Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tuwon kuma ya tabbata yabata zuwa dare in bahaka zata dawo gobe tabata da kanta.

    Kafin Anas ya dawo gida Fannah tariga tayi bacci, wani sabon ruwa yasa mata kamar yadda Dr. Mansoor ya koya masa sannan ya rage kayan jikinsa ya haye gadon shima tare da aza kanta a k’irjinsa yana me shafa bayanta a hankali anan shima yasamu yayi bacci se Maghrib ya tashi yayi alwala ya tayata tayi itama sannan yajasu Sallah, jikin nata alhamdulillah tunda har tasamu tayi Sallah duka a tsaye.
   Tana manne a jikinsa jiki ba k’arfi tace, “Habeebi zansha black tea.” Kai ya girgiza mata “Flower kinga Mami tace kar inbarki kina shan tea zallah tace se in kinci tuwon d’azu inbarki kisha tea.”
     “Habeebi wallahi tuwon ba dad’i please ka had’amin tea.”
    “Mom Hanan I know” yayi pecking goshinta “kinason Hanan koba haka ba?” Kai ta gyad’a “good then eat well se Hanan namu tafito healthy, kinji Mom Hanan?” Shiru tayi bata ce komai. “Yawwa Mom Hanan tashi inje in d’ebo miki toh.”
    Koda ya kawo abincin k’inci tayi da k’yar cike da dabara yasata ta soma ci har ya gama bata bata harar ba anan ne ya had’o mata black tea ya bata. Bayan sun idda Isha yasa mata last drip nata suka kwanta.

      Washegari ma da zazzab’i ta tashi sede ba kaman na jiya ba nayau da d’a  sauk’i, kamar yadda Mami ta buk’acesa ya mata reheating tuwon jiyan yau harda ‘yar kukanta dak’yar yasamu taci sam batason ci gashi kuwa shi kad’ai ne in taci bata hararwa bayan shi duk wani abinda takai baki seta fito dashi waje. Da rana Mami ta turo Afrah da miyan ayayo da d’anyen kub’ewa duka a had’e. Fannah kamar ta k’urma ihu shikansa Anas dayake bata amai abincin ke sasa amma haka ze dage yabata.
   
  ★★★
    Mami bata fasa kawo wa Fannah miyar gargajiya ba, acikin ikon Allah Fannah ta fara samu sauk’i in two weeks time tadawo old self nata sede sometimes da take tashi da morning sickness, jiri dakuma k’warnafi bayan nan bawani ciwo again. Babynsu da suka bata ko shi suna Hanan kuwa nan cikin k’oshin lafiya.
     Yau ranar ta kasance Sunday Fannah na zaune akan dining table ba abinda babu shi agabanta inde kayan k’walama ne sauran ma ba iya cinsu ta iya ba amman tasa Anas ya siya mata ta tab’a wannan ta tab’a wancan ayayinda Anas ke a parlour se famana latsa wayansa yake da alama abu very important yake dan yadda yayi focussing akai. Chan data gaji da ciye ciyen nata ta tattara ragowar tasa cikin leda sanna ta miqe, sanye take da baggi T shirt da befi tsakiyan cinyarta a tsayi ba da hannunsa d’aya an jefar, gashinta kuwa takamasa gud’aya chan a saman kanta, zare zaren ragowan da basu samu shiga packing d’inba na akan fuskarta kasancewar sakwa-sakwa tayi packing d’in. Parlourn ta iso ta baje kan cinyansa ko uffan bece mata ba se harkar gabansa yake.
   “Habeebi” ta kira sunansa tana kallonsa.
   “Uhm Mom Hanan what is it? Har kingama shanye duk tarukuchan dake kan table d’inne?”
     “A’a.” Ta basa takaicaccen amsa.
   “Toh me kikeso?” Har a yanzu be d’ago kai ya kalleta ba hakan ya d’an b’ata mata rai. “Habeebi wai me kake haka da ko kallona baraka d’ago wannan blue eyes nakan barakayi ka kalleni ba.” Seda ya sake latsa wayan na kusan seconds talatin sannan ya d’ago blue eyes nasa “yes Baby machine me zan miki?”
   “Bansani ba seda ka gama replying nata kasan ina a raye ka cigaba da abinda kake” kafin tace zata tashi ya zagaye hannayensa a ‘yar kunkuminta ya dakatar da ita.

     “Wani irin magana kuma kike Flower? Yanzu har kina tsammanin akwai macen da zata iya snatching maki ni a duniya? (ko Fans albarka😜) i’m not replying any gurl kiduba wayana kigani.”
   “Eh daka yi deleting chat d’inba ai nasan baka sonmu da Hanan yanzu.”
    “Flower wai mena miki yaune kam? Naga alaman ba abinda ke miki dad’i kamar kiga kin k’untatamin, niko meh kikamin it will never change the love I have for you” daidai zeyi kissing nata kenan tasa hannu ta riqo lips nasa “kad’au yau ma wannan magic kiss nakan zeyi tasiri akaina neh? Toh bareyi ba sakeni nikam.” Sake matso da ita jikinsa yayi “tell me Mom Hanan why are you mad?”
     “Aww ma tambayana kake koh? Bayan tun d’azu kake ta danne dannen ka a wayanka baka damu ko *_INA TARE DA KAI_* ko bana *_TARE DA KAI_* ba, your phone is more important than me.”
    “Inji waye Mom Hanan? Kinason kisan me nakeyi a wayan neh?”
    “Banaso ai na riga na san-” bata k’are maganan ba yayi shutting nata dawani hot kiss sam tak’i basa had’inkai a farko dan tasan sa sarai he is such a bad kisser nan danan zesa ta mance da dukkannin problems nata ta yafe masa ba tare da tasan tayi hakan ba, sam yak’i sake ta, ya d’au alwashin se ya kashe mata jiki liqis tukuna, yana meh bin duk wani saqo a jikinta da hannayensa yana meh mata sending electric sparks. Ai duk yadda tayi dan k’in basa had’in kai ta kasa daga k’arshe seda tayi giving in wa kiss nasa, ta sa hannayenta duka cikin gashin kansa pulling him closer, se kissing juna suke so deeply, sun d’au tsawon lokaci suna abu d’aya sannan da hanzari suka hau romacing junansu ganin abin bana tsayawa bane na bugo legediz benz d’ina na rufo musu k’ofar parlourn harda cin tuntub’e na.

   ****_An hour later..._
     “Nikam kabar kallo na da wannan mayun blue eyes naka haka bad boy kawai.” Fannah tayi maganar tana mayar da T-shirt nata jiki. Anas kuwa na a kishingid’e jikin 3 seater da nickers zallah a jikinsa, ya yi crossing arms nasa a kan chest da wani killer smile a fuskarsa yana mata wani mayen kallo next abinda yaji shine shirt nasa da Fannah ta wurga masa a fuska, hannu yasa ya cire har a yanzu bebar murmushin ba. “Flower menayi kike cemin bad boy?”
    “Ai kafi kowa sani” daidai tazo wucewa ta gefensa kenan yajata ta fad’a jikinsa ya saketa sam yak’i.
    “Bansani ba tell me” yayi maganar numfashinsu na had’ewa dan yadda fuskokinsu ke kusa kusa.
    “Gashi kuwa I can’t resist you koda nace barin baka had’in kai ba at last senayi because you got it all Abu Hanan.” Pecking nata yayi a kumatu “so do you Mom Hanan.” Kanta tayi adjusting a jikinsa sannan tace, “Habeebi meh kakeyi amman d’azu a wayan?”
     “Baby Mamah bakiyi trusting d’ina bane?”
   “Nayi mana Habeebi kawai ina son sani ne.”
   “Okay kinsan yau Baba yacika 1 year 10 months da rasuwa koh?”
    “Ya Salam! Habeebi wallahi na mance I’m so sorry kaji?”
    “Is okay nasan bada gangan kika manta ba, ban tab’a fad’a miki bane saboda aikin lada ba’a son ana yad’awa, so kowani 2-2 months nake sa akai kud’i da kaya gidan marayu in memory of Baba.”

     “Owww! Kayi tunani me kyau Habeebi, Allah tura masa ladan kabarinsa kaikuma Allah cigaba da bud’i dakuma kare mana kai, Hanan and I love you so much.” Tayi pecking  nasa shima a kumatu.****

     _3 weeks later..._
Daidai cikin Fannah nada 8weeks (2 months) kenan alhamdulillah jikinta da sauk’i sosai. Yau ranar ta kasance Monday as early as possible k’arfe 4:30AM Anas ya tashi shikad’ansa yahau shirya musu akwatinsu shida Fannah, suprise yakeson mata. Duk wani abinda zasu buk’ata be bari a baya ba seda yagama had’a komai sannan ya d’au ‘yar k’aramar hand luggage ya cika da kayan wasa da teddies na Baby Hanan kafin Asubah yagama had’a komai ya ajiye boxes d’in a parlour yadda Fannah barata gani ba.

****
Fitowan Fannah daga bayi kenan tayi alwala, ta d’au hanyan wardrobe nasu dan ciro hijabinta Anas yayi sauri ya dakatar da ita “Mom Hanan wait hijabi kike nema koh?” Kai ta gyad’a masa. “Good gashi.”
“Thanks amman banason wannan yanada nauyi nafison d’ayan barin d’auko yana cikin wardrobe d’in ai.” Gabanta yasha sabida kuwa duk hijabanta masu laushi yasa su cikin akwatin bayason ta bud’e wardrobe d’in tayi ruining suprise daya tanadar.
“Habeebi wai me haka? Muna chin lokaci fah, kamatsa in d’auko hijabi na muyi Sallah.”
“Ga wannan kisa.” Ya miqa mata k’in amsa tayi “banason wannan yanada nauyi.”
“Toh nikuma nace kisa wannan.”
Haba manah! Habeebi so kake in jik’e kafin mu idar da Sallan ne?”

“Flower ai sanyi ake karb’i kisa mana.” Kafad’a ta buga “ni banaji, matsa min.” AC’n d’akin ya k’ure “kinji sanyi ake karb’a kisa.” Seda ta galla masa harara sannan ta amsa tasa bayan da suka idar da Sallan ta nad’e hijabin as always zata miyar cikin wardrobe d’in, takai hannunta kan handle d’in kafin ta bud’e Anas ya dakatar da ita ta hanyan sa hannunsa akai seda ta firgita. K’irji ta dafe “Habeebi kasan ka ban tsoro please kadaina what if wani abu yasamu Hanan fah?”
“I’m sorry in shaa Allah ma ba abinda ze sameta kawo in ajiye miki jeki kwanta.” Kallonsa tayi na ‘yan lokuta. “Habeebi wallahi you are hiding something from me, meh abun? Kuma mesa bakason in bud’e wardrobe d’in dakaina?”

“Saboda Dr. Yace in hanaki yin any form of labour kuma ai bud’e wardrobe ma aiki ne, prince charming naki ze miki jeki kwanta.” Har a yanzu bata yarda ba. “Sekuma meh? There is still something you are not telling me.”
“Oh! Mom Hanan kin cika bincike sekace wani spy” Turata gefe yayi ya sa hijabin sannan yaja hannunta suka koma suka kwanta. Daman tun jiya ya sanar da ita bareje office ba yau dan haka tasamu takwanta peacefully.

_8:07AM_



*© MIEMIEBEE*

beeenovels.blogspot.co.ke
[12:59, 12/18/2016] ‪+234 903 612 6826‬: •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫

❣🎀❣🎀❣

*_written by miemiebee👄_*

In dedication to *Aunty Sis💕*

8⃣9⃣






Daidai tashiwan Anas daga bacci kenan, da k’yar ya iya ya raba jikin Fannah da nasa dan wani sabon salon baccin da ta koya bata bacci se in akansa. Bayan ya tura ta gefe yasake lullub’eta da bargo sannan yayi pecking nata a goshi. Bayi ya nufa yayi wanka agurguje yasa mint blue shirt da farin ¾ wando. Kitchen ya nufa yasoma had’a musu Chocolate-chip cookies for breakfast, in less than an hour yagama komai se coffee daya had’a musu, dining table ya shirya tsab sannan ya koma d’aki dan tayar da ita, zaune ya tarar da ita se murza idanunta take. “Good morning Flower har kin tash-” besamu daman k’arisa maganan ba dan yanayin daya tsince ta ciki kamar kuka take, daya gama k’arisowa kusa da ita kuwa seya tabbatar da hakan zama yayi a gefenta.
   Cike da tashin hankali yake maganar. “Omg! Flower why are you crying?” Kasa amsa shi tayi kawai tayi hugging nasa a yayinda kukanta ya tsananta. Bayanta yake bubbugawa a hankali, “shhh! Kibar kuka kinji I’m here stop crying Flower” seda ya tabbata tayi shiru ya d’agota. “Meya faru?”
    “Habeebi promise me baraka tab’a barina ba, promise me please.” Ta sake matsesa ajikinta tana meh cigaba da kuka.
    “Shhh! I will never leave you Fannah, never ki kwantar da hankalinki *_INA TARE DA KE_* forever.” Hannu yasa ya share mata hawayen ”meya kawo wannan zance? Kinyi mafarki ne?” Kai ta gyad’a masa. “You want to talk about it?” Nan kuma ta kad’a mai kai “I’m afraid Habeebi.”
    “Toh shikenan is okay, tashi kiyi wanka yanzu.” Ba musu ta miqe ta amshi towel dayake miqa mata bayan ta cire kayan jikinta ta d’aura towel d’in “Habeebi ka rakani bathroom d’in wallahi tsoro nake wai Ya Farouq na ciki.”
     “Mafarkin Farouq kikayi dama?” Cike da tsoro ta gyad’a kai. “Karki damu Farouq is gone foever.”
   “Nasani Habeebi still ina tsoro ka rakani please” hannunta ya riqe yakaita har bathroom d’in tabarsa yafito tak’i labule taja ta tare kanta shiko yana zaune akan hand basin bayan data gama suka fito tare man shafawanta ta nema kap kan mirron babu. “Habeebi kaga lotion d’ina?” Se ayanzu ya tuna ya had’a cikin akwati d’azu. “Bangani ba Flower, babu akan mirron?” yayi qarya.
   “Babu” tayi maganar tana nufan wardrobe dan ciro sabo.
   “Wait wait!” yayi sauri ya dakatar da ita, “babu achan ga vaseline chan ki shafa.”
  “Habeebi wai me kake b’oyewa cikin wardrobe d’innan ne?”
   “Kan Farouq ne aciki kika kuskura kik-” be samu daman k’arisa maganan ba sanadiyar tsallen da Fannah ta daka se a jikinsa ta tsaya chak! hannu yasa ya tare ta kafin ta fad’i. “Na tuba wallahi barin bud’e ba, dan Allah kabari ina vaseline d’in zan shafa.” Dariya sosai ya tsaya yi “toh muje mu shafa miki amman sauk’a tukuna.” ya gwada cire hannyenta dake rataye a wuyansa, kafad’a ta buga nufin barata sauk’a ba tare da sake kankamesa, haka tana zaune kan cinyarsa ta shafa manta. Kayan ta daya cire mata wani baqin abaya ya miqa mata, “gashi sa.”

     “Habeebi abaya nefah.”
   “Ina sane ai” ya gyad’a mata kai.
   “Toh ina zamuje da zan sa abaya?”
  “Ikon Allah! Mom Hanan ko d’an bincike seya baki hanya wani irin bincike ne haka?! Allah kika sake questioning d’ina zan bud’e wardrobe d’in Farouq yafito.”
   “Nabari nabari please kabar fad’in sunansa Hanan zatayi kuka.”
   “Toh Mom Hanan na dena” yayi managar hannunsa na akan cikinta. “Flower yaushe Hanan zata soma motsi I want to feel her.”
    “Dr tace se pregnancy’n yakai zuwa 16 weeks and Hanan is just 8 weeks yanzu kaga da saura.”
    “Ohh kice min se cikin ki yayi k’aaaatoo Hanan zata fara motsi.” Hannunsa ta d’aga daga kan cikin nata “nifa na fad’a maka bawai wasan nan na sani dariya bane banaso.”
    “Toh I’m sorry yi sauri kisa kayanki.”
  “In nasa ina zam-” bata k’arisa maganan ba tayi tsit dan ta tuna da abinda Anas yace mata akan ta sake masa tambaya ze ciro kan Ya Farouq cikin wardrobe. Kamar baby ya riqota a hannu zuwa dining table yasan ta da kewaye kewaye kar idanunta sukai kan akwatinan nasu.

    “Habeebi harda breakfast kamana yau wow!” Yana bud’e flask d’in k’amshin abincin ya mamaye wajen gabad’aya se shaqa Fannah ke tana d’igan miyau. “Baby hurry up and serve me yunwa nakeji.”
   “Kwad’ayi kike ji de.” K’aramar tsuka taja ta bugesa gefe ta amshi flask d’in taja gabanta ta soma chi. Tsayuwa yayi yana kallon ta cike da mamaki ganin takusa cinyewa ba shi yayi magana “Flower nifa ban chiba karki cinye duka.”
    “Ayyah Habeebi, Hanan kuma fah? Kayi hak’uri kabarmu mu cinye mana.”
    “Bawani Hanan d’innan glutton (meh shegen cin abinci) kawai.”
   “Kafad’i koma meh mu cinye?” Kai ya gyad’a mata yana murmushi yadda takecin abinci na bala’in kashesa. Bayan da ta gama yaje yayi frying sausages ya karya dashi shima. Bayan da suka gama ya tattara dining table d’in “Flower jekisa mayafin abayan naki we are going somewhere.”
   
     “Ina kenan Habeebi?”
   “Aww! inje inciro kan Farouq ko?”
   “A’a please nayi shiru.”
  “Better jeki shirya ina jiranki and karki bud’e wardrobe d’in ni na fad’a miki.”
   “Toh Habeebi kazo muje tare wallahi tsoro nakeji” seda yayi ta mata tsiya sannan ya rakata yana ganinta tana shiryawa har tagama tayi arabian rolling mekyau me amsarta sannan ta feffesehe da turare d’ayan da kad’ai tagani kan mirron ta tambayi Anas ina sauran turarukanta kuma tana tsoron kar yaciro kan Farouq daga cikin wardrobe. “Kingama?” Ya k’are maganar hannunsa k’ark’ashin hab’anta yana kallon fuskarta datasha light makeup.
    “Eh nagama semeh kuma yanzu?”
  “Se...” Yakai bakinsa kan nata “Habeeb-” be sake mata baki ba seda ya tand’e maroon strawberry flavor jan bakin data shafa tas.
    “Haba! Habeebi” tayi maganar lokacin da ta juyo tana kallon bakin nata a mirror. “Mena sharemin jan bakin yanzu?” Tayi pouting lips nata.
   “Saboda yamiki kyau sosai and banason in mun fita mutane suna kalla min ke, because you are mine Flower, as from today banason ki sake yin makeup in zamu fita okay?”
   “Nikam wannan Habeebin” tayi maganar chan k’asa k’asa tana zumbure zumbure.
   “Yes Flower kajol da nude lipstick kawai na yarda kina sawa kinji?” Shiruu “nace kinji?”
   “Naji-” katsesa yayi “good, agida kawai na yarda kina kwalya.”
   “Habeebi gaskia akwai ka da son kai amma kaika iya d’aukan wanka kamar me zuwa gidan biki idan zaka fita.”
    “Toh mijinki neni ai” be jira ta sake magana ba yajata waje zuwa mota sannan ya dawo ya kai boxes nasu mota dake se game nata take ta  bugawa ko kad’an bata ga me yake ba seda ya shigo mota ya tambayeta “Mom Hanan are you ready?”
   “Do I have a choice bayan baka sanar dani ina zaka kaini ba.”
   “Karki damu you’ll find out soon.” Seda ta bari sukayi nisa da tafiya ta yadda barasu iya komawa gida ba, balle yace ze ciro kan Farouq tasoma jero masa tambayoyi wanda duk ciki ba wanda ya bata straight answer.

     Wani tambayan ma seda ta ga sun dosa hanyan airport “Habeebi wai me zamuyi anan?†
    “Flower inda zaki d’an k’ara hak’uri everything will turn out cool.” Badan tanaso ba tayi shiru waje yanema yayi parking sannan ya fito da ita a yayinda wani security ya cicciro musu luggages nasu “Habeebi wannan fa akwatina ne a hannun mutumin nan” tayi maganar tana bin mutimin da kallo.
  “Yes ina sane Flower” ya jawota jikinsa.
   “Toh a ina ya samu?”
   “Acikin booth kayakin mune aciki.” Cike da mamaki da rashin yarda tsantsan mamaki ta d’ago kai tana kallonsa. “Kayan mu aciki? Kana nufin tafiya zamuyi?” Gira ya d’aga mata.
    “What?! Habeebi-” yatsansa ya aza a lips nata “shhhh! Nasan me zakice ban fad’a miki ba you are not ready barakije ba but please don’t say so kinji? Don’t ruin this I’ve worked hard for it.”

    Hugging nashi tayi abinda beyi tsammani ba a tunaninsa she will freak out tace masa barata jeba. Cikin sauti cike da jin dad’i tayi maganar, “Taya zance barinje ba Habeebi bayan nasan you worked hard for it I just hope we will enjoy inda zaka kaimu. Me, you and our Hanan Habeebi.” Dad’in kalamunta yaji sosai yayi hugging nata back “we will in shaa Allah Flower, I love you dearly.” Bayan tayi breaking hug d’in ta ciro wayarta daga jakarta “me zakiyi Mom Hanan?”
   “Zan kira Mami in sanar da ita.” Wayar ya amsa “don’t worry na riga na sanar da ita lets just go, hope you are ready to go fly to Abuja?”
   “Abuja? Okay I am ready.” Wajen private jet nasa wanda be tab’a tafiya dashi ba yau ne karo na farko suka nufa se admiring jirgin Fannah ke bata tab’a ganin kalan jirgin ba se a TV.
    “Habeebi mu kad’ai zamuyi tafiyan ne?”
    “Yes Flower this is my private jet ba public jirgi bane.”
   “Ohhh wow! Its amazing baka tab’a fad’a min ba.”
   “Sorry nima ban tab’a using nashi ba seyau tun kafin muyi aure na saya I mean tun lokacin dana fara sonki Flower I was hoping Allah ze kawo min ranan da zan shiga ciki dake that is when we’ve accept each others love just as we did a very long time ago now, I love you Flower” Kyakkyawar fuskarsa ta shafa “I love you too Abu Hanan.” Hannunta ya riqe suka shiga ciki bayan angama komai da komai sauran tashiwar jirgi Fannah tasa suka karanto add’o’in kariya. Tun anan Anas yagano ta soma jin tsoro dan kuwa this is her first time shiga jirgi.

    Seatbelts Anas yamusu tighting aiko ta riqo hannunsa gagam “Habeebi na fasa tafiyan ina jin tsoro please su tsaya.” Dariya yakeson yi amman ya b’ata rai. “Flower just keep calm muna tashi everything will be normal.”
    “No Habeebi ni kawai kace musu su tsaya” a hankali jirgin ya fara tafiya bata wani ji tsoro ba seda jirgin ya fara tashi anan ta fara kuka harda hawaye hannunta Anas ya matse cikin nasa yana fad’a mata dad’ad’d’un kalamu ahaka har suka tashi da suka fara flying kuwa seta bar jin tsoron. A hankali ta bud’e idonta d’aya sannan d’ayan. “Kin dena jin tsoron?” Kai ta gyad’a a hankali “are we flying already?”
   “Yes Flower we are kiduba window kiga.”
   “A’a tsoro nakeji.”
   “Ki leqa ba abinda ze sameki am here.” Cike da tsoro ta leqa kad’an da wuri ta dawo da kanta ciki “calm down Mom Hanan ki kwanatar da hanakalinki ko kinason Hanan ma taji tsoro ne?” Kai ta kad’a masa “good” yace tare da pecking nata, headphone ya ciro yasamata akai tare da kunna mata qira’a. Cikin ‘yan mintuna suka iso Abuja nan ma da suka zo landing kad’an ya rage Fannah batayi kuka ba.

   Transcorp Hilton Hotel Abuja suka sauk’a zuwa Azahar bayan sunchi abinci sun sake wanka suka wuce embassy’n USA  kasancewar a New York Anas yakeson suyi rainon Baby Hanan. Dad’i sosai Fannah taji daya sanar da ita plans nasa, sun gaji iya gajiya wai haka ma dan da sanin ido kenan aka samu aka gama musu abubuwan on time zuwa jibi everything will be ready seya rage sauran tafiya. Koda suka dawo gida Fannah takasa fitowa daga mota dan gajiya Anas ne ya cirota da kansa yakaita har zuwa d’akinsu. Akan gado ya direta kafin ya juya ta riqo kolan rigarsa tajasa jikinta kafin yayi wani k’wararren motsi ta kifa bayansa da gadon ita kuma ta haye kansa. “Habeebi bacci nakeji.”
    “Flower bamuyi Sallan isha bafa.”
   “I know Habeebi mubari zuwa 10-11 haka se muyi please.” Shiru yayi tare da aza hannunsa kan bayanta yana shafawa a hankali. In the next 5 minites Fannah tayi bacci. “Flower!” ya kira ta shiru ba amsa.
    “Flower har kinyi bacci?”
   “Uhmm” tayi groaning cikin baccin. D’an murmushi ya saki tare da pecking kanta. A haka shima ya samu yayi bacci se 11:27PM Anas ya tashi anan sukayi Sallah suka chi abinci sannan suka watsa ruwa suka sake komawa bacci.

     Kwanan su biyu a Abuja Anas ya sama masu visa. Washegari around 8:00AM suka d’au flight zuwa New York kamar sabon shiga haka tata jin tsoro ma yau.

     _10 hours later... Exactly 6:00PM a Nigeria 1:00PM a kuma New York_
 
     Su Anas suka shigo NY gajiya kam ansha sosai, musamman Fannah kusan duk a kwance kan gadon dake jet d’in ta yini amman hakan be hana k’afafunta kumbura dam ba.
    A MANDERIAN ORIENTAL HOTEL NY suka sauk’a. Fannah de takasa b’oye k’auyancinta inwhich Anas found so adorable and cute komai tagani seta tambaya. Warming jikinsu sukayi cikin had’ad’d’en jacuzzin dake bathroom d’in sannan suka yi ordering abinci sukaci.

     Baccin sauk’e gajiya suka yini sunayi ranan da daddare bayan sun idar da Sallan isha sunci dinner Anas yahau massaging wa Fannah k’afafunta da suka kumbura bayan daya gama mata kuma suka kwanta.
     Washegari basu

Please Login or Register in order to submit comment