, koda Anas ya sanar da Abuu be gama gina gidansa ba shida Fannah zasu zauna a hotel for the mean time bayan bikin ba’a samu matsala ba, Abuu ya amiche haka zalika su Baba ma. Duk wani had’in magunan addini na gyaran jiki Mami ta tanadar wa Fannah, itade Fannah ba wanda take sha saboda ba point koda ta sha. Tun ranan da aka yo tambaya aka sa rana, kalma be sake had’a Anas da Fannah ba, iya k’ok’arinsa yake ya mance da ita tun batun da Baana yataho masa dashi. Akan ya kuskura yacigaba da coming in contact da Fannah to dole soyayyan dayake k’ok’arin kashewa yayi rising yazamo end nasa kenan. Shikuma abinda bayya so kenan, bayason soyayyar dayake ma Fannah yaje ko ina dan haka yafita daga harkarta gabad’aya.

Ta fannin Fannah ma dad’i taji atleast kwana biyu da bayya kirarta tsoron da take masan ma ya d’an ragu. Ko Shettima besan contract marriage ne tsakanin Anas da Fannah ba. Inbanda Baana ba wanda yasani, shima d’in dan ya fiye gane-gane ne Anas ya sanar dashi.
Ana saura sati uku biki ne su Ummie suka kawo kayan lefe, komi ita ta siya kud’i kawai Anas ya bada. Akwatuna ne turum ba adadi, koban fad’a ba kuma kunsan ya auren youngest billonaire ze kasance komai over aka yisa. Kud’in d’inkin da aka kawo ma nan yayi over. Abinda ya kama gowns da Fannah zata sa a duk events da za’ayi sun d’inka sun kai mata. Ummie che tasa Anas a gaba se anyi events d’in dan ko kad’an baya so, shi be k’i a tofe fatiha ba kad’ai.

★★★★

A yau ana sauran sati biki, tsabagen tunani har wani rama Fannah tayi. Zaune take ta had’a tagumi a d’aki da plate na abincinta gabanta da alama ko tab’awa batayi ba, da shigowar Mami kusan minti biyu ammmana Fannah batayi noticing inta ba tsabagen yadda tayi zurfi cikin tunani. “Habibti” Mami ta kira ta cikin salon mahaifiya cike tausayi. A firgice ta d’ago kai “na’am Mami, yaushe kika shigo?”
Bayan Mami ta zauna a kusa da ita tace, “Habibti wai me haka ne? Tun da aka sa ranar bikin nan kika soya, tunanin me kike?”
“Mami babu” ta mata k’arya.
“Ko bakison Anas d’inne naga ko duban kayan lefen bakiyi ba.”
“Ina sonsa mana Mami.” tayi faking murmushi.
“Toh magunanki fa kina sha? Kinsha yau fa safe?”
“Eh Mami nasha.”
“Ki gama cin abincin ki, seki huta zuwa anjima me gyaran jikin zatazo kema kin sani.”
“Mami ni walllahi asaran kud’i ne kawai wannan abu, na fad’a miki ba amfani.”
“Yoh! Ji ‘yar mutane. Ummie su kawo kud’i suce ayi maki gyaran jiki sekice asaran kud’i? Uhn uhn fa Fannah, tam! Maza gama ci ki huta.” Tana kaiwa nan ta fice.

*****

“Ummie wai dan Allah se anyi wani shirmen dinner d’innan ne?” Cewar Anas daya baje kan gado da wayarsa a hannu se latsawa yake.
“Se anyi Anas ace bikin d’a na guda bikin billonaire kamar ka bara ayi hidima ba? Ni na fad’a maka kayi kayi ka amso d’inkunan ka gun tailor nan. Nan da gobe za’a fara events d’in.” Banza yayi da ita. “Ko bakaji ba?”
“Naji” yabata amsa blankly. Bayan ta fita ya saki numfashi tare da rufe idanunsa yana tunanin wai aure zeyi in just a week time. Kap friends nasa ba wanda ya yarda dayayi inviting nasu d’aurin auren, suna ganin invitation card amman sunka k’i yarda.

Ya rasa me ke damunsa yanzu, a da daya tafi Morocco tsantsan yadda yake missing Fannah yasa yayi pushing through da maganan auren amman a yanzu seyaji bayaso, dukda kuwa contract marriage ne amman bayyaso anymore, yasani the more suke cigaba da zama under thesame roof da Fannah he will develop feelings for her sesa ya yanke hukunci koda anyi bikin bare na shiga harkarta ba bayan wata shida ya sallameta ta huta shima ya huta.
Rurin da wayar sa ya soma yi ne ya tsamo sa daga duniyar tunanin daya wula. ‘Fannah’ yaga rubuce kan screen d’in. Yana gani har call d’in ta tsinke be d’aga ba se a karo na biyu nan ma be amsa ba.

“Hello Mr. Fauzi” siririyar muryata tace.
“Yes Miss Aleeyu” ya amsa back. Sosai yayi missing muryarta, fuskarta and everything amman babu kamar coffeen ta.
“Mr. Fauzi batun wedding events d’inne nace please kasa ayi cancelling.”
“Why?” Ya tambayeta straight forward kafin ta amsa yace, “nid’in an fad’i miki so nake ne? Auren entirely ma ba so nake ba, so kamar yadda nayi hak’uri kema yazamo miki dole kiyi hak’uri ayi komi ya k’are. Is this the reason why you called?”
Chan k’asa k’asa tace, “yes.”
“Then I’m hanging up.” Karap ya katse wayar. Takaici ne da bak’in ciki ya rufe Fannah. Wai mesa Mr. Fauzi yake behaving haka? Ko wani abun ta masa? Inma hakan ne chan ta matse masa.

_1 day later..._

A yau ne aka soma events na bikin ANAS IBRAHIM FAUZI dakuma FANNAH ALEEYU. Da walimah aka soma wanda Anas beje ba. Kyau kam ban tab’a gabin Fannah tayi erinsa kamar na yau ba, danko this is her first time applying heavy makeup. Sede sam ba fara’a a fuskarta kasancewar aske mata gira da makeup artist tata tamata wanda batasan tayi ba seda aka gama. Sosai taji haushi tata mata masifa kuma. Tsayuwa dan bayanin had’uwan wajen kuma b’ata lokaci ne, wajen cike yake da fans na (Tana Tare Da Ni) kowani corner na wajen su ne duk sunsha kyau cikin bak’in aboyoyinsu. Wa’azi sosai aka zage wajen wanda har yasa Fannah kuka in ta tuna ba auren gaske bane. The next day akayi English dinner wanda Anas yasha b’akar suit nasa da white shirt ta ciki dakuma black tie, kyau kam mashaa Allah a yayinda Fannah take sake da white ball gown. Duk sunyi kyau.

Fans de su suka cike hall d’in kowacce tasha had’ad’d’en gown nata se kashe selfie akeyi da Mr. Fauzi kad’an ne masuyi da Fannah sabida duk masu son Mr. Fauzi ne cike wajen nima de ina d’aya daga cikinsu.
The next day akayi Mother’s Eve wanda Anas yasha farar babbar rigar da ban tab’a ganinsa ciki ba. Tsayuwa dan bayanin kyan da yayi shima b’ata lokaci ne. Kamar yadda yayi kyau haka ma Fannah tayi. Makeup artist nata gaba take wajen fidda kyan mutum. Itama farar gown ne a jikinta. Shikansa Anas yakasa d’auke idanunsa daga kan Fannah, skin nata wani glowing yake dan yadda yasha gyara. 2 more days aka d’auka ana events, a takaice events biyar akayi a bikin wanda a safiyar ranar Asabar aka d’aura auren ANAS IBRAHIM FAUZI da FANNAH ALEEYU akan sadaki dubu d’ari biyu da gwalagwale. Da yammacin ranan su Ummie da sauran dangin miji sukazo d’aukan amaryarsu. Kukan da Fannah tayi bana misantuwa bane har cewa take ta fasa auren ma ita kawai Anas ya saketa. Kuka take wanda har tasa Mami dasu Afrah ma, Aiman kam sanda tama wata babbar mace rashin kunya ita sam a bar mata Ya Fannar ta.

Da hawaye da majina aka samu aka ciro Fannah daga gidansu. Kwalyan yau shine beyi kyau ba cikin sauran dan yadda fuskar nata ya kumbura tam idanun sunyi ja suma sun kumbura. Shikansa Anas daya ga fuskarta a wajen event d’in seda yaji wani eri, wani irin kuka tayi? Wani irin hawaye tayi asararsu a yau? How he wished he was there da take kukan ya hanata. Daga wajen dinner driver ya wuce da Fannah da Anas masauk’insu. Ba abinda take cikin motar se kuka ba makawa afarko yayi niyyan ya share ta dan ma wani haushi ta soma basa, sekace aljani aka aura mata ai yaga shima ba san auren yake ba inji sa da fad’i. Shi mesa bai kukan se ita? Ganin tak’i yin shiru yace;
“Fannah kukan ya isa mana, meh hakan please? Ke kikayi signing da kanki to kukan meh?”
“Ni na fasa, nafasa kawai ka kaini gidanmu dan Allah.”
“Aww hakane? Toh nak’i bara a kaikin ba, ai ke kikayi signing da kanki. Driver lets go I beg.”
Sautin kukanta ta k’ara ayayinda ya ciro headphone ya k’ure da wak’a a farko, sekuma ya tuna wa’azin da Fannah ta masa dukda ayanzu haushi take basa seyaji still bayason ya sab’a wa promise daya d’aukar mata. Switching yayi daga wak’a ya miyar qira’a sautin Sudais. Haka ta ta kuka har seda suka iso hotel d’in. Tafito ma tak’i.

“Fannah wai me haka ne? I’m tired I want to rest kifito lets go will you?” Ko tanka sa batayi ba se kukan ta data tasananta.
“Ohhhh God!” ya fad’i a fusace. Zagayo wa yayi ya bud’o k’ofar natan tare da finciko ta da hannu. Se k’ok’arin k’watan hannunta take amman takasa be saurara mata ba seda suka isa har d’akinsu bayan ya rufe k’ofar ya sake ta. K’asa ta sauk’a tana kuka. “Thank God na fito da headphone d’ina.” yace tare da mak’ala headphone d’in a kunnensa ya zauna kan wata couch tare da juya mata baya. Bare iya sauraron kukanta ba kamar yadda bare iya ce mata tayi hak’uri ba saboda haushin data basa na kukan da take tayi. Tafi minti talatin tana kuka wajen, ganin ba ubangiji se Allah ta tashi tare da tattara gown nata, inda aka ajiye mata kad’an daga cikin akwatinta ta nufa tare da jawo na kayan baccin ta. Toilet ta nufa dashi se anan Anas ya juyo yaga tarufe k’ofar toilet d’in. Rigar jikinsa ya rage ya bar daga vest se short nicker. Wayarsa ya d’auko yana d’an danne-dannensa ciki chan ya kira waya ya musu ordering abinci dan rabuwansa da abinci tun breakfast he is sure Fannah ma haka. Fried rice and chicken lafiyayye aka kawo musu plates biyu, ko tab’a wa beyi ba yana jiran fitowarta su ci tare.

Doguwar tuska Fannah taja a bathroom d’in wanda daba dan famfo na a bud’e ba da Anas ya jiyo ta. Akwatin tas ta zazzage ba kayan baccin daya mata duk sunyi tsireci dayawa daga wanda sama a bud’e se wanda k’asa a bud’e se wanda tsayin dududu iya guiwa ne. Kamar wacce zata sakeyin kuka ta soma miyar dasu cikin akwatin duk takaici yabi ya isheta. Chan tasamu wani d’an dama dama ciki tsayinsa iya guiwa ne yanada dogon hannu amman kuma transparent. Wajen k’irjinta kuwa kad’an ne a bud’e, ahakan wai shine salihi cikin night gowns d’in. Bayan ta ajiyesa a gefe ta soma jan zip nata dan cire babban gown me uban nauyin dayake jikin nata. Dambe take da zip d’in amman takasa ja, harda guntun hawayenta. Ganin ba ubangiji se Allah ta ciro wayarta daga jakar ta dannawa Mami kira tana kuka sama sama.

“Hello Habibti na.”
“Mami” takira sunanta cikin sautin kuka.
“Habibti kukan be isa bane har yanzu?”
“Mami dan Allah kizo ki d’aukeni mu koma gida dan Allah.”
“Wace erin magana kike Fannah? A fasa auren kenan ko meh?”
“Eh Mami a fasa na hak’ura.”
“Fannah ai hak’uri zakiyi nima haka na hak’ura, nan da lokaci k’alilan zaki saba kinji Habibti?”
“Mami tsoro nakeji.”
“Ya isa haka kinji? Ba abinda ze faru in shaa Allah.”
Majina taja, “Mami na kasa jan zip d’ina kizo ki ja min please.”
“Habibti yaushe ne zan bar gida inzo har inda kike na ja miki zip d’in? Ina Anas yake?”
“Mami ni bansani ba dan Allah kizo.”
“Kiga Fannah jeki sami Anas kice ya ja miki zip d’in kinji? Ze ja miki.”
Kuka ta fashe da cikin wayar. “Mami ni banaso dan Allah kizo.” Da k’yar Mami tayi convincing nata ta yarda zataje tasamu Anas d’in. Bayan ta ajiye wayar ta wanke fuskarta data kumburo kamar ba gobe. Anas bawan Allah har yagaji da jirarta amman still be tab’a abincin ba.

K’in fitowa daga bathroom d’in tayi se k’ok’arin jan zip d’in take ganin ba mahalicci se Allah ta fito daga baya, kallonta Anas yake danko ya rasa me take tun d’azu ciki. Ba wanka tayi ba, ba kuma rage kayan jikinta tayi ba. Toh me ta tsaya yi? Kallonta yake a yayinda take takowa har gabansa ta k’ariso da kanta a sunkuye ko kallon sa batai ba. A nitse ta juya bayanta tare da tsugunawa, kallonta yake cike da mamaki me take shirin yi?
“Sir help me kaja min zip please.” Se yanzu ya gano dalilin daya sa ta jima a bathroom d’in. Yi yayi kamar be jita ba. “Sir please help me” ta fad’a cikin sautin kuka. “I’m not Sir I’m your husband Fannah, so correct yourself.”
“Anas kaja min zip d’in please” ta fad’a ba gardama. Zip d’in ya k’are ma kallo sannan ya aza hannunsa akan bayan ta. Wani electrification sukajiyo within them dukansu biyu, kansa ya kawar dan bai son kallon bayan nata gudun abinda ze iya haifar wa. A hankali yaja mata zip d’in zuwa tsakiyar bayanta. Da sauri ta mik’e kafin ya gane mata tsireci. “Thank you” tafad’a a hankali alokacin da ta d’ago kai tana kallonsa. Da mamaki taga bama kallonta yake ba nufin bema ga bayan nata ba keman, hamdala ta saki ganin baida niyan amsa godiyar da ta masa ta koma bayin ta sa lock sannan ta cire kayan, ruwa ta watsa ta goge jikin ta da kayan data ciren sannan tasa na baccin. Babban hijabin ta data d’inka na musamman ta zira akai tafito tare da jawo akwatin nata. Ko kad’an Anas be kallanta. Akwatin ta miyar inda ta d‘aukosa.

“Come lets eat” yace da ita.
“I’m not hungry.”
“Fannah banason surutu, you didn’t eat I know kizo muci abinci.”
“Banajin yunwa.” ta fad’a dukda kuwa yunwa takeji kamar ba gobe, rabuwarta da abinci tun safiya sede batada appetite na cin abincin ma.
“As your husband nace kizo muci abinci.” Zata sake magana ya daka mata tsawa “now!” A hankali ta tako zuwa inda abincin yake ta d’au plate nakusa da itan daidai zata juya ta koma kan gadon kenan ya rik’e hijabinta “sit here lets eat.”
“Anas zanci achan.”
“Nikuma mijinki nace anan nakeso.” Gudun tsinuwan mala’ikun rahma ne kad’ai ya sata zama a kusa dashi. Spoons bekai goma ba tayi tace masa ta k’oshi ko tab’a kajin kai batayi ba. Bece mata komai ba illa binta da kallo da yake, wayanta ta duba taga k’arfe 11:30PM. Pillows da aka jera kan gadon wanda sun kusan kai goma ta zubar duka k’asa kallonta Anas yake bece ko uffan ba.

“Anas wani side kafiso? Zan kwanta.” Banza yayi da ita. “Kaji Anas?”
“I prefer the rightside.” yace cike da nuna rashin damuwa. Tokari taji a zuciyarta wanda harta fuskarta seda ta nuna. Ko a gida a gefen dama take kwanciya, shi Anas kuwa da gangan ya ce gefen daman yafiso dan yasan sarai itama daman zatace tafiso tunda take tsaye ta wajen. Ba dan tanaso ba ta koma leftside d’in tare da tattaro duka pillows d’in shide Anas kallonta yake. One by one tasoma jera pillows d’in ta hanyan yin katanga tsakaninta dashi.
Lallai ma Anas yace a zuciyarsa. Me take nufi? Tunani take waiko insun kwanta ze mata wani abu? Toh she is decieving herself. Bece da ita komai ba seda ta gama raba tsakaninsu sannan yace, “ni barin had’a kwanciya dake ba, zan kwanta kan kujerar nan so ki kwantar da hankalinki” ya nuna dogon 3 seater dayake zaune akai. Bata ko kallesa ba sede ta kasa b’oye dad’in da taji.

Da hijabinta ta kwanta, bayan tagama tofe addu’o’inta ta rufe ido. Nanne Anas ya tashi ya fad’a bathroom ya watsa ruwa shima. Sabuwar nicker yaciro yasa. D’aya daga cikin blankets dake kan gadon ya zaro da pillow d’aya ya koma kan kushion d’in. Alokacin Fannah tayi nisa da yin bacci, wuta ya kashe ya koma ya kwanta.
Da misalin k’arfe 3:23AM na dare Fannah ta farka tare da tsala wani irin ihun daya firgita Anas lokaci guda a sanadin mafarkin data sabayi datayi.

“Wayyoo Allah! Dan Allah kayi hak’uri karka tab’ani dan Allah bawan Allah dan Allah.” Hawaye take sosai tana b’ari gawani gumin dake k’eto mata duk da AC’n dake huruwa. “Mami! Mami! Mutumin.” Anas besan lokacin daya taso

Please Login or Register in order to submit comment