Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bisa marar sa sosai suke neman ruɗa junansu da salon nasu, juyawa yayi da ita ta koma ƙasa ya dawo saman ta, bakin sa ya manna a Breast ɗinta yana musu wani irin tsotsa hanunsa na murza nipple ɗinta babu abunda yake sai nishi da sambatu yana cewa.

" Karki barni A'ishat idan kika barni mutuwa zanyi Wlh ina........"

Ɗaka masa duka da Habeeb yayi wanda ya damesa da uban nishi shine ya katsewa Mustafa mafarkin da yake, saurin tashi Mustafa Yayi ya zauna ya haɗa Uban gumi riƙe kansa Mustafa Yayi cikin tashin hankali, A fili ya furta

"meke shirin faruwa dani karde ace son yarinyar nan nake, banta wannan mafarkin da ko wata mace ba sai ita, meyasa zata ziyarci mafarki na, *YA ALLAH*"

Habeeb dake gefen sane yace.

" Wacce yarinyar kake magana, wacce har kayi mafarkin kana saduwa da ita?"



____________________________

Tirƙashi lallai da akwai Magana a gaba, ko wacce Irin amsa Mustafa zai bawa Habeeb shin ya zaman RAUDA zai kasance a gidan Mustafa, shin zaman lafiya zai ɗaure tsakanin Habeeb Hasina da Indo tunda gadai Habeeb kamar yana son Indo, wannan shi ake kira ana wata ga wata kenan, ku cigaba da biyoni domin jin yanda zata kasance.

Kuyi hkr da typing error banyi editing ba🙏🏻

*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*


*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*


*(Ummu Nasmah ce)*
[3/11, 10:45 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*



👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻


*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*


*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.


*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻

😄😄😄 Sai tambaya ake min kan cewa Aunty Hauwa (Maman Uswan) da Aunty FAUZA ƴar Amanar kainuwa uwa mabada Mama, meye ɗina ne😄.

To bari na baku amsar ku👇🏻

To gaskiya duk cikin media sune wanda zan bigi ƙirji nace ina ji dasu yayuna ne kuma aminai nane, sune waɗanda sukafi kowa kula da lamurana cikin media, domin kuwa ina Ƙaunar su tamkar yadda nake ƙaunar ƴan uwana na jini.

_*sis Munaya And sis Maryam ina mungun ƙaunar ku kamar yadda kuke ƙaunata ana mungun tare🤝🏻❤*_


*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

_*P*••••_ 6️⃣9️⃣ ➡️ 7️⃣0️⃣

Dafe kansa Mustafa Yayi yana jinjina wannan mafarkin da yayi, dole ma sai yayi wankan tsarki, Habeeb ganin Mustafa baida niyar basa amsa ya sashi ƙara maimaita masa tambayar, dubansa Mustafa Yayi kafin yace.

"Bani da amsar tambayar ka Mlm, tunda kaga nayi shuru ban baka amsa ba ai sai ka ƙyale maganar ko kai ka cika yawan ƙwaƙƙwafi"

Taɓe bakin sa Habeeb yayi cikin nuna halin ko inkula yake cewa.

" Baza dai ka bayar ba kawai zakace, idan ma mafarkin RAUDA kayi ai sai kayi hkr gobe warhaka kuna nan tare gado ɗaya Sarkin ƴan jarabar tsiya wlh har tausayin RAUDA nake yi😄."

Tsuka mai ƙarfi mustafa yaja tare da tashi ya shige tollet tsabar haushin maganar Habeeb yasa bai tanka sa ba, murmurshi Habeeb yayi ya koma ya kwanta yana tunanin Indo, ko tayi bacci ta daina kukan ko har yanzu tana kukan, wayarsa ya ɗaga tare da dannawa Hasina kira, dan gaskiya bazai iya bacci ba sai yasan halin da Indo take ciki, cikin bacci Hasina taji wayanta yana ringine buɗe idanunta tayi ta ɗauki wayar My Sweet ta gani rubuce saman screen ɗin wayar ɗagawa tayi tana mamakin kiransa cikin wannan tsohon dare, ɗagawa tayi tare da Sallama, yana amsa sallamar yace

" ina Indo, Allah dai yasa ta daina kukan tayi bacci?"

Shuru Hasina tayi tana jinjinawa irin tausayin da Habeeb yake yiwa Indo duban Indo Tayi da take manne jikin Zarah taci kuka harta gaji bacci ya ɗauke ta, sannan ta mayar da hankalin ta kan wayar tace mishi.

" Tayi shuru tun ɗazu tayi bacci saika kwantar da hankalinka ka kwanta kayi bacci"

Murmushi Habeeb yayi tare da cewa.

" Da ɗin hankali na a tashe yake aka ce miki" ya faɗa mata yana dariya.

Murmurshin itama tayi tace.

" Gashi kuwa alamun ka ya nuna hakan RAUDA ne dai har yanzu ba tayi bacci ba ta sawa kanta tunani"

Girgiza kansa Habeeb yayi yana tausayin RAUDA domin kuwa dole sai tayi hkrn rayuwa da Mustafa.

" Kinga Sweet heart dan Allah ki rarrasheta tayi hkr ta kwanta ta cirewa kanta damuwa, daman tasan dole ne saita fiskanci ƙalubale akan rayuwar aurenta da Mustafa so ki bata hkr ta kwanta dare yayi."

" Shikenan zan gwada sai da safe"

"Allah ya tashe mu lfy" Habeeb ya furta yana kashe wayan sai yanzu hankalin sa ya kwanta jin ance Indo tayi shiru har tayi bacci kwanciya shima yayi yana jan bargo cikin nishaɗi, Mustafa kuwa bayan yayi wankan tsarki ne ya dawo ya kwanta tare da rufe idanunsa saurin buɗe idon yayi domin kuwa yana rufe idon nasa hoton Indo yake gani tsaye gabansa tana murmurshi, ƙara rufe idon nasa yayi still dai Indo ce yake gani, wani irin dogon tsaki yaja tare da tashi ya zauna tsakiyar gadon yana riƙe da kansa, kusan wannan daren zance Mustafa baiyi bacci ba, haka ya ƙaresa cikin tunanin Indo domin kuwa itace ta kwana tana yawo cikin ƙwaƙwalwar sa.


Washe gari da safe Indo ta watstsake ta farka bata tashi cikin wata damuwa ba duk da dai Abunda Momy da Mustafa suka mata yana zaune dam cikin ranta bata kuma yadda ta haɗu da Momy Mustafa Habeeb ba, ta kama hanun Zarah suka gudu driver ya kaisu gidan Aunty Hindu, da yamma kuwa akazo aka ɗauki zarah zuwa gidan gwamnati, sanda Habeeb yake jajen Indo ne Hasina ta sanar dashi cewa ta koma gida tunda safe, Habeeb yaji haushin komawar Indo ba tare daya sata cikin idanunsa ba, da daddare Daddy gaba ɗaya ya haɗa iyalan nasa yana musu faɗa game da rayuwar Aure sanda Daddy ya gama musu faɗa sannan Momy tayi nata, a ƙarshe suka sa musu albarka kafin kowa ya shige da matarsa cikin gidan sa, part ɗin nasu yayi mungun kyau ita RAUDA komai Ash color suka samata cikin gidan nata, ita kuma Hasina suka sa mata pink and purple color.

Habeeb ne dake zaune da matar sa ya furta.

" Alhamdulillah yau rana ce mai matukar muhimmanci a cikin rayuwata, ranar da Allah yasa na ganki cikin gidana a matsayin matar Aure"

Murmushi ɗauke bakin Hasina tace.

" Tabbas Allah shine abun godiya daya haɗa masoya biyu a ƙarƙashin inuwar Aure ɗaya waɗanda suka juma suna ƙaunar junansu, ina roƙon ubangina daya bani ikon maka biyayya har ƙarshen rayuwata, bana fatan Allah ya nuna min ranar da zan saɓa maka"

Murmushi Habeeb yayi tare da cewa.

" Ameen ya Allah yanzu sai ki tashi muje muyi alwala muyi Sallah raka'a biyu mu godewa UBANGIJIN mu"

tashi Hasina tayi ta shige tollet ta ɗauro alwala kafin shima Habeeb ya shiga ya ɗauro tasa alwalar, sallah sukayi raka'a biyu kafin Habeeb ya kama goshin HASINA yana jero addu'a.
اللهم اني اسالك خير ها و خير ما جبلتها عليه و اعوذ بك من شرها و شرما جبلتها عليه.

Bayan ya gama Addu'ar ne ya mata wasu ƴan tambayoyi game da addinin ta, kuma Alhamdulillah HASINA ta amsa su, sosai Habeeb yayi farin cikin yanda HASINA tasan addinin ta sosai, shirin bacci sukayi suka kwanta, cikin dare Hasina taji kamar ana lalubarta a hankali ta buɗe idanunta, cikin dump light ɗin dake ɗakin taga Habeeb ne domin kuwa har yayi nasarar rabata da ƴar rigar dake jikinta, daren ranar Hasina tasha wuya Hanun Habeeb daman ance duk wayon amarya sai ango yasha romonta.

RAUDA kuwa tunda suka shigo cikin part ɗin nasu suka rabu da Mustafa domin kuwa a falo ya barta ya wuce bedroom ɗinsa, ba tare daya ko kalleta ba, zama RAUDA tayi falon tana jiran ko Mustafa zai shigo, har 12:00pm shuru babu labarin Mustafa, har bacci ne ya ɗan saceta tayi ta farka babu Mustafa, tashi tayi da niyar ta shiga bedroom ɗinna sa, har ta fara tafiya sai kuma tayi tunanin karta shiga ya mata wulaƙanci, baya ta dawo tare da neman nata bedroom ɗinta ta shige, Zama RAUDA tayi bakin gado tare da sakin wani marayan kuka, sosai take kukan domin kuwa baƙin ciki ne ya cika mata zuciya, wai ace yauce First night ɗinta, yazo mata cikin baƙin ciki, mijin da take so take ƙauna shine ya ɓata mata darenta na farko gidan miji, sosai RAUDA ke kuka tana baƙin cikin yanda wannan Ranar data daɗe tana jira yazo mata a haka, tabbas bacci ɓarawo ne, amma wannan daren baiyi nasarar sace RAUDA ba, kwana tayi tana shan kuka.

Shi kuwa Mustafa yama manta da wata halitta RAUDA cikin gidan, yana shiga bedroom ɗin nasa tollet ya shige ya watsa ruwa daman babu wani abokin da suka gayyata ya rakosu, su kaɗansu suka taho da matan su, bayan ya shirya tsaf cikin shirin Bacci, ya jawo system ɗinsa, ya juma sosai akan system ɗin kafin ya kashe tare da turata gefe ya kwanta, yana kwanciya kuwa saiya Indo ta fara yawo cikin idanunsa tun daga rayuwar ta na ƙauye har zuwa yanzu shi kaɗai yake murmurshi tare da ƙanƙame filo yana juyi a fili ya furta cewa.

" Shatuu kina mungun kyau idan kina cikin firgici" mirginawa gefe yayi yana riƙe da filonsa a ƙirjinsa, ya cigaba da cewa, " alhamdulillah bishiyata ta girma tunda harta fara fidda reshe, Burina ya cika na ganin Indo Tayi Hankali, sai kuma yanzu na sa miki ido game da ko wanni namiji, domin ke ɗin mallaka tace, tun ba yau ba, murmurshi mai sauti yayi yana tuno sanda ya kaiwa Inna ziyara randa zai dawo gudun da Indo take tana Cewa " *ya Mustafa dan Allah karka tafi ban gaji da kallon ka ba, ya Mustafa kifiyar sonka ta sokeni* still dai murmurshin ya ƙara yi yana cewa, " Abunda ya hanani sauraron ko wacce mace kenan duk da lalurar da nake tare da ita domin ni naki ne ke kaɗai ba tare da wata ba."

Mustafa kwana yayi yana shauƙin Indo har mafarki yayi suna saduwa, sosai kuwa ya samu farin ciki cikin wannan bacci domin kuwa ta jiyar dashi daɗin da bai taɓa jiba cikin wannan mafarkin yayin da RAUDA kuwa ta kwana cikin baƙin ciki.

Washe gari da safe RAUDA tana idar da sallar asuba ta fara gyaran gidan ta, domin kuwa RAUDA fannin iya girki da tsafta gwanace a wannan fagen tas ta gyara gidan ta, kitchen ta shiga da niyar ɗaura girki taga gas ɗin ba'a ɗura mata gas ciki ba, gashi kuma electri ɗinta ba'a mata setting ba, dole yasa RAUDA dawowa falo ta zauna badan taso ba, Mustafa shine bai fito ba sai 11:00am cikin shirin aiki ya fito hanunsa riƙe da ƙaramar jakar aikin sa, tare da key ɗin motar sa, nocking sukaji anayi a ƙofar falon, Mustafa ƙofar ya nufa tare da buɗewa, Ishaq ne tsaye hanunsa riƙe basket na Abinci, waje Mustafa ya basa ya shige, sannan shima ya dawo falon, gaishe shi Ishaq yayi, Mustafa ya amsa yana dariya tare da cewa.

" Autan Momy ina Sharif ɗin na ganka kai ɗaya?"

Dariya Ishaq yayi tare da cewa.


" Tare muka zo yayi part ɗin ya Habeeb zai miƙa abinci nima yanzu zan tashi na shiga can ɗin kallon RAUDA yayi yace Aunty RAUDA ga Abinci inji Momy"

Murmushi RAUDA tayi ta karɓa tare da cewa.

" Ka cewa Momy mun gode, idan kaje ka gaishe min da sharifa."

Da to Ishaq ya amsa tare da tashi ya fice daga part ɗin nasu, duban Mustafa RAUDA tayi tace.

" Sannu da fitowa, ina kwana"

A taƙaice ya amsa mata da cewa "lafiya" yana ƙoƙarin fita.

Ganin fita zaiyi yasa RAUDA cewa.

" Ya Mustafa ba kayi breakfast ba zaka fita"

Bai kalleta ba yace.

" Bana buƙata ko kinga na miki kama da wanda yake jin yunwa? Koko na taɓa buƙatar abinci daga wajen ki?

Girgiza masa kai RAUDA tayi alamar a'a, shima bai ƙara cewa komai ba ya fice.

RAUDA ba tayi ƙoƙarin dakatar da Mustafa ba daga fitar da zaiyi duk da bata ji daɗin fitar tasa ba, amma dole tayi shuru gudun kar tayi magana ya zageta.

Dafe kanta tayi hawaye na ƙoƙarin zubo mata tasa hanu ta goge tare da dafe kanta tana Addu'ar Allah ya kawo mata sauyi cikin rayuwar Auren ta, tana son mustafa Kuma insha Allah zata yi ƙoƙarin ganin ta dawo da hankalin mijinta gare ta da wannan tunanin RAUDA ta wuni.

Su kuwa Hasina Rayuwar su suke cikin farin ciki, da mutunta juna, suna matuƙar son junansu, Habeeb ya ɗauki hutun aiki harna tsawon sati biyu domin yaci amarcin sa, sai dai duk da wannan cin amarcin da Habeeb yake Indo tana maƙale cikin zuciyarsa, da ita yake kwana yake tashi haka kuma kullum yakan yawan damun Hasina da zancen Indo, bata kawo komai cikin ranta haka take biye masa.


A kwana a tashi babu wuya wajen ubangi yau satin su Mustafa biyu da Aure yayin da kuma RAUDA sam bata samun farin ciki, kullum cikin ɓacin rai take cikin gidan ko sau ɗaya kuwa Mustafa baiyi tunanin shiga ɗakin RAUDA ba, ma'ana babu wata alaƙar aure da ya taɓa shiga tsakanin su, suna Zaune ne kowa yana harkarsa cikin gidan, koda wasa kuwa RAUDA ta shiga zabgar Mustafa ranar ta shiga uku wuni zaiyi yana ci mata mutunci, haka RAUDA take zaman hkr cikin gidan bata kuma taɓa tunanin gayawa Mamy halinda take ciki ba

INDO kuwa yau baki har kunne, sun kammala zana jarabawar barin Secondary School, wato neco, cikin dariya Indo ta dubi Zarah tace.


" Bestie na har yanzu ba'a zo ɗauka ta ba, kawai ki wuce, dan gaskiya yau bazan biki ba, dole zan jira azo a ɗauke ni."

Dariya Zarah tayi tace.

" Ai kuwa ni na tafi sai munyi waya kawai"

" Shikenan ki gaishe da momma sai nazo"

Zarah bata juma da tafiya ba Habeeb ya shigo cikin school ɗin, tun daga nesa ya hango ta tana tsaye ta harɗe hanun ta a ƙirji, har gabanta yaje yayi parking, buɗe motar yayi yana dariya, sai yanzu Indo ta lura da Habeeb domin bata ɗago kanta ba, bare taga waye yayi parking saida taji ƙamshin turarensa ne, sannan ta fahimci ya Habeeb ne, murmurshi tayi tare da cewa.

" Ango kasha ƙamshi kaine tafe."


Murmushi Habeeb yayi tare da cewa.

" Ba kin manta da niba, tunda kika koma wajen AUNTY Hindu, shigo mu wuce."

Shiga Indo tayi tana dariya tace.


" Ai ya Habeeb ko zan manta da kowa, bazan manta da kai cikin rayuwata ba, ya Habeeb ina Aunty Hasina tana lfy."

" Ban sani ba, tunda kinƙi zuwa gidan mu, itama tayi fushi dake tunda akayi Auren nan baki taɓa zuwa wajen mu ba."

Murmushi Indo tayi tace.

" Ya Habeeb bawai naƙi zuwa bane Allah banson naje ne Aunty Hasina tace saina je wurin Sarkin muguntar nan, Allah ya Habeeb na tsani ganin ya Mustafa, bana sonsa na tsane sa."

Zaro ido Habeeb yayi sai kuma yayi murmurshi yana ɗago wata ƙaramar leda tare da cewa.

" kinga ni ba Wannan ba, hingo riƙe alƙawarin ki, tare da ciro wani ƙaramin gift ya buɗe, zobe ne mai kyauwun gaske anyi masa kwalliyar love cikin sa kuma anyi rubutu da *A&H* ya miƙa mata tare da mata umarni da ta saka, ƙarba tayi ta saka tana murna sannan ta buɗe ledar da ya bata, waya ce mai kyawun gaske ƴar dai-dai ƙirar infinix hot 8..............



Ku ƙara hkr dani a kan hkr na rashin typing akai-akai da kuma typing error dan gaskiya kwana biyun nan Banda time ɗin editing.


*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*


*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*


*(Ummu Nasmah ce)*
[3/15, 9:54 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*



👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻


*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*


*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.


*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*P*••••••7️⃣1️⃣ ➡️ 7️⃣2️⃣

Sosai Indo take dariya tana murnar wayar da Habeeb ya bata domin kuwa tana mungun son waya, kallon Habeeb Indo tayi cikin dariya tace.

" Ya Habeeb na gode sosai Allah ya saka da Alkairi, ya Habeeb kamin abubuwan Alkairi da yawa cikin rayuwata, kaine mutum na farko daka fara kawo min haske cikin rayuwata, har abada bazan taɓa mantawa da Alkairin ka gare ni ba, ina roƙon ubangina daya bani ikon kyautata maka nima, duk da nasan bazan taɓa biyanka Abunda ka min ba."

Sosai Habeeb yaji daɗin yanda Indo tayi farin ciki da wannan kyautar daya mata, murmurshi yayi cikin jin daɗin ganin farin ciki kwance fuskar ta yace.

" Karki ƙara min godiya danna miki wani abu, haƙƙi ne a kaina na miki, nidai fatana karki taɓa cire wannan zoben daga hanunki domin kuwa yana da matukar muhimmanci a rayuwata, ke bazaki gane muhimmancin saba sai nan gaba kaɗan, kimin alƙawarin cewa duk sanda na sanar dake manufata ta baki wannan zoben zaki amshi buƙatata kimin alƙawarin cewa bazaki kula ko wani Namiji ba da sunan SOYAYYA"

Dam! Dam! Dam! Gaban Indo ya buga domin kuwa ita yanzu ba yarinya bace da zata kasa gane manufar wannan maganar da Habeeb ke mata tabbas idan ta fahimce sa dai-dai ya Habeeb yana sonta, innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un ta maimaita cikin zuciyarta domin kuwa tabbas zargin ta idan ya kasance gaskiya to da wani Ido zata kalli Aunty Hasina, wata Zuciyar ce tace mata, ina bama haka bane ya Habeeb bazai taɓa sonki ba, kawai ya Habeeb yana son yaga kin mayar da hankali ki akan karatun kine shiyasa yace karki kula ko wani Namiji, nasan ya Habeeb bazai taɓa sona ba, domin ni ɗin ba ajinsa bane ƴar ƙauye wacce ta fito cikin ƙauyen ƙayau, bazai taɓa sona ba, kawai so yake yaga rayuwata ta inganta, har yanzu idonta bai gane mata irin zoben daya bata shima akwai a nasa hanun ba, Habeeb ne ya katse mata tunanin ta da cewa.


" Kinyi shiru ƙanwata, baki bani amsa ba."

Rasa me zata cemasa tayi, domin kuwa tana mungun jin kunyar ƙin yarda da buƙatar sa, tana kuma tsoron ta amincewa bukatar sa ya zamo mata matsala daga baya, wani dabara ne ya faɗo mata cikin ranta, kafin tace masa.

" Ya Habeeb Babu kyau ɗaukar alƙawari saboda kar wata rana a samu matsala mutum ya kuskurewa wani abu guda ɗaya daga ciki, kaga sai Allah ya kama mutum da wannan alkawarin, domin shi alkawari ba abun wasa bane abune mai girman gaske, *ya Habeeb insha Allah zan kiyaye wannan dokar taka, zan kiyaye sosai amma sai dai ban ɗauki alƙawari ba, zan dai ga nayi ƙoƙarin kiyayewa*."

Ajiyar Zuciya Habeeb ya sauƙe sai yanzu ya ƙara tabbatar da cewa Indo tayi Hankali ba Indon da ya sani bane a baya, sai yanzu ya gane cewa Indo tasan addinin ta yanda ya kamata, tabbas yaji daɗin yanda ta masa bayani kuma ya fahimce ta, duban ta yayi cikin murmurshi yace.

' shikenan Allah ya baki ikon kiyayewa."

" Ameen ya Habeeb na gode sosai."

Sun ɗan juma suna hira kafin Indo ta shiga cikin gida shi kuma Habeeb ya wuce.

Daf da zata shiga ɗaki taji Muryar Aunty Hindu tana cewa

" Ke Nana ( dake haka take kiran ta dashi) ina kika juma haka, lokacin tashin ku harya wuce, driver taje school ɗin bai ganki ba kinsa Hankalin mu ya tashi nida Abban ku?"

" Ummi ya Habeeb ne ya ɗauko Ni, mun jima dashi a compaunt ɗin gidan nan, ina ga saɓani mukayi da driver Kuma shima drivern ai na jirasa baizo ba har ya Habeeb yazo."

" Okey to maza haura ki samu ki cire uniform ɗin, kizo kici abinci, Abban ku tun ɗazu yake jiranki yana sama kije ki sanar dashi kin dawo ."

Tana dariya tace.

" Yanzu kuwa Momy daman Nima ina son ganin Abba zan nuna masa wani abu."

Murmushi Aunty Hindu tayi tace.

" Zaki nuna masa wani ko zaki karɓi kuɗin shopping ƙarshen wata yayi kayan makeup Yayi Low."

Dariya Indo tayi ta shige bedroom ɗinta da gudu tana cewa " Ammi babu ruwan ki tsakanin mu da Abba munfi kusa"

Dariya itama Aunty Hindu kafin tace.

" Ai daman bance da ruwana ba bare naji kunya, naga alamar yanzu so kuke ku haɗe min baki cikin gidan nan."

Dariya kawai Indo tayi kafin ta wuce ɗaki.

💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞

Rayuwa gudu yake, yayin da rana ku suke komawa awanni sati biyu ke komawa sati ɗaya, su Indo results ɗin su ya fito kuma alhamdulillah tayi nasaran samun 9 credit, results Yayi kyau sosai, kowa yayi murna da wannan result ɗin mussaman Daddy da Abba, kwatsam lokaci ɗaya komawar su Aunty Hindu Egypt ya taso cikin gaggawa, Aunty Hindu da Abba sun yanke shawarar cewa zasu tunkari Daddy da zancen ya basu Indo su koma Egypt da ita idan yaso sai tayi joining ɗin University ɗinta acan Egypt ɗin da wannan shawarar suka yanke cewa zasu je su sami Daddy da zancen Domin suna matuƙar son zaman Indo tare dasu, Aunty Hindu ta yanke shawarar cewa satin gaba kafin su koma Egypt zata ɗauki indo suje Dasina.

Kwance yake bisa cinyarta, taɗi suke cikin SO da ƙaunar juna tare da mutunta juna, domin kuwa suna matuƙar son junan su hakan ne ya basu damar samun kyakkyawar alaƙa a tsakanin su, cikin SO da ƙauna ta dubesa tace.

" Sweetie na gaskiya nayi fushi sosai da ƙanwar ka, har nayi 5 month cikin gidan nan taƙi zuwa kai kuma ka hanani zuwa gidan, gaskiya nayi missing ɗin su sosai pls ka barni mana koda daddare ne naje shap-shap na gansu na dawo."

Murmushi Habeeb dake kwance ya ɗaura kansa bisa cinyar Hasina yayi tare da cewa.

" to ina dai ga wannan ƙanwar tawa ba zuwa gidan nan zatayi ba, dan wlh kullum na mata zancen nan saita fara min kwana kwana ita a dole bata son zuwa ta haɗu da dodonta Mustafa ki haƙura da zuwa gidan nan tukunna sai nan gaba kaɗan."

Murmurshi SOSAI HASINA tayi tace.

" Lallai Indo ta sawa kanta aiki, nifa ina tunanin akwai Abunda ya haɗata da ya Mustafa RANAR denern mu, akwai Abunda ya mata tun Ranar na fahimci bata son ƙara haɗuwa dashi, amma dan Allah sweetie na, ka taimaka ka jawo min Indo cikin gidan nan koda ƙarfi ne tunda ka hanani zuwa."

Dariya sosai Habeeb shima yayi tare da cewa.

" Har da ƙarfi zan jawo ta ko kin manta cewa shalelena ne ita na dai jawo ta a hankali banda ƙarfi kam dan banson shalelena tasha wahala."

Dariya Hasina tayi tace.

" To mai shalele jawo ta a hankali, nifa gani ma nake kamar da biyu tsakaninka da Indo, ko dai zaka ƙara ƴar gida-gida ne, kaga shikenan gani ga ƙanwata kusa mu zauna abunmu."

Dam! Ƙirjin Habeeb ya buga cikin zuciyarsa yake cewa " kardai HASINA ta gano Abunda yake cikin zuciyata,

Please Login or Register in order to submit comment