Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kai ina bazata gane ba domin soyayyar da nake yiwa Indo batayi ƙarfin da za'a ganeta cikin sauƙi haka ba, kawai ta faɗa ne cikin wasa" Kafin ya maida dubansa gareta cikin waskewa yana dariya yace.

" Idan kina buƙatar haka aini a wajena babu laifi, kawai sai kije ki nema min Soyayyar ƙanwata kinga shikenan na zama ɗan gata, nasa ƙannena a tsakiya nake kallon ku ina walwala."

Murmushi yaƙe HASINA tayi domin kuwa ita tuntuni ta gama ganewa cewa Habeeb son Indo yake, cikin rashin nuna damuwa tace.

" Ai kuwa zanje ka amsa cewa kana sonta kaga idan banje na nemo maka Soyayyar ba, nasan kuma da wuri zata amsa domin kuwa mijina ajin farko ne babu macen da zatace bata sonsa, nasan kuma mijina mai adalci ne akan komai, dole kuma naso Abunda mijina yake so, domin farin cikin sa shine nawa" ta karasa maganar tana murmurshi tare da kanne masa Ido.

Sanyi ƙalau jikin Habeeb yayi tare da jin wani irin kunyar HASINA, tabbas Hasina matar soce itace ake ƙira da matar rufin asiri mai danne damuwar ta, domin farin cikin mijinta, anya kuwa zuciyata kin min adalci da kike neman haɗani da matata mai ƙaunar ganin farin ciki na, tabbas da ana iya cire Soyayya da ƙarfi cikin Zuciya to dana cire soyayyar Indo cikin zuciyata, domin kuwa Hasina bata cancanci kishi da Indo ba, tashi Habeeb yayi daga cinyar Hasina yana cewa.

" Wato ko kishi na baƙya yi, shikenan saiki ɗebi ƙafa kije nema min Soyayya, saboda ki nunawa duniya baƙya sona, shikenan aina gane matsayina a wajen ki tunda har neman kai kike dani" yana gama faɗin haka ya wuce bedroom ɗinsa yana haɗa fuska shi a dole yaji haushi matarsa , bata kishin sa.

Murmushi HASINA tayi tana dafe ƙirjin ta, cikin zuciyarta take cewa " nafi kowa kishin ka, mijina sai dai Soyayyar da nake maka bazai sani tauye maka haƙƙinka ba, ina maraba da duk abunda zaka kawo a matsayin kana sonsa, zan kuma tayaka sonsa koda zuciyata bata so hakan ba' tashi tayi tare da shigewa kitchen itama domin gabatar da Abincin Rana.


Zaune take ta haɗa uban tagumi, tayi baƙi ta rame bata da abunyi kullum sai tunanin rayuwar aurenta da sam bata jin daɗin sa, " anya kuwa Mustafa yana tsoron Allah wani irin ƙiyayya yake mata, bata masa gwaninta komai tayi a kushe yake, kullum yana cikin mata faɗa anya kuwa bazan sanar da Mamy halin da nake ciki ba ko zan samu mafita, sai kuma wata Zuciyar tace mata, a'a karki fara sanar da ita domin kuwa bata da wata mafita data wuce na wajen malamai kiyi hkr ki cigaba da zama da mijinki a haka har Allah ya kawo miki ƙarshen wahalar ki" tana cikin tunanin ne taji Muryar sa yana cewa.

" Kee! An kawoki cikin gidan nan ne domin ki share gindi ki zauna, ki tashi ki fita ki wanke min mota tayi datti ina son zan fita yanzu, maza na baki 30minute Kuma Wlh kika haura koda 5 minute ne, zaki gane kurenki a waje na, badai kince Aure na kika zaɓa ba, dole kuma ki bauta min shashasha mayya kawai."

Runtse idonta RAUDA tayi da ƙarfi wasu zafafan hawaye na gudu bisa fuskar ta tana jin wani zafi cikin ƙirjin ta, kafin ta buɗe idanunta tana duban Mustafa tace.

" Haba Ya Mustafa ganan masu wanke motoci cikin gidan nan, ni kuma meye zai haɗani da wanke mota, yanzu fa na gama maka wanki na share compaunt ɗin gidan nan yanzu na zauna ko hutawa banyi ba, kuma yanzu kace naje na wanke idan mutane suka shigo suka ga ina wankin mota me zance musu gani nake kamar ba mutunci na bane."

A fusace Mustafa ya yo kan RAUDA yana cewa.

" Uban waye ya tilasta miki Aure na daman an faɗa miki cewa kina da mutunci ne, to bari kiji na gaya miki duk abunda ya kasance nawane cikin gidan nan, dole ne sai kin bauta masa domin kuwa ke baki da wani banbanci da karen cikin gidan nan kinga kuwa aishi kare baida mutunci dan haka Babu ruwana da wani amsar da zaki bawa mutane, ki fice kije ki wanke min mota zan fita kafin ki hasala ni, Wlh na miki ɗan banzan duka kuma ki wanke dole *ai daman na sanar dake cewa zaman kabari sai yafi miki wannan zaman gidan nawa daɗi, kikace kinji kin gani, kinga kuwa ke kika jawa kanki*"

Sanin halin Mustafa yasa RAUDA ficewa daga falon cikin takaicin abubuwan da Mustafa yake mata na rashin mutunci ko kunya baya ji wajen motar ta nufa tana zubar da hawaye tana fita shi kuma ya jawo system ɗinsa, pictures ɗin Indo ne, wanda Habeeb ya taɓa ɗaukar ta sanda yaje dasina ya turo masa ta whatsapp, tare da video, murmurshi ya sake yana duban pic ɗin tare da danna video dariya sosai Mustafa yake yana kallon shiriritar Indo na da, A fili ya furta *MY SHATUU NA INA MATUƘAR KAUNAR KI HAƘIƘA SONKI YA DAƊE A CIKIN JININA DA TSOKA TABBAS KECE RAYUWATA, NASAN KUMA KEMA NINE RAYUWAR KI, DOMIN KUWA NASAN KO YAUSHE NINE MAƘALE CIKIN ZUCIYAR KI, KINA MIN SON DA BAKYA YIWA KANKI NI NASAN WANNAN, LOKACI KAWAI NAKE JIRA NA BAYYANA MIKI SOYAYYA TA, I LOVE SHATUUU NA*" ya ƙara sa maganar kamar wacce Indon take kusa dashi yana sakin murmurshi, cikin shauƙi da annashuwa.

Ita kuwa RAUDA Allah daya taimake ta har ta gama wankin motar babu wanda ya zo ya ganta sai mai gadi cikin sauri ta shiga cikin falon sanda ta isa daf dashi tace.

" Ya Mustafa na gama wankin motar"

Yana jinta yayi shuru bai kulata ba, sanda tayi magana kusan baki uku sannan ya ɗago kansa tare da duba agogon hanunsa, ganin da yayi ta gama da wuri Kafin ma time ɗin daya sa mata ya cika ya ɗago tare da cewa.

" Na fasa fita da ita ki koma ki wanke min farar da take gefen waccar ɗin da ita zan fita"

Wani irin baƙin ciki ne ya zowa RAUDA wuya gagara Magana tayi domin kuwa tasan tana buɗe baki kuka ne zai kwace mata, juyawa kawai tayi da gudu ta fice daga falon, shi kuwa wani murmurshin mugunta ya saki tare da furta " kaɗan ma kika gani ba kince ke mayya bace to mu zuba mu gani waye zai gaji tsakanin ni dake."


Wanke motar kawai take lokaci zuwa lokaci tana goge hawaye, kamar daga sama Indo ta faɗo cikin gidan, har zata wuce kamar wadda akace ɗago idanunki, sai ta hango RAUDA sai famar wanke mota take, ƙara leƙawa Indo Tayi domin tabbatar da gaskiyar Abunda idanunta yake gane mata, tabbas kuwa RAUDA ce, taɓe bakin ta Indo tayi tasa kanta da niyar shigewa part ɗin Habeeb sai kuma taji bazata iya wucewa ba sai taji Abunda yasa RAUDA wankin mota Bayan kuma ga mai wankin motar a cikin gidan, nufar wajen Indo Tayi tare da Sallama, ɗago idanunta RAUDA tayi da sukayi jawur tabbacin sunci kuka ta amsar sallamar, karo na farko da Indo ta fara kiran RAUDA da Aunty tace.

" AUNTY RAUDA, lafiya kike wanke mota da kanki bayan ga mai wankin a cikin gidan?"

Murmushin da yafi kuka ciwo RAUDA tayi tace.

" Ehh Wlh haka kawai yau nake son wankewa mijina motar da zai fita da kaina, shima sanda yace min na bari baya so na wahala , yanzu ma yana tollet baisan na fito ina wankin ba, ya su Aunty Hindu naji ance kina wajenta yanzu."

Shuru Indo tayi badan ta yarda da maganar RAUDA ba domin tana da masaniyar cewa Mustafa baya son RAUDA a Dole ya aureta, tasan kuma halin muguntar sa, sarai zai iya sata wankin motar ma, cewa tayi.

" Ayya to kawo na tayaki ki samu ki gama da wuri Kafin ya fito daga wankan"

" A'a ki barsa kawai Indo YANZU zan gama ai nama kusa"

Murmushi kawai Indo tayi tare da sunkuyawa ta ɗauki tiyo ɗin ruwan tana cewa, ki dinga wankewa ni zan dinga zuba miki ruwan, haka kuwa sukayi RAUDA na wankewa Indo na zuba mata ruwa.

Tashi yayi daga zaunen da yake tare da zuwa bakin window domin ganin halin da RAUDA take ciki, fes idanunsa suka sauƙa kan Indo da suke wankin mota tare da RAUDA, zaro idanunsa yayi tare da cewa.

" What INDOn tasa wankin mota Lallai wannan YARINYAR ta raina ni, ta rasa wa zata saka aiki sai *SHATUU NA* lallai kuwa yau zaki gane kurenki cikin gidan nan"

fitowa yayi a matuƙar harzuƙe ya nufosu yana huci..........



Please bazan gaji da cewa kuyi hkr da yanayin typing ɗina ba, ban samu ina muku typing kullum hakan ta faru ne sakamakon makaranta daya sani gaba🙏🏻


*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*



*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*





*(Ummu Nasmah ce)*💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*



👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻


*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*


*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.


*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah! Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin taliƙai daya bani lafiya cikin ikon sa da hikimar sa, Gaskiya masoyana bansan da wani irin baki zan muku godiya da nuna farin ciki na gareku a bisa addu'oin ku gare ni, naji daɗin yanda kuka nuna kulawa gareni wanda suka kiran a waya tare da text message gaskiya bazan iya lissafa yawan ku, na gode sosai Allah ya bar zumunci.*


*ZULAIHAT MUSA GARBA* Na gode ƙwarai da Alkairin ki gareni Allah ya bar ƙauna.


*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________


*P*••••••7️⃣3️⃣ ➡️ 7️⃣4️⃣

" Keeeeeeee RAUDA!"

Ya furta da ƙarfi tun kafin ya ƙaraso wajen, a matuƙar tsorace ta juyo tana kallon sa, domin kuwa tasan wannan kiran da yake mata babu Alkairi a cikin sa, itama Indo juyowa tayi tare da haɗa fuska tamau tana kallon sa, domin kuwa yau da shirin ko ta kwana tazo gidan yana mata mugunta zata rama wlh.

" Uban waye ya saki bata wankin mota?" Ya karasa maganar yana nuna mata Indo.

RAUDA bakinta na rawa tsabar tsoron sa tace .

" Bani na bata ba itace tace zata tayani shine ta ɗauki tiyo nike wankewa ita ruwa kawai take zuba min ba wani aiki mai wahala take min ba."

" Jakar gidan ubanki ne da zaki bata aiki ko ruwan da take zuba miki shima ba aiki bane koko cewa nayi kije ki nemi wanda zai taya ki raguwar banza raguwar wofi"

"Daman za'a rina nasan kaɗan daga cikin muguntar sa baƙin azzalumi" Indo ta furta cikin zuciyarta Da ƙarfi ta furta masa cewa.

" Kaiiiiiiii! Kaiiiiii! Zaginki fa yake kina jinsa kin sunkuyar da kanki ƙasa bazaki rama ba, uba fa baifi Uba ba, kinyi shuru kina jinsa ai Wlh duk wanda baiji kunyar zagin ubanka ba to kaima karkaji kunyar zagin nasa Uban domin kuwa kowa yana son nasa Uban ke kuma kinyi shuru kina jinsa yana zage miki Uba."

Ita dai RAUDA bata ce MUSU komai ba ta cigaba da wankin motar amma cikin zuciyarta tana jin zafin abinda Mustafa yake mata har tana jin kamar ta rama.

Shiko Mustafa Duban Indo yayi tare da cewa.

" Allah ko rasa kunya ɓerar tanka to Ko zaki rama mata ne, idan zaki rama mata to bismillah ƙaramar marar kunya taho ki rama mata nace ."

Taɓe bakin ta tayi tare da cewa.


" Akan me zan rama mata, kunfi kusa ƙauye da haɗeja matar kace tunda ita tace bata da Zuciya ai shikenan sai taje tata haɗiyar baƙin ciki amma wlh dama ni mutum ya zaga Wlh babu abunda zai hanani ramawa, tunda shi mutum baƙin azzalumi ne mungun gaske wanda matar sa ma bazai raga mata ba, ni dai daga yau na daina tsoron ka, *NA DAWO MAKA INDON ƘAUYEN DASINA DA KA SANI A BAYA YANZU BABU BARIN BASHI KANA MIN YASIN ZAN RAMA NA DAINA TSAYAWA KANA ZALUNTA NA BABU GAIRA BABU DALILI*, Aunty RAUDA ki ja masa Allah ya isa tunda kina tsoron ki rama ya kasheki Allah ya miki sakayya mungu kawai mai cin zalin mutane." Tana gama faɗin haka ta juya a guje tayi part ɗin Habeeb tana murguɗa masa baki.

Murmushi kawai Mustafa Yayi domin kuwa duk kalma ɗaya data fito daga bakin ta wani sanyi yake ji take masa cikin kunnen sa da zuciyarsa, sanda ya gama murmurshin sa yaga ta ɓacewa ganin sa kafin ya kalli RAUDA data zuba masa yace.

" Sai ki ƙarasa wankin ai kin zuba min ido kamar zaki cinyeni nama ɗanye."

Kauda kanta kawai RAUDA tayi sannan ta maida hankalin ta ga wanki shi kuma ya juya ya fice zuwa part ɗin Momy yana murmurshi, ajiyar Zuciya RAUDA ta sauƙe tare da neman sauƙi cikin rayuwar Auren ta wajen ubangi.

Faɗawa ɗakin tayi kamar wacce aka jefota tana dariya tare da haki.

"AUNTY HASINA! AUNTY HASINA!"

Fitowa Hasina dake cikin kitchen Tayi tana cewa.

" Muryar wa nake ji kamar ta Indo kodai kunnena yake min ƙarya."

Dariya Indo dake zaune bakin kujera tayi tace.

" Ni ɗin ce dai Kinsan Ammi ce ta aiko ni wajen Momy shine na fara shigowa nan kafin na ƙarasa Wajen MOMYN yau dai nazo naga Aunty na kafin na wuce."

Hararar ta Hasina tayi tana cewa.

" Wato ma ba zuwa min kikayi na musamman ba, Albarkacin aiken Ammi naci kika ratso min, lallai Indo kirkin ki yayi over to ki tashi ki koma na yafe gaisuwar tunda bani da darajar da zaki kawo min ziyara."

Cikin shaƙiyanci da dariya Indo take cewa.

" Please sorry my AUNTY na my sweetie na my hantata my tsokar jiki na, kinsan dai bama haka dake, zanzo ne mu kwana biyu next week kiyi hkr."

Zama Hasina tayi tare da cewa.

" Ƙarya kike babu wani zuwan da zakiyi mu kwana biyu, hakanma da kika zo na gode miki badan halin kiba."

Dariya kawai Indo Tayi Kafin suka cigaba da hiran duniya da Hasina sun ɗan juma kafin Indo ta tambayi ya Habeeb sanar da ita Hasina tayi cewa yana bacci har Indo ta fito daga cikin gidan Habeeb bai tashi ba, Hasina kuwa har bakin get ta rakata, wannan karon Indo bata ga RAUDA da Mustafa ba, haka kuma bata sanar da Hasina Abunda ya faru ba, saka hanunta Indo da zatayi ta buɗe get ɗin idanun Hasina suka sauƙa kan zoben da Habeeb ya bawa Indo, Ras gaban Hasina ya faɗi (idan ba ta ɓata gani ba kamar Habeeb yana da Wannan zoben exactly a hanun sa, *H$A* me waɗannan kalmomin suke nufi idan zargina ya kasance gaskiya yana nufin *HABEEB & A'ISHATU* innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un tabbas Habeeb son Indo yake na shiga Uku sai kuma tayi saurin cewa Auzubillah")tayi saurin koran sheɗan dake shirin mata haɗuba tare da cewa Indo.

" Ki gaishe da Ammi da Abbah idan kin koma naji ya Habeeb na cewa next week zasu koma Egypt ko"

" Zasu ji ba next week sai ƙarshen watan nan, dan sai munje Dasina mun dawo ma"

" Okey Allah ya kaimu kya gaishe su"

" Zasuji"

Indo ta furta tare da ficewa daga cikin gidan, ta nufi part ɗin Momy DARECT sallama tayi carap taji Muryar sa ya amsa mata da cewa

" amin Wa'alaikimussalam ƴan Mata har kin gama gudun kinzo kin sameni."

Zaro ido Indo tayi tasan tabbas sai ya ci ubanta cikin gidan nan, gashi kuma babu halin juyawa Momy na cikin falon, wani mungun murmurshi Indo ta saki tuno yanda Momy ke son RAUDA gashi kuwa yanzu ya gama gana mata azaba harda zagin uba, ai kuwa cikin mugunta tace.

" Allah ya baka hkr ya Mustafa gani nayi gaskiya na faɗa maka bai kamata ka dinga sa Aunty RAUDA wankin mota ba, sannan kuma ai zagin da ka mata bai dace ba ka zagi ubanta, duk wanda ya zagi uban wani kuma malamai sunce nasa Uban ya zaga" ta ƙarasa maganar tana maida dariyar ta ciki tare da kallon action ɗin Momy.

Zaro ido Mustafa Yayi cikin tsoron Indo da mamaki ta " wato dai shi mai hali baya fasa halinsa sai dai ya ɗauki hutu tana nan dai a Indon da ya sani ta ƙauye har yanzu, ko kafin ya gama maganar zucin nasa ya jiyo hargowar Momy tana cewa.

" Ke ƴar nan waida gaske ne abunda kike faɗa, RAUDA ya yiwa wannan ɗiban albarka haka wankin mota"

" Kwarai kuwa Momy idan ƙarya nake kije ki tambayeta kiji ko ki tambayi mai gadi kiji tana wankewa yana zagin ta, shine danna faɗa masa gaskiya yake neman cin zalina nima."

Ta ƙarasa maganar tana dariyar zuci, duban Momy Mustafa Yayi tare da cewa.

" Karki yarda da maganar ta Momy ƙarya take wannan ma ai ba Maganar da hankali zai ɗauka bane taya zansa mace wankin mota Bayan kuma ga mai wankin motar, idan ma babu mai wankewa ai nima zan wanke kayana, amma kuma tunda tace kije ki tambayeta to bari na kira miki ita tazo sai ki tambayeta"

Ya ƙarasa maganar yana duban Indo yanda Momy bata gansa ba ya kanne mata Ido domin kuwa yasan RAUDA bazata taɓa cewa shine ya sata wankin Mota ba.

Zaro ido itama Indo tayi tana kallon Mustafa daya dage yake ƙaryata ta akan gaskiyar ta, ita kuwa Momy dukkan su dubansu take kafin tace.

" Nifa daman bawai na yadda da maganar wannan *HATSABIBIYAR YARINYAR BANE* nasan kaɗan daga cikin sharrin ta taga ta haɗa tsakanin ɗa da uwarsa kuma ta Allah ba taki ba munfi ƙarfin ki."

Wani irin ƙuna Zuciyar Mustafa take jin kalmar da Momy take kiran Indo dashi marar daɗin ji ya rasa menene Indo ta tsarewa Momy a Rayuwa da ta tsaneta haka, ita kuwa Indo bata damu da kalmar Momy ba saboda ba yau ta fara zaginta ba, juyawa kawai tayi ta fice daga cikin gidan ba tare data isar da sakon da Aunty Hindu ta aiketa ba, duban Momy Mustafa Yayi yace.

" Haba Momy haba Momy meyasa kika tsani YARINYAR nan ne haka, Momy ƙiyayyar da kike gwada mata yayi yawa pls ki sassauta wannan ƙiyayyar, saboda baki san me zata zama a gareki gaba ba, duk ɗan adam da kika gani yana da ranar da zai maka wata rana."

Cikin masifa Momy take cewa.

" To ubana yimin wa'azi kaji, wannan YARINYAR banzar bata da wani rana da zata min cikin Rayuwata yarinyar da bata yiwa iyayen ta rana ba saima gagarar su da tayi suka kawo mana masifa cikin gida ni ranar me zata min bana buƙatar Ranar ta."

Mustafa ya buɗe baki da niyar Magana kenan yaji gyaran Muryar Daddy a bayan su hakanne ya sashi fasa maganar da zaiyi tare da cewa.

" Barka da fitowa Daddy"

" Yauwa barka, kana nan kenan"

" Ehh Daddy ina nan "

" Daman kuwa ina son ganinku ai, Uwarku Hindu ta sanar dani cewa tana son ranar Friday za ayi family meeting a Cikin gidan nan, so shine daman zan sanar daku saboda ku samu ku Hallaci wajen idan kun haɗu da Habeeb zuwa Anjuma ka sanar dashi."

" To shikenan Daddy Allah ya kaimu ranar Friday ɗin zan sanar dashi insha Allah"

Mustafa sun juma suna taɗi da Daddy har aka kira azahar suka tafi masallaci tare.

Tafe Barrister Umar yake cikin motar sa, duk wani binciken sa ya gama akan Indo ya kuma tabbatar da cewa bata da wani saurayi, har yanzu, so dan haka yanzu ne yake da damar da zai dasa Soyayyar sa cikin zuciyarta dashen da babu wani mahalukin da zai iya tonewa, da wannan tunanin ya tsaya bakin get ɗin gidan Aunty Hindu hon ya danna sannan mai gadi ya buɗe parking space dake cikin gidan ya nufa ya samu yayi parking sannan ya fito yana Cewa mai gadi ya shiga ya sanar da AUNTY cewa Barrister Umar yazo, haka kuwa akayi mai gadi yaje ya sanar da AUNTY Hindu zuwan Barrister Umar sanarwa tayi cewa ya shigo, bayan mai gadi sanar da Barrister Umar sakon sane ya shiga falon da Sallama, Indo dake zaune ta haɗa fuska tamau Aunty Hindu tayi tambayan duniya Indo taƙi sanar da ita Abunda ya faru amsa sallamar Barrister Umar Aunty Hindu tayi, tana cewa.

" Ashe dai yau ina da babban baƙo cikin gidan nan, lallai wata sabon gani yaushe rabon da na ganka wajena."

Dariya Barrister Umar yayi yana zama saman onester yace.

" AUNTY Aikin namu ne sai a hankali kinsan bamu da wani lokaci na kammu, kullum muna cikin aiki, daga mun gama wannan shara'ar muke shiga wannan."

Duk Maganar da Barrister Umar yake hankalin sa yana kan Indo take Zaune tana tsume ta haɗa fuska kamar wacce zata danna ihu Aunty Hindu ce tace.

" Gaskiya ne kuna fama da aiki, to ya aikin naku da Hajiyar taka."

" AUNTY aiki alhamdulillah! Hajiya kuma tana lafiya, AUNTY Wannan ƙanwar tawa kuma meya sameta naga sai famar haɗa fuska take, ko dai dukanta kikayi" ya ƙarasa maganar cikin zolaya yana dariya kasancewar sa mutum mai son wasa da dariya.

Dariya Aunty Hindu tayi tace.

" Gata nan dai babu laifin tsaye babu na zaune tunda ta dawo daga gidan su abokan ka take famar baƙin hali take ta haɗa fuska, ta kuma ƙi sanar dani Abunda ya faru" duban ta ta mayar kan Indo tace.
" A'isha kina ganin yayanki bazaki gaishe shiba"

Tana turo baki tace.

" Ina wuni yaya"

Dariya Barrister Umar yayi yace.

" Bazan amsa wannan gaisuwar ba, tunda tun farko baki son gaida ni, dubi yanda kukayi muni da kika tsume ko kinsan kinfi kyau idan kina dariya, mussaman wannan dumple ɗin naki idan suna loɓawa, sai kiyi kyau haƙwaran ki kuma tamkar tauraro idan kina murmurshi haka kuma suke haske tamkar watan dabya kwana sha huɗu, to meyasa kike son ɓata kyawun ki da haɗa fuska, ki daina fushi bai dace da kyakkyawar fuskar kiba."

Kunsan Indo da son ganin ana yabonta aikuwa take ta fara murmurshi harda dariya, tace.

" Da gaske ina da kyau haka kullum Zarah take cewa ina da kyau amma ni bana yadda sai kuma gashi ka sanar dani yanzu"

Murmushi Aunty Hindu tayi sannan ta tashi ta buɗe frich ta kawowa Barrister Umar ruwa ta shige ɗaki tana murmurshi ganin har Barrister ya kauda ɓacin ran Indo, shima dubanta yayi yace.

" Ehh ke kyakkyawa ce ta ajin farko duk inda ake neman kyau to idan akazo aka sameki ayi fatiha a tashi domin an gama samun kyakkyawa."

Sosai Indo take dariya cikin mintuna ƙalilan Indo ta saba sosai da Barrister, har takai ga sunyi exchange ɗin numbern waya, amma Barrister bai sanar da ita cewa yana sonta ba, har ya tafi a cewar sa sai sun shaƙu sosai kafin ya sanar da ita.

A cikin kwanaki kaɗan shaƙuwa mai tsanani ya shiga tsakanin Indo da Barrister Umar inda ko yaushe suna cikin chart ko waya amma duk wannan shaƙuwar Indo bata taɓa ɗaukar sa da sunan soyayya ba, mutunci kawai take ɗaukar sa, haka kuwa Habeeb domin kuwa Indo tafi kowa shaƙuwa dashi, duk randa bata ji muryar sa ba takan shiga cikin damuwa wanda hakan yakan hanata sukuni har sai ya kirata ko ta kirasa tukunna ta samu walwala, Mustafa kuwa har yanzu rashin jituwa yana nan tsakanin sa da Indo, idan baya

Please Login or Register in order to submit comment