Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dashi ba, shi kanshi ya Habeeb ba wai yana zargin ki bane kawai ransa ne ya ɓaci kan cewa yace miki karki dinga shiga ɗakin saida izini kuma yana da gaskiya, ke kuma kika taka masa dokarsa, Allah A'isha bansan wannan Mustafan naku ba, amma na tsane sa, mussaman yanda kike bani labarin tsanar da ya miki."

" Yanzu Zahra meye mafita?"

" Mafita ɗaya ce A'isha kije ki bawa ya Habeeb haƙuri ina da tabbacin kuma zai yafe miki."

" Shi kenan zanje in sha Allah."

" To ki tashi mu koma Class kinga an kaɗa tun ɗazu, kafin malami ya shigo Class."

Tashi Indo tayi suka shige Class ita da Zahra.


" Ina ƙara sanar dake a karo na biyu dan ubanki! Idan har na kara kashe kuɗi na, naje na karɓo miki taimako wajen malami kikayi sakaci dashi, ƙyale ki zanyi kije kisha wahalar, don wannan karon har uwar tasa ba zamu bari ba, naga ƙiyayyar tasa tayi yawa."

RAUDA ce tace.

" Wallahi Mamy wancan lokacin ma ba wasa nayi da shiba nayi iya ƙoƙarina, abunne kawai yaci tura, amma yanxu kam in sha Allah zanyi ƙoƙari."


" Dako kin taimaki kanki, munyi magana da Gambo tace na bari sai anyi Auren muje wajen malamin."


" To Allah ya kaimu Mamy."


________________________________


Fan's kuyi hkr da rashin bin comments ɗinku da banayi kwana biyun nan hakan ta faru ne sakamakon rashin times da banda shi amma ina ganin sharhin kowa kuma ina matukar jin daɗin yanda kuke comments domin kuwa kuna bani ƙwarin gwiwwa.



*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*




*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*



*(Ummu Nasmah ce)*
[2/24, 12:47 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*



👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻


*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*


*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.


*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻

Fan's Kuyi hkr da rashin jina da ba kwayi akai-akai wlh banda time ne sosai.

Masu min sharhi ina mungun jin daɗin sharhin ku domin kuwa yana faranta min rai, kuyi hkr da rashin reply da bana muku, ina mungun sonku irin sosai ɗin nan❣👌🏻


*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*P*•••••••5️⃣3️⃣ ➡️ 5️⃣4️⃣

" Mamy jiya naso tambayan Daddy kuɗin less ɗin nan sai kuma ya fita kafin na tashi."

" Oh kinga nima na manta aida na tambaya miki shi, yanzu kam sai dare kuma idan Allah ya dawo dashi lfy, ni ya Maganar Salma ne da khabeer, har yanzu shuru ko babu wani labari?"

" Hmm! Bari kawai Mamy abun babu daɗi domin kuwa khabeer ya yaudari Salma, ya koma neman ƙawarta Safiya, harma ya tura gidan su an basa."

" Subhanallah! Shi khabeer ɗin ne ya aikata haka, amma gaskiya yayi asara wlh ya cuci yarinyar nan duk irin soyayyar da take masa, to Allah ya saka mata."

" Ameeen dai Mamy amma dai khabeer ya cuci Salma."

" Tashi RAUDA kije ki shirya kixo ki tafi min aiken nan."

Tashi RAUDA tayi tare da cewa "to Mamy" kafin ta wuce ɗakin ta.


Tsaye suke bakin get ɗin makarantar tun ɗazu aka tashi amma driver baizo ya ɗauke su ba su Ishaq sun damu su tafi gida yunwa suke ji, itama Zahra taƙi tafiya a cewar ta, sai anzo an ɗauki Indo kafin itama su tafi, shuru shuru har wajen 3:00pm babu labarin drivern gidan su Indo, hakan ce tasa Zahra duban Indo tace.

" A'ishatu Musa, ya kamata fa ku shigo motar gidan mu, sai mu sauƙeku unguwar ku, mu wuce."

Hararar Zahra Indo tayi tace.

" Yau kuma wani salo kika ɗauko na kiran sunana harda na tsoho na, to muje ku sauƙe mu, bansan uzirin daya hana Idi zuwa ɗaukar mu ba gashi harna bari school bus ta tafi aida mun bisu."

Dariya Zahra tayi tace.

" Ganan motar gidan mu ne zaki hau school bus, aiko har mu gama school ba zamu taɓa hawa school bus ba, dalla! Malama shiga mota mu wuce."

Cikin dariya Indo suka hau motar sannan driver yaja suka wuce, suna tafiya Habeeb na shigowa cikin school ɗin cikin sauri domin kuwa Daddy ya kirasa yace yau Idi driver bazai samu fitowa aiki ba, baida lafiya dan haka koshi ko Mustafa wani yaje ya ɗauko yara a school, fitowa Habeeb yayi yana dube-dube cikin makarantar babu kowa ciki, dawowa yayi wajen mai gadi yake tambayar sa yaushe ɗalibai suka watse, sanar dashi mai gadi yayi cewa

" ai yanxu wasu suka wuce da yara tun ɗazu suke jiran mai ɗaukar su baizo ba, shine naga sun hau motar gidan gomnati, sun tafi maybe ko zasu sauƙe sune a unguwar su."

Ajiyar Zuciya Habeeb ya sauƙe tare da hura iska daga cikin bakinsa yace.

" Okey na gode Baba Bari na koma gidan nagani."

A ƙofar Estate ɗin suka sauƙe su Indo sannan suka wuce suna ɗaga musu hanu, da gudu su Ishaq suka wuce ita kuwa Indo cikin nutsuwa ta shigo, babu kowa cikin falon sai Mustafa shi kaɗai yana kallon ƙwallo, Indo Bata kallesa ba, ta ɗaga kanta ta shige har ta fara haura step ɗin taji Muryar Mustafa yana cewa.

" Keeeeeeee! Ƴar ƙauye."

Murmurshi Indo tayi ba tare data tsaya ba, ta cigaba da taka step ɗin abunta cikin nutsuwa tare da aji, domin kuwa yanxu Indo tasan ciwon kanta, amma har yanzu tana nan da halinta na rashin son raini da wulaƙanci, a karo na biyu taji ya ƙara cewa.

" Keee! Fitinanniyar ƙauyen DASINA, ko bada ke nake Magana bane?"

Juyowa Indo tayi still har yanxu fuskar ta ɗauke da murmurshi tace.

" Na'am mungun cikin birni Sarkin girman kai na cikin gidan su."

Zaro ido Mustafa yayi yana kallon Indo cike da mamakin yaushe ya fara wasa da Indo harta raina sa haka, shi idanunsa ma idan ba ƙarya suka masa ba, gani yake kamar yarinyar tayi fresh ta girma, har wani hips ta ajiye haka ma ƙirjin ta ya ɗan taso, lallai girman ɗan mutum babu wuya, zaro ido yayi cikin tsawa yace.

" Wa! Kike gayawa wannan maganar?"

Cikin rashin tsoro Indo tace.

" Ga wanda ya kira fitinanniyar ƙauyen DASINA dashi nake."

Murmurshi Mustafa yayi yace.

" Eh lallai Bahaushe yayi gaskiya da yace ɗan ƙauye yafi ɗan dako sanin hanyar tashi, tabbas ɗan ƙauye bai iya samun waje ba, sai yafi ɗan gari zaƙewa, ko da yake ai babu damuwa tunda daman haline tunna ƙauye kuma ai daman shi ɗan ƙauye kullum yana cikin jahilci bazai taɓa wayewa ba."

Cikin jin Zafin maganganun Mustafa Indo ta cije laɓɓen ta, ta mayar masa da amsa da cewa.

" Ashe kuwa jahillai suna da yawa cikin gidan nan ina ga zasu iya kai su uku, kaga kenan ai ƴan ƙauyen muna da yawa saimu haɗu muje muta jahilcin" tana gama fad'in haka ta haura da sauri ba tare da ta tsaya ta saurari Abunda Mustafa zaice ba.

Ai kuwa Indo tabar Mustafa cikin tunanin waye ƴan ƙauye jahilai ukun, wannan shine idan baki yasan Abunda zai faɗa baisan me za'a mayar masa ba, ya daɗe yana nazari sai can amsar ta faɗo masa, wato Indo tana nufin *INNA DA DADDY DA KUMA ITA KANTA* lallai yarinyar nan ta faɗa masa baƙar magana wato wai itama ta iya azanci lallai kuwa bashi taci kuma saita biyasa.

Habeeb da sauri ya shigo falon jin hayaniyar su Ishaq a sama shine ya tabbatar masa cewa sun dawo, duban Mustafa yayi yace.

" Wai daman kana cikin gidan nan baka fita ba?"

Mustafa bai dubi Habeeb ba idanunsa na bisa tibi yace.

" Eh yau banda aiki, sai tomorrow, harka dawo kenan?"

" Ba dawowa nayi ba, yanxu zan koma Daddy ne ya kirani yace, naje na ɗauko yara a makaranta shi yasa na dawo."

Indo dake cikin ɗaki sama-sama take jiyo Muryar Habeeb cikin sauri ta fito daga cikin ɗakin Habeeb kamma harya fice, da gudu ta fita itama, kallo ɗaya Mustafa ya mata sannan ya kawar da kansa.

" Ya Habeeb! Ya Habeeb! Ya Habeeb!"

Jiyowa Habeeb yayi tare da tsayuwa har Indo ta ƙaraso ta tsaya a gaban sa tare da haɗa hanunta biyu tayi narai-narai da idanunta tace.

" Dan Allah ya Habeeb kayi hkr na tuba bazan sake ba, wlh zanke jin maganar ka."

Murmurshi Habeeb yayi tare da cewa.

" To sarkin kuka maida hawayen naki ya isa haka, daman so nake ki gane laifin ki da kanki ki gyara kuma kin gane, komai ya wuce."

Dariya sosai Indo tayi tace ya Habeeb na gode sosai in sha Allah kuma bazan sake ba, ya Habeeb ina Aunty Hasina ban ganta ba, nasan dai Aunty Sharifa ta tafi school?"

" Hasina taje gidan su sai next week zata dawo."

Ɓata ranta Indo tayi tace.

" Shine ta tafi kota jiran na dawo muyi sallama, gidan bazai min daɗi ba tunda babu Aunty Hasina."

Murmurshi Habeeb yayi tare da cewa.

" Haba Mamana ai next week kamar yanxu ne, karki damu kinji idan na dawo zamuje gidan nasu."

Dariya Indo tayi sannan ta koma ciki shima Habeeb ya wuce nasa wajen aikin.


Hausawa sunce sannu sannu bata hana zuwa saidai a daɗe ba'aje ba, cikin wata huɗu su Mustafa suka gama ginin gidan su na a gani a faɗa, domin kuwa gidan ya amsa sunan sa gida, Momy itace da kanta ta haɗa kayan Auren su, komai Momy itace da ƙawarta Hajiya Ruƙayya suka haɗa sun kuma haɗa musu kayan aure masu inganci Atampopi da less a shagon Daddy aka ɗauko su, sauran kaya kuma a kasuwa suka saya set ɗin akwati ma kowacce 12 aka mata, shidai Mustafa duk wannan Abunda ake baya gabansa domin kuwa shi mantawa ma yake da wata RAUDA bare kuma yayi tunanin zaiyi Aure, haka Itama Indo duk abunda ake akan harkar bikin babu ruwan ta ciki, bai kuma dameta ba, saima murna da take ya Habeeb ɗinta zaiyi Aure, RAUDA kuwa tunda taji labarin za'a kawo kayan Auren ta ranar talata take rawar kai ita da mahaifiyarta.

Ranar talatar kuwa Momy ta gayyaci ƴan uwa da abokan arziki aka kai kaya gidan su RAUDA, Mamy da ƙawayen ta, da ƴan uwa sai buɗe kayan suke suna son barka, tsakanin ta da Allah Mamy take guɗa tana cewa RAUDA tayi goshi, bayan kowa ya watse daga gidan Mamy da RAUDA suka nutsu suna kallon kayan duba Mamy RAUDA tayi tace.


" Ikon Allah Mamy ko a mafarki ban taɓa zaton cewa ya Mustafa zai aure ni ba, sai gashi cikin ikon Allah wai wannan kayan aure nane nake gani gaba na wanda ya Mustafa, sai dai kullum tunani nake wani irin zaman Aure zanyi da ya Mustafa, Mamy baya soni ko kaɗan cikin rayuwar sa, nasan wannan auren nawa da zaiyi umurnin Momy kawai yabi ya kuma sanar dani cewa rayuwar kabari sai yafi min daɗi fiye da rayuwar gidan sa, ina tausayin kaina Mamy."

Tsuka mai ƙarfi Mamy taja tana duban RAUDA tace.

" Kuma sai aka ce miki tsayawa zanyi ina kallon ana walaƙanta ki kullum ina gaya miki cewa bazan taɓa bari Mustafa ya wulaƙanta ki ba, domin kuwa saina mayar miki dashi kamar tandar waina zaki juya sa cikin son ranki, dan haka ki daina saka damuwa cikin ranki lokaci kawai nake jira nayi maganin sa."

Duban Momy RAUDA tayi tare da cewa.

" Mamy bana son ace da asiri nake neman Soyayyar Mustafa, Mamy jiya na karanta wani Novel mai suna *Sara da sassaqa* Mamy na tsorata da soyayyar da ake neman ta da asiri, domin kuwa baya tasiri, komi jumawa asirin zai karye Mamy wannan littafin dana karanta ya ƙara min haske mu daina asirin nan Mamy mu nemi Soyayyar Mustafa da addu'a, nikam Mamy har ga Allah ko kinje wajen malami bazan yi amfani da maganin ba."

Duka Mamy ta kawowa RAUDA tana cewa.

" Dan ubanki ance miki Abunda ake faɗa cikin Novel gaskiya ne da har zai sanyaya miki jiki duk ƙarya ne kuma dan ubanki sai naje wajen malami kuma dole kiyi amfani da shi."

" Mamy Wlh gaskiya suke faɗa kuma wlh haka ne abun yake kasancewa ni dai Mamy wlh ba zanyi amfani dashi ba, domin kuwa ina son ya Mustafa bana son ace gaba zai rabu dani......"


________________________________

Mu haɗu next Page wlh da ƙyar na samu nayi wannan typing ɗin, ina school kuma gashi banjin daɗin jiki na.


*Vote*
*Share*
*And*
*Comment*


*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*


*(Ummu Nasmah ce)*
[2/25, 10:23 AM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*



👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻


*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*


*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.


*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻


*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*P*•••••••5️⃣5️⃣ ➡️ 5️⃣6️⃣

Cikin masifa da bala'i Mamy ta taso tayo kan RAUDA da zagi.

" Dan ubanki! Ni kike gayawa Allah to tun kafin a haifeki na sansa, kuma shi wannan asiri da kike cewa baya tasiri, to shima ubanki dashi na gama samun kansa, meyasa nawan har yanzu bai karye ba, tashi ki bani waje dan ubanki shegiya marar zuciya wai ke ga mai soyayya, to ki biye soyayya kisha wahala har kina kira min wai wani kin karanta novel kin tsorata da harkar malamai."

Ita dai RAUDA tashi tayi ta shige bedroom ɗinta ba tare da ta kula Mamy ba, mita mami ta dinga yi ita kaɗai tana cewa "ita kanta RAUDA ma, zata ci ubanta tunda ita ƴar Soyayya ce, shegiya mai son maso wani, kina sonshi yana tsangwamar ki, amma tsabar rashin Zuciya kice kina tausayin sa."

_______________________________
Kallon Hasina Momy tayi tace.

" Hasina kinga kayan naki sunyi ko?"

Murmurshi HASINA tayi tace.

" MOMY ai ba sai na gani ba duk abunda kuka saka ai sunyi kyau, jiya ma Ammi ta kiran tace zasu zo next week tunda bikin saura one month."

" Eh ta sanar dani munyi waya ai jiya, har take.........

Shigowar Indo da gudu ne ya sasu maida hankalinsu gareta tana haƙi ta sun kuya gaban Momy tana kuka tana cewa.

" Momy! Inna Momy! Inna" tana maganar tana nuna ɗakin Inna cikin tashin hankali.

Tashi Momy tayi tana cewa.

"Meya samu Inna, ki faɗa min mana?"

Hasina ce tace.

" Momy muje muga menene yake faruwa" ai kuwa cikin sauri suka shiga cikin ɗakin tana kwance sau ɓari jikinta yake yi hancinta kuma sai fitar da jini yake, idanunta kuma sun ƙafe sai rawar sanyi take, cikin tashin hankali Momy ta kira Daddy tana sanar dashi, Hasina ce da tayi nisan Hankali ta kira Habeeb a waya kasancewar sa babban likita, cikin minti talatin suka shigo cikin gidan Habeeb Daddy Mustafa, a gigice sukayi Hospital da ita, take akayi emagency da ita Habeeb da doctor Ibrahim sune akan Inna, su Daddy duk suna tsaye suna jirin fitowar su, sun kusa 2 hours kafin aka fito da Inna zuwa ɗakin hutu, Habeeb duk ya haɗa gumi cikin tashin hankali, yake duban Indo domin ita yake tausayawa yanda take ta famar sharɓar kuka harda majina, Daddy ne da Momy sukayi kan Habeeb suna tambayar ya jikin Inna, jikin sa a sanyaye ya dubesu yace.

" Da sauƙi Daddy tana ɗakin hutu amma karku shiga tukunna saboda tana buƙatar hutu mun mata allurar bacci" Daddy da Mustafa ya duba yace" Daddy muje office ." Bin bayansa sukayi suma cikin sanyin jiki, Bayan sun zauna ne Habeeb ya fara magana.

" Daddy ko kasan Inna tana ɗauke da ciwon jeji kuwa, ma'ana (conser)?"

Cikin tashin hankali Mustafa yace.

" What conser fa kake faɗa anya kuwa binciken ku ya baku dai-dai kuwa?"

Shi kuwa Daddy ajiyar Zuciya ya sauƙe tare da cewa.

" Yes tana dashi amma gaskiya ya daɗe da barin jikinta tun kafin na baro ƙauyen mu?"

" Daddy bai bar jikin ta ba, saima ƙara ƙarfi da yayi a jikinta, Daddy meyasa baka kai Inna hospital ba, domin a dinga mata check up, tunda kasan tana da wannan mummunan ciwon, kuma yana da hatsarin gaske."

Mustafa ne ya dakatar da Habeeb da cewa.

" Please Malam ka daina mana Maganar baya, kayi mana bayanin Abunda ke faruwa yanzu meye kuma solution?"

Iska Habeeb ya hura daga bakin sa yace.

" Inna tana cikin step ɗin da mawuyacin abune ta ƙara sati ɗaya a duniya domin kuwa, ya tsinka mata hanjin ta, gashi kuma ya taɓa mata huhu so Daddy babu wani solution, sai dai muta addu'a akwai kuma maganin da zamu ɗaura ta, akai amma ba wai lallai bane yayi amfani a jikin ta."

Wasu hawaye ne masu zafi suka zubo a fuskar Mustafa tare da jingina kansa jikin kujerar yana furta.

" Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un Allahumma ajirni fil musibati! Wacce irin ƙaddara ce ta faɗo kan Inna, yanxu Inna ce take cikin wannan tashin hankalin Habeeb yanzu babu yanda za'ayi koda ƙasar waje a fitar da ita, wlh zan iya sadaukar da dukiyata gaba ɗaya muddun za'a ceto rayuwar Inna, please Habeeb ka taimaka karmu rasa Inna."

Duban Mustafa Habeeb yayi shima idanunsa sun ciko da hawaye yace.

" Bros banda wani solution wlh ko ƙasar waje aka fitar da Inna bazata wuce wannan lokacin ba, tabbas Ubangiji shine wanda yasan iya rayuwar mutum a duniya babu kuma wanda yasan ranar mutuwar wani, amma ciwon Inna yana nuna cewa bazata haura wannan kwanakin ba, domin kuwa hanjin ta yayi damege ga kuma huhunta ya samu matsala shima, amma zan kira doctor John naji tunda shi babban likita ne cikin ƙasar Indiya."


" Yauwa ka kira sa, Allah yasa a dace."

Daddy kuwa yayi shuru yama rasa me yake masa daɗi, baya kallon laifin kowa sai na mai bawa Inna maganin gargajiya a ƙauye domin kuwa yasan mahaifiyar sa tana da wannan mungun ciwon, yayi la'akari da cewa ta warke tuntuni sakamakon maganin gargajiya da take amfani dashi, hakan yasa mahaifinsa yace Inna ta warke inji mai basu maganin kuma tun daga lokacin ciwon bai ƙara tashi ba, hakance tasa suka ɗauka da gaske ta warke, ashe Inna bata warke ba, ɗaga Hanun sa Daddy yayi sama yana cewa.

" Ya Allah kaine wanda ka ɗaurawa mahaifiyata wannan ciwon ya Allah idan wannan ciwon na sauƙi ne, Allah ka yaye mata, idan kuma na tafiya ne Allah ka bata sa'ar tafiya cikin sauƙi ka kuma gafarce ta" cikin hawaye Daddy ya ƙarasa Addu'ar kafin ya dubi ƴaƴan nasa yace " kuyi hkr kusa Inna cikin Addu'ar ku Allah ya zaɓa mata abinda yafi zama Alkairi cikin wannan ciwon rayuwa ko mutuwa, Habeeb ka tambayi likitan duk yanda kukayi ka sanar dani, sannan bana son ku sanar da mahaifiyar ku da ƙannan ku wannan maganar kunsan su mata ne, Zuciyar su bata da ƙarfi."

Da to suka amsa kowa jikinsa yayi sanyi, haka suka fito, Habeeb hanun Indo ya kama suka zaune gefe yace.

" Wai kukan me kike haka ne, bayan jikin Inna da sauƙi har ta samu bacci."

Cikin kukan ta dubi Habeeb tace.

" Ya Habeeb jinin meye yake fitowa daga hancin Inna, kuma sai rawar sanyi take, ya Habeeb haka Jummalo tayi rawar sanyi da zata rasu, bana son Inna ta mutu ta barni ina sonta ya Habeeb."

" Wa yace miki Inna zata mutu, Inna bazata mutu ba, muna tare da ita zata samu sauƙi mu koma gida muyi rayuwar mu tare, ki share hawayen."

Goge hawayen Indo tayi tana ɗan dariya Habeeb yace Inna zata warke, ɗakin da aka kwantar da Inna Habeeb ya shiga ya dubata har yanzu tana Bacci bata farka ba, fitowa yayi yace zasu iya shiga amma banda hayaniya, da gudu Indo ta shiga kafin su Momy suka shigo, gefen Inna Indo ta zauna tare da kifa kanta dai-dai fuskar Inna tana kallon ta, ta kuma riƙe hanunta, shima Mustafa gefen Inna ya zauna tare da rike ɗaya hanun nata yana tofa mata addu'a, haka suka kasance har ƙarfe biyar na yamma Kafin Inna ta farka kuma a nutse ta farka, bin kowa take da kallo tare da ƙarewa ɗakin kallo, Indo ta duba ta dubi Mustafa da Habeeb, sai hawaye ya zubo mata hanun Indo ta ƙara danƙewa tana murmurshi mai haɗe da kuka cikin ƙarfin hali tace.

" Indo kinyi kuka ko? gashi idanunki sunyi jajur, ki daina kuka zan samu Lafiya kinji."

Girgiza kansa Habeeb yayi cikin tausayin halin da Indo zata shiga idan ta rasa Inna domin kuwa Rayuwa bazata mata daɗi ba, babu Inna.

" Inna da gaske zaki tashi bazaki mutu ki barni ba? Dan Allah Inna karki mutu kinji."

Murmurshin ƙarfin hali Inna tayi tace.

" Mutuwa ai dole ce babu wanda zai hana kansa mutuwa idan lokacin sa yayi" Mustafa ta kalla daya sunkuyar da kansa yayi shuru cikin damuwa, dukan kafaɗar sa Inna tayi cikin wasa duk dan ta basu ƙarfin gwiwwa su daina shiga cikin damuwa tace " kai kuma Sarkin baƙin rai me yake damunka? Kaima baka so na mutun ne, to ai mutuwa dolece akan duk wani ɗan adam, amma dai bazan mutu ba, saina ga auren ka, nasan shine damuwar ka ko?"

Wannan karon Mustafa bai ɗago kai ya kalli Inna ba, domin kuwa yasan suna haɗa ido da ita dole sai hawaye ya zubo masa cikin idanunsa, tashi yayi cikin sauri ya fice daga ɗakin, duban Habeeb Inna tayi tace "zo Habeeb kusa dani muyi magana" matsowa Habeeb yayi kusa da Inna ta dubi su Indo da Momy tace su fita zatayi Magana da Daddy da Habeeb, fita sukayi ya saura ɗakin daga Inna sai Habeeb da Daddy, duban su tayi ta fara magana.

" Amana nake son na baku, dan Allah ko bayan rayuwata karku bari Indo ta walaƙanta ku kula da ita ku riketa amana kamar yanda zaku riƙe ƴaƴan ku, idan har kuka bari Indo ta wulak'anta bayan rayuwata to nice kuka wulaƙanta idan har kuka bari hawaye na baƙin ciki ya zuba fuskar Indo to hawaye nane ya zuba, ku kula da rayuwar ta, ku bata farin ciki idan ta kauce daga hanya ku dawo da ita kan hanyar dai-dai ina ji a jiki na bazan rayu ba, naso ace na rayu har naga ƴaƴan Indo, amma Ubangiji na bai nufi hakan ba, Haruna ku dinga kai Indo ƙauye tana gaishe da iyayen ta sannan cikin Habeeb ko Mustafa ka Aurawa ɗaya a cikin su Indo karka umarni ne wannan, bana son wani ya auri Indo ba ɗaya daga cikin su ba, wannan itace amanar da zan baku idan Hindu ta zo bayan raina ku bata Indo ta tafi da ita kafin zafin mutuwata ta fita daga zuciyar ta, sai ku dawo da ita cikin gidan ka, nasan matar ka A'isha bazata kula da Indo ba shiyasa ku na baku amanar ta."

Ga baki ɗayan su hawaye ne yake gudu saman fuskar su, murmurshi Inna tayi sai kuma ta fara tari tare da jini cikin bakin ta, gabaki ɗayan su kalmar shahada suka ɗauka, bakin su Inna

Please Login or Register in order to submit comment