Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Indo, da akwai Inda zan kaita, na samu tabar garin wlh dana kaita na huta, kullum cikin jawo min magana take wajen al'ummar gari

Murmurshi daddy yayi tare da duban Baba yace.

" Haba Mlm Musa, yarinta ce ke damun Indo, zata gyara idan ta girma, addu'a ya kamata mu dinga mata,a matsayin mu, na iyaye gareta, Kuma da kake maganar inda zaka kai Indo, ina ka barni, nima ai ubane ga Indo, insha Allah da Indo zamu koma Birni, karka damu.

Murmurshi Baba yayi tare da cewa.

" Alhamdulillah dako naji daɗi wlh, na samu na huta da kawo togaciya.

Dariya Daddy yayi sannan suka cigaba da zancen duniya.

Karfe tara dai-dai na safe mustapha ya shigo cikin garin Dasina.......



Kuyi hkr wlh school ya sani gaba, wannan ma dakyar na samu nayi typing ɗinsa, idan kunci karo da typing error kuyi hkr banyi editing ba.

Karku manta da cewa bana typing asabar da Lahadi.


*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*


*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah)*
[2/2, 9:16 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*INDO* *ABIRNI*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


Na

Rasheedat Usman

Ummu Nasmah


Marubuciyar

Sauyin Rayuwa
Nasmah ko Nasirah
Sada da Sassaka


Tallah Tallah Tallah Tallah


Rabarine dake dauke da tsantsar soyyayah, tare da munafurci.
Akwai darasin rayuwa sosai a ciki.
Zai kuma fad'akar daku ya kuma nishad'antar daku.
Kudai ku biyo ni karku sake a baku labari.


*Ga kad'an daga ciki.*


" Wacce irin mahaukaciya ce ke, ki duba kiga yanda kika bule ni da k'asa, wawiya marar hankali, zaki kauce min da gani ko sai na makeki, useless kawai.

Tura bakin ta INDO tayi, tace wlh baxan bar nan ba sai kace kana Sona, shikenan, sai dai ni kad'ai nata sonka kai baxaka soni ba, wlh yau sai kamin irin Abunda nake gani a tibin Hajiya Inna,
Bari na tuno abun ma 🤔
Yawwa kiss, kiss suke cewa wlh sai kamin kafin nabar nan.

Zaro ido waje Mustapha yayi, yace.

" Allah ya sauwak'a naso k'azama irin ki, k'azamar k'auye, waima tukunna uban waye zai Miki kiss, da wad'annan yellow hak'waren, b'ace min da gani kafin na targad'a ki.

Murgud'a masa Baki tayi, tace
" Wlh sai ka mini, rarumo rigarsa sa tayi ta dugungune a ciki, sai tsalle take, cikin rigar sa, tana ihu, tana cewa, wayyo Allah na shiga Uku Ya mustapha yak'i mini kiss, wayyo Allah Juma'a kuxo, ni kad'ai nake sonshi shi baya Sona.



Da gudu ta shigo cikin gidan,.
Hajiya Inna dake zaune gindin murhu, ta tashi a birkice tabi bayan INDO da gudu itama.
Gudu suke sanda suka shiga d'akin innah, sannan dukan su suka tsaya, cikin Hakki Hajiya Innah tace,

" Ke Indo gudun me kike haka, meya faru macijin nan ne, ya K'ara biyo ki yauma koh.

Dariya Indo ta shek'e dashi tana nuna Innah da yatsa, tace

" Amma dai Inna ke ba k'aramar matsoraciya bace wlh, daga gani na ina gudu sai ki biyo baya na.
K'ara shekewa da dariya tayi, tana nuna Innah yanda taga Innah tayi tsamo a gefe.



Na rantse da Allah Alhaji baza'ayi wannan Auren ba sai dai kuma Idan mutuwa nayi ayi, Amma banda dai ina Raye, yarinyar da ake labarin ta addabi kowa a garin su, hatta iyayen ta sun gaji da ita bata ragawa kowa, shine ni za'a d'auko masifa a kawo min gida, to Wlh baxai yiwu ba, ku sanja lale.

" K'arya kike Habiba wannan Auren dole sai anyi shi karki manta da cewa Umarnin Hajiya ce kuma dole nabi umarnin mahaifiya ta.

" Oh haka kace koh.

" Eh haka nace.

" Shikenan to ayi mugani.


Na shiga uku ni Maryam, yarinyar nan, zaki kashe ni kwana na bai k'are ba, Yanxu INDO mai garin Kika zaga, hankalin ki ya kwanta, gashi can sun Kama mahaifin ki ta dalilin masifar ki.

" Mama kiji ki da wata magana dai, wai na jawa baba masifa, masifar mai na jawo Masa, mai garin bashi ne ya fara zagin ubana ba, shine nima na zagi Uban sa, kinga ai Anyi One One Babu bashi, kuma wlh Mama, muddun mai gari ya zagi baba koya sa aka rufe sa, to Wlh ya jawa kansa masifa dan wlh baxan barshi yasha iska a cikin garin nan ba.




Mun gaji mlm Musa, ka d'auki y'arka kubar garin nan, tunda y'arka tafi k'arfin ka, har yaushe zamu zauna yarinya tana samu cikin masifa.

Kayi hkr mai gari d'an yaune ka haifesa baka haifi Halin sa ba, wlh ina iya bakin k'ok'arina akan yarinyar nan.




" Malam zan iya kashe ko nawa ne, muddun zaka wargaza wannan Auren koda dukiya tace gaba daya zan iya mallaka maka ita, indai za'a fasa Auren nan.



Batayi tunanin ko yana d'akin ba, kawai tasa kanta cikin d'akin, dressing mirror ta nufa, tasa hanun ta da niyar d'auko turare, cikin rashin sa'a Gaba d'aya kayan saman mirrorn suka yo kasa, ji kake tas !! tas !! tas kwalabe sun fashe, a matuk'ar Razane mustapha ya farka daga baccin, dafe kansa yayi sanadin ganin INDO tsaye, ta zubawa kwalaben ido sai dariya take tana cewa.
" Maganin d'an gwalli, idan ba iskanci ba, meya had'a namijin da kayan kwalliyan Mata.

Tsawa ya daka mata, yace

"Ke mahaukaciya uban waye ya baki damar shigo min d'aki

Harara ta daka masa tare da murgud'a masa Baki tace.

" *Uban Kane*



Habiba kiji tsoron Allah ki kyale yaran nan suyi Auren su, karki bari Rabo ya kashe ki.

"Wlh Yaya baxan bari ba, sai dai Rabon ya kashe ni, idan yaso ayi bayan Raina.

Ku biyo Alkalamin Rasheedat Usman



Karku bari a baku labari
[2/2, 10:06 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*



👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻


*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*


*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.


*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻


*GODIYA*

Gareku *Hassan Tanko Hussaini 80k Mu'az* baxan gajiya da godiya gare kuba, Ubangiji Allah ya saka muku da alkairinsa, ya baku abinda kuke nema duniya da lahira, ya rabaku da baƙin cikin duniya🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻


*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*P*•••••••3️⃣1️⃣ ➡️ 3️⃣2️⃣

Bayan yayi parking ɗin motar sane, ya nufi wajen su, Baba, dake zaune suna zancen duniya, har ƙasa ya sunkuya ya gaishe da iyayen nasa.

" Baba ya haƙurin rashi, jummalo kuma anxo ƙa'ida.

" Hkr alhamdulillah Mustapha, ya hanya.

" Hanya alhamdulillah Allah ya jiƙanta Baba yasa ta huta.

Da ameen Baba ya Amsa, Daddy ne, yace.

" Muhammad Mustapha ya hanyar dai.

" Daddy hanya alhamdulillah, tun jiya naso shigowa, to ban samu na ƙarasa Abunda nake bane shiyasa, bari na shiga cikin gidan nayiwa Mama ta'aziya.

A fito lfy daddy ya masa sannan mustapha ya shiga cikin gidan su, Indo.

Sallama yayi Mama dake sunkuye tana alwala, ne ta ɗago kanta, ta amsa Sallamar tana yiwa Mustapha sannu da zuwa, tare da ajiye masa kujera ƴar tsugunne, zama mustapha yayi yace.

" Ina wuni Mama,

" Lfy lau Muhammad ka samu isowa kenan.

" Ehh Mama na samu shigowa, ya haƙurin rashi, jummalo taxo ƙa'ida.

" Hrk alhamdulillah, jummalo kwana ya ƙare.

" Allah ya jiƙanta da rahama yasa mutuwa hutuce a gareta.

" Ameen Muhammad ameen na gode sosai, da ya aikin naka.

" Aiki alhamdulillah mama.

INDO da fitowar ta kenan daga banɗaki, tayi tozali da mustapha, wani irin tsalle ta daka tare da tahowa gaban mustapha da gudu ta tsugunna tana kallon sa, ba tare da tayi magana.

Gabaki ɗayan su, kallon Rashin hankalin Indo suke, ta tsugunna, ta zubawa mustapha ido ba tare da tace komai ba, shikam mustapha daman can kallon mahaukaciya yake yiwa indo, domin kuwa bai taɓa ɗaukar ta, cikakkiyar mutum ba, tsaki yaja tare doka mata harara.

Mamace ta dakawa INDO tsawa tace.

" Meye haka, kinxo kinsa shi a gaba sai kallonsa kike, kamar wanda kika samu tibi.

Sai yanxu Indo tayi magana, dariya tayi tace.

" Kai Mama ya mustapha nane fah, kallon sa, nakeyi ina jin daɗi cikin raina, kuma fah Mama na daɗe bangan saba, kullum fah sai nayi mafarkin sa, sai kuma ta maida kallon ta, wajen mustapha tace.

" Ya mustapha ka ƙara kyau Alkur'an, kaga yanda kayi kyau kuwa, yawwa ya mustapha, ashe daman ku biyu ne, masu kama ɗaya, kamarku ɗaya da ya Habibu, sai dai shiya fika kyawun hali, wallahi yana da kirki, ga son mutane da fara'a, amma kai kuma kullum cikin ɓata rai kake da faɗa, Allah ya Mustapha kai baƙin Hali gareka, ni da badan badan ba, koh Aradu da ya Habibu zan koma so.

Girgiza kanta Mama tayi, cikin haushin Indo tace.

" To shashasha tashi ki tafi tunda kin gama jero maganar taki, kedai Indo zanga Ranar da zakiyi hankali.

Carap Indo tayi tacewa Mama.

" Sai randa na Auri ya Mustapha zanyi Hankali Mama.

Maganar Indo dariya ta bawa mustapha sosai yake dariya yana kallon Indo, Wai sai randa na Auri mustapha zanyi Hankali, cikin Zuciyar sa, yake cewa, ashe kuwa bazaki taɓa Hankali ba, a duniya.


Ita kuwa Indo tsayawa tayi tana kallon dariyar mustapha, domin kuwa bata taɓa ganin sa, yayi dariya Kamar haka ba, sai dai idan ta mugunta ce.

" Lah Mama kiga irin abun kumatu na, a kumatun ya mustapha, tana nunawa Mama dumple ɗin mustapha, wallahi munyi anko, sai kuma ta tsume tace, Toshi ya Habibu baida shi, nidama shine yake dashi mukayi anko.

Sallama mustapha yayiwa Mama tare da bata 30k yace, gashi Mama babu yawa.

" Mai yawan kenan mustapha Allah yayi muku albarka na gode.

Fita mustapha yayi, Indo zata rufa masa Baya, Mama ta riƙo hanun ta, tana cewa.

" Komo sakarai, uwar rashin Hankali, jeki ƙarasa min, sharata maza.

Komawa Indo tayi tana tura baki tare da ɗaukar tsintsiya tana yiwa Mama ƙananun magana.
Ita dai Mama bata kulata ba, saima sallah data tayar.

A kofar gida mustapha ya samu su Daddy wannan karon harda Tanimu, hanu mustapha ya miƙawa Tanimu sukayi musabaha, har mustapha zai shige yayi gidan Innah daddy ya dakatar dashi da cewa.

" Kaga Muhammad Mustapha, kaima kazo muje, wajen mai garin tare, kafin ka shiga cikin gidan.

Dawowa mustapha yayi ba tare daya san me zasuyi wajen mai gari ba.

Baba ne yace Tanimu ya kira Indo, kiranta Tanimu yayi suka sata a gaba, har gidan mai gari.

Fadar mai garin cike take, da mutane, Mlm Usman mahaifin Garba shima yana zaune, har da garban, zama sukayi tare da gaishe da mai gari, cikin fara'a mai gari ya amsa yana cewa.

" Haruna ashe ka shigo cikin garin nan, wato dabadan abokin ka, Mlm Musa ba, bazan ganka ba harka tafi.

Dariya Daddy yayi Yace.

" Daman zanzo yallaɓoi, ai ban isa naxo garin nan na tafi ba, banxo mun gaisa ba.

Shidai Mustapha gefe ya zauna yana sauraron su, kafin mai gari ya dubi, Mlm Musa yace.

" Mlm Musa sai kuma kaji kirana koh, yanxu Mlm Usman yaxo ya kawo min togaciyar ƴarka Indo, kallon Mlm Usman mai gari yayi yace, ya faɗi Abunda yake ƙarar Indo dashi.

Dallah dallah Mlm Usman ya maida magana, ya ƙarasa da cewa, dan haka bazan yadda ba, tunda har Abun ya zamo da neman rai.
Ga nan Alhaji Haruna a gabansa akayi.

Mai gari ne yace.

" kaji Abunda yace, ke Indo anyi haka ja'ira marar mutunci, sheɗaniya, faɗa min anyi haka, dan ƙaniyar ki.

Babu tsoro fuskar Indo tace.

" Anyi mai gari, Kuma wlh ko yanxu ya sake zagina, sai nayi masa shegen duka, a wajen nan, tunda shi ɗan marar mutunci ne ni so nayi ma ace mutuwar yayi ai ba suma ba, kuma wlh niba sheɗaniya bace😏.

Baba ne ya daki bakin Indo, Yace.

' rufe min baki dan uwar ki, wayace kiyi magana wato dai Indo bazaki daina nemo min magana ba koh.


Narai narai Indo tayi da ido tana Cewa.

" Waye yace nayi magana kuwa idan ba, mai gari ba, sai kuma ta kalli Mlm Usman, tace wato Baba Usman kaima haka kake koh, har zaka kawo ƙarata wajen mai gari ina ƴar mitsitsiya dani, ka kawo ƙarata wajen mai gari, to mai garin ubana ne, shi da kakawo ni wajen sa, to ai saiya kashe ni idan shi mala'ikan mutuwa ne, aikin banxa kawai mai garin banxa mai garin wofi😏.

Zaro ido mustapha yayi, yana kallon Indo cikin tsoro da mamaki, to wlh yanxu kam yarinyar nan ta fara bashi tsoro, wannan wacce Irin yarinya ce.
Sam bata tsoron kowa cikin rayuwar ta.

Daddy ne, ya nisa tare da cewa mai gari

" yallaɓoi dan Allah ina neman alfarma, a sallami yarinyar nan Indo ta tafi, muyi wannan maganar mu kaɗai.

Kaɗa kansa mai gari yayi shima cikin tsoron lamarin Indo yace taje ta.
Domin kuwa wannan yarinyar tacacciyar shaiɗan ce.

Baba kuwa ya kasa magana tsabar bakin ciki har Indo ta tafi.

Mai gari ne ya fara magana, cikin kaushin Murya, da kuma fushi, domin kuwa yafi ganin laifin Baba fiye dana Indo, gani yayi kamar sune suka barta take Abunda taga dama.


" Mlm Musa, mun gaji da halin yarinyar ka, cikin garin nan dan haka kasan yanda zakayi da ita, kawai tabar garin
nan, tunda tafi ƙarfin ku, ku iyayen ta, wannan wacce irin Fitina ce, duk yaran garin nan babu wanda ake kawo ƙarar sa sai ita.

Murmurshin takaici Baba yayi sannan ya cewa mai gari.

" Kuyi hkr mai gari ɗan yaune ka haifesa baka haifi halin saba, wlh ina iya bakin ƙoƙarina akan yarinyar nan, amma kuyi hkr insha Allah indo zata bar garin nan.

Gabaki ɗaya wajen alhamdulillah suka furta, mai gari ne, yace shikenan magana ta ƙare, zaku iya tafiya.

Ran Daddy Idan yayi dubu toya ɓaci, domin kuwa yaga rashin hankali wajen mai gari, taya zaice ya kori yarinya daga gari, idan bata da wajen zuwa kuma shikenan sai dai ta shiga duniya, lallai ana mulkin jahilci cikin garin nan, tashi Baba yayi a fusace ya cewa mai gari.

" Naji na gode tunda har ka kori ƴata cikin garin nan nima ka koreni, karka manta da cewa Indo Macece ba Namiji ba, da za'ace tabar garin, wannan kujerar bata kamace kaba, domin kuwa mulkin Zalunci kake cikin wannan garin.

Kowa shuru yayi yana sauraron Baba, shiko mustapha baiga laifin Baba ba, ko kaɗan, domin kuwa duk rashin mutuncin Indo bai kamata ace an koreta, cikin garin ta, na haihuwa ba, tabbas da za'a kira Human Right suji wannan hukuncin da mai gari ya yanke Wlh sai sun ɗaure sa.

Shiko Tanimu baice komai ba, domin kuwa duk abunda akayiwa Baba indo ce ta jamasa, tashi Tanimu yayi ya fice daga fadar cikin ɓacin rai.


Cikin ɓacin rai mai gari tace, a kama Baba aje a rufesa, tashi dogarawa sukayi, Baba musu Baba ya tashi zai bisu.

A matuƙar Harzuƙe mustapha ya tashi, zaiyi kan dogarawa, Daddy yayi saurin riƙe hanun sa, tare da girgiza masa kai.

Ficewa mustapha yayi daga wajan a matukar Harzuƙe, gidan su Indo yake da niyar zuwa, domin kuwa yau sai yayiwa Indo dukan mutuwa, tunda har ta jawa mahaifinta cin mutunci.

Shi kuwa Daddy duban mai gari yayi, sannan yace.

" Yallaɓoi dan Allah kayi hkr, ka saki Mlm Musa, indai magana akan Indo ce, ta ƙare daga yau, domin kuwa nine zan tafi da Indo birni, dan Allah kayi hkr mai gari.

Abunka da mai kuɗi, dole idan ya faɗa aji, ko dan kuɗin sa, da ake son maula, umarni mai gari ya bayar aka saki Mlm Musa, tashi daddy Yayi tare da ajiyewa mai gari kuɗi, suka wuce tare da Mlm Musa.

Basuyi gida ba, sai sukayi shagon Baba, domin kuwa baba baya son komawa gida yayi tozali da Indo.

Cikin ɓacin rai ya shiga cikin gidan nasu, Mama ya samu Zaune, ina Indo kawai ya tambayi Mama ba tare da yayi sallama ba.

Tashi mama tayi da sauri tana cewa.

" Wani abun tayi maka koh?

" Wai Mama yaushe wannan yarinyar zatayi hankali ne, kodai tana da ciwon Hauka ne,?

" Me ta maka Mustapha ka faɗa min mana, oh ni Maryam na shiga Uku da halin Indo, ni rabona da ita, tun ɗazu da suka fice da Tanimu.

Ƙwafa mustapha yayi, sannan ya mayarwa Mama da Abunda ke faruwa.

Salati mama ta ɗauka, tana cewa.

" Yanxu an kama malam ɗin, shikenan ai hankalin ta, ya kwanta ta ɗaure ubanta, na rasa yaya zanyi da Indo, nayi dukan nayi faɗan nayi Addu'an amma Sam Indo Bata gyaru ba, saima Abunda ya ƙaru.

" Kici gaba da mata Addu'a zata gyaru insha Allah, domin bakin uwa baida hijabi da Ubangiji akan yaransu, ni bari na shiga cikin gida.

Har mustapha ya fice Mama na salallami.

Ita kuwa, hankali kwance ta shigo cikin gidan tana rera waƙar ta, Mama dake zaune ne, ta tashi tayi kan Indo.

" Indo kin kusa kasheni kwana na bai ƙare ba, yanxu Indo mai garin kika zaga, to hankalin ki ya kwanta, gashi can sun kama mahaifin ki, ta dalilin masifar ki.

" Mama kiji ki da wata magana dai, wai na jawa Baba masifa, masifar mai na jawo masa, mai garin ba shine ya fara zagi naba, shine na rama, ko banza anyi one one, kuma wlh mama muddun mai gari ya rufe Baba, to wlh ya jawa kansa masifa da bala'i dan wlh bazan barsa ba, saina ramawa Baba.

Aikuwa kamar wanda aka jefo mustapha cikin gidan, domin zai shiga gidan Innah ya hango shigowar ta, shine ya fasa shiga ya dawo, domin fara koyawa Indo hankali.



*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*


*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*


*(Ummu Nasmah ce)*
[2/4, 6:10 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*



👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻


*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*


*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.


*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻


Masoyana bazan manta daku ba, domin kun nunawa wannan book ɗin ƙauna, nima Rasheedat ina ƙaunar ku, sosai, ina kuma jin daɗin comment ɗinku, ALLAH YABAR ƘAUNA.


*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*P*•••••••3️⃣3️⃣ ➡️ 3️⃣4️⃣

Alhamdulillah Mama ta furta tare da cewa.

" Gara da Allah ya shigo dakai, gata nan dan Allah karka barta da lafiyar ta, ka sanja mata kamannu dan ubanta, tunda ita rashin kunya tasa a gaban ta.

Danƙo Indo mustapha yayi, wannan karon bai tuna da ƙyamar taba, domin kuwa ranshi a matukar ɓace yake, gashin kanta ya riƙe da ƙarfi, wanda yasa Indo danna ƙara da ƙarfi tana cewa.

" Wayyo Allah na shiga uku Innah, mungu azzalumi zai kashe ni, ka sakeni nace mungu.

Ƙara jan gashin nata yayi da ƙarfi, saka ɗayan hanun sa, yayi ya riƙo hanunta, tare da murɗe hanun, yana murza sa, cikin salon mungunta, ba kuma tare da yace mata uffan ba, azaba iya azaba Indo ta fara kwasar sa, domin kuwa ji take kamar ana tsinka mata jijiyar hanun ta, kanta kuwa ba'a magana, bata kuma fasa ihu da zagin mustapha ba, murmurshin munguta mustapha yayi cikin izza da salon mungunta yace.

" Badai ke marar kunya fitsararriya ba, to yau zanga ƙarshen rashin kunyar ki, na rantse da Allah yau sai kinji azabar da baki taɓa jiba cikin rayuwar ki, daga yau mu ƙulla nida ke, muga shegen da zai haƙura.

Yau fah ran Indo ya ɓaci da mustapha ta manta da Soyayyar da take masa, idanunta sun juye da tsantsar jin haushin mustapha, ƙoƙarin kwacewa take amma ta kasa, duk kuma da haka bakin Indo bai mutu ba.

" Sakkani nace, baƙin mungu, azaba Kuma da kake kira aiko yanxu ka sake ni naji shi, ɗan isk.............

Bata ƙarasa ba, mustapha ya sake mata gashi tare da ɗauke ta, da wasu mahaukatan maruka, tankaɗata gefe yayi, sannan ya zaro Bell ɗinsa, yahau jibgar Indo dashi, wasu taurari masu hasken gaske Indo ta gani sakamakon marin daya sauƙa fuskar ta, tun Indo na zagin mustapha har bakinta ya mutu ta kasa magana, sai ruwan hawaye dake gudu bisa fuskar ta, wani nabin wani, idanunta kam sun koma kamar gauta tsabar ja, amma tsabar rashin imani irin na mustapha bai ƙyale Indo ba, sauƙe mata Bell ɗin da mustapha yayi na ƙarshe saiga fitsari Indo ta sake a jikinta, kallon ta yayi tare da cewa.

" Banxa ƙaramar ƴar iska, ko zaki rama ne, da kike kallo nah, da wasu shegun idanunki kamar na mujiya, gobe ma ki ƙara jawa iyayenki magana, kiga yanda zanyi dake.

Kallon Mustapha kawai Indo take ba tare data, tanka masa ba, domin kuwa wannan karon kallon tsana take binsa, dashi, tunda Uwarta ta haifeta ba'a taɓa mata irin wannan dukan ba, kuma wlh bazan taɓa ƙyale kaba dole saina rama Abunda ka min, bashi kaci, koba juma koba daɗe saina rama, duk cikin Zuciyar ta, take wannan maganar.

Mama kuwa ko kollon indo bata yiba, harkokin gabanta kawai takeyi, ta kuma ji daɗin hukunci da mustapha yayi wa Indo.

Ficewa mustapha yayi, ya tafi abunsa ba tare daya saurari Indo ba.

Tashi itama Indo tayi ta shiga ɗakin mama ta ɗauki, zanin ta, ta fito ta ɗebi ruwa da niyar shiga tayi wanka, sai me, hanun Indo ya kasa ɗaga bokitin ruwan, tsabar murɗan da yasha wajen mustapha, ihu Indo tasa da ƙarfi, a razane mama ta taho wajen, a tunanin ta wani abunne ya sami Indo.

" Meya sameki, kike wannan ihun.

" Ya karya ni, mama wlh ya karya ni, gashi hanuna ya kasa ɗaukar ruwa, ya karya ni, baƙin mungu azzalumi ɗan iska.

Kaɗa kanta Mama tayi, sannan ta ɗauki bokitin tana cewa.

" Maganin ki kenan ai badai ke marar kunya ba, wlh ni dai-dai yamin.

Zuwa mama tayi taje ta sa mata ruwan zafi, sannan ta kai mata banɗaki, domin kuwa tasan bakin Indo bazai taɓa mutuwa ba, shigewa tayi banɗakin tana zage zage.

Da sallama ya shiga gidan, da gudu su Ishaq suka taho suna, Oyoyo ya mustapha, murmurshi Mustapha yayi tare da kama Hanun su, suka ƙarasa kusa da Momy ya zauna yana cewa.

" Sannu da hutawa Momy kina shan ƙauye fah.

Dariya Momy tayi tace.

" Kaga ni kuma yanayin ƙauyen ya min, naso ace muyi sati, sai kuma Daddyn ku, yace jibi zamu koma.

" Ai dole daddy ya koma jibi, ko dan

Please Login or Register in order to submit comment