Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lokacin Ya Khaleel ya hallaro shima, ganin d’ansa cikin motan polisawa ya falfala da gudu izuwa wajen.

    “Officer ina zaku kaimin d’a dan Allah ku sako shi kuyi hak’uri. Farouq me kayi?” Nan ya juyo wajen Anas da Fannah. “Mr. Fauzi dan Allah kayi hak’uri kasa su sake min d’a wayyo Allah! Kayi hak’uri dan Allah bare sake ba.”
    “Ka sake had’a ni da Allah believe me kaima zaka bisa cell d’in. Take him away” yace da polisawan.
    “Fannah dan Allah karki bari atafi miki da miji ki rok’i Mr. Fauzi please.” Hawaye sosai Fannah take dan tausayi irin nata setaji duk she is ready to forgive them abubuwan da suka mata. “Mr. Fauzi dan Allah kayi hak’uri.”
   “NO” yace mata a tsawace “take him away, NOW!” A 360 suka bar wajen da Farouq. Kuka Ya Khaleel yake “Allah ze sak’a min wallahi, d’a na be maka komai ba kasa aka tafi dashi simply because kaga baida gata in shaa Allahu zan tara kud’i inyi bailing nasa, kekuma Fannah kisani Farouq shine mijinki ba wannan dayake miki wasa da hankali ba.” Yana kaiwa nan ya fice.

    Kuka me sautin gaske Fannah ta fashe da, “Mr. Fauzi why? Dan Allah ka dawo dashi I beg you please, banasan ka mutu, banasan wani abu ya tab’a ka. Ni nace zan aure sa ka sa a sakar dashi, ka sakar min miji.”
    “*Nine mijinki Miss Aleeyu* and that stays that.”
    Cikin kuka tace, “what are you saying Mr. Fauzi kana cikin right mind naka kuwa taya zakace kaine mijina? Ko baka san ba’a wasa da kalman aure bane? Ni ka sa su sake Farouq kawai dan Allah.”
    “Yes Miss Aleeyu nasan me nake fad’a ni zan aureki ba Farouq ba, you are going to be my wife” hannunta yaja tare da zaunar da ita cikin motar. Shima ya zaga ya zauna.

     Hawaye take sosai “Miss Aleeyu for goodness sake kukan ya isa. I’m going to marry you so as to protect you from Farouq atleast duk rashin kunyarsa inyaga ke matar aure ce ze saurara miki koda Babansa yayi bailing nasa, marry me Miss Aleeyu.”
    Kai take girgizawa continiously No! No! No! This can’t be happening bareyi in auri Boss d’ina koba dan haka bama bareyi in barsa ya aureni ba, *BANIDA BUDURCI, BANIDA MARTABA* duk ranan da Mr. Fauzi ya gano hakan ze tsaneni fiye da yadda ya tsani mutuwar sa, I can’t marry him saboda barin iya fad’a masa sirri na ba kamar yadda barin bari yagano hakan ba da kansa kuma.

     “No Sir I can’t marry you, I can’t dan Allah kabar wannan magana, ni kawai release Ya Farouq.”
   
   “Yes, yes you will marry me Fannah Aleeyu. In ma tunani kike ko wani abu ze shiga tsakanin mu ki kwantar da hankalinki. *CONTRACT MARRIAGE* zamuyi.”
   “Contract marriage?” Ta tambayesa cike da rashin fahimta.
   “Yes contract marriage nima some weeks ago Abuu yace se nayi aure, seya aura min wata ‘yar uwarshi Falmata saboda yana ganin I’m still young wataran baran iya managing Enterprise d’ina ba kuma wai ban gama mallakin hankali na ba so yakeson yamin aure, nikuma nace masa barin aureta ba, mukayi deal dashi akan in 6 months time zan nemo mace in kawo masa gida wanda zan aura. Ni koda nan da infinity, k’arshen duniya za’a bani banga macen da zata min ba har inji ina sonta zan aureta ba, I will use you  Miss Aleeyu and fake up a relationshop with you. Ni a rayuwa na banason aure, duk abinda ze had’ani da mace ma hasali banaso ke kad’ai ne...” Ya nisanta “when it comes to you I just don’t feel thesame way. Mu rufa wa junan mu asiri and help each other. Zan aureki for just *6 MONTHS TIME* after then semu rabu ince wa Abuu kinci amana na kin tafi kin barni, kince you don’t love me anymore, you see daga lokacin nan bare sake tak’ura na da zancen aure ba zece I’m broken I cannot move on kamar yadda shima har yau yakasa sake aure tunda Ummimi ta tafi ta barsa. Ke kuwa kinga nasan by 6 months time d’innan Farouq halan ya gaji da jira ya koma inda yafito kinga seki cigaba da tafiyar rayuwarki kamar yadda take da. Nikuma I promise you a k’arshen 6 months d’innan bayan munyi ending marriage d’in zan baki 6 million tunda dama contract marriage ne.” Ido sosai Fannah ta zaro 6 million???? Ta fad’i a ranta.

    
        “Kinga inma so kike kubar garin nan da family’nki zuwa wani garin zaku iya, yadda Farouq bare sake tak’ura muku ba. Kuma a kowani k’arshen wata zanna biyanki albashinki na aiki N500,000 sede bawai zakina min aiki bane still, zan sauk’e ki daga zama min PA, bareyi ace mata ta PA ta ba. I’ll get the papers ready gobe, all you have to do is sign them So what do you say?”

     Shiruu tayi dan tunanin ma ta kasa. Taya zatayi agreeing wa qudurin nan? Contract marriage, how? Setayi decieving kowa kenan tasa su yarda eh soyayya sukayi da Mr. Fauzi har ya kai ga aure? Kuma seya b’ata mata image gun iyayensa, yace taci amanar sa? Gaskia baratayi ba amman kuma intayi la’akari itace ma zata fi benefiting. Dubu d’ari biyar sau 6 miliyan uku kenan plus miliyan shida daze bata ta tashi da miliyan tara kenan. Wow! Zata samu takai Babanta har k’asar waje ayi masa aiki takuma tattara family’nta subar Maiduguri su koma ko Kano ko Kaduna inda su Farouq bara su sake saminsu ba. Zata samu ta sa Afrah ma a makaranta. To yanzu ya? Ta yarda kenan?

     “Miss Aleeyu?” Ya tsamota daga cikin duniyar tunanin data wula. “Have you make up your mind?”
    “Sir naji komai amman seka b’ata min image gaban iyayenka ne su d’au mutumiyar banza ce ni?”
    “Yes Miss Aleeyu this is the only way zan kub’uta, the only way Abuu zeji tausayi na bare sake min maganar aure ba har se in ni na masa.” Kai ta gyad’a a hankali “Sir amman baramu na had’a kwanciya bako?”
    Lallai ma yace a ransa, shi d’inda ko wace mace nada burin ganinsa kan gadonta ita tasamu zata tsaya tana masa tsiya.

     “Miss Aleeyu nima ba so nake ba dan yazama dole ne, ofcourse we will share a bed amman ba abinda ze shiga tsakanin mu, in ma gudun abinda kike kenan, kisani banida interest cikin wancan abin ko physical contact ban yarda ba, lokacin da zamu iya tab’a juna shine only if either your family or my family visits saboda kar su gane faking auren mukeyi.”
     “Sir you mean barin sanar da su Mami ba? Ai ya kamatasu su sani-”
     “Bekamata ba” ya katse ta. “Ko Afrah ban yarda ki fad’a mata ba, this is our secret dan the moment kika sanar da mutum d’aya kin mana ruining komai kenan. Don’t tell anyone, clear?”

    Kai ta gyad’a tana nazarin ya zata soma b’ullo wa family’nta da wannan zancen auren Mr. Fauzi. Ai se suce dama tuni soayyaya ke kai ta office nasa ba aiki ba.
     “Good” yace. “So starting today zakiyi faking zama girl friend d’ina saboda kar mutane suyi suspecting relationship namun bana gaskia bane.”
       “Is that necessary Sir? Senayi pretending zama girlfriend naka a idan mutane?”
     “Yes Miss Aleeyu kidena san abu kina kaiwa kasuwa, bakiya san zama girlfriend d’inan ne? Sure kinaso so stop pretending and let urself celebrate.”

    “No ni banaso” ta kare kanta.
   Wani shu’umin murmushi ya saki mata. “In ma saboda Yusuf saurayin kine kike wannan abu gwamma tun wuri ki bari, kije kiyi breaking up dashi dawuri dan baraki b’ata min reputation ba ace kina dating d’ina kuma kina dating me aiki k’ark’ashi na ba.”
     “Sir Yusuf ba saurayi na bane.”
   “Allah sa” yace ba tare da ya nuna danuwa ba. “So ki bud’e kunnwanki da kyau ki jini, akwai rules da zan kafa miki regarding wannan aure;.
   Na farko shine don’t fall for me, saboda fake relationship ne I will show you love and care amman kisani bana tsakani da Allah bane, so in kika yi falling min ba ruwa na ke zaki karya wa kanki zuciya dan ni ba sanki zanyi in return ba.” Dad’in abin ba yau ta soma jin munanan kalamunsa ba so ko damuwa batai ba. “Ka kwantar da hankalinka Sir ni barin tab’a falling maka ba, business is business”
         “Allah sa ki iya ignoring beauty na. Na biyu we will be hanging out tare, duk inda zanje tare zamuna zuwa irin su dinner ko lunch da ake inviting d’ina so as inyi introducing naki wa bussiness colluegues d’ina. Inada business trip nan da 1 month da 2 weeks zuwa Morocco dake zanje.
   Na uku, I will re transform you, you are now my girlfriend ya kamata ki fara sa kayaki masu tsada saboda mu nuna wa public kin kai ince ina sonki.” Wannan wace erin zagi ne? Meyake nufi? Kaya masu arha take sawa kenan ko meh? Baki ta bud’e zata masa gana. Ya dakatar da ita ta hanyan aza hannunsa kan lips nasa “shh! Bangama ba karki katse ni. I know kinasan kice you are not ashamed, if you are not toh ni I am and that stays that. Hope am clear for now, more rules will follow afterwards...”


*© miemiebee*

beeenovels.mywapblog.com

[12:53, 12/18/2016] ‪+234 903 612 6826‬: •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫

❣🎀❣🎀❣

*_written by miemiebee👄_*

In dedication to *Aunty Sis💕*
4⃣7⃣




  “Baki jini bane?” Ya tambayeta tare da d’age gira.
   “Naji Sir” ta amsa a hankali. “Good and one more thing, learn to call me Anas in public. Bareyi kina kiran boyfriend naki sir ko Mr. ba. Am I clear?” Wani banbarak’wai maganganunsa suka sauk’a a kunnenta, ita rabuwan ta data kira sa da asalin sunan sa tun kafin ta fara masa aiki ta riga ta saba da Boss ko Sir ko Mr. Fauzi. “But Sir na riga na saba.” ta fad’a.
    “Seki saba da Anas d’in shima. Yanzu rufo min k’ofar mota.” Ba gardama ta rufe, basu tsaya ko ina ba se babban shopping mall dake Maiduguri bayan yayi parking ya juyo ya kalleta kallonsan take itama amman take ta kau da kanta. “So kinga cikin mutane zamu shiga am now your boyfriend dan haka karki kirani da wani suna banda Anas, clear?” Kai ta giad’a a hankali. “Me zamuyi anan amma?” Ta tanbayesa.
   “What else? To shop for you.” Ta kai da bud’e k’ofarta kenan ya dakatar da ita “wait, I’m your boyfriend ko kin manta ne? Let me.” Hannunta ta mayar tana jiransa bayan minti d’aya k’ofarta ya bud’u. Hannunsa ya mik’o mata a yayinda ta tsaya tana kallansa dan bata san me zata masa ba. “Grab my hand” yace da ita romantically.
    “Sir-” kallo ya watsa mata “I mean Anas kai fa kace ba body contact.”
     “If we are alone ba, yanzu kuma cikin mutane zamu shiga we have to pretend like other lovers do, now grab my hand.”
     “Sir I mean Anas amman haramun ne ba kyau, you are not yet my husba-” bata k’are maganar ba yakama hannunta tare da fito da ita daga motar. Janta ya fara suna tafiya se k’ok’arin k’watan hannunta take takasa, bece mata komai ba sanda suka iso daidai gaban k’ofar ya tsaya ya kalleta. Chak itama ta tsaida damben k’watan hannun ta datake kanta a sunkuye.
     “Fannah” ya kira sunanta abinda be tab’a yi a gabanta ba. “Stop it okay? Behave yourself.” A haka suka shiga cikin mall d’in idanu ne sosai akansu dan ko ba’a tab’a ganin Mr. Fauzi da mace ba segashi yau da PA’rsa. Wani business colleague nasa ne dayazo shopping shima da family’nsa ya gansa.

    “Mr. Fauzi” ya danna masa kira from far behind atare Fannah da Anas suka juya suna kallon inda suka jiyo muryar. Anas na ganinsa yakira sunansa shima “hey Mr. Mahmoud!” bayan Mr. Mahmoud sun k’ariso da matarsa sukayi hand shake sannan akayi gaisuwa. “This is Miss Aleeyu your PA ko?” Mr. Mahmoud ya tambaya.
     “Yes this is Fanna” ya sake rik’o hannunta gam da nasa yana mirzawa a hankali, electric sparks Fannah tajiyo cikin jikinta. “My girlfriend.”

    “Your girlfriend?” Mr. Mahmoud ya nanata abinda Anas ya fad’i cike da mamaki a iya saninsa de Anas baida time na girlfriends.
   “Yes!” Anas ya jaddada masa, “she is no more my PA right *BABE?* ” Ya juyo yana kallon Fannah. Rasa na cewa tayi chan k’asa k’asa cike da kunya tace, “yy..yyess” ta nisanta “honey ” Wani shu’umin murmushi Anas ya saki. “So Mr. And Mrs. Mahmoud semun sake had’uwa girlfriend ita tanada gajan hak’uri kar mu b’ata mata lokaci se anjima.”
    “Ayi shopping lafiya Mr. And Mrs Fauzi.” A haka sukayi sallama, hannunta rik’e cikin nasa suka nufa wajen inner wears. Me kuma zamuyi anan? ta tambayi kanta a zuci. Me kula kayan wajen tana ganin Mr. Fauzi ta soma washe hak’wara “Mr. Fauzi you’re welcome have a sit please.”
   “No thanks” yace mata tare da k’arisowa gabanta da hannun Fannah cikin nasa. “Dubata wani size ne ze mata.” Baki wangalau Fannah ta bud’e cike da mamaki da kunya gabad’ai wai mesa Mr. Fauzi baida kunya ne? Hijabinta ta hura sede its too late matar ta riga tayi figuring out komai. “Lets say maxi B cup.” “Okay thanks” yace da ita tare da jan hannun Fannah suka shige ciki, wajen bra zalla ya kaita bi yake yana duba tags na jikin bras d’in har ya kai kan tag B hannunsa ya raba da nata tare da d’iban bras d’in ba iyaka ya jibge mata ajiki, da sauri ta tare a hijabinta.

    “Sir I mean Anas meh haka? Its embarrasing dan Allah ka bari.”
     “What so embarrasing Fannah? You are my girlfriend me aciki dan na saya miki inner wears?” Wani sabon row ya kwasa ya sake zuba mata cikin hijabinta. Janta yayi zuwa side na panties yana duddubawa chan ya d’aga guda d’aya yana duddubawa a sama “Mr. Fauzi I mean Anas dan Allah kabari kar a ganka.” Banza yayi da ita tare da ajiyewa, wani daban ya sake d’agawa shima da be masa ba ya sake d’ago wani.

     “Saboda Allah Mr. Fauzi kabari.”
    “I won’t stop se kin fad’a min size naki.”
    “NOO!!” ta fad’a da ihu.
   “Then fine haka zan cigana da nema har sena samu.” Haka yatayi har wucewa ake ana nuna su. Ganin ba mahalicci se Allah ta rufe ido kawai “Sir size na hannun kan ne.” Juyowa yayi kalle ta dawani shu’umin murmushi a fuskarsa. “Good” ya ce da ita kalan size d’in ya riga d’iba har rows uku ganin kayakin sun soma mata yawa ya buk’aci akawo masu trolley dam ya cika d’aya da inner wears zalla sekace kayan lefe ze had’a. “Anas ya isa please ina zan kai wad’annan kayaki?”
“Basu miki bane akawo wasu desingers d’in daban?”
“NOOO MR. FAUZI!!!” Ta masa ihu, trolley’n yaja tare da rik’e hannunta wajen biya suka nufa ya ajiye tare da jawo wani trolley’n daban. Siyayya na fitan hankali yayi wa Fannah tun tana yabari har tagaji, shi kansa be bari taji total amout d’in ba. Har gaban gida ya kaita yasa yara suka shiga da kayakin ciki. “So are you telling Mami ko in shiga in fad’a mata da kaina?”

“Zan fad’a mata da kaina.”
“Yaushe yanzu?”
“A’a se in bikin ya kusa.”
“Kina nufin har se na gama gina gidan tukunnah?”
“Yes Sir.”
“Lallai kam!” yayi exclaiming. K’ofarsa ya bud’e yafita tare da bud’o nata. Hannunta yaja ya fito da ita sannan yasoma janta zuwa cikin gidansu. “Mr. Fauzi dan Allah kar ka shiga zan fad’a mata da kaina.”
“When gobe jibi? I don’t have that time.” Already su Mami suna tsaye jikin kayakin duk mamaki ne d’auke karara a fuskarsu da Afrah harda Aiman. “Laaaa Mami kiga harda bressier” cewar Aiman. D’aya taciro “kuma wallahi daidai dana ya Fannah ne ko Ya Afrah.” Daidai lokacin su Anas suka iso tsakar gidan bra d’in Mami ta amsa tare da b’oye wa a bayanta ganin Mr. Fauzi.

“Sannu dazuwa” ta musu duka. Bayan an shimfid’a musu tabarma suka zazzauna, sede Anas yak’i sakin hijabin Fannah dan dolenta ta zauna kusa dashi. Mamaki ne yacika Mami, Afrah kam gani take kamar a mafarki. Gyaran murya Anas yayi;

“Ermmm Mami you must be wondering me ya kawo ni nan as well as kayakin chan ko? Well Fannah and I have been wanting to tell you amman Allah be bamu iko ba.” Ya juya ya kalli Fannah tare da mata wani killer smile dataji zuciyarta na k’ok’arin fashewa dak’yar ta iya ta mayar masa da murmushin itama. “We two... We two...” Sekuma yakasa k’arisawa nanne Mami tagano bakin zaren.
“Ya Anas soyayya kuke da Ya Fannah?” Aiman ta tambaya, bakinta Mami ta buge “tashi kishiga ciki.”
“Mami nayi shiru.”
“Tashi nace!” Mami ta bud’e mata ido, a sanyaye ta tashi tashiga d’akin Baba.
“Toh Anas shine har se kai da kanka zakazo ka fad’a min? Ke Fannah meya hanaki fad’a min iyyeh?”
Kame kame ta soma “erm.. Erm...” Anas ne ya karb’eta “Mami ni na hanata saboda nayi laifi nafara soayyaya da ‘yarku ban tambayi izini wajen ki ko Baba ba, I’m sorry please.”

“Bakomai Anas nasan bada gangan kayi hakan ba, toh inde blessing d’ina kuka zo nema ni kam na baku, Allah sanya alheri, naji muku dad’i sosai.”
“Mungode Mami” cewar Anas a kunyace. “Yau ma Baba yana bacci ne inasan mu gaisa.” ya tambaya cike da girmamawa.
“A’a idansa biyu barin masa magana” nan ta fice. “Congratulations to you two” cewar Afrah. Kallo Fannah ta watsa mata a yayinda Anas yace, “thank you sistaaa.”
“Toh Ya Anas, Fannah kad’ai aka sani aka ma siyayya mufa?”
“Ke Afrah bakida hankali ne?” Cewar Fannah tana zaro mata ido.
“Toh ke me ruwanki?” Anas ya katse ta “don’t worry Afrah” hannu yasa cikin aljihunsa yaciro bundle na d’ari tare da mik’a mata. “Gashi gobe keda Aiman kuje kuyi shopping kinji? In ya kasa muku ki karb’i number na wajen Fannah ki kirani se in k’ara muku kinji?”

“Yeyy! Ya Anas mungode.” Daidai da fitowar Mami kenan “bismillah Anas kashigo” a hankali ya saki hijabin Fannah tare da mik’ewa ya nufa d’akin. “Ya Fannah ya akayi Ya Anas yasan size naki naga harda bressier ya sayamiki.”
“Afrah wallahi in baki rufa min baki ba sena cicci miki.”
“Uuuhhh! Kode harda panties ne? Soyayya dad’i” hannu Fannah ta d’aga zata bugeta take ta gudu d’akinsu wane ta cinye kud’in.

Bada dad’ewa ba Anas ya fito murmushin dake d’auke a fuskarsa kad’ai amsa ne game da tambayan ya had’uwansa da Baba ya tafi, it was a success. Mami ce ta rakosa waje “toh Anas kaide kullum seka mana wahala mungode Allah saka da alheri ya k’ara bud’i.” “Ameen Mami ni zan wuce.”
“Toh masha Allah Fannah baraki raka Anas nakin bane?” Mami ta tambayeta tana mata murmushin tsiya.
Kamar tace barin raka sa ba sekuma ta fasa tace “zan raka sa Mami.” “Yawwa toh mungode ko Anas a gaida gida.” A sanyaye ta mik’e ta bi bayansa bayan sun fito gaban gidansu yace da ita “toh Mrs. Fauzi thank you koma ciki.”
“Niba Mrs Fauzi bace tunda ba’ayi auren ba tukuna.”
“Ohonki nide adena so ana kaiwa kasuwa. Cikin jakar inner wears d’in akoi kud’in d’inki ciki also akwai wani paper da phone number rubuce ajiki, number’n tailor’n Amal ne naga yana k’ok’rin d’inki seki kirasa kuyi magana, okay?” Can k’asa k’asa tace “okay nagode” tare da ficewa.

Tana dawowa taga su Afrah kan kayan se bud’e bud’e sukeyi. Sanda ta ganta sannan ta soma maganar; “ai dama Mami na fad’a miki akoi b’oyayyen al'amari tsakanin Ya Fannah da Ya Anas bakiga kullum tana zuwa office ba.” Yi tayi kamar bata jita ba takai da shiga d’akinsu kenan Mami ta kira sunanta “Fannah! tsaya” chak ta tsaya. Mami ce ta k’ariso wajen ta “mu shiga daga ciki.” Bayan sun shiga suka zauna kan gado Mami tasa hannunta cikin na Fannah.
“Fannah shin kin sanar da Anas labarinki kuwa? Banasan ku gina relationship kan k’arya ki fad’a masa komai akanki please dukda da k’yar ne agane wani d’a na miji ya tab’a shiganki amman yakamata ki sanar dashi, k’arya ba abar yi bace.”

Rasa na fad’i tayi.
“Fannah Habibti kinyi shiru ko baki fad’a masa bane?”
Qarya ta mata; “ko kad’an Mami, karki damu na sanar dashi komai ahakan kuma yace yana sona ze aureni, ya kuma buk’ace ni da kar in sake kawo masa zancen koda wasa same goes to you to please Mami, maganan ya wuce kar mu sake d’agowa.”
“Toh Alhamdulillah na matuk’ar jin dad’i wallahi, mahak’urci mawadaci kinga amfanin hak’uri kenan. Yanzu koda Ya Khaleel ya dawo se mu fad’a masa kinada mijin da zaki aura.”

“Mami Baffah Khaleel ma bare sake dawowa ba sabida a yanzu haka Ya Farouq yana cell...” nan ta labarta wa Mami komai. Ba abinda Mami ke inbanda sunbud’a wa Anas albarka.

****

Shima Anas d’in daga gidansu Fannah gida ya zarce cinye sa ne kawai su Ummie basuyi ba dan murnan ganinsa da sukayi. Abuu, Shettima kowa yaji dad’in ganinsa. Bayan sun gama cin abinci ya dawo d’akinsa ya jinguna jikin gado, besan dalili ba kawai ya tsinci kansa cikin nishad’i da jin dad’i musamman inya tuna reaction na Fannah data fad’a masa size na panties nata. Knock ne yazo daga k’ofar sa. “Come” yace.
Shettima ne yashigo ya nemi waje ya zauna kusa dashi. “So Ya Anas ina kashiga kwana biyu ka kusan sama Ummie hawan jini Amal kuma ciwon hauka?”
“Nowhere maza just that I needed space to think.”
“Sure?” Ya tamabayesa yana wani murmushin tsiya.
“Yau kuma dawani surutun ka taho?” Ya tambayesa.
Well d’azu aka kirani w“ai an ganga a mall kai da Fannah kuna shopping.”

“Mutane da gulma!” abinda yace kenan.
“Aww dagaske ne kenan?”
“Nima ban sani ba” ya amsa sa a takaice. “Tashi ka fita ma please don’t ruin my day. Nifa na fad’a maka ba san Fannah nake ba I’m just using her and thats all.”
“Toh in tayi tsami mua ji nide a dage ko weekend ne

Please Login or Register in order to submit comment