Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lokacin ki ba guda 7 ne kacal lets go in.” Haka yajata zuwa main door d’in. K’ofar kad’ai ma abar kallo ce. Irin manyan security doors d’innan ne. Password d’in yasa anan k’ofar tayi kukan “welcome home Mr. Fauzi and unknown.” Nanma seda Anas ya rufa ma Fannah baki yau tana ganin ikon Allah k’ofa na magana. ‘Yan danne danne yayi jikin k’ofar se ya sake managa “Mrs. Fauzi added to family list, welcome home.” A hankali ya bud’u suka shiga ya sake rufe kansa.

Kaftareren parlour ne da had’ad’d’un frames, wallpaper da verses, cushions na cikin farare swal seda colourful throw pillows jere akai. Rug d’in dake parlour’n na nan colourful shima. Cinema (babban TV) ne manne jikin bangon kai tsayuwa dan bayanin had’ewan gidan youngest billonaire b’ata lokaci ne ayita imagining kawai nagaji(LOL) Haka yabi ko ina cikin gidan ya nunnuna mata Fannah de takasa magana har a yanzu inbanda wow datakeyi ba abinda ta iya tace, jacuzzi ko ina cikin bathrooms banda d’akin Anas dake nan harda Live CNN connected ciki.

Bayan da suka gama biye ko ina cikin gidan suka sake dawowa parlour, daba dan Anas ba da Fannah ta b’ace cikin gidan danko ta manta hanyan da suka bi. “So kinga d’akin ki ba? The purple one, nikuma nawa ne farin, we will no more be sharing a room.” Cewar Anas, da biyu yayi maganan danko yasan sarai Fannah da uwar tsoro barata iya kwana ita kad’ai a d’aki ba. Idanun ta ta d’aga ta aza akansa. “Eh nagani this is a wonderful house, kudos to you. Amman Anas nikad’ai zanna kwana cikin makeken d’akin chan??” Ta tambaya tana zaro idanunta.
“Yes ke kad’anki-” katsesa tayi.
A’a dan Allah Anas wallahi barin iya kwana ni kad’ai ba kayi hak’uri please, ko a k’asa ne a d’akin ka zan na kwana.”
“Why?” Ya tambayeta yana me jin dad’i amman se nuna ma ta yake kamar bayyaso.
“Anas a list na contract namu ai bakace za’a na raba kwanciya ba, kuma kafa san mutumin, wallahi ze dawo dan Allah karka min haka.” Cruel smile ya saki, “I will think about it.”
“Anas please...” Ta rok’esa.
“Okay naji” yace ganin zata soma masa kuka. Dad’i taji sosai wanda ta kasa b’oyewa.
“Ermmm... Anas nace d’akuna nawane a gidan duka?”
“Ke wani irin brain ne dake daman ba k’irgawa naga kinayi ba d’azu?”
“Nafara irgawa sena rikice.” Kallonta yayi ta gefen ido, “fish head” yace a hankali. Sarai tajisa amman tayi shiru. “Guda 7 ne including guest room seda parlour biyu dakuma toilets 7 se kitchen d’aya da store room biyu. Clear?” Kai ta gyad’a a hankali tare da had’iye miyau. Sede daya kalli fuskarta ya gane tanada tambaya.
“Say it out”,yace da ita.
“Ermm. Anas duka d’akuna 7 d’in zanna sharewa ni kad’ai?”
“Eh da meh aikin ki? Aure fa kikazo yi ba hutu ba Fannah.”
“Anas nasani amman...” se kuma tayi shiru “kad’an taimaka please ga shara ga mopping gakuma girki yi hak’uri.” Murmushi ya saki wanda fararen hak’waransa na sama kad’ai suka bayyana.

“Karki damu akwai masu aiki zasu na zuwa morning and evening suna duk wani aike-aiken, abinda zakina yi kawai cooking ne dan ba daga hannun kowa nakecin abinci ba, kema se kinyi sanitizing hannunki tukuna, clear?”


*© miemiebee*
[12:57, 12/18/2016] ‪+234 903 612 6826‬: •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫

❣🎀❣🎀❣

*_written by miemiebee👄_*

In dedication to *Aunty Sis💕*
6⃣3⃣



*Assalam, as I promised zan bud’e new blog address, I did and its* beeenovels.blogspot.co.ke *so to my blog readers lets hit! Thanks for the love and support and also for the warm prayers, love you all!*
*Also masu cewa nayi repeating page 62 twice a’a ku gane mutane ke yi ba ni ba, ina miyar da hankalina sosai wajen numbering pages so take note bana mistake anan. Masu editing min pages nasan kwad’ayin son next page ke saku yi amman kuyi hak’uri ku dena please kuna janyo confussion*




     Kallonsa ta tsaya yi danko be isheta da kallo ba wai har setayi sanitizing hannu tukuna ta masa girki, shima kallon nata yake da gira d’aya a d’age. “Baki jini bane? Nace you need to sanitize those hands” ya kalli hannun nata “before cooking for me” Kallonta ta kawar daga garesa ba tare da tace komai ba. Taku d’aya ya k’ara kusa da ita tare da rufe gab dake tsakaninsu da sauri tayi taking step backward, ganin haka ya k’ara 1 step forward haka suka tayi seda yakaita jikin bango, wani irin kallon tsiya yake mata da tuni yasa zuciyarta bugawa fat-fat.
        “Kinji ni?” Yasake cewa da ita alokacin dayake kallon lips nata. Kai ta gyad’a cike da tsoro “nn... Na... Naji.” bending wuyansa yayi ta hanyar matso da fuskarsa kusa-kusa da nata dududu ratan dake tsakaninsu befi inchi d’aya ba. K’ara dad’uwa bugun zuciyarta yayi a yayinda k’arfin numfashinta ya dad’u. “Anas pl-” bata k’are maganar ba ta matse idanunta gam ganin Anas yasake matso da fuskarsa kusa da nata, har had’ewa numfashinsu yake.

         Juyawa tayi zata bi gefen damanta dan guduwa, karap ya aza hannnsa jikin bangon ya dakatar da ita, haka ma yayi a gefen damanta “Anas please ka ba-” bata k’are maganar ba taji ya kunna switch d’in wuta daga jikin bango tare da matsawa baya. Shu’umin murmushi ne fal d’auke a fuskarsa “Da me kika d’au zan miki? LOL such a negative thinker. You thought I’ll kiss you right?” Wani irin kunya taji ya rufeta ji take kamar ta tone k’asa ta b’oye kanta, gabad’ai ta gama tsorata ta d’au kissing natan zeyi, amman dan iskanci ze kunna wuta shine seyayi kalan abinda ya mata? Mschww.
       “Ni ba abinda nake nufi ba kenan” ta fad’a dan kare kanta tana kallon k’asa.
       “Whatever ba sekin min k’arya ba.” ya fad’i da wani murmushin tsiya fal a fuskarsa. Ganin batada abinda zata ce masa kawai ta fara tafiya dan barin parlour’n although batasan ina take dosa ba. Kallonta yake ganin ta d’au hanyan store room ya tsayar da ita ta hanyan kiran sunanta, “Fannah!” Banza dashi tayi tana me cigaba da tafiyarta. “In d’akin ki kike nema that is not the way, you go right” ya nuna mata da yatsa. Bata ko tanka sa ba tabi right d’in ta fice. Achan ta samu d’akinta.

        Akan gado ta zauna se kai take girgizawa ta matse idanunta gam har a yanzu kunyan abinda ya faru tsakaninta da Anas d’azu take. Tsuka taja a fili “mscwh! Ai seya d’au dama tunba yau ba ina expecting kiss daga garesa, Ya Salam!”
        Knock ne yashigo daga k’ofarta. Kafin tace zata bud’e tajiyo muryan Anas “ga luggages naki and ba zama zakiyi cikin d’akin ba am hungry kifito ki dafa min dinner, kinji?”
     “Naji” tace chan k’asa k’asa. Seda ta tabbata yabar wajen ta bud’o k’ofar tashigo da akwatunan nata tare da ajiyesu wajen ‘yan uwansu. Hijabin jikinta tacire had’e da kayan ta, sannan ta ciro wani silky white fitted doguwar riga me spaghetti hands tasa tare da sake maida hijabin nata. Anan ne ta fito, seda ta tabbata ta rufe kusan rabin fuskarta da hulan hijabin nata sannan ta fara neman hanyan kitchen se addu’a take Allah sa kar su had’u da Anas aiko tana leqa parlour ta gansa zaune kan one seater, vest ne da shorts a jikinsa kad’ai yayi cross legging k’afa. Kafin ta koma baya yaganta “come back” ya fad’i a lokacin da yake ajiye newspaper’n hannunsa a kan side table. Numfashi ta saki sannan ta tako parlourn idanunta matse gam.

        “Gyara hijabin naki.” Banza dashi tayi, “don’t let me repeat myself.” A hankali ta miyar baya idanunta na a k’asa har yanzu. “Good, so me zaki dafa mana.”
       “Nima bansani, tell me what you want.”
       “Just cook anything yummy good. I hope kin iya girki banason jagwal-gwale.” lallai ma tace a ranta. “Yes...? Kin iya?” Kai kawai ta gyad’a masa seda ta juya ta soma tafiya yasake kiran sunan ta kamar wacce zatayi kuka ta juyo.
      “Cire hijabin, ko bakisan ba’a shiga kitchen da hijabi ba? Ba fata ba what if mistakenly hijabin naki yakama da wuta fah? Kicire.” Ba k’arya a maganansa dankuwa ko Mami ta hanata shiga kitchen da hijabi hannu tasa zata cire sekuma ta tuna kayan dake jikinta ai seta miyar da hannun nata baya.
       “Cire hijabin ne baki iya ba?”
      “Na iya excuse me inje d’aki incire.” nan ta juya.
      “Not excused, dawo kicire anan Fannah banason surutu.”
      “But Anas-”
    “But Anas what?” Ya katse ta. “Mene a jikin naki ban gani ba” se yad’an tsaya ya murmusa, baki ta murgud’a masa ganin bai kallonta. The moment ya sake d’ago idanunsa ya aza akanta kuwa seta kawar da kanta “just take it off before I lose my temper.”
      “Anas ai zan cire amman ka bari inje d’aki mana ko anan zan ajiye?”
     “Eh anan zaki cire kuma ki ajiye, I’m hungry kina b’ata min kokaci.” Zata sake magana ya daka mata tsawa “Now!!” Bata san seda ta cire ba se b’ari take. Mak’ale hijabin tayi a k’irjinta da hannayenta bibbiyu akai se kallon gefe da gefe take tana b’ari.

Wai ita da ace atamfa ne a jikinta da barata damu ba amman wannan shegen kayan datasa dan shan iskan ne ke damunta.
     “Oya ajiye ki bani waje.” Fuska ta maraice “Anas kayan jikin nawa ne... Erm... Erm...” Yi yayi kamar ze nufi wajenta atake ta ajiye hijabin kan kujera. Murmushi ya saki tare da sake daidaita zamansa cikin kujeran. Kallo ya k’are mata up-to-down anan ne ya gano dalilin da batason cire hijabin.

        Hannu tasa ta soma kare k’irjinta ganin haka ya mata nuni da hannu da nufin ta basa waje “go am not interested” yace da ita chan k’asa k’asa kuwa ba abinda yakeso kaman kallon jikin Fannah. Juyawa tayi ta soma tafiya. Bin bayan ta yake da kallo yana murmusawa abinsa. Se anan ta tuna kayan jikinta silky ne showing komai yake gashi batasa underwear skirt ta ciki ba, kayan nata ta soma ja tana kare bayanta, ahaka harta fice daga ganinsa. Murmushi kawai yake, leb’b’an k’asan sa ya cize tare da d’ago newspaper’n dan cigaba da karantawa sede sam yakasa dena tunanin Fannah.

    _50 minutes later..._
 
           Rik’e Fannah ke da wani had’ad’d’en food warmer a hannunta ta lab’e jikin k’ofar kitchen d’in tarasa ya zata k’ariso gaban dining table ta ajiye, ganin ba Ubangiji se Allah kawai tasa kai ta ajiye idanun Anas na akanta. Bayan ‘yan mintuna ta gama jera kan dining d’in tare da d’iba macaroni da co-slow data girka musu a plate nata. Parlour’n ta k’ariso har a yanzu Anas bebar kallonta ba ignoring nasa kawai tayi. Seda ta d’aga hijabinta da d’ayan hannun ta tace, “dinner is ready.” Daidai ta juya kenan Anas yayi tsalle daga kan kujerar dayake zaune akai se gabanta har tsorata tayi. Plate na hannuntan ya soma amsa, “Anas my plate gachan naka a flask a dining.”
      “I know” yace da ita tare da amshe hijabin d’ayan hannun nata ya miyar kan kujerar. “Anas hijabi na.” ganin ta mik’a hannu zata d’aga yayi saurin d’agawa yayi wulli dashi achan k’asa yayi decending. Kafin tayi magana ya rik’o hannunta har gaban dining table ya jata.

      D’aya daga cikin kujerun yaja mata kallonsa ta tsaya yi. Abincin ya ajiye a gabanta sannan yace, “sit.”
      “But-”
     “Anan zakici so sit banason surutu.” Badan tanaso ba ta zauna yaja mata kujerar ciki. Opposite da ita ya zauna shima. “Serve me.” Kai ta d’ago tana kallonsa lallai ma Anas, ayi masa girki akawo masa, zubawa ma yace se anyi masa? Sauran chi ma kace ni zanbaka. Katse mata tunani yayi “well? I’m hungry.”
       “Toh Anas barin d’auko hijabi na please.”
      “Fannah I like you this way, the only time zakisa hijabi is in zamu fita ko munyi bak’i but in ni da ke ne banaso, kinji?”
     “Naji amma-”
      “Chapter closed” ya katse ta. “Now serve me dinner.” Mik’ewa tayi duk she is feeling uncomfortable ta bud’e flask d’in ta zuba masa abincin da co-slow se binta da kallo yake adaidai gabansa ta ajiye tare da tsiyaye masa exoctic juice cikin cup sannan ta koma ta zauna. Spoon d’aya yakai ciki har ya bud’e baki ze fara mata masifa seyaji girkin yayi dad’i komai is perfect, be tab’a cin macaronin daya mai dad’i kamar wannan ba no offense amman Fannah tama fi Ummie iya girki. Wasu biyun ya k’ara kaiwa cikinsa itade Fannah kallonsa kawai take. “Anas bakace komai ba” ta fad’a kanta a sunkuye.
    
      “Me kikeson inche? Maggi yayi yawa kokuma gishiri?” Gira ta had’e takai spoon d’aya baki itama sekuma taji komai yafita daidai. “Amman Anas ba abinda yayi yawa fa, zak’in is okay.”
     “Toh ni bemin dad’i ba, ahaka ne kin iya girkin? Dan de inajin yunwa ne kawai zanchi mschw!” yaja ‘yar k’aramar tsuka. Haka yata loda abincin ita de Fannah na ta ido ne. Mutumin dayace abinci beyi dad’i ba amman yafita chi. Bayan daya k’are plate nasa ya sake dad’awa. Baki tabud’e sosai tana kallonsa.
      “I thought kace beyi dad’i ba kuma nga harda k’ari kayi.”
      “Nayi ina ruwanki? Yunwa nakeji is not as if kin iya girki.” Murmushi kad’an ta saki danko tasan he don’t mean what he said. Bayan da suka gama chi ta kimtsa wajen. Sallan isha ya jasu.

Bayan nan takoma d’aki tasoma tsefe kitson da Afrah ta mata last 2 weeks. Guda uku kacal tayi tasoma jin tsoron zama a d’akin ita kad’ai, ina ma ace gidan da hayaniya amman sekace mak’abarta shiru. Fitowa parlour tayi ta tsinci Anas zaune kan kujera yana kallon football. Kamar ance Anas juyo ya juya idanunsa basu sauk’a a ko ina ba sekan Fannah dake tsaye da kayan jikinta na d’azu. Kai ta kawar ta tako a hankali ta zauna kan d’aya daga cikin kujerun ta cigaba da tsifarta. Bayan daya k’are mata kallo ya miyar da kallonsa kan TV’n lokaci zuwa lokaci yake satan kallon Fannah, da ta tsefe biyu se ta tsaya taja hannunta normally agida daman ko Mami ko Afrah ke taya ta, dama dama ache kalaba ne takan iyawa da kanta. “Come let me help you” yace da ita. Kai ta d’ago cike da mamaki tana kallonsa. “Eh?” Ta tambayesa fuskarta cike da neman k’arin bayani.

Hannu ya nuna mata “come.”
“Erm Anas don’t worry thanks zan iya da kaija.”
“Baraki iya ba wannan uban gashin kin just come.” Tunanin taje ko a’a karta je take ganin haka ya taso daga mazauninsa ya dawo kan kujerarta. Baya ta matsa da wuri sede kafin tayi hakan ya cafko hannunta tare da karb’e kibiyan. Ta bud’e baki zatayi magana ya kwantar da kanta kan cinyarsa. Wani irin baqon yanayi ta tsinci kanta ciki. “Anas zan zauna a k’asa kar cinyoyonka su maka tsami.”
“Dake ance miki rago ne ni ai.” Shiru tayi bata ce komai ba a hankali taji yasoma tsefe mata kitson. Sake jikinta tayi sannan tace, “thank you.” Yi yayi kamar be jita ba, ”Anas I said thank you.”
“No big deal.” Haka yata tsefe mata kitson har yayi rabi saura rabi wanda seta juya tana fuskantanshi ze iya tsefe mata. “Fannah turn around.” Shiru beji amsar taba. “Ke Fannah!” Fuskarta ya leqa yaga bacci ma take mekyau, lallai ma yace a ransa yana murmushi wato dan dad’in tsifar har tayi bacci. Juyo da ita yayi gabad’ai sannan ya cigaba da mata tsifan. Yanayi yana kallon fuskarta cikin baccin tace, “taya ka iya tsifa haka? Kafi Afrah ma iyawa.” Murmushi kad’an ya saki be amsata ba chan ta sake cewa “haka kitso ma ka iya, god bless you Mr. Fauzi.”

Dariya kad’an yasaki wanda ya k’ara masa kyau seda ya gama ya kama mata gashin gu d’aya tare da d’aga ta ya kaita d’akinta ya kwantar da ita ya rufeta da bargo sannan ya kashe wutar d’akin ya rufo mata k’ofar. D’akinsa ya nufa ya kwanta shima.

_2 hours later..._
Firgit Fannah ta tashi daga bacci around 11:30PM ganin ta soma mafarke mafarken nata, hamdala ta saki ganin mafarkin beyi nisa ba. Gefenta ta tab’a taji wayam ba Anas. “Anas!” Ta kira sunansa, a 360 ta janyo pillonta da bargo tabar d’akin. Ta bud’e nan ta bud’e chan har ta isa d’akin Anas gwada bud’ewa tayi taji a rufe. Knocking take bam-bam. Cikin bacci yace, “who is it?”
Hamdala ta saki jin muryarsa. “Anas please let me in Fannah ce.”
“Bakiyi bacci ba dama?”
“Anas dan Allah ka bud’e.” A kasalnce ya mik’e ya bud’e mata, kallonta ya tsaya yi “what now?”
“Anas mutumin” ta sanar dashi a kidime
“Muje in rakaki ki kwanta toh.” Kai ta kad’a “please lets sleep together.” Abinda yakeson ji kenan dama. “Kaifa kace d’azu ka yarda zamuna kwana tare.”
“Noo Fannah ba abinda nace ba kenan ce miki nayi naji I’ll think about it.”
“Eh toh ni whatever please let me in.” Kafad’a ya buga mata. “Anas please...” Ta maraice fuska tana k’ok’arin k’irk’iro hawaye. “Okay naji shigo” ya matsa mata. Cike da murna tashiga kan gadonsa ta haye.

“No! No! No! No way sauk’a min akan gado, ke baki iya bak’wanta bane? Kin wani zo kin hayemin kan gado, off my bed.” Cike da kunya ta sauk’o tana tattara pillonta da bargo. “Kin manta me kikace d’azu? Cemin kikayi ko a k’asa ne zaki kwana ko ba haka ba?”
“Eh Anas but-” nan ya katse ta ta hanyan aza yatsansa bisa lips nasa. “Shh! so a k’asan zaki kwana.”
“Ayyah Anas mana...”
“Oya zo ki koma d’akin ki.” Da wurwuri tace, “a’a na yarda zan kwanta a k’asan.”
“Good” yace yana murmusawa. Wani babban bargo ya ciro ya mik’a mata “gashi shimfid’a achan” yamata nuni da hannu “ki kwanta in kin gama ki kashe min wuta” yana kaiwa nan ya haye gado. D’agawa tayi ta shimfid’a kusa da gefen gadonsa dan tsoro. A hankali ya bud’e idansa daya rufe “Fannah bafa anan nace ba, achan” ya sake nuna mata da hannu. “Anas I know please let me sleep here chan d’in ina tsoro.”
“Whatever” ya miyar mata. Bayan data gama komai ta kashe wuta ta dawo ta kwanta har a yanzun tsoro takeji, be isheta ba seda tajawo kad’an daga bargon da Anas ya ruhu dashi ta rik’e se b’ari take ta kasa komawa bacci. Shima kasa baccin yayi hankalinsa duk na a wajenta.
“Fannah” ya kira sunanta a hankali.


*beeenovels.blogspot.co.ke*
*© MIEMIEBEE*
*beeenovels.blogspot.co.ke*
[12:57, 12/18/2016] ‪+234 903 612 6826‬: •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫

❣🎀❣🎀❣

*_written by miemiebee👄_*

In dedication to *Aunty Sis💕*
6⃣4⃣





   Cikin murya me rawa cike da tsoro ta amasa , “na’am.”
      “Are you still afraid?” Kai ta gyad’a wane yana kallonta jin shiru ya juyo ya kalleta, ganin hannunta rik’e da blanket nasa ya tabbatar masa tsoro takeji har yanzu. “Come” yace da ita. Abinda take jira dama kenan ba tare da b’ata lokaci ba ta d’ago pillonta ta haye gadon daga chan k’arshe. Matso da pillow nasa yayi kusa da nata. “I’m here kinji?” Yace da ita a lokacin daya aza kanta bisa k’irjnsa. Kai ta gyad’a a hankali tare da zagaye hannunta kan cikinsa, yana shafa bayanta a hankali har tasamu ta koma bacci.

          _7:00AM_

            Yanzu take gama had’a dining table, jin shiru Anas be fito daga d’aki ba har yanzu yasa ta mik’e dan duba ko lafiya, tana bud’e k’ofar Anas na bud’e towel nasa dan gyarawa tun d’azu yak’i shiga wanka se a yanzu ya ke fitowa. Ido wuru-wuru Fannah ta zaro tare da sako baki in shock, sandarewa Anas yayi ya kasa rufe towel nasan. Daga bisani taja k’ofar ta rufe alokacin hankalinsa ya dawo jikinsa ya d’aure towel d’in gam bakamar yadda ya saba yiba sakwa-sakwa. “What just happened?” Ya tambayi kansa disbelievingly. “Did Fannah.... Did Fannah? Oh God! No!” Hannu yasa yana hargitsa gashin kansa tare da jan wani doooogon tsuka.
         Fannah data sandare har yanzu a bakin k’ofa ta rasa gane ma ko a duniya take ko lahira, kallon k’ofar take har a yanzu baki wangalau har d’igan miyau take. Daga bisani ta kad’a kanta “La ilahi! Ya Salam! Astaghfitullah, Astaghfirullah, Astaghfirullah...” Sede har yanzu bata bar tunanin abinda ta gani ba. “Ya Salam ina

Please Login or Register in order to submit comment