Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saboda shago, Ina Innah ta shiga ne, najita shuru gidan yayi daɗi babu hayaniyar ta.

" Tana tollet, za kuma ta fito ta sameka, yanxu ka shigo garin ne.

" Na juma da shigowa fah Momy, daddy ne kawai suka shiga dani gari, bai kuma sanar da Momy Abunda Indo tayi ba, kasancewar shi ba mai yawan zancen wani bane.

Sharifa ce, tace.

" Ya Mustapha sannu da zuwa, ya hanya.

" Alhamdulillah Sharifa, yauwa jiya munyi waya da Habeeb yake cemin nace miki kin manta da sakonsa ne, waiya kira layinki baya tafiya.

Kama kanta Sharifa tayi, domin kuwa sai yanxu ta tuno da aiken ya Habeeb, nata haɗasa da Indo a waya, tashi tayi tana cewa.

" Ai kuwa na manta, Momy bari na shiga gidan da akayi rasuwar nan, naje nakai sakon ya Habeeb, na ta'aziyar da yace na isar masa.

A dawo lafiya Momy tace mata, sannan Sharifa ta fice, riƙe da wayar ta ɗauke a hanunta.

Innah kuwa sai yanxu ta fito daga banɗaki, mustapha ta tarar zaune kusa da Momy, kan Mustapha tayi ta sauƙe masa ranƙwashi a kansa, tana cewa.

" Iyayen baƙin rai kuma an iso ne, guntsu iyayen baƙin hali.

Dariya Mustapha yayi, domin kuwa idan da sabo ya saba da halin Innah.

" Na iso, sai akayi yaya, wannan wacce irin mugunta ce, daga shigowata, ki tarbeni da ranƙwashi, waini Innah menene damuwar ki dani ne, kika sawa rayuwata Ido, to dai ko mayya ce, ke zaki ƙyaleni domin kuwa nafi ƙarfinki.

Harara Innah ta daka masa tana cewa.

" Koni mayya ce babu Abunda zanyi da namanka, naman baƙin hali, naci na kwashi tsiya baƙin rai, Allah ya sauwaƙa.

Dariyar draman Innah da mustapha, Momy keyi, domin kuwa tun mustapha yana ƙarami basa jituwa da Innah, gashi kuma har yanzu girman sa, tashi mustapha yayi yana cewa

" Sai kiyi kuma ai, ni bari ma naje nayi Abunda ya dameni, Momy bari naje nayi wanka

Carap Innah tayi tace

" Allah ya tura ƙeya.

Da sallama ɗauke a bakinta sharifa ta shiga gidan su Indo, Mama ta samu tana zaune tana tankaɗe, sai Goggo Asabe data shigo yanxu, gaishe su tayi, suka amsa, cewa Mama tayi Indo tana nan.

" Tana nan mama tace amma ta shiga wanka, ki zauna ga taburma yanxu zata fito.

Zama Sharifa tayi, tana jiran Indo, Baba ne, ya shigo cikin gidan da faɗa yana cewa.

" Yarinyar nan tana jamin cin mutuncin cikin garin nan, wlh da badan Alhaji Haruna yace zai tafi da ita ba, wlh da aurar da ita zanyi sadaka na huta da baƙin cikin ta.

Zaro ido Sharifa tayi jin ance mahaifinta zai tafi da Indo.

Mamace tace.

" Kayi hkr Mlm yanxu nan mustapha ya mata shegen duka, hatta hanunta ma kasa ɗagasa tayi, dan Allah kayi hkr.

" Naji nayi hkr, ki tashi ki haɗa mata kayan ta, domin kuwa Alhaji Haruna yace min gobe zasu wuce Birni.

" Birni Mama tace birni dai Mlm, yanxu Mlm kana ganin idan, ka bawa Alhaji Haruna riƙon Indo baka cutar dasu ba, kafa san Halin Indo ba mutunci gareta ba, bata tsoron kowa, muma iyayen ta, yaya muka ƙare da ita bare kuma wasu, ka duba wannan lamarin fah Mlm.

INDO data fito daga banɗaki take jin maganar Baba kamar sauƙar Aradu, " waini Indo zanje birni, wayyo Allah wayagan ni a birni, Allah yakai damo ga harawa ko baici ba, yayi ɓarna.

" Kinga Maryam bana so karki sake min wata magana, maza ki tashi ki haɗa mata kayan ta, Abunda na saki kenan, ba cewa nayi kimin wata magana ba.

Tashi mama tayi tare da cewa, " Allah ya baka hkr Mlm, bari naje na haɗa mata.

Ɗakin sa ya shige, cikin ɓacin rai, fitowa Indo tayi murna cike fal ranta, ita a dole zata birni, har zata shige taji Muryar Sharifa tace, " Indo wajenki nazo ni.

Juyowa Indo tayi, tazo kusa da sharifa tace.

" Ni kike nema kuma, to gani me zan miki.

" Ya Habeeb ne, yace na kirasa a waya na baki kuyi magana.

Wangale baki Indo tayi tana dariya tace.

" Allah sarki ya Habibu ɗan albarka ashe bai manta da niba ba, haɗamu kinji, baiwar Allah.

Dariya sharifa tayi tace.

" Sunana Sharifa, kike kira na da haka.

" Sharifa, kirasa, aima bakiji Baba yana cewa zan koma garin kuba, nima naje na zama ƴar gaye kamar ke, ina zaki koya min gaye koh.

Dariya sharifa tayi sosai tace.

" Sosai ma kuwa, Indo zan koya miki, bari daina kira ya Habeeb ɗin, kiran wayar tasa Indo tayi, cikin Sa'a kuwa ta samesa, ringine biyu ya ɗauka, kasancewar video Call ta kirasa.
" Ya Habeeb kasan na kusa mantawa da aiken ka, saida ya Mustapha yaxo yanxu yake sanar dani, shine nayi maza nazo na haɗa ku.

Murmurshi Habeeb yayi tare da cewa.

" Ai daman nasan shirmen ki, zaki iya mantawa, ina Momy?.

" Tana gidan Innah ni nazo gidan su Indo ce, bari na bata.
Miƙawa Indo wayar tayi.

Karɓa Indo tayi tana dariya tace.

" Ya Habibu, shine kai kaƙi zuwa koh, sai wannan mungun ne, yaxo, sai kuma tasa kuka, ya Habibu kaga dukan daya min a jikina, duk zanen bulala, yasin Allah ya isa ban yafe masa ba.

" Zaro ido Habeeb yayi yace Indo bulala kuma me kika masa ya miki wannan ɗanyen aikin haka, kin masa laifi koh?

" Wlh ya Habibu ban masa laifin komai ba, kawai baƙar mugunta ce, irin tasa, da kuma *shishshigi shiga dangi da gana masgo, kawai fah Baba ya da mai gari ya tararwa faɗa, yauwa ya Habibu, ina ƙosan Innah data aiken na sayo mata Ranar da zaka tafi, har mukayi faɗa da wani Garba ya zubar min ka tuna.

Shuru Habeeb yayi yana tunani sai can yace.

" Ehh na tuna, ranar meya faru?

" To shine fah jiya na kama garba naci ubansa la'ada waje, shine suka kai ƙarata wajen mai gari, wai dan mai gari ya zagi Baba, shine wannan ya Mustapha yanxu ya dakeni, waini najawa Baba.

Dariya Habeeb yayi yace.

" Kai amma baki ƙyauta ba Indo, yanxu Abunda ya wuce ɗin shine kike ƙulle dashi ni ai harna manta da wannan case ɗin, yanxu kinsan me zai faru.........

Ƙit kiran ya katse sakamakon ɗaukewar network, kasancewar network ɗin garin yawo yake.
Kallon sharifa tayi tace kinga ya mutu kuma bana ganin ya Habeeb ɗin

Karɓar wayar Sharifa tayi tace.

" Kinga network ne, ya ɗauke, ki bari sai zuwa Anjuma idan ya dawo saina kawo miki ni yanzu bari na koma gida.

" Shikenan idan ma baki zoba, ni zanxo da kaina ki cewa Innah ina son zuwa kuma Mama ta hanani fita, yau.

Murmurshi sharifa tayi tace.

" To zan faɗa mata sannan ta tafi ita kuma indo tayi ɗakin Mama, ta samu mama sai famar haɗa mata kayan ta, take.

Daddy zaune shida Momy da mustapha yana sanarda ita cewa zai ɗauki indo, su koma birni kuma gobe da azahar zasu tafi.

Zabura Momy tayi, cikin ɗaga murya take cewa.

" Me kake shirin faɗa minne alhaji, wacce yarinyar zamu tafi da ita, yarinyar data addabi garin su, ta gagari iyayenta, shine ni zaka kawo min masifa cikin gidana, gaskiya bazai yiwuba Alhaji.

" Kinga A'ishah baki isa hanani Abunda nayi niyya ba, nace zan ɗauki indo kuma saina ɗauketa, ina dai gidana ne, inda zata zauna ba gidan kiba, amma gaskiya kin bani mamaki A'ishah bantaba zaton haka kike ba, yanxu idan ƴarki ce haka ta faru da ita, wata tayi Abunda kikayi zakiji daɗi, karki manta da cewa ɗa na Kowa ne, ba'a masa mugunta, dan haka ɗaukar Indo Dole, kuma kema ki riketa.
Sannan kuma ki daina kiran ɗan musulmi da masifa, saboda baki san me zai zama ba gaba.


" Babu dole Wlh na faɗa bazamu tafi da itaba, kuma babu inda zamu da ita.

" To shikenan bari muga ta yanda zaki iya dakatar dani, cewar daddy.

Mustapha cikin ɓacin ran Abunda mahaifiyar tasu keyi yace.

" Haba Momy haba dan Allah, tunda yace zai tafi da ita ke ina ruwanki, kibarsa mana, meye Indo zata ƙara zata rage cikin gidan mu, dan Allah ki bari Momy ki riketa kawai saboda Allah karkiyi tunanin Halin ta.


" Rufe min baki shashasha, to bazan tafi da ita ba, wlh babu mai kaimin masifa cikin gida, yarinyar da bata da mutunci bata ragawa kowa, ina nan tamin rashin kunya har tana neman zagina to wlh banda gidana kam.


Murmurshi daddy yayi yace.

" Gyara kalamanki, kice gidan Haruna ba naki ba, idan kuma a gidan ki nake zaune saiki faɗa min naji.

Cikin fushi Mustapha ya tashi yana cewa.

" Daddy Momy dan Allah kuyi hkr da wannan maganar, ku bari dan Allah.........

__________________________


Tirƙashi ana wata ga wata koya zata kasance, kudai ku cigaba da biyo ni domin jin yanda zata kasance.


*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah ce)*
[2/5, 4:45 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*



👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻


*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*


*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.


*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻


*TALLAH TALLAH TALLAH*

*INA KUKE MAKARANTA LITTATTAFAN HAUSA TO KU MATSO KUSA GA DAMA TA SAMU, SHAHARARRIYAR MARUBUCIYAR NAN TAKU WATO ZAHRAN ABDUL MOMYN AHLAN TAZO MUKU DA SABON SALON LABARINTA, MAI TAKEN SUNA, (COLONEL UBAIDULLAHI) WANDA ZATA SAKE MUKU SHI FREE BA TARE DA KO SISIN KUBA SABODA TSANTSAR ƘAUNAR DA TAKE MUKU*.

*GA KUMA (WAYA KASHE ZAHARA'U) CANKAƊI WAYYO DAƊI ƳAN UWANA MAKARANTA, KARKU BARI A BAKU LABARI DOMIN WANNAN BOOK ƊIN ZAI NISHAƊANTAR DAKU, YA KUMA SAKU CIKIN RUƊANI, LITTAFINE WANDA AKA TSARA SHI, A NUTSE CIKIN HIKIMA DA FASAHA, NAIRA 200 KACAL ZAKU BAYAR KUSHA KARATU, CIKIN NUTSUWA DA KWANCIYAR HANKALI, 200 NE KAWAI*.

*SAI KUNXO GAMAI BUKATA SAIYA TUNTUƁEMU TA NUMBER MU.*


*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*P*••••••3️⃣5️⃣ ➡️ 3️⃣6️⃣

" Sai kace ta bari, karma ta bari, idan bai mata ba daga nan saita koma gidan su ƙofa a buɗe take, amma dai Indo saita koma cikin gidana da Rayuwa.

Innah da tun ɗazu take jiyo hayaniyar sune ta shigo ɗakin tana cewa.

Hayaniyar me nake ji haka, tun ɗazu kamar waɗanda kuke faɗa da girman ku, a gaban ɗanku, wannan abin kunya haka.

Sanin Halin faɗan Innah Daddy shida mustapha har suna haɗa baki, wajen Cewa.

" Babu komai fah Innah muna tattaunawa ne, akan wani lamari.

Murmurshi Momy tayi cikin gadara da Kuma power tacewa Innah.

" Babu wani Abunda ake tattaunawa, sai masifa da ake neman ɗaura mana, mubar ƙauyen nan dashi.

Mustapha ɗaura hanun sa yayi a kansa, cikin tausayawa kansu, na masifar Innah da zasu kwasa idan taji Abunda ke faruwa.

" Masifa kuma, wacce irin masifa, kuma zaku kwasa, cikin garin nan, kinga A'ishah faɗa min meke faruwa?

Murmurshi daddy yayi domin kuwa, shi Momy sauƙaƙa masa magana tayi, gata ga Innah ta isheta riga da zani harda wando.

MOMY cewa tayi.

" Innah wai wannan yarinyar, hatsabibiyar wacce ta zamewa kowa masifa cikin garin nan, wai ita zai ɗauka ya koma da ita birni ni akaimin masifa gidana.

" Kinga A'ishah waye ce, Harunan zai ɗauka ya tafi da ita.?

" Waye kuma masifar da zai ɗauka, idan ba Indo ba, ƴar gidan Mlm Musa.

Zaro ido Innah tayi ta kalli Momy tace

" wa kika ce, masifar maimata min sunan naji, kamar banji da kyau ba?

Murmurshin jin daɗi Momy tayi ganin kamar Innah zata goyi Bayan ta.

" *INDO yar Mlm Musa nace Innah wannan fitinanniyar yarinyar data gagari iyayen ta*

Gyara tsayuwar ta Innah tayi tace.

" *Alhamdulillah na tabbatar da Abunda kika faɗa yanzu, A'ISHAH !! A'ISHAH !! A'ISHAH sau nawa na kira sunan ki*.

" Sau Uku ne kika kira INNAH.

" *To buɗe kunnen ki dakyau kiji, Wlh Wlh zan iya sawa Haruna ya Sakeki take yanxu anan, kuma dole ya sakeki, Indo da kike kira masifa, to nafi ƙaunar ta, fiye da Shi Haruna dana haifesa, ke uwata da ubana kawai zan iya ragawa akan Indo, Babu kuma Babbar masifa sama dake, da baƙya son ɗan wani Indo ba masifa bace, masifar da kike kira ya ƙare a kanki ke kaɗai, shi gidan harunan da kike cewa, indo bazata zauna ba, gidan uwarki ne kona ubanki, to bari kiji Indo tafi min waɗannan ƴaƴan naki 👉🏻, ta mata nuni da mustapha, ashe A'ishah kema baki da mutunci, ban sani ba, munafuka, mai siffar mutanen kirki*••••••••••

Cikin ƙunar rai da jin zafin abinda Innah ke faɗawa Momy mustapha yace.

" Ya isa haka ya isa, dan girman Allah kubar maganar nan, ina dai akan Indo ce, to ta koma Birnin mana, meyene danta koma, Momy ki janye ƙudirinki dan Allah, idan taje ma ba'a kanki zata Zauna ba, haba Momy meyasa kike haka ne, dan Allah kibar zancen nan haka ya isa.

" Karma ta janye cewar Innah, kallon Daddy tayi tace, kai Haruna, naji daɗin zumuncin da zakayi na ɗaukar Indo, ada kace na koma Birni nace maka bazan koma ba koh, to yanxu na janye, *ZAN KOMA BIRNI NIMA DA ZAMA DOMIN KUWA ƘAFATA ƘAFAR INDO, NAGA ALAMA IDAN NABAR INDO TA SHIGA BIRNI ITA KAƊAI WANNAN MATAR TAKA SAITA KORATA DUNIYA, KUMA DUK BAƘIN CIKIN KI, SAI INDO TA KOMA GIDAN HARUNA, KUMA TARE ZAMU TAFI*

Shuru Momy tayi domin kuwa bata da bakin magana tunda sun haɗe mata baki, amma ta ƙullaci, tsanar Indo cikin Ranta, kuma ta ɗau aniyar yaƙar Indo har saita nemi komawa ƙauye da kanta.
Muryar Daddy Momy taji yana cewa.

" Ya kikayi shuru A'ishah itama INNAH kiyi mata musun mana, hmm wato ni kika raina koh, nine ma rainin wayonki, ƙwafa Daddy yayi tare da ficewa daga cikin gidan ma gabaki ɗaya.

Itama INNAH fita tayi tana cigaba da zagin Momy, kallon Momy mustapha yayi, yace.

" Kiyi hkr Momy dan Allah karki sake cewa komai akan wannan lamarin, kibar maganar haka, idan zaki riƙe Indo saboda Allah ki riƙeta, Momy Indo ba gagararriya bace, *domin kuwa babu gagararre sai bararrare na tabbata zaki iya sanjawa Indo ɗabi'ar ta, meyasa baza kiyi shahada ba, wajen gyara rayuwar ta, Momy nasan halin nafiki sanin waye Indo, a cikin shaidancinta ke bakiga komai ba, Please Momy ki daina sa'insa da Daddy, Momy koni zan tayaki gyarawa Indo zama, dan ........

" Kai rufe min baki dallah ka tashi ka tafi kaban waje.

" But Momy ki fiskance ni mana.

" Ka tashi ka bani waje nace, ko bazaka tashi bane sai na ɓata maka rai.

" Allah ya huci Zuciyar ki.
Dole mustapha ya tashi ya fita yabar Momy, zaune cikin fushi da ɓacin rai.

Innah ma dai kayan ta, ta hau haɗawa, cikin gana masgo, tana shirin tafiya birni.

Tafiya take riƙe da kara a hanun ta, tana waƙenta, har ta iso ƙofar gidan Innah, a ƙofar gida ta samu mustapha zaune yana danna wayarsa, sanda tazo daf dashi ya ɗaga idonsa, karaf suka haɗa dana Indo, harara Indo ta dakawa mustapha tare da jan doguwar tsuka, zaro idon sa Mustapha yayi, ya nuna kansa da yatsa yace.

" Ni kikewa tsuka, da harara?

Taɓe bakinta tayi, cikin halin ko inkula ta shige abunta ba tare da ta kulasa ba.

Ƙwafa mustapha yayi yace,

" Baki san waye mustapha amma Babu komai, zamu haɗu ai zaki san kin min tsuka.
Ringine ɗin wayarsa ne yasa shi maida hankali wajen wayan baƙuwar NUMBER ya gani, da kamar bazai ɗaga ba, sai kuma ya ɗauka.

Assalamu alaikum, ina wuni ya Mustapha.

Shuru mustapha, yayi indai ba ƙarya kunnen sa ya masa ba, kamar Muryar RAUDA yake ji.

" Wa'alaikumussalam, ya furta tare da cewa waye ne bangane mai magana ba.

" ya Mustapha RAUDA ce.

Murmurshin takaicin rashin Zuciya Irin na RAUDA mustapha yayi, tambayar Rainin wayo ya mata yace.

" Waye kuma RAUDA, bangane ba, wacce RAUDA kenan?

Zaro ido RAUDA tayi, cikin mamakin wai mustapha bai ganeta ba, nunawa ma yake baisan wata RAUDA ba cikin rayuwar sa.

" Ya mustapha RAUDA ce, ta gidan Alhaji Ahmed.

tsuka Mustapha yaji, tare Cewa.

" Naji menene me kike so, kiran me kika min, me zan baki?

Dibirbircewa RAUDA tayi, ta fara kame kame.

" Amm amm daman na kira na gaishe kane.

Tsuka Mustapha yaja tare da kashe kiran yana cewa.

" Allah wadaran rashin Zuciya Wlh, mutum sai kace maye ance ba'a sonka amma ka nace.

Ita kuwa Indo sarkin hankali, Babu sallama Indo ta faɗa cikin gidan tana ƙwaƙwalwa Innah kira.
Momy dasu sharifa dake zaune suka ɗago ido suka kalli Indo, Momy ji tayi kamar ta kama Indo da duka tsabar haushin ta, Indo bata ji Innah ba, saima hango su Momy da tayi zaune da murnar ta, ta ƙarasa wajen su, Momy ta fara cewa.

" Ina kwana.

MOMY bata ɗago kai ta kalli Indo ba, bare kuma ta kulata, Sharifa ce tace.

" MOMY ana gaishe ki baki jiba

Harara Momy ta saukewa Sharifa tace.

" Da ban kwana ba zata ganni.

Dariya Indo tayi cikin shiririta da rashin sanin ciwon kai, danko ita har cikin ranta bata gane Momy bata sonta ba tace.

" *Aradu kuma haka ne, da baki kwana ba bazan ganki ba, gaskiyar kine, Sharifa baki kira min shiba har yanzu.*

Murmurshin sharifa tayi tace,

" Zan kira miki shi sai ko zuwa Anjuma, yanxu banda caji.

To Indo tace, tayi ɗakin Innah tana kiran sunan ta.

Kallon sharifa Momy tayi tace.

" Wa zaki kira mata.?

" MOMY Ya Habeeb ne zan kira Mata.

Shuru Momy tayi bata sake cewa Sharifa komai ba.

Innah ce ke cewa Indo.

" Ke Uwar ƴan kira, gani nan ina haɗa kayana tare zamu koma Birni, dan bazan barki ki tafi ke kaɗai ba, aje ana miki mungun Hali, gara mu tafi Sawu da sawu, watakil idan anga idona a rage miki.

Tsalle Indo ta doka tana cewa.

" Yawwa Innah tawa nita Allah, ko a lahira ni ina aljanna ke kuma kina kano da daron masa ɗaure a kanki.

" Oh baƙar fata zaki mini, ni bazan shiga aljannar ba saina tsaya ɗauke da daron masa naga dama saina fasa zuwa birnin.

" Kiyi haƙuri Innah ta, bazan sake ba wasa nake miki.

Washe gari da safe Mama ta fitowa Indo da kayanta, suka sata gaba ita da Baba, suka mata faɗa sosai, akan ta rage rashin Hankali, tayiwa su Alhaji Haruna da Momy biyayyah domin yanxu sune iyayenta a hanunsu zaki Zauna.
Ya Tanimu ne yace

" Allah dai yasa zuwa wannan birnin ya zama sanadin shuryuwar ki.

Ameeen Baba suka amsa dashi.

Sosai Indo ta nunawa su Baba taji maganar su, sannan suka sata a gaba har gidan Innah, sun samu suma su Innah harsun fito, bayan gaishe gaishe ne, Mama tacewa Momy.

" To Hajiya A'ishah, ganan Indo, tabar hanuna yanxu ta koma hannun ki da zama, Indo bata da kirki, dan Allah kiyi hkr da ita, kisata a hanya idan kinga tayi ba dai-dai ba, dan.........

Dakatar da Mama Innah tayi tace.

" Mairo ya isa haka, Indo hanuna zata zauna ba hanun wannan ba, ta nuna Momy, dan haka daina bata hkr.
Ku ɗauki kayan mu shige mu tafi, Allah ya sake haɗamu gaba tunda nayiwa makwata ban kwana, ladi ce kawai ban samu ba, kya faɗa mata.

Dole tasa Mama shuru badan taso ba, ita kuwa Momy ko a jikinta domin kuwa koda ance an bata amanar Indo ba karb'a zatayi ba.

Girgiza kansa Mustapha yayi, yana kallon Innah.

A ƙofar gida suka taradda lami da Hansai tsaye, da gudu Indo ta ƙarasa wajen su, tana cewa.

" Lami Hansai kunji zan tafi birni koh?

Hararta lami tayi tace.

" Shine ko kixo ki faɗa mana, sai ɗazu muke ji cikin gari wai zaki koma birni mai gari ya koreki daga garin nan.

" Ke nifa jiya da magaruba nake jin zamu koma birni tare da Innah, kuma dare ne yayi shiyasa ban faɗa muku ba, ƙarya ne kuma ni mai gari bai kore niba.

" To dai haka Garba yake faɗi wai an koreki daga wannan garin, yanxu shikenan Indo mun rabu.

" Ke zan dinga kawo muku ziyara, baga su Mama ba, ai zanke zuwa.

Shikenan to Hansai ta furta tace Allah ya kiyaye hanya.

Ameeen Indo tace, sannan suka je wajen motocin tare.

MOMY da Daddy dasu Ishaq mota ɗaya suka hau motar direban Daddy, shi kuma mustapha da sharifa da Innah sai Indo motar mustapha suka hau, Sharifa ce a gaban Mota Innah da Indo kuma suna baya, ƙauyanci Indo ta fara tun shigar ta motar, hanunta tasa zata kamo wani danja daga cikin motar tana cewa.

" Oh bature ma dai shege ne, Innah kiga yanda yanda motar nan ke sanyi sai kace firji, harfa ƙamshi motar take kiji kujerar ma laushi aradu.


" Hararar Indo mustapha yayi ta madubin motar ba tare daya kalleta yaja motar sa.

INDO tana ɗagawa su lami hanu har suka ɓacewa kallon ta.

*DUTSE LOCAL GOVERNMENT*

____________________________

🤪🤪🤪🤪🤪🤪 Kuyi hkr gaskiya bazan shiga cikin dutse yauba ku biyoni next page, domin ganin *INDO A BIRNI* dan yanxu ne littafin zai amsa sunan sa.

*COMMENTS ɗinku yayi sanyi, to ku sani idan baku gyara ba, nima typing ɗina zaiyi sanyi, na fara slow daman school ya sakoni gaba, daurewa kawai nake ina yin typing wlh domin ku masoyana*.


*Vote*
*Share*
*And*
*Comment*


*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*


*(Ummu Nasmah ce)*
[2/7, 3:57 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*



👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻


*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*


*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.


*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*P*••••••3️⃣7️⃣ ➡️ 3️⃣8️⃣

"Mamy na rasa ya zanyi, mustapha baya saurarata, ko kiran sa nayi, sai ya faɗa min baƙar magana, kafin ya kashe kiran."

Cikin faɗa Mamy take cewa RAUDA.

" Nifa RAUDA na gaji !! na gaji !! Da lamarin ki da mustapha, akan me kullum abu ɗaya yaƙi ci yaƙi cinyewa, keba mace bace, da bazaki jawo hankalin Saba, maganin ma, dana baki kin kasa Zuba masa, to yaya kike so na miki, zuwa zanyi na jawo sa, nace dole ya soki, RAUDA ki saurareni da kyau, idan zaki tashi ki nemo soyayyar mustapha to ki tashi, domin kuwa, nunawa mustapha da kike a Soyayyar ki, a fili, bazai kaiki ba, dole sai kin rage shigar masa, ki daina nuna masa maitarki a fili, ki kama Class ɗinki, cikin kirsa zaki samu ki sawa mustapha wannan maganin abincin sa, domin kuwa idan yaga kin fita harkar sa, to fah dole zai ɗauke Idonsa a kanki, sai ke kuma kibi wannan hanyar ki, samo kansa, ina fatan kin

Please Login or Register in order to submit comment