Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dake neman any chance yabar wajen. “Anas ina wuni?” tasake fad’i cikin wata anniyar murya ganin shine be amsa ba. Shiru yamata, “Shettima ko nama Anas wani abu ne baimin magana?”

      Murmushi k’adan Shettima yayi sannan yayi k’arya “ko kad’an Hafsah mura yake saisa bai iya magana.” Wani kallo Anasa ya watsa masa wanda shi Shettima yamayar da murmushi. Kafin yace wani abu Hafsah tace, “dama zuwa nayi na tayaka murna ne kan scholarahip daka samu cewa nanda ‘yan kwanaki zaka London shine na had’o ma wannan pepper soup sekuma gashi kana mura I'm sure ze d’an wassakar maka da muran ma. Gashi please ka amshi”

        Ganin Anas baida niyan karb’a Shettima yasa hannu ya amsa “kai sannu Hafsah kamar kinsan mura na damunsa kika kawo wannan.” Shettima ka tabatta Anas yasha please ze taimaka masa sosai.”  “Aii karki damu” cewar Kashim “consider it done, zamu tabbata yasha.”
  
      Da murmushi a fuskarta tace, “toh nagode seda safenku.” Sanda ta sake kallon Anas sannan ta fice. Nan Anas ya finciko Shettima tare da kama masa kunne ya murd’a da iya k’arfin da Allah ya basa. “Awchhhh!” Shettima ya sakar da k’ara. Karb’e kulan abincin Anas yayi ya soma tafiya. Baana yace, “ya haka kuma? Nad’au ai baraka ci ba.” Duk suka k’yalk’yale da dariya. Bece dasu komi ba yacigaba da tafiya, “anji kunya” cewar Shettima nan ma be tankasu ba. Yana isa gida ya tarar da Ummee tana ‘yan wanke-wanke kafin ya b’oye flask d’in har ta riga ta gani.

       “Baba na me wancan kake k’ok’arin b’oyewa?” Cewar Ummee da murmushi fal a fuskarta. “Oh wannan!” Ya d’ago flask d’in sama “erm... Erm... Na-”

      “Iyye baba na manya har ‘yan matan naka sun soma kawo maka abinci ne, to yayi kyau. Me aciki?”

    Kamar ya mata k’arya sekuma ya fasa, “pepper soup ne nakawo wa Amal ko kema zaki tab’a?”  “Noo haba! Budurwa takawo wa Baba na kaji kuma se inci je kaci abinka.”  “Kai Ummee da Allah bafa budurwata bace.”  “Hehe!” tayi dariya sosai “yanzu uwar taka kake jin kunya?”  Rashin sanin me zece mata yasa ya wuce ta kawai ya kira Amal suka wuce d’akinsu ya bud’e masu suka sha pepper soup nasu. Ni miemie nace Anas ba kunya yanzu sha yake!? Lol

       Sun ci kusan rabin kazan Shettima yashigo senishi yake da alama gudu yayi ya iso nan. “Yanzu Anas cinye kazan nan zakayi da wannan maras kunyan baraka d’an bani ba nima?”  “Eh bara'a bayar ba” cewar Amal “Ya Shettiman nan shegen kwad’ayi wallahi ko Ya Anas?” Ta sake p’antarar kazar ta kai baki. “Sosai ma Angel” Anas ya amsata. “Wallahi Amal ki kiyaye ni” gwalo ta masa sanin in Anas na gefe da ita ba abinda Shettima ya isa ya mata.

          “Ka kwantar da hankalinka bari mu fita sallan Isha har gidansu Hafsah zanje in fad’a mata ka cinye kazan kap ko k’ashi baka bari ba.” Murmushi kad’an Anas yayi “to ai ko ka fad’a mata ba yadda zatayi ba saboda ban bata fuska ba.” Haka ya dake sanda suka cinye kazan tas shida Amal, pippike da wuya suka ragar sannan Anas ya ceda Amal ta mik’a ma Shettima da yawunsa ke d’iga k’asa.

      Itako ta d’aga ta ajiye mai “gashi Ya Shettima.” Hannunta ya rik’e tare da danna mata nank’washi aiko tasaki kuka harda na munafirci take Anas ya k’ariso ya rama mata.

     ***

     Haka ma da suka dawo sallan Isha Aishar d’azu ta tsaresu tare da masu sallama kap suka amsa illa Anas. Sak batun da Hafsah tayi haka Aisha ma tayi sede nata chips da omalet ne, itama na taya Anas murnan samun scholarship da yayi. Anas na jiran Shettima ya amsa kamar na d’azu aikuwa yak’i. “Dan Allah kayi hak’uri ka karb’i Anas ni badan kasoni na kawo ma ka ba, consider it as a friendship gift please.”

      D’ago blue eyes nasa yayi ya kalleta ciki ciki wanda tuni ta soma shaking tare da kawar da kanta. Ajiye flask d’in tayi a k’asa “dan Allah ka d’auka se da safenku.” Aiko tana shigewa cikin gdansu ba kunya Anas ya d’aga yakama tafiya. Baana yace “andeji kunya” haka suka ta masa tsiya amman ko a kolan rigarsa, duk yasan so suke suci kuma bayarwan ne bareyi ba. Nanma dashi da Amal ne suka cinye wannan karan ko ragowar ma ba’a baiwa Shettima ba.

    ****

        Da misalin k’arfe goman dare bayan kowa ya kwanta a gdan. Anas da Shettima suna kwance kan seperate gadonsu bayan sun gama shan wiwinsu cikin tea. Shettima daya zura wa Anas kallo na kusan mintuna yace, “tunanin me kake haka?”

      “Anas?” Nanne ya dawo hankalinsa “yes! kace me?” Shettima ya kuma nanata kansa “nace tunanin me kake?”

     Murmushi sosai Anas yayi wanda yasa dimple nasa lotsewa sosai, kad’an daga cikin fararen hakwaransa suka bayyano. “My dreams are about coming true.”  “Wani dream kenan?” Shettima ya tambaya tare da tasowa ya zauna kan gadonsa tare da jingina bayansa a jikin kan gadon.

      “Don't tell me bakasan dreams d’ina ba! Ofcourse to be a billonaire se in samu inyi breaking hearts na thousand of women by then kaga na ramawa Abuu abinda mamarku ta masa.”

    “Wai wace erin magana kakeyi Anas? Wai yanzu kana ganin in Abuu yaji wad’annan munanan kalamu daga bakinka zeji dad’i? Haba mana kai baka yafiya ne?”

      “Yafiya! Har yau bansami defination na word d’in a dictionary ba plus in wa’azi kakeson yi kaje masallaci kayi, kagannin nan? Banasan jin wannan wa'azi allow me to get some sleep yadda nasha ’ya’yan wiwin nan.” Nan yaja bargo tare da rufe kansa ciki a hankali bacci me nauyi ya daukesa.

*© miemiebee*              beeenovels.mywapblog.com
     

    
 

         
[16:09, 12/19/2016] Swtbaby:    •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫

❣🎀❣🎀❣

*_written by miemiebee👄_*


0⃣3⃣




   *FANNAH*

      ‘kauyen Bama dake jihar Maiduguri, Borno.

       Kyakkyawar budurwa ce zaune cikin wata ‘yar k’aramar d’aki bisa gaban wata ‘yar madubin da aka mak’ala a jikin bango. Ba komai bane a d’akin illa katifan dake shimfid’e a k’asa seda bakunan sa kaya da leather carpet ciki. Ba shakka basu da arziki. Dududu wannan ‘yar budurwa baratafi 15 years old ba. Tanada haske sosai, da sirirn hanci dakuma plumpy lips, idanunta ba laifi ‘yan manya ne dadai. Gashin girarta acike yake mekyawun gaske ba ruwanta da zana artificial gira [ba erinsu ni ba;( ] in kuwa aka k’are mata kallo sosai za’a ga alamar had’ewar girar ta guda biyu gu d’aya sede be munanta taba hasali kyau ma yak’ara mata. Gashin idanunta a cike suke kuma dogaye, saje ne a fuskarta kwance luf-luf wane na miji (kaman nawa, lol) gashin kanta dana girarta sun had’e dan yawansu. Hannunta gashi ne a kwance dogaye masu mugun kyau.

           Siririya ce de tanada tsawo daidan shekarunta, tana sanye da wata atamfa maroon da torches na white and green, se murza wata ‘yar jan baki pink take a lips nata hankalinta kwance da anganta ansan batada matsala. A lokacin da wayarta k’irar Nokia Asha dake kan cinyarta tayi k‘ara, a hanzarce ta duba tana ganin sunan daya bayyana kai _Ya Ahmad_ tayi murmushin jin dad’i sannan ta bud’o sakon ta karanta kamar haka;

    _my Fannah I'm outside waiting for you yanzu shigowa na gari ko gida ban lek’a ba just wanted to see you_ 
            “yeyy!!” Ta fad’a a fili tana murna. Data gama sa jan bakin ta shafa powder tareda sa kwalli a fararen idanunta take ta dawo wata balarabiya. A garin mike’wa d’an kwalinta ya since ya fad’i k’asa tare da ribbons data k’ukk’ula gashin nata dashi. Fans ko kunsan ya gashin buzayen Maiduguri yake? Erin bak’i k’irin me santsi da tsawo kamar haukan nan? Haka gashin wannan ‘yar budurwa yake.

     Ni kaina miemie dana gani sanda na tsorata dukda cewar ita kad’ai ce a d’akin hakan be hanata yin saurin tattara ribbons d’in gu d’aya da sauri ba tasoma k’ok’arin faka gashin nata gu d’aya saidai dan cikar gashin ta kasa, hannun nata suna nan sirara ba fad’i ga uwa uba gashi har tsakiyar bayanta. Kamar wacce zatayi kuka tafito d’akin “Mami! Mami!” Shiru kukeji wani mutum ne wanda bara’a kirasa da dattijo ba danko befi shekaru irin 44-45 dinnan ba ya lek’o daga wata d’aki wanda ya kasance opposite daga d’akin da Fannah tafito da alama mahaifinta ne dukda cewar basu kama kuwa. “Fannah uwata ya akayi? Tsaya mesa kike yawo da kanki a bud’e haka?”

     Kamar wacce zatayi kuka tace, “Baba ribbon d’in ne yafita kuma nakasa d’aure gashin, Mami nake nema ta tayani.”
“Shine zakiyi kuka uwata?” Cewar mahaifin nata “Mami batanan tashiga mak’ota.”
“To baba Ya Ahmad fa yazo yana jirana a waje ko gida be wuce ba ya zosa nan.”

      “Oh! Keda Ahmad d’inkin nan se Allah. Ina Afrah da Aiman toh?”
“Sun tafi islamiya Baba.”
“Yoh! Kekuma fah?”

         “Kai Baba wai yanzu so kake kace ka manta sauk’an nawa? Abinda har Hajji kaje da kujerar da aka bani danayi na biyu.”  “Haka fah, taho to in kama miki kan.”
“ Yawwa Baba na.” Da gudu taje ta zauna gabansa shima sanda yayi dagaske sannan ya kama uban gashin nata gu d’aya. Banda tsawon gashin gu d’aya. Wawan cika ne dashi saisa Fannah batta iya kamawa. “Toh nagode Baba.” “Yawwa ‘yar akbarka se ganin Ahmad ko?” Ta giad’a masa kai. “Ki sa hijabi fa tukun kuma kice ya gaishe min da mahaifinsa naji wai ya d’anyi rashin lafiya kwana biyu kuma ban samu na lek’a sa ba.” “Toh Baba zan fad’a masa in shaa Allah.”

      D’akinta takoma tad’au wata maroon hijabi wanda ya sake ciro da hasken ta tasa, tare da d’aukar wayarta sannan tafito waje idanunta suna sauk’a kan Ahmad nata ta sakar dawata murmushin jin dad’i. Ahmad saurayi ne me k’imanin shekaru 23. Chocolate skinned yake, yana da kyau dadai gwargwado gasan murmushi. Tsayyayen na miji ne masha Allah!

     “Ga sarauniyata ta fito.” Ya fad’a yana mai murmushi. “Gaskiya wankan nan yayi kyau sosai Fannah, kin ganki kuwa? Looking so take away.”
           “Ya Ahmad kaide kullum seka riga zolayata. Ina wuni? Ya hanya? Gashi ko ruwa ban samu na d’auko maka ba duk na k’osa in ganka.”
          “Laaa ai sarauniyata bata laifi ae, karki damu ni ganinki kad’ai ya kashe min k’ishi.” Hannu tasa ta tare fuskarta a kunyance. “To ya Ahmad mu zauna anan mana kar ka kaji a tsaye.” ta nuna wat benchi.
        “Haka sarauniyar tawa tace? “Haka to za'ayi.” Bayan sun zauna Fannah tace, “ya hanya toh? Ya makarantar?” Hannu yasa ya dafe goshi sannan yace, “so hectic fa Queen, biochemistry akoi wahala. Ga Maiduguri zafi like hell”

       “In shaa Allah ka kusa gamawa, Allah baka sa’a yaya na.” “Ameen sarauniyata.” Kefa ya school ‘yan matan ss2 koh?”
“Kai yaya! School alhamdulillah” Ta fad’a tana murmushi. Hira suka d’an tab’a na ‘yan mintuna. Shi Ahmad ba abinda yake sake jan ransa kan Fannah kamar san addininta dakuma yawan yarintar ta dakuma sa sa dariya da takeyi in suna tare. Fannah batta magana d’aya biyu seta sa alhamdulillah, subhanallah, masha Allah ko jazakallahu bikhair ciki. Yarinyace me tarbiyan gaske, ga hankali da girmama na gaba da ita koda wasa bata tab’a kiransa da sunansa gatsau ba dole seta sa yayan nan kuma bawai they are related bane tsantsan girmamawa ne kawai.

     “Toh yaya na kar na ta jan ka da surutu nasan su Mama duk suna jiran ganinka, kaje gida ka huta.”
            “Toh sarauniyata” hannu yasa cikin jakarsa yaciro wata leather sannan ya mik’a mata.
       “Me wannan kuma yaya na?” ta tambaya suprisingly.
        “ ‘yar tsarabar Maiduguri ne nace barin kawo wa sarauniyata, yi hak’uri ba wani abu me tsada bane.”
         “Yanzu yaya karatu kakeyi amman seka rik’a kashe kud’inka a kaina? Ni gaskia kadena banso nafison kana kula da kanka a school.”
       “Ko kad’an Fannah baran iya zuwa nan ba tare da na kawo miki komi ba. I prmise you this duk sanda na fara earning salary’n kaina I will spend it on you, ina sonki sosai Fannah ta.”
             “Nima ina sonka yaya na. Nagode sosai, jazakalllahu bikhair Allah taimaka ya baka sa’a yaya.” nan ta mik’e.
  
     Mik’ewan yayi shima “ameen my Fannah inasan addu’o’in ki agareni, ba k’aramin taimaka min suke ba.”
Ai saisa kullum nake including d’inka cikin prayers d’ina. Baba na naka sannu dazuwa also, yace ka mim’a gaisuwan sa gun Abba da jiki”
Toh my Fannah, I'll tell him so se munyi waya ko?” kai ta giad’a a hankali. Wai! Ai na manta kun kusa fara exams ma, barinso jn hana Queen d’ina karatu ba”
“Haba mana yaya ko wayan minti ishirin baramuyi ba?”
Da murmushi a fuskarsa yace ai baki tab’a neman abu kirasa guna. Allah kaimu daren toh”
“Yawwa yaya bo-bye” tamasa murmushi. Murmushin ya mayar mata “bo-bye Queen.” Ahaka tashigo ciki.

Tun kafin ta yo d’aki ta soma bud’o ledar, abaya ce me kyan gaske ga stones kota ina. Wowww kukeji tana fad’i kamar Ya Ahmad yasan yadda nakeson abayah. Nan ta hau gwada wa kan kayarta bayan ta cire hijabin nata. Aiko daidanta tazo gwada yafa gyalen se kud’i ya fad’i daga ciki tana irgawa taga dubu biyar. Yanzu Ya Ahmad wannan d’inne zece ba yawa. Baba! Baba! Ta k’olla masa kira tana nufo d’akin nasa.

Ya akayi uwata ta kaina? Ya tambayrta a kiabingid’e tare da kashe radio’n dayakw ji. Wannan kaya fa daga ina?
Masha Allah Ya Ahmad ne yakawo min yanzu kaga harda dubu biyar kuma.
Kai Allah shi mashi albarka, shi kullum cikin wahala yake miki? Gashi ko kayan yamiki kyau kka fito kamar balarabiya.
“Kai! Baba dagaske?” Ta tambaya tana tsalle. “Sosai ma kuwa uwata.” ya amsata. Nan ta irga dubu biyu ta mik’a masa “gashi Baba ka rik’e wannan, Mama ma dubu biyu nida Afrah da Aiman kuma semu raba wannan.”
“A’a uwata rik’e abinki kinji? Ki saya abubuwan da bakida dashi” ya mik’a mata.
“Baba ni komai danake buk’ata inadashi ka karb’a kaji? Ko cafani sekayi dashi.”
“Toh nagode uwata, Allah miki albarka ya cigaba da kare min ke.” “Ameen Baba zan koma d’aki.” Nan ta fice, isarta d’aki bada jimawa ba k’annenta Afrah da Aiman suka dawo.

Atare suka shigo d’akin d’ayan tana nan kamar Fannah baratafi 13 years old ba whereas d’ayan kuma dududu intayi shekaru shine 3. “Ke wai Aiman kullum ne sekin tsaida mu akan hanya da sunan fitsari?” cewar 'yar babban (Afrah) kenan. “Anyin!” cewar Aiman yarinya ‘yar shekara uku se uban baki.

“Ni kike ma rashin kunya? Iyye?”
Fannah dake kwance kan katifa tana karatun History ta d’ago ta zauna “wai ke Afrah me damuwarki? Shikenan yarinya bara tayi fitsari ba?”

“Ya Fannah ni ban tsoma bakinki ba, nida Aiman nake magana.”
“Aww rashin kunya zakimin? Dama d’azu Ya Ahmad yazo ya bani kud’i nayi niyan baki kad’an daga ciki amman tunda rashin kunya zakimin na fas-”
Afrah ta katse ta, “a’a yi hak’uri Ya Fannah ta.” Da gudu ta haura kan katifar “yaushe Ya Ahmad d’in yadawo?”
“D’azu bakiga abayan daya kawo min ba!” Nan ta mik’a hannu taciro daga cikin wata bako take Afrah data kusan kamota tsayi ta amshi zata soma gwadawa Fannah ta k’wace “kefa bakida seti, akawo min kaya kiwani ce zaki gwada?”

“Su Ya Fannah manya masu samari.”
“Samari? Ai Ya Ahmad ba saurayi na bane miji na ne, kinga yana level 5 yanzu ina ss2 ina ss3 yana neman aiki ina gamawa se muyi aure by then yasamu aiki in shaa Allah”

“Ahh lallai fa soyayya ruwan zuma. I'm envious.” Cewar Afrah.
“Don't be, kema lokaci ne beyi ba Allah ze had’aki da mijin dayafi Ya Ahmad sona.” “Allah sa!” Afrah tafad’a da sauri “Ameen habibti” cewar Fannah.

****
“Fannah! Fannah! Zo da sauri da Allah” kirar Mami. “Na’am Mami gani zuwa.” Sunnah take da niyar yi kafin tayi nafilar Maghrib kasancewar lokaci ya kusa yi amman dan kirar Maminta ta fasa tajeta. “Gani Mami”
“Fannah yi hak’uri ki siyo min maggi ashago nan kusa wallahi bansan ya akayi ba har ya k’are ban sani ba yi hak’uri kinji mamana?”

“Yanzu Mami aike zakiyi shine sekin had’ani da Allah harda bani hak’uri. Ina kud’in?”
Nan Mami taciro hamsin ta mik’a mata. “Kinga ai kece babba Afrah yakamata in aika amman shegen yawonta tashiga nan mak’ota ganin jaririyar da Ameenatu ta haifa.”

“Ayya ba komai Mami barin yi sauri kafin su rufe shagon.”
“Toh Allah kare.” “Ameen” ta amsa sannan ta fice.

*ANAS*

“So Anas sauran ka 3 days kafire London kenan?” Cewar Shettima suna zaune a kan wata benchi a bak’in k’ofar gidansu. “Gonna miss me?” Anas yafad’a yana d’aga gira.
“Eh mana I will miss you, nide Anas wallahi ka canza tsoron zuwanka London d’innan nake nan da Bama ma kana shaye shayenka a b’oye bale ace kaje can inda ba idan kowa.”

“Toh yau kuma wa’azi zaka min? Kagannin nan yanzu haka akoi inda mukayi appointment da su Baana I will have my last drink a Bama yau kasan gobe zamu wuce Maiduguri, so kaga dole in sha in bugu tunda na k’arshe ne.”

“Amman kasan Abuu nagari ko? In ya ganka a buge fah?”
“Make up stories for me then, kamar yadda ka saba kace masa fad’a mukayi da wani. I'm going now.”
“Toh masallaci fah?” Cewar Shettima.
“Sena dawo zanyi sallar.” Daga nan ya fice inda suka saba had’uwa in zasuyi shaye shayensu ya je chan suka bugu like never, ko sanin ina suke in aka tambayesu ba sani zasuyi ba.

Daidai Anas ya tashi ze tafi gida kenan aka soma wani erin masifaffen ruwa ba yadda Baana basuyi dashi yajira ruwan yad’an tsaya kafinnan ma hankalinsa yad’an dawo jikinsa ba amman sam yak’i jinsu ana ruwan yasoma tafiya, yazo ma besan ina yake dosa ba dan yadda ya bugu.

****
*FANNAH*

“Oh No! Shagon Ya Wakil a rufe gashi Mami battada maggin da zata yi amfani dashi dole in k’ara gaba” haka tatayin gaba duk shagunan a rufe amman still bata hak’ura ba. Bada jimawa ba aka soma ruwa me k’arfin bala’i gashi daga can tana hango wata shago a bud’e ta koma gida ba maggin kuma battaso. Cikin ruwan ta cigaba da tafiya daidai ta shiga wata lungu taga wani na miji daga gani a buge yake, duda acikin duhu ne hakan be hanata tantance kyansa da blue eyes nasa daya d’ago yana kallonta ba. Take ta soma b’ari Allah sa ba gamo tayi ba. Mutum da blue eyes.

Addu’o’in kariya tasoma yi jikinta se rawa yake gu d’aya ta tsaya jiran yazo ya wuce tayi gaba itama. Daidai yazo kusa da ita seya tsaya hannu ya d’aga yakai kan fuskarta tuni Fannah ta soma kuka tunda take ba d’a na mijin daya tab’a tab’ata inba Babanta ba. Ga k’arfin ruwan saman koda tayi ihu bame jinta shagon data gani a bud’en ma har sun rufe.


*©miemiebee*
beeenovels.mywapblog.com
[16:09, 12/19/2016] Swtbaby: •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫

❣🎀❣🎀❣

*_written by miemiebee👄_*


0⃣4⃣




Cikin kuka tace, “dan girman Allah bawan Allah kayi hak’uri I beg of you please.” Jikinta se rawa yake tana hawaye. “Bawan Allah dan Allah kayi hak’uri I'm just 15 ba abinda zan iya baka have mercy on me please dan Allah.” Ko k’adan be saurareta ba hijabin jikinta yasoma k’ok’arin cirewa. “Wayyo Allah Mami na! Baba! dan Allah kuzo ku taimakeni! ihu take sosai.”

     Hannu yasa ya rufe bakinta. “Duk mata haka kuke, mesa zanji tausayinki? Data gudu tabarmu ta tausaya mana neh? Why will I have mercy on you? I hope you tell her abinda zan miki yanzu saboda itama ta d’and’ana little daga cikin bak’in cikin data sanyamu time da ta tafi ta barmu” Yana d’aga hannu daga bakin nata ya yaga hijabin nata into two. Ihu ta sake sakarwa “bawan Allah dan Allah kayi hak’uri karka lalatani dan girman Allah, kaji tausayi na I'm just 15 years dan Allah ka rufa min asiri karka b’ata min future”

     “Data tafi ita taji tausayin mu ne?”

    A rikice bakin ta na rawa tace, “ww..wa ce? Ni bansan wacce kake fad’a ba bawan Allah ban tab’a ganinka ba seyau kayi hak’uri dan Allah, karka lalata ni.”

Please Login or Register in order to submit comment