Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da mustapha.

" Ga saƙon dan Allah ka tabbatar ka bata hanu da hanu, ka shiga har cikin falon nasu, ka gaishe da mamyn nasu, koh.

Karɓa yayi tare da ce mata insha Allah zan shiga, sannan ya tashi ya fice Momy na masa a dawo lfy, tare da fatan Allah ya haɗa kansu da RAUDA, dan ta fahimci kamar akwai ƙiyayyar RAUDA cikin Zuciyar mustapha.

A falo ma, a dawo lfy Daddy yayiwa mustapha, sannan ya fice daga cikin gidan.


Hajiya Turai mahaifiyar RAUDA, suna zaune tare da Hajiya Hindatu, ta kawo mata saƙonta, na Niger, dariya Hajiya Turai tayi tare da cewa.

" Amma dai Hindatu na gode sosai, Wlh ai daman nasan harkar ki Babu wasa cikin sa, kinsan yanda nake jin tausayin yarinyar nan, na rasa wani irin soyayya take yiwa wannan yaro, bata sauraron ko wani Saurayi ita dai kullum mustapha shine a bakinta, shiko ya maida ita shasha baya ma sauraron ta.

Dariya Hajiya Hindatu tayi tare da cewa.

' to yanxu kam ya shigo hanu, dan wlh muddun kunyi amfani da wannan magani dai-dai to tabbas sai Mustapha ya shigo hanun ku, kunyi yanda kuke so dashi, na gaya miki, wannan cikin abinci za'a sa masa ku tabbatar yaci abincin, wannan kuma ƙofar ɗakin sa, zaku barbaɗa, shima ku tabbatar ya, tsallaka, sai wannan turaren kuma, RAUDA ta tabbatar ta shafa shi duk sanda zasu haɗu dashi.
Idan kuka bi wannan dokokin dana lissafa muku, to kun sami mustapha kun gama, ina ita RAUDA take, taxo na ja mata kunne sosai ma tukunna.


" Bata Nan ai Hajiya ta tafi makaranta, amma insha Allah yau tana dawowa, a gidan su zata kwana, domin ganin ta gabatar mana da wannan aikin.

Yawwa da dai zaifi, bari na koma gida Hajiya, nabar sakina kwance zazzaɓi na damunta.

" Ayyya Allah ya bata lfy, na gode sosai Hajiya Insha Allah zaki ganni duk abunda ke faruwa zakiji.


Allah yasa muji Alkairi cewar Hajiya Hindatu.

Har compaunt ɗin gidan Mamy ta rakata, Hajiya Hindatu na fita mustapha na shigo da hancin motar sa cikin gidan.

Salim ƙanin RAUDA dake buga boll tsakar gidan Mamy ta shige zuwa cikin falon ta.

Parking mustapha yayi ya ɗan juma kafin ya fito daga cikin motar, kiran salim yayi, da gudu salim ya ƙaraso.
Tambayar sa Mustapha yayi ko Abban su nanan.


" Ya mustapha yana nan, ka shiga yana nan ɗakin da suke ganawa da baƙi, yana tare dasu.

Ɗakin Mustapha ya nufa, yana riƙe da hanun salim suka shiga.


Mustapha bai daɗe da shiga ɗakin baƙin Abban nasu ba, itama RAUDA ta shigo cikin gidan, dawowar ta kenan daga school.........


Kuyi manage da wannan🙏🏻🙏🏻🙏🏻

*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*


*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*



*(Ummu Nasmah ce)*
[1/24, 10:06 AM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*



👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻


*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*


*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.


*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

Kuyi hkr masoyan Indo a birni na rashin jina kwana biyu da bakwayi, hakan ta faru ne, sakamakon tafiya da nayi zuwa garin Jigawa, gashi muna hidimar bikin, sister na, Please kumin afuwa zuwa ranar talata idan Allah ya dawo dani Gombe lafiya, sai mu ɗaura daga inda muka tsaya, karku gaji da jira na, abunda yasa kuma nake ɗan yin typing ɗin Sara da sassaqa, Saboda shi book ɗin na kusa gamasa ne, Please kumin afuwa, tare da addu'ar Allah ya dawo dani gida lfy.


Please ku taya ni share ɗinsa domin ya samu ya isa zuwa ga masoyana.


*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah ce)*[1/29, 11:53 AM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*



👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻


*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*


*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.


*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻

_________________________

*Masha Allah my ƙawalliya ƙawar Arziki Zarahn Abdul, momyn Ahlan, ina tayaki murnar kammala wannan shahararren book ɗin naki wato (Shuhuda) Allah ya bamu ikon amfani da darusan dake cikin sa, Abunda kikayi kuskure kuma Allah ya yafe miki, congratulation momyn Ahlan🤝🏻*

_________________________

*Alhamdulillah fan's gani na faso dole na daure nayi muku typing yau saboda ƙaunar da kuke yiwa wannan book, waɗanda suka kira ni, suka min murnar kammala book ɗina na Sara da sassaqa baya hana gamji toho da kuma waɗanda suka turo min text har zuwa kan waɗanda suka min murna ta online tare da fatan Alkairi, na gode sosai da ƙaunar ku gareni.*

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*P*•••••••2️⃣5️⃣ ➡️ 2️⃣6️⃣

Cikin gajiya RAUDA ta shiga cikin falon nasu, a saman kujera ta faɗa tare da cewa.

" Wash Wlh Mamy yau na gaji sosai, wani text mukayi mai zafi kaina ciwo yake ina gani ma, wanka zan shiga nayi na kwanta.

" Amma dai ke RAUDA akwai malalaciya, yanxu kin dawo bazaki zauna kici abinci ba, sai kije kiyi wankan, idan yaso saiki kwantan, waya sani ciwon kan ma kona, yunwa ne.

" Bafa yunwa bane Mamy, kawai text ɗinda mukayi ne, ya samin wannan ciwon kan.

Shigowar Salim da gudu ne ya hana Mamy yin maganar da tayi niya, tace.

" Lafiya ka shigowa mutane ɗaki da gudu salim cewar Mamy.

" Mamy daman zan faɗawa Aunty RAUDA ne, ya mustapha yaxo yana ɗakin ganawar Abba yanxu haka.

Murmurshi Mamy tayi domin kuwa mustapha yaxo mata a dai-dai, wannan shine first tagget ɗina akanka, daga yanxu zan fara wannan maganin, duk cikin Zuciyarta take wannan zancen, kallon salim tayi tace.

" Naji koma wasan ka, manga na, ta masa maganar cikin sigar rarrashi, fita yayi abunsa, sannan Mamy ta dubi RAUDA tace, maza jeki ɗaki ki kwaskware fuskar ki, turaren da Hajiya hindatu ta bata wanda zata shafa a fuska, Mamy ta miƙo mata, tace maza ki shafa yanxu Hajiya hindatu ta kawo sa, tace indai kin shafa mustapha ya kalle ki, anwuce wajen, domin kuwa dole ya soki.

Aiko cikin murna da zumuɗi RAUDA ta karɓi turaren tare da shigewa bedroom ɗinta da gudu, murmurshi Mamy tayi tare da yin kitchen domin yiwa Mustapha barbaɗe barbaɗe cikin ruwa da abinci, kasancewar tasan indai mustapha yaxo gidan Abba yana nan, dole saiya ci abinci, kafin ya tafi.

Mustapha kuwa shigar sa, part ɗin bakin Abban ya samu saura mutum ɗaya ne, har ƙasa mustapha ya sunkuya ya gaishe su, kafin Abba ya masa nuni da gefen sa, yace yaxo ya zauna.
Bayan Abba ya sallami bakon nasa ne, ya dubi mustapha Yace.

" Muhammad Mustapha ne, ko Muhammad Habeeb, kasan bana gane ku, idan kuka haɗu waje ɗaya, gashi kuma Alhaji Haroun yace min shima Habeeb ya shigo ƙasar.

Murmurshi Mustapha yayi yace.

" Nine mustapha Abba, daman Daddy ne, yace naxo na karɓi sako wajen ka.

" Ayyya Muhammad Mustapha, tashi mu shiga ciki to, sai kaci abinci, kafin na baka saƙon koh.

Mustapha bai yiwa Abba musu ba, ya tashi ya bisa cikin gidan, a daining suka tarar da Mamy ta shirya abinci, gaishe da Mamy mustapha Yayi ta amsa cikin sakin fuska tana tambayar sa, mahaifiyar sa, tana lafiya yace mata, kafin Abba ya umurce shi da cewa ya zauna a daining ɗin, zaman kuwa sukayi, Mamy itace tayi seving ɗinsu, yayin da ta zubawa mustapha mai maganin, basu Kuma juma da zama ba, itama RAUDA ta fito cikin kwalliya, ta zauna kujerar dake kallon ta mustapha, wanda yana ɗaga idanun sa, ita zai kalla, tunda RAUDA ta zauna mustapha bai ɗago idanun sa, ba bare su haɗa da RAUDA, yadai ji Muryar ta, Abba ne ya kalli mustapha Yace.

" Muhammad Mustapha, kaci abinci mana, an zuba maka Kuma.

Sai a lokacin RAUDA tace.

" Sannu da zuwa ya mustapha ina wuni.

A dakile Mustapha yace.

Lfy tare da ɗaukar spoon.

Daga Mamy har RAUDA murna suke mustapha zaici abincin domin kuwa sunsan yana ci yaxo hanu.

Ɗebo abincin mustapha yayi, har zai kai bakinsa sai yaji Ringtone din wayar sa, maida spoon ɗin yayi ya fasa kaiwa bakin nasa, tare da ɗaga wayarsa, ji nayi yace.

" Ka samu bayanan, to tsaya dai-dai roat block ɗin gani nan zuwa yanzu, tashi mustapha yayi yacewa Abba.

" Amin afuwa Abba, wlh wani sako zan karba mai mahimmanci, gun wani, gashi kuma baƙo ne, hanyace ta biyo dashi tanan garin zai shige, idan zai yiwu da an bani sakon saina samu na shige.

Murmurshi Abba yayi yace.

" Babu damuwa Muhammad Mustapha ai kana cin abinci cikin gidan nan, ke Turai jeki ɗauko masa wannan karamar jakar dana shigo dashi.

Daga Mamy har RAUDA ji sukayi kamar an soka musu mashi cikin ƙirjin su, da mustapha ya tsallake wannan tarkon nasu, sunji mungun bakin ciki, haka dole Mamy ta shige ta ɗaukowa mustapha sakon ta basa, ƙarɓa yayi tare da yiwa Abba sallama, ya fice da sauri, tashi RAUDA tayi itama cikin sauri tabi bayan sa, tana cewa.

" Ya mustapha baka jiba.

Tsayawa mustapha Yayi daga buɗe murfin motar tasa, ya ɗago kansa, carap kuwa sukayi ido biyu da RAUDA, wani irin tsinkewa zuciyar mustapha yayi, kansa kuwa neman juye masa yake.

" Subhanallah ya furta da ƙarfi tare da ambaton, innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un, la'ilah ha'illah anta subhanaka inni kuntu minnazalimin, tare da zama cikin motar da sauri yana dafe da kansa, yafi 15 minute yana Zaune yana ambaton Ubangiji, Kafin yaji komai ya dawo masa normal, har lokacin kuma RAUDA na tsaye wajen, bai ƙara ɗago kai ya kalleta ba, saima wani tsawa daya daka mata.

" Wai RAUDA me kike nema dani ne, kin dameni kin dami rayuwata, RAUDA duk wani take taken ki, na sani, Sona kike, to dan Allah zan roƙeki, ki ƙyale Ni, nikam bakya cikin matan da nake burin Aura, baki min ba, dan haka, ki sawa zuciyar ki, salama ki daina wahalar da kanki, iya gama faɗa mata haka, yasa hanun sa, ya dauko sarkar da Momy tace ya bata, ya wurgo mata tare da cewa idan kinga dama ki ɗauka Momy ce tace na kawo miki, sannan yaja motarsa da ƙarfi yabar wajen.

Tsabar takaici RAUDA ta kasa motsi daga inda take, tsaye, hawaye kuwa ya wanke mata fuskar ta, sunkuyawa tayi ta ɗauki sarƙar sannan ta shige cikin falon nasu, tsayawa tayi ta goge hawayen ta, kafin ta shige su Mamy tayi bedroom ɗinta, Abba ne, ya kalli Mamy yace.

"Turai Kamar akwai Abunda ke damun RAUDA koh naga yanayin ta, kamar ya sauya?.

" Meka gani abban RAUDA, cewar Mamy.

" Haka dai na gani kamar mood ɗinta ya sauya ba kamar yanda ta fita ɗazu ba.

" To gaskiya ban sani ba dan ban lura da shigewar ta ba amma dai gaskiya Babu Abunda ke damunta.

" Okey shikenan tunda haka kikace, bari na shige bedroom ɗina, ki samu kisa a gyara part ɗin baƙin nan.

" Shikenan Abban RAUDA, za'a gyara.

Bayan Abba ya shige bedroom ɗinsa ne, Mamy tayi bedroom ɗin RAUDA, tana kwance tayi rup da ciki sai kuka take mai tsuma Zuciya, hawaye kuwa harda majina, girgiza kanta Mamy tayi, tare da zama, ta fuskanci RAUDA tace.

" Shikenan ke yanzu haka zaki zauna kullum kina yiwa namijin kuka, yanxu ke bazaki dage a matsayinki na mace ba, ki jawo hankalin mustapha, sai kace wacce kika fito daga ƙauye, ki tashi ki wanke fuskar ki, ki shirya zaki koma gidan su, mustapha da Zama har sai buƙatar mu ta biya, zan miki bayanin duk yanda zakiyi amfani da maganin, zamuyi nasara akansa insha Allah.

Cikin kuka RAUDA take cewa.

" Mamy na haƙura da ya mustapha domin ya faɗa cewa baya sona, Kuma mun haɗa ido shi, wannan maganin ƙarya ne Mamy, tunda Bayan mun haɗa ido dashi ne ya furta min cewa baya sona, na haƙura Mamy nasan mutuwa zanyi, domin soyayyar ya mustapha bazata barni nayi nisan kwana b........


Toshe mata baki Mamy tayi tace.

" Ki daina furta waɗannan mugayen kalaman, dole ma mustapha ya soki kota Halin yaya, magani kuma yana da kyau, ki tashi nace kibi umurni na, ki shirya ki tafi, karkiyi zuciya akan abunda zuciyar ki, bazata ita haƙuri dashi ba.

Tashi RAUDA tayi ba tare da ta kara cewa Mamy komai ba, tayi tollet.


Shiko mustapha yana fita darect, wajen mutumin da sukayi waya yaje, wasu takaddu ya basa sannan sukayi Sallama ya wuce bank ya ajiyewa Daddy kuɗin sa, sannan ya dawo gida, a falo ya samu Habeeb Zaune yana danna waya suna game shida Sharif, ware idonsa mustapha yayi tare da cewa.

" Yaushe ka dawo kai kuma.

Murmurshi Habeeb yayi tare da cewa.

" Tun ɗazu nakai 2 hours da dawowa.

Zama mustapha yayi yana cewa.

" Kace yau kabar Innah da kewa, ni nayi zaton ma ai sai mun bika da kayan kane.

Dariya Habeeb yayi tare da cewa.

" Wlh ƙauyen ne, yamin daɗi, mussaman dana samu Indo, gaskiya yarinyar tayi a rayuwa.

Taɓe bakin sa Mustapha yayi, tare da cewa dake shashancin ku ɗaya ba, amma inbanda haka meye abun burgewa wajen, wannan taɓaɓɓiyar wacce ta addabi al'ummar garin, ni kaga bari na shige inada abunyi cikin ɗaki, tunda naga kaima baka da abun faɗa.

Murmurshi Habeeb yayi tare da cewa.

" A fito lfy daman ai nima bance ka zauna ba,.

Shidai Mustapha bai tankawa Habeeb ba ya haura sama.

Sharif ne ya cewa Habeeb.

" Ya Habeeb, ya mustapha ya cika masifa, kullum yana cikin faɗa, ni tsoronsa ma nake ji wlh, kuma fah ya Habeeb ance duk mai faɗa mungu ne.

Haɗa ransa Habeeb yayi tare da cewa.

" Kul na ƙara jin wannan maganar a bakin ka, yayan naka ne, yake masifa, har kike cewa mungu, to wlh idan ya jika, wlh saina lahira yafika jin dadi kadai san halinsa.

Tura bakin sa Sharif yayi tare da cewa.

" Kayi haƙuri ya Habeeb bazan sake ba.

Murmurshi Habeeb yayi yace.

" Ya wuce Autan Momy, game ɗin suka cigaba dayi, sallama RAUDA tayi hanun ta janye da akwati.

Amsawa Habeeb yayi cikin fara'a yace.

" A'a baƙuwar muce ta dawo, kinga mun dawo a dai-dai kuwa, nima ban juma da shigowa, ba.

Murmurshi RAUDA tayi kafin ta ƙaraso, tace Lallai munyi anko, kenan nima yanxu ina zaune naji kawai ina son dawowa, Sharif ne ya amshi akwatin nata, yana ƙoƙarin haurawa dashi, ita kuma ta zauna kusa da Habeeb suka cigaba da magana.

Mustapha daya fito da key a hanun sane, yayi turus sakamakon ganin RAUDA Zaune yarinyar daya bari yanxu cikin gidan su, tsuka yaja tare da cewa.

" Mayyah kawai, sannan yasa kansa ya fice ba tare daya kallesu ba.

Girgiza kansa Habeeb yayi, cikin takaicin mungun hali irin na mustapha, da nunawa mutum ƙiyayya a fili.


*DASINA*

Tafe take riƙe da kara a hanun ta, tana raira waƙarta.

" Ayya raye ayye ayye, ayyya raye ayye dije, zaman gidan wani tilas ne, ba'a kanki ne aka fara ba, ba'a kanki ne za'a ƙare ba, ƴar tsohuwa mai lallen zo yaki nan, kunsa mata amaryar nan n........

Maganar da malam Yakubu makaho ya mata shine ya katse mata waƙar tata, cikin murna tana dariya tace.

" Lah Baba Yakubu kaine, Aradu ban lura dakai ba, ina zakaje da sassafen nan haka.

" Yo Indo ina zanje kuwa idan ba Bara ba, bara zan fita mu sami na cefenen gida.

" Kai Baba Yakubu yanxu yanda kake da tiƙeƙen ƙaton Yaron nan, Sani bazai je yayi sana'a ya kawo muku na cefenen ba, har sai kai da kake makaho kaje kayi bara ka Kawo kuma yaci, to aradu ni a gidan ya Tanimu shine yake bada kuɗin cefene, gashi kuma baban mu yana da idanunsa, amma dai Aradun Allah Sani yayi Asara.

Dariya Mlm Yakubu yayi, domin kuwa yasan duk haukar Indo, yaudai maganar data faɗa tana kan hanyar gaskiya, sannan Yace.

" To ya za'ayi Indo tunda shi bazai nema ba, aini dole na nema, kodan ƙananan yara.

Kallon dubu ɗayan da Mama ta aiketa siyo kwanon shinkafa da rabin mudun wake tayi, sai kuma ta kalli Mlm Yakubu, ta sake kallon dubun kai tsaye tace.

" kaga Baba Yakubu karka je barar nan, dan wlh na tsani barar nan, gashi kai Kuma ba ɗan jagora kake dashi ba, badai kuɗin cefene kake nema ba, ta gashi wannan dubu ɗayan kaje kayi cefene ba shikenan ba.

" Ina kika samo dubun indodo, da zaki bani?, ya tambaye ta cikin mamaki.

Ƙarya Indo ta zafgawa domin tasan idan tace masa kuɗin aika ne bazai karɓa ba, domin kuwa jinin Indo da Mlm Yakubu yaxo ɗaya sosai suke shiri, sannan tace.

" Tsintarta nayi ɗaxo daman zan kaiwa Mama ne nace nayi tsintuwa, kaga tunda yanxu kai kana buƙata, saika karɓa.

Karɓa Mlm Yakubu yayi yana shiwa rayuwar Indo albarka, kama sandar tasa Indo tayi tace muje Baba Yakubu na rakaka gida, sai ni kuma na wuce gida.
Tafiya sukayi Indo ta raka Mlm Yakubu har ƙofar gidan sa, sannan ta ruga da gudu tayi gidan su.

Mama na Zaune ta ɗaura ruwa a murhu tana zaman jiran Indo ta kawo mata shinkafa ta tsince ta saka cikin tukunyar, sai ganin Indo tayi ta shigo mata hanu ziƙau babu komai, tsayawa tayi akan Mama tayi shiru ba tare da tayi magana ba.

Kallon ta Mama tayi sannan tace.

" Ya kika tsaya a kaina ne, yiwa zaki bani magani ina aiken dana miki.

Kai tsaye Indo tace.

" shagon ɗan tasin a
rufe ne.

" Arufe kuma cewar mama, to bani kuɗin na aika jummalo gidan su, Hadiza ta sayo min.

Kallon mama tayi tana turo baki gaba tace.

" *Nayi miki sadaka da kuɗin*

" Kinyi min sadaka da kuɗin, mama ta tanbaya, ban gane kinyi sadaka da kuɗi ba.

" *Mama Baba Yakubu makaho ne, na haɗu dashi yanxu a gangare, zai tafi bara, shine yamin magana, yace zaije Bara ne, ya samo kuɗin cefene, shine ni kuma ya bani tausayi, na basa sadakar dubun taki, tunda ke kina da mai baki, ya Tanimu, shi kuma bashi da wanda zai basa, Sani ma shege ne, baya basa*.

Kallon takaici Mama ke bin Indo dashi, domin kuwa yanxu ta fara tsoron lamarin Indo, kodai tana da aljanune a kanta, cikin haushi Mama tace.

" Shikenan kin raya gidan wasu ke kuma kin kashe naku gidan, yau wasu zasu ƙoshi mu kuma zamu wuni da yunwa, yanxu Indo idan banda sakarci Irin naki kin taɓa ganin inda mutum yayi kyauta da abunda ba nasa ba, to Kuma Wlh yau sai kinsan kinyi kyauta da dubu, danko yau Babu mai hanani cin ubanki cikin gidan nan.

Danƙo Indo Mama tayi, ta rufeta da duka, ihu Indo take tsakanin ta da Allah kamar wacce mama take yanka ta, Baba saude maƙwabciyar su, da taji ihun Indo yayi yawa ne, yasa ta, zagowa cikin gidan, daƙyar ta ƙwaci Indo hanun Mama tana cewa.

" Haba mero yanxu wannan dukan da kike yiwa yarinyar nan ai yayi yawa, babu kyau fah yawan duka.

" Ki barni mero na daki yarinyar nan yau ko zan huce, wlh na gaji da halin Indo, kullum da Abunda yarinyar nan take jawo min, masifar yau daban ta gobe daban, yanxu dan Allah Saude ki duba ki gani, tun da hantsi na ɗaura sanwar abinci, na aiki yarinyar nan Indo taje ta siyomin shinkafa na bata gudan dubu, jummalo na kwance bata da lfy, kinga har yanzu ƙarfe 1:00 na azahar ta dawo min, babu aiken dana mata, wai take cemin tayi sadaka da dubu ɗayan, sai kace ƴar gidan wani babban attajiri, da zakiyi kyautar dubu.

" Ashsha haba yanxu ke Saboda baki da hankali, ki ɗauki kuɗin abincin ku, ki kyautar, baki kyauta ba, Indo dan Allah mero kiyi hkr, kibar maganar ta shige yaran yanxu ne saida hkr, duk yawanci haka suke.

" Zan haƙura Saude sai wlh yau baxan bawa Indo abinci cikin gidan nan ba, sai daita kwana da yunwa, kallon Indo Mama tayi tace, zaki fice minne da gani kosai na taka miki wuya, shashasha marar lissafi.

Ihu Indo ta ɗauko ta zunduma, sai kuma tayi waje da gudu tana ihu, girgiza kanta Baba Saude tayi, sannan ta kara bawa Mama hakuri ta koma cikin gidan ta.
Tashin jummalo Mama tayi ta dauki ɗari biyar tace taje ta sayo musu shinkafa.

Da gudu ta shiga gidan Innah tana ihu.

" *Wayyo Allah na shiga Uku na lalace wayyo Allah Mama zata kasheni, wayyo Allah bayana ya kare*

Jin ihun Indo yasa Innah fitowa da gudu rike da zani a hanu, tana cewa.

" Subhanallah wani shegen ne, zai kashe ki?

" Innah Mama zata kashe ni, ta karya min bayana, tamin duka saura kaɗan ma ta jefani wuta Allah ya kawo Baba Saude ta ƙwaceni kuma tace wlh yau bata bani abinci ba.

" Ita mairon ce, tace haka, cewar Innah, me kika mata to, nasan dai ruwa baya tsami banxa.

Tura bakinta Indo tayi tace.

" Wai dan kawai ta aikeni da dubu, shine na haɗu da Mlm Yakubu, zashi bara, wai basu da kuɗin cefene, shine fah na mata sadaka da kuɗin nace yaje yayi cefene.

Salati Innah ta ɗauka tare da cewa.

" Yanxu daman akan ɗan wannan abun mairo ta miki wannan mungun dukan, dan kawai kin mata sadaka kin nema mata lada a wajen Ubangijin ta, to muje gidan naku naji dalilin da ta miki wannan dukan.

Mayafinta Innah ta ɗauka tasa Indo a gaba tana mita har gaban Mama.

Ganin Innah da Mama tayi ta tashi da sauri ta ɗauko mata taburma tana Cewa.

" Sannu da zuwa Innah lale maraba.

Cikin masifa Innah tacewa Mama.

" Bana son sannu da zuwan ki, ki riƙeta, yanxu mairo kan dubu shegiya kika yiwa indo wannan dukan, saboda kawai ta nemo miki lada wajen Ubangijin ki, kunce bakin zanin ta, Innah tayi, ta ɗauko gudan dubu ta wurgawa Mama tace, ga kuɗin ki, ladan sadakar kuma Allah ya bawa Indo, duka kuma da kika mata kin daki Allah ya Isa.

Murmurshin takaici Mama tayi sannan tace.

" Kiyi hkr Innah, ki karɓi kuɗin ki, nikan bazan riƙe kuɗinki ba, Allah ya huci Zuciyar ki, kiyi hkr dan Allah.

Harar Mama Innah tayi tace.

" baxanyi hakurin ba, abinci Kuma kar Allah yasa ki bata, muje Indo kici abinci harki kyautar.

Shigewa Indo tayi tana yiwa mama dariya harda gwalo, tabi Innah suka tafi, gidan ta.

Girgiza kanta Mama tayi cikin

Please Login or Register in order to submit comment