Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya fice.

A Mota ya samu Mustafa yake sanar dashi sakon nasu murmurshi Mustafa yayi yana ganin RAUDA tama raina masa Hankali, ai yasan da falon nasu yace tazo ta samesa a nan, kuɗi ya ciro ya miƙawa Baba mai gadi yace.

" Gashi Baba dan Allah kayi hkr ka miƙa mata wannan kace gashi inji Momy kuɗin data aiko tana bukata na hidimar biki, sannan kace mata banyi niyar shigowa ba ba kuma zan shigo ba."

Shidai Baba ɗan aike ne karɓa yayi ya tafi kaiwa, shi kuma Mustafa jan motarsa yayi ya fice daga cikin gidan, bayan Baba mai gadi ya isar da saƙon Mustafa ne Momy ta tashi cikin hasala tana cewa.

" Tirƙashi lallai wannan yaron ya raina mu, ta dubi RAUDA tace gashi dai dan ubanki da kike tausayin sa ya fara shuka miki tsiya tun kafin ki shiga cikin gidan sa, kuma dan ubanki dole ne kibi umurni na, domin ganin na kwato miki ƴancin ki."



To fa fan's sai ku shirya zuwa biki, dan nasan akwai ƴan hana biki maraici musamman iklas ƙamshi da sis munaya da maryam, Hafsat ma dai ba'a barta a baya ba😄


*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*


*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*


*(Ummu Nasmah ce)*
[3/5, 9:33 AM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*



👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻


*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*


*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.


*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻


*WANNAN PAGE ƊIN SADAUKARWA NE A GARE KA AUNTY MU'AZ KYAUTA NA BAKA IDAN KANA SO SAI KA TAIMAKA WA KULSUM ƊINKA TA KARANTA KODA KAƊAN IDAN KASO KA HANATA NIDAI INA BAYA INA SHAN KALLO, UMMA MUHAMMAD NAJAMANGA HAJIYAR AUNTY MU'AZ*😆😆


*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*P*••••••6️⃣3️⃣ ➡️ 6️⃣4️⃣

Ajiyar Zuciya RAUDA ta sauƙe tana kallon Mamy cikin damuwa kafin tace.

" Shike nan Mamy duk abunda kika ce dai-dai ne ni wannan magani da kika damu dashi banga amfanin sa ba amma........"

Dakatar da ita Mamy tayi tana cewa.

" Amma meye marar zuciya, wa'azi zaki minne uwata, shige kibar wajen nan na daina ganin ki a gabana dan ubanki."

Shigewa ɗaki RAUDA tayi ta zauna bakin bed ɗin ta, tare da haɗa tagumi tana tausayin kanta na son mutumin da baya sonta, bata kuma ganin laifin kowa sai na Zuciyarta da ta tilasta mata son Mustafa, goge hawayen idanunta tayi a fili tace.

" Kiyi hkr Mamy koda kin bani maganin nan bazan iya amfani dashi ba, baida wani fa'ida sai ma biyu babu da mutam zaiyi, dan haka bazan yi wannan kuskuren ba Mamy kema Allah ya ganar dake, da na yiwa Mustafa Asiri na gwammaci naje nata zaman Hkr da wahala a gidan Mustafa, Allah ya sa ya soni wata rana ni shine fata na" ta ƙarasa maganar tana goge hawayen nata kafin ta kwanta tana tunanin duniya.

A falo kuwa mamy ne ta dannawa Yana kira tana ɗagawa Mamy ta fara cewa.

" Aunty Yana karfa ki manta da saƙona na maganin nan wajen Malam Alamguburo, kinsan dole sai munyi maganin yaron nan naga alama baida mutunci, dan namiji zuma ne saida wuta, kice masa karya manta harda na mahaifiyar yaron dan gara mu ƙara riƙeta sosai karta kawo mana matsala gaba." Shuru Mamy tayi sai can naji tace "to shikenan Aunty Yana sai kin zoki Allah ya kawo ki lafiya" kafin ta kashe wayar tana ƙwafa tana zagin Mustafa.

Washe baki Indo da take tsaye ita da Zarah tayi sakamakon hango motar ya Habeeb da tayi, da sauri ta ƙarasa tana cewa Zarah "sai mun haɗu gobe ki gaishe min da momma"

"Zataji" Zarah tace tana dariya kafin ta gaishe da Sharifa da Habeeb cikin fara'a kuwa Habeeb ya amsa kafin Indo ta faɗa cikin motar tana dariya, Habeeb yaja suka tafi.

" Aunty Sharifa gidan Ummi zaki kema kenan?"

Murmurshi Sharifa tayi tace.

" Eh mana kun gudu kun barni ba dole na biyo ku ba, gidan ya min shuru babu daɗi."

Habeeb ne yace.

" Ai kurame ne mu Dole gidan ya miki shuru, aiko da nasan Abunda yasa kika baro gida kenan da bansa Momy ta barki kin fito ba." Ya ƙarasa maganar yana murɗe mata kunne.

Dariya Sharifa tayi tana ƙwace kunnen ta daga hannun Habeeb tace

" Ya Habeeb ai fast is fast present continue, yanzu kam, tunda harna fito magana ta ƙare."

Dariya Indo tayi tace.

" Ya Habeeb, an fara biyan kuɗin neco kasan mun kusa gamawa, Daddy kuɗin waec kawai ya biya min kuma duka ƙawaye na biyu suka biya neco And waec."

Murmurshi Habeeb yayi tare da cewa.

" Oh sweet ƙanwata kice mun kusa girma zamu gama Secondary School, eyye babyn na ta girma to karki damu gobe in Allah ya kaimu zan shigo makarantar naku na biya miki ina ga dai idan ban manta ba 25k suke biya ko?"

" Eh ya Habeeb haka ne 25k ne."

" Okey to zan shigo gobe in Allah ya kaimu dole sweetie na tayi duka biyu Itama, har jam ma zan biya miki insha Allah."

Dariya Indo tayi cikin farin ciki, sai kuma Malam sani ya faɗo mata cikin ranta yanda yake rarrashin ta kullum tayi karatu da tsafta, duban Sharifa tayi tace.

" Aunty Sharifa akwai uncle ɗinmu na ƙauye Mlm Sani ina alfahari dashi sosai, ko yaushe shine yake sani a hanya cikin rarrashi har minti da doya yake saya min dan nayi karatu da tsafta, kamar dai yanda ya Habeeb yake min, bazan manta da alkairinsa gare ni ba, Aunty kullum naga ya Habeeb sai na tuno dashi ko yana koyarwa har yanzu sai Allah."

Murmurshi Sharifa tayi tace.

" Allah sarki daman haka wasu Mlm suke suna da kirki wasu kuma mugaye, Allah ya saka masa da Alkairi, ni kuwa duk sanda zaki ƙauye sai na baki ƙyauta kin kai masa."

Dariya Habeeb yayi tare da cewa.

" Ai kuwa nima zan kawo tawa gudumowar insha Allah."

Dariya sosai Indo tayi cikin murna da farin ciki, haka suka ƙarasa suna raha, a ƙofar gidan Habeeb ya sauƙe su yace shi bazai shiga ba, yana sauri sai dare zai shigo, shigewa sukayi cikin gidan Indo na ɗagawa Habeeb hanu.

Murmurshi Habeeb yayi tare da jan motar sa har ga Allah duk sanda ya saka Indo cikin idanunsa yakan ji wani sanyi cikin ransa, yana samun nutsuwa sosai a duk sanda yake tare da ita koda kuwa yana cikin damuwa ne sai yaji duk wannan damuwar ta kau sakamakon gani Indo kusa dashi, Muryar ta kuwa jinta yake kamar sarewa amma duk da haka Zuciyarsa bata yadda son Indo yake ba, cikin shauƙi da Happy Habeeb ya nufi inda zaije.


Shiko Sarkin baƙin hali, H/court ɗinsu ya ƙarasa darect, office ɗin sa ya nufa, Barrister Umar ya tarar Zaune yana duba wasu files dariya Mustafa yayi ya zauna yana cewa.

" Mutanen sama kuma yaushe aka fito, yau harka rigani shigowa kenan?"

Dariya Barrister Umar yayi yana cewa.

" Ai yanzu dole na rigaka shigowa ango, tunda kasa Auren nan a gaba naga alamar ka fara let."

Murmurshi Mustafa yayi ba tare daya ɗago ba yace.

" Kuna bani mamaki wlh kaida Habeeb, ni wannan auren da kuke kiran sa da suna Aure, ni fah bai dameni ba dashi da babu duka ɗaya ne a wajena, so ni har mantawa nake da Auren, kasan kuwa sunan dana sawa wannan auren?"

Girgiza kansa Barrister Umar yayi yana duban Mustafa yace "a'a"

Murmurshin gefen baki Mustafa yayi tare da cewa.

" *Auren tushe Auren ko oho* domin kuwa bana buƙatar matar da ake ƙoƙarin liƙa min, kallon ta nake tamkar maciji kububuwa wlh babu Soyayyar RAUDA ko kaɗan cikin Raina " ya ƙarasa maganar yana ɗago kansa ya dubi Barrister Umar.

Barrister Umar kuwa cikin mamakin irin ƙiyayyar da Mustafa yake gwadawa RAUDA yake kallon sa kafin yace.

" Ni ko Mustafa menene Aibun RAUDA da baka sonta haka, naga duk abunda miji yake nema ga matar sa RAUDA ta haɗa su, so meyasa kake ƙinta? Tana da ƙyau diri zati, tana da ilimin addini tare da na zamani, tana da tarbiyya Uwa Uba ta iya girki, to ka faɗa min menene Aibun ta?"

Murmurshi Mustafa yayi shima yana duban Barrister Umar yace.

" Barrister Umar ai ita soyayya babu ruwan ta da ilimi ko kyau ko wani nasaba, idan kana son Mutum ko yaya yake bazaka gani ba komai kuwa munin halinsa, haka kuma ƙiyayya idan baka son mutum duk qualities ɗin sa shima bazaka gani ba, so kaga kenan amsar tambayar da kamin ta fito anan, mu buɗe wani shafin wannan kam mu ajiye sa a gefe domin naga alamar baka son Gaskiya."

Taɓe bakin sa Barrister Umar yayi ba tare daya cewa Mustafa komai ba akan maganar yace.

" Okey ga files ɗinnan na Case ɗin Sadiya Ibrahim ne, na gama haɗa duk wasu information yana ciki amma SADIQ yace na sanar dakai cewa an ɗaga shara'ar sai ranar 5 ga watan 5."

Karɓar files ɗin Mustafa yayi yana cewa

"sun ƙara wata ɗaya kenan nan gaba? Hakan ma yayi zamu ƙara samun enough time na bincike, bari na duba su idan ina neman wasu information ɗin zan maka magana."


" To" Barrister Umar yace yana ƙoƙarin tashi tare da cewa.

" Bari na koma nawa office ɗin akwai ayyukan daya kamata nayi."

"A fito lfy" Mustafa yace Kafin Barrister Umar ya tafi.

HASINA sosai taji daɗin zuwan Sharifa, haka Aunty Hindu, ranar tare suka fita kasuwa har Indo, Dake Hasina bata da wata ƙawa cikin Nigeria, Sharifa ta ɗauka matsayin ƙawa duk da cewa ta girme ta.

Habeeb kuwa bai karya alƙawarin Indo ba washe gari yaje ya biya mata kuɗin neco da jam.

Biki yanzu sai kankama yake yayin da ko wani ɓangare biyun suke gyara ƴaƴan su, Aunty Hindu kuwa da kayan fruit da kuma na gargajiya take yiwa Hasina nata maganin matan dan kuwa sosai take bawa Hasina fruit wani ta haɗa tayi blanding ɗinsa wani kuma ta bata shi haka taci zuma kuwa sosai take bawa Hasina take amfani dashi, sosai Aunty Hindu ta gyara Hasina ciki da waje, wani shegen kyau Hasina tayi domin kuwa tunda aka fara mata gyaran jiki Aunty Hindu ta hana koda Habeeb yaga Hasina, Aunty Hindu cewa mai gyaran jikin tayi, itama Indo a mata gyaran jiki, haka kuwa akayi matar tare ta dirje musu jiki, su kuwa Mamy maganin mata ta dinga ɗirkawa RAUDA, amma gyaran jiki kam babu laifi ta gyaru sosai domin kuwa kunsan gyaran barebarin Barno, ba daga baya ba.

Duk hidimar bikin Mustafa babu ruwan sa ciki Habeeb ne yake shi ɗaya, dan shi Mustafa rabonsa da yaga RAUDA ma harya manta, bare kuma ya wani damu da hidimar Auren ta, a cewar sa fa kenan.


Yau dai biki saura kwana Uku, sosai gidan Momy ya cika da ƴan Uwa da abokan arziki hatta ƴan uwan su Daddy dake garin Dasina sunzo mama kuwa bata samu damar zuwa ba wannan karon, Indo da taji labarin zuwan ƴan Dasina taso zuwa gidan Momy tagansu Aunty Hindu ta hana tace ta bari sai gobe suma zasu zo su wajenta, Aunty Salima ƙanwar Momy da Hajiya Addiyo yar Momy, suna zaune a ɗakin Momy, Aunty Salima take tambayan Momy cewa.

" Nikam Hajiya a'isha wani holl aka kama ne na dener, kinsan fa dole zani."

Murmurshi Momy tayi tace,

" Ni dai gaskiya bani da masaniyar inda zasuyi, amma bari su shigo kya tambaye su."

Ai kuwa haka akayi Mustafa yana shigowa Aunty Salima ta tambaye sa, taɓe bakin sa Mustafa yayi cikin halin ko inkula yace.

" Ban sani ba amma ki tambayi Habeeb ya sani shi tunda shine uban ƴan rawar kai na bikin, ya faɗa min inda za'ayi amma gaskiya na manta" Kuma sarai Mustafa yasan inda za'ayi kawai ya tsani yaji ana masa maganar auren nan domin yaga Aunty Salima kamar neman magana take.

Sake baki Aunty Salima tayi tana kallon Mustafa cikin mamakin Angon da baisan inda za'ayi denern sa ba, taɓe baki itama Aunty Salima tayi tace.

" Allah ya yaye maka wannan shegen halin naka da wannan miskilancin naka idan ma ka sani kaƙi faɗa minne kaika sani zan kira Habeeb ɗin ai zai gaya min" ta ƙarasa magana tana ranƙwashin kan Mustafa ta wuce tana kiran Habeeb a waya.

Murmurshi Mustafa yayi yana cije bakin sa ya shige ɗakin su sakamakon jin mararsa ta fara ƙullewa, drower ya buɗe ya ɗauki tablet ɗinsa yasha, saurin faɗawa saman bed yayi domin kuwa yasan ciwon nasa ne yake neman tashi masa lumshe idanunsa yayi yana jin wani irin felling.

Zama Indo tayi tana duban Hasina tace.


" Dan Allah Aunty Hasina ki ƙira min Zarah na sanar da ita maganar Auren nan nima dai ya Habeeb yace ina gama Secondary zai saya min wayar nan na huta da aron taku."

Dariya Hasina tana cewa.

" To ƴar gidan Habeeb ta hanun daman sa, jeki ɗauko wayar tawa saman wadrop ki kira ta"

Tashi Indo tayi tana dariya tace.

" Faɗi kanki tsaye Aunty Hasina nice nan ta hanun daman ya Habeeb ɗina" ɗaukar wayar taki ta dannawa Zarah kira kasancewar ita zarah tana da waya.

Can gidan su RAUDA kuwa sosai Mamy take ɓarin kuɗi na auren ƴarta ta, ta shirya family friend da za'ayi gobe misalin ƙarfe goma na safe, za'ayi kamu Kuma da yamma ƙarfe huɗu, ita dai Hasina tace ba zatayi wani bidi'a ba, ko dener ma da zatayi Habeeb ne yasa dole sai tayi da dan ita ne wlh bazata yi ba, walima kawai ita tasa a ranta za tayi.

Da sauri Mamy ta shiga kitchen ta buɗe wani coler da yake ɗauƙe da naman kaza sai ɗayan kuma tuwon semo ne lafiyayye Mamy ta barbaɗa wani magani mai kamar gishiri a saman miyar, Gambo ta ƙwalawa kira ƙawar sheɗancin nata, da sauri Gambo ta shigo tana cewa

" ya akayi kin gama komai?"

Ajiyar Zuciya Mamy tayi tace.


" Na gama gashi kije cikin gidan ki tabbatar da cewa Hajiya a'isha taci Abincin nan, Bayan ita karki bari wani yaci ki tabbatar ita kaɗai taci ƙawata, kinsan dole ne mu riƙe Hajiya A'isha a Hanun mu sai yanda mukayi da ita, kafin mu dawo kan shegen ɗannata mai taurin kan tsiya."

Dariya Gambo tayi kafin tace.

" Ai karki damu Hajiya Turai kinsan ni kin san halina, dole nayi aiki bisa ƙa'ida."


Kuyi hkr da typing error idan kun samu wlh ban samu nayi editing ba yau🙏🏻

Ku sani cikin Addu'ar ku ina da abu mai mahimmanci da zan aiwatar Allah ya bani Sa'a yasa nayi cikin nasara🙏🏻



*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*


*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*


*(Ummu Nasmah ce)*
[3/7, 4:41 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*



👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻


*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*


*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.


*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*P* 6️⃣5️⃣ ➡️ 6️⃣6️⃣

Gambo har ɗakin Momy ta shiga, suna cike cikin ɗakin Momy da ƴan uwanta, bayan sun gaggaisa ne, Gambo ta dubi Momy tace.

" Hajiya A'isha, aiko ni fa Hajiya Turai tayi wajen ki, ina son mu ɗan fita daga waje."

Murmurshi Momy tayi tare da tashi tana cewa.

" Okey muje babu matsala."

Aunty Salima ne tayi carap tacewa Gambo.


" Menene cikin kulan kike riƙe da ita gam, idan abun daɗi ne ai sai ki bamu mu sawa bakin salatin mu," tana maganar tana ƙoƙarin jawo kular daga hannun Gambo.

Ƙara damƙe kular Gambo tayi tana cewa.


" Babu komai fa ciki na biya gidan ƴar uwata ne na karɓo ta tafi da abinci bata dawo da ita ba, shine yau nabi na karɓo"

Maida hanunta Aunty Salima tayi tana cewa.

" Okey ai nayi zaton abun daɗi ne ciki"

Fitowa falo sukayi Momy ta dubi Gambo tace.

" Lafiya kuwa Turai ta aiko ki yanzu cikin wannan hatsaniyar bikin?"

Murmurshi Gambo tayi cikin salon munafurci da yaudara tace.

" Lafiya lau wlh Hajiya, daman abinci ne ta girka muku tace tasan yanzu haka kina can baki samu kinci abinci ba, shine tace dan Allah na taimaka mata na kawo miki abincin nan na tabbatar kinci kafin na tafi."

Murmurshi Momy tayi tana tace.

" Allah sarki ai kuma kamar tasan banci abincin ba, ai da wannan maganar ne dama baki taso ni ba, sai muyita can to na gode kawo na shiga dashi ciki, na ci acan"


Ai kuwa Gambo ƙin bawa Momy tayi ta shiga da kwanon ciki, sai ta wayan ce da cewa.

" Ai kuwa Hajiya bazan baki abincin nan ki shiga dashi ba zaki iya mantawa dashi, ko kuwa a cinye gashi abincin baida yawa, ita kuma danke kawai tayi, gashi ta bani amanar cewa na tabbatar kinci kinga kuwa ai dole na cika amana."

Ita kuwa Momy Zuciyarta ɗaya tayi dariya tana Cewa.

" Oh ikon Allah Hajiya Turai sai kace wata yarinya ta ɗauke ni, to shikenan bani naci kya sauƙe amanar taki" Momy ta faɗa tana zama.

Ai kuwa cikin farin ciki Gambo ta miƙawa Momy kular tana zama itama, Momy na cin abincin Gambo na mata taɗi harta cinye abincin duka, ta dubi Gambo tace.

" Shikenan ina ki ce mata na gode daman kuwa yunwa nake ji"

Dariya sosai Gambo tayi tace.

" Insha Allah saƙonki zai isa da wuri yanzu ma kuwa."

Murmurshi Momy tayi tace.

" To na gode"

Tafiya Gambo tayi cikin happy tana dariya, Gambo bata juma da fita ba Momy ta yunƙura da niyar tashi sai taji wani irin jiri taji ya fara ɗibanta, kanta kuwa ji tayi kamar yana juya mata dole yasa Momy komawa ta zauna, tana dafe kanta, tafi 15minute a haka kafin taji komai ya lafa mata, sannan ta tashi ta shiga ciki.

Bacci sosai Mustafa yayi sakamakon tablet ɗin da yasha, ya tashi kenan ya shiga wanka yana fitowa Habeeb na shigowa cikin ɗakin ransa a haɗe cikin faɗa Habeeb ya fara magana.

" Abunda fa kake Mustafa baya dacewa Wlh, wani irin rashin imani ne wannan Mustafa, tunda aka fara maganar auren nan, sam baka saka bakin ka, ciki baka san komai kan wannan auren ba, hatta sabuwar riga kaƙi ɗinkawa a dalilin wannan auren, sai nine naje na kai a ɗinka mana, na gaya maka cewa a Ammar holl za'ayi dener nan kayi burus dani kamar baka jiba, ɗazu nake magana da RAUDA take sanar dani cewa rabon da ta ganka tun ranar da tabar gidan nan, tunda aka fara maganar auren nan baka je kun tattauna ba, wlh kaji tsoron Allah, kuma wlh dole kaje dener."

Mustafa share Habeeb yayi kamar baiji Abunda yake faɗa ba, ya cigaba da shafa mansa, ƙara tunzura Habeeb yayi wato ma Mustafa ya maida shi mahaukaci ko, da zaiƙi kulasa, gaban mirron Mustafa yaje tare da ƙwacen man dake hanun Mustafa yana cewa.

" Wai mahaukaci ka maida nine, ina faɗa maka gaskiya akan rashin kyautatawar ka kayi banza dani, Abunda kayiwa RAUDA ya dace kenan ka burus da yarinyar mutane, wlh kabar ganin yarinyar nan tana sonka shi yasa kake wulaƙanta ta, ka sani cewa ka sani cewa jarabawa ce Soyayyar ta a gareka, Kuma kaima bakafi ƙarfin Allah ya ɗaura maka wannan jarabawar ba, wlh mai Sonka yafi maƙiyinka ko yaya yake, ka gyara rayuwar ka, domin kuwa akwai kurakurai cikinta da yawa duk da nasan ɗabi'ar kane tun muna yara amma dai kayi ƙoƙarin gyarawa, shi ɗan adam ba abun wulaƙantawa bane"

Murmurshin gefen baki Mustafa yayi yana duban Habeeb kamar yau ya fara ganin sa kafin yace.


" Oh ƙarata ta kawo maka, to gani hukunta ni ubana, ita dan uwarta meye damuwar ta da rayuwata ne, idan ƙarata ta kawo sai ka hukunta ni, idan kuma saƙo ta baka kace mata injini ta tuno maganar da mukayi da ita a cikin makarantar su, ya isheta amsarta ya fito, banza nacecciyar Mace marar aji da kamun kai" Mustafa ya ƙarasa maganar yana tsuka.

Murmurshin takaici Habeeb yayi tare da cewa.

" Bazan hukunta kaba, duniya ce kayi duk abunda kaga dama, akwai ranar da zaka ɗebi adashen daka zuba cikinta shi Allah ai ba azzalumin bawa bane." Yana gama faɗin haka ya wuce tollet ba tare daya ƙara cewa komai ba, Mustafa bakinsa ya taɓe tare da ɗaga kafaɗar sa alamun wannan damuwar kane.

Yau juma'a, da misalin karfe tara na safe, RAUDA sukayi family And friends su Aunty Salima sunzo sosai ƴan uwan Momy sai dai basu gayyaci ƴan dasina ba wai acewar su ƙauyawa ne su, cikin tsari kuwa sukayi family friends ɗin RAUDA tayi kyau sosai, cikin doguwar riga, baka su Indo basu ko leƙo wajen family And friends ɗinsu ba, da yamma akayi ma akayi kamu, washe gari kuma sukayi walima har da Hasina waje ɗaya sukayi, sosai amaren sunyi kyau, Halima wacce suka zo daga Dasina sanda ta hango Indo bata gane ta ba, domin kuwa tayi kyau sosai harta gaji, gashi tasha ƙunshi baƙi da ja hanu da ƙafa, tasa wani blue ɗin doguwar riga an mata rolling ɗin ɗankwalin rigar a kanta, tasha makeup kuwa, sosai tayi kyau, suna gefe tare da Zarah suna taɗi harda dariya, har aka watse a wajen walimar Indo Allah baisa taga Halima ba.

Washegari da safe asabar tun ƙarfe tara Habeeb yake ta ƙoƙarin shiryawa zuwa wajen taron ɗaurin Auren nasu wanda za'a ɗaura 11am Mustafa kuwa yana kwance ko a jikin sa, sai famar games yake, wacce wayar Habeeb yayi daga hanun sa ɗago kansa Mustafa yayi yana kallon Habeeb yace.

" Ya dai malam zaka wani wacce min waya kamar wanda taka na ara."

Kafin Habeeb yayi magana Barrister Umar ya shigo yana cewa.

" Wai ya baku fito bane kam, tun ɗazu baƙi suƙe jiran ku, ga inspector khabeer ma can Angon Nasreen da Zuhura mutanen Gombe ya samu isowa, harda inspector Muhammad Angon Saude, Doctor Naseer ma Angon Nasmah shida Na'eem Angon Nasirah suma ba'a barsu a baya ba, duk suna jiran ku a falon baƙi, harda Conel Ubaidullahi Sarkin miskilanci, sai kuyi hanzari naga kamar time na neman ƙure muku."

Saurin tashi Mustafa yayi yana cewa

"seriours su Doctor Naseer sunzo da gaske?"

Dariya Barrister Umar yayi yana cewa.

" Zuwan nasu ya baka mamaki ko? Sunzo da gaske yanzu haka suna falon baƙi na Daddy."

Tollet Mustafa ya nufa yana cewa Habeeb

" kaci Albarkacin su da babu wanda ya isa ya fitar dani daga cikin ɗakin nan duk nacin mutum."

Girgiza kansa Habeeb yayi tare da cewa.


" Gani nayi danni suka zo tunda nine na gayyace su ba kaiba, kuma zuwa ɗaurin aure dole mutum yaje duk iskancin miskilancin mutum."

Murmurshi kawai Mustafa yayi ya shige tollet, cikin 50 minute Mustafa ya shirya, wow yayi

Please Login or Register in order to submit comment