Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yanzu sede abu d’aya da nakeson sanar dakai shine shi muslimi da tawakalli aka sansa, Fannah tamin bayanin komai na maka k’arya akan bata fad’a min ba saboda inason ji daga bakinka inkuma tabbatar da eh ka tuba dagaske kuma kayi. Hak’ik’anin gaskia ba na mijin da zeyi zaman mutunci da Fannah kamar yadda zakayi Anas hasali ma mune da godiya zanyi iya qoqari na dan ganin Fannah ta koma gidanka amman barin tilasta mata ba saboda abinda yafaru a tsakaninku da ciwo Anas she needs some space kuma ni na yafe maka duk mun yafe maka ina fatan Fannah ma zata yafe maka wannan abu yazame sirri a tsakaninmu ko Babansu barin sanar dashi ba zan barku tare” tana kai nan ta mik’e haka Fannah ma.

Da sauri ta dakatar da ita “A’a Fannah ki zauna ku gana kikuma yafe masa kinji Habibiti?” Kai kawai take girgizawa tana hawaye “yi hak’uri ki zauna” nan ta shige d’aki. Itama Fannar hanyan d’akinsu ta kama bi dan ko batasan me zata fad’a mai ba, kamar a kyaftawan ido Anas ya mik’e ya riqo hijabinta “Fannah dan Allah karki tafi I’m sorry please forgive me.” Har a yanzu takasa furta koda ‘A’ a nitse ya juyo da ita suna fuskantar juna yunk’urin sauk’a kan guiwoyinsa ya gwada tasa hannu da sauri ta tarosa cikin sautin kuka tace “Anas dan Allah kabari dan Allah stop it na gamsu da tubar da kayi kuma na yafe maka zaka iya tafiya.” Hannunta daya gwada tab’awa taja da sauri tak’unsa cikin hijabinta. “Fannah thank you, thank you so much yanzu ne zan iya samun sukuni a rayuwa na, I can be free now amman dan Allah karki barni Fannah lets go home please I love you.”

“Anas I can’t dan Allah kabarni katafi please” tana kaiwa nan ta fisge hijabinta ta shige d’akinsu. Kuka sosai ya tsaya yatayi awajen Mami ce tafito ta riga basa hak’uri takuma tabbatar masa cewa Fannah zata dawo a garesa saboda tana sonsa da k’yar ta iya tura Anas ya tafi koda yafito beyi takansu Afrah ba motarsa ya nufa ya wuce a 360 isarsa gida keda wuya ya had’a akwatin kayansa dawani duk abinda ze buk’ata ya rufo gidan ya wuce paint house nasa daga ranan ya soma rayuwa achan abinci ma ba ci yake ba se in yunwa ta gasa sa. Koda su Ummie suka mai waya za suzo dubansa da Fannah kuwa k’arya ya musu yace sunyi tafiya basu gari. A kullum cikin tunanin Fannah yake har kamar ya fara zarewa dan yana zaune shi kad’ansa seyaji wai Fannah na kiran sunansa cikin sarqarqiyar muryarta me bala’in masa dadi hotunanta ne suka zamo masa farillah dan a kullum pictures nata na a gabansa yana kalla.

Akwai lokacin da damuwa suka ma Anas yawa kad’an ya rage ba’a koma gidan jiya ba tunda ya sanar da Mustea halin da yake ciki Mustea ya k’arfafa masa guiwa kan yanemi syrup kawai yasha amman dan promise daya d’aukar wa Fannah ya hana kansa da k’yar, bare iya explaining how much yayi missing Fannah ba duk yabi ya rame ya fita daga kamanninsa gabad’ai office ma yabar zuwa duk yamusu k’arya yace yayi tafiya.

Morning, afternoon and night messages kam bebar sending ma Flowersa ba dukda ba replying nasa take ba. Ya kirata har ya gaji amman bata picking koda ya kira ta wayar Afrah dan a had’asu ma nan bata karb’a.

A takaice de rayuwar wannan masoya biyu ya jagule cikin sati biyun da sukayu batare da sunsa juna a ido ba. Ba aikin Fannah a kullum se kuka, bata tab’a sanin tanason Anas ba seda ta dena ganinsa a ganga da ita da daddare kuwa kullum tazo bacci seta rungumo pillonta setanaji kamar Anas nata ne. Wayarta na maqale a hannunta a koda yaushe tana karanta lovely heart touching messages da Anas yake mata sending wanda take matuk’ar jin dad’insu amman batajin zata iya replying nasa back aduk lokacin da tunanin abinda ya faru tsakaninsu yayi crossing mind nata.

Ba yadda Afrah batai da ita ta gaya mata meke faruwa ba amman tak’i ta d’au alk’warin riqe wa mijinta sirri. Abinci kam ba takansa take ba se sunyi fad’a da Mami take chi shid’inma kad’an take tab’awa. Akoi lokacin da su Mami sukayi Eghusi soup da pounded yam tana gani kawai ta tuna da Anas ta tuna da yadda yakeson miyan kawai ta b’arke musu da kuka.

*****
“Fannah! Fannah!” Kiran Mami daga d’akinsu da Baba. Fannah dake d’akinsu miqe kan sallaya tana aikinta na kullum wato kuka tayi saurin share hawayen ta danko in Mami taganta zasuyi fad’a. “Na’am” ta amsa agigice tare da zabura ta nufa d’akinsu Baba chan ta samu Mami.
“Bade kuka kike ba?” Cewar Mami kafin Fannah ta amsata ta cigaba, “karki damu na riga na ma Anas waya yau zezo ya d’aukeki kowa ma ya huta kinsan gobe Babanku ze dawo-” katseta Fannah tayi.

“Mami dan Allah karkimin haka ko kwana biyu kibarni in k’ara anan.”
“Nak’i Fannah ke wai bakida tausayi ne? Kinsan irin halin da kika jefa Anas tafiyarki kuwa? Yaron nan ya tuba mesa baraki yafe masa kukoma ku cigaba da zaman ku tare kamar yadda kuka saba ba? Ko wai acewarki akoi d’a namijin da ze kula dake ne kamar yadda Anas zeyi? Tun ina ganin abin naki da hankali na dena yanzu maza wuce ki shirya kayakin ki da La’asar Anas zezo ni na fad’a miki.”

Har k’asa Fannah ta sauk’a tana had’a Mami da Allah amman ko a bakin zaninta ta fice tabar mata d’akin. Seda tayi me isarta sa’annan takoma d’akinsu takasa koda shirya kayakin nata zube take kan gado tana kukan da ita kanta batasan dalilinsa ba tana cikin haka taga call daga Anas bayan ya kwana biyu be kiranta se saqonnin dayake mata me zece mata yau? Ze zo ya d’auketa ko meh? Tana gani har yamata 2 missed calls tak’i picking bada jimawa ba ya turo mata message.
_Flower please don’t be mad I’m sorry and I love you #kisses_

Wani sabon kukan ta fara seda tayi ta godewa Allah sannan ta tashi ta jawo akwatin ta sam takasa cika kayakinta ciki daidai nan da shigowar Mami kenan baki ta sake ganin akwatin Fannah empty batako soma shirya kayakin nata ba. “Yanzu Fannah baki ko fara shirya kayakin naki ba bayan kinsan La’asar ya kusa?” A marairaice ta d’ago idanunta tana kallom Mami. “Mami dan Allah kibari ko gobe se in tafi.”
“Mschww! maganan banza” wardrobe nasu tanufa ta bude tare da ciro kayakin Fannah kap tasasu cikin akwatin tayi zipping se roqarta Fannah ke amman ko ta kanta Mami batai ba tsab ta had’a mata kayakinta masu dotti tasasu cikin leda ta had’esu gu d’aya.

_4:12PM_
Shigowar Anas gidansu Fannah kenan Mami kanta data gansa seda ta tsorata tana cewa Fannah ta rame ta lalace amman farillah ramanta yake aganga dana Anas sam kamar ba shiba bayan gaisuwa Mami ta sake basa hak’uri sosai sannan kuma ta masa nasiha daga nan tashiga dan fito da Fannah drama sosai suka riqayi sannan da qaqani qaqa tasamu ta fito da ita, akwatin ta Anas ya amsa.

Wa’azi me ratsa jiki Mami ta musu sosai duk jikinsu ya sake mutuwa barin ma Fannah, da k’yar tafito daga gidan iya bakin k’ofa Mami ta musu rakiya ta koma ciki.
“Fannah please lets go kinji? Kiyi hak’uri kibar kukan nan please lets go.” Sam tayi kamar bada ita yake ba sun kusan minti biyar tsaye wajen ganin batada niyyan ko motsawa ya finciko hannunta. “Anas ka sakeni ka sakeni nace” da dambe ya k’arisa motan da ita ya bude’e mata gidan gaba yasata sannan ya sanya jakarta a baya yazagayo shima ya shiga. Tunda suka fara tafiya take masa kuka a mota koda suka isa gida kuwa tafito bata ce masa komai ba akwatinta taciro ya karb’e mata.

Shigarta ciki ta nufa d’akinta ta baje kan gado, bayanta yabi yakai mata akwatinta. “Flower kinci abincin rana?” Ya tambayeta baya ta juya masa. Nufowa gabanta yayi nanma ta sake juyawa “Flower meh kikeson ci? Yi hak’uri ki fad’a min” nanma banza dashi tayi haka yata suratansa har yagaji bata tanka sa ba seda ya fita ta mik’e tashiga bayi ta watsa ruwa fitowarta yayi daidai da shigowar Anas da plate na kaza a hannunsa.

A farko tayi niyyan komawa cikin bathroom d’in dankuwa gajeren towel ne ajikinta daga baya data tsaya tayi tunani cikin d’an k’ank’anin lokaci kuwa setaga yin hakan bayida amfani tunda ya tab’a ganinta ba kaya ma a jikinta. Ignoring nasa tayi ta nufa wajen dressing mirror har anan bebar kallonta ba he can’t explain how much he missed her body. Daga bisani ya girgiza kai “Fannah I’m sorry bansan...” Sekuma yayi shiru yaja k’ofar ze rufe kenan ta ce dashi “ba komai.” ba tare da ta kallesa ba. Sam be yarda da abinda kunnuwansa suka jiye masa ba be d’au Fannah zata sake masa magana bama, lallai inta haka he has a chance. A nitse ya k’ariso cikin d’akin “gashi incase you are hungry eat please” ya ajiye mata plate d’in kan dressing mirror. Seda ya kai da bakin k’ofa sannan tace masa “nagode.” Dad’i sosai yaji “you are welcome Flower.” Yana kaiwa nan ya fice yakoma parlour ya zauna yana jirar ko zata fito.

Bada dad’ewa ba k’ofarsu yayi k’ara yana dubawa yaga sabin fuska guda biyu da alama ma mata da miji ne wani button ya danna se main gate ya bud’u nan ya fito dan tarerayarsu. Bayan ya shigo dasu sika gaggaisa.
“So gidanmu ne kusa da naku by the left lokacin da kuka zo nan munyi tafiya nida HASKE NA dawowan mu kuma mukaji wai kuma kunyi tafiya d’azu Haskena kecemin ta ga shigowarku shine nace mata yakamata mushigo mu muku sannu dazuwa.” Cewar mijin. “Suna na MUS'AB wannan kuma is my wife NAINAH” yajuyo ya sakar mata dawata lallausassar murmushi, murmushin ta miyar masa itama. Haka kawai se Anas yaji sun burgesa se ya tuna lokacin da suke a haka shima shi da Flowersa he misses her alot, da k’yar ya iya bud’a baki yayi magana drinks yayi serving nasu ganin Fannah batada niyyan fitowa ya shiga mata managa mik’e kan gado ya tarar da ita. Bayan ya k’arisa ya zauna agefenta yace, “Flower munyi bak’i neighbours namu ne suka shigo mana inda zaki iya fitowa seku gaisa da matarsa.” Kai ta gyad’a masa. Daman da hijabi jikinta bayansa tabi suka fito daya gwada yunk’urin riqe mata hannu kuwa setaja da baya.

“Flower just for this once se mun nuna musu we are not on good terms ne? Please corperate” Sam tak’i barinsa ya tab’a mata hannu haka ba yadda ya iya suka fito kai a rabe idanunta basu sauk’a ako inaba se hannun Mus’ab da Nainah data gani a had’e se hirarsu suke suna dariya gwanin sha’awa a hankali ta dawo da kallonta kan Anas ita kanta she miss yadda suke a da. Ahakan suka k’ariso parlour’n suka zauna a seperate kujera tun anan hankalin Mus’ab yabasa da akwai matsala bayan sun gaggaisa cike da dabara ya buk’aci Fannah dasu shiga ciki da Nainah, hakan kuwa akayi. Alokaci guda Fannah taji san Nainah yashigeta ganin yadda take small of age amman ga hankali da ladabi da biyayya sede ashe ba Mus’ab ne kad’ai yagano abinda ke faruwa tsakanin Anas da Fannar ba har ita Nainan ma tayi. Suna zaune kan gado bayan Nainah tagama yabawa d’akin Fannah dama gidan entirely tayi gyaran murya.

“Aunty Fannah” tace da ita.
“Na’am Nainah” ta amsata.
“Ba shisshigi ba Aunty amman senaga kamar da akoi matsala tsakaninki da Uncle.” Bata bar Fannah tayi magana ba ta cigaba “shi zaman aure se hak’uri Aunty koni da kike gani na nan inada kishiya kuma bawai shiri muke da ita ba sau dayawa tana cewa seta kasheni hakan be bani daman fad’a da miji na ba ina sonsa kuma shima yana sona kamar yadda nasan kuma kuna son junanku.” Wa’azi sosai Nainah ‘yar shekaru sha bakwai ta tama Fannah liqis ta kashe mata jiki gakuma wani kunyan dataji ache k’anwar bayanta tamata gyara bisa ganganci irin nata dan ko bata tambaya ba tasan Afrah ta girmi Nainah. Godiya sosai Fannah ta mata tare da bata kyautan wasu bangles had’ad’d’u.

Shima Anas tun zamansa da Mus’ab ya riga masa wa’azi da nasiha sosai.

****

Bayan sun yi masu rakiya suka dawo ciki har Fannah takai da bakin k’ofar d’akinta sekuma ta tuna alk’awarin data ma Nainah nacewa zata bawa Anas hak’uri bisa hurting nasa datayi. Seta juya zata masa magana sekuma ta kas, shiko yana tsaye a tsakar parlon ya k’ura mata ido ji yake kamar yaje yayi hugging nata ya fad’a mata how much he loves her. Da k’yar ta iya kiran sunansa muryarta se rawa take. “Anas” daman jira yake ya amsa “na’am Flower” tare da takowa har gabanta dududu space daya rage a tsakaninsu befi inches shida ba.
Kanta ta sunkuyar “Anas I’m sorry kayi hak’uri” ta fad’a dashi sincerely. Hannunta duka ya rik’o cikin nasa d’aya yana murzawa a hankali tare da mata wani erin kallo alokaci guda yaji bak’in cikinsa duk sun gushe, murmushi ne fal kwance a kan fuskarsa. Dad’i yaji sosai da bata hanasa rik’e mata hannu ba.


*© MIEMIEBEE*

beeenovels.blogspot.co.ke
[12:58, 12/18/2016] ‪+234 903 612 6826‬: •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫

❣🎀❣🎀❣

*_written by miemiebee👄_*

In dedication to *Aunty Sis💕*
7⃣4⃣


   



     D’ayan hannunsa ya aza a hab’arta tare da d’ago fuskartata. “Flower you don’t have to be sorry baki min komai ba, ni ya kamata in baki hak’uri and not the other way round I’m sorry kinji?” Kai ta gyad’a ba tare da tabari sun had’a ido ba. “Flower baraki kalleni ba?” ta kad’a masa kai. “Then look at me” ba musu ta miyar da kallonta kan kyakkyawar fuskarsa, murmushi ya saki mata yana kallon cikin idanunta. “I miss your body can I hug you?” Hannun ta taraba daga nasa tare da gyad’a masa kai nan ta rungumeshi shima haka, hugging juna passionately “I miss you too Anas.” Sun d’au tsawon lokaci suna manne da juna suna jin dad’in k’amshin jikin junansu sannan daga bisani tayi breaking hug d’in tare da juyawa zata shiga d’akinta, hannunta ya riqo da wuri “Flower muje muci abinci kinji?” Kai ta girgiza masa nufin bazata ba.

      “Flower bakiya jin yunwa?” Ta gyad’a kai “please muje nasan kinaji lets go.”
      “Barin jeba” ta fad’a tare da shigewa d’akinta. Badan yanaso ba yajuya ya shiga d’akinsa ya canza shiri bayan ya fito ya rufo k’ofar juyawansa kawai ya tarar da Fannah tsaye gefen motarsa idanunsa ya sosa da kyau dan tabbatar da abinda yake gani. Murmushi ta saki masa “yi sauri ka bud’e min rana.”  Kasa danna security d’inma yayi duk ya kid’ime sosai navy blue hijabin dake sanye jikinta ya mata kyau seda ya gama k’arisowa gabanta ya tab’a hannunta dan tabbatar da ko eh dagaske itan ce sannan ya bud’e motar mata da kansa, bayan tashiga ya rufe sannan ya zagaya shima ya shiga suka fice. Hira d’ad’d’aya yake mata wanda ba duka take amsa shiba har suka isa inda zasu.

     Daidai gaban DERIBE HOTEL suka tsaya dan chan yayi reserving bayan ya bud’e mata k’ofa ya rik’o hannunta, shigansu ciki taga yayi reserving as always. Cikin wani irin salon da bare basa haushi ba tace, “Anas baka iya chin abinci se kayi reserving?” Kai ya gyad’a mata “why?” Ta tambayesa “saboda banason hayaniya.” ya amsata.
     “Kasan meh?”
   “A’a meneh Flower?”
    “Inason yau muje inda bakayi reserving ba muci abinci inason ka koyi cin abinci in public its fun.” Sam beji dad’in wannan shawara na Fannah ba haka yake bai iya cin abinci in public ba, ko days back dayake boarding school sede ya taho da abincinsa hostel yaci inkuma aka hanasa, abincin da bayya chi kenan. “Anas Habeebi” ta kira sunansa ganin baida niyyan magana.
     “Bakaso?”
    “Inaso Habibti lets go” ya mata k’arya nan suka juya GRAND PINNACLE HOTEL
LUXURY suka dosa bayan sunyi placing order bada jimawa ba abincin nasu ya iso tun anan yanayin Anas ya canza daya juya yaga mutane anan mutane achan ga wasu yara masu uban surutu se distracting nasa suke abinda ya wasa kenan. Har takai spoons biyar Anas be tab’a nasa ba. “Anas mesa baka chi?”
     “Flower the truth is am not used to it ban iya chin abinci cikin mutane ba.”
    Qasaitacciyar murmushi ta sakar masa tare da matso wa kujeran dake kusa da nasa ta zauna spoon d’aya ta d’aga ta kai masa baki. Kallonta yake kawai cike da adoration wani sabon santa na sake shigansa. “Ahhh” ta buk’ace sa. Murmushi ya mata sannan ya bud’e bakin nasa ta basa, haka ta riga basa seda yace ya k’oshi anan ne itama ta jawo na ta plate zata cigaba daci amsar plate d’in yayi “my turn my lady.”
      “No nikam zanci da kaina.”
    “No Flower let me kinji?” Kai ta gyad’a masa haka yariga bata itama seda tayi nak!
    “Look around you” ta buk’ace sa bayan ya juya ya k’are wa mutanen cikin kallo sosai yaga lessons kowa da kalan rayuwarsa ga masu jiran mutane su gama cin abinci su d’au nasu suma su samu su chi, da wanda suke sharing abincin plate d’aya mutane de daban-daban. “Kaga yawan shiga cikin jama’a nasa mu sake godewa Allah cikin yanayin da muka tsinci kanmu for instance kalli wanda suke tsaye bakin k’ofa achan ko kud’in abincin ma basuda kaga anan se ka sake godewa Allah right?”
      “Right Flower” ya amsata cike da jin dad’i “Alhamdulillah!” nan ya biya musu kud’insu da suka fito kuwa irin mutanen wajen nan duk yabisu ya rarraba musu kud’i dad’i sosai Fannah taji tun daga ranan Anas ya koyi chin abinchi cikin jama’a although atimes seyayi reserving waje still.

     Koda suka dawo gida shi ya taimaka mata ta had’a kayakinta cikin wardrobe nata bayan nan suka miqe kan gado suna hira abinsu gwanin sha’awa Fannah na viewing pictures nata da Anas yakeda su cikin wayansa wanda kap batasan lokacin daya d’aukesu ba tana cikin haka Angel ta soma kira nan ta miqa wa Anas. Bayan sun gaisa Amal tasoma k’orafi.
     “Shikenan Ya Anas tunda kayi aure kadena sona nasani yanzu se Ya Fannah kakeso.” Dariya sosai shida Fannah sukayi “inji wa Angel? I love you both, no one like you kinji? Kibar had’a kanki da Fannah.” Amsar wayar Fannah tayi.

      “Amal karki ce haka kinga nima yanzu mukayi fad’a da Anas cemin yayi yafi sonki akaina.”
     “Kai Ya Fannah bawanin nan.”
     “Dagaske Angel na Ya Anas.” Dad’i sosai taji toh shikenan ba-bye tayi hanging. 
     “Toh Mr. Fauzi kaji Amal tana k’orafi gobe yakamata ka mata shopping ka kaimata.”
     “Angama Mrs. Fauzi your wish is my command.”
    Oh hakane yanzu? Ko ka manta kaine Boss d’ina?
     “Ada kenan Flower but now kece Boss... Me kikeyi?” ya tambaya ganin ta seta cameran wayarta kansa.
     “Abinda ka saba min, now I have 5 of your pictures”
     “LOL kin rama kenan? Let me see them”
     “Fad’i gaskia de so kake ka goge barin bada ba” tana kaiwa nan ta miqe da sauri ya jawota ta fad’a jikinsa k’ok’arin k’wace wayar yake ta duk’un’kunesa cikin hannunta tasa a kayanta acewarta ahakan bare iya amsa ba. Murmushi yasaki sannan yasa hannu cikin kayan nata ya zaro wayar sanadin haka yasata dariya se kamar chakulkuli yake mata. Fuska ta maraice “karka goge please kaji Habeebi.”
   “Tell me you love me.”
    “In nafad’a baraka koge ba?”
   “Yes Baby” ya gyad’a mata kai.
   “Okay Mr. Fauzi I love you I love you so much” tayi pecking nasa a kumatu. “Bani toh.”

   *****
        _5:20AM_
      Bayan sun idar da Sallah suka koma suka kwanta kamar yadda suka saba a kullum. Hannunsu ya had’a “Flower yau bakiyi mafarki ba”
     “Yes I’ve found you already ai bawani mafarki kuma.”
    “I’m sorry kinji Flower for hunting you like that.”
     “Nima I’m sorry lets sleep kasan akoi office yau.”
    “Ni barinje ba.”
    “Lallai kuwa Mr. Fauzi kafara wasa da aiki.”
    “I don’t want to leave you Flower.”
     *_“INA TARE DA KAI_* My Lion am never leaving you.” Dad’i sosai yaji yayi pecking cikin gashinta. “Aha! I have a suprise for you yau around 1:30PM zanzo in d’aukeki kinji?”
     “Naji meh suprise d’in?”
     “Ai ba’a fad’an suprises Flower just keep calm.” Ahaka suka koma bacci.

    _7:40AM_
       
      “No goodluck kiss Flower?” Cewar Anas suna tsaye bakin k’ofa hannunsa rik’e da nata d’ayan kuma lunch nasa. Murmushi ta saki masa “babu sakemin hannu inkoma ciki take care of yourself for me, I love you.”
       “You must kiss me first.” Kafad’a ta buga masa “seka dawo.”
    “No ni yanzu nakeso”
     “Then ka fad’a min meh suprise d’in ko hint ne kabani kaji Habeebi then I will kiss you” ta k’arisa maganan hannunta biyu zagaye a wuyansa.
     “Flower suprise ne I can’t tell you.”
     “Shikenan nima I can’t kiss you” hannayenta ta cire daga wuyansa, da sauri ya zagaye nasa hannun a ‘yar kunkuminta “you must Flower.” murmushi ta masa sannan tayi d’agel tayi grabbing lips nasa batasan a lokacin da ta kai hannayenta cikin gashin kansa da yayi styling ba d’azu kap ta hargitsa masa dan yadda kissing nasa ke tafiyar mata da imani se chan da tayi pulling out ta masa murmushi, shima murmushin ya mata.
    
      Idanunta na sauk’a kan gashinsa ta waro idanu. “Ya Salam Habeebi kaga gashinka its all a mess!”
      “Toh ai kece, ke kika hargitsa min.”
    “Toh ai kaine I lose control whenever I’m kis-” sekuma tayi shiru takasa k’arisa maganan dan wani kunyan dataji ya ratsa ta ita kanta batasan ya akayi ta fad’i wannan maganganu ba. Kai ta sunkuyar a yayinda yasa hannu a k’ark’ashin hab’arta ya d’ago fuskarta, fuskarsa d’auke dawani shu’umin murmushi.

      “Flower me kikace?” Kamar

Please Login or Register in order to submit comment