Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rik’e dana Fannah se k’ok’arin k’wata take amman ta kasa. Wani erin mahaukacin kishi yaji ya bugesa inba wai kashe koma waye mutumin yayi ba yana ganin bare samu sukuni ba.

A fusace ya k’ariso wajen. “Matata me haka dan na kama miki hannu? Ke wai bakiyi missing d’ina bane? Ko d’an shafaki bara ki bari inyi ba?” Cewar Farouq dawani shu’umin murmushi fal a fuskarsa.
“Ya Farouq ka sake min hannu niba matar ka bace let me go” ta fad’i tana hawaye tare da k’ok’arin k’wace hannunta.
“Ka sake mata hannu!” Anas ya fad’a cike da isa. Fannah da Farouq tare suka juya suna kallon Anas. “Waye kuma wannan baturen?” Farouq ya tambaya.
“Mr. Fauzi please ka tafi, don’t involve yourself in here.”
“Kinsan sa kenan” Farouq ya sake tambaya. “Bade shima saurayin ki bane kina kwana dashi, kinsan sana'a sa’a.” Anas be san lokacin daya kai wa Farouq naushi a fuska ba da zobobin azurfa a hannunsa. Take hancin Farouq ya fashe gefen bakinsa yasoma na d’igan jini.


*© miemiebee*

beeenovels.mywapblog com
[12:52, 12/18/2016] ‪+234 903 612 6826‬:         

•° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫

❣🎀❣🎀❣

*_written by miemiebee👄_*

In dedication to *Aunty Sis💕*
4⃣2⃣





Baki Fannah ta bud’e tare da aza hannunta bibbiyu kai cike da mamaki da tsoro duka. Hannu Farouq yasa tare da tab’a inda yaji moisture a fuskarsa yana dubawa yaga jini ta hanci da bakin sa, “Kai! Ni ka fasawa baki? Dama nasha jin cewa ku turawa bakuda tarbiyya yau zan koya maka.” Hannu ya d’aga da k’arfin da Allah ya bashi shima ze kai wa Mr. Fauzi punch ai karap Anas ya kama hannun nasa tare da murd’awa cike mugunta ta bayansa. K’ara sosai Farouq ya saki dan azaba.

    Fannah duk ta rikice “Mr. Fauzi please ka sake sa ya isa please” ko saurarenta Anas beyi ba k’ara murd’a hannun nasa yayi a bayansa k’ara sosai Farouq ya sake saki dan azaba. “Repeat what you just said.” Anas yace dashi, daga yadda yake magana ma kad’ai za’a san ransa a b’ace yake, na bala’i ma kuwa. Duk zafin da Farouq ya keji be hanasa misbehaving ba. “K’arya nayi dan nace kuna kwana tare karuwarka ce”
     “You really want to die” Anas ya sake shi, kafin Farouq ya sake wani k’wararren motsi Anas ya sake kai masa punch a fuska fiye da yadda yayi d’azu sosai jini yake fita daga baki dakuma hancin Farouq.

     “Mr. Fauzi please ya isa dan Allah” Fannah ta fad’i duk a kid’ime idanta tuni suka cike da hawaye.
    “Kai ko kasan waye ni? Mijinta ne fa ni, aurenta zanyi banza da kai zakazo kana intruding. In ita karuwan kan bata fad’a maka yanzu ai kaji I’m her husband. Ke Fannah dan iskanci ya miki yawa kin kusa aure ma baraki fad’awa ‘yan iskan samarukan kin su hak’ura bako?” Hannu ya mik’a ze jata dan wanke ta da mari. Kamar a kyaftawan ido Anas yajata bayansa kamar ‘yar baby tare da rik’e hannun Farouq, rik’o kawai ya masa amman idan Farouq sanda ya cike da hawaye. D’ayan hannunsa ya d’aga ze sake kaiwa Farouq mumunar punch Fannah ta rik’e hannunsa da nata bibbiyu. Hawaye take sosai “Mr. Fauzi please ya isa kayi hak’uri ya isa please.”

     Hawayen da takeyi ne kawai ya hana Anas kaiwa Farouq punch da ze iya kwantar dashi a asibiti. Kwalan rigar Farouq ya chukumo. “In bakada manners na magana wa kamilallaiyar mace I will teach you some, the next time ka sake kwatanta Fannah da wad’annan munanan suna I assure you zakayi kwanan cell, pathetic fool kawai, idiotic bastard.” Sannan yayi wulli dashi har k’asa Farouq yayi landing, daidai lokacin Ya Khaleel ya yanko kwanan gidansu Fannah shi a dole yazo cin abincin ranan da surikarsa ta dafa masa kamar yadda yace jiya.

     Ai ganin his only son a k’asa ga kuma jini ko ta ina fuskarsa ya falfala da gudu yayi kan Farouq. “Farouq meya same ka? Wani d’an shegiyan ya maka wannan tsiyan, waye shi?”
       “Baba kafin ka kira wani da d’an shegiya make sure ka cire sunan d’anka daga number a list d’in. Nayi warning nasa but I think I have to warn you too, the next time ya sake shiga harkan Fannah bare kwana a garin Maiduguri qalau ba.”
 
     “Tohh sannu fa, sannu shugaban k’asan Nigeria. Toh kaine d’an shegiyan ba d’ana ba, kai har kanada da right da zaka hana Farouq shiga harkan Fannah ne? Ka tab’a jin inda aka shiga tsakanin mace da miji?”
   Fannah dake tsaye bayan Anas tace, “Baffah Khaleel Ya Farouq ba miji na bane.”
    “Ke karuwa rufa min baki.”
   Ran Anas in yayi dubu be b’aci ba, taku yayi yunk’urin yi zuwa gaban Ya Khaleel dan kai masa had’add’en punch shima, “how dare you call Fannah karuwa!” yace a yayinda Fannah ta rik’e rigansa dan hanasa aiwatar da abinda yayi niyyar yi. “Mr. Fauzi let them be please, ya isa ka tafi wannan problem d’ina na ne bansan na jaka ciki, please go.” Wayarsa ya ciro a fusace bayan an d’aga yace, “Hello send me 10 men, I mean 10 a unguwar Polo...” Nan ya masa kwatance. Baki na b’ari police d’in yace, “yy.yyyes Sir right away!”

    Aiko cikakken minti biyar da gama wayan Anas beyi ba sega motan polisawa guda biyu. Farouq harda rud’ewan ciki Ya Khaleel kuwa sanda ya saki fitsari a wando shi be d’au dagaske baturen yake ze kira polisawa ba, toh waye shi.
     “Take them both, kuje ku rufesu right away” ya fad’a a fusace.
    Farouq da baki ke jini yace, “wallahi kayi k’arya me mukayi da zakace aje a rufe mu?” Can k’asa k’asa Ya Khaleel yace, “kai kayi shiru se yanzu nagane waye wannan mutumin, ba bature bane shine wanda aka nunasa da Fannah ranan a BRTV wallahi babban mutum ne mu basa hak’uri in bahaka ba in aka rufemu me bailing namu se Allah.”

     “Mr. Fauzi ko? Dan Allah kayi hak’uri, wallahi misunderstanding aka samu anan my apologies please karka sa a rufe mu dan Allah. Farouq baraka basa hak’uri bane?”
     “Officer take them away banasan jin komai.”
    Nanne bakin Fannah ya bud’u. “Mr Fauzi please kayi hak’uri karka rufesu dukda cewar basuda kirki ‘yan uwana na ne, Ya Khaleel Baffah na ne Ya Farouq kuma cousin d’ina kayi hak’uri and set them free please.”
    “Miss Aleeyu why? Bakiji munanan sunan da suke kiranki dashi bane?”
    “Naji Sir just please set them free, please.” Ta fad’a idanta na cikowa da hawaye.
    “Officer let them be zaku iya tafiya sorry for the disturbance.”
   “Ba komai Mr. Fauzi muna da godiya”
  “Zuwa anjima zakuji alert thanks.”
    “Mungode sir, mungode sir” a haka suka ja motocinsu suka fice.

    “Miss Aleeyu kinasan in samusu retricting order from the law yadda barasu sake zuwa kusa dake ba? So they won’t disturb you in na bar nan?”
     “Sir thank you but karka damu in shaa Allah ba abinda zasu iya min you can go kadena b’ata lokacinka akaina please, thank you”
    “Call me in wad’annan foolish mutanen suka sake miki wani abu” ya k’are maganan yana ma Ya Khaleel da Farouq kallon banzaye cikin banzaye. Farouq zeyi magana Ya Khaleel ya taka masa k’afa dan haka yayi shiru.
    “Ki shiga ciki.”,Ba musu bale gardama ta shige ciki sanda ya tabbata ta shiga ya dawo da kallonsa kan like father like son yana nuna su da yatsa “kun ji na rantse in kukayi ma Fannah wani abu zaku k’are rayuwanku a jail, assholes.” Yana kaiwa nan yashige motarsa driver ya rufe yajasa suka fice.

      Se yanzu bakin Farouq ya bud’u. “Shege se meh? Wallahi kasani ka tab’o tsuliyar dodo, zancen kakeso.”
    “Kai Farouq ya isa saurayin nan babban mutum ne a garin nan ka rufa mana asiri muyi abinda ya kawo mu mukoma da Fannah Bama cikin kwanciyan hankali.” cewar Ya Khaleel.
    “Wallahi Baba be isa ba ya zubar min da jini ya kwana lafiya Allah kaimu gobe. A ina yake aiki kace?”
    “Wai meka isa kayi masa ne dawani fashasshen bakin ka da hancin ka, se uban kurin baki wai kana zuwa gym ji yadda kabari wancan Fauziya ne ko Fauzi ya maka tatas. Kona fad’a maka inda yake aiki me ka isa ka masa?†
   “Niko nasan me zan masa just tell me ina yake aiki?”
    “A Flames Enterprises shine CEO’n wajen naga sun sa a TV”  
   “Good” Farouq yace tare da ficewa. Babansa na kiransa ko a kwalan rigarsa, Ya Khaleel kuwa shegen tsoro ne dashi sekace farar kura. So yake ya shiga cikin gidansu Fannah amman kuma yana tsoron abinda Mr. Fauzi  ya fad’a masa. Dan haka ya nufa masauk’insu kawai.

    Anas kuwa isar sa gida ya wuce d’akinsa tare da sa lock ba tare da yace da kowa komi ba. Wani irin tausayin Fannah yaji ya kama sa, ba abinda yakeso yanzu kamar yayi protecting Fannah daga wannan shegun Baffan nata da d’ansa. Mesa zasu na kiranta da karuwa? Mesa zasu na kiran yarinya me tarbiyya kamar Fannah da karuwa? To kode ta tab’a yin hakan ne da a baya se Allah yamata shiriya? “No!” ya fad’a a fili no matter what Fannah batayi kalan wanda zata iya aikata abinda uncle nata yake fad’a ba. Ai inhar dagaske karuwan ce da bare so ya aura wa d’ansa ba k’azafi kawai suke mata, ayyah ashe shiyasa taketa kuka a office yau, shiyasa ko abinci ta kasa ci. “I will protect you Fannah no matter what.” Ya fad’a a fili.

   *****

_9:23PM_
     Fannah da family’nta ne zaune d’akin Baba yanzu tagama basu labarin abinda ya faru d’azu, abinda Mr. Fauzi yama su Ya Khaleel. Kowa wajen yasha mamaki matuk’a.
   “Alhamdulillah! Alhamdulillah! Allah sak’a wa Anas da alhkairi, abinda yama Ya Khaleel daidai ne Allah saka masa da alkhai” “Ameen” kowa ya amsa wajen.
     “Habibiti amman har duka Anas yama Farouq?” Mami ta tambaya cike da mamaki.
   “Eh Mami, Mami tsoro nakeji wallahi Ya Farouq ze iya cewa ze rama dukan akaina.” Rungumota Mami tayi gam ajikinta tana shafa jelar gashinta da d’ankwalinta be samu ya rufe ba. “In shaa Allah ba abinda ze miki kina da Allah bayan haka kuma ga Anas na tabbata bare bari wannan shegen Farouq d’in ya miki wani abu ba.”

    *****

    _10:30PM_
“Wai ina wannan hegen yaron yajene?” Cewar Ya Khaleel da kansa for the 100th time yana duban k’ofar one room apartment da suka d’an kama da d’ansa. Chan ya hango shadow’n mutum, torchin hannun sa ya haska, ganin Farouq ke tahowa ya saki hamdala tare da nufan wajensa. “Kai Farouq ina kashiga tun d’azu? Kasan na rasa mahaifiyarka barin iya juran rasaka ba kaima. Kuma dan rashin hankali haka kata yawo a gari da fashasshen baki da hanci?” K’eyarsa ya tand’e “wuce ciki mu goge maka.”

_5 minutes later..._
 
Farouq ne mik’e kan ‘yar katifarsu a yayinda Ya Khaleel ke treating masa ciwon da Anas yaji masa a fuska da dettol. “Ina kaje ina tambayarka tun d’azu kamin shiru.”
    “Kai de Baba Allah kaimu gobe se Mr. Fauzi ne ko Fauziyan nan ya raina wa kansa nan gaba ko kafad’an juna muka buga bare min koda kallon banza ba.”
   “Wai me kake nufi Farouq? Kaga fa ka rufa mana asiri ni na fad’a maka kokuma in anzo tafiya damu in ce mai kai kad’ai ne banda ni, am warning you.” Lebb’an sa yacize irin mazan nan mana aikuwa yacize wajen ciwon.

★★★
_Washegari..._
  
      K’arfe 8:10AM ya ma Fannah a office na Mr. Fauzi tun 8:00AM yake jiranta a zatonsa ma ko barata samu zuwa ba se kawai ya ganta, har cikin ransa yaji sanyi sede yau ma fuskarta ba walwala kamar jiya. As usual ta k’ariso gaban table nasa ta gaishe sa kanta a sunkuye. “Good morning Mr. Fauzi.”
     “How are you feeling?” ya tanbayeta a hankali.
   “Alhamdulillah, thank you for yestarday.”
   “Ba komai” yace mata.
    “Sir bansamu nayi making schedule naka jiya ba am sorry.”
  “Is okay” yace mata ba tare da ya nuna damuwa ba. “Mesa baki fad’a min ba?” Ya tambayeta. A hankali ta d’ago kanta idanunsu na had’uwa ta sake sunkuyar da kanta, “I’m sorry” tace sincerely.
    “Baki amsa min tambaya na ba, mesa baki fad’a min abinda wad’ancan biyun suke miki ba. Saisa kikazo jiya kika ta kuka kenan koh? Akansu ne?” Kai ta giad’a a hankali.
   “Mesa baki sanar dani ba?”
  “Sir I thought there will be no point in fad’a maka sesa kawai nayi shiru.”
    “Next time call me up and tell me kinji?” Kai ta giad’a tare da godiya.
   “Sun sake miki wani abu?”
   “A’a.”
“Dagaske ne zaki auri wancan Farouq d’in?” Ya tambayeta kamar me jin kishin ta. Kai ta giad’a a hankali.
“Mesa? Kina son shi ne?” Nanma kai ta giad’a.
“Miss Aleeyu” ya kira sunanta “na’am” ta amsa kan ta a sunkuye. “Look at me.” A hankali ta d’ago kanta tana kallonsa kamar yadda shima yake kallon nata. Ba komi ne tattare da idanunta ba inbanda tsoro. “Do you really love him?” Ya sake tambayar ta cikin sanyin murya.

Hawaye tajiyo na ciko mata, “no Mr. Fauzi banasan sa, ban tab’a san sa ba, mugu ne, azzalimin da besan daraja ta ba.”
“Shhh is okay kar kiyi kuka, bakiya sansa baraki aure sa ba kinji?” Har hawayen nata sun soma sauk’owa ya ciro hanky ya mik’a mata amsa tayi ta share hawayen. “Sir how? Baffah Khaleel is powerful ni nasan dole zan auri Ya Farouq.”
“No baraki aure sa ba I promise, jeki huta Kacallah ze kula da aiki ki yau.”
   “Sir don’t worry zan iya yin aik-” bata k’are maganar ba ya katse ta “banasan musu idanunki sun riga sun nuna baki samu bacci ba jiya so just go before I change my mind.” A hankali ta juya sanda takai bakin k’ofa sannan ta juyo tana kallonsa taga yana tattara files na gabansa “Mr. Fauzi” ta kira sunansa chak ya bar abinda yakeyi tare da d’ago blue eyes nasa yana kallonta. “Yes?” Ya bata amsa.
    “Thank you” tace dashi. D’an murmushi ya saki wanda ya sake bayyano da kyan sa. Giad’a mata kai yayi as an answer sannan ya cigaba da abinda yake a yayinda tafice zuwa office nata ita kuwa.

    Batasan me ba amman kwana biyun nan in *_TANA TARE DA_* Mr. Fauzi setaji she is safe kuma setaji ta ba damuwa. Kan cushion nata ta baje a hankali bacci me uban nauyin gaske ya isketa wanda takasa yi jiya da daddare dan yadda damuwa suka mata yawa.

  _30 minutes later..._

A nitse kuma a hankali Anas ya bud’e office na Fannah. Taku d’ai d’ai yake a hankali har yashigo cikin office d’in zube ya sameta kan 3 seater tana bacci peacefully. Har gabanta ya tako tare da tsugunawa d’an hijabin daya tare mata fuska yasa hannu ya gyara dogayen eyelashes nata yatsaya yana kallo sannan yakoma kan girarta dayake nan kamar na Kajol na india yadda ya had’e me kyan bala’i. Sekuma d’an siririn hancinta dayake nan madaidaici dakuma d’an bakinta dakenan ba k’aramin chanba bakuma babba ba tsakatsakiya.

    Besan dalili ba amman kawai ya tsinci kansa cikin jin dad’i, killer murmushi ne kwance kan kyakkyawar fuskarsa wanda ya lotsar da dimple nasa na gefe d’aya. Jakanta dake saqale a kafad’arta ya zira hannu ya cire a hankali yadda bare tada ita ba, tare da ajiye wa a gefe guda, k’afafunta ya daidaita kan kujerar tare da kunna AC’n a medium ta yadda beyi yawa ba bekuma yi kad’an ba. Ficewa yayi zuwa d’akinsa ya d’au wani arabian bargonsa me uban laushi da pillow yazo ya rufeta dashi tare da aza kanta kan pillow’n    ya juya ze fita kenan Fannah ta kama bakin suit nasa ta baya chak ya tsaya tare da juyowa hannun nata ya raba da kayansa a hankali sannan ya rufo mata k’ofar ya fice zuwa office nasa. Yau yagama had’a model nasa sauran asalin gini yanzu. Already filinsa na nan kawai abinda yarage shine asa drawing d’in into action.

*© miemiebee*

beeenovels.mywapblog.com
[12:53, 12/18/2016] ‪+234 903 612 6826‬:    
•° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫

❣🎀❣🎀❣

*_written by miemiebee👄_*

In dedication to *Aunty Sis💕*
4⃣4⃣




      “Miss Aleeyu barin je ba kema leave I can take care of myself” hannu ya mik’a ze amsa pillow’n se kawai ya saki k’ara dan zafin dayaji a cikinsa saboda blows da Farouq ya riga kai masa. A rikice tace, “meneh Mr. Fauzi?” Kafin ya amsata ya mata k’arya ta kwaye bedsheet d’in daya ruhu dashin, hannu ta aza kan bakinta cike da mamaki “Subhanallahi Mr. Fauzi dan Allah meya sameka? Ina kasamu wannan ciwuka? Kalli cikin ka? Ya Salam!!!” Ta fad’i tana hawaye tana kallon cikin Anas da yayi har wani purple brownish colour dan azaba.
  
       “Mr. Fauzi meya same ka please?” Ta sake tambaya hankali tashe.
      “Nace miki babu in kinsan kuka zaki tayi anan kuma go, leave, I can take care of myself.”
    Innalillahi! what do I do now ta tambayi kanta barata iya barin Anas haka ba he is badly wounded ga fuska ga ciki meya samesa ko b’arayi ne suka shigo suka masa duka? Amman kuma ai gidan tsaf yake ba abinda aka b’arnata. Toh meneh?
          “Mr. Fauzi please kayi hak’uri mu kaika asibiti kaji? Yi hak’uri.” Ta fad’a still tana hawaye dan tsantsan tausayi. Danko ba wanda zega ta’addancin da aka ma Anas be tausayawa masa ko be zubda hawaye  ba.

             “Nace miki barinje ba kitafi please.” Wayarta ta ciro zata soma dialing number’n Amal dan sanar da ita halin da ake ciki.
    “Me zakiyi?” ya tambayeta.
   “Zan kira Amal ne in sanar da family’nka I’ve found you tun jiya suke neman ka.”

     “No karki kira su hang up.”
  “But Sir-” katse ta yayi ta hanyan daka mata tsawan da seda shi kansa ya masa ciwo “I said hang up!” Kansa ya dafe yana muntsika fuska cike da azaba. Nan ta katse ta matso kusa dashi “Sir kanka ke ciwo?” Niyan shareta yayi da farko sekuma ya giad’a mata kai a k’arshe. Jakarta ta ajiye kan side drawer ta nufa toilet tare da fitowa da bowl cike da warm water data d’iga dettol ciki dakuma towels guda biyu, jakarta ta ture gefe tare da ajiye bowl d’in akai. Kallonta yake “me zakiyi?”
   
    “Sir your face is a mess, zan goge maka ne.”
   “Banaso just leave.”
   “No Sir I’m not leaving mesa kai zaka taimaka min amman ni bakasan na taimaka maka? Saboda bankai inyi offering maka help bane? Saboda ka raina ni banida standard? Saboda ni talaka ce? Is that it Sir?”
   “No Miss Aleeyu that is not my point...” sekuma yayi shiru.
    “Toh kabari in biyaka taimakon dakake min koda na yau ne.” Shiru yayi chan ya giad’a mata kai.
   A ranta tace, Ya Allah kar ka kamani da laifi saboda zan tab’a na mijin da ba muharrami na ba, baida lafiya ne taimako zan masa, astaghfirullah.

   Nan ta tsoma d’ayan towel d’in cikin ruwan d’umin tare da matsewa a hankali ta d’an tab’a gefen bakinsa daya fashe. Towel d’in na tab’a wajen yajiyo zafi sosai hannunta ya kama “Sir nasan zeyi zafi hak’uri zakayi kaji? Sorry” a hankali ya sake hannun nata. Tana sake tab’a wani waje ya saki k’ara “arghhh! Ya isa kibari ze warke da kansa, go home”
    “Mr. Fauzi please mana kabari koda germs d’inne a kashe tunda baraka je asibiti ba. Please”
    Haka a nitse cike da tausayi ta riga bin duk ciwon da ke kan fuskarsa tana gogewa a hankali, sosai Anas ya riga sakin k’aran azaba in towel d’in ya tab’a masa kan ciwon ita kuwa duk lokacin daya yi d’an ihu seta basa hak’uri. Tagama da fuskarsa sauran cikin. D’ayan tsumman ta d’aga ta sa cikin ruwan kamar yadda tayi d’azu bedsheet daya rufe jikinsa dashi tasa hannu ta kwaye zuwa cibiyar sa.
    “Me kuma zakimin?” Ya tambaya yana k’ok’arin jan bedsheet din gam ta rik’e tana me hanasa yin hakan. “Ba abinda zan maka Sir zan d’an matse maka wajen ciwon ne.”
    “Don’t worry ze warke da kansa. Wai ke bakia jin tsoron zama da namiji kad’ai ne under thesame roof?” ya gwada tsorata ta ko zatace ta hak’ura zata tafi.

      “Ina ji amman in da kaine bana ji, I trust you Mr. Fauzi nasan ba abinda zaka min shiyasa. Yi hak’uri in d’an matse maka cikin kaji?” sanda ya k’are mata kallo sannan ya giad’a kai.
    A hankali ta aza hannunta kan cikinsa ta matse towel d’in kai. K’ara ya saki sosai dan azaba tare da rik’o hannunta. “Awwchh! Kibari ya isa ze warke da kansa, arghhh!”
     “Sir hak’uri zakayi sauran kad’an sorry.” Haka tata lalashinsa kamar d’an yaro. Towel tasake canzowa tare da k’aro ruwan zafi kan ruwan dan ya riga ya huce. Bayan ta zauna ta sake tsoma towel d’in ciki, cikin siririyar muryarta tace, “Sir did you get drunk yestarday”  Shiru yayi kamar be jita ba. “Sir?” Ta kirasa. “No” ya mata k’arya danko besan taga kwalban a bakin k’ofa ba.

     “Toh wancan fa kwalban meh?” Ta tambayesa a nitse. Kai ya d’aga yaga kwalban sekuma yaji kunya. “Toh me ruwanki dan nasha? You are not my mother ko ita mahaifiyar tawa bata isa ta hana niba, stay out of my personal li-” be k’arisa fad’in ‘life’ ba yasaki ihu “arghh!” Sanadiyar tab’a masa kan inda ke masa zafi sosai da Fannah tayi. “I’m sorry” tace “sauran kad’an.” Chan ta nisanta, “Mr. Fauzi will you listen to me in na fad’a maka wani abu?” Kamar wanda bare ce komai ba seyace “meh abun?” Sanda ta sake matse towel d’in ta mayar kan cikinsa tana daddanewa kan ciwon a hankali

Please Login or Register in order to submit comment