Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wacce baratayi mgana ba kuma setace “babu zakayi latti katafi kaji?”
    “Se kin d’ago idanun ki kin kalleni ki kuma nanata min abinda kika fara fad’i dazu zan tafi.” Sun d’au minti uku suna tsaye ahaka ganin baida niyyan tafiya tasa ta d’ago idanunta ta azasu kansa. Hannu ta d’aga ta soma gyara masa gashin kansan duk anan yana binta da kallo seda ta gama sannan ta maido da kallonta garesa. “Habeebi I lose control whenever I’m kissing you.”
     “Mesa?” ya tambayeta
    “Because...” ta aza yatsanta kan lips nasa “they are sweeter than honey.” Sam seji yake kamar a mafarki anya kuwa wannan ce Fannar daya sani me uban kunya? “And yours too Baby.” Murmushi tamasa “off you go nima I have a suprise for you se in ka dawo.”
    I love you sukayi exchanging sannan ya fice farin ciki fal kwance a fuskarsa.

        By 12:30PM Fannah tagama had’a girkinta wanka tashiga da wuri-wuri tayi ta fito ta shirya cikin wani A shaped doguwar riga na lace, light makeup tayi applying ta kama gashinta gu d’aya sannan ta sanya hijabinta violet akai. K’arfe d’aya nayi ta idar da sallah tasoma zaman jirar Anas yau tunda ya tafi office be kirata ba ko aiki ne ya masa yawa oho.
     1:40PM Anas ya dawo gida d’aukanta, kasa ignoring kyan da tayi yayi daya sata a ido seda ya sata gaba ya riga d’aukanta pictures, sam yak’i sanar da ita ina ze kaita sede daga baya taga sun fara dosan Enterprise nasa.
      “Habeebi meh zamuyi a Enterprise naka kuma?”
    “Kede tsaya ki gani mana Flower” kafin su kai da Enterprise d’in ya tsaya tare da ciro wani d’an bak’in k’yalle. “Turn around” ya buk’ace ta. “Meh zaka min da wannan kuma?”
    “Just trust me Flower.” Ba gardama ta juya ya d’aure mata ido sakwa-sakwa yadda bare dameta ba. Bayan sun k’arisa ciki yayi parking sannan yafito da ita a hankali daidai gaban Enterprise d’in ya tsaya da ita. “Are you ready?” Ya tambayeta. Kai kawai ta gyad’a. “Okay” anan ya kunce k’yallen. Kallonsa take a yayinda ya mata nuni da idanunsa akan ta kalli sama hakan tayi. Mamaki ne sosai ya cikata ganin sunan Enterprise d’in Anas ya canza daga FLAMES Enterprises zuwa FAHNAS Enterprises.

       “Woowww!” Ne kad’ai abinda bakinta yake iya furtawa har ayanzu takasa believing. “Habeebi this is amazing yayi kyau sosai, OMG! FAHNAS... me ma’anarsa?”
    “FAH-FANNAH NAS-ANAS.”
     “Awwwn! This is so romantic yayi kyau Allah k’ara bud’i ya karemin kai Baby I love you.” Hannunsa ya zagaye a kunkuminta daga gefe “I love you too Flower.” peck ta manna masa a kumatu.
     “Yaayi kyau sosai and I love it, much appreciated” wayarta ta ciro ta d’au gaban Enterprise d’in hoto. “So zamu koma gida kokuma zaka zauna anan se 4 kadawo gida?”
     “Kinason in biyoki mukoma gida yanzu?”
    “Ofcourse yes Habeebi.”
    “Toh muje Mrs. Fauzi” dad’i sosai taji bayan isowarsu gida duk suka rage kayakin jikinsu. “Ina suprise nawa Flower?”
“Yana nan a dining table muje muchi abinci.” Hannunsa ta riqo bayan sun k’arisa dining ta bud’e d’aya daga cikin manyan flasks d’in tuk’ek’k’en tuwon semovita ne had’ad’e ciki nan tayi serving nasu duka shide Anas ya zuba mata ido tana bud’e flask na miyan ya toshe hanci tare da miqa wuya dan tabbatar da abinda zuciyarsa ke saqa masa.

“Flower what is this?”
“Meh kuwa ? Abinci mana Babe.”
“Da gangan kikayi hakan koh? Eww! Close it please kinfa san banason wannan miyan kukan.” Nan ya miqe da wuri ta sake zaunar dashi. “Wai me haka Habeebi? Se wani toshe hanci kake sekace something is smelling.”
“This is smelling Flower” ya nuna flask d’in “dan Allah ki rufe.” D’ago flask d’in tayi ta matso dashi gabansa tare da sauk’e hannunsa daya toshe hancin sa dashi daga fuskar nasa. “Flower stop it please” sewani yamutsa fuska yake. “Wannan ne suprise d’in? Na gani thanks sosai zanje in dafa noodules yau kowa yayi dining shi kad’asa kuma kisani nima se na rama ewww!” Ya watsa wa miyan kukan kallo. Kafin ya miqe ta dakatar dashi ta hanyan zama kan cinyarsa.

“Flower yau neman tsokana na kike ko? Tashi please warin ya isheni.”
“Haba Babyn Fannah, my Habeebi, my lion, my life and happiness” ta zagaye hannayenta a wuyansa cikin wani erin salon dake sosa masa zuciya. “Wani wari kuma miyan yakeyi? Trust me Allah ka tab’a kaji da akwai dad’i.”
“Flower baya min dad’i please ki rufe.”
“Yi hak’uri Baby ka tab’a kaji?” Kai ya girgiza mata “I will kiss you over and over and over yau kaji?” Nanma kai ya kad’a. Haka itama tak’i tashi masa daga cinya miyan ta zuba kan d’ayan plate d’in ta wanke hannunta sannan ta gutsira kad’an daga tuwon ta had’a da miya takawo masa baki. Hannu yasa da wuri ya toshe hancinsa “Flower please kibari” d’ayan hannunsa yasa ya shure hannunta baya aiko ta maidoshi gabansa.

“Open up mana Baby.” Kai kawai ya kad’a mata, dabara ce ta fad’o mata. “Okay toh naji baraka chiba zan dafa maka noodules” nan ta miyar da plate d’in ta ajiye kan dining. “Toh ta-” bata bari ya k’are maganan ba ta cusa masa tuwon a baki nan danan ya fara yunk’urin cirowa “uhm-uhm Habeebi” ta kad’a masa kai tare da toshe masa hanci. “Had’e kaji Babe in bahaka ba barin sake maka hancin ba, sekace baturen gaske kace bakacin miyan kuka! Oya had’iye” da k’arfin da Allah ya bata ta matse hancin nasa ko kasa koda k’watan kansa ya yi. Idanunsa sun kad’a sunyi ja dan rashin numfashi sam yak’i had’iwa ganin ba mahalicci se Allah ya rufe ido ya had’iye badan yanaso ba.

Se anan ta sake mai hancin tare da miqa masa ruwa tas ya kwankwad’e “tashi min Flower” ya buk’ace ta yana k’ok’arin k’irk’iro amai.
“Ina zakaje?” Ta tambayesa.
“I need to throw up kitashi please.”
“Ai ina nan Anas yau seka koyi cin miyan kukan nan ina zanzo in kaika? Bakacin cous-cous, d’an wake, kuka, kub’ewa komai ma bakaci se abincin turawa? Gomma ka kwantar da hankalinka dan yau sekaci tuwon nan.”
“Naji zanci tashi toh.”
“Saboda kasamu chance na guduwa ba? Ba inda zani” nan ta d’au plate d’in ta sake had’a tuwon da miyar “oya open up.” Se toshe hanci yake har a yanzu yak’i bud’e bakin “Flower wai d’anki ne ni? Kibari in kika haihu sekiyi ma d’anki wannan forcing d’in ni baran ci ba.”
“Naji amman kafin in samu d’an da zan masa zan fara akan Daddynsa oya open up.”
“Naqi.”
“Aw in sake toshe maka hancin kenan koh?”
“Flower manaaa.” ya maraice fuska.
“Yi hak’uri ka bud’e Baby na...” seda ta kusan kuka sannan Anas ya yarda ya bud’e bakinsa ta basa bayan ta basa kusan sau biyar sekuma yaji kukan ya masa dad’i compared to wanda ake musu a boarding house lokacin wanda sanadin rashin dad’insa yabar cin kuka kwata kwata.


*© MIEMIEBEE*

beeenovels.blogspot.co.ke
[12:58, 12/18/2016] ‪+234 903 612 6826‬: •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫

❣🎀❣🎀❣

*_written by miemiebee👄_*

In dedication to *Aunty Sis💕*
7⃣5⃣



    Sede still bayason miyan kukan yafison ire-iren abincin daya saba ci a London su burger, pizza, bufallo wing, glorified rice, louisiana da sauransu. Datazo sake basa hannunta ya rik’e “na k’oshi a banza bakin mutum ya fara warin kukan nan”
       “Ai sekayi brushing bale ma bawani warin nan, open up”
     “Na k’oshi”
    “Dameh?” Ta tambayesa.
    “Wannan” ya nuna mata da yatsa.
   “Haba Habeebi guda biyar fa kacal kachi yi hak’uri ka k’ara nasan kana jin yunwa yi hak’uri Baby” haka tariga lalashinsa kamar d’an yaro tana basa abincin da wayo cikin k’issa kafin su hankara har yagama plate nasa bakinsa ta wanke masa da kyau se anan ta tashi mai daga chinya dan chin nata itama. Tana tashi shima ya mik’e zasa toilet ya k’wak’ulo amai.

     *“Mine* ina zakaje? Bade toilet ba! Please karka je ka harar da abincin nan.”
    “Ohh! Flower ni barin iya zama da wannan kukan acikina ba.”
    “Nasani hak’uri zakayi Habeebi na zauna a parlour kajirani I want us to play a game today.”
    “Wani game?”
     “Just wait for me.”
    “Toh naji excuse me” nan ya juya.
   “Baby promise baraka je ka harar ba.” Shiru yayi yana nazari. “Baby please.”
   “Okay okay I promise shikenan?” Nan ta gyad’a kai bayi ya nufa yayi brushing shi wai a dole miyan kuka nasa bad breath (warin baki) dawowansa ya zauna kan d’aya daga cikin sofas na parlour’n tare da kunna cinema. Kasa kallon news d’inma yayi se kallon Fannah yake yadda take chin tuwon sekace wani abun arziki me dad’i. Da idanunsu ya had’u ya wani yamutsa fuska “zaka k’ara neh?”
     Da sauri ya kad’a kai “a’a banaso thank you.” Murmushi ta saki “karka damu gobe dashi zamuyi breakfast zanyi mana d’umamensa.”
     Blue eyes nasa ya k’wararo “zaki d’uma meneh?”
      “D’uma wannan ko bakasan meh d’umameh ba? Zan sake reheating tuwon mana muyi breakfast dashi.”
    “Keda wa?” Ya sake tambaya
    “Nida Habeebi na.” Kai ya gyad’a “lallai kam zaki nemi new Habeebi dan ni barinci d’umamen wannan abin ba.”
    “LOL” tad’an murmusa “ai kai ne kad’ai Habeebin nawa, trust me d’umamen ma yafi dad’i yafi taste kasan da me yau zamuyi dinner?”
     “A’a bansani ba and banason sani ki rik’e please ni kawai zansha coffee in kwanta barin chi komai ba.”
    “Kai Habeebi d’an wake de zan mana inyi slicing egg and cabbage akai its way yummy. Gode kuma in Allah ta kaimu miyan kub’ewa zanyi” Yamutsa fuska yayi “a’a Flower please kiyi abinki ke kad’ai naji yunwa ko sausages zan soya inchi.”
    “Oho nide d’an wake zamuci da Baby na.” Be sake ce mata komai ba har tagama chi ta tattara dining d’in sannan ta dawo ta samesa da paper dakuma biro biyu a hannunta, gefensa ta zauna.

       “X and O zamuyi.” Yana jin haka ya kad’a mata kai dan ko sam be iya game d’inba bayason kuma yayi losing a gabanta ta raina sa kokuma ya fad’a mata be iya ba ta masa dariya. “Baby kayi shiru.”
     “Barinyi ba ki kawo wani game daban wannan ba dad’i.”
     “Toh Habeebi ni shi kad’ai nasani Allah da dad’i lets try kaga.”
    “Ohh!” dabara ta fad’o masa “ni se yanzu ma na tuna inada aikin da yakamata inyi attending to a laptop” ya k’arisa maganan yana k’ok’arin miqewa hannunsa ta riqe ta dakatar dashi “Habeebi I can tell you are lying kode kana tsoron kar inyi winning naka ne” tamasa gwalo.

     “Ke kiyi winning d’ina? Impossible lets play it muga.” Nan da nan ta zazzana musu sannan ta mik’a masa pen d’aya zuciyan Mr. Fauzi fa se bugu yake dan sam be iya game d’in ba at all. “So deal d’in shine if I win zan d’aneka anan” ta nuna goshinsa. Shiru yayi yana nazarin yau d’ani nawa zesha gun Flower.
      “Baby kayi shiru ko kanajin tsoro ne? Karka damu I’ll take it easy on you” tana masa wani shu’umin murmushi. Ina irin shikuma bari ya nuna mata shina miji ne bayajin tsoron nan. “Ba tausayi in na nad’e ki se goshin naki yayi ja.”
      “Haka kace?”
    “Yes Flower haka nace.”
    “Fine lets start.” Shi yafara placing X bayan yayi itama tasa O kafin ya hankara Fannah ta masa baki biyu kafin yace meh tariga tayi crossing ta chi sa. Tsalle ta daka “yeyy! I won nachi!”
     “Taya ya kikaci? Ai wannan cuwa-cuwa ne niban yarda ba.”
     “Kamar ya Baby? Gashi nan nacika kuma kana gani bring your forehead.”
     “Gaskia ban yarda ba asake wani kinyi magud’i anan.”
     “No vex asake wanin.” Hankali sosai ya miyar yana coffan yadda tayi d’azu shima dan mata baki biyu sede nan ma kafin ya hankara tasake chi nanma tata daka tsalle “yes!! yanzu ka yarda na cika?”
        “Ni fa gaskiya ban yarda ba kina min cuwa-cuwa ne kawai.”
     “Koma me ka kawo goshinka saboda deal ne.” Fuskarsa ya ajiye mata daidai tsakiyan goshin sa tasa hannu ta danna masa d’ani me uban zafi take wajen yayi pink. K’ara ya saki “argghhh!”
   
       “Aww” tayi pouting bakinta “da zafi ne Baby?”
    “Nima bansani ba” ya watsa mata kallo. Zuciya yayi “lets play again I must win this time.” Nanma da suka buga ita ta sake chi haka ba yadda ya iya ta ya sake a jiye mata goshinsa ta d’anesa fiye dana d’azu nanma k’ara ya saki sosai amman kamar maye yak’i hak’ura shi a dole seyaci ta aiko sun buga har sau 7 duk Fannah kechi gashi ko saurara masa batayi tunda yace no pity haka take d’aninsa da zafi-zafi goshin Anas daga fari yakoma pink yanzu jazir ya koma duk yabi ya galabaita.
      “Mschww! Ni na fasa game d’in.” a fusace ya mik’e yashiga d’akinsa. Murmushi kad’an tasaki sekuma ya bata tausayi ga dukkan alamu be iya game d’in bane daman shegen ajeboncin sannan dama ina ze iya? K’aramar hand towel da warm water tasa a bowl tabi bayansa mik’e kan gado ta tarar dashi yana ganinta ya juya mata baya a nitse ta k’ariso ta ajiye bowl d’in akan side drawer sannan ta zaro robe daga ciki ta ajiye a gefe.
     “My Baby” ta kira sunansa. Ko juyawa ya kalleta ma beyi ba.
     “Habeebi yi hak’uri ka juyo kaji inga goshin naka.” Nanma shiru ya mata.
    “Yi hak’uri mana Baby.”
    “Me zaku gani? So kike ki gani kimin dariya komeh?”
    “Ko kad’an Habeebi taya zan maka dariya? Gani zanyi kaji yi hak’uri kajuyo.” Ganin baida niyan juyawa tasa hannu ta juyo dashi a hankali tare da aza kansa kan cinyoyinta ita kanta seda ta tsorata ganin abinda ta mai da goshi, wani erin fata ne dashi sekace na mace da baison wahala haka? “Ya Salam Baby I’m sorry bansan haka goshin naka yayi ba.” hannunta ta miqa ta tab’a goshin nasa k’ara ya saki sosai.
    “I’m sorry kaji? Kai kace fa no sympathy ba tausayi shiyasa.”
     “Toh kuma seki yarda? Aikinsan in nine barin miki haka ba.” yayi maganar kamar wanda zeyi kuka.
    “Baby I’m sorry da ka fad’a min baka iya ba ai.”
    “Flower its embarrassing ace ban iya playing simple game kaman wannan O and X d’inba.”
     
       “Baby its X and O ba O and X ba.”
   “Naji whatever” kansa ya d’ago daga cinyar nata ze juya mata baya kenan ta rik’o hannunsa. ”Don’t be mad kaji Habeebi? Game ne kawai ba komai ba I’m sorry kuma bar kan naka kan cinya na zan d’an matsa maka wajen  ne”
     “Kin manta kwanaki da cintoyin sukayi tsami ne?”
     “Ina sane ai ba dad’ewa zakayi akai ba tsaya” Batare da yace da ita komai ba ta matse towel d’in ta aza kan goshinsa da wuri yasa hannu ze d’aga dan azaba ta dakatar dashi “sorry kaji? Nasan da zafi hak’uri zakayi” haka tata matse masa a hankali yana sakin k’ananun k’ara time to time bayan data tabbata ta matse masa ta bud’e robe d’in ta lak’uta tasa a goshin nasa tana fara murzawa yayi saurin d’aga hannunta.

     “Flower ya isa haka barshi.”
    “Habeebi ka tsaya ko kad’an ne in mirza in bahaka ba ze iya kumbura fah”
    “Toh ai laifin ki ne, ke kika riga d’ani na sekace ba mijin kiba”
     “Baby nace I’m sorry be wuce ba? yanzu tsaya mu shafa maka semu kwanta mu huta... Yawwa Baby naa” a hankali take shafa masa har tasamu ta gama taje ta zubar da ruwan sannan ta dawo suka d’aura alwala tare da yin Sallah. Gado suka haye suka kwanta tana a gefensa suna fuskantan juna. “I love you Anas.” Shiru ya mata shi a dole har yanzu yanajin haushi. “Baby baraka cemin I love you too ba?” Kai ya gyad’a.
     “Har yanzu wai baka hak’ura ba?” Nan ma kai ya gyad’a. Matsowa tayi gab dashi kafin ya gane me takeson yi kawai ta hau kissing nasa ganin basuda niyyan tsayawa nima naja legediz benz d’ina na bar musu d’akin gudun kar su cinye kansu a idanu na (LOL)

       Koda na leqosu bayan minti uku still basu bari ba haka na sake komawa nabasu minti goma anan ne dana leqo naga Fannah kwance kan k’irjin Anas murmushi fal kwance kan fiskokinsu yana shafa doguwar sumanta a hankali cike da soyayya.
     “So can I hear it now?” Ta tambayesa.
     “Yes Flower I love you too.” Dad’i sosai taji ta sake matse jikinta a nasa ahaka har sukayi bacci.

*****
       _7:30PM_
     Tun idar da Sallan Maghrib da sukayi Fannah ta shjge kitchen ta fara aikin d’anwake acikin d’an k’ank’anin lokaci tagama ta had’a musu dining table tayi serving kowa a saucer, Anas na ganin haka ya saci jiki ya koma d’aki ya miqe kan gado shi a dole yana bacci bare chi d’anwake ba. Har d’akin ko ta biyosa “Habeebi tashi muje dinner is ready.” tayi maganan lokacin da take tsaye akansa, shiru yayi tare da sake gamme idanunsa shi wai adole yana bacci. “Baby tashi mana” ta gwada jijjik’ashi “meneh?” Ya tambaya sleepishly.
       “Baby wai bacci kake? Yaushe ne muka tashi daga bacci har kake wani? Tashi muje kaci abinci yaso seka dawo ka cigaba kaji?”
    “Banajin yunwa Flower.”
   “Nasani hak’uri zakayi karfa ya huce yayi sanyi tashi kaji My Lion.” Badan yanaso ba ya mik’e yabita bayan sun zauna ta ja mai saucer’n sa gabansa “bismillah lets eat” nan da nan ta soma kai nata ciki shide kallon saucer’n nasa kawai yake seda ta kusan rabin nata taga Anas beko tab’a nasa ba.
     “Habeebi inzo in baka ne?”
   “A’a chi naki zanchi da kaina.”
   “Toh chi mana ai yamayi sanyi” fork ya d’aga yasa ciki tare da danno kan d’aya seya kai baki seya sake maidoshi baya da abin ya isheta seda tabari yakai baki sannan ta tura hannunsa yasa d’an waken ciki yana fara k’ok’arin fito dashi a girgiza masa kai “karkayi please gwada chi mana kaji kaikam.” Tsotse zak’in jikin yayi kap ya jawo plate ya tufar da d’an waken akai. Kallonsa kawai ta tsaya yi cike da mamaki, wasu biyun ya sake kaiwa baki yana gama tsotse zak’in se ya fito dasu ya ajiye.

      “Wai Habeebi me haka? Haka ake cin d’anwake? Ai wannan almubazaranci ne.”
    “Kefa kikace senaci yanzu kuma da nake ci kina min surutu.” Nan ya cigaba da abinda yakeyi, ganin yakusan kai rabin saucer’n tace, “Baby kabari mana” sake matsowa kusa dashi tayi ta danna kan d’aya ta kai masa baki gashi karb’a ba musu ya karb’a “kuma karka tsotse Baby ka tauna ka had’iye.”
     “I can’t.” Ya sanar da ita.
    “Yes you can” ta tabbatar masa. Bayan ya gama tsotse zak’in yafara k’ok’arin cirowa aiko ta rufe mai baki “Baby ka tauna ka had’iye mana ko so kake yunwa ya soma damunka? Had’iye.” Kai kawai yake girgiza mata aiko daram ta zauna kan cinyarsa “yau seka had’iye in ba haka ba...” ta matso kusa da kunnensa ta rad’a masa abu ai take ya gyad’a kai. “Goood thats my Man” anan ta sake mai baki. Goran ruwa ya jawo kamar yadda ake had’iyar magani haka ya had’iye d’an waken haka yabi sauran yariga had’iyesu sekace meshan magani. Ita de Fannah nata ido ne.

    Bayan da suka gama dinner ta d’anyi assisting nasa wani aikin da yakeyi se 10:30PM suka kwanta. Washegari Anas yace sam bazasa office da jan goshi bah ba yadda Fanah batayi dashi ba yafa ce shi ba office da zeje haka suka sha baccinsu se to 11 suka tashi sukayi wanka tayi musu d’umamen as promised sam Anas yak’i chi ba yadda batayi dashi baya da yachi yace bare chi ba sede in fresh new one zata dafa bayan ta karya ta masa nasa breakfast daban kasancewar wheather’n garin yayi cloudy ba rana yau yasa suka fita baya wajen garden suna shaqatawa suna hiran masoya gwanin sha’awa abinsu. Honk da ake tayi yasa Anas ya miqe ya duba ko suwaye ne ganin motar Shettima yasa ya danna wani button gate d’in ya bud’u musu duk suka d’uru sukayi ciki.

Amal da ba’asan an girma ba chak ta d’ale cinyan Anas tasa Ummie kunya. “Haba Amal ya haka kuma? Sauqo kinji?” Tana maganan tana kallon Fannah.
“Ayyah Ummie barta ba komai she missd him thats why.”
“Laaaaa Ya Anas me haka a goshin ka?” Cewar Amal nan hankalin kowa ya koma kan goshin Anas a tare Shettima da Ummie suka ce “dagaske fa amma meya samu wajen haka yayi pink?” Hannu yasa ya rufe goshin tare da bin dukkaninsu da kallo yana nazarin wani k’arya ze had’a musu idanunsa na had’uwa dana Fannah ta kawar dakai se k’ok’arin maze dariyan dake san kub’uto mata take.
“Kayi shiru Anas” cewar Ummie “meya samesa Fannah?” Ta yi redirecting kallonta zuwa Fannah. Nan ta soma raba ido dan batasan me zata ce dasu ba.
“Ermm... Erm-” katse ta Anas yayi.
“D’azu ne zuma suka harbeni a garden ina d’an gyaran wani flower.”
“Eh zuma suka harb’esa d’azu” ta mara masa baya.
“Ayya sannu” duk su uku suka ce alokaci d’aya Amal na tab’awa yaja hannunta “da zafi stop it.”
“Sorry.” Hira suka sha sosai da Fannah tama Ummie tayin d’umamen kuwa tace akawo mata haka suka zauna ita da Shettima suka narki tuwon banda Amal dake nan kamar Anas itama wai batachin miyan kuka se bayan Azahar suka tafi.

****
“Kai aman gaskia Habeebi ka iya had’a k’arya sosai fah” ta kwashe da dariya. Banza da ita yayi.
“Habeebi is a liar.” Wani kallo ya watsa mata “ki ka sake kirana liar sena miki abinda baki tsammani Flower.”
“Do your worse” tamasa gwalo “My Baby is a liar” da gudu ta wuce kitchen tasa lock a duka k’ofofin se dariya take masa. “Ai ba kwana zakiyi ciki ba, zaki fito ki sameni.” Ya fad’a mata.


Please Login or Register in order to submit comment