Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ki ajiye."

Murmurshi Habeeb yayi tare da cewa.

" Tunda nine ciccika rumbu ko, to nima na koshi tunda tare muka sha yoghout ɗin, ƙanwata miyar da abincin kinji."

Wani irin baƙin ciki ne ya shaƙewa RAUDA ƙirji yanxu kam ta fara cinkewa da lamarin Mustafa dole tayi hkr dashi koda kuwa hakan zai zamo sanadin mutuwar tane, juyawa tayi cikin haushi ta koma falo, ranta ɓace ta cewa Momy.

"sunceƙoshi wai sunsha yoghout."

" Okey mayar kitchen sai kixo muci abincin."

Mayar RAUDA tayi taxo ta zauna, haka suka ci Abincin ranta ɓace.

Bayan sun gama cin abincin ne Indo ta tashi tayi ɗakin su, tare da kwanciya har yanzu Zuciyarta tunanin maganganun Habeeb yake, a haka RAUDA da sharifa suka shigo suka sameta, babu wanda ta kula cikin su, sai Sharifa ce taxo kusa da ita tace.

" Wai Indo meye yake damunki ne, naga tun ɗazu jikin ki da sanyi?"

Murmurshi Indo tayi tace babu komai Sharifa kawai bana jin daɗin jiki nane, bari ma naje nayi wanka Naxo na kwanta kawai."

" Shi kenan Amma ni sai nake gani Kamar akwai Abunda yake damunki?"

Murmurshi tayi tare da shigewa tollet tana cewa babu komai.

RAUDA tabe baki tayi, tana yiwa indo kallon banxa, ita kam Indo bata sanma tana yiba.

A falo kuwa Habeeb ne ya sauƙo, suke taɗi da Daddy inda Daddy yake cewa.

" Wato Habeeb na muku magana akan aure duk kunyi shuru ko, to wlh na kusa maganin ku, tunda baza ku fito da mata ba, ni zan fitar muku, sadakar ku zan bayar."

Daga Momy har Habeeb dariya sukayi sosai, Habeeb ya dubi Daddy yace.

" Haba Daddy abun kuma har ya kai ga sadaka?"

" Ya kai mana tunda kinƙi nemowa ai saini na nemo muku, tunda na gaji da ganin ku haka, kun riƙa min cikin gida har kun riƙe."

Dariya Habeeb yayi tare da cewa.

" Kwantar da hankalin ka, Daddy nikam na samu matar aure, verry soon zan kawo muku ita ku ganta, sai dai kuma kayi sadakar Mustafa nikam na samo."

Dariya Momy tayi tace.

" Shina Babu mai sadakar sa, domin kuwa ya sanar dani cewa, ya fidda matar Aure shima, Kuma ba kowa bace face RAUDA."

Da sauri Habeeb ya ɗago ido ya kalli Momy cikin mamaki, domin kuwa zai iya rantsuwa da Ubangiji cewa Mustafa bazai furta wannan maganar ba, sai dai kawai Momy ta faɗi son ranta.

Daddy kuwa cikin farin ciki ya furta.

" Masha Allah! Lallai abu yayi kyau Allah ya sanya Alkairi, insha Allah gobe zan zauna dashi Mustafa naji daga bakin sa."

Murmurshi Momy tayi tare da cewa.

" Allah ya kaimu."

Tashi Habeeb yayi haura sama yana mamakin maganar Momy, sai kuma ya kasa sanar da Mustafa Abunda yake faruwa.

Washegari bayan sunyi breakfast misalin sha ɗaya, Habeeb ya fita cikin sauri yana sanar da su cewa zaije ya taro *HASINA* a airport, murmurshi daddy yayi yace adawo lfy.

Murmurshi Mustafa yayi yana cewa.

" A dai rage rawar kai Bros ka taka a hankali kar zumuɗi ya saka gagara riƙe sitiyarin motar."

Dariya Habeeb yayi tare da cewa.

" Kai dai zauna kawai cikin gida tunda ka gamo da lalurar ƙafa, da nace kazo kamin rakiya."

Murmurshi Mustafa yayi yace.

" Haba Yaro waya fada maka, ai tunda na hauro wannan step ɗin babu inda bazanje ba, kai dai baka son rakiyar ne."

Dariya Habeeb yayi tare da ficewa yana cewa " ba wani."

Indo kuwa tashi tayi da gudu rike da hijab ɗinta a hanu ta bi bayan Habeeb tana kiran sa, tsayawa Habeeb yayi sanda ta iso kusa dashi tace.

" Ya Habeeb zan raka ka?"

Murmurshi Habeeb yayi tare da cewa.

" Muje Mamana" tare da buɗe mata murfin motar, dariya Indo tayi sannan ta shige, shima ya shiga yaja motar yana tsokanar Indo.

Sun ɗan juma cikin airport ɗin kafin jirgin Egypt ɗin ya sauƙa, tunda ta fara saukowa Habeeb ke kallon ta yana murmurshi, itama murmurshin ne ɗauke fuskar ta, tana kare masa kallo, fara ce kyakkyawa doguwa, tasha doguwar riga, fuskar ta yane da farin gyale, sanda taxo daf dasu Habeeb cikin farin ciki yace.

" Welcome to the Nigeria my sweet heart."

Cikin murmurshi ta mayar masa amsa da cewa.

" Welcome sweetie na."


Please karku mantani cikin Addu'ar ku dan Allah🙏🏻🙏🏻


*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah ce)*
[2/17, 6:17 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*



👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻


*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*


*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.


*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*P*••••••4️⃣7️⃣ ➡️ 4️⃣8️⃣

Kallo *HASINA* take bin Indo dashi cikin rashin sani, lura da hakan da Habeeb yayi ya sashi murmurshi tare da cewa.

" Ƴar Inna kenan sunan ta Indo wacce nake baki labarin ta kullum."

Murmurshi HASINA tayi tare da rungumo Indo jikin ta, tana cewa.

" Sannu sis, ashe da rabon zamu gana, ina jin labarin ki kullum wajen sweetie na, na ƙagu na ganki, sai kuma gashi yau mun haɗu, ina sonki" HASINA ta furta tare da mannawa indo kiss a kumatunta.

Murmurshi Habeeb yayi sosai cikin jin daɗin yanda HASINA ta ɗauki indo ƴar uwa.
Indo kuwa murmurshi tayi tana cewa.

" Nima ina sonki Aunty HASINA, sannu da zuwa."

" Yauwa sannu ƴar ƙanwata" duban Habeeb tayi tace " sweetie zamu iya ƙarasawa gida yanzu."

Murmurshi Habeeb yayi tare da buɗewa HASINA gaban motar ta shiga, ita kuma indo ya buɗe mata baya sannan shima ya shiga suka tafi.

Duban Mustafa Momy tayi tace.

" Mustafa kazo ka sameni cikin ɗaki ina son magana da kai."

Da to Mustafa ya amsawa Momy sannan Momy ta haura sama, bayan ta Mustafa ya tashi yabi yana ɗan ɗingishi, a bakin gado Mustafa ya zauna yana duban Momy kafin Momy ta fara magana.

" Mustafa tambayar ka nake son nayi,?"

" Ina sauraron ki Momy Allah yasa na sani."

Duban Mustafa Momy tayi cikin haɗa rai tace.

" Mecece ni a wajen ka?"

Cikin mamaki Mustafa ya dubi Momy yace.

" Momy! Wacce irin tambaya ce wannan? ke uwace a gare ni, wacce banda wanda ya fiki duk faɗin duniyar nan."

" Alhamdulillah! To idan har ka ɗauke ni matsayin uwa, umarni nake son na baka, Kuma dole sai kabi domin kuwa na yanke hukunci tun jiya, dan haka baka isa tsallake umurni na ba."

Duban Momy yake cikin son jin wani Abu ne wannan wanda Momy ta ɗauke sa seriours haka.

" Momy Please faɗa min menene wannan wani irin umarni ne, wanda bazaki faɗa min kai tsaye ba, har sai kin min tambaya?"

" Umarni nake baka, da ka Auri RAUDA a matsayin Suruka ta, ka sanar da mahaifin ka cewa itace ka zaɓa a matsayin matar Aure, karkuma ka sake ka sanar dashi cewa nice na saka ka Aure ta."

Tunda Momy ta fara maganar Mustafa yake kallon ta, domin kuwa jin maganar yake kamar almara, wai shine zai Auri RAUDA, kai! Ina inpossible! Bazai taɓa yiwuwa ba, banda dai RAUDA kam.

" Magana nake kayi shuru" cewar Momy.

" Momy Please da gaske kike wannan maganar ko wasa kike min, in wasa ne dan Allah Momy ki daina?"

Duban sa Momy tayi tace.

" Kaga wasa cikin Ido na, nace! Kaga wasa cikin ido na, na faɗa maka RAUDA itace zaka Aura, ko bazaka iya bin umarnin nawa bane?"

Tashi Mustafa yayi yana kallon Momy tare cewa.

" Dan Allah! Momy ki sauƙe wannan umarnin a kaina, wlh bana son RAUDA ban taɓa sonta ba, kuma bazan taɓa sonta ba, Momy bana sonta dan Allah ki janye maganar ki akaina Please Momy."

Cikin tsawa Momy tace.

" Umarni nake baka a matsayi na na uwarka, Kuma dole kabi idan kana neman albarka cikin Rayuwar ka, idan kuma kace ka tsallake magana ta, to kuwa babu ni babu kai, RAUDA ita nake so ka aura ta kasance surka cikin gidan nan kuma ina da tabbacin zamuyi alfahari da ita matsayin Suruka cikin gidan nan haka kaima sai kayi alfahari da ita kasancewar ta mata gareka."

Ƙaɗa kansa Mustafa yayi yana duban Momy kafin yace.

" Momy ki faɗa min ko wani irin umarni zan bisa Amma dan Allah ki janye wannan maganar Auren, wlh Momy bana son RAUDA, bana kuma tunanin akwai wani alfahari da zanyi da Auren ta, karki sa na kasance cikin nadama bazan taɓa ganin hasken RAUDA cikin idanuna ba, Momy kibar kowa ya auri zaɓinsa, idan ita tana sona, tofa Momy ni bana sonta, Please Momy?" Ya ƙarasa maganar yana haɗa hanun sa biyu alamun roƙo.

" Kaga babu sauyi cikin magana ta, na riga da na yanke hukunci dan haka ka daina faɗa ina faɗa!" Momy ta ƙarasa maganar cikin tsawa.

Shima Mustafa tashi yayi cikin fushi yace.

" Bazaki faɗa na faɗa ba Momy tabbas ina neman albarka cikin Rayuwata, ba kuma zan tsallake umarnin ki ba, zanbi umarnin ki, kamar yadda kika umarce ni, sai dai Momy ina son kisan cewa, zan Auri RAUDA ne badan soyayya ba kuma duk Auren da babu soyayya cikin sa, ba'a samun farin ciki shi kuma aure yana buƙatar farin ciki, sai dai zanbi umarnin ki zan aure ta kamar yadda kika ce, sai dai bazan taɓa sonta ba cikin rayuwata, ke kike son RAUDA ba niba, zamuyi wata irin rayuwar Aure ne, wanda babu daɗi cikin sa bare kuma a samu kula da farin ciki na tsaneta bana sonta, na sanar dake haka ne, saboda duk abunda zai faru daga baya karku zarge Ni, ku fara zargan kanku kiyi idan na ɓata miki rai cikin maganganu na, ina faɗa miki ne iya gaskiyar Abunda yake cikin raina ne" yana gama faɗin haka ya fice daga ɗakin cikin ɓacin rai, gabaki ɗaya gidan ya bari.

Taɓe bakin ta Momy tayi tana cewa.

" Auren RAUDA babu fashi, ko baka sonta dole zaka sota gaba ko dan ladabin ta, da biyayyar ta, yaushe zan barka ka fita waje neman aure bayan ga yarinya mai hankali da nutsuwa cikin gida, ka gama fushin ka, Aure dole sai anyi shi."

da wani irin matsiyacin gudu ya figi motar sa, gudu kawai yake kan hanya, ba tare daya damu da gangancin da yake yi bisa titi ba, Allah ne kawai ya isar da Mustafa Inda ya nufa, lfy wani madaidaicin gida ya shiga, ko sallama baiyi ba, ya faɗa ɗakin bisa kujera mai ɗaya ya zauna tare da riƙe kansa dake ƙoƙarin barin jikin sa, Umar dake kwance bisa kujerun falon ne, ya tashi yana cewa.

" Mustafa lfy, ka shigo haka a birkice?"

Mustafa bai kulasa ba, saima kwantar da kansa da yayi jikin kujerar har yanzu yana riƙe da kansa.

" Haba Mustafa Please mana tell me, what is your problem?"

Sai yanxu Mustafa ya ɗago idanunsa da sukayi jajur kamar gauta, yayi magana cikin ƙunar rai yace.

" Umar wai ni! Wai ni! Za'a yiwa Auren dole, momy ta rasa waye zata haɗani da ita sai wannan macen marar kamun kai, wacce sam bana ƙaunar ta cikin Rayuwata ban taɓa tsanar mutum ba irin yanda na tsaneta."

" Bangane mai kake nufi ba Barrister, wani irin Auren dole kuma wa zai maka Auren dole kana ɗa namiji, ba mace ba, naga dai mata akewa auren dole to kai kana namiji wa zai maka Auren dole?"

Ɗago kansa Mustafa yayi ya fara bawa Umar labarin Abunda Momy ta sashi ya kare maganar tare da cewa, "meyasa Momy bazata haɗa ta da Habeeb ba, tunda sunfi shiri."

Umar abokin Mustafa ne, har Habeeb tare sukayi makaranta shima kuma Barrister ne, court ɗaya suke aiki da Mustafa wannan shine dalilin da yasa umar sukafi shiri da Mustafa fiye da Habeeb, duban Mustafa Umar yayi tare da zama yace.

" Hmm! Babbar magana Lallai Momy ta kira ruwa, amma ni sai nake gani tun farko wannan abun kamar laifin kane mustapha."

Ɗago idanunsa da suka ci ja kamar borkono Mustafa yayi yana duban Umar kafin yace.

" Laifi na kamar ya ban fahimce kaba?"

" Eh laifin kane kamar yadda kaji na furta, tunda Daddy ya daɗe yana muku maganar ku fidda matan aure, kaga shi Dr Habeeb yana da tasa budurwar Hasina, amma kai kullum aka maka maganar Mace sai kace har yanzu baka ga matar Aure ba, wlh Mustafa da badan nasan halinka ba, zan iya cewa kana neman matan banxa ne tunda kake ƙin maganar Aure, Hujja ta Kuma itace, kana da jaraba ma'ana kai namiji ne mai buƙatar mace, amma sai kace ko wacce mace bata maka ba, idan kuma bance kana neman mata ba, to zance kana da ALJANAR da ta Aure ka take hana ka Aure."

Tsuka Mustafa yaja yana duban Umar yace.

" Uwar Aljana ce ta Aure Ni, ba Aljana ba, ya ina faɗa maka matsala ta, domin samo solution kana kawo min wata nonse magana."

Dariya sosai Umar yayi kafin yace.

" Ai baka da wani solution Barrister, domin kuwa duk wani masoyin ka na gaskiya shawara ɗaya zai baka shine yace maka kabi umurnin mahaifiyar ka, kuma ni gaskiya banga wani aibi a wajen RAUDA ba, duk inda cikakkiyar mace zata tsaya mai ji da kanta, RAUDA ma zata tsaya a nan, tana da ilimi da wayewa, kawai Mlm kabi umurnin mahaifiyar ka, ni shawarar da zan baka kenan, duk kuma wanda zai baka shawara saɓanin wannan ba masoyinka bane."

Murmurshin ƙarfin hali Mustafa yayi tare da cewa.

" Kun kasa fahimta ta, Umar ana Aure ne domin a samu kulawa da kwanciyar hankali, kuma waɗannan abubuwan basa kasancewa sai tare da Soyayya, ka sani cewa ni mutum ne, mai son soyayya da kulawa, taya zan iya bawa RAUDA kulawa tunda bana sonta, taya zan saurari kulawar ta, tunda bata burgeni, wlh Umar bana hango Alkairi cikin wannan Auren da ake shirin kulla min, wlh bana son RAUDA ina tsoron Abunda zai faru bayan Auren nan, domin kuwa zamuyi zaman cutar kaine, kuma bana fatar haka cikin rayuwar Aure na, ina cikin tashin hankali Barrister Umar."

" Kayi hkr Mustafa ka daurewa zuciyar ka kabi umurnin mahaifiyar ka, na tabbata Allah zai dubi wannan biyayyar da kayiwa mahaifiyar ka, ya baka farin ciki, cikin Rayuwar ka, koda daga baya zaka iya ƙara Aure idan ka samu wacce kake so ko nace zaɓinka, ka sawa zuciyarka salama."

" Hmm! Shi kenan Umar zanyi amfani da shawarar ka, amma dai RAUDA kam bana sonta, bazan kuma taɓa gajiya da furta cewa bana sonta ba."

Rarrashin Mustafa Umar ya cigaba da yi har ya ɗan sake kaɗan, suka ci gaba da zancen duniya.

" Momy! Momy! Momy!
Hasina ce mai ƙwalawa Momy kira tun daga falo, tana dariya, Inna ta hango zaune tayi wajen ta da gudu tana cewa.

" Oyoyo tsohuwa mai ran ƙarfe."

Ture hanun Hasina Inna tayi tace.

" Ni cika ni, ƴaƴan yahudu, kunje kun tare can wata uwa duniya kun manta da iyayen ku, barin ma ke, ko ta wayar ma bakya neman mutum, to ita uwar taki, ai tana nema na, dana zama mata dole ta neme ni, tunda nice uwarta dana haife ta."

Dariya Hasina tayi tace.

" Haba tsohuwa ban manta da kece kika haifi ummin ba, ai bare ki min tuni, yanxu ba gashi nazo ba, ai sai kuma kiyi hkr Inna na, kakata ta kaina."

Dariya Indo tasa tana duban Inna tace.

" To kiyi dariya mana Inna kin haɗa fuskar, ya Habibu zo mu mata cakulkuli tayi ta Dole."

Dariya Habeeb yayi tare da cewa.

" Ai kuwa ƙanwata ina ga hakan zamuyi tunda taƙi sakin fuskar."

Hararar su Inna tayi tana dariya tace.

" ja'irai sai kuxo kuyi cakulkul ɗin mu gani, ke kuma na yafe miki badan halin ki ba."

Gabaki ɗayan su dariya sukayi Hasina ta faɗa jikin Inna tana cewa bari naji ɗumin kakata.

Sosai sukayi hira da Inna kafin HASINA ta haura sama bedroom ɗin Momy da taji shuru tun shigowar ta babu labarin Momy, itama Indo nasu ɗakin ta nufa Momy tana Bacci HASINA ta sameta murmurshi tayi sannan ta fice zuwa ɗakin su Indo, ta samu Indo zaune tayi tagumi tana tunani, zama HASINA tayi ta dafa kafaɗar Indo tace.

" Sweet sis tunanin me kike haka?"

Ɗago kanta Indo tayi ta dubi HASINA, sai kuma idanunta suka ciko da hawaye tace.

" Aunty Hasina ina son ganin Mamana, jiya sanda nayi mafarkin jummalo tazo tana kuka tace min wai nabar Mama ita kaɗai babu mai taimaka mata da aike, ni dai gida zan koma, kuma kinga kullum Momy sai ta dinga hantara ta, tana zagina."

Shuru Hasina tayi kafin tace.

" Kinga sweet sis, ya Habeeb ya faɗa min dalilin da yasa aka kawo ki, gidan nan domin kiyi karatu, dan haka ki daina zancen zaki koma ƙauye ki dinga yiwa Mama addu'a wata rana ai zakije ki ganta, kuma zata ji daɗin ganin ki, idan kina karatu, karki damu da zagin da Momy take miki, zai shige wata rana Babu Abunda yaxo zama duniya, komai nisan jifa ƙasa zai faɗo ki dinga sawa zuciyar ki salama, kiyi hkr kinji sweet sis, ki kuma cire damuwa a cikin ranki."

" Shi kenan Aunty na daina."

" Yauwa sweet sisi na, yanxu bari na watsa ruwa na fito."

Mustafa daga gidan su Barrister Umar darect school ɗin su RAUDA ya wuce dake yasan department ɗin su, cikin Sa'a kuwa ya hango ta, tana zaune gefe ita da wasu ƴan mata biyu, tsayawa yayi gefen su tare da harɗe hanun sa a ƙirji cikin taƙama da gadara ya ce.

" Ƴan mata kuyi hkr ku bamu waje zanyi magana da wannan yarinyar" yana nuna RAUDA da baki.

Tashi ƴan matan sukayi ɗayar tana kallon Mustafa har tana tuntuɓe, harara RAUDA ta zabgawa Salima kafin ta maida kallon ta, kan Mustafa tace.

" Ya Mustafa sannu da zuwa, yau kaine da kanka?"

Cikin gadara Mustafa yace.

" Ba wannan bane ya kawo ni, na zone na baki shawarar da zata amfani Rayuwar ki, dashi."

Cikin mamaki RAUDA tace.

'' shawara Kuma ya Mustafa?"


" Yes Shawara, gaskiya na jinjinawa ƙoƙarin ki da kuma jajurcewar ki, akan Abunda kike so, kinyi Nasara gaskiya, Amma akan mahaifiyata! Ba niba, tunda har kikayi nasarar sace Zuciyar mahaifiyata, har take bani umurnin cewa na Auri Mace marar aji da kamun kai Irin ki, to kisani ina mai baki shawarar Cewa kije ki warware wannan Auren da ake shirin ƙullawa, domin kuwa wannan Auren muddun kika kuskura kika bari akayi wannan Auren, to ki sani cewa, Lahira sai yafi miki wannan Duniyar daɗi, domin kuwa gidana *KABARI NE ZAI ZAMA MIKI KI SHIRYAWA LIKKAFIN KI, DOMIN KUWA DOLE SAI KIN LULLUƁA SA, A ƘARSHE INA SON NA ƘARA SANAR DAKE CEWA BANA SONKI NA TSANEKI*." Ya ƙarasa maganar yana takewa RAUDA ƙafa tare da murza yatsun ƙafar tata da takalmin sa.


Ɗago kanta RAUDA tayi tana murmurshi ta cewa Mustafa.

" Gaskiya naji daɗin wannan Albishir naka, domin kuwa ban taɓa jin farin ciki a rayuwata Irin na yau ba, bazan je na dakatar da Momy ga hana wannan auren ba, domin kuwa koda ace yau aka ɗaura min Aure da kai gobe na fito, alhamdulillah buri na ya cika, na shiryawa Rayuwar *ƘABARI* a cikin gidan ka, muddun kuwa dakai zanyi Rayuwa cikin wannan Kabarin, a ƙarshe ina son na sanar da kai cewa *INA SONKA INA KUMA ƘAUNAR KA*."

Murmurshi mai sauti Mustafa yayi Kafin yace.

" Kin taɓa ganin inda akayi rayuwar kabari mutum biyu, kabari gida ne na mutum ɗaya tal dan haka ki daina kusanto inuwar rayuwar ki, dani domin kuwa ban kamace kiba, bare har nayi rayuwa dake, da zaki shekara kina furta kalmomi soyayya gare ni ni kuma sai na shekara goma ina furta kalmomi na ƙiyayya gare ki, yafi miki Alkairi ki nemawa kanki abokin rayuwa wanda ya dace da rayuwar ki, ki daina ƙoƙarin shiga gonata domin kuwa duk mutumin da yayi ƙoƙarin kutse cikin wannan gonar tawa, a ƙarshe mummunan irin ne yake fitowa daga wannan gonar."

A razane RAUDA ta ɗago kanta ta kalli Mustafa, shi kuwa murmurshi ya mata tare da ɗaga mata gira, cikin ƙarfin hali tace.


" Me kake nufi cikin waɗannan kalaman naka?"

" Ba kya buƙatar amsa daga gare ni, zaifi miki Alkairi kije ki yiwa kanki hisabi" yana gama faɗin haka ya juya ya tafi, sai kuma ya tsaya tare da ƙara duban RAUDA yace "Hukunci ya rage gareki ki zaɓi wuta ko ki zaɓi ni'ima, dan dabara ya rage ga mai shiga rijiya, idan kunne yaji." Kafin ya shige cikin motar sa yana murmurshi, tare da kannewa RAUDA ido.


_______________________________

Wlh naso nayi typing yafi haka yawa, amma kwana biyun nan ina busy kuyi hkr dani, dan Allah ku sani cikin Addu'ar ku, ina da matsala🙏🏻🙏🏻🙏🏻



*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*



*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*


*(Ummu Nasmah ce)*
[2/19, 8:53 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*



👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻


*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*


*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.


*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻

Masoyana na gode sosai da Addu'ar ku gare ni, kuma ina sa tsammanin Ubangiji zai amshi Addu'ar ku gare ni.

Masu min magana akan book ɗin Ruɗanin zuciya biyu, kuyi hkr dan gaskiya ba yanzu zan fara posting ɗin sa ba, Saboda bani da full times ɗin da zanke posting book biyu, kuma kunga bazan karɓi kuɗin kuba nazo bana muku typing akan lokaci, dan haka ina ga sai na gama wannan book ɗin na Indo a birni, ga waɗanda suka min magana cewa zasu turo kuɗin su, kuyi hkr har sai randa zan fara sakin book ɗin, dan gaskiya bazan karɓi kuɗin ku yanxu ba, ban fara posting ɗin book ɗin ba.

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*P*••••••••4️⃣9️⃣➡️5️⃣0️⃣

Shan gaban motar RAUDA tayi tana cewa.

" Koda kuwa kullum zaka dinga yankan naman jikina ne bazan taɓa bijirewa Auren ka ba, sai ma farin ciki da zanyi masoyina shike yankan naman jikina, ba kuma zanji zafin wannan yanka ta da kake ba, Saboda tsantsar soyayyar da nake maka, ina sonka me yasa ba zaka soni ba? a tunani na, nice macen da nafi dacewa ka Aura ka Kuma soni iya iyawar ka."

Dariya sosai Mustafa keyi yana nuna RAUDA da hanu.
Cikin ƙula da jin haushi RAUDA tace.

" Meyasa kake min dariya bayan ni ba mahaukaciya bace?"

Cikin dariyar Mustafa yace mata.

_"To kuwa tabbas kin haɗa jini da mahaukatan, domin kuwa muddun ke ba mahaukaciya bace, ba zaki dinga furta waɗannan munanan kalaman naki ba, ke mahaukaciya ce, ta gaske ma kuwa mai shirin zuwa turu ma'ana (gidan mari) idan ba mahaukaci ba babu wanda zaiyi ƙoƙarin shiga inda aka tsane sa, ki kauce ki

Please Login or Register in order to submit comment