Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

JAMAKA YASIN DOGUWA, MAI JAN WANDO KUMA BULLUƘUTU BAƘAR MUTUWA TSAKANINA DAKAI ARADUN ALLAH BAN YAFE BA*.

kaɗa kansa Habeeb yayi cikin jinjina yarintar Indo, Yace.

" Badai akan mustapha kike jamin Allah ya isa ba, to zo na miki hoto saina kai masa gida yaga wankan naki, ba shikenan ba.

Shuru Indo tayi tace.

" A shagon waye zamuyi photon shagon salisu zamuje.

" A'a a wayata zan ɗauke ki, wayar ya ciro daga cikin aljihun wandon sa, tare da cewa kin gani, fito waje na miki.

Tana washe bakin ta, Indo, Indo ta fito, Innah kuwa haɓa ta riƙe tana kallon rashin mutunci da Indo ke tsulawa, Habeeb ya yiwa indo pictures wajen kala Uku kafin ya mata da Innah, sai kuma sukayi sulfie shida INDO, suka zo sukayi su Uku harda Innah.

Cikin son zolayar mustapha Habeeb ya cewa Indo zo mamana, na miki video, ki faɗi saƙon ki, wajen masoyin naki, yana gani motsin bakin ki.

Zaro ido Indo tayi tace.

" Nice mamanka ƴar mitsitsiya dani, kai kuma ƙatoto dakai, nidai ka kira ni da indo na.

Dariya Habeeb yayi Yace.

" Nikam baxan kira sunan kiba, Saboda sunan mamana ke gare ki, idan kuma kince baxan kira ki da mamana ba, to na fasa miki video.

" Shikenan to na yadda, ka shirya na fara.

Dariya Habeeb yayi tare da saita Indo da wayarsa yana cewa ehh na shirya.

Gyaran murya Indo tayi sannan ta fara jero kalamai.

" *Assalamu alaikum yaya Mustapha ina kwana ya birni, da kuma mutanen cikin ta, yaya Mustapha yaushe zaka zo, Wlh nayi kewar ka, kuma gashi kullum kibiyar sonka harbi na, yake, ina sonka da yawa da yawa yaya Mustapha na, kaga wannan kwalliyar ma, kaine nayiwa, tana maganar tana fari da ido tare da washe haƙwara*

Dariya sosai Habeeb yasa sanda yake kallon videon, kafin ya bude data ya turawa mustapha su.

A wunin Ranar sabone sosai ya shiga tsakanin Indo da Habeeb.
Kusan tare suka wuni Habeeb na cin dariyar indo, tana basa labarin soyayyar da takewa mustapha, sam Habeeb bai nunawa INDO ƙyama ba, yanda kika san ƙanwar sa ta jini haka suke mu'amala da indo.



*Dutse local Government*

Da gudu RAUDA ta shigo cikin gidan nasu, shige Mamy tayi a falo tayi ɗakin ta, a saman gadon ta, ta zube tare da sakin wani marayan kuka, mai tsuma Zuciya.

Tana kukan mamy ta shigo cikin ɗakin, cikin tashin hankali, kusa da RAUDA ta zauna tare da ɗago kanta ta ɗaura bisa cinyar ta, tace

" RAUDA menene meya faru, wani Abu aka miki, kika shigo min gida haka.

Cikin matsanancin kuka, harda majina RAUDA tace.

" Ya mustapha ne, Mamy ya Mustapha baya sona, ya tsaneni mamy ƙirjina nauyi yake min, soyayyar ya Mustapha zata kasheni Mamy, ki taimake ni Mamy, Wlh idan ban Auri ya Mustapha ba mutuwa zanyi Mamy.

" Tsuka mai ƙarfi Mamy taja, tare da cewa.

" Haba RAUDA ke baki da wani aiki sai Mustapha Mustapha kullum ke kenan wannan sunan ne a bakin ki, waye ma mustapha me yake dashi da kika liƙe masa yana wulaƙanta ki, ga samarin da suka fi mustapha suna zuwa miki amma kinƙi sauraron su, meya fiki dashi da zai ke wulaƙanta ki, *kyau ya fiki Asali ko gata, ba komai ba laifin ki bane laifin wannan shegiyar Zuciyar taki ce, mai nacin tsiya, zanje na nemo miki soyayyar mustapha koda kuwa komai nawa zai ƙare, dole zanbi shawarar Habiba, zanje Niger wajen malamin nan, mustapha sai yayi dana sanin wulaƙanta ki a cikin rayuwar sa, Mu zuba mu gani, nida kai shege ka fasa, domin kuwa karen bana shike maganin zomon bana*
Kiyi hkr ki share hawayen ki, bari na ɗauki gyale na, naje gidan Hajiya Habiba mu tattauna.

Ɗagawa mamy kai kawai RAUDA tayi, Mamy na ficewa daga ɗakin RAUDA ta tashi taje gaban babban ilajimen ɗin mustapha dake maƙale a bangon ɗakin, ta tsaya tana magana kamar wacce take gaban sa.

" *Why mustapha why baka sona menene Aibuna, meyasa ka tsaneni, shin laifi ne danna soka, ko kuwa haramun ne, idan na soka,? tabbas nasan kasan zafin soyayyah, bai kamata ka Azabtar dani ba, kaji tausayi na, dan Allah ya Mustapha, ta ƙarasa maganar cikin kuka tare durƙushewa a wajen tana kukan hade da ajiyar zuciya*.

Shiko mustapha yana zaune cikin office ɗinsa hankali kwance yake harkokin sa, yama manta da wata RAUDA cikin rayuwar sa, zama yayi tare da kunna ƙira'ar Mlm Ibrahim Abdulrasheed, yana sauraro tare da bin karatun, cikin suratul Muminun.
Kamar wanda akace ya kunna datar sa, yana kunnawa saƙon Habeeb na shigowa.
Buɗe wa yayi, sai kuwa yaga pictures ɗin Indo guda Uku tare da video, da kamar bazai buɗe ba, sai kuma wata Zuciyar ta sashi buɗewa.

Duk tsare gidan mustapha da haɗe ransa sanda video nan ya basa dariya, sanda ya gama dariyar sa, sannan Yace.

" *Wannan kece mahaukaciyar kam cikakkiya ma, Habeeb kuma an haɗu da indo, lallai Innah kema kin shiga Uku da shiririta, HABEEB HABEEB mutum ya girma amma har yanzu baisan ya girma ba, ita kuma shasha, waini tayiwa kwalliya, koda yake ance idan baka da hankali ka aikata komai.*..............



*YAWAN SHARHI YAWAN TYPING*


*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*


*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*


*(Ummu Nasmah)*
[1/14, 3:19 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*



👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻


*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*


*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.


*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*BANSO YIN MAGANA BA, AMMA DOLE SAI NAYI MAGANA, HABA ƳAN UWANA YA KAMATA KUKE YIWA WRITERS UZURI, IDAN HAR KIN BIYO WRITERS PRIVET KINCE TA TURO MIKI BOOK, BATA KULAKI BA KAMATA YAYI KI MATA UXIRI HAR ZUWA WASHE GARI, KIGA IDAN BATA KULAKI BA, BAREMA IRINA DA YAU DUK SAƘONNI NA A WAITING MESSAGE SUKA ZO MIN KAƊAN NE WANDA SUKA ZOMIN A BUƊE, KU DAINA KIRAN CEWA WANE NADA GIRMAN KAI DAN ALLAH.*

*DUK DA DAI BANI AKA ZAGA BA, AMMA DAI ƳAR UWATA CE WRITERS, KUMA ABUN YAMIN ZAFI, TAYA BAƘYA COMMENTS CIKIN GROUP ƊINTA, DAN TA CIREKI SAI YA ZAMA LAIFI ITA BATAJI GANDAN MIKI TYPING BA SAI KENE ZAKIJI GANDAN MATA COMMENT, TA CIREKI KUMA KIN BIYOTA PRIVET DA ZAGI, HAR KINA KIRAN CEWA, IDAN KINGA DAMA SAIKI MATA MUGUNTA KI ƁATA MATA SUNA.*

*KIJI TSORON ALLAH DOMIN KUWA BABU ABUNDA ZAKI IYA MATA, SAI DAI IDAN UBANGIJIN TANE YA ƘADDARA MATA DOMIN IDAN UBANGIJIN TA BAI YADDA BA BABU ABUNDA KE KIKA ISA KI MATA.*

*DUK WACCE NA ƁATAWA RAI SANADIN WANNAN MAGANA YAYI HKR 🙏🏻 NI DAI NA FAƊA NE DOMIN WACCE TAYI MAGANAR TASAN CEWA BABU MAI ƘADDARAWA MUTUM ABU SAI UBANGIJIN SA YA SO*

*P*••••••1️⃣9️⃣ ➡️ 2️⃣0️⃣

Hanun sa yasa da niyar goge video da pictures ɗin sai kuma yaji kira a wayar tasa.
daga kiran yayi tare da amsa Sallama.
Ya daɗe yana wayan kafin daga ƙarshe naji yana cewa, shikenan Abdul Babu damuwa sai kazo goben, yana gama wayar.
tana mutuwa Babu chage, tsuka yaja tare da tattara, kayan sa, ya kulle office ɗin, ya nufi motar sa, kasancewar lokacin tashin sa daga aikin yayi.

" Kinga sharifa tashi ki ajiye wannan wayar da tun ɗazu kika sata gaba kin kasa min Aikin komai, tunda shi girkin nayi, aikuma dai zaki samu ki min gyaran kitchen ɗin koh.

Ajiye wayar Sharifa tayi tana haɗa rai ta nufi kitchen ɗin, wayar ta Momy ta ɗaga tare da dannawa RAUDA kira, ringine ɗaya RAUDA ta ɗauka tare da cewa, barka da yamma Momy.

" Yawwa RAUDA Barka dai, ya naji Muryar ki, kamar wacce kikayi kuka.

Goge guntun hawayen ta RAUDA tayi tace.

" A'a Momy ba kuka nake ba, ina ga ko network ne yake rawa, dan nima haka nake jin muryar ki.

" Ayyah cewar Momy, ai network ɗin mtn sai a hankali, daman na kira naji kin koma gida lafiya ne.

Murmurshi RAUDA tayi cikin jin daɗin yanda Momy take sonta tace.

" Na koma lfy lau Momy, yanxu ma haka aiki nakewa Mamy ta fice unguwa.

" Ayyah to bari na ƙyaleki kiyi aikin ki, kya gaida Mamyn naku idan ta dawo.

" Zataji RAUDA tace tare da kashe wayar, sai kuma ta ƙara goge hawayen daya gangaro mata, sannan ta kira raihana ƴar aikin su, domin taya ta haɗa abinci a daining.
Har Mamy ta dawo babu walwala a fuskar RAUDA.
Dafa kafaɗar RAUDA Mamy tayi, tace

' ki kwantar da hankalin ki, insha Allah kin kusa samun mustapha a tafin hanun ki, munyi magana da Hajiya Habiba, tace bama sai naje ba, ita zataje mana chan Niger ɗin wajen malamin.

Gyaɗa kanta RAUDA tayi tace.

" Allah ya jiyar damu Alkairi, Mamy maganar kuɗin, wayar da nayiwa Abba har yanzu shuru yace zai baki ki bani, kuma naji shuru har yanzu.

" Cap kin ganni da shiririta ko, ya bani kuɗin nan fah, dubu ɗari, suna cikin dressing mirror na, kije ki ɗauka, ina gama wataƙil abban naku gobe ya dawo.

" Allah ya dawo dashi lfy, Sallah RAUDA ta shiga yi, yayin da itama Mamy tayi nata ɗakin.

Sanda ya tsaya yayi sallar magriba kafin ya shigo cikin gidan nasu, a falo ya taradda duka family na gidan har Daddy.
Gaishe dasu Daddyn yayi tare da ƙoƙarin haurawa sama, yaji Muryar Daddy ya kirasa.
Dawowa yayi tare da zama ƙasa gefen ƙafar Daddyn.

" Mustapha waiko ka manta da cewa kun girma ne, har yanzu banji kun fara maganar Aure ba, ya kamata kuma, yanxu haka kuna tare da iyalan ku fah, yanxu fah kuna da shekara 30 me kuke jira?

Shuru mustapha yayi kasancewar shi harga Allah yanxu Babu maganar Aure a gaban sa, baya kuma neman ƴar Kowa, bai kuma shiryawa aure ba yanxu.
Jin shurun yayi yawa ne yasa daddy cewa,

" Ya naji kayi shuru, ko bada kai nake magana bane.?

" Daddy kayi hkr, a yanxu kam gaskiya bana neman Aure, a ɗan ƙara mana lokaci, insha Allah ZAMU nema.

" Allahu yasha, dan ya kamata ku fara nema tun wuri, tashi Allah ya maka albarka.

" Ameen Daddy na gode.

Kallon Daddy Momy tayi tace,

" Alhaji ni Kuma ga wani shawara, me zai hana mu haɗa Auren yaron nan mustapha da RAUDA, kaga yarinyar tana da hankali, shikenan sai muyi tuwo na maina, hankali kwance, koya ka gani?.

" To A'ishah baxan ce miki a'a ba, amma gaskiya da hakan zata kasance sai nafi kowa farin ciki, sai dai kuma karki manta da cewa su yaran yanxu ba'a musu dole cikin al'amuran su, mu barsu idan akwai rabon Aure tsakanin su, Allah ya haɗa su, ni bana son takurawa yaro cikin lamarin sa.

Ɓata rai Momy tayi domin kuwa bata so haka ba, taso ne Daddy yabi bayan ta, sai kuma ya mata tozon raƙumi ya yasar da zancen ta gefe, shuru tayi bata ƙara cewa komai ba, domin kuwa tasan daddy kaifi ɗaya ne, baya magana biyu.

Ƙarfe takwas daidai mustapha ya sauƙo suka ci abinci bai wani juma ba ya koma ɗaki kasancewar yanda yake jin marar sa, na famar ƙulle masa, kwanciya yayi tare da yin shuru, tun marar tasa na masa kaɗan kaɗan har ta dawo tana masa ciwo sosai, muƙurƙuso kawai mustapha keyi saman gadon sa, domin yasan Halin ciwon nasa, Babu Abunda ke sasa wannan shegen ciwon sai munguwar sha'awar da yake da Ita, gashi yanxu ya kai matakin da bazai iya tashi ya ɗauko tablet ɗin dayake amfani dashi ba, riƙe marar yayi sosoi, yana jin wani mungun felling na taso masa babu Abunda yake buƙata yanxu irin yaji mace kusa dashi, gashi shi Allah yayi shi da kyankyamin tsiya, bazai iya kusantar matar da batasa ba, yana cikin wannan Halin Allah ya jefo Ishaq cikin ɗakin, da hanu mustapha ya masa alamar yaxo, tahowa Ishaq yayi da sauri wajen yayan nasa, a hankali Mustapha yake masa magana cewa ya buɗe drower akwai tablet yellow ya kawo masa tare da ruwa a prich.

Ɗaukowa Ishaq yayi ya basa, da ƙyar mustapha ya miƙe yasha maganin sannan ya koma ya kwanta, aikuwa bai juma da shan maganin ba, wani irin gumi ya yanko masa, duk jikin sa ya sake, a haka bacci ya ɗauke sa.


*DASINA*

Yau kwanan Habeeb huɗu a ƙauye dasina, sosai Kuma yake jin daɗin zaman garin, Zaune suke Shida Indo cikin gidan Hajiya Innah, tashi Habeeb yayi tare da nufar bishiyar maina dake tsakiyar gidan, hawa bishiyar yayi Yayin da Innah da indo suka zuba masa Ido, ƙaryo mainar yayi, sannan ya sauko yana gyara ta, sanda ya gyara ta, tsaf sannan ya kalli Indo yace.

" Ungo karbi.

Kallon sa, Indo tayi tace.

" Bangane ungo ba, me zanyi dashi kuma.

" Yawwa tambaya mai kyau, kinga dai na farko kince kina son Mustapha koh?

Gyaɗa kanta Indo tayi alamar ehh, harda ɗan murmurshin ta.

" Yawwa to kinga shi kuma mustapha yana son mace wacce haƙwaran ta, suke fari tas, kamar dai nawan nan, kinga ke Kuma naki hakwaren kin barsu sun ɓaci da datti, to shine naga cewa mai zai hana tunda nida ke, mun zama ƙawaye, na taimake ki, na taya ki, neman soyayyar mustapha, kuma ta yanda zamu fara dole sai mun fara da gyara ki tukunna, ki dinga wanka kina wanki kina goge haƙwaran ki, idan mustapha ya ganki fes, dole zai soki, kinga shi mace mai tsafta yake so, shiyasa ma, na ɓallo miki wannan iccen mainar dan ki fara goge bakin ki, kuma ba iya yau kawai zakiyi ba, kullum sai kinyi, ni Kuma na ɗau alƙawarin duk sanda na koma birni zan turo miki maclean da brush, wanda zaki dinga wanke haƙwaran ki dasu.
Kin yadda?

"Na yadda ai nasan kai kana sona baxaka cuceni ba, na yadda da kai fiye da yanda na yadda da Innah.

Harara Innah ta dokawa Indo tace.

" Kuji ja'irar yarinya, yo to ni ina ruwana dake, balle kuma yardar ki, shima Habibun wuyar sa, kukai Anjuma ne, sai an jiku a rana.

Dariya Habeeb yayi tare da cewa.

"Kinga rabu da Hajiya karɓi, ki fara goge bakin, ki goge fah sosai.

Karɓa Indo tayi ta tauna sannan ta fara dirjan bakin ta, dashi, sosai ta dage take goge haƙwaran ta, har jini suke tana goge, sanda ta fara jin zafi tayi wurgi da magogin gefe tace.

" *Kan bala'i Wlh ya Habibu kai mungu ne, kaji yanda bakina ke min zafi, kuma kasan yana zafin tsabar baƙar mugunta shine zaka bani kace na goge baki, to aradu baxan goge ba*.

Haɗa Ransa Habeeb yayi sannan yace.

" Nine mungun koh, shikenan na gode, daga yau kuma Babu ruwana dake, baxan ƙara taimakon kiba akan mustapha, daman akwai wacce take sonshi a can birni, kinga shikenan idan yaga ta fiki gaye da haɗuwa, mai fararen haƙware, tas tas dasu, sai ya sota, shikenan ke kuma kin tashi a *TUTAR BABU YA MANTA DA WATA INDO MA A DUNIYA, NI KUMA INA CAN INA WAJEN AIKINA BAZAMA KI GANNI BA, BARE MA KICE NA TAIMAKA MIKI* .

Zabura Indo tayi cikin masifa da bala'i ta miƙe tsaye tayo kan Habeeb tana cewa.

" *Ita yarinyar taci ubanta, kaji shegiya wai ya Mustapha take so, to Wlh ƙarya take ya Mustapha ƙwalelenta, yafi ƙarfin ta ya Mustapha na Indo ce, ita ɗaya, YASIN NASHA RUWAN ARADU DUK SANDA ALLAH YA HAƊANI DA ITA SAI NACI KUTUMAR UBANTA, SAITA GWAMMACE KIƊA DA KARATU, KAIMA HAR WANI MAIMATA WA KAKE KAMAR WANDA KA FAƊI ABUN ARZIKI, TO YASIN NA HAƊU DA ITA SAINA SANJA MATA KAMMANI, KAN UBAN CAN WAI YAYA MUSTAPHA NA, TAKE SO, LALLAI KAM, SANNU SARAN MAI BAƘAR TA KASHI GATA BULU GATA JAJA, SHEGIYA, KAWAI*.
Sunkuyawa tayi ta ɗauko magogin tace, badai kan goge baki bane, *TO YASIN INDAN NA FARA GOGE BAKI NA, SAI YAFI NAKA HASKE, TA ƘARASA MAGANAR DA HARARAR HABEEB TAYI ƊAKIN INNAH TANA GOGE BAKIN*.

Dariya ce ta kwacewa Habeeb ganin yanda Indo ta taso kansa da Bala'i kamar shine yace yana son Mustaphan.
Kallon Innah yayi yace Hajiya.

" Lallai kuna fama da indo cikin garin nan.

Dariya Innah tayi tace.

" Wai damma kwanan nan bata ɗebo magana, amma ai Indo Rana ɗaɗɗaya ne, bata jawowa iyayen magana da zagi a cikin gari, amma naga kai yanxu kana iyawa da Ita.

Dariya Habeeb keyi, yaji wayar sa, na ringine, Bros ya gani manne a jikin screen ɗin wayar dariya Habeeb yayi ya ɗaga tare da cewa.

" Allah ya taimaki Barrister sai yau aka ga sakon nawa ne.

Murmurshi Mustapha yayi daga can Yace.

" Badai kaje ka zaune wajen Hajiya ka manta da muba, kodai mu biyoka da sauran kayan kane.

Dariya Habeeb yayi tare da cewa.

"A'a kuyi hkr ba sai kun biyoni dashi ba zan dawo, jiya da daddare munyi waya ai da daddy, har ya bawa Momy wayar.

Sai yanxu mustapha yayi dariya yace.

" Ya sanar dakai kenan.

" Meya sanar dani, ni babu wani Abunda ya sanar dani, taɗin duniya kawai mukayi ya kashe wayar sa.

" Cewa yayi ya fara gajiya da mu, ya kamata mu nemo matan Aure.

Dariya sosai Habeeb yayi sannan Yace.

" Nine dai ya kamata na nemo matar aure ba kai ba, kai kam ai kana dasu, ko baka zaɓi sauran ba, ya kamata ka zaɓa cikin *RAUDA DA INDO, kaga daman kullum cikin felling kake, shikenan saika huta da shan tablet*.

Tsuka Mustapha yaja tare da cewa.

Daɗi na dakai kenan ba'a maganar arziki dakai, kaika sansu har kake tunawa dasu cikin rayuwar ka, kaga ni sai Anjuma ma.

Dariya Habeeb keyi yace.

" Allah ya huci Zuciyar ka, ga Innah zakuyi magana.

Da gudu ya ƙarasa ɗakin Innah ya ɗaura wayar kunnen Indo, cikin raɗa yanda mustapha bazai jiba, yace kiyi magana mustapha ne.

Cikin ɗoki da murna indo ta ƙankame wayar tare da cewa.................




*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*


*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*


*(Ummu Nasmah)*
[1/17, 6:16 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*



👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻


*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*


*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.


*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________


*P*•••••••2️⃣1️⃣ ➡️ 2️⃣2️⃣

" *Wayyo Allah daɗi kashe ni, ya Mustapha na, Aradun Allah ina sonka, kibiyar sonka ta soke ni, kaji wani irin daɗin da naji kuwa da ya Habibu yace ga mustapha na*.
Jin shurun da tayi ne, yasata kallon Habeeb tace.
Ya Habibu banji yayi magana ba, fah.

Mustapha bai kashe wayar ba, shuru yayi yana jin su, domin kuwa yana jin sanda Habeeb yake, cewa Indo gashi mustapha ne kiyi Magana, shiyasa yayi shuru ba tare daya kashe wayar ba, yana jiran Habeeb ne ya karɓi wayar ya masa rashin mutunci.

Karɓar wayar Habeeb yayi tare da dubawa, cikin mamakin ganin mustapha bai kashe wayar ba, kuma bayan yaji Muryar Indo, sa wayar yayi a kunnen sa, tare da cewa.

" Bros ya kuma kayi shuru kana jin masoyiyar ka, tana sanar dakai yanda kifiyar sonka yake sukan ta kayi mata banxa.

Murmurshi mustapha Yayi cikin jin takaicin yawan wasan Habeeb, shi dai komai zai iya yiwa mutum wasa akansa, koda kuwa mutum yana cikin Halin da baya buƙatar wasa.

" Hmm to Uban ƴan neman magana, naji sai kuma akayi yaya, Sarkin ƴan neman magana na duniya, Kuma bari kaji na sanar dakai daga yau baxan ƙara neman ka a waya ba, har sai kabar wannan ƙauyen, Kuma karka Ƙara nema na, dan ko ka kira baxan ɗaga ba, tunda kaima kana son biye wannan shashashar ku zama iri ɗaya.

Murmurshi Habeeb yayi, cikin serious ya cewa mustapha.

" Bros naji abunda ka faɗa min kuma na ƴarda, sai dai ina son kasan Wani Abu guda ɗaya, kallon Indo yayi da ta mayar da hankalin ta wajen sa, ficewa yayi daga ɗakin Innah yayi nasa yana cewa.
*Duk yanda mutum yake, bai kamata ka wulaƙanta shiba, domin kuwa, gobe baka san mai zai zama ba, sannan aini a tunanina, shi mai Sonka yafi maƙiyin ka, kuma bai cancanci wulaƙanci daga gare kaba, Amma kai Bros........*

" Enough Habeeb bana buƙatar wani magana daga gare ka, cikin tsawa yace, *akan me zaka bawa wannan shashashar Iblis ɗin wayata, yarinyar data gagari Uban kowa cikin wannan ƙauyen, ƙazama marar Hankali da lissafi, idan har kaima ka koma shashasha, toni ban koma ba, da nawa hankalin a jiki na*
Yana gama faɗin haka ya kashe wayar.

Zuciyar Habeeb idan tayi dubu to, ta ɓaci domin kuwa yaji zafin maganar da mustapha ya faɗa masa, duk da yasan halin zafin zuciyar mustapha, zai iya yiwa kowa ihu idan ranshi ya ɓaci, sai dai baiyi tunanin, dan ya bawa Indo waya, ranshi zai ɓaci haka ba.
Shigowar Indo ne, ya katse masa maganar zucin daya ke yi.

" Ya Habibu ya kuma ka tafi baka bani wayar munyi magana da shiba, kuma har nasa raina zanji Muryar yaya Mustapha na, tana maganar ne tana tura baki.

Murmurshi Habeeb yayi tare da cewa.

" Babu network ne, shiyasa wayar ta tsinke, Amma ki bari sai gobe, idan ya sake kira sai na haɗaa ku.

Tsumewa Indo tayi, tana murguɗe murguɗen baki, tace.

" Nidai Wlh ya Habibu ban yadda ba, ai naji kuna magana dashi yanxu, shine ka gudo nan dan karka bani muyi magana, toni ban yadda ba, sai dai ka kira min shi yanxu ko Kuma kayi min video Irin na ranan sai ka kai masa tunda kace gobe zaka koma birni, idan kuma kaƙi min to Wlh *ALLAH YA ISA BAN YAFE BA JAMIN RAI DA KAYI*.

Haɗa Ransa Habeeb yayi, ya gallawa ya Indo harara, tare da cewa.

" Wato dai ke Indo baki da kunya, ni kika jawa Allah ya isa koh, ban girme ki bane da zaki jamin Allah ya isa, kamar wani sa'an ki, dan kinga ina kulaki koh, shine zaki

Please Login or Register in order to submit comment