Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[12/31/2019, 11:20 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*IཽNཽDཽOཽ Aཽ BཽIཽRཽNཽIཽ*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


*Na*

*Rasheedat Usman*

*(Ummu Nasmah)*


*(MAKAMAR KAINUWA)*👸🏻


📱
*08147537180*


*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*
(Baya hana gamji)
Toho


*1 / 1 / 2020*

Tsarabar sabuwar shekara domin ku masoyana.


*Deducated to*


*Aunty Fauza yar Amana*

Uwa mabada mama k'aunar ki dabanne gare ni, domin ke d'in shugaba ce, dake Adalci ga duk na k'asa dake, Allah ya barmu tare Aunty nah.



*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

Alhamdulillahi Ala kulli Halin dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah madaukakin Sarki, salati da d'aukaka da Aminci su tabbata ga cikamakin Annabawa Annabin k'arshe muhammad S'A'W da iyalan gidan sa da sahabban sa har izuwa Ranar Sakamako.

Ina godiya ga Allah daya sake dawo dani lfy, domin sake nishad'antar daku, ina rok'on Allah da yasa yanda na fara lfy ya bani ikon gamawa lfy, Allah ya bamu ikon Amfana da Abunda ke ciki. Ameen 🙏🏻



*P* 1️⃣ ➡️ 2️⃣

Yara biyu na hango suna cin Uban gudu, yayin da wacce ke gaban take gudun ceton Rai, sosai take gudun Saboda kar wacce ke bin bayan nata ta kamo ta, wani gida naga yarinyar ta fad'a, binta cikin gidan itama yarinyar dake biye da itan tayi, da Gudu ta fad'a wani madaidaicin d'aki, cikin haki.
d'akin da yarinyar ta shiga, itama wacce ta biyo tan take k'ok'arin shiga.
Cikin Sauri wata matashiyar mata ta tare ta tare da cewa.

" Lafiya *INDO* kuke wannan Uban gudu, sannan kuma zaki bita har d'aki, aiko mutuwa ma tana kunyar Idon Uwar d'a, meye *Zainabun* ta Miki?
kika biyo ta har gidan ubanta ba ko kunya.

Huci wacce aka kira da *INDO* take Cikin masifa da bala'i take cewa.

" Sai mutuwa taji kunyar Idon ki, ni kuma *INDO banji taki ba, wlh yau Babu mai hanani cin Uban Zainabu cikin gidan nan, gobe koda kud'i aka Had'a ki baxaki k'ara nema na da tsokana ba, cemin fah tayi *INDO BALA'I* a gidan uban waye aka yanka min suna da *INDO BALA'I* Kinga *Goggo Hali* ki kauce ki bani hanya, kar nayi gefe dake kiga rashin kunya ta, dan wallahi, na ture ki na shige cikin d'akin nan baxai bani tsoro ba, ehe sai dai duk abunda zai faru ya faru, ta k'arasa maganar tana murgud'a baki.

Gam sukaji An rufe k'ofar d'akin tare da dannawa k'ofar sakata, daga rufen zainabu tace

" Baxan fiton ba, kuma na fad'a *INDO BALA'I* ko k'arya nayi ke ba masifaffiyar bace.

Matsawa wacce ta kira da *Goggo Hali* tayi tare da cewa to Kinga ma ta rufe d'akin sai dai idan ni zaki Kama ki daka, tunda ke baki da mutunci, kowa ya miki shaidar tsiya a cikin garin nan.

Cewa *INDO* tayi
" Idan anga dama Amin shaidar Abunda yafi Rashin mutunci ma, kuma wlh yau sai kinga yanda ake tsiya a cikin gidan nan, badai y'ar ki ta rufe d'aki ba, d'aga murya *INDO tayi, tace zainabu kina jina ai idan ba tsoro ba ki fito, mana shegiya y'ar matsorata, kuma wallahi Yau saina huce haushi na akan *UWARKI*.

Juyawa *INDO tayi, karaf kuwa sai idon ta yayi toxali da Randar k'asar Goggo Hali, Wacce take cike fal da Ruwa, Da Gudu tayi madafin Goggo Hali ta d'auko tab'aryar ta, Randar k'asar INDO* ta nufa da Gudu tare da buga tab'aryar akan Randar, fashewa Randar tayi, take kuwa Ruwan ya zube kasa, bokiti na k'arfe dake ajiye gefen Randar k'asar *INDO* ta raruma tare da shek'awa a d'akin mahaifin Zainabu, tsayawa Goggo Hali tayi tana kallon ikon Allah a gun *INDO* domin kuwa Idon ne kawai tsakanin ta da ita, tasan Idan tayi gangancin zuwa ta tare *INDO* to Babu shakka zata iya sauk'e mata tab'aryar a kanta ba damuwar ta bane, domin kuwa tasan Halin INDO tsaf babu wanda ta gyale kaf fad'in kauyen.

Cikin Huci INDO tace.

" Kuma na watsa Ruwan a d'akin Malam Hamxa idan ya dawo shima yasan cewa y'ar sa ta tab'o *INDO* yau,
Bata jira mai Goggo Hali zata ce ba tayi ficewar ta tana rera wak'a.

" Ikon Allah cewar Goggo Hali, yarinya ta Addabi gari, kowa yake Allah wadarai da Halin ki, Yanxu fah ki duba kiga b'arnan da yarinyar tamin, Amma dai wallahi Albasa batayi Halin Ruwa ba dan dai iyayen ki kam, mutanen kirki ne, Su kuma tasu jarabawar kenan, na Samun fitinanniyar yarinya, to Allah dai ya shirye ta.
Jin motsin mutum a bayan ta ne yasa Goggo Hali juyawa, zainabu ta gani tsaye tana sauk'e Ajiyar zuciya, ai kuwa nufar ta Goggo Hali tayi, tare da sauk'e mata rankwashi a kanta, tace.
" Yanxu ke zainabu ki Rasa wa zaki tsokana sai *INDO*, sai kace wacce baki san Halin ta ba, to maxa shiga d'aki ki d'auko min mayafi na, naje wajen Uwar ta wlh sai sun biyani Randa ta, dan baxan yi Asara ba wlh.

D'akin Zainabu ta nufa tana cewa.

" Kije ki wlh Goggo a biyaki Randar ki, tunda y'ar su bata da mutunci.


Ita kuwa INDO fitar ta daga gidan su zainabu, hanyar gidan su ta nufa, tun daga nesa ta hango motar sa, cikin murna da zuwan sa, garin nasu yasa *INDO* kwasa a guje, cikin zumud'i, ta nufi motar, kasancewar Gudu baya bawa *INDO* wahala, kullum a cikin sa, take sam bata da nutsuwa, k'azanta kuma wajen *INDO* subhanallah ba'a magana, domin kuwa k'azama ce ta ajin farko, duk inda ake neman k'azama, to idan aka Samu indo ayi fatiha a tashi, domin kuwa kaf fad'in K'auyen Babu wanda yakai *INDO* k'azanta.
Wannan kenan.

A nutse ya fito daga cikin motar, tare da tsayawa jikin motar yana duba yaran da zasu shigar masa da Kaya cikin gidan, tsohuwa mai ran k'arfe *HAJIYA INNAH* da Gudu INDO ta k'araso wajen nasa tare da yin turus da k'afar ta cikin bak'ar kasa mai k'urar dake shinfid'e a wajen, take kuwa k'asar ta bulewa wannan bawan Allah k'afar sa.
Da sauri ya daga kansa ya dubi *INDO* cikin takaici kuma cikin tsawa yace.

" Wacce irin mahaukaciya ce ke, ki duba kiga yanda Kika bule ni da k'asa, wawiya marar Hankali, Zaki kauce min da gani ko sai na makeki, Useless kawai.

Tura bakin ta INDO tayi, tace

" Wlh yau Kam baxan bar nan ba sai kace kana Sona, shikenan kullum sai ni kad'ai zanta sonka, kai baxaka soni ba, wlh yau sai kace kana Sona, ko kuma kamin Irin Abunda nake gani y'an India suna yiwa y'an matan su, a tibin *Hajiya Innah*, Bari ma na tuno sunan Abun 🤔
Yawwa na tuno kuss, suke cewa, sai kamin sannan zan tafi, turo masa bakinta tayi, tace gashi kamin, kaji mustapha na.

Zaro Idon sa, mustapha Yayi tare da saurin kawar da kansa gefe, jin bugun warin bakin INDO ya bigi hancin sa, wani Irin hucin wari yaji mai tayar da zuciya, cikin k'yank'yamin ta yake cewa.

" Allah ya sauwak'a naso k'azama irin ki, k'azamar k'auye, waima tukunna uban waye zai miki kiss, da wad'annan yellown hak'waren naki, b'ace min da gani kafin na targad'a ki, mahaukaciya kawai, marar lissafi, Amma dai wlh Allah ya isa tsakanina dake, ki rasa waye zakice kina so saini, to wlh Allah ya isa kin cuceni.

Murgud'a masa Baki tayi tace.

" Niba mahaukaciya bace wlh, kuma sai kamin kuss d'in nan, rarumo rigarsa tayi, ta duk'unk'une a ciki.

kasancewar babbar riga yasa, sai buga k'afa take, tana ihu tana cewa.

" *Wayyo Allah na shiga uku wayyo jama'a kuzo ku tayani rok'ar ya mustapha ya min kuss wayyo Allah Jama'a kuxo ni kad'ai nake sonsa shi baya Sona.*

Rasa Yaya mustapha zaiyi da INDO yayi, gashi kuma yana hango wasu dattawa biyu suna, tahowa, ta inda suke,

"Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un Allahumma ajirni fil musibati, nidai wannan yarinyar ta zamo min masifa wlh, Duk Randa zanzo k'auyen nan, da tsinkewar zuciya nake Zuwa, tunda nasan zan had'u da Bala'i.

da k'arfi mustapha yasa Hanun sa cikin kyamar INDO ya b'anb'aro ta da kyar, tare da hankad'a ta, gefe.

fad'uwa tayi tare da bige kanta jikin bango, wani Irin zafi taji a kanta, Amma duk da haka Bakin *INDO* bai mutu ba, cikin Rashin Kunya, ta taso kamar wacce zata Doki Mustapha, tace.

" Ka ture Allah ya Isa wlh, mungun Azzalumi, kuma wlh Bashi ka d'auka, sai na Rama wlh.
Tana gama fad'in haka ta juya ba tare da ta k'ara Kallon mustapha ba.

Tsuka mustapha yaja, tare da tab'e bakin sa, yace.

" Wawiya kawai marar Hankali da nutsuwa, ai ko d'aura min ke Akayi a kaina, saina sinke ki da k'arfin tsiya, nayi wurgi dake gefe, *K'AZAMAR K'AUYE* kawai.
Yara biyu ya hango, Kira ya k'wala musu, bayan sunxo ne, ya umurce su, da su kwashi kayan sukai masa gidan *Hajiya Innah.*

Tsayawa yayi har suka gama shigar da kayan sannan yasawa motar sa security, yayi gidan, *Hajiya Innah*.
Sauk'ar Ruwa a jikin sa mustapha yaji' wani Irin shid'ewa Yayi, a gigice ya bud'e Idon sa, karaf suka had'a Ido da *INDO* tsaye da bokitin Ruwa a Hanun ta wanda ta juyewa Mustapha a jikin sa, takaici da haushin ta, shine ya hanasa magana, saima wani mungun kallon daya tsaya yana aika Mata.

Juyawa INDO tayi a guje tana dariyar k'eta tace.

" Na Rama tureni da kayi, daman ai na fad'a maka Bashi kaci, kuma na Rama Yanxu Babu bashi tsakanin mu, masoyina mustapha, *INA SONKA ARADU* tana gudun ne take wannan zancen.

Kad'a kansa mustapha yayi, cikin Jin haushin *INDO* da mamakin ta, yake cewa.

" Anya kuwa wannan yarinyar bata da Aljanu, don ba k'alau take ba, Kam, wai *masoyina mustapha* ko a gidan uban waye na zama masoyin nata, sai Allah, shigewa Yayi cikin gidan, tare da Sallama.

Tana Zaune gefe tana b'arar gyad'a ga kuma tarin kayan da mustapha yasa aka shigo masa dashi, a gefen ta, d'aga kanta tayi tare da cewa

" Lale maraba' da mutanen Binni, sai Kuma tayi shuru tare da tsurawa jik'ak'k'un kayan jikin sa Ido, cikin mamakin meya jik'a masa Kaya, kasa hakuri *Hajiya Innah* tayi tace.

" Muhammadu dake haka take kiran sa dashi, menene ya jik'a maka kayan ka, kodai ka biya Rafi ne kayi wanka?

Tambayar *Hajiya Innah* ta k'arshe itace ta bawa mustapha Haushi, *wai ko ka biya Rafi ne kayi wanka* sai kace ta tab'a ganin nayi hanyar rafin nasu, cikin gatse ya mayar mata amsa da cewa.

" *A'a ba Rafi Naje ba, tekun Maliya na biya nayi wankan na dawo*.

" To Uban y'an bak'ar magana da zafin Zuciya, Idan da Akwai inda yafi tekun Maliya ruwa ma kaje kayi wankan, aikin banxa kawai daga tambaya sai cibi ya zama k'ari.

Tabe bakin sa yayi tare da d'aga kafad'ar sa, Alamun wannan damuwar kine, shigewar sa Yayi d'akin daya kasance nashi idan yaxo k'auyen.
D'akin fess dashi gwanin ban sha'awa komai a tsare kamar d'akin Mace, kan dressing merron shi kuma kayan shafe shafe ne kalakala masu tsadar gaske na maxa.
Wanka ya shige yayi a ban d'akin Hajiya Inna dake tsakar gidan ta.

Itako Hajiya Inna sai mita take ita d'aya.

" Yaro ace sai shegen Bak'ar Zuciya gare sa, ga rashin hak'urin tsiya, shiyasa nake Allah Allah *Habeebu* ya dawo ya dinga ziyarta ta, sai munfi shiri dashi, fiye da wannan mai Bak'in Ran tsiyar, dan *Habeebu* yaron kirki ne d'an Albarka, na Rasa wani Irin Aiki yake a k'asar wajen Nan, da yak'i dawowa k'asar sa ta haihuwa.


Mustapha daya fito daga ban d'aki ne, yana jin duk mitar da take yi ne, yake ce Mata.

" Kamata yayi ki bisa k'asar wajen ai, ki dawo shi wannan K'auyen da Zama K'arshen K'auna, hakan ne zai tabbatar da kina sonshi, Nima banda k'addara da biyayyar iyaye mai zai kawo ni wannan, Bak'in k'auyen harma wannan jarababbiyar yarinyar ta Addabe ni.
Kuma wlh Hajiya koda wasa naga k'afar yarinyar nan *INDON* cikin gidan nan sai na b'allata.

" Kan Uba cewar Hajiya Innah, to a Bak'in k'auyen aka binne cibiyar Uban ka, kuma baka da wajen daya fi wannan K'auyen tunda shine Asalin Ubanka Haruna.
da kake maganar cewa *INDO* karta shigo cikin gidan Nan, gidan kane koko akwai kud'in ka cikin ginin gidan, to ko ubanka Haruna bai isa ya hana *AISHATU* shigowa cikin gidan Nan ba, bare kuma kai *Karan kad'a Miya* , sai dai Kuma Kai kabar min gidana, badai *INDO* ba Zan Kuma ga Uban da zai hana ta shigowa.

Hararar Hajiya Innah mustapha Yayi, tare da shigewa cikin d'akin nasa ba tare daya k'ara tankawa Hajiya Innah ba.

Itama D'akin ta ta shige tana ci gaba da zagin mustapha, wanda shine gaisuwar da sukayi daga isowar sa. 😄

" Gafaran kudai masu gida cewar Goggo Hali, dake tsaye k'ofar d'akin, Mama mahaifiyar *INDO*.

Fitowa mama tayi, tare da cewa,

"Lale marhaban da Halima, kece yau tafe a gidan nan.

" Eh Nice cewar Goggo Hali, na sameki lfy.

" Lafiya lau Halima ki zauna mana, mu gaisa, naga kin tsaya bayan ga shimfid'ar taburma.
Cewar Umma.

Kad'a kanta Goggo Hali tayi tare da cewa.

" Ba zama bane ya kawo ni Mairo, Y'arki ce tayi min D'ibar Albarka, yau a cikin gidana tare da Kuma b'arna, shine naxo a biya Ni, dan baxan iya Asara ba wlh, tunda ku y'arku tafi k'arfin ku.

Mama taji Zafin maganganun da Goggo Hali ta mata, sai dai Kuma ba laifin ta bane *d'an kuka ne mai jawa uwarsa jifa* da Indo mutum ce mai jin magana da tuni ta daina jawo musu zagi a gari, amma kunnen k'ashi gare ta, sai dai kullum tana mata Addu'a tare da fatan shiriya, ta kintsu ta dawo y'a ta gari wacce kowa zaiyi Alfahari da ita, kuma tasan Allah maji rok'on bawan sa ne, yana jinta yana ganin ta kuma zai Amshi Addu'ar ta.
Bata tsaya tambayan Goggo Hali me Indo tayi mata ba gudun kar taji abunda zai b'ata mata rai, yasa ta cewa goggo hali.
" Kiyi Hkr Halima, *d'an yaune ka haifesa baka haifi halin sa ba* Nawa ne kud'in b'arnan da INDO tayi Miki.

" Randata ta fasa min, sabuwa gal Ranar da naje, garin Sauro na sayo ta, Naira D'ari Uku da hamsin 350.

Kunce bakin zanin ta mama tayi, ta Ciro gudan d'ari biyar ta mik'awa Goggo Hali, tace.

" Gashi Idan kin sanja sai ki Aiko min da d'ari da hamsin.

Karb'a Goggo Hali tayi Babu ko kunya ta fice tare da cewa zan Aiko miki sanjin ki anjuma.

Shuru mama tayi tana tunanin Halin, *INDO* ita tsoron ta ma kar wani ya mata mungun Baki ya kamata, domin kuwa ita kanta Da ta haifi INDO hakuri take da ita, bare Kuma Al'ummar gari.
Tana cikin tunanin ne INDO ta shigo gidan da Gudu tana dariya, tare da zama kusa da Mama tace.

" Mama ina Abinci na, yunwa nake ji wlh, d'azun nan naci Abinci Amma wlh Yanxu ji nake kamar na kwana biyu banci Abinci ba.

Kallon ta Mama tayi, tare da cewa.

" Za kuma yau ki kwana baki ci Abinci ba, domin kuwa kud'in cefenen da Malam ya bani d'ari biyar, na d'auka na biya, Halima kud'in Randar ta, da kika fasa, kinga yau sai mu wuni da *Azumin Dole* d'ari da hamsin ta saura, kuma k'annen ki, zan sayawa garin rogo da suger su Sha.

" Kutumar Uban nan, Goggo Halin ne taxo tace na mata b'arna, ita bata gaya Miki Abunda Zainabu tamin ba.
To wlh Mama sai Goggo Hali ta gwammace Bata karb'i kud'in nan ba, dan wlh sai nayiwa Zainabu mungun dukan da sai sun kashe DUBU a kantin Hassan mai magani.

Gwanb'are bakin ta Mama tayi tare da cewa.

" Ke dai INDO bakya nemawa Rayuwar ki Albarka wlh, yanxu ma sake komawa zakiyi gidan nasu, ki jawo min wani maganar ne, to wlh ko a hanya kika had'u da Zainabu, karki kuskura kisa hanu a jikin ta, Idan Kuma kika sa Hanu jikin ta, to kuwa ranki zai b'aci a wajena shashashar banxa marar kunya.

Tashi INDO tayi tana tura baki tare da maganganu k'asa k'asa, wanda bakin ta ne kawai ke motsi, Sanda taxo daf da k'ofar barin cikin gidan nasu tace.

" Wallahi Mama Babu mai hanani cin Uban Zainabu yau, sai dai Idan bamu had'u ba, gara ma kiyi hakuri kawai.

Tashi Mama tayi na dawo ki samu waje ki zauna INDO yau wuni zakiyi cikin gidan nan tunda Allah ya yoki mai kunnen k'ashi.

INDO bata tsaya sauraron Mama ba ta fice a d'ari tana dariya.
Gidan su k'awar ta Hansai, shigar ta Zauren gidan su hansai ta jiyo muryar Baffah mahaifin Hansai, tsayawa INDO tayi tare da dafe k'irji tace

" Alhamdulillah Allah yaso ban shiga ba, Ashe wannan masifaffun tsohon yana nan.

Kasancewar Baffah mahaifin Hansai ya hanata kula Indo acewar sa zata Lalata masa tarbiyar yarinya.

Juyawa INDO tayi tare da zagawa, ta katangar Ban d'akin su Hansai da nufin ta dirk'a ta ban d'akin yanda zata samu shigewa d'akin Innar su Hansai ba tare da Baffah ya ganta ba.
Kama katangar INDO tayi, kasancewar katangar guntuwa ce, ta dira cikin ban d'akin.
Lami kishiyar mahaifiyar Hansai dake tsugunne Kan shadda tana bayan gari, taji dirowar mutum cikin ban d'akin, cikin tsoro ta fara bin k'afar INDO da kallo, ba tare da ta d'aga kai ta kalli fiskar taba, ihu Lami tasa cikin tsoro, tana cewa.

" Na shiga Uku ni Lami, dan Allah kuyi hkr wlh mantawa nayi, na shigo ba tare da nayi addu'a ba, kuyi dan Allah *ku kuke ganin mu, ba muke ganin kuba ba* wayyo Allah ku kawo min agaji yau Kuma Nayi gamo.
Yayin da fitsari ke bin k'afofin Lami.

Dariya INDO ta shek'e dashi har hawaye na fita cikin idanun ta, ganin yanda Lami ta gigice ta fice hayyacin ta har tana fitsari a jikin ta, yayin da Idon ta, ke rufe gam tak'i bude su.
D'alewa saman katangar INDO tayi ta zauna tana cin dariyar ta, tare da nuna Lami da yatsa.



Nan zan dakata sai naji yanda kuka karb'i book d'in kafin naci gaba da typing.


*Yawan sharhi yawan typing.*


*Share*
*And*
*Comment*

*Alk'alamin Rasheedat Usman✍🏻*


*(Ummu Nasmah)*
[1/2, 8:05 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽* *A͓̽* *B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


*N̸͟͞A̸͟͞*

*R̸͟͞A̸͟͞S̸͟͞H̸͟͞E̸͟͞E̸͟͞D̸͟͞A̸͟͞T̸͟͞* *U̸͟͞S̸͟͞M̸͟͞A̸͟͞N̸͟͞*

*(U̸͟͞m̸͟͞m̸͟͞u̸͟͞ N̸͟͞a̸͟͞s̸͟͞m̸͟͞a̸͟͞h̸͟͞)*



*( ოႩlႩႪႩR kႩiႶႮwႩ)*👸🏻



*Marubuciyar*


*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*
*(Baya hana gamji)*
*Toho*


*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza yar Amana*

Uwa mabada mama k'aunar ki dabanne gare Ni, domin ke d'in shugaba ce dake Adalci ga duk na k'asa dake, Allah ya barmu tare Aunty nah.


*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*P* 3️⃣ ➡️ 4️⃣

Ilu d'an Lami ne da Baffah sai Innar Hansai sukayo ban d'akin da gudu jin ihun Lami, turus suka tsaya sakamakon ganin *INDO* zaune saman katanga sai washe yellown Hak'waren ta take, tana cin dariya, Salallami Innar Hansai ta d'auka cikin Al'ajabin meya kawo INDO ban d'akin su.

" Ke INDO meya kawo ki nan, yau kuma tsiyar taki cikin gida na kika kawo sa, cewar Baffah.

Jin an Kira INDO ne yasa Lami saurin bud'e idon ta, fes kuwa ta sauk'e su kan INDO dake ta famar dariya ta maida su mahaukata, Cikin Haushin INDO Lami tace.

" Amma dai Allah ya isa tsakanina da ke INDO, tsabar rashin mutunci duk k'ofar gidan nan bai isheki sai kin diro ta ban d'aki, baki sani ba koda mutum koko Babu, ki shigo ki sami

Please Login or Register in order to submit comment