Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dashi dan Allah.”

“Fannah I can’t say no to him kawai kije ki rufa wa coffe shop namu asiri.” Zata sake magana ya fice juyowa tayi ta kalli Asma’u da take ta kau da kallonta elsewhere. Miyau ta had’iye sannan ta fice kaiwa Anas kujerun ta duba sannan can ta hangesa dukda bata ga fuskarsa ba amman daga farinsa ta ganesa. A hankali ta k’arisa kan table d’in ta ajiye a lokacin yana kan waya yana kallon window. Tana ajiyewa ta juya zata tafi holding wayar yayi “Boss naki be fad’a miki inasan miki magana bane?” Ya fad’i authoritatively ba tare da ya kalleta ba. Cak ta tsaya tare da kewayo wa...



*© miemiebee*

beeenovels.mywapblog.com
[12:47, 12/18/2016] ‪+234 903 612 6826‬: •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫

❣🎀❣🎀❣

*_written by miemiebee👄_*


1⃣9⃣   


 

Wayar da yakeyi ya cigaba da, tafi minti uku tsaye sannan yayi hanging, ba tare da ya kalleta ba ya d’au coffee’n ya kai baki be cire ba sanda ya kwankwad’e tas mamaki ne ya cika Fannah datayi mutuwan tsaye tana kallonsa cike da mamaki waiko d’umi d’umin coffeen ma baiji? “I will appreciate it in zaki bar kallo na haka kinemi waje ki zauna.” cewar Anas. Miyau ta had’iye wai shi ya yake gane mutum na kallonsa ne? A kunyace taja kujera ta zauna d’an nesa dashi har yanzu be d’ago kai sunsa juna a ido ba. Bayan ta zauna ya d’ago kyakkyawan fuskansa ya aza blue eyes nasa kan Fannah.

Idanunsu na had’uwa Fannah ta saki salati. “Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!” tare da dafe k’irjinta. Kallonta Anas yake cike da mamaki. Kallon cikin ido suke ma juna shide baya manta fuska yau ya soma sa Fannah cikin ido mesa take kallonsa kamar ta sansa? “Hey!” Ya fad’i da kallon ya ishesa. “Are you okay?”
Shiru har yanzu tayi tana kallonsa tana tuna ina ta tab’a kallonsa, wannan idanu tasan ta tab’a sata cikin idanunta amman takasa tuna a ina. Tayi tayi amman takasa. Table d’in ya buga firgit ta kyafta idanunta tadawo reality. “Aljani kika gani neh?” Ya tambayeta. Kai ta kad’a masa. “Better” ya fad'i relieved.
“So kece kike had’a wannan coffee?” Shiru tayi bata amsa ba se kallonsa take wanda har yafara feeling uncomfortable. “Please na kiraki nanne to give you an offer bawai ki tsaya kina kallo na ba, hold it after natafi you can admire me.”

Kut lalle ma wannan Anas, jijji dakai ya maka yawa, well kanada kyau amman ni ba kyanka nake kallo ba cewar Fannah a zuci. “Ba kallonka nake ba” ta fad’a tare da kawar da kanta daga ganinsa. “Allah sa you mean what you said just now. So ke kike making coffeen nan?”
Kai ta giad’a. “See Fannah kike koh?” Nanma kai ta giad’a.
“Damn it!” Ya buga table d’in a tsorace ta d’ago kai tana kallonsa. “I hate it in ina wa mutum magana yana using body signal, kimin magana as I do you, clear?” B’ari take ta giad’a kai take tace “eh.” “Good” yace sannan ya cigaba “maganan gaskia I like your coffee.”
“Thank you”+ tace a hankali.
“And inason ina sha kullum like safe rana yamma dare all the time.”
“Sir but coffee shop namu k’arfe shida muke rufewa kuma ni 2:00PM -3:30PM ship d’ina yake k’arewa.” Tafad’i tana kallonsa
“Exactly! sesa na taho miki da offer yau. And for the last time kidena kallo na will you?”
Kau da kanta tayi da alqawarin barata sake kallonsa ba so take ta tuna ina ta tab’a ganinsa sarai tasa wannan blue eyes nasan sede ta rasa a ina ta tab’a ganinsu.

“So kinsan ni waye ne ba sena fad’a miki ba Anas Ibrahim Fauzi CEO’n Flames Enterprises inason inyi offering naki better job a company na kina making min coffee 24/7 meaning duk lokacin da nakeson shan coffee I’ll give you a call and komin me kikeyi a lokacin zaki bari kizo ki had’a min abinda kawai zaki na min kenan and zanna biyanki ko wani k’arshen wata da salary me kyau. So what do you say?”

“Mr. Fauzi nagode da wannan dama but am sorry baran iya karb’a ba saboda as you can see ina da aiki a nan kuma am satisfied with it. In zakayi excusing d’ina zankoma aiki.” Tana k’ok’arin mik’ewa ya daka mata tsawa “sit! This should be the last time, ba’a dismissing d’ina sede inyi dismissing mutum clear?”
“I’m sorry” tace “now sit.” Ba gardama takoma ta zauna ita bata ga mesa zesa tama wannan arrogant mutumin aiki ba, ita tausayawa masu aiki k’ark’ashinsa ma take. Mutum kullum cikin tsawa da masifa ba dariya? Chabdi!
“Nawa ake biyanki anan? I mean whats your salary?” Tambayarsa ne ya dawo da ita daga duniyar nazarin data fad’a.

“Mr. Fauzi me zakayi da albashi na, naga kamar its personal.”
“Zaki fad’a min salary’n kine kokuma sena sa an rufe coffee shop nakun?”
Zaro ido tayi wai wannan wani irin mutum ne? “N10,000 (dubu goma) ne.”
D’an murmushi yayi baki rufe wanda kawai dimple nasa ne kad’ai ya lotsa. “N10,000 kad’ai salary’nki? Work for me I’ll pay you double.” Zaro ido tayi. “Ko ya kasa? N30,000 then.” K’ara ciro ido tayi waje “N40,000 toh.” Kai ta sosa “induk yakasa miki toh N100,000 inshima ya kasa tell me ko nawa kikeso I’ll pay you as long as zakina making min coffee.”

Mamaki ne yacika Fannah lallai wannan Anas baida matsala jibi yadda yake irga kud’i sekace dutse?
“So, you accept my offer?”
“Mr. Fauzi kayi hak’uri inasan aiki na anan dukda albashin bame yawa bane amman Allah nasa min albarka kuma i’m satiafied.”
“Oh common Fannah karki yaudari kanki dubu goma bare rik’e ki har na wata ba, dubu goman da ake kashewa in just a minute? accept my job ko nawa kikeso I’ll pay you.”
“Mr. Fauzi I’m sorry please, nagode zan tafi.”
“Kiyi tunani Fannah anytime kika canza mind naki you can call me” hannu yasa yaciro card nasa tare da ajiye mata kan table d’in. “Koda zaki kira karki kira around k’arfe 5:00PM to 8:00PM.” Be jira me zatace ba ya d’au jakarsa ya fice.

Hararan card nasan tayi, ta ja tsaki sannan ta d’aga ta karanta, phone numbers nasa biyu tagani kai. “Aiko nasha giyan wake barin kira ka ba, bana buk’atan dubu d’ari d’arin ka mschww” d’aga katin tayi da nufin yagawa karap Asma’u tasa hannu ta wabce. “Ke bani!” cewar Fannah.
“Nak’i barin bayar ba. Ke yanzu Fannah Mr. Fauzi gabad’aya yabaki card nasa shine kike k’ok’arin yagawa? Meya sa yabaki?”

“Oho! kiya tambayesa ni bakisan wani abu ba tsoro yake bani wannan da blue eyes nasa kuma kinsan wani abu? ji nake kamar na tab’a ganin sa awani waje kuma kamar yadda muka had’u bawai irin yamin mutunci bane kamar... Sharri” Tayi shiru tana kad’a kai “ya Allah a ina nasan wannan bawan naka?” Ta tambayi kanta.
“Kefa Fannah anyi mutum yanzu Mr Fauzin ne harzaki wani tambayi a ina kika sansa ko kika tab’a ganinsa? Abinda har office nasa kin tab’a zuwa aikunsha had’uwa.”

“A’a Asma’u duk had’uwar mu dashi bamu taba had’a ido dashi ba se yau kuma ayau d’in naji na tab’a had’uwa dashi wani wajen amman nakasa tunawa.”
“Kide tuna” cewar Asma’u. “Seki tashi lokacin tafiyar ki yayi.” A sanyaye Fannah ta mik’e, Asma’u tabi bayanta. “Ina jakarki Fannah?” Akoi wayata ciki in cire.
“Yana chan kan counter a kitchen please kifito min dashi” murmushi Asma’u tayi sannan tafice zuwa kitchen chan ta d’au jakar Fannah ta bud’e daman bawani wayarta ciki, card na Anas tasa cikin jakar cikin wata zip sannan ta rufe takai wa Fannah.

Isar Fannah gida keda wuya ta tarar da Afrah kad’ai a gida har su Mami sunkai Baba kenan ta fadi a zuciya. “Sannu da zuwa Ya Fannah ya haka kuma yau? Tun shigowarki kinyi shiru.” Bayan ta zauna kusa da Afrah tace, “wallahi Afrah wani abu ke damu na.”
“Wani abu kenan Ya Fannah?”
“Yau Mr Fauzi yazo coffee shop namu-”
Katse ta Afrah tayi “dan Allah!? Omg! Kunsamu kunyi magana? Wayyo Allah!”
Marinta Fannah tayi a hannu “da Allah kimin shiru. Kinaji ba?” Afrah ta giad’a kai Fannah ta cigaba; “I mean jiya ma yaje shagon namu to da yasha coffee na seyace wai yamasa dad’i yau ma yadawo na k’ara had’a masa.” Afrah zatayi magana Fannah ta katse ta “please kiyi shiru kiji ni.” “Ina kaiki, bayan na kai masa...”
Nan ta kwashe labarin komi tabawa Afrah sosai Afrah tasha mamakin erin sokancin da Fannah tayi. A yadda suke shan bak’ar talaucin nan ne har za’a bata aikin dubu d’ari tace battaso? Lallai kam.
“Afrah kinyi shiru.” Cewar Fannah

“Saboda kin ban mamaki ya Fannah at thesame time kuma kin ban haushi yanzu har a baki aikin dubbai kice bakiso? Seyau nasan bakisan Baba yasamu lafiya gaskia.”

“Afrah wace erin magana kike haka? Baki tsaya kinji dalilin dayasa nak’i aikinsan ba fah.”
“Toh ina jinki wani dalili ne haka?”
Hannunta Fannah ta rik’o. “Wallahi Anas baida mutunci kinfi kowa sanin yadda nake tsoron masifa da tsawa banasan amin masifa shiko Anas ba aikinsa se ma mutum masifa wallahi ko yau danne zuciyata nayi banyi kuka ba daya daka min tsawa. Bayan haka kuma kinga ai bareyi inbar aiki haka kawai da su Ya Suleiman ba, bareji dad’i ba mun saba najima ina aiki dasu kawai dan an bani aiki me kyau se na mance dasu? Na kyauta kenan?”

“Haba Ya Fannah mesa masu aiki suke barin gun aikinsu in sun samu me kyau? shi kansa Ya Suleiman inhar yana sanki murna ze miki dan wannan promotion. Dan Allah Ya Fannah ki karb’i wannan aiki, for once a rayuwarmu muma muji dad’in da akeji, Baba yasamu lafiya.”

Kad’a kai Fannah tayi “Afrah niba wannan bama. Afrah inada wrong idea da feeling akan Mr. Fauzi yau na soma sasa a idanu na amman kuma ji nake kamar natab’a ganinsa wani waje kuma kamar had’uwan mu sharri ne, Afrah bansan meke damuna ba.”

“Lallai! Ya Fannah ai dama kin sha kallonsa mana, ko kin manta shi kikaje office nasa ranan?”
“A’a Afrah believe me wallahi duk had‘uwar mu dashi bamu tab’a had’a ido hud’u dashi ba.”
“Toh in banda abinki ranan ai na nuna miki shi a TV.” Shiru Fannah tayi tana nazarin abu..
“Kuma fa haka ranan kin nuna min shi a TV lokacin da Babansa ya rasu” zata k’ara magana sekuma tayi shiru “amman fa kaman bangansa ba ma ranan na tuna bangansa ba”

“A’a Ya Fannah kituna dakyau kin gansa koda kad’an ne, kinsan dama wani sa’in ai haka ne sekaga kamar baka ga mutum ba amman ka gansa next in kuka had’u kuma seka ta wondering ina kuka tab’a had’uwa. In bahaka ba ina ke ina had’uwa da Anas d’an billonaire ko kin manta a ture can London yayi rayuwarsa. Bansani ba ko kema kinje London d’in a mafarki” Afrah ta fad’a taja dariya.

Maketa Fannah tayi “LOL kuma fa kinyi gaskia nakega hakan ne a TV na gansa ranan in bahaka ba kam ina zan had’u da mutum kan Anas.”
“Yawwa ‘yar garin so yanzu zaki karb’i aikin?”
“Eh” tama Afrah k’arya dan kar taji haushinta amman kam har cikin ranta bata san amsar aikin, kuma bataga abinda ze sa ta amsa ba. Gara ta soma neman sabon aiki datayi aiki k’arkashin Anas, mutum ne kullum cikin masifa baya murmushi bale dariya. Sekace dodo!


Da daddare da misalin k’arfe tara bayan su Fannah sun idda sallah suna shirin kwanciya wayarta ya soma ringing tana kai dubanta taga Ya Suleiman cike da mamaki ta d’aga dan kuwa be tab’a kirarta warhaka ba se addu’a take Allah sa ba magana ze mata gameda Anas ba.
“Assalamu Alaikum Ya Suleiman.”
“Ff... Fannah!” Se jin muryar tasa tayi na rawa.
“Ya Suleiman meya faru? Wani abu ne? Ya muryarka ke rawa?”
“Fannah shagon mu... Shagon mu Fannah!!”
“Ya Suleiman dan Allah meya sami shagon namu please tell me” hankalinta tashe take maganar. Afrah dake gefenta itama ji tayi zuciyarta na bugawa.
“Shagon mu yakama da wuta Fannah k’urumus ya k’one ba abinda aka samu aka cire. Wutan NEPA ne yasoma gobarar kafin akira fire service k’urumus komi ya k’one.”
Salati Fannah keyi ba makawa. “Innalillahi!” take idanunta suka cike da hawaye “Ya Suleiman kayi hak’uri mud’au wannan a matsayin jarabawa dole kayi hak’uri ka rungumi k’addara innalillahi! Gobe in shaa Allahu zan fito dare yayi yanzu dana fito am so sorry kayi hak’uri dan Allah.”
“Nagode Fannah” ahaka sukayi sallama.

“Ya Fannah meya faru?” Cewar Afrah.
“Afrah shagonmu ya k'one wutan NEPA ne yasoma gobarar.” Salati Afrah tayi sannan tayi calming Fannah dake hawaye down. “Daman kinada niyyan barin aikin segashi dalili kwararre ya zo ayyah, Ya Fannah da rabon Allah baisan kiyi witnessing a day without a job.” Kallonata kawai Fannah take cike da damuwa ita shikenan nata ya k’are mesa hakan ze faru da shagonsu? Yanzu ya zatayi da kud’in asibitin Baba? Dole a gobe taje tasoma neman aiki.”

Washegari da sassafe ta tashi taje ta shagonsu k’urumus komai ya k’one abin tausayi. Ya Suleiman da Babansa da angansu anga wanda suka kwana suna kuka. Condoling nasu tayi gashi dama k’arshen wata yayi jiran albashi take ta k’arisa biyan kud’in asibitin Baba gashi yanzu da abinda yafaru ba su ba albashi dan koda za’a bata ma barata amsa ba da wannan masifar daya same su.

_One week later..._

Yau k’imanin sati kenan Fannah na neman aiki ba rana ba dare amman har yau ba labarin aiki, abin har kuka yake sata ga kud’in asibitin Baba ‘yan asibitin sun dameta harda cewa in bata k’arisa biya ba zasu kaita gun ‘yan sanda. Abinci ma yasoma k’arewa masu agida abinde ba kyau. Ita nadaman mesa ta yasar da card na Anas ma take ta hak’ura da duk walak’anci da masifan da ze mata inhar ze bata kud’i tabiya kud’in asibitin Babanta. Kuka tasha a waje sannan tashigo ciki. Mami da Baba da Aiman suna d’akinsu. Tana k’arisawa d’akinsu da Afrah ta tare ta zaune kan gado yau ko chatting d’inma battayi dan ba kud’in kati.

“Afrah ba magana ne?”
“Ya Fannah me zance miki? Nariga na gaya miki abinda yakamata. Kinada halin da zaki warkar damu daga wannan hali amman kika k’i. Kalli yadda kowa yake shan wahala haba Ya Fannah dan Allah.”
“Afrah wallahi ba haka bane na miki k’arya dana ce miki zan karb’i aikin da Mr. Fauzi yabani wallahi tun a ranan daya bani card nasan na yasar bansan ya zanyi ba yanzu. Afrah nayi nadamar yin hakan ban zata shagon mu ze k’one ba kuyi hak’uri ina kan neman aiki har yanzu kuyi hak’uri dan Allah.”

Afrah bata ce mata komi ba. Jakarta ta zazzage kan gado dan tattara credentials nata. Fitsari ne ya matse ta, bayan ta shige bayi Afrah ta lalimo kan gadon tana duba papers d’in dan ko bata yarda da abinda Fannah tace mata ba nacewa ta yaga card d’in. Kap ta duba bata ga komi ciki ba har ta hak’ura se kuma ta d’au jakar ta, dudduba zip nacikin jakar take can tajiyo takarda tana cirowa taga card d’inne daidai lokacin Fannah tafito “Afrah me kike min da jaka.”

“Ya Fannah me wannan?” Da sauri Fannah ta hauro kan katifar ta amshe card d’in, baki ta bud’e wangalau “aina kka samu?”
“Ina kuwa? Cikin jakarki? Dama baki yasar ba kenan dan bakisan karb’an aikin ne kika min k’arya kin kyauta.”
“Wallahi tallahi Afrah kinji rantsuwan muslumi kenan bansan ya akayi abin nan ya dawo jakata ba aida nansan da zamansa da na kirasa tuni nida ake threatning d’ina kan za'a kaini gun ‘yan sanda?” Shiru tayi tana nazarin wani abu can tace, “aikin Asma’u definately ita tasamin cikin jakata” nan taba wa Afrah labarin komai.

_10 minutes later... Dadai k’arfe 5:30PM_

Fannah ce zaune kan kujera d’ayan hannunta katin Anas ne d’ayan kuma wayarta a kunne tana jiran Anas ya d’au wayar. Zuciyarta se bugawa yake bababam! Babam!


*© miemiebee*

beeenovels.mywapblog.com
[12:48, 12/18/2016] ‪+234 903 612 6826‬: •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫

❣🎀❣🎀❣

*_written by miemiebee👄_*


2⃣1⃣




Yusuf nada mutunci sosai cikin d’an k’ank’anin lokaci suka saba da juna, dake yanada surutu sekuma gashi shekarunsu d’aya, ma’aikaci ne shima a company’n. Har kitchen d’in ya kaita yajira bayan ta gama had’awa ta bashi ya amshi yakai wa Anas sannan ya dawo dan rakata har waje. wajen wata elevator suka nufa wanda is different from na d’azu dan haka ta tambayesa ko ina zasu. Murmushi yamata sannan yace, “sauk’a zamui zuwa first floor saboda in fita dake kar ki b’ata a wannan babban gini.”
Murmushin ta maida masa “amman naga ba tanan muka hawo da Mr. Fauzi ba.”
“Hakane, ta private elevator’nsa kuka hauro wannan kuma da zamu shiga shine na public, wancan nasa ne shi kad’ai ke shiga you are lucky ma kinsamu kin shiga wancan.” Ya mata bayani. ‘yar murnushi tayi tabi bayansa har waje ya rakota ya tsara mata napep sannan ya koma ciki. Daga can kasuwa ta wuce ta musu siyayyan abinci sosai tunda sun samu kyauta.

Isarta gida keda wuya ta tarar da ‘yan sanda tsaye daga gani ita suke jira fuskar su Mami duk ya jik’e da hawaye. “Yawwa ga ta nan” cewar wata nurse.
“Ku tsaya please.” Fannah tace da polisawan.
“Dalili?” Cewar nurse d’in.
“Ga kud’in kunan nasamu dan Allah” nan ta irga dubu goma ta bata sannan suka fice. Godiya Mami tayi wa Allah da gudu ta ruga tayi hugging Fannah.
“Fannah dan Allah kiyi hak’uri ban tab’a san d’aya daga cikin abubuwan da suke faruwa dake su kasance haka ba dan Allah kiyi hak’uri.”
“Haba! Mami wace erin magana kike inda kunji good news danake tattare dashi ma da duk kunbar kukan nan. Ga nan siyayya na mana nasamu aiki!!”

Atare duk sukace “dan Allah???” “Alhamdulillah.” cewar Afrah.
“Aina?” Mami ta tambaya.
“A Flames Enterprises wallahi Mr Fauzi ya d’aukeni aiki wai zanna had’asa masa coffee...” nande ta musu bayanin komai. Sosai Mami sunji dad’i musamman ma dasukaji albashinta dakuma kyautan da ya mata. Nasiha sosai Mami tama Fannah dukda cewar tasan Fannah da hankali. Albarka tata sawa Anas data ta tsine masa da a baya.

***
Tun k’arfe 4:40PM Fannah ke rik’e da wayarta gudun karta k’ara ko minti d’aya kan lokacin da Anas ya bata. 4:50PM na yi ta kirasa yana kwance kan gado alokacin call d’in yashiga yana gani yagane ita ne beyi picking ba instead seya katse nan yayi saving number’nta da *COFFEE MAKER* cike da mamaki ta sake kira mesa ze katse bayan shi yace ta kirasa be d’aga ba sansa ya kusan tsinkewa. Cike da tsiwa yace “ke baki gane kan aiki ne? Kinga nayi declining call meaning na gane kece kenan haba!.”
“I’m so-” bata k’are maganar ba ya katse wayar. Miyau Fannah ta had’e ita kam Allah bata ikon jure wulak’anci da masifan Anas.

_Washegari..._
Da safe da misalin k’arfe 7:40AM Fannah da Aiman da Afrah suna kwance kan katifarsu se bacci suke rafkawa an samu an k’oshi jiya wayar Fannah yasoma ringing firgit ta farka dake wayar na k’ark’ashin pillownta a gigice ta d’aga ganin sunan daya bayyana kan screen d’in ya wassakar mata da bacci. *MR. FAUZI* giara muryanta tayi sannan ta d’aga.
“Assal-” be jira ta k’are sallaman ba ya katse ta “be here in my office at 8:00AM. Don’t be late” kafin tace “okay” ya katse wayarsa. Ita ba ma wannan ba duban agogonta tayi taga 7:42PM
“YA SALAM!!” ta d’anyi ihu “yaushe zanyi wanka in karya in tsari napep in isa har NEW GRA cikin minti 18 wayyo Allah help me.”

Ko tafasa ruwan zafin wankanta batai ba da ruwan sanyi tayi wankan anayi ana ihu har ta k’are tafito ko shafa mai batai ba, da k’yar da fad’a da kokuwa tasamu ta kama gashinta hakan ma be kamu ba sakwa-sakwa kawai de aje ne. Tea da biredi ta karya da, ba Butter bale Jam haka gayansa taci ta saka wata

Please Login or Register in order to submit comment