Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

away and leave her, aduk lokacin data tuna da wannan seta yayyafa wa zuciyarta ruwan sanyi dan huchar da zazzafan son Mr. Fauzi. Haka har tagama shirinta tana tuna jiya yadda Anas ya riga mata hidima ko da daddare da take kuka ya hana kansa bacci ya zauna da ita yana pompering nata, haka kawai taji tana murmusawa.

    Shima Anas zaune yake cikin one of hotels daya saba chin abinci, ga abincin agabansa amman yakasa ci se murmusawa yake musamman ya tuna rananda take tsaye da towel a gabansa dakuma lokacinda cinyoyinta sukayi tsami yake shafa mata muscle pain reliever. Da k’yar ya iya ya kai spoons biyar yaji yama k’oshi tunanin Fannah kad’ai ya ciyar dashi. Be jira aka tashi ba yabar office ji yayai kawai Fannah yakeson sawa a idanunsa, it hasn’t been long amman seji yake like shekara da shekaru ne.
  
    _K’arfe 3:00PM_
   Tsaye Anas yake bakin hotel room nasu ya kasa shiga dan girman kai. “What if tace mena dawo yai since before lokacin tashi yayi, me zance mata? That I miss her I want to see her? No! No way ai seta raina ni ta d’au ko sonta nake.” Ya juya ze koma kuma yaji bare iya ba Fannah yakeson gani and no one else. Seya d’aga hannu zeyi knocking seya sake maida hannun nasa baya.

     Fannah kuwa tayi waya da Afrah ta buga game, ta kalli pictures na bikinsu, tayi kallo, tagaji zaman shirun ya isheta. Sanin ba kowa a floor dasuke daga ita se Anas, Anas kuma baya nan ba wanda ze hauro ta d’au wayarta kad’ai. Atamfa ne d’inkin fitted riga da skirt ya mugun mata kyau a jikinta, kayan ya zauna tip tip. D’aurin ta ta daidaita sannan ta bud’e k’ofar, baki ta sake ganin Anas tsaye jikin k’ofar.
    Mutuwan tsaye sukayi duk a wajen suna kallon juna sun kusan minti biyu suna abu d’aya sannan ta kawar da kanta zata rufe k’ofar dan komawa ta d’auko mayafinta kenan Anas ya rik’o hannunta. Be d’aga idanunsa daga kan k’irjinta ba har ayanzu se kallonta yake.

    “Uhm Anas kasakeni in d’au mayafi na please.”
     “Why?” Ya tambayeta se anan ya dawo da kallonsa kan kyakkyawar fuskarta data sha d’an light makeup.
     “Anas hakan ba kyau-” katseta yayi.
   “No I like it this way, kinfi kyau haka kar ki rufe jikin ki kinji?”
    “But Anas-” katse ta ya kuma “Fannah I’m your husband nace nafison ganinki haka” se yanzu ya tuna da kalamun ta na ranan cewa batason tsinuwan mala’ikun rahma. “Ko ki zauna haka kokuma inyi fushi dake mala’ikun rahma suyita tsine miki.”
    “A’a dan Allah don’t talk like that kaji karkayi fushi.”
    “Zaki zauna hakan?” Kai ta gyad’a a hankali. “Good” ya saki brightest smile nasa.
     “Da ina zakije ahakan?”
   “Babu kawai nagaji da zaman cikin ne nace barin d’an lek’o waje.” Ta basa amsa tana k’oka’rin raba hannunta da nasa. “Shine zaki fito ahaka ba hijabi ba mayafi?” Ya fad’a a little bit pissed off, daga yadda yake magana za’a san kishi ya motsa.

    “Toh Anas naga ba kowa a floor d’inmun, mu kad’ai ne.”
  “I know what of room services? Insuka hauro alokacin da kike k’ok’arin fitowa ahaka fah? Se suganki?”
    “Yanzu fa kace nafi kyau a haka kar insa mayafi.” Hannu yasa ya hargitsa gashinsa cike da haushi. “For goodness sake Fannah I’m your husband, taya zaki had’ani da room service? Nine kad’ai am aloud to stare at your body and not them.”
   “I’m sorry” tace dashi tana kallon k’asa.
   “No you are not Fannah, daga yau karki sake fitowa koda bud’e k’ofa ne ba hijabi ko mayafi do you get me? Banason mayafin ma hijabi constant kinji?”
   “Haba mana Anas ai dan bud’e k’ofa kam mayafi ma yayi.”
   “Ni bemin ba banaso, Fannah I’m serious.”
   “Okay naji barin k’ara ba.”
   “Better” yace yana hararta. “Matsa min in wuce.”
    “Ka wuce ina? Anas lokacin tashi daga office fa beyi ba, meka dawo yi?”
    “Me ruwanki? Ko kin d’au wai dawowa nayi saboda nayi missing naki? Hell No nadawo d’aukan wasu files ne, mema zan kalla a fuskarki ko jikin naki, excuse me?”
    “Niba abinda nake nufi ba kenan” gefe ta matsa masa ya shiga tabi bayansa. Briefcase dayake adana files nasa ya ciro shi a dole yadawo ne dan d’auko abu tana tsaye akansa se dube-dube yake yakasa koda d’aukan d’aya ciki. Ganin har yaci minti biyar be samu ba Fannah tace, “Anas anya kuwa files d’in kazo d’auka ba wani abu daban ba?” Da biyu tamasa tambayan dan kuwa hankalinta ya bata ba file yazo d’auka ba wayasani ma ko missing nata yake dagaske tunda har ya bud’e baki yafad’a d’azu indirectly.
 
    “Mind your business mana meh ruwanki da abinda nakeyi kin wani zo kin tsaya min akai sekace soldier (soja.)”
   “Allah baka hak’uri niba abinda nake nufi ba kenan, I was thinking ko kanaso in tayaka nema ne.”
   “Neman meh?”
  “File da kake neman, koba file kace kana nema ba?” Shi se yanzu ma ya tuna eh file yazo nema.
    “Toh banaso, zan nemi abu na dakaina.”
    “Yi hak’uri in taya ka” tace dawani mocking smile tattare da fuskarta.
   “Fannah yaushe na soma wasa dake? Mind your business.” Juya baya tayi tasoma tafiya zata kan couch ta zauna. “Mutum bare fito fili ya fad’a meya kawo sa ba se shegen zurfin ciki” tace chan k’asa k’asa almost kamar da kanta take maganar.
    Bejita gabad’ai ba amman yaji some part. “Ke! Me kikace?” Take ta juyo dan bata tsamman yajita ba.

     “Babu kawai cewa nayi Allah sa kasamu file d’in.” Harara ya galla mata tare da cigaba da nan file dayayi qarya yana nema. Chan ya d’ago kai yaga se lastse wayarta take, tsayuwa yayi yana kallonta ko kyafta ido baiyi data d’ago kai seya juya daga k’arshe ya ciro wani file yayi hanyan fita ai dagangan ya sakar da k’ara “awwchh! My ankle.” ya tsuguna yana rik’e k’afar. Da sauri ta nufa wajen “Anas meya faru?” Ta tambaya tana dubansa.
   “My ankle nakega nayi spraining. Awcchh!”
    “Ya Salam! But how?” Ta tambaya.
   “Nima bansani ba, argh!!” Hannunta ta zagaye ta bayansa tayi assisting nasa ta kwantar dashi kan gado. Se faman “awch!” na k’arya yake, sam yaji bayason rabuwa da ita koda na second ne shiyasa yayi coming up da wannan plan na spraining ankle nasa.

     Takalmasa ta cire masa da socks d’in, da ta tab’a k’afan hagun nasa seya sa ihu. ”Sorry, d’an tsaya in gani.”
    “A’a barshi.”
    “Anas kasan fa bareyi abar k’afar haka ba, nida cinya na sukayi tsami kwanaki ba haka kasani a gaba ka riga shafa min man zafi ba? Ka tsaya inga.”
    K’afan nasa ta aza kan cinyarta tana d’an mammatsa wajen ankle nasan. Sekuma abin yasoma masa cakulkuli, dariya yakeson yi amman ya matse se faking “awch!” Yake tayi.
   “Amma Anas banga alaman koda b’ullowan muscle bafa, kuma kace kayi spraining.”
    “Aww maqaryaci kikeson cemin komeh?”
    “A’a kawai de da abun ban mamaki ne.”
   “Sakemin k’afa ba sekin zagen ba.” Nan ya d’aga k’afarsa daga kan cinyar tatan.
   “Anas ba abinda nake nufi ba kenan I’m sorry.”
   “Banaso, tashi kibani waje.” K’afar nasan ta mayar kan cinyarta. “I’m sorry kaji?”
  “Naji” yace ba tare da ya kalleta ba. “In shafa maka magani awajen?”
    “No you don’t have to.”
   “Anas in ba’a shafa ba baraka iya taka k’afan bafah.”
    “Don’t worry just come lets sleep.”
   “Sede inkai ni banjima da tashi daga bacci ba.” Nan ta mik’e ta rage masa kayan jikinsa ta juya kenan ya rik’o hannunta “lets sleep kinji?” Be jira amsarta ba ya jata ta fad’a jikinsa.

     “Anas me haka?” Ta fad’a a lokacinda take k’ok’arin tashi.
   “Lets sleep.” ya sake matseta jikinsa.
   “Ahaka? Ai namaka nauyi barin kwanta a gefe kaji?”
  “No I want it this way.” Bata sake cewa komai ba sede sam ta kasa samun sukuni, wani erin baqon yanayi ta tsinci kanta ciki.

_20 minutes later..._
   “Anas” ta gwada kiran sunansa jin yayi shiru, ta d’aga hannunsa daya zagaya akan bayanta a hankali sannan ta taso daga jikinsa ta yadda bata tadashi daga baccin nasa ba.

*© miemiebee*
[12:56, 12/18/2016] ‪+234 903 612 6826‬: •° ★°•❣🎀❣🎀  •°•★•°•                         °•★•°                          °•       •°
                                       °•°
*TANA TARE DANI...*👫

       ❣🎀❣🎀❣

              *_written by miemiebee👄_*

    
                 6⃣2⃣
  



*YEYYY! ALHAMDULILLAH SISTERS FOR YOUR WARM PRAYERS, JIKIN MAMA DA SAUKI, ANYI OPERATION AND IT WAS A SUCCESS*

Suit da shirt nasa data cire d’azu ta d’au tasa a laundry basket. Bayan ta dawo tana tsaye akansa ta gwada tab’a k’afar sa dayace yayi spraining to her suprise taga beko motsa ba, sake tab’awa tayi da d’an k’arfi nanma be motsa ba se baccinsa yake. Mamaki ne ya rufeta mutumin dayace yayi spraining k’afar ne ana tab’awa amman baiko jin zafi? Lallai kam! Komawa kan side drawer’n gefensa tayi ta zauna tana k’ure masa kallo daga gashin girarsa, idanunsa hanci dakuma lips nasa, batasan seda takai hannunta kan lips nasa ba haka kawai taji tanason ta tab’a, taji tanason tab’a lips nasa masu uban fidda bak’ak’en kalamu ganin yad’an motsa ta miyar da hannun nata baya haka tata kallonsa har seda La’asar prayer yashiga.

       “Anas!” takira sunansa a hankali. “Anas katashi lokacin Sallah yayi.” Nanma shiru seda tasa hannu ta tab’a sa ya bud’e ido ya azasu kanta. “Lokacin Sallah yayi” tace tare da kawar da kanta.
      “Kefa barakiyi ba?” Ya tambayeta dan kwata kwata ya manta batayi. Yi tayi kamar bata jisa ba ta mik’e.
        “Yes?” Cewar Anas.
       “Anas banayi ka manta ne.” Ba tare da yace da ita komai ba ya mik’e kan gadon kwata kwata ya manta da k’aryan spraining ankle nasa daya mata, garau ya mik’e yana tafiya. Baki ta sake tana kallon ikon Allah.
       “Anas har k’afan ya warke ne?” Se a yanzu ya tuna ya mata k’arya kuma tariga ta gano gaskiyar.
      “Da sauk’i be warke ba” yace da ita yana basarwa tare da d’an karkata tafiyar tasa. Daga yadda take kallonsa yasan tagano gaskiyar no point ya cigaba da k’aryan. “Okay, okay naji you caught me lying actually ba spraining ankle d’ina danayi I just faked it are you okay?” Dariya sosai ta b’arke da, Anas be tab’a ganinta tana irin wannan dariya ba se yau and he find her cute, admiring nata ya tsaya yi se dariya take harda ‘yar hawaye se chan tad’anyi shiru. “I’m sorry” tace tana girgiza kai hannunta na akan cikinta.
       “Kin gama?” Yace da ita.
        “I’m sorry but Anas why do you have to lie?”
       “Nima bansani ba, meh ruwanki?”
          “Anas daga tambaya.”
          “I miss you thats it” yace da ita sincerely dan dama haka yake he is straight forward. Wani irin yanayi ta tsinci kanta ciki a yayinda bugun zuciyarta ya k’aru. She couldn’t help it batasan seda ta soma blushing ba. ‘yar k’aramar tsuka yaja;
       “Mschw! you can stop blushing, not anymore I don’t miss you again” daga nan ya shige bayi tana zaune kan gado har ya idar da Sallah. Abinci yamusu ordering  bayan da suka gama ci ta d’au towel nata da hijabi ta nufa bayi dan sake watsa ruwa tad’an kwanta kafin Maghrib.

       A yayinda ya cigaba da gudanar da harkar gabansa a laptop shikuwa, bayan like 2 minutes ya tashi ya fice bada dad’ewa ba ya dawo yatsansa na yoyon jini da alama yankewa yayi. A gurguje yashigo d’akin, bayi ya nufa ya bud’e kasancewar Fannah batasa lock ba. Idanunsa basu sauk’a a ko ina ba sekan Fannah dake wanka, kwata kwata ta rasa me ya hanata sa lock bakin k’ofar a tunaninta wai ai Anas yasan tana ciki bare bud’e taba shiko yankan da yayi yasa ya mance da tana cikin bayin. Seda ya k’are mata kallo sama da k’asa sannan tasa wani irin masifaffen ihun da bata tab’ayin irinsa ba. Hannu yasa yakai baki kan wanda zeyi amai sannan da wurwuri ya rufe k’ofar. Both of them were speechless for the mean time, Fannah can’t believe Anas yaganta a haka kamar yadda shima yakasa believing yaga Fannah ba komai a jiki.

        Kuka tasa a bayin wanda har shi Anas d’in ya jiyota, tissue yaja ya tare zubar jinin sannan ya dawo kusa da k’ofan ya tsaya yana sauraron sautin kukanta, yarasa nayi ganin bata da niyyan barin kukan yakira sunanta “Fannah.”
         K’arfin kukan nata ta k’ara. “OMG! Fannah kukan me kuma? Stop crying please.” Banza tayi dashi takoma cikin jacuzzi ta zauna se kuka take. “Fannah stop crying na manta kina ciki ne, kinji?” Nanma bata ce komai ba.
“Kema mesa baki rufe k’ofar ba?” Cikin sautin kukan tace, “toh ai naga kasan da shiga na, kawai kawani kama ka bud’e mutum...” ta fashe da kuka.
     “Fannah ai ba da gangan na bud’e miki ba na manta ne.”
     “Bawani mantuwa wallahi...” ta k’are maganar cikin kuka.
       “Toh acewarki zan bud’e ki ne da gangan? Mezan kalla a jikin naki? Mschw!” ya fad’a a tsawace. K’arfin kukanta ta dad’a.
       “Okay, okay I’m sorry I should have knock still, bar kukan kinji?” Batace dashi komai ba tacigaba da rera kukarta.
       “I said I’m sorry, kinji?” Nanma shiru.
       “Ko sena shigo zakiyi shirun?” Still batace komai ba. Handle na bayin ya waina.
      “A’a dan Allah karka shigo” ta fad’a cike da tashin hankali, k’ok’arin jawo towel nata take amman takasa.
        Murmushi kad’an ya saki, ,“zakiyi shirun?”
      “Eh zanyi, nama nayi, nayi dan Allah karka shigo.” Daga nan ya koma kan gado ya zauna yana jiran fitowarta se canza tissue yake jinin bebar zuba ba har yanzu. Tuntuni Fannah ta gama wankan amman tak’i fitowa batasan dawani idon zata sake kallon Anas ba. Har yanzu takasa believing abinda ya faru d’azu. Ganin about 10 minutes har yanzu tak’i fitowa Anas yace, “Fannah wai haihuwa kike cikin barhroom d’inne?” Chan k’asa k’asa tace, “bansani ba wallahi da kallon tsireci ba haramun bane dana rama nima, nasan dagangan ka bud’eni.”
       “Fannah I will open the door in baki fito ba.” Ya fad’a a lokacin dayake takowa zuwa bakin k’ofar. “I have a cut on my finger I need to wash it ki bud’e.” Tana jinsa tak’i koda motsawa, tsaye take sanye da hijabinta gaban mirror.
        “I’m couting to three in baki bud’e ba I will saboda nasan kin gama wankan tun d’azu. One... Two...” Duk tana tsaye tana jinsa “Three!” Karap ya bud’e k’ofar tsaye yaganta gaban mirror “awww kinaji na dama?”

         A ranta tace kad’au yanzun ma ba kaya zaka ganni ko? Seka koma.
      “Fannah I’m talking to you.” Ko d’ago kai ta kallesa batai ba dan batason sake had’a ido dashi gefensa tabi ta fice nan yayi treating ciwon nasa yafito shima.
         Bayan fitowarsa ya tarar da ita zaune kan gado tayi jugum ga d’an hawayen dake forming cikin idanunta. A farko yayi niyyan ignoring nata sekuma ta basa tausayi, itan da ko cinyar ta batason agani bale ache duka aka ganta. Takowa yayi zuwa gabata batako noticing nasa ba saboda yadda tayi zurfi cikin tunani. “Fannah” ya kira sunanta a nitse, nanne hankalinta ya dawo jikinta kai ta d’ago, idanunsu na had’uwa tayi saurin kawar da kanta tare da sa hannu tana share hawayenta. Mik’ewa tayi dan ciro mai nata ta shafa tazo bin gefensa kenan ya rik’o hannunta tare da dawo da ita baya. Kukan da take k’ok’arin had’iyewa ta soma, kallonta ya tsaya yi be hanata yiba seda tayi me isarta sannan yasa hannu yana share mata hawayen. “I said I’m sorry I didn’t mean for it.” yace cikin wani irin salo. Kai kawai ta gyad’a masa tana k’ok’arin karb’an hannunta.

“Baki hak’ura ba?”
“Na hak’ura” tace ba tare da ta d’ago kai sun had’a ido ba. Hannu yasa k’ark’ashin hab’anta tare da d’ago ‘yar fuskarta yana kallo har a yanzu tak’i barin su had’a ido.
“Fannah you’re not, look at me” k’in kallonsa tayi. “Please...” anan ne ta d’ago idanunta ta azasu kan fuskarsa “I’ve looked at you, shikenan?” Tasa hannu ta sauk’e hannunsa daga fuskarta. Gefensa tabi ta d’au mai nata zata shiga toilet dan shafawa ya dakatar da ita ta hanyan kiran sunanta. Chak ta tsaya “I’ll excuse you kinji? You don’t have to go in there.” Be jira jin me zatace ba ya fice, ajiyar zuciya ta sauk’e. A nitse tasamu ta shafa manta tasa wani sabon atamfa d’inkin riga da skirt tagama shirinta tsaf sannan ta mik’e a kan gado. Har ayanzu Anas be dawo ba, da kwanciyarta bekai da minti biyu ba akayi knocking bisa k’ofar. Tashi tayi dan bud’ewa seta tuna da dokar da Anas ya kafa mata seda tasanya hijabi sannan taje ta bud’e.

Tsaye ta tarar da Anas, “can I come in?” Ya tambayeta. Kai ta gyad’a masa tare da matsa masa. Bayan ya shiga ta rufo k’ofar tare da ajiye hijabin a gefe, tayi miqarta kan gado. “kishirya Amal said she wants to see you.” Dama zaman nan d’in ya isheta ba musu ta mik’e ta soma shiri shima haka. Mayafi kalan atamfarta ta yafa duk Anas na kallonta seda ta gama shirin sannan yace, “ina zakije ahaka?”
       “Kamar ya ina kuma? Kaifa kace Amal wants to see me.”
       “I know I mean da wannan shirin.” Ya nuna ta da hannu.
     Kallon kanta tayi up to down bataga wani abin aibantawa ba. “Anas wani abu ne?”
       “Yes kisa hijabi baraki fita da wannan gyalen ba.”
       “Anas gidanku fa kace zamuje ba wani wajen ba”
       “Nasani nide ki cire kisa hijabi.”
     “Haba mana Anas nan da gidan kun ma sena sa hijabi ai naga bawani gun zamuje ba gidanku fa zamuje, waze kalleni achan?”
      “Shettima da me gadi zasu kalleki nikuma banaso.”
        “Yanzu Anas kishin Shettima kakeyi?” Ignoring nata yayi ya nufa wajen akwatunanta, medium red d’in ya bud’e sannan ya d’ago kai yaga kalar atamfar tata yaciro color’n hijab daze shiga dashi. Daga nan ya nufa wajenta mutuwan tsaye tayi takasa koda motsawa se binsa da kallo kawai take. Gyalen nata ya cire ya ajiye a gefe “gashi sa wannan lets go.” Se ayanzu hankalinta ya dawo jikinta “but An-”
       “Fannah banason surutu just wear it” ta gefen idanunta ta watsa masa harara sannan ta cire d’an kwalin nata ta b’urma hijabin.
       “Perfect!” yace a lokacin dayake kallon ta. “Lets go” ba abinda Fannah ke banda bin Anas da harara ahaka har suka isa zuwa wajen motarsu ya bud’e mata tashiga sannan ya rufe.

★‡★‡★‡

            Haka de rayuwa tacigaba da kasance ma Anas da Fannah. Anas yana tsantsan kishin Fannah, ko kad’an bayason wani d’a na miji yagane mata jiki musamman inya tuna ranan da ya ganta a bathroom. Shi karan kansa yasan yasoma sonta yanzu saide bayya tsammanin ze tab’a fad’a mata ‘cause har a yanzun bawai yayi accepting bane yasan sarai da ze samu wani yayi mai bayanin how he feels towards Fannah cemasa za’ayi yana sonta, abinda bayya son ji kenan. Sesa har ayau yak’i yarda wai sonta yake. Ko zaune yake a office muddin da pen a hannunsa bai sanin seda yake soma rubuta sunanta akan paper, a kullum burrinsa yadawo hotel nasu ya samu Fannah.

       Ta b’angaren Fannah ma duk kanwan ja che, sede ita tayi accepting son da take masa amman kuma barata bari son yaje ko ina ba saboda rashin martabar ta, she don’t want to be broken.

Ba laifi Fannah da Anas suna shiri yanzu danko se su d’au kwana biyu basuyi fad’a ba amman gasa bak’ak’en kalamu kam na nan, da abun ya tab’o Mr. Fauzi kuwa se yayi dalilin dazesa zasuyi fad’a at the end kuma yazo yana bata hak’uri.

*****

Da bikin auren Anas da Fannah wata d’aya cus kenan, cikin wattani shida dasukayi agreeing akai. Anas ya biya Fannah first salary nata wanda yake N500,000 duka ta d’au ta dank’ala wa Mami akan sukai Baba National Hospital Abuja a dubasa dakyau amasa duk wani abinda ya kamata. Koda da Mami ta tambayeta a ina tasamu uban kud’i haka ce mata tayi Anas ne ya bata shiko koda da Mami takira sa dan masa godiya be nuna mata wani abu ba.
Alhamdulillah! Su Mami sunje sun dawo lafiya qalau da zaran Baba ya shanye magunansa ana fatan masa waraka.

****
Yanzu Fannah take gama had’a musu kayakinsu ansamu an gama masu sabon gidansu, she is super excited taga gidan musamman ma dataji Anas ne ya zana da hannunsa. Bayan ta gama had’a musu kayakinsu duka yasa aka sauk’o masu dashi aka kai mota wajen biyan bills ya nufa yayi settling. Fannah na zaune a mota tana jiransa. “Lets go?” Yace da ita alokacin daya kunna motar. Kai ta gyad’a masa cike da jin dad’i “yes.”

Unguwar Giwa Barack yajasu chan inda sabon gidansu yake, daidai gabar wani mansion Anas yasa kai, gate d‘in na identifying plate number’n motar nasa seya bud’u da kansa. Baki Fannah ta sake cike da mamaki, kasa b’oye mamakin nata m tayi ta tambayesa. “Anas dakansa yake bud’uwa?” Be amsata ba seda yayi parking a lot sannan yace, “yes ‘yar k’auye dakanshi yake bud’uwa dakuma kulluwa muddin anyi registering plate number’n.”
“Owwww!” tayi exclaiming tana gyad’a kai. “In d’an wannan kina sake baki nakega by the time muka shiga ciki zakimin littering marble floor na miyau.” Harara ta galla masa ta gefen ido. “Lets go in” yace da ita. Atare suka fito ta tsaya k’are wa gidan kalloi, flat mansion ne me penti fari daga sama se divider milk k’asan kuma brown, tunda Fannah take bata tab’a ganin gida katafare me kyau ba kamar wannan ba sede a TV show. Juyowa yayi ya kalleta seyayi murmushi ganin yadda ta kasa rufe baki, hannunta ya fisga “lets go” wajen garden yasoma kaita gabad’ai wajen green carpet ne seda coloured flowers wanda suka sake k’ayata wajen, a gefe guda kuwa bishiyoyi ne da dama kamarsu guava, mango, banana, dates (dabino) da sauransu. Gaba da wajen kad’an aka yi wani ‘yar runfa me kyan gaske, cikinsa tables ne guda biyu da kujeru hud’u-hud’u a kowanne. Daga gun garden ya wuce da ita swimming pool an k’ayata sa sosai, daga chan suka sake dawowa gaban gidan inda yake ajiye motocinsa da ko plate number ba’a sa musu ba alaman na kwalya ne bawai na hawa ba. Sabin motoci ne pil sauran ma ko b’are ledojin jikin ba’ayi ba, irgawa ta soma da Anas ya gano haka seyace “ba sekin b’ata

Please Login or Register in order to submit comment