Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mungun kyau kuwa cikin fararen shaddar, gashi kuwa ya kifa hula zanna idan ka gansa saika rantse da Allah yana son Auren nan kuwa zuwan abokanan nasa ne yasa shi wannan shirin tare suka fita Habeeb yana zungurin Mustafa cikin tsokana, murmurshi kawai Mustafa yake yiwa Habeeb domin kuwa yau yasan Habeeb yana cike dashi ne, wajen su Daddy suka fara nufa suka gaishe shi tare da abokanan harkokin sa, kafin suka wuce wajen abokanan nasu.

Isar su wajen sun tarar su zaune sai faman hira suke da Sallama suka shiga Habeeb yana cewa.

" Barkan ku da zuwa ashe dai za'a Hallaci bikin namu."

Dariya Inspector Muhammad yayi yana cewa.

" Mun Hallaci wannan bikin ne dan kai badan wannan Sarkin miskilancin ba, daya kasa gayyatar mu."

Murmurshi kawai Mustafa Yayi tare da zama yana cewa.

" Bafa Aure na kuka zo ba auren Habeeb kuka zo domin kuwa shine wanda zaiyi Aure ba niba."

Sai a lokacin inspector khabeer yayi Magana yana cewa.

" Ayya yaro daina cika mana baki sanda zakuyi ƙumus a ɗaki kaida RAUDA waya sani, bare kuma gashi Allah ya ɗaura maka jarabar Mata, kunga kuwa kura taga nama ai kuma sai kai hari, ansamu Abunda ake nema har cikin gida."

Gabaki ɗayan su dariya sukayi Naseer yace.

" Jarababbe ko kuma jarabbabu kai ɗin ma khabeer baya ne, ko dan kai yanzu ka haɗa mata biyu abun yazo maka da sauƙi, bari dai nayi shuru karka ce zan maka gori."

Sosai Mustafa yake dariya yace.

" Wow Doctor Naseer daɗi na da kai badai faɗan gaskiya ba, kuma dai alhamdulillah duk jarabata bana neman matan banza ko?"

Murmurshi khabeer yayi tare da cewa.

" Kaima da kace, yanzu kuma an wuce wajen sannan kuma duka mata na babu matar tushe duk nice na zaɓosu da kaina."

Murmushi Habeeb yayi yana Duban Conel Ubaidullahi Kafin yace.

" Ganan ɗan uwan ɗayan ai Uban miskilancin tsiya, ana magana kayi shuru, halin naku ai ɗaya ne, gaka har yanzu shuru ka kasa fitar da matar aure Allah yasa kaima Momy ta maka Auren dole Irin na abokin tsiyar taka."

Hararar Habeeb Ubaidullahi yayi yace.

" So what kai Auren haɗi yake ɗagawa hankali, an gaya maka dan ammin Auren dole sai ya dameni, wlh ko a jiki na, sai naga dama na kalleta, bare har ta dameni."

Dariya Habeeb yayi tare da cewa.

" Ƙaryar banza kawai, ku tashi mu tafi kunga 10:45 saura 15 minute so ku tashi muje."

Tashi sukayi suna raha har wajen ɗaurin Auren, Allahu Akbar alƙawarin Allah ya cika inda Mlm Musa mahaifin Indo da yazo ɗaurin Auren Daddy ya wakilta shi daya amshi Auren ƴaƴan nasa, cikin ƙanƙanin lokaci aka ɗaura Auren Muhammad Mustafa Haroun da RAUDA Ahmad muktar akan sadaki dubu hamsin wanda Daddy shine ya biya musu sadakin, bayan an ɗaura nasu ne aka zo aka ɗaura na Muhammad Habeeb da Hasana Yusuf (Hasina) suma akan sadaki dubu hamsin, cikin murna da farin ciki jama'a ke musabaha dasu suna musu murna, a wannan lokacin bazaka taɓa gane halin da Mustafa yake ciki ba farin ciki ko baƙin ciki, Habeeb kuwa sai washe baki yake yana murna.

Malam musa har gidan Aunty Hindu yaje ya mata murna suka gaisa da Indo sun daɗe suna hira kafin Mlm Musa ya koma, da saƙon Indo na cewa ya gaishe da Ya Tanimu da Mama.

Guɗar Gambo shine ya tabbatarwa da mutanen gidan an ɗaura Auren Mamy itama guɗar ta ɗauka tana murnar cikan burin ƴarta, da kuma nasarar da tayi na cin maganin da Momy tayi, dama an riga da anyi jere tun jiya.

Camma gidan su Hasina ƴan uwa sai taya ta murna suke, Indo kuwa sai shiga take cikin kaya tana fita, zarah ma tazo zata kwana washe gari ta koma, Abba mahaifin Hasina da Aunty Hindu sosai suka yiwa ƴar tasu nasiha game da rayuwar Aure, haka ƴan uwa da abokanan Arziki ma, Hasina tasha kuka sosai, kafin da yamma akazo aka ɗauke su zuwa gidan Momy, an riga kai RAUDA kafin HASINA, a ɗakin su da suke kwana sanda suke gidan aka ajiye su, da nufin bayan an watse su koma ɗakin su, Da daddare misalin ƙarfe tara aka fara shirye-shiryen zuwa wajen dener sosai ake haɗa amaren wajen kwalliya, Bayan mai kwalliyar ta gama musu ne Hasina tace ta yiwa Indo, sosai matar ta yiwa Indo makeup, Wannan karon ma baƙar doguwar riga mai ɗauke da fararen Stone, Indo ta saka dake tana mungun son dogin rigunan, matar yanewa Indo kanta tayi da mayafin rigar, sosai tayi wani mungun kyau.


" Kaga Mlm dan Allah ka shirya mu tafi kaga fa dare yana yi, kuma wajen yana can cike da mutane mune ake jira, dan Allah kayi hkr ka tashi ka shirya mu tafi, karka nunawa duniya cewa baka son zaɓin mahaifiyarka Idan kayi haka Momy ka tozarta ba RAUDA ba, domin kuwa duniya zata ɗauka cewa babu girmamawa tsakanin mu da mahaifiyar mu, pls dan girman Allah badan niba ka shirya mu samu mu wuce."

" Kaga Habeeb kaje kawai babu Inda ni zanje, ai biyayya kam na yita tunda harna yarda aka ɗaura Auren, to dan banje dener ba sai me, ai tun wuri na sanar dakai cewa bazanje ba, kaga ka tafi kar dare ya maka, ka ƙyale ni karka samin ciwon kai."

Habeeb ƙin tafiya yayi ya tsaya yiwa Mustafa magiya, da ƙyar da suɗin goshi Mustafa ya yadda zaije kafin ya tashi ya shirya.

Zarah ce take cewa Indo.

" Wai A'isha wata motar zamu shiga ne kam, tun ɗazu muna tsaye anan ya kamata ace mun tafi wajen dener nan koh."

" Gacar Mota muje mu shiga naga yanzu kamma kamar saura su Aunty Hasina, idan wannan motar ta tafi muje kawai mu shiga wannan ɗin."

Ita ɗin kuwa suka shiga suka wuce wajen dener, Indo basu shiga cikin hole ɗin ba, suka tsaya a waje, sun juma sosai zaune kafin motar amaren ta shigo hole ɗin, kiɗa aka sake, tare da sauƙe musu wani red ɗin capet tun daga bakin hole ɗin har wajen motar tasu, Habeeb yana riƙe da hanun Hasina suka fito, shiko Mustafa yafi 20minute daga cikin motar ya ƙarewa RAUDA kallo wacce taci kwalliya cikin wani green ɗin less, kanta na sunkuye, taɓe baki Mustafa Yayi tare da damƙo hanunta cikin salon mugunta yana murza jijiyar hanun, runtse idonta RAUDA tayi cikin azaba, murmurshin gefen baki yayi tare da cewa.

" Ina tayaki murnar kawo kanki da kikayi cikin maƙabarta, gaskiya na jinjinawa ƙoƙarin ki na ganin kin dage sai da kika *AURENI DOLE* sai dai ina ƙara tuna miki cewa karki manta da maganar da na miki cikin makaranta" yana gama faɗin haka ya jawo hanun nata yana murmurshi a yanda suka fito zaka rantse da Allah suna Soyayya, tsabar bariki irin na Mustafa, sanda suka gama shiga kafin su Indo suma suka shiga, sosai wajen ya tsaru da decoretions kayan ciye-ciye da Shaye-Shaye kuwa kala-kala a wajen, babu abunda yake tashi a wajen sai sautin kiɗa, kafin aka fara gabatar da dener, Barrister Umar tunda ya hango Indo yaji wani Soyayyar ta ta tsarga masa cikin zuciyarsa, komai yake hankalin sa yana kanta, ai kuwa sai kace wacce akace Mustafa ya ɗago kansa carap ya hango Indo, da farko bai gane ta ba, saida ya ƙara tsura mata Ido Kafin ya gane Indo ce, tayi wani bala'in kyau lokaci ɗaya yaga ta dawo masa cikakkiyar budurwa, ga ƙirjinta ma masha Allah wani bugawa Zuciyar Mustafa Yayi da ƙarfi wani irin baƙon yanayi yaji a jikin sa tun daga babbar yatsar ƙafarsa har zuwa cikin ƙwaƙwalwar sa, saurin dafe ƙirjin sa yayi yana cigaba da kallon ta, haka shima Habeeb duk abunda ake hankalin sa, yana kan Indo ya kasa ɗauke idanunsa a kanta, ita kuwa Indo duk abunda suke sam bata san suna yiba, zancen su kawai suke da zarah suna dariya, jin an sanja salon kiɗa, mai sautin waƙar da Hamisu bireka yayi wai taken son dangin mutuwa, da sauri Indo ta ɗago kanta tana duban inda sautin ke fitowa domin kuwa tana mungun son waƙar, ai kuwa tashi Indo Tayi ta shiga tsakiyar taron ta ɓalle da rawa sosai Indo take rawar jin salon waƙar yana tsumata, komai na jikinta juyawa yake, ga shi Allah ya azurta Indo da hips, aikuwa mazan dake wajen kamar wanda suke jira suka rufu kanta suna sake mata kari, dam dam! Zuciyar Mustafa take harbawa wani irin ɗaci yake ji cikin Ransa ganin yanda wasu ƙatti suka rufu kanta suke mata kari, Habeeb kuwa wani irin zafi shima yaji cikin zuciyarsa tare da mungun jin haushin Indo na Wannan rawar da take wasu ƙattin banza su ruhu kanta, yunƙura Habeeb yayi da niyar zuwa ya janye Indo daga wajen, amma ina kafin ya tashi tuni Mustafa ya rigasu, ita kuwa ko a jikinta idanunta sun rufe rawa kawai take, taji an danƙi hanunta da ƙarfi, da sauri ta tsaya da rawar tana duban Mustafa idanunsa sunyi jawur gwanin ban tsoro, kowa dake wajen shuru yayi yana ƙare musu kallo, ganin yanda fuskar ango ta sauya lokaci ɗaya, itama RAUDA kallon ikon Allah take, da ƙarfi ya fisge ta, yayi waje da ita tana tirjewa amma ina sanda ya fita da ita, saurin tashi Habeeb yayi zaibi Bayan su Hasina tayi saurin riƙe hanunsa tana girgiza masa kai ƙwace hanunsa Habeeb yayi yabi bayan su cikin sauri....


Wayyo Allah fan's ku fa yi hkr dani na rashin samun typing akai-akai ina da uzuri da yawa, kunsan bana typing asabar amma wlh yau haka na dage na muku, saboda na kwana biyu banyi typing ba, kuyi hkr da typing error ban samu nayi editing ba typing ɗin sauri nayi🙏🏻.

*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*


*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*


*(Ummu Nasmah ce)*[3/10, 3:04 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*



👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻


*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*


*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.


*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻


Gaskiya fan's I love you Lodi-Lodi da alamun dai page ɗin jiya ya muku sweet yanda naga kuna ɓarin ruwan sharhi daga ko wani groups gaskiya kun matuƙar burgeni😘


*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*P*••••••6️⃣7️⃣ ➡️ 6️⃣8️⃣

Mota Mustafa ya buɗe tare da wurga Indo ciki ya rufe ƙofar da ƙarfi kafin ya zaga ya buɗe gaba ya shiga, ya tada motar da ƙarfin gaske cikin tashin hankali Indo ke kallon Mustafa tunda taga Mustafa yana mata wannan jan cikin haɗa rai to tabbas yau baƙar muguntar sa kanta ya sauƙa, cikin ranta take cewa ( yau kuma kaina zai sauƙe hashin Auren dolen da Momy ta masa, wayyo Allah na mungu zaici zalina ) shiko jan motar kawai yake baya ko kallon gaban sa yanda ransa yakai matuƙa wajen ɓaci, Habeeb daya fito da sauri ne, yaga Mustafa ya ja motar harya fice daga cikin hole ɗin, kama kansa Habeeb yayi tare da jan dogon tsaki, tunani ya fara na yabisu ne kokuwa ya dakata har a gama dener, wata zuciya ce tace masa (karka bita ka tsaya wajen dener karkuyi abun kunya babu kai babu Mustafa, Idan kunyi haka duniya zata zage ku) komawa ciki Habeeb yayi amma duk hankalin sa ya tafi garesu.

Cikin hole ɗin kuwa RAUDA sai raba Ido take taga ta inda Mustafa zai iso shuru-shuru babu Mustafa sai ma ganin Habeeb da tayi ya shigo hole ɗin, shi kaɗai, ga baki ɗaya hole ɗin ya birkice da kananun magana kowa yana tofa albarkacin bakinsa akan Mustafa da Indo wasu suce sonta yake wasu kuma suce babu wata soyayya kawai ƙanwar sa ne, shiyasa baiji daɗin rawar da tayi ba, wasu kuma suce Masha Allah yarinyar ta burgeni wlh dubi yanda take rawar nan fa kamar na sace ta na gudu wannan zata dace da zama jarumar Film, shima Barrister Umar hankalin sa ya tashi ganin kamar alamar Mustafa kishin Indo yake, kasa zama yayi cikin hole ɗin ya zille ya gudu gida cikin matsanancin ƙaunar Indo, duban Habeeb da ransa ke ɓace RAUDA tayi tace.

" Ya Habeeb ina ya Mustafa yake? Ta tambaye sa cikin sanyin jiki Zuciyarta sam babu daɗi.


Habeeb ma da ransa ke ɓace a taƙaice yace mata.

" Ya koma gida."

Dam ƙirjin RAUDA ya buga, Hasina kuwa zaro ido tayi waje kusan tare suka ce.

" Ya Habeeb gida kuma yanzu? Bayan ba'a gama dener ba."

Cikin gajiya da tambayan tasu gashi kuma ransa yana ɓace a hasale yace.

" Ehh! Abunda kuka ji nace dan Allah ku ƙyale ni."


Cikowa idanun RAUDA yayi da hawaye sai yanzu ta fara gaskata Maganar Mustafa wato da gaske yake wulaƙanta rayuwar ta zaiyi, tabbas ko yanzu ya wulaƙanta ta, tunda har ya iya tafiyar sa gida tun kafin a tashi daga dener ya wulaƙanta ta a gaban ƙawayenta da ƴan uwan ta, da ta gayyata wajen, me zata ce musu indan sun tambaye ta, ina Mustafa ya tafi, ita har ga Allah bata kawo komai tsakanin Indo da Mustafa ba, domin tasan babu shiri a tsakanin su bare tace yabi mace, dafe kanta tayi tana ambaton Allah cikin ranta dake mata ƙuna tana hangen wacce irin rayuwar aure za suyi da shi, a fili tace "Allah ka kawo min ɗauki cikin lamari na" kafin ta tashi tana layi zata fice daga hole ɗin, tashin da tayi shine ya fara jawo hankalin mutanen dake hole ɗin, lura da hakan da Habeeb yayi ne, yasa shi saurin tashi ya tare ta yana cewa koma ki Zauna.

Zama tayi tana kallon Habeeb idanunta na ƙoƙarin zubar da hawaye, taji Muryar Habeeb ƙasa-ƙasa yanda babu mai jinsa sai ita yana cewa.

" Kiyi hkr ki zauna a ƙarasa dener nan pls kar muyi abun kunya cikin hole ɗin nan kina son muji kunya ne, na rantse da Allah da nasan Mustafa zai mana wannan abun kunyar Wlh da banyi tunanin fara wannan dener ba, nima kaina daure zuciyata nake domin ji nake kamar zata faso ƙirji na, pls sorry ki zauna har a gama denern nan."

Cikin rawar murya RAUDA tace.

" Abun kunya kam ai an riga da an yisa idan na Zauna ina zan cewa mutane miji na yaje, ko yanzu ya nunawa duniya cewa bana gabansa babu amfani zama na a wajen nan ka barni na tafi kawai babu wani abun kunya daya saura wanda baiyi shiba."

" Ki zauna nace babu ruwanki da Abunda mutane zasu ce, ni nasan Abunda zan faɗa musu."

" Amma ya Habeeb........"

Ɗaga mata hanu Habeeb yayi yace.

" Please ya isa haka maganar na baki Hkr idan idan kuma bazaki iya zama ba, ga hanya jeki sai ku bawa duniyar ƙofar zagin namu da tushe."

Komawa RAUDA tayi ta zauna tana jin wani baƙin ciki cikin zuciyarta tare da danasanin zuwa wannan dener, Habeeb kuwa zuwa yayi ya karɓi speaker ya sanar cewa, Mustafa bazai samu dawowa ba a masa afuwa sakamakon kanshi dake ciwo, haka kawai ya faɗa yayi shuru tare da komawa ya zauna, yawanci babu wanda ya yarda da maganar Habeeb tunda a idanunsu mustafa ya fice da Indo, haka denern ya kasance wani iri, sanda aka kira ango da amarya Habeeb umurtar RAUDA yayi da ta fito, tare ya watsa musu kari duk abinda zai yiwa Hasina ya yiwa RAUDA duk dan ya rage mata damuwa hakanne kuwa ya ragewa RAUDA raɗaɗin Mustafa cikin ranta, sosai Sharifa ma ta zuba musu kuɗi ranta babu daɗi akan Abunda yayan nata Mustafa Yayi, shi kuwa da yake can gida Zaune Barrister Umar Indo ta tafi da zuciyarsa, ya kuma sawa ransa cewa saiya nemo Soyayyar ta, haka aka tashi denern badan yayi daɗi ba.

Hon! Hon! Hon! Hon! Mustafa yake ta dannawa, a ƙofar Estate ɗin nasu, da sauri mai gadi ya buɗe masa, danno hancin motar yayi, ba tare daya dai-dai ta parking ba, ya tsaya ya fito tare buɗe gidan gaba, ya finciko Indo da ƙarfi, yana jan hanunta binsa kawai Indo take kamar raƙumi da akala domin tasan yau ta shiga uku hanun Mustafa, duk da babu abunda ta masa tana ganin zaluncin sa ne kawai ya juyo kanta, babu kowa cikin falon duk sunyi bacci wasu kuma suna can wajen dener kasancewar dare yayi kusan 12pm ɗakin sa Mustafa Yayi da ita tare da wurgi da ita tsakiyar ɗakin faɗuwa Indo tayi tare da bige kanta jikin mirror, riƙe kanta tayi tare da bin Mustafa da kallon tsana, komawa yayi ya sawa ɗakin key sannan ya dawo wajen dressing mirrom su ya buɗe kuɗi ne masu shegen yawa ya ɗebo tare da watsawa Indo a jiki yana cewa.

" Gasu nan domin ina da tabbacin sune suka shigar dake filin rawar, to gasu basai kin saida jikinki ba kafin ki samu, wai kema kin girma ko kinga kin fara ajiye nono da hips shine bari ki fara neman kuɗi da jikin ki, bari ki fara tallen su shine za'a san kin girma, shidai ɗan ƙauye har abada baya taɓa hankali" ya ƙarasa maganar yana take mata yatsun kafar ta tare da mitsikkesu a tayels, wani irin ƙarar Azaba Indo tasa tana ƙarewa kuɗin kallo tare da mummunan tsanar da tayiwa mai su cikin sakewar zuciya take cewa.


" Allah ya sauwaƙa na saida jiki na don kuɗi, wlh nafi ƙarfin haka domin ni kuɗi basa gaba na tunda babu abunda aka rageni da shi ana biya min dukkan buƙatu na, da kake cewa ƴan ƙauye basu da hankali, ai bani kaɗai bace Yar ƙauyen cikin gidan ashe sauran ma kenan basu da hankali Kuma wlh Allah ya isa ban..........."

Bata ƙarasa ba Mustafa ya shaƙo wuyan ta ya haɗa ta da gini ya matseta wanda har tana iya jiyo sautin numfashinsa yanda jikin su ya haɗu cikin ɗaga murya yake cewa.

" Faɗa min waye sauran ƴan ƙauyen faɗi nace kafin na illata ki cikin gidan nan, wato Daddy ya baki kinci kin ƙoshi ai dole ki fara zagin sa." Yana murɗe bakinta da ƙarfi.

Cikin azaba Indo ta fisge hanunta daga bakin ta tana masa wani mungun kallo tama kasa tanka masa domin kuwa yanzu ya kawota wuya, tasan tana buɗe bakinta zata iya zagin Mustafa gara kawai tayi shuru ta barsa da Allah, Momy da tazo wucewa ne taji kamar magana ta cikin ɗakin su Mustafa yasa ta zuwa wajen ta tura ƙofar cikin Sa'a kuwa ta buɗu ashe sanda Mustafa yasa key ɗin ya manta bai murɗa ba, sake baki Momy tayi yanda taga Mustafa maƙale jikin Indo sun manne a bango cikin tsawa tace.

" Sannun ku munafukai nace sannun ku"

Saurin juyowa sukayi dukan su suna kallon Momy yayin da Mustafa Yayi saurin komawa gefe, yana sosa kansa cikin mamakin yanda Momy ta shigo ɗakin bayan yasa key, Indo kuwa ta kasa magana sai ma sunkuyar da kanta ƙasa da tayi, matsowa Momy tayi kusa dasu tare da ɗaga hanu ta wankawa Indo mari tana nunata da yatsa bakinta har ɓari yake take cewa.

" Daman ai biri yayi kama da mutum shegiya munafuka jarababbiya, ai wannan uban nono da kika tara a ƙirjinki lokaci ɗaya da alamar tambaya da waɗannan shegun masaka-masakan ɗuwawu da kika haɗa, ashe maza ake bi, wato duk na wajen basu isheki ba, har sai kinzo zaki lalata min ɗa ko baƙar munafuka."

Wannan ne karo na farko da Indo taji ta fara tsanar Momy wani irin baƙin ciki tare munguwar tsanar Mustafa take ji cikin ranta domin kuwa koma me Momy zata gaya mata shine ya jawo mata, wasu hawaye ne masa zafin gaske suke tsere saman fuskar Indo, Inna ce kawai ta faɗo cikin ranta domin kuwa tasan da tana nan babu mai ci mata mutunci, shima kansa Mustafa yaji mungun haushin maganganun Momy mussaman ma da take kiran cewa Indo tana bin maza ya tabbata da kowa zaiyi shaidar cewa Indo tana bin maza, shi kuwa zai iya tsayawa a ko ina ya ƙaryata wannan zargin domin yasan wacece Indo tun tana cikin zanin goyon ta, duk halin sai dai masifa da neman magana da kuma rashin jin magana, amma Banda dai neman maza kam tabbas wannan ba halinta bane, domin kuwa bata kula wasu maza ma bare kuma harta bisu da lalata, muryar Momy itace ta katsewa Mustafa tunanin sa ta hanyar cewa.

" Kai kuma shashashan banza mace tazo ta sakaka gaba ka fara biye mata za kuyi shashashan ci, to dan ubanka daga yau na raba ka da ita, kallon Indo Tayi tace, fice kibar ɗakin nan wacce ta kasa samun tarbiyya wajen iyayen ta."

Da gudu Indo ta fice tana kuka mai tsuma Zuciya ta faɗa ɗakin su, shi kuwa Mustafa sai yanzu ya dubi Momy yace.

" Momy meyasa kikayi haka, Abunda kike tunani ba haka bane, Indo bata da laifi bata kuma neman mazan banza Momy laifi tamin nake..........."

Cikin tsawa Momy tace.

" Rufe min baki dan ubanka munafiki kaima, Uban meya dawo da kai daga wajen dener bayan su suna can babu wanda ya dawo idan ba jawo ka tayi kuzo ku tambaɗe ba, kai kuma gaka na mamajo shine ka biyota simi-simi kuka taho, kasan Allah ka fita harkar yarinyar nan kafin raina ya ɓaci da kai ka riƙe wannan yarinyar RAUDA itace matar ƙwarai ka fita harkar wannan ƙaramar karuwar."

Runtse idonsa Mustafa Yayi yana jin Zafin maganganun Momy ya rantse da Allah da wani ne yau yake munanan waɗannan munanan maganganun akan indo wlh Allah ne kawai zai rabasa dashi, sai dai babu yanda ya iya da Momy, gefen ta yabi ya fice ba tare da yace komai ba, domin bazai iya tsayuwa yana sauraron maganganun Momy ba.

Fita itama Momy tayi tana mita, sosai Indo take kuka bata taɓa zaton tsanar da Momy ta mata yakai haka ba, wanda har zata mata ƙazafin zina Abunda bata taɓa kusanta ba, harsu Hasina suka dawo Indo tana cin kuka, zama Zarah tayi kusa da ita cikin tashin hankali tana tambayan Indo me mustafa ya mata amma Indo ta ƙi musu magana harta su Hasina sunyi sunyi Indo taƙi magana ga mutane cike cikin ɗakin ganin Indo bata da niyar shuru yasa Hasina kiran Habeeb a waya ta sanar dashi daman kuwa shima ya kasa zaune ya kasa tsaye na rashin sanin wani hali Indo take ciki, domin kuwa yasan mawuyacin abune su wanye lafiya da Mustafa tunda daman kanwarsu ba jiƙa take ba, cikin sauri ya ƙarasa cikin ɗakin daman ita RAUDA nata damuwar ya isheta tana gefe ko kallon Indo batayi ba, Habeeb duk yanda yaso Indo Tayi magana taƙi dole yasa ya ƙyaleta ya fita cikin tashin hankali, Habeeb ranar kasa runtsawa yayi yana tunanin halin da Indo take ciki sai yanzu ya fara fuskantar cewa son Indo yake, saurin dafe ƙirjin sa yayi yana cewa.

" Na shiga uku zuciyata baki min adalci da zaki kamo da Soyayyar Wanda nakewa kallon ƙanwar da muka fito ciki ɗaya wacce matata ta ɗauke ta ƴar uwa, Allah ka taimake ni karka ɗaura min abunda bazan iya ba, karka ɗaura min abunda zai zamo damuwa a gareni" haka Habeeb ya kwanta ba tare daya kalli Mustafa dake gefen sa ba domin kuwa yana jin mungun haushin sa.


Da gudu ta faɗo jikinsa tare da raɗa masa cikin sanyayyiyar Muryar ta mai daɗin sauraro cewa.

" Sweet heart yau nayi let ɗin shigowa ɗakin nan ko, sorry na tsaya rarrashin Amra be, har tayi bacci kafin nazo ga Daddyn ta" tura sa tayi suka faɗa saman bed ɗin haɗe bakinsu tayi waje ɗaya tana masa wani irin hot kiss hanunta kuwa yana

Please Login or Register in order to submit comment