Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jikin Inna ya kifa mata mari, ƙafarta ya jida da ƙarfi Allah ya rufa asiri ta faɗa kan kujera, (domin kuwa da ta faɗa saman tayels ɗin nan kanta kam sai Abunda Allah yayi)
Tashi Inna, tayi itama zata ɗauke Mustafa da mari, yayi saurin sunkuyawa, ta mari iska, cikin zafin rai Inna, take magana.

" Uban! me ta maka? da zaka mareta, idan banda munguwar zalunci, to wlh ka mari Allah ya isa, bata yafe ba, yi hkr kinji indona tashi ki barsa da Allah."

"Wlh Allah ya" kasa ƙarasawa tayi sakamakon mummunan kallon da Mustafa ya aiko mata, haɗiye maganar tayi, ta shige ɗakin Inna tana magana ƙasa-ƙasa, Momy ce ta kalli Mustafa tace.

" Ka min dai-dai Mustafa, gobe ma ka mata, dukan da yafi wannan, shegiya gayyar na aiye gayyar tsiya, an ɗebo min tsiya an kawo min cikin gida."

Shidai Mustafa bai tankawa Momy ba, yayi ficewar sa, abunsa.


********************************

" Wlh Mamy kin bani dariya, yanxu to meye laifin, Abba, a nan dan kawai ya bawa ƙanin sa, 2millions ni dai gaskiya a waje na, ba komai bane sai zumunci da yayi."

" A wajen ki, da baki da hankali ba, amma ni so nayi ya basa 50k ya ishesa, amma yaki saurara ta."

Sallamar Mustafa ne ya katse musu zancen nasu, amsa Sallamar sukayi, sannan Mustafa ya cewa, Mamy.

" Barka da dare Mamy."

" Barka ya hanya, da fatan kun bar Kowa lafiya?"

" Lfy lau alhamdulillah! Kowa yana lafiya."

Yau dai RAUDA bata kula Mustafa ba, ko gaisuwa bai haɗa su ba, shima dai Mustafa ko oho, domin kuwa, baima kalli inda RAUDA take ba, bare kuma yasan da ita a wajen."

" Mamy ni zan koma cikin mota, daman Momy ne tace nazo na ɗauki RAUDA, idan ta shirya ina jiran ta, cikin mota idan kuma bata shirya ba, driver ya kawo ta da safe."

" A shirye take, ke RAUDA tashi kije ki ɗauko kayan ki, ku tafi."

Tashi RAUDA tayi ba tare da tayi magana ba, shi kuma Mustafa ya fice, jim kaɗan sai ga RAUDA ta fito, kararaki sosai Mamy tayiwa RAUDA, akan ta kula sosai, da wannan maganin wannan karon."

Gaba ta buɗe ta shiga ba tare da ta kalli Mustafa ba, tana jawo murfin motar shi kuma yaja, har suka isa cikin gidan babu wanda ya cewa ɗan uwansa komai."

Da Sallama RAUDA ta shiga cikin falon dukan su sunq zaune har Inna da Daddy, cikin murmurshi Momy tace.

" Oyoyo my daughter, sannu da dawowa."

Murmurshi itama RAUDA tayi tare da zama gefen Momy, ta dubi Inna cikin girmamawa tace.

" Sannu ina wuni."

" Lafiya" Inna ta amsa, itama cikin fara'a.

Sannan ne, ta gaishe da Daddy, amsawa Daddy yayi tare da cewa Inna.

" Wannan itace jikar Alhaji muktar, Uban gida na, ƴar ɗansa ne, Ahmad takan zuwa gidan nan ta kwana biyu."

" Ayya Allah sarki sannu RAUDATU ya iyayen naki?"

"Lafiyar su lau" RAUDA ta amsa.

Momy ce tacewa RAUDA.

" Inna ne mahaifiya a cikin gidan nan."

Shigowar Indo da sharifa ke nan falon, Sharifa tana cewa.

" Oyoyo Aunty RAUDA, tun ɗazu nasa ran zuwan ki, naji shuru ashe kina hanya."

Magana RAUDA zatayi, sai kuma ta fasa sakamakon haɗa Ido da sukayi da Indo, Dam! Dam! Dam! Ƙirjin RAUDA ya buga, haka kawai taji Zuciyar ta, na dukan uku-uku sakamakon ganin Indo da tayi.

" Waye wannan Momy?" RAUDA ta tambayi Sharifa.

Murmurshi sharifa tayi tace.

" Oh Sunan ta, Indo ƴar uwar mune, ta dawo gidan nan yanxu da zama, Indo ga Aunty RAUDA, wacce nake gaya miki jiya.

Murmurshi Indo tayi cikin halin ko inkula tace.

" To Sannun ta, nikam zanje na kwanta Allah bacci nake ji."

Sharifa ne tace.

" Bismillah kije ki kwanta amma dai ki tabbatar kinyi wanka kafin ki kwanta."

"To" Indo tace sannan ta haura, Mustafa dake tsaye ƙofar ɗakin su yaga shigewar Indo, da sauri ya bita cikin ɗakin tare da dannawa ƙofar key.........




*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*


*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*


*(Ummu Nasmah ce)*
[2/11, 3:11 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*



👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻


*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*


*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.


*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*Congratulation ƙawalliyata momyn Ahlan ina taya ki murnan fara sabon book ɗinki, COLONEL UBAIDULLAHI Allah ya baki ikon rubuta Abunda zai amfani al'umma*.🙏🏻


*PLEASE ƴan Uwa ku tayani da addu'a, ina da muhimmiyar buƙata, kusani cikin Addu'ar ku a sallar ku, biyar, Allah ya biya min buƙata ta*🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻


*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*

*P*••••••4️⃣1️⃣ ➡️ 4️⃣2️⃣

Danƙo gashin Indo Mustafa yayi, cikin zaro mata Ido ya ce.

" Uban waye kika zaga ɗazu, ɗan ubanki! Nace! Uban waye kika zaga?"

Cikin azaba Indo ta ce.

" Cewa nayi uban wanda ya tsargu, ai bance uban..........."

Ba ta ƙarasa ba, Mustafa ya haɗata da bango, tare da shaƙo wuyan ta, ya fara magana cikin zafin rai.

" Na rantse da Allah, idan baki fita harka ta ba, wlh wata rana sai na illata rayuwar ki, ki bar ganin kina tsiya cikin ƙauye ana ƙyale ki, to wlh nan ba ƙauye ba ne, ko ni nan sai na ɓatar dake a duniya a neme ki a rasa, banza daƙiƙiya jakar ƙauye, a kan me zaki dinga shiga harkata? da kinsan yanda na tsaneki na tsani ganinki ma a duniya, wlh da baki shiga harkata ba."
Wata ƙaramar wuƙa Mustafa ya ciro a cikin aljihun sa, wacce take ajiye a cikin ɗakin su, suke yanka fruit da ita, ya nunawa Indo ya ce "Muddun ba ki fita cikin harkata ba, sai na illata ki da wannan wuƙar na kashe ki kowa ma ya huta."

Idon Indo yayi jajajur, duk rashin hankalin Indo da haukarta, yau ta ji zafin abin da Mustafa ya mata, domin kuwa Indo tana da zuwa, mussaman ma idan taga za'a ci mata mutunci, da ƙarfi ta ture Mustafa, cikin faɗa ita ma take ce masa.

" In sha Allah kuwa zan bar cikin harkar ka, kamar yanda kace ka tsaneni haka nima yau na tsaneka, bana sonka, idan ka kashe ni sai meye, Inna ce take tsoron mutuwa, ba niba, ka rubuta ka ajiye, daga yau idan ka ƙara ganin na shiga cikin rayuwar ka, ka kashe ni, amma muddun ka shiga cikin rayuwata saina shiga taka."

Tana gama faɗar haka ta faɗa saman bed sai kuma ta sake wani marayan kuka, tana kiran sunan Mama. Tabbas yau ne rana ta farko da ta ji tsanar mutum cikin ranta, domin kuwa duk mutumin da zai ce ya tsaneka ba ƙaramin maƙiyinka ba ne.

Sake baki Mustafa yayi yana mamakin maganganun da Indo ta faɗa masa, shi kallon yarinyar da ba ta san komai ba yake mata, sai ƙauyanci da hauka, amma ji yanda take zaro magana, cikin mamakin nata ya fice daga ɗakin. Yana buɗewa Sharifa da RAUDA na sako kansu za su shiga cikin ɗakin, hararar su yayi tare da musu mungun kallo ya shige, cikin sauri Sharifa ta faɗa ɗakin domin kuwa ta san Indo tana cikin ɗakin kuma ga Mustafa ya fita, aikuwa zarginta ne ya zama gaskiya yanda ta samu Indo kife tana sharɓar kuka.

" Lafiya Indo? me ya same ki, Please me aka miki, ki faɗa min mana Indo?"

Shuru Indo tayi ba ta kulasu ba, sai ma shafa gashin mta, da tayi tana tuno yan da Mustafa ya jamata da ƙarfi.

" Dan Allah Indo kiyi hkr ki faɗa min me ya same ki?"

Tashi Indo tayi cikin tsawa da kuma ƙarfi ta ce.

" Na rantse da Allah duk randa aka wayi gari Mustafa ya karye, to ni ce, wlh! Sai ya san ya min mugunta, na kuma tsanesa kamar yanda ya tsaneni, nida shi shege ka fasa a cikin gidan nan"

" Haba Indo, Mustafa kawai kika kira babu yaya, bai kamata ba, koma meya miki ai yayanki ne koh?"

Cikin tsiwa ta ce.

" Ba yayana ba, ubana ne shi, nace ubana ne shi, na faɗa Mustafa, idan sunan ubana na kira, sai na ji?"

Cikin tsawa RAUDA ta ce.

" Wai ke ya haka ne sai rashin kunya kike yiwa mutane, ana baki hkr kina rainawa mutane wayo, to kar Allah yasa ki hakuran mana."

Hanu Indo ta ɗagawa RAUDA tana cewa.

" To fa! wai daman cin danƙo harda su kaza, ke kuma a suwa, to wlh kar ki kuskura ki fara shiga cikin sha'anin Indo, domin kuwa Indo ba kanwar lasa bace, idan kuma kika ƙi, to kema *mu zuba mu gani*, mtsss."

Ta ja doguwar tsaki tana, hararar RAUDA, hannu RAUDA ta ɗaga za ta zabgawa Indo mari, Indo tayi saurin riƙe hanun RAUDA kafin ta ƙarasa fuskar ta, tana cewa.

" Karki fara wannan gangancin! Domin kuwa duk randa hanun ki, yayi kuskuren taɓa fuska ta, sai kin gwammace ba ki sanni ba cikin rayuwar ki, idan kuma kin ce ƙarya ne, ki gwada ki, gani ki bar ganin kin girme ni, to wlh girman ki ba zai bani tsoro ba, *dan funkun-funkun bata kilishi* tsap zan iya dukan ki Wlh, ni maza ma basu share wajena ba, bare kuma ke, *girman kazar Agric, girman falo ni kuwa girman ƙauye ce, naci tuwo na ƙoshi dan haka ƙarfin mu, ba zai taɓa zuwa ɗaya ba* Dan haka ki kiyaye, *in kunne ya ji jiki ya tsira*."

Tana gama faɗin haka tayi saman gado ta kwanta ba tare da ta kalli Sharifa ba.

Shuru sharifa ta yi, kawai ba tare da ta tankawa Indo ba, sai ma nema mata shirya da tayi wajen Ubangijin halitta ( lallai Indo wannan halin naki kin dinga shan wahala kenan wajen ya Mustafa) cikin Zuciyarta, Sharifa ke wannan maganar.

Cikin tsawa RAUDA ta cewa Indo.

" Ke! Jakar ƙauye tashi ki bani gadona, na kwanta domin wannan gadon mallaki nane, saboda ni aka sashi a ɗakin nan, dan haka sai ki sauƙa kiyi shimfida a ƙasa tunda daman an saba da kwanciya a gadon bono."

Murmurshi Indo tayi tana daga kwance ta ce.

" To Jakar Birni, dole ai na tashi na baki gado, tunda ubanki ne ya ajiye gadon, idan kin isa ki zo ki ɗaga ni da ƙarfi."

Cikin jin haushin su, Sharifa ta ce.

" Ya isa ya isa! Haka haba wannan wani irin masifa ce, yanxu ke RAUDA fisabilillah da girman ki, zaki biye Indo kuke sa'insa, kinyi ƙanwa ta biyu fah da Indo, just 12 years he is younger akan me to zaki biye ta, ni kaina nafi Indo bare ke, just ki kama mutuncin ki dan Allah, idan akan gado ne, mu kwanta a nawa gadon mana gani nayi zai ishe mu."

Carap Indo tayi ta ce.

" Kar ma ta kama idan har *ba ta ji kunyar yasar da girman ta ba nima bazan ji kunyar takawa ba*."

Kallon sharifa RAUDA keyi tana cewa.

" Bayan wannan yarinyar kike bi Sharifa, duk wannan rashin Kunyar da tayi wa ya Mustafa, ba ki ga laifin ta ba, har kike bani rashin gaskiya iye Sharifa?"

" Mustafa ubanki ne shi, da zakiji haushi danna masa rashin kunya, to sai kixo ki rama masa *ƴar shishshigi mai kalen dangi*."
Cewar Indo.

" Kinga RAUDA ni fa ba bayan Indo nabi ba, gaskiya ce kawai na gaya miki, idan kuma ranki ya ɓaci kiyi hkr."

RAUDA ba ta ce musu komai ba ta fice a fusace daga cikin ɗakin.

Kallon Indo Sharifa tayi ta ce.

" Ke kuma kin ƙyautawa kanki, yanxu fisabilillah meye amfanin masifa, dan Allah ki ragewa zuciyarki wannan faɗan ki zauna da kowa lafiya," zama tayi ta ce, dan Allah Indo kiyi hkr ki daina cewa Mustafa, ki kira sa da yaya dan Allah, ki daina masa rashin kunya."

Indo za tayi magana kenan, Momy ta faɗo ɗakin cikin faɗa tare da ɗauke Indo da mari.

" Gidan ubanki ne! nan da har zaki zage ta, koko ke gadon na ubanki ne! da kinsan yanda na tsaneki da ba zaki dawo gidan nan da zama ba, kin addabi al'ummar garin ku, kin fi ƙarfin iyayen ki, shine ni za'a ɗauko min ke akawo min cikin gida, to bari kiji na gaya miki, RAUDA ta fi ki power cikin gidan nan, domin kuwa nafi ƙaunar ta, fiye dake, sauƙa ki bata gadon ta, idan ya so ki kwana a ƙasa daman kin saba da wahalar ƙauye, fitinanniya."

Tunda Momy ta fara magana Indo take binta da ido Yayin da hawaye ke tsere saman kumatunta, tashi tayi ta fice da gudu tana ihu da ƙarfi.

" Wayyo! Allah Inna na shiga uku na lalace, wayyo! Za su kashe ni, Inna ki taimake ni."

Da gudu Inna ta fito jin ihun Indo, shima Daddy fitowa yayi daga nasa ɗakin a firgice, Mustafa da yasan hali bai wani damuba a nutse ya fito ya tsaya bakin ƙofar ɗakin sa, tare da harɗe hanun sa, a ƙirji yana kallon ikon Allah.

Inna ce tace.

" Meya sameki? Kike ihu da tsohon daren nan, Amanar Allah."

" Inna zagina tun ɗazu RAUDA take da suna ko waye? Takeyi wai bazan kwana a saman gado mai laushin nan ba, wai sai dai na kwana a ƙasa, shine ta turo Momy ta ce na kwana a ƙasa, tunda ni fitinanniya ce."

Salati Inna ta ɗauka tare da tafa hanu tana cewa.

" A cikin gidan nan aka miki wannan tozartar, saboda ita RAUDATU gidan ubanta ne, nan, bani hanya na wuce?"

Girgiza kansa Daddy yayi shi wlh yayi tunanin wani mungun abu ne ya sameta, har zuciyarsa tana tsinkewa, Daddy a zuciyarsa yake cewa (lallai Mlm Musa kana shan haƙurin zama da Indo, yarinta yayiwa yarinyar yawa) haurawa sama Daddy yayi ya shige ɗakin sa, ba tare da yayi magana ba.

Inna na shiga ɗakin ta samu RAUDA tsaye tana gyara gadon, ita kuma Momy tana tsaye tana zagin Sharifa kan shiga harkar Indo da takeyi, mari Inna ta ɗauke RAUDA dashi ta ce.

" Kema nan ɗin gidan ubanki ne, da har zaki mallaki gado, iye! Samun waje kiran sallah da usur, ki ji min yarinya da ina miki kallon mai hankali ashe kema tantiriyar shegiya ce, to bari na sanarda ku, har ita uwar taku dake tsaye, ko wannan 👉🏻 tayi nuni da sharifa, ba ta isa tayiwa Indo gadara cikin gidan nan ba, duk abun da take so cikin gidan nan sai tayi shi, haura gado ki kwanta, Indo daga yau wannan gadon ya zama mallakar ki, na ga shegen da zai hanaki kwana a kansa."

Dariya ce ta ƙwacewa Mustafa dake tsaye bakin ƙofar shi abun da ya basa dariya yanda Inna ta ɗauke RAUDA da mari, ta riƙe kumatunta sai zubar da ƙwalla take, a zuciyarsa cewa yayi ( Allah yasa tayi zuciya gobe ta koma gidan su, maganin mutumin da ba zai zauna inda Allah ya ajiye sa ba, sai ya ƙetaro iyakar wasu, wannan daidai kikayi Inna) juyawa yayi, yayi shegewar sa, cikin ɗakin sa.

Indo kuwa hayewa tayi ta kwanta abunta tana dariya ƙasa-ƙasa, ƙwafa Momy tayi ta cewa RAUDA.

" Ki hau gadon Sharifa ku kwanta, gobe zansa a kawo wani gadon, kiyi hkr."

Taɓe bakin Inna tayi ta ce.

" Oho dai, wannan gadon kam na Indo ce, Amanar Allah, kuma ki shige kiyi ɗakin ki, karma na kauce ki samin yarinya a gaba.

Shigewa Momy tayi, ta fice, itama Inna ficewa tayi, RAUDA kuwa gadon Sharifa ta kwanta cikin ƙunar rai da tsanar Indo, Sharifa kuwa tsabar haushin su, duka mussaman RAUDA, domin kuwa ita ce ta jawo wannan masifar da tun farko ta bi shawarar ta, sun kwanta tare ba ta je ta kira Momy ba, ai da duk bata kai ga haka ba, tollet ta shige tayi wanka sannan tazo ta kwanta cikin kayan Bacci ba tare da ta kalli ko ɗaya daga cikin su ba.

Washe gari da wuri RAUDA da sharifa suka tashi, tare da tashin Indo suka fara aikin gida tare, kasancewar ita Indo ba ta da ƙiwiyar aiki, ita ce ta musu wanke wanke, su kuma suka ɗaura breakfast, Indo da RAUDA kuwa suna haɗa ido sai hararar juna, san da suka gama aiki sannan suka koma ɗaki, jan hanun Indo Sharifa tayi har toilet ta miƙa mata brush ta ce goge kamar yadda kikayi jiya, tsayawa tayi kanta har ta gama, sannan ta fito ta bata waje domin tayi wanka.
Bayan Indo tayi wankan ne ta fito kamar jiya ta shirya, Sharifa rasa wani kaya zata bawa Indo tayi kasancewar ta fi Indo ƙiba, ba lallai bane kayan ta, yayiwa Indo, wata doguwar riga ta ƙara bata ta saka, sun ɗan mata yawa kaɗan haka tasa su.
Haka dukkan su suka shirya suka fito daining, kowa ya haɗu a daining ɗin har Inna, gaishe su sukayi, sanda Indo take gaishe da Momy daƙyar ta amsa tana kumbure-kumbure.
Bayan sun gama breakfast ɗinne Daddy ya dubi Mustafa ya ce.

" Habeeb ya kiran a waya yace zai taso, 6:00am but ka ga kenan zai iso before 12 dan idan ka fita office zaka je ka ɗauko sa, sannan kuma munyi magana da principal na matrix acadamy, akan karatun Indo, mun gama magana dashi cewa, Indo zata Zauna a ss1 tunda acan garin nasu tana js2 ne, yace zai bamu amma ya ce dole sai an mata enterview idan taci sannan hakan za ta kasance, so za ku tafi tare da ita."

Da to Mustafa ya amsawa Daddy ba tare daya masa musu ba, duk da ransa bai so ba.

Sharifa kuwa karɓar kuɗi tayi a hanun Daddy ta ce zata kasuwa ta sayowa Indo kaya.

Himar Sharifa ta bawa Indo, ta fito tana tura baki ta bi bayan Mustafa.
Gaba Indo ta shiga Mustafa ya ja da ƙarfi ba tare daya kalleta ba, suka ɗauki titi, sunyi nisa sosai ba tare da kowa ya kula ɗan uwansa ba, parking Mustafa yayi a gefen hanya tare da ficewa yana waya ya shiga, wani shago, Indo kuwa kalle-kallenta kawai take, karaf idonta ya hango mai baro cike da *KARKASHI* buɗewa tayi ta fice da gudu tayi wajen mai karkashin, tsayawa tayi ta ce.

" Sannu mai KARKASHI"

" Yauwa sannu yarinya"

" Baba dan Allah taimaka ka bani karkashin nan guda biyu dan Allah badan halina ba."

Murmurshi mai karkashin yayi tare da bata, ya samata cikin leda, godiya ta masa ta ruga da gudu ta koma cikin motar tana dariya, Mustafa ya ɗan juma cikin shagon kafin ya fito suka tafi, ba tare daya lura da wani leda hanun Indo ba.

Alhamdulillah cikin ikon Allah suka yiwa Enterview kuma alhamdulillah ta samu ta haye, saboda Indo ko a ƙauye bata ƙin karatu Kuma tana da lura da fahimta, muddun kuma ba ta gane abu ba sai ta tambaya, gida ya dawo da ita ya sauƙe ta sannan ya wuce ɗauko Habeeb yana mitar yau an kashe masa times ɗin aikinsa.

A nutse yake sauƙowa daga jirgin cikin nutsuwa fuskarsa kuma ɗauke da murmurshi, har ya karasa sauƙowa, da sauri Mustafa ya karasa ya rungume ɗan uwan nasa, suna dariya, cikin.

" Your Welcome my Bros"
Cewar Mustafa.

Habeeb yana murmurshi yace.

" Welcome bros ya aiki."

" Aiki alhamdulillah bros."

Jerawa sukayi suna hira har cikin mota, suna taɗin su cikin farin ciki, a harabar gidan Mustafa ya sauƙe Habeeb yana cewa.

" Sorry bros, bazan samu ƙarasawa cikin gida ba, akwai wani case ɗin da zan karɓa ne, so munyi agriment da mutumin zamu haɗa yanxu, jibi zamu shiga kotu, so ina so naje ƙara bincike sosai."

Murmurshi Habeeb yayi tare da cewa.

" Karka damu bros Allah ya dawo da kai lafiya ya kuma bada Sa'a."

Murmurshi Mustafa yayi tare da cewa "ameen" sannan yaja motar sa ya fice shi kuma Habeeb yaja postal dinsa zuwa cikin gidan, babu kowa cikin falon sai Indo ita kaɗai ta zubawa tibi ido sai dariya take ita ɗaya kamar suncacciya, kasancewar RAUDA ta tafi makaranta, ita kuma Sharifa ta tafi kasuwa, sayowa Indo kaya, sallama Habeeb yayi yana murmurshi, da gudu Indo ta tashi tana "Oyoyo ya Habibu"

Dariya Habeeb keyi, yace.

"Oyoyo Mamana, ke ɗaya ce cikin gidan?"

" A'a Inna da Momy suna ɗakinsu, Daddy ya fita ita Kuma Sharifa taje kasuwa siyomin kayan ƴan gayu"

Dariya Habeeb yayi sosai yace.

" Eyye kice zamu sha kallon gayu cikin gidan nan, gaki kuma ƴar cas-cas dake gwanin ban sha'awa, amma fa zakiyi kyau har ki gaji."

Dariya Indo tayi tana fari da ido tace.

" ai ya Habibu sai nafi kowa kyau cikin gidan nan, wankan safe daban na rana daban, ya Habibu nayi kyau har saina gaji"

Dariya sosai Habeeb yayi yace.

" Kinga Mamana bari naje nayi wanka tukunna na fito, dan zancen mu bazai ƙare ba"

Sama ya haura yana murmurshi ɗakin Momy ya shiga tare da Sallama, amsawa Momy tayi tana zaune bakin gado ta haɗe rai fuskar ta a haɗe, cikin sauri Habeeb ya ƙarasa yana cewa.

" Momy lafiya meya same ki?"

Kallon Habeeb Momy tayi tace.

" Ka iso kenan?"

" Eh Momy na iso Please Momy meya sameki?"

Ajiyar zuciya Momy ta sauƙe tace.

" Hmm! Habeeb yarinyar nan ce, bana son ganin ta, cikin gidan nan, na tsane ta, na tsane ta, gashi kuma Alhaji yace dole saita zauna cikin gidan nan"

Cikin rashin gane inda zancen Momy ya dosa Habeeb yace.

" Momy wacce yarinya ne, kike faɗa, wacce har zata takura ki haka?"

" Wannan yarinyar mana Indo wacce mahaifinku ya taho da ita nan, daga zuwa ta'aziya aka haɗomu da masifa"

Cikin zaro ido da tsantsar mamakin Momy Habeeb yace.

" What! Momy Indon ce masifar, ƴar mutum ce, Momy kamata yayi ki nema mata shiriya wajen Ubangiji, ki kuma taya iyayen ta, gyarata, bawai ki dinga, faɗar magana marassa kyau a kanta ba, Momy yanxu Indo ce, zata zame miki matsala cikin gidan nan, duk yaran dake cikin gidan nan basu zamo matsala gare ki ba, sai ita, Momy shifa ɗa na kowa ne, baka san wanda zai taimake ka ba gaba, Please Momy dan Allah karkiyi............"

Cikin tsawa Momy ta katse Habeeb ta hanyar cewa........


Wlh typing wahala.

Please dan Allah karku manta ku sani cikin Addu'ar ku🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻

*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*


*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*


*(Ummu Nasmah ce)*
[2/12, 2:34 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*



👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻


*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*


*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.


*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*TALLAH TALLAH TALLAH*

Ina kuke makaranta littattafan Hausa to ku matso kusa ga dama ta samu, domin kuwa na sake kintsawa da shirin tsaf domin sake gabatar muku da sabbin Novel's ɗina

Please Login or Register in order to submit comment