Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ganin kiran ɗan uwan sa, Habeeb.

" Mutanen India, kwana biyu kun manta da mu fah.

Dariya Habeeb yayi cikin zolaya yace.

Ni waye na isa da mantawa da ɗan uwana na haihuwa, kasan dai kaima hakan baxata kasance ba, rai ya mata da rai.

" Ba wani nan cika min baki kake yi kwana biyu ka jini shuru ai zaka neme ni meya faru.

" Nafa nemi layin ka naji unable to connection, na kira Momy take cemin, ai ka tafi ƙauyen dasina, wajen *Tsohuwa mai Ran Ƙarfe Hajiya Innah*, Gaskiya nayi missing ɗin tsohuwar nan, kasan rabo na da ita, 8yrs.

" Ƙauyen Dasina ko ƙauyen masifa, kullum naje wannan ƙauye sai na dawo da ciwon kan wannan mahaukaciyar Aljanar yarinyar.

Dariya mai sauti, Habeeb yayi, yace.

" Gaskiya zanso ganin wannan, Aljanar taka, da kullum nake shan labarin ta, *umm Waya ga Musty Angon Aljana INDO* zanso ganin Ranar da zaka cewa INDO *I love You*

" Amma dai Allah ya isa tsakanina da kai Habeeb, ashe kuwa zaka mutu baka ga wannan Ranar ba, Allah ya kiyashe ni, ɗiban yayi, kaga ma sai Anjuma naga Alamu, yau da baƙar Fata ka tashi, kafin bakin ka yayi tasiri kaina gara na kashe waya ta.


Dariya ce sosai Habeeb yake tun yana kan kujera saida ya sauƙo ƙasa, yanda Mustapha ya hasala kai kace, ance gobe za'a ɗaura masa Aure da INDO, duba wayan yayi yaga harma ya kashe wayar.

" Mustapha Sarkin Zafin Zuciya, gaskiya duk matar da ta Aure ka, zata sha wahala kafin ta gane halin ka, domin sanin Halin ka sai wanda yayi dogon Zama da kai.

Tashi yayi daga ma daidaicin falon da yake ya shige bedroom ɗinsa tare da turawa Mustapha saƙo kamar haka 👇🏻

Allah ya huci Zuciyar ka ɗan uwana, sannan ka shirya tarbata gobe ina hanya insha Allah, zanzo hutu.


Murmurshi mustapha yayi bayan ya karanta saƙon Habeeb, tura masa yayi da cewa.

Kai amma gaskiya naji daɗi sosai Allah ya kaimu goben da rai da lafiya, bari ma naje na fara yiwa Momy Albishir.



*DASINA*

Kwanan Mustapha Uku da tafiya, Indo dai tsiyar tata da sauƙi, domin kuwa yau har ruwa Mama ta samu Indo ta jido mata, Bayan ta gama ɗibawa mahaifiyar tata Ruwan ne, cikin girma da Arziki tace Mama na tafi gidan Innah.

A dawo lfy Mama ta mata, sannan Indo ta fice daga gidan zuwa na Innah, a hanya ta gamu da Baffah mahaifin, Hansai, har ƙasa Indo ta sunkuya ta gaishe shi, mamaki ne ya cika, Baffah ganin Indo a nutse, har mutuncin gaisuwa ya samu, Amsawa yayi ta shige, abunta gidan Innah.

Baffah ne yace,
" Allah dai yasa *ba nutsuwar kwantan ɓauna tayi ba*

Indo ta samu Innah sai shan Baccin ta takeyi hankali kwance, bata tashe ta ba, saima tsintsiya da ta ɗauka ta sharewa Innah gidan ta tsaf, tare da wanke mata kwanukan ta, sannan ta hura wuta, ta dafa taliyar ta, sanda taci ta ƙoshi tayi gyatsa sannan tace

" Alhamdulillah, to bari na lissafa aikin ladan da nayi yau, na farko dai, nayiwa Mama ɗiban ruwa, na gaishe da Baba, na kuma gaishe da Baffah, yawwa sai yanzu da nayiwa Hajiya Innah aiki, wataƙil zan iya samun, lada, guda *ɗari da tamanin* ko haka na tsaya a cikin satin nan na samu, yawwa to yanzu bari na tashi Innah ta bani Naira hamsin na tafi shagon ɗan tasi na sayo maganin ɓera, dariya tayi tace, ya Tanimu nida kai shege ka fasa cikin wannan ƙauyen, tashi Innah ta hau yi, da salati a bakin ta, Innah ta farka, washe baki Innah tayi tace.

" Kaji ƴar Albarka ina mafarkin ki, sai kuma gaki.

Naɗe kafar ta Indo tayi tace dan Allah Innah gaya min me kika ganni inayi cikin mafarkin.

Dariya Innah tayi tace,

" Ganin ki nayi, a Makeken gidan da Muhammadu Mustapha ya gina, kina zaune hakince, komai sai dai kisa amiki, ga kayan ciye ciye kala kala, ke harda fah ƴarinya na ganki wai harkin haihuwa.

Rufe idon ta Indo tayi wai ita a dole taji kunya, ance an ganta da yarinya ta haihu, cigaba da cewa Innah tayi.

" Kinga wasu maka makan kujeru dake cikin ɗakin ki, harda wani ƙaton tebi.

Dariya Indo tasa tace.

" *Wayyo Allah, Allah ya Kai damo ga harawa ko baici ba yayi ɓarna chap Innah waya ga INDO A BIRNI, za'a ga tsiya Aradun Allah, dan zan tsula ciyata son Raina, kinsan Innah, nifa Idan na Auri ya Mustapha ya daina fita kenan, karma wata shegiya ta gansa tace tana sonsa*.

dariya Innah tayi tace.

" Idan kin hanasa fita naga shegen da zai nemo muku abinci kuci, bare ma kekam mai cin tsiya, nifah nama fi sonki da Habibu, domin kuwa yafi wannan mai zafin ran tsiya, sauƙin kai.

Tura baki Indo tayi tace.

"Kinga Innah Idan kina son mu zauna lfy ki daina zagin ya Mustapha, waye ma habibu, sunan ma ko daɗi Babu, wai *HABIBU* nidai ya Mustapha nake so.

Kama bakin ta Innah tayi, tace

" Ikon Allah, wai damma ba kyale ki yake yiba kullum yana cikin Hantarar ki, da tsangwama.

" Naji nidai yanxu bani Hamsin, tunda sharar da nayi miki ma baxaki gode min ba, sai ki bani ladar shara na da wanke wanke, dan nayi ne domin ki biyani.

Sai lokacin Innah ta lura da sharar da Indo tayi mata, fes ta share gidan ya fita, dariya Innah tayi, tace.

" Sannu ƴar Arziki Irin Albarka, ai ɗari ma zan baki ba hamsin ba, laritarta Innah ta buɗe ta ɗauko gudan Ɗari ta bawa Indo.

Aiko kuɗin nan na shiga Hanun Indo ta tashi a guje, sai shagon ɗan tasi, maganin ɓera tace ya bata na hamsin, karɓar kuɗin ɗan tasi yayi, tare da danƙa mata maganin ɓerar.

A hankali Indo ta shigo cikin gidan nasu tana leƙen, gidan domin bata son kowa yasan ta shigo gidan, cikin Sa'a kuwa Babu kowa tsakar gidan, ɗakin tumakin ta shiga, suna ɗaure sunfi goma, dusar dake gaban su ta zazzagewa maganin ɓerar, sannan ta dama shi sosai, kallon tumakin tayi tace.

" Kuyi hkr fah tumaki ba da son raina ba zaku mutu, wanda ya ɗaure ku shine ya jawo muku dan haka sai ku ɗauki hkr, wuf tayi ta fice tabar gidan kafin kowa ya ganta, a dakalin ƙofar gidan nasu ta zauna, zuwa azhar kafin ta shiga cikin gidan nasu.

Fitowar Mama daga ɗakin ta, zatayi madafi ne, sai taji tumaki na wani irin gurnani, leƙa ɗakin tayi, sai tagan su gabaki ɗaya kwance, bakin su kuwa sai fitar da kunfa yakeyi, zaro ido Mama tayi, da sauri tayi ɗakin Tanimu ta kira sa tare suka fito duka harda Baba, Salati Baba ya ɗauka, cikin mamaki yake cewa

" ikon Allah dobbobi kamar wanda suka ci guba, maxa Tanimu, tafi ka kira idi mahauci yaxo ya siyi dabbobin nan dan Wlh mutuwa zasu yi.

Da gudu Tanimu ya fice daga gidan, a gigice, INDO dake zaune taga ficewar Tanimu, Dariya tayi, tace.

" Lallai magani ya fara aikin sa.

Tare Tanimu suka dawo da idi mahauci, ko Kafin su iso ma tuni tumaki kam sun mutu, gaba ɗaya ko ɗaya bai tsira ba, shuru Tanimu yayi tare da zamewa ya zauna a ƙasa, sai Kuma hawaye ya fara bin idanun sa, Mama ma taji tausayin sa ainun, domin kuwa ko wani rago ɗaya zaiyi dubu Arba'in, Baba kuwa, Haƙuri ya fara bawa Tanimu da cewa ya ɗauki ƙaddara.

INDO da ta shigo cikin gidan ne, ta samu Tanimu na zaune sai famar kuka yake, salati ta ɗauka tare da cewa.

" *Subhanallah me zan gani haka, GARDI da kuka, sai kuma tasa dariya, Allah sarki daɗi na da gobe saurin zuwa, haka Nima jiya iwar haka, ka Sani kuka, sai gashi nima yanxu Allah ya saka min.*

Jin furucin INDO yasa Mama, zargin kodai Indo ce tasawa dabbobin nan wani Abu suka mutu.

" Zo nan Indo cewar Mama.

" Naxo kuma Mama me zanyi ni Kuma?

" Kixo nace ko, idan kuma baxaki zoba, sai ki faɗa min.

Tahowa Indo tayi, kusa da mama, tace

" Gani nan tana tura baki tayi maganar.

" INDO kece kika kashe dabbobin nan koh?

Saurin ɗago kansa Tanimu yayi jin abinda Mama ke furtawa.

Cikin rashin tsoro, Indo tace.

" Ni kuma Mama, akan me zan kashe masa dabbobin sa?, nikam bani bace.

Murmurshi Mama tayi kasancewar tasan Halin Indo, indai kin haɗa ta da Allah to zata faɗa miki gaskiya, sannan tace.

" Dan Allah dan Annabi na roƙeki da Allah ki faɗa min idan kece kika kashe dabbobin nan?

" Shikenan tunda kince Allah, ai kin gama magana, dole zan gaya miki gaskiya.
Har ga Allah Mama ganin da nayi Ya Tanimu haka kawai jiya yata jibgata akan wata banxa lami, Babu wanda ya hanasa cikin gidan daga ke har Baba, shiyasa ganin da nayi bani da gata cikin gidan nan, ba'a sona yasa ni ƙwatawa kaina ƴanci ta hanyar, zuwa gidan Innah nace ta bani hamsin, tana bani kuwa nayi shagon ɗan tasi na sayo maganin ɓera, kuna cikin uwar ɗaka, na shiga na juye maganin ɓarar cikin Abincin dabbobin, Amma fah Kafin na saka musu saida nace dabbobin su yafe Min ai.

A fusace Tanimu ya tashi zai rufe Indo da duka.

Dakatar dashi Baba yayi ta hanyar cewa tsaya Tanimu.
Kallon Indo yayi yace.

" Haba yanzu dan Allah akan ɗan dukan, da ɗan uwan ki, ya miki jiya shine shine zaki masa wannan mungun Aikin, kisan Asarar da kika masa kuwa, haba Indo meyasa bakya jin magana ne, innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un, yanxu Indo, tsiyar taki, harmu ma baki barmu ba, to wa zaki bari, iyayen kima baki kyale ba, bare Kuma Wasu, kiji tsoron Allah Indo ki gyara alaƙar ki da al'umma.

" Haba Baba wacce nasiha zaka tsaya yiwa wannan shaiɗaniyar, Ka kyale ni kawai yau na koya mata hankali cikin gidan nan na karya ta, ta zauna kowa ma ya huta da bala'in ta, dan Indo masifa ce.


Mamace tace.

"Subhanallah, haba Tanimu, ƴar uwar taka kake kira da masifa, baxaka nema mata sauƙi ba, sai kake binta da mungun baki, to karna sake jin ka kirata da masifa, da kake cewa a barka ka koya mata hankali, jiyan da ka doke tan, meya jawo maka yanzu, Bayan Asarar da tayi maka, a yanzu ni kaina Uwar Indo lamarin ta ya fara bani tsoro, idan kace ma dukan ta zakayi, gobe sai ta maimaita maka abinda yafi na yau, addu'a kawai ya dace mu bita dashi, Allah daya bamu ita, shi zamu roƙa ya shirya mana ita.

Baba ne yace.

" Tabbas Maganar mahaifiyar ku gaskiya ce, addu'a shine mafita tsakanin mu, da Indo.


Kallon ta Mama tayi tace.

" Kinyi sallar Azhar ne?

" Banyi ba cewar Indo tana haɗa rai tare da hararar Tanimu.

" Jeki ki ɗauki buta maza kiyi Alwala, kiyi Sallah.


*Ni fah Mama ba yanxu nake yin Sallah ta ba, sai da isha'i nake haɗa Asuba magriba Azhar da kuma isha'i.*



Kuyi hkr da rashin jina jiya da bakuyi ba, hakan ta faru ne ta sanadin bana typing Ranar Asabar, fans ɗina dake group ɗin Sara da Sassaqa sun san hakan.

*Share*
*And*
*Comments*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah)*
[1/6, 4:33 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*



👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻


*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*

*D̸͟͞E̸͟͞D̸͟͞I̸͟͞C̸͟͞A̸͟͞T̸͟͞E̸͟͞D̸͟͞ T̸͟͞O̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni, domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

Aunty Hauwa Maman Uswan ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya.🙏🏻


😄😄😄😄 Sara da Sassaqa fan's kuyi hkr wlh ban manta daku ba, ina nan ina typing ɗinsa, za kuma kuga posting, gobe insha Allah.


*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*P*•••••••9️⃣ ➡️ 1️⃣0️⃣

Tsawa Mama ta dakawa INDO tace,

" Maza ɗauki buta kije kiyi Alwala kiyi Sallah maxa, sannan ki ɗauko uniform ɗinki, na boko ki wanke gobe Litinin kuna da makaranta, Anjuma kuma zakije makarantar Allo.

" Nifa Mama Babu wani wanki da zanyi, haka zansa uniform ɗin, ni bokon ma ba wani damuna tayi ba.

Tanimu dake jifan Indo da mungun kallo ne ya tashi ya fice daga cikin gidan, domin Wlh ji yake kamar ya shaƙe wuyan ta, sai dai babu damar yin hakan sakamakon hanasa da Mama tayi.

INDO tana haɗa rai haka ta ɗauki buta tayi alwala, bayan tayi sallar ne, ta ɗebo uniform ɗin bokon nata, ta wanke su, tas kuwa ta wanke, domin Indo badai iya wanki ba, sai idan bata ga dama ba, tayi jiƙa jiƙa.
Jummalo ce ƙanwar INDO ta shigo cikin gidan hanun ta ɗauke da ledar shinkafar da Mama ta aike ta, ta siyo mata shagon ɗan tasi, da Sallama jummalo ta shigo, amsawa Indo tayi, tare da cewa.

" Zona aikeki jummalo ɗakin Mama ki ɗauko min ɗankwalin uniform ɗin nan.

Babu musu jummalo ta shige ɗakin Mama, tana sallah ta same ta, ajiye ledar tayi tare da duba cikin kayan wankin Indo, da ƙyar jummalo ta samo ɗan kwalin, ficewa tayi ta miƙa mata, cikin neman faɗa Indo ta fara cewa jummalo.

" Wato ke kuma jummalo tsabar baƙar mugunta, shine jiya kika wanke uniform ɗinki ko ki haɗa da nawa ki wanke, kinyi Asara ai ke kam, *mai shegen wariyar Launin fata*,
To gashi ai na wanke yanxu banga abunda ys ya cinye ni ba.

" Kiyi hkr na duba uniform ɗin naki ne ban gani ba shine yasa na wanke nawa kaɗai, Amma ai kinsan kullum nice nake wanke mana uniform koh.

" Kuma haka ne, kinsan nifa idan ana min abu kullum Rana ɗaya banga ammin ba, ji nake kamar ba'a taɓa min ba, shikenan jeki, nima na gama gari zan shiga dan wlh ba xanje makarantar Arabbi ba yau.

Ita dai jummalo shigewar ta tayi ɗakin Mama ba tare da ta tankawa INDO ba.

Washe gari da safe jummalo tayi shirin makarantar ta, kunu da ƙosai taci, sannan tayiwa Mama sallama ta tafi, ita ko Indo bata da Alamar, zata makarantar ma, dan ko karin kumallon ma batayi ba, tana zaune, kawai tayi shiru.
Mamace ta dube ta tace.

" INDO baxaki makarantar bane, jummalo har ta juma da tafiya, takwas fah yanxu, ko karin kumallo baki yiba.

" Zani mana, nafi son sai sun gama wannan tsayuwar tukunna, mema yake da suna, asandabilyu, ko Assambly, oho sai sun gama tukunna.

" Tashi maxa kisa uniform ɗinki, kixo kici abinci, ki shige makaranta, bana son shashancin banxa, ko dan kinga ina kyale ki, shine kike min abunda kika ga dama dan ubanki, ki tashi nace, cikin tsawa Mama take maganar.

Tashi Indo tayi tana ƙunƙuni tasa uniform ɗin, ko karin kumallon ma ƙinyi tayi, ta fice daga gidan.

" Allah ya shirya ki Indo cewar Mama.

A hanya Indo ta ɓelɓelce, ba ita ta shiga cikin makarantar tasu ba, sai ƙarfe tara na safe.
Taxo daidai bakin window na ajin nasu taji for master nasu yana kiran sunan ta.

" *Ashatu Musa*

Daga jikin window INDO ta amsa da ƙarfi.

" *Labbaika Present Sir Naxo, gani nan ma a nan*.

Gabaki ɗaya Ajin juyo da kallon su sukayi zuwa ga Indo, yayin da Mlm Sani ke cin dariya, suma Ajin dariyar suka ɗauka.
Cikin dariyar ne, Mlm Sani yace.

" Sannun ki da zuwa to, sai ki samu damar ƙarasowa koh.

Shigowa Indo tayi ba tare da tsoron lattin da tayi ba, tsayawa tayi gaban mlm Sani tace.

" Mlm gani.

" Meyasa kika zo a latti? Me kuma yasa kika amsa min sunan ki daga waje?
Wa kuma yace kin amsa sunan ki sau biyar?
Mlm Sani ya jefo mata tambaya tare da ƙara gyara zaman bulalar sa, a hanun sa.

Haɗa fuska tayi, tana kallon bulalar hanun sa, kafin tace.

" Mlm duka wannan tambayar zan amsa ni kaɗai.

Ɗago bulalar Mlm Sani yayi, tare da cewa zaki amsa min koh saina lillisaki tukunna.

" Zan baka ta fada masa tana turo bakin ta gaba.

" Ina jinki, tell me.

" Mlm to ka fassara min Abunda kace na ƙarshen, toll ma, meye ne shi da Hausa.

" Murmurshi Mlm Sani yayi kasancewar yasan Indo tana da ƙoƙari, indai akayi darasi bata fahimta, ba, to fah sai tayi tambaya, kuma dags wannan lokacin ta riƙe kenan a kwakwalwar ta, gaskiya Indo badai brench ba.

" Tell me, yana nufin cewa faɗa min.
Kin gane.

Kaɗa kanta INDO tayi alamun ehh ta gane sannan tace.

" Mlm Abunda yasa nayi latti tsakani da Allah bana son tsayuwar asandabilyu ne, na biyu kuma, na amsa ne saboda bana son ka samin banxo ba, sai na Uku kuma, da nace *Labbaika* wai dai Mlm na maka *Larabci ne* dan kasan na iya, *Present Sir* kuma wai na amsa maka ne da yaren turanci, sai kuma *Naxo* da Hausa na maka.
Kaga Mlm ai nayi ƙoƙari dana iya Yaren Uku koh.

Kaɗa kansa Mlm sani yayi tare da jinjina shirme irin na Indo, da yarinta, wato dai Kowa da irin tasa yarintar, duban ta yayi yace.

" Dan Allah INDO daga yau duk ranar monday ki dinga zuwa kina halartar Asembly yana da amfani sosai, sannan daga yau ki daina amsa suna daga waje, ki bari sai kin shigo class tukunna, sannan daga yau idan an kira sunan ki, ki amsa da Present kawai kinji.

" Naji Mlm kuma baxan sake ba in Allah ya yarda.

Muga farcen hannu ki, da kuma kitson ki, uniform dai naga kin wanke.

Miƙo masa hanun Indo tayi, wayyo Allah, farcen Indo sunyi zaƙo zaƙo sai kace wacce bata taɓa yankan farce ba, tunda uwar ta, ta haife ta, kayin ta kuwa da ta buɗe Babu abunda yake tashi sai tsamin datti, kitson ta kuwa tsabar daɗewa har ba'a ganin tsagun.

" Subhanallah cewar Mlm Sani, meye haka INDO, wani irin ƙazanta ne wannan, ki dubi farcen ki, da kayin ki babu ko daɗin gani, haba Indo kike tsafta dan Allah.
Kinji, kinga yanda kike babbar yarinya haɗaɗɗiya, da zaki ke tsafta haba wa, karki ga kyan da zakiyi.

Su Indo Mlm Sani ya fasa mata kai, cikin dariya tace

" Allah Mlm ni kyakkyawa ce.

Dariya Mlm Sani shima yayi domin a iya zaman sa da Indo ya gane idan zaka bita a hankali tana da sauƙin kai, za kuma ka ribance ta, idan kuma da faɗa kake binta, baxata taɓa gyarawa ba.

" Sosai ma kuwa, a wani fitowar kyan naki ma, sai kin yanke farcen ki, kin tsefe kanki kin wanke, kije kiyi kitso, ai Babu mai gane ki Indo tsabar kyan ds da zakiyi.

Ƙara washe yellown hakwaren ta Indo tayi, tace


" Wlh Mlm yau zanyi kitso, na yanke farce na, har ƙunshi sai nayi, Allah sarki ashe ni kyakkyawa ce, nake ɓoye kyawuna.

Murmurshi Mlm Sani yayi cikin jinjinawa yarinta irin na Indo yace.

" To Allah ya kaimu jeki zauna maxa zamu fara lesson.

Rasa wajen zama Indo tayi sakamakon cika teburin zaman da akayi, sai dai ta zauna a ƙasa, hango Zainabu Indo tayi zaune ita da su Hansai, wajen nasu ta nufa, cikin gadara da bata rai, tace, ke Zainabu tashi ki bani waje na zauna.
Saurin tashi Zainabu tayi, kasancewar tana tsoron taƙi, tashi, Indo taci uban ta.
Ta koma ƙasa ta zauna.
Girgiza kanta Hansai tayi ganin fin ƙarfin da Indo tayiwa Zainabu.



*ⓓⓤⓣⓢⓔ*


Dariya sosai RAUDA keyi, har tana riƙe ciki, tace.

" Wlh ya Habeeb ka bani dariya, wai yaushe zaka gane ka girma ne, wai camma, London ɗin haka kake musu irin wannan calikancin.

Dariya shima Habeeb yayi tare da cewa.

" Zan girma amma sai randa nayi Aure dan har yanzu a matsayin Yaro nake.


Momy dake sauƙowa daga step ne take cewa.

" Kai kam baxaka girma ba, tunda har yanxu ka gagara yin hankali, kullum wasa shine cinka da shan ka.

Murmurshi Habeeb yayi, yace

" Kai Momy kema abunda zakice kenan, Momy ai rayuwa saida wasa da Dariya, har yaushe kullum mutum zai zauna cikin haɗe fuska, gaskiya ni baxan iya wannan rayuwar ba.

RAUDA ce tace.

" Shiyasa Rayuwar ka take burgeni ya Habeeb, kana komai cikin sauƙin kai saɓanin ya Mustapha da baya sakewa da kowa, daga Momy sai kai.

Dariya sosai Habeeb yayi yace.

" Bros sai a hankali haka yake tun tashin mu, bai cika sakewa akan komai ba, so kar wannan ya dameki, domin *A JININ SA YAKE*.

Momy ce ta nisa tare da cewa.

" Abinda nake faɗi mata kenan, ta daina damuwa da Halin mustapha, Amma ta kasa ganewa wataƙil idan ka faɗa mata, sai ta gane naka.

" Hmm RAUDA Amaryar mustapha, tun yanxu kin tsoron sa, ina kuma ga anyi Auren, ya faɗa mata tare da kanne mata ido😉.

Murmurshi RAUDA tayi tare da cewa.

" Ya Habeeb kaima dai da tsokana kake, nine muke soyayya da ya Mustapha, lallai zolayar ka bata baka dai dai ba.

Dariya Habeeb yayi yace.

" Shikenan *Abar Kaza cikin gashin ta*
Amma nidai nasan abinda ke wakana.

Jin motsin mutum ne yasa Habeeb juyawa, Mustapha ya hango yana sauƙowa daga step, cikin haɗewar fuska, dariya Habeeb yayi ganin kallon da Mustapha ke aikawa RAUDA, kallon wulaƙanci.
Sanda ya zauna kusa da Habeeb sannan yace

" Sannu da hutawa Momy.

" Yawwa sannu sai yanxu ka fito, Tun ɗazu ɗan uwan ka ke jiran ka, kuma kasan dai Daddyn ku, yace by four ku samesa kasuwa.


" Sorry Momy wlh bacci ne ya danne Ni, amma yanxu ma bata ɓaci ba, zamu tafi, kallon Habeeb yayi yace, muje bros.

" Muje ina ai idan kaga na tashi anan sai Momy ta mana Shari'a, Momy gani ga Barrister mustapha, ki mana Shari'a.


" Ina sauraron ku kaji iyayen faɗa badai ku haɗu ba sai kunyi cece kuce tsakanin ku, cewar Momy.

Dariya Habeeb yayi Yace.

" Momy cewa fah nayi gobe muje ya rakani DASINA wajen Hajiya Innah, amma bawan Allah nan yace baxai jeshi ba.

Murmurshi Momy tayi tace.

" Yana da gaskiya Habeeb, kwata kwata kwanan sa uku da dawowa, kuma gashi ya koma bakin Aikin sa, kaga kuwa kai kaɗai zakayi tafiyar ka.

Dariya mustapha yasa tare da cewa.

" Yes Momy daɗi na dake Adalci, Mlm Habibu Angon Hajiya Innah, tafiya DASINA ya kamaka kai ɗaya, sai ka tashi mu dangana zuwa ga Daddy.

RAUDA ko Babu abunda take sai kallon mustapha Kamar wacce zata haɗiye sa, shiko suna haɗa ido zai maka mata harara.




*Share*
*And*
*Comments*





Please Login or Register in order to submit comment