Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*



*(Ummu Nasmah)*
[1/7, 5:31 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*



👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻


*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*


*D̸͟͞E̸͟͞D̸͟͞I̸͟͞C̸͟͞A̸͟͞T̸͟͞E̸͟͞D̸͟͞ T̸͟͞O̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar amana*

Uwa mabada mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.


*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

Aunty Hauwa Maman Uswan, ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya🙏🏻.


*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________

Masoyana bani da bakin da zan muku godiya, na gode na gode sosai, da ƙaunar ku gare Ni, yanda kuke Son book ɗin *INDO A BIRNI* abun ba'a cewa komai, waɗanda suka min magana ta privet cewa na sasu a group ɗin *INDO A BIRNI* suyi hkr dan Allah wlh group ɗin ya cika, ku nema a wani group nasan baxaku rasa ba.🙏🏻

*P*••••••1️⃣1️⃣ ➡️ 1️⃣2️⃣

Kauda kanta RAUDA tayi cikin ƙunar rai, ta rasa menene ya gaxa a jikin ta da mustapha yake mata wannan wulaƙancin, gashi Dai Mamy tace mata malamin ta, ya tabbatar mata cewa Mustapha zaiso ta, amma har yanzu shuru, sai ma uban wulaƙanci da take fuskanta a wajen sa, yau dai ta ƙudurce a ranta, dole sai ta koma gida, kodan Mamy tasan halin da ake ciki, domin kuwa baxata iya Rayuwa Babu mustapha ba, shine numfashin ta, taya to rayuwa zata kasance Babu numfashi, dole ma sai ka soni mustapha, dole ne.
Maganar da Habeeb ke mata shine ya dawo da ita daga duniyar tunanin data faɗa.

" Dan Allah Sis RAUDA anjuma ki haɗa min Abinci, mai kyau, ai kinsa abubuwan da nafi buƙata.

" Ba komai ya Habeeb zan haɗa maka insha Allah, adawo lfy.

" Habeeb ne kawai ya amsa da Ameen shikan mustapha, kallo ma bata isheshi ba, bare kuma ya amsa sai ya dawon ta.

Sallama sukayi wa Momy sannan suka wuce wajen daddy kasuwa.

RAUDA kallon ta, ta mayar wajen Momy tace.

" Momy bari na haura sama na ɗan miƙe, kafin Anjuma na sauƙo na ɗaurawa ya Habeeb girki.

A fito lfy ta mata, sannan ta haura sama.
Kwanciya RAUDA tayi akan gadonta tare da ɗaukar wayan ta ta dannawa mamyn ta Kira.


Da sallama Mamy ta Amsa, tace RAUDA lfy naji Muryar ki kamar wacce taci kuka.

" A'a Mamy ba kuka nayi ba, kawai raina ne yake ɓace, Mamy na shiga Uku, ya Mustapha baya sona, Mamy ko kallo na, baya sonyi, ya zanyi Momy, ta ƙarasa maganar cikin kuka mai tsuma Zuciya.

" Ya isa Haka RAUDA, ki daina kuka, domin kuwa muddun ina numfashi dole sai Mustapha ya durƙusa a gaban ki da gwiwwowinsa yana roƙarsa soyayyar ki, Dani yake zancen, tunda shi butulu ne, baisan Alkairi ba, ai yana da tarihin Halaccin da mahaifin ki yayiwa ubansa, ki kwantar da hankalin ki, zai shigo hanu, sai kin juyasa kamar wainar tanda.

Cikin farin ciki RAUDA tace.

" Promise Mamy, wlh ina son ya Mustapha, fiye da yanda nake son kaina, jiya ma ya Habeeb yake cemin, zasuxo Anjuma su gaishe ki.

" Okey Allah ya kawo su lfy.

Da Ameen RAUDA ta amsa sannan sukaci gaba da zancen Duniya.


Menene Asalin Mustapha?
Menene alaƙarsu da RAUDA?
Menene Dangantakar su da ƙauyen su Indo?
🤔🤔🤔🤔🤔


*Dangantakar su*

Alhaji Mamman babban limami ne, a cikin ƙauyen *DASINA* mutum ne mai karancin da mutunci, ana girmama sa, sosai cikin wannan garin, Yana da matar sa ɗaya mai suna Harira yaran ta suna kiran ta da INNAH, yaransa biyu, Haruna shine babba, sai Hindu wacce ake kiran ta da Hinde a cikin ƙauyen, Mlm Mamman takaka ne sosai, wani sa'in abincin da zasu Ci ma gagarar su yake, kasancewar ya samu matar rufin Asiri, bata taɓa nuna gajiyawar ta akan Rashin Abincin gidan Mlm Mamman ba, haka zata san dabarar da zatayi, yaran ta, su sami Abinda zasu Ci, maƙocin Mlm Mamman, Mlm Hadi mutum ne, mai kyautatawa maƙoncin sa, duk da shima bawai yana dashi bane sai dai rufin Asiri, amma yawanci idan yayi cefenen gidan sa, to sai yayiwa, Mlm Mamman, zumunci ne mai ƙarfi tsakanin su, matan Mlm Hadi, Safiya, da Rabi, suna zumunci sosai da INNAH, musamman Rabi, kusan zaka iya kiransu ƙawaye da INNAH, Rabi tana da ɗanta ɗaya mai suna Musa, Musa da Haruna ɗan Innah kusan komai tare suke yinsa, shaƙuwace mai ƙarfi, tsakanin su.

Tafiya suke suna, zance, dawowar su kenan daga, makarantar Allo, Haruna ne yake cewa Musa.

" Musa ina ganin fah xan tafi birni neman kuɗi, dan kaga mun gama Secondary School, Bamu da Halin da zamuje gaba da Secondary, Kuma gaskiya ni, ina da burin cigaba da karatu, kodan na taimaki rayuwar iyaye na, da ƙanwata.
Shiyasa na yanke wannan shawarar, idan kaima kana da wannan burin, sai mu haɗa hanya.

Shuru musa yayi kafin yace.

" Gaskiya Haruna ni bani da burin cigaba da karatun Boko, iya Secondary ɗin ma, da nayi ya isheni, gara na nemi sana'a na fara, tunda kai kayi niya, kaje ka, Allah ya baka Sa'a yasa ka shiga, birni a Sa'a.

" Shikenan Musa na gode sosai, kuma baxan taɓa manta Addu'ar ka gare niba, Haka Abotar ma baxata taɓa yankewa ba.
Har suka iso gida tattaunawa suke kan tafiyar Haruna birni, da la'asar Haruna da musa suka sami iyayen su, a majalisar su, na dattawa da maganar tafiyar, Haruna birni, domin neman kuɗin da zaici gaba da karatunsa, da farko Mlm Mamman yaƙi, yarda, da tafiyar Haruna birni, sai da Mlm Hadi yasa baki tukunna, nan ma daƙyar mlm Mamman ya Yadda, bayan ya amince masa ne, suka nufi wajen Innah, domin sanar da ita, dan shi Haruna a niyarsa gobe yaƙe son wucewa, birni.

A zaune suka sami Innah bakin murhu tana iza wuta, tsugunnawa sukayi, tare da mata barka da gida.

Kallon su Innah tayi tace.

" Musa kune tafe yanxu, ya Rabin take.

" Lafiyar ta ƙalau Innah, tace ma na gaida ki.

"Ayya Ina amsawa, Haruna ka shiga ɗaki na akwai abinci rufe ku ɗauka kuci koh.

Da to Haruna ya Amsa tare da cewa

" Innah idan kin gama, muna son zamuyi magana ne, dake.

" Ba damuwa kuje kuci abincin ina zuwa nima.

Bayan sun gama cin abincin ne Innah ta shigo cikin ɗakin, tare da zama.

Musa ne ya dube ta, tare da sanar da ita ƙudirin Haruna, na son zuwa burni neman kuɗi, ya kuma sanar da ita yanda sukayi da Mlm Mamman.

Innah bata wani hanasa ba, illa ma cewa da tayi.


" Tunda har Mlm ya yarje maka, ni babu abinda zance, sai dai a duk inda kake Haruna ka kasance mutum mai ruƙe amana tare da haƙuri, ka kuma ji tsoron Allah, ka zauna da duk mutanen da kayi tarayya dasu, Allah ya baka Sa'a yasa ka sami Abinda kaje nema, kake zayartar mu, duk lokacin daka samu zama, hakanne zai nuna mana kana lfy.

Haruna yaji daɗin addu'ar mahaifiyar sa sosai, cikin farin ciki da murna suka fice daga cikin gidan.

Washe gari da safe Haruna ya ɗauki dangwalin sa, tare da yiwa ƴan uwa da abokan Arziki sallama, har bakin gari, Musa ya raka Haruna da ƙyar suka iya rabuwa cikin kewar juna, kafin musa ya dawo cikin ƙauyen shi kuma, Haruna ya kama hanyar tashar mota domin hawa motar da zata kaisa birni.

Cikin sa'a kuwa Haruna ya shiga birni da farko ya fara sana'ar sharan shago ne a kasuwa, a biyasa ɗari hamsin, a wuni yana samun Dubu biyu kullum, na sharar shagon, akwai Ranar da Haruna yake yiwa Wani Alhaji sharan shago, sai tsinci kuɗi, wajen dubu goma rafar su, komawa Haruna yayi ya kawowa Alhajin kuɗin yace gashi tsinta yayi, yana masa shara, shiko Alhajin ashe da sanin sa, ya ajiye kuɗin domin ya gwada amanar Haruna, kasancewar yana son ɗaukar sa yaron shago,

Alhaji muktar yaji daɗin samun, Haruna daga cikin masu Amana, daga nanne fah ya ɗauki, Haruna, yaron shago suna saida Atampopi, akwai ɗan Alhaji muktar, Bello, zai ɗan girmi Haruna kaɗan sanshi a lokacin ma yana da mata, muktar da Haruna, jinin su ya haɗu sosai, shaƙuwace mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu, inda kullum suke tare.

Akwana a tashi Babu wuya wajen Ubangiji, Alhaji muktar ya yadda da amanar Haruna sosai, inda hakan tasa ya ɗauke sa ya kaisa gidan sa da zama, tare da sashi, kawo takaddun sa, ya nema masa University.

Alhamdulillah Rayuwar birni tayiwa Haruna daɗi, tunda gashi, yana sana'ar sa, kuma yana zuwa makaranta, haka ƙauyen suma yana kaimu musu ziyara sa'i da lokaci, bai Kuma manta da abokin sa, Musa ba, inda yakan yawan nasa Alkairi.

Haruna cikin nasara ya gama karatunsa inda ya fito da good result, wato first class, Babu ƙyashi Alhaji muktar ya basa Aron kuɗi kimanin, 20 millions yace ya buɗe shagon sa na kansa, idan yaso yake biyansa kuɗin sa da kaɗan kaɗan, Haruna yaji daɗin alkairin da Uban gidan nasa ya masa.

Cikin ikon Allah, kasuwa rake jawa Haruna inda ya samu ninkin kuɗin da Alhaji muktar ya basa aro a cikin shekara ɗaya.

Fili Haruna ya saya tare da fara ginawa, ya kuma fara neman, Auren A'ishah wacce suka haɗu da ita taxo siyan zani shagon nasa, soyayyah mai ƙarfi ne ta shiga tsakaninsu.

Cikin ikon Allah kuma yayi nasarar samun Auren, A'ishah, inda Alhaji muktar shine ya karɓi Auren bisa umarnin Mlm Mamman, ƴan ƙauyen Dasina suka zo Aure.
Harda Musa ma ya sami Halartar Taron ɗaurin Auren.

Bayan shekara Uku.

A'ishah matar Haruna ta haifi yaranta, maza kyawawan gaske, Hatta Hajiya Innah ta halarci wannan sunan, inda yara sukaci sunan, Muhammad Mustapha, da Muhammad Habeeb.

A lokacin ne kuma Musa Nasa Auren ya tashi, Haruna kusan shine yayi hidimar bikin, Musa, Tare sukaxo da matar sa A'ishah, da ƴan biyun sa, sunan matar da Musa ya Aura Maryam itama ƴar cikin ƙauyen nasu ne, bayan bikin ne Haruna suka koma cikin Birni, da matarsa A'ishah.
Inda ya buɗewa Musa shagon sai da kayan tireda.


Acikin wannan shekarar ne, Allah ya ɗauki Rayuwar mahaifin su Haruna da mahaifin musa tsakanin su sati ɗaya ne kacal, sunji zafin mutuwar sosai, Innah kuwa tasha kukan ta, har ta godewa Allah.
Haruna ya ɗauki kanwar sa, Hindu ya koma da ita birni yaso ya tafi da Innah, amma Innah taƙi, tace Babu inda zata, a barta anan ƙauye har mutuwar ta.

Bayan shekara biyu da mutuwar mahaifin Haruna, ya biya musu kujerar hajji, dashi da Innah da kuma matarsa A'ishah, suka sauƙe falari, a cikin shekarar.

Ƙanin Alhaji muktar, Usman shine ya auri Hindu, inda ya tafi da ita birnin Istanbul kasancewar acan yake aiki.

Shekaru sunja rayuwa sai tafiya take, yanxu ƴaƴan A'ishah biyar bayan ƴan biyun ta na farko, ta sake haihuwar Mace mai suna Sharifa sai kuma ta sake yin wasu ƴan biyun, ishaq da Sharif, inda zumuncin Haruna da Bello tayi ƙarfi sosai, har ta kai ga Bello yakan ɗauko ƴarsa RAUDA ya kawo ta weekend, gidan Alhaji Haruna, Inda ita kuma RAUDA ta taso da tsantsan ƙaunar Mustapha, wanda shi yake ɗaukar hakan a matsayin, Hauka take yi.
A lokacin su mustapha sun gama karantunsu a ƙasar London, har sun kama aikin su, inda Mustapha ya karanci Lawyer shi Kuma Habeeb ya karanci medical doctor, Hospital ɗin da Habeeb yayi practical, suka ɗauke sa. Aiki


Shima Musa yanxu yana da yaran sa, biyar, Tanimu, INDO, jummalo, Abubakar sai kuma Haruna mai sunan Abokin nasa.


Haruna da iyalansa suna ziyartar mahaifiyar sa, sosai wacce yanxu suke kira da Hajiya Innah.

Wannan shine tushen labarin su.

Ku biyo Alƙalami na gobe insha Allah domin komawa cikin labarin *INDO A BIRNI*.


*Share*
*And*
*Comment*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah)*
[1/8, 5:26 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*



👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻


*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*


*D̸͟͞E̸͟͞D̸͟͞I̸͟͞C̸͟͞A̸͟͞T̸͟͞E̸͟͞D̸͟͞ T̸͟͞O̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.


*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya.🙏🏻


*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________


🙏🏻🙏🏻🙏🏻😩😩😩😩

Ya Ubangiji ina roƙo gareka daka sa *Farisa* ƴar sister Ladingo marubuciyar matar GwamnaTana hanu na gari, Allah ka kareta a duk inda take, ka Bayyana ta cikin gaggawa.
Ameen 🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻


*P*•••••••1️⃣3️⃣ ➡️ 1️⃣4️⃣

*Mu Dawo cikin labarin mu* 🏃🏻‍♀

Yau Indo tun dawowar ta daga makaranta, ta nemi Ruwa a baho da dutsin goge kaushi, ta jiƙa ƙafarta, yayin da kuma reza ke riƙe a hanun ta tana yanke farcen ta, ita dai Mama tana tsaye gefe tana kallon ikon Allah, ɓarawo da bacci, wai yau Indo ce ke yanke, farce harda gugar ƙafa, yarinyar da ko zaka mutu kana cewa Indo wanke ƙafarki baxata wanke ba, sai dai ki mutun, bare kuma gugar ƙafa, yau kuma sai gashi ita ɗayan ta, tanayi ba tare da kowa ya sata ba, bayan ta gama yanke farcen Hanun nata ne, sai Kuma tahau gugar ƙafa, cikin mamaki Mama ke kallon ƙafar Indo, yanda ta fita fes, Babu wani alamar kaushi, ashe daman datti ne, yasa kafar Indo fita hayyacinta, yanke farcen ƙafarta, tayi, sannan ta dubi Mama tace.

" Mama tsammin Omo na wanke kayina dan Allah, ina son zanje gidan Laure ne, kitso Anjuma.

Zaro ido Mama tayi tace.

" Me kika ce, zaki kitso gidan Laure, ke ɗin kuma yau Indo, kece zakiyi kitso.

Dariya Indo ta kwashe dashi tace.

" Eh wlh Mama, Mlm Sani yace idan na yanke farce na, nayi kitso, ba ƙaramin kyau zanyi ba, sai nafi duka ƴan matan garin nan kyau, tana fari da Ido take yiwa Mama maganar, kuma yace gani ƴar ɗagwas ɗagwas kyakkyawa son kowa ƙin wanda yarasa,.

Dariya ce ta suɓucewa Mama ganin yanda Indo ta dage, wai a dole ita kyakkyawa ce, haba ai daman wannan tsaftar bata Allah da Annabi bace, dole da biyu, cikin dariyar Mama ta nunawa Indo gun wanke wanken ta, tace

" Jeki ki ɗauko gashi can kixo na wanke miki kayin, tsifar ma ni sai nayi miki, Mlm Indo kyakkyawar garin nan, Mama ta faɗa tana cin dariya.

Indo dai bata Wani damu da dariyar da Mama ke mata ba, ta shige ta ɗauko Omon, tas Mama ta wanke mata kayin tana zolayar ta, tsifa Mama tahau yi mata, gashin Indo yana da masifar tsayi, ga yawa, kuma yana da ɗan tauri kaɗan, runtse idon ta, take, tana jin zafin yanda mama ke figar gashin nata, cikin fara gajiya da jin zafin tace

" Mama ki daina min da mugunta Mana, wannan ai mugunta ce, sai jamin kike da ƙarfi.

" Nice kuma nake miki muguntar Indo, cewar Mama.

" Yo to Mama, gani nayi sai jamin gashi kike da ƙarfi, dole nace munguta mana, ai sai kimin a hankali, Allah kika cigaba da jamin gashi zan fasa kitson ma, sai nabar gashin a haka.

" Wannan shegen taurin gashin naki, daya kusan wata biyar baiga kitso ba, ai dole aja shi da ƙarfi, idan kuma bakya so to sai na ƙyale ki, adunga miki kallon ƙazama, mummuna, kinga yanxu ma yanda kika fito fes dake ƴar ɗagwas ɗagwas kyakkyawa.
Ta ƙara zugata.

Washe baki Indo tayi tace.

" Wasa fah nake miki Mama, kedai ita jan gashin zanyi hkr, kuma wlh Mama yau har ƙunshi zanyi, a gidan Hajiya Innah ma zan kwana nayi ƙunshi na, mai shegen kyau, bari ma jummalo ta shigo na aiketa gidan su Zainabu ta siyo min gam ɗan yanka, ina zaki bani kuɗin koh Mama harda na kitson ma.

" Dole na mah kuwa, ai yau komai kike so zan baki shi cikin gidan nan, Hajiyar kyau.

Jummalo da ta shigo gidan ne, ta ga Indo anyi fes, sai faman tsifa suke yi, dariya ne yaso ƙwace mata, amma sanin Halin Indo da tayi kamar yunwar cikin ta yasata maida dariyar ta ciki, tasan tana dariyar nan, to yau kuma ta shiga Uku mai kwatarta hanun Indo sai Allah, ƙara sowa tayi wajen nasu tare da cewa.

" Ganan aiken naki nan, Mama wai inji innar talatun kuma, ki aiko da kuɗin dashen naki, harda na wancan satin.

" Kinga jummalo shiga ɗaki, cikin samira ta, na ukun nan akwai kuɗi ciki, ki ɗauko dubu ɗaya, ki kawai innar talatun, kixo ga ashirin ki karɓowa, Indo gam a wajen Goggo Hali.

Cikin mamaki Jummalo tace,

" Gam kuma Mama, me Indo kuma zatayi da gam, chap Abun mamaki, wai da gaske ƙunshin nan zakiyi ne.

Ko kafin Mama ta bawa jummalo Amsa Indo ta mayar mata da cewa.

" *Ubanki zanyi da Gam, kinji shegiya dai, har wani tambaya ta kike mai zanyi da gam har da wani mamakin ki, to kyau zan fuki dan uban.............*

Buge bakin Indo da Mama tayi ne ya hanata karasa maganar tata.

" Wai Indo me yasa baxa kiyi hankali bane, yanxu uban naku kike zagi dake ke baki da mutunci, kedai ba'a zama dake lfy wlh, sai kin nemo masifa, yanxu dan ta tambaye ki, shikenan sai ya zama laifi.

Tura baki Indo tayi tace.

" Tambayar Rainin wayo fah tamin, kuma na rantse da Allah, sai na yiwa jummalo shegen duka yau cikin gidan nan, badai kin daki baki na akanta ba.

Sake mata kai Mama tayi,tare da cewa.

" Tashi kije ki kashe ta, baki dake ta, ba tunda ke baki da mutunci, kuma naga wanda zai biya miki kuɗin gam ɗin dana kitson, marar mutunci.

Cikin Rau Rau da baki Indo tace.

" Idan kin hanani sai me, *ko a kwalar Rigata tunda Innah tana duniya ai dai baxan ga baƙin ciki ba, ehe*
Kan jummalo tayi da gudu yayin da itama jummalo tayi waje da gudu, Rufa mata baya Indo tayi, kira Mama take ƙwala musu, amma basu ma san tanayi ba.

A kofar gidan, Ɗan Birija, Indo ta ritsa jummalo da duka, sai kokuwa suke yayin da yara suka cika suna musu waƙa.

Jin hayaniya da Ɗan Birija yayi ne, ƙofar gidan sa, ya sashi fitowa, Indo ya gani tasa JUMMALO gaba sai duka take, kamar wacce ta samu jaka, kasancewar ƙarfin su ba ɗaya ba, ya indo tafi ƙarfin jummalo.
Da ƙyar Ɗan Birija ya ɓanɓare Jummalo daga hanun INDO, huci Indo take tana cewa.

" *Ko yanxu kinji A jikin ki, harda dukan Asarar kuɗin da Mama zata bani, kika min bakin ciki na miki, gobe ma ki sake shiga safga ta*.

Juyawa jummalo tayi tana zabgar kuka, ta koma gida, yayin da ita kuma Indo tayi hanyar gidan Hajiya Innah tana zagin ɗan birija ƙasa ƙasa, ya jita sarai amma ya ƙyaleta saboda yasan ba kunya gareta ba, ta basa Kunya cikin mutane ba abu bane mai wahala wajen ta.

" Innah !! Innah !! Innah !! Innah dai wai ina kika shiga, ina kiran ki, kinyi shuru, idan baxaki amsa ba, sai nayi tafiyata Wlh.

Innah da ta fito daga banɗaki ne, tace.

" To Uwar ƴan marassa hakuri, saboda ina tsoron ki, Uwata karki tsine min na shiga duniya, sai na taka dokar Ubangiji na amsa miki ina daga cikin banɗaki, Uwar ƴan mita.

" Mtss, wannan kuma matsalar kice, ni yanxu kuɗi zaki bani na tafi kitso gidan Laure kinga na yanke farce na, Idan na dawo daga kitson kuma zaki bani Lalle na ƙunsa.

" Muje ɗaki na baki, yau kuma aljanun tsafta ne, kenan suke kusa.

" Kinga Innah idan zaki bani ki bani, idan baxaki bani ba, shikenan, sai na haƙura, basai kin tsaya kina jero min magana ba.

"Muje nace ai na baki ko, Uwar marassa Kunya.

Tura baki Indo tayi, suka shiga, Innah ta bata ɗari ɗaya.
Ficewa Indo tayi tana cewa Innah sai na dawo.

Adawo lfy Innah ta mata, bayan fitar indon ne Innah tace.

" Ikon Allah yau kuma
A indon ta take, to Allah dai ya raba yaran gari da shiga gonar ki, dan Wlh yau duk Wanda ya shiga gonar ki yau baxai fito lfy ba.


*Dutse local government*

Sai wajen ƙarfe tara na dare, su mustapha suka shigo cikin gidan, tare da mahaifin nasu Alhaji Haruna.

Zubewa mustapha yayi saman kujera tare da cewa.

" Wash Allah Wlh yau na gaji Momy, kaina ke ciwo.

" Momy gaskiya Rayuwar ɗanki akwai gyara cikin ta, ace mutum shi a rayuwarsa baya ƙaunar Hayaniya, tun ɗaxu yake mita, cikin kasuwar nan.
Cewar Habeeb.

Daddy ne yayi murmurshi cikin ƙaunar yaran nasa, yace.

" A'a Habeeb bana son takura, kasan dai kowa da yanayin sa, dan haka karka takura min Yaro.

Dariya Mustapha yayi tare da cewa,

" Yawwa daddy gaya masa dai ko zai gane, tunda ya kasa fahimta ta, har yanzu.

Tsumewa Habeeb yayi, tare da tura baki yace.

" Na dai gane cikin gidan nan, ba'a sona anfi son mustapha, RAUDA kawai ke kulawa dani cikin gidan nan.

Dariya RAUDA tayi tana satar kallon Mustapha tace.

" Sannu da dawowa Daddy.

" Yawwa sannu RAUDA, ya kike jin zaman gidan namu, ina fatan dai baki da wata matsala, idan akwai kuma kiyi gaggawar sanar dani, domin magance miki shi.

Shuru RAUDA tayi tare da duban mustapha tana jin a cikin zuciyarta kamar ta sanar da daddy buƙatar ta, na son Auren Mustapha, sai dai kuma tana jin nauyin Daddy baxata iya sanar dashi wannan zancen ba.

" Babu wata matsala daddy, ina jin daɗin zaman cikin gidan nan sosai.

Alhamdulillah daddy yace, haka ake buƙata.
Kallon Momy yayi yace.

" A'ishah muje ki haɗa ruwan wanka ina son zan kwanta da wuri, bacci nake ji, kai kuma Habeeb, karka wuce DASINA ba tare da mun haɗu ba, saboda akwai saƙon da zan baka.

Da to Habeeb ya amsa sannan daddy suka haura sama shida Momy.

RAUDA ce tace.

" Ya Habeeb ganan abincin naka yana daining.

" Yawwa RAUDA na gode sosai bari na cika tunbi na kafin na haura sama, wannan bawan Allahn kan sunci abinci da Momy ta aika kasuwa, ya nuna Mustapha da hanu.

Taɓe bakin sa Mustapha yayi tare da cije lips ɗinsa, ya tashi yana ƙoƙarin haurawa sama, sai idon sa ya hango masa Sharifa tana zaune tasa, su ishaq da Sharif gaba sai buga games suke, tsawa ya daka masu.

" Keeeeeeee.

A gigice su Sharifa suka ɗago idon su, jin muryar Dodon nasu Mustapha, Uban ƴan takura, cewar Sharifa.

" Uban

Please Login or Register in order to submit comment